Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul★ Gold
Book Page

Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel

Author: Bilyn Abdul★ Gold
Paragraphs: 1366
Starting position: 1
Reading position: 1 / 1366
Listen Mode
Login and upgrade to premium to unlock listening.
Reader Top
Ad slot ready: reader_top

[6/9, 6:34 PM] iyammaimuna: Bismillah rahmanir rahim. Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai wanda cikin ikonsa, yardarsa, amincewarsa tare da tagomashin aron rai da numfashi da ya ba ni na rubuta wannan littafin mai suna DAFIN HARSHE bayan kammala littafin KE CE MADADI, wanda har yanzu ana dillancinsa a kasuwar online. Ina rokon Allah da ya tsare mini hannayena daga rubuta abin da zai zama ɓarna ko cutarwa ga al'ummar musulmai tare da tarbiyyansu da kuma al'ada. Ga mai buƙatar litattafaina *MATAN AREWA *SALON ƘADDARATA *UWATA CE SANADI *ƁOYAYYAR MANUFA *KE CE MADADI Zai iya samun su kai tsaye a wajena ko kuma ya tuntunɓi wannan layin 07038908713, ba kya bi na ba shi rantsuwa duk wanda ya karanta tabbas ba zai yi dana sanin sayan guda daga cikin su ba.

Page 0️⃣1️⃣

Kamar ko wacce safiya yau ma ba ta sauya zanin ba, kururuwa da ihun ƙiran da Ummata take doka mini shi ya farkar da ni daga baccin da ya sace ni, bayan iddar da sallan asubahi. A firgice na tashi Ina rarumar kallabina na saka na bayyano waje. Inda da yawa daga cikin mutanen gidan sun tashi sun fara aikace-aikacen gabansu a ƙofar ɗakunansu. Kasancewar gidan haya ne da ba mu da wadataccen fili sai yawan ɗakun da take ɗauke da su guda goma reras, hakan ya sa mutanen unguwar suke yi masa laƙani da gidan yawa wasu kuma su ce gida goma.

"Za ki iso ki ɗauka tallan kunun nan ko kuma sai na zo na saɓa miki? Oh! Hafsatu ina ganin takaicin rayuwa. Ya tabbata in ban kai zuciya nisa ba baƙin cikinki ke da ubanki sai ya kai ni ƙasa".

Zantukan Umma kenan da suka yi nasarar dawo da ni duniyar zahiri daga kogin tunanin da na dulmiya, na yi ƙasa da kaina ina sauraron zancen da ta ɗaura da shi. Wanda tun suna yi mini ciwo har sun zame mini jiki duk nusar da ita da Abba yake kamar yana zuba ruwa ne a bayan ƙwarya. "Umma yanzu fa garin ya waye. Kuma ba sayan kunun nan suke yi ba da safe". Ta yi hanzari katse ni tana nuni da ƴar manuniyar ƴatsarta. "Kunun ne aka daina shan sa ko kuma mene ne? Ai kuwa da safe ake cinikin kunu tun da ga masu fita aiki nan suna shiri".

Ta ƙare zancen tana yi mini nuni da ido zuwa ga Baban Adnan da yake saka takalmarsa sau ciki cikin shigar jami'an ƴan sanda. Matarsa da take tsaye kusa da shi ta bankowa Umma harara babu wata-wata ita ma ta rama kafin ta juyo kaina a zafafe. "Za ki zo ki ɗauka ko sai ya huce? Ƴar iska mai baƙin hali irin na Ubanta". Tana kai wa aya Abba yana sako kan sa cikin gidan muka yi ido huɗu da shi kafin ya sadda kaina ƙasa.

"Mu je ciki mu yi magana Hafsa". Abba ya furta cikin sanyin amon, don mutum ne marar son hayaniya, uwa uba yana son sirri duk dambarwar da za a yi zai yi wuya ya tattauna da Umma akan abin da ya shafe mu a filin gidan.

"Daga zuwanka ba za ka kafa min ƙahon zuƙa ba. In naje cikin uwar me ye zan yi maka? Kai ba yaro na goye ba balle ka ce ina mun shiga shayar da kai zan yi".

Da hanzari na ɗauko kaina na kafe Umma da idanuna da suka kawo ruwan ƙwalla. Shewar da Maman Adnan ta saka game da tafa hannu ya yi daidai lokacin da hawayen da suka wadaci kurmin idanuna kwaranya a bisa dandamalin fuskana. Takaici ya zo mini a wuya wanda ina da tabbacin shi ne ya tunzura zuciyar Abba har ya soma cewa. "Wani irin magana ne wannan haka Hafsa? Ko za ki furta min wannan furucin zai ki yi a nan".

"Mtschew! Ka ji da shi yanzu kam kanka ake ji, wai mahaukaci ya faÉ—a rijiya ya ce ni wanka na nake yi. Ki zo ki É—auka kunun nan shegiya mai zubin munafukai".

"Babu inda za je shin sau nawa zan ce da ke ba na son wannan tallan da kike ɗaura wa Amatullah?". Ba ta amsa masa da baki ba illa tsakin da ta buga tana wurga masa harara tare da yatsina fuska tamkar ta yi tozali da ɗanyen kashi sakin yanzu. Na jayo ƙafafuna da ƙyar na zo na ɗauki gammo na naɗa na ɗaura a kaina ina kici-kicin ɗaura bokatin kunun a kaina. Baban Adnan ya zo wuce wa har ƙasa Umma ta durƙasa tana gaishe shi tare da yi masa addu'ar a dawo lafiya, kalamanta na ƙarshe su suka fi komai shayar da ni ruwan mamaki.

"Allah ya yi wa Adnan albarka, ya raya shi bisa turban addini. Al'umma su yi alfahari da shi". Daɗin addu'ar ya sanya Baban Adnan washe baki yana amsa da amin wani na bin wata. Sai da Maman Adnan ta fizgi hannun rigarsa ta ja shi waje kana ya rufe bakinsa. Babu kunya Umma ta miƙe ta kakkaɓe jikinta ta yi ciki Abba ya ce na dakata daga fita tallan ya rufa mata baya ina daga tsaye ina jiyo abin da suke tattaunawa.

"Hafsatu ki ba ni hankalinki mu yi magana na fahimta ba na jin daÉ—in abin da kike yi min a cikin gidan nan, musamman wannan tallan da kike É—aura wa Amatullah. Ba mu rasa abin sawa a bakin salati to mene ne na tada hankali?".

Ta ya wata doguwar tsaki kafin ta zarce da cewa"Cimar gidanka da kullum babu canji, buhun masara ce in ka jingine ta sai kuma ta ƙare a kawo wata ina shi ne alfaharinka?. Da an yi magana ka ce ba mu rasa ci ba ba mu rasa sha ba. Dole na nema kuɗi kuma wajibi ne na ɗaura wa Amatullah talla". "Yanzu abin da kika yi kin kyauta kenan? Kin kasa sawa ƴarki ta cikinki albarka balle ki yi mata fatan gama wa da duniya lafiya amma ki na yi wa ɗan wasu. Kullum cikin jifan ta kike yi da munanan furuci, Hafsatu ke uwa ce bakinki yana da tasiri akan Amatullah shi yasa nake tsoron ranar da DAFIN HARSHEnki zai kama ta". Cikin ɗaga sauti na ji ta mayar masa da martani kamar za ts rufe sa da duka.

"Dole kuma aka ce idan zan sa mata albarka sai na yi a fili kowa ya gani? Ka san adadin abubuwan da nake roƙa mata a cikin sujjadana?". Daga nan ban ƙara jin muryar Abba ba sai ganin Umma na yi ta fito daga ɗakin kamar an jefo ta na zabura na matsa gefe. "Don ɗiban albarka har yanzu kina tsaye ba ki tafi ba? Allah na gode maka ni kam. Kowa yana haihuwa don ya huta amma ni kam ko kusa ko alama, tsinanniya mai baƙin hali". Ta ƙare zancen tana suran murfin tukunya da nufin wurga mini, babu shiri na fice ƙafafuna suna harɗewa cikin ɗaurin zanina. A ƙofar gidan na iske raguwar mazajen gidan zaune akan taburma suna zaman sa ido, kaina a ƙasa na wuce ta gabansu sai dai hakan bai hana jikina ba ni tabbacin cewa idanunsu yana kaina ba har na fice daga layin. Na nema wani waje na zauna tare da zabga tagumi na faɗa cikin duniyar tunani na yi nutso sosai da har ya hana ni jin sallamar da matashin saurayin da yake bisa kekensa yake yi, sai da ya tafa hannayensa kana na dawo daga karatun wasiƙan jakin da na faɗa.

"Na nawa kake so?".

Na jefa masa tambayar ina ciki-cikin É—auro robar da zan zuba masa. Amsar da ya ba ni ya dakatar da ni daga abin da nake yi, na cira kai ina bin sa da wani irin kallo.

"Mai kunun nake so".

Kallon da na tsare shi da shi ya sanya sa É—age mini ido guda yana ci gaba da cewa. "Ayi min farashi ko nawa ne zan biya. Don kyawunki ya kai a kashe ko nawa ne".

"Dalla! Malam ba na son maganar banza, idan za ka saye ka faɗin na nawa kake buƙata. In kuma ba saya zaka yi ba ka ba wa masu saya waje". Kallon da yake bina da shi yana lashe baki kamar tsohun maye ya ƙara ƙular da ni na doka tsaki ina ci gaba da zancen.

"Malam ka matsa mini daga ka, kana wani lashe baki kamar maye".

"Ke kar ki yi min rashin kunya don kawai na yaba ki".

Na taɓe baki kafin na ce"idan sarki bai ji kunyar hawa jaki ba ai kuwa jaki ba zai ji kunyar jefar da shi ba". Ya sauƙo daga kan keke ya nufo ni gadan-gadan yana zazzare idanu, nima na miƙe tsam na kamfato kunun na watsa masa a fuska. Kafin ya yi wani yunƙuri na tattari kayana na saɓa hanya.

Sai da na yi nisa na fice daga layi gabaɗaya kana na waiwaya na sauƙe ajiyar zuciya. Ganin ba ya bibiyata gida cikin faɗuwar gaba izuwa yanzu mazan da suke zama a ƙofar gidan duk sun watse kowa ya tafi harkokinsa. Kamar ƙadangaruwar bayan murhu kana na shigo ciki ina raɓe-raɓe iwa munafuka. Na yi kiciɓus da Ummi a zaure tana zance da wani mayatatcen saurayinta da inda ya zo tun safe har yammaci bai kula ta na sa kai na yi wucewa ta.

Na dire bokitin a ƙofar ɗakinmu yayin da duk ragowar matan da suke waje suka kafe ni da na mujiya. Na tsinkayo amon Umma daga bayana na waiga tana riƙe da buta ta fito daga banɗaki ta washe baki kamar gonar auduga. "Ba shakka! Tsuntsu daga sama gashashshe. Amatullah har kin sayar da kunun kenan?".

Ba ta jira amsar da zan ba ta ba ta ajiye butar da ke hannunta ta nufo inda na ajiye bokiti, turus ta tsaya ganin kunun shaƙe taf a cikin bokitin. "Me nake gani haka?Wani irin ɗanyen aiki haka kika jiƙa min Amatullah? Don tsabar mugunta da baƙin hali yanda na ɗaura miki haka kika dawo min da shi, shegiya ƴar iska wacce ba ta gaji abin azurki ba".

Tana rufe bakinta ta jayo ni ta rufe ni da duka kamar ba za ta bar ni da rai ba, matan gidan duk suna tsatstsaye suna kallo amma cikin su aka rasa samun wacce za ta kawo mini ɗauki. Tun ina ihu da kururuwar neman taimako har na gaza samun ƙarfin yin hakan, Anty Maryam ce kaɗai ta kawo mini agaji da ƙyar ta ƙwace ni daga riƙon da Umma ta yi mini tana tambayar ba'asi, Umma ta daka mata tsawa.

"Ki kauce ki ba ni waje kafin ke ma na haɗa da ke. Ki ba ni waje na lillisa wannan ƴar iskan yarinya mai baƙar zuciya. Kowa yana abin kansa amma ban da ni, kunun dubu biyu kacal ki kasa sayarwa ban da lalaci da mutuwar zuciya". Umma ta yi bayanin tana ƙoƙarin kai mini mari na kauce, Anty Maryam ta mai da ni bayanta.

"Haba ke kuwa Maman Amatu ki yi haƙuri mana ki fara sauraran dalilin da ya sa ta dawo kafin ki yanke hukunci. Sannan kin ga wannan furucin da kike yi mata sam bai dace ba a matsayin na uwa. Yau idan ta zama ƴar iskan sai kin fi kowa shiga damuwa".

Kafin ta kai aya Umma ta dakatar da ita"kin ga Malama ba zamanki nake yi balle ki zaunar da ni kina faɗa min abin da zan yi ko wanda zan bari. Kuɗin haya mijinki yake biya ni ma haka mijina yake biya don haka babu abin da za ki nuna min. Ki ji da abin da yake gaban ki, ban da lalacewar zamani da samun wuri wai har wacce ba ta taɓa haihuwa ba ce za ta faɗin yadda za a yi tarbiyan ƴaƴa". Cikin tushewar numfashi Anty Maryam ta ce"Allah ya ba ki haƙuri, ga Amatullah idan kin ga dama ki ɗauko wuƙa ki daddatsa namanta ki zuba a tukunya, ki sulala".

Tana gama maganar ta bar wajen ya koma É—akinta. Umma ta hau bambami kamar za ta yi aron baki. [6/11, 11:58 AM] iyammaimuna: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_________________________________________

Page 0️⃣2️⃣

Ina tsaye a wajen hawaye suna wanke mini fuskata tsabar laushin da jikina ya yi mini na gaza motsa ko da ƴatsun hannuna. Sallamar Baban Adnan shi ya dakatar da Umma daga feshin masifar da ta yunƙura za ta furzo mini. Cikin rawar jiki ta zube har ƙasa tana yi masa sannu da zuwa. Fuskarsa a washe yake amsawa kafin ya tambayi dalilin ganin mu cirko-cirko da ya yi Umma ta kwashe komai ta labarta masa.

"Na wane kuÉ—in kunun gabaÉ—aya? Sai na ba ki kuÉ—in gudun kar ayi asararsa".

"A'a Baban Adnan ayi haka? Ai kawai ka bar ni da ita tun da ita ƴar duniya ce zan nuna mata na dame ta na shanye". Ya yi saurin taran numfashinta"A'a ai ba za a yi haka ba". Yana dasa aya ya zaro wasu kuɗi daga aljihun uniform ɗinsa ba tare da ya irga ba ya miƙa wa Umma yana faɗin"ga wannan na san zai isa".

Bakinta har kunne ta miƙa hannu za ta karɓa sai dai kafin ta kai ga yin hakan aka fizge kuɗin. Duk muka ɗaga kai muna duban Maman Adnan da ta faɗo cikin gidan kamar an cillo ta ko kallabi babu a kanta balle hijabi, rabin kanta a kitse rabi a tsefe. Asabe da take bayanta tana zarrare idanu ya tabbatar mini da hashashen zuciya na cewar ita ta bi Maman Adnan har gidan kitso ta shaida mata abin da yake faruwa kasancewar gidan kitso muna kusa da shi.

"Me nake gani haka Ibrahim? Yaushe ka dawo gidan? Sannan wannan kuɗin mene ne kake ba wa wannan matar?". Sai da ya ƙare mata kallon tsaf kafin ya ba ta amsar da ta ƙara tunzura ta ta cika ta yi fam tamkar kwaɓin fanken da ya ji yis rana ta buge shi ya tashi ya yi fum. "Kunun da ta yi ne na saye gudun kar a yi asararsa".

"Me ye haÉ—inka da ita ta balle kunun da take sayar wa? Ko kuma kai kaÉ—ai ne ka san zafin asara da kake gudun ta yi sa? Idan sau gudu É—ari za ta dama kunun ya yi kwante sai me ye Ibrahim".

Ya tsoka mata tsawar da ta tilasta mata yin shuru ba tare da ta gama furzar da takaicin da ya ƙunsa mata ba. "Ke Safina! Me ye haka za ki tara min mutane kamar wanda ya yi sata. Ko wani aikin ashsha kika ga muna aikatawa da ita iya tijarar da za ki yi min kenan".

"Ai da wannan munafurcin gwara ma ku aikata komai".

Bai yi wata-wata ba ya ɗauke ta da marin da ya ba da sauti mai ƙarfi ya nuna ta da ƴar manuniyar ƴatsarsa. Sai dai bakinsa ya gaza cewa komai illa rawar da jikinsa yake yi. Ya fizgo hannunta ya ja ƙofar ɗakinsu sai da ya sa makulli ya buɗe kana ya wurga ta ciki ya rufa mata baya ya turo ƙofar. Ihu da kururuwarta ya cika wa kowa kunne jibgarta yake yi da dukan ƙarfinsa kamar ya sama baiwa ko kuma jaka, Adnan ya zo ƙofar ɗakin yana bubbugawa yana kuka. Kamar gidan babu kowa babu wanda ya yi yunƙurin taimakawa Maman Adnan kowacce mata ta gama harkan gabanta, ga wanda ihun ya dame su kuwa suka ja hijabi suka fice wasu suka shige ɗakunan su.

Tausayin Adnan ya kama zuciyata na ja ƙafafuna da ƙyar na nufi wajensa kafin na ƙarisa Umma ta dakatar da ni cikin kakkauran amo. "In kika ɗaga ƙafarki guda kika isa wajen yaron nan sai na saɓa miki kamamnin. Munafuka mai baƙin hali sai an yi magana ki yi fiƙi-fiƙi da ido kamar shege a rabon gado".

Simi-simi na juyo zan shige ɗaki kalamanta a karo na biyu suka sanya ni yin mutuwar tsaye. "Ina kuma kike ƙoƙarin shiga? Wannan kunun da kika bar ni da shi gidan uban waye zan kai shi?. Ai wallahi tun da na dama kunun nan sai ki sayar da shi kin kawo min kuɗina cas babu gara bin zago". Hawaye suka ciko mini kurmin idanuna muryarta a dushashe na soma cewa"Umma na ga yanzu Baban Adnan ya saye gabaɗaya kuma ya ba ki abin da ma ya fi karfin kuɗin kunu...". Hararar da ta watsa mini ya tursasa mini haɗiye raguwar kalaman ba tare da na furta su ba.

"Maman Amatu halin nan yana burge ni. Wani lokacin har mamaki nake yi anya ba ki haɗa jini da yarabawa ba kuwa? Don son kuɗina kin dama ni kin shaye". Furucin da Sahura ta yi kenan da ya sanya Maman Ebuka ɗago labulen ɗakinta tare da yaɓa wa Sahura magana. "Ko wani ƙabila suna da son kuɗin ba sai yarabawa ba. Ko hausa ma akwai mutanen da suka fi ku son kuɗi, ku da har mutum kuna iya yankawa akan kuɗi".

"A'a Allah ya ba ki haƙuri ba ni na kar zomon ba rataya aka ba ni". Sahura ta furta tana wurga mata harara a faƙaice, ba ta ce komai ba ta saki labulen ta koma ɗakinta. Sallamar Amira ɗiyar Sahura da take fita tallan waina da miya ya dakatar da Umma daga zancen da ta yunƙura za ta furta. Tsam! Sahura ta miƙe tamkar wacce aka yi alluran doki ta sauƙar wa Amira kulan dake kanta, ta ja mata kujera ta zauna kafin ta ce"ya na ga yau kin dawo da wuri? Ko dai dawa ce ta yi nama?".

"Mama ai na gaya miki ko wainar dubu É—ari kika yi min sai na sayar ta ita cas. Ina fita ko awa guda ban yi ba na sayar, daman mun haÉ—u da Bilyamin ne shi yasa amma da tun É—azu na dawo".

Guɗa Sahura ta rangaɗa yayin da Amira ta sinco kuɗi daga gefen zaninta ta miƙa mata. Ta karɓa tana riƙa su ƴan dubu-dubu da su. Tsabar murna rawa ce kawai ba ta daka ba amma ta rumgume Amira da ci mata albarka ya fi a irga.

"Allah kai ne abin godiya daman an ce da haihuwar gwamna gwara haihuwar matarsa. Duk da Allah bai azurta ni da haihuwar É—a namiji ba ya ba ni mace mai kamar maza wacce za ta huce min takaici ta share min hawaye. Ni kam na yi farar haihuwa ko yanzu kasuwa ta watse É—an koli ya ci riba".

Sake da baki Umma take bin Sahura da ido kuÉ—in da Amira ta kawo kuwa cas sai da ta irga su, duk kusan tare suka irga da Sahura. Kamar kububuwa ta juyo kaina. "Dan ubanki za ki É—auki kunun nan ki tafi ko sai na lahanta ki? Shegiya Æ´ar iska mai mataccen zuciya. Kowa yana abun kansa amma ban da ni, ni kam na haiho ruwan dafa kaina gantafalalla É—an kurciya da gashin baki".

Babu shiri ya suri bokitin na ɗaura a kaina har ina ƙoƙarin cin karo da Baban Adnan da ya fito fu ya fice daga gidan kamar iska. Har yanzun Ummi da saurayinta suna zaune a zaure ina jin ta tana tambayata lafiya na fito ina kuka ko kanzil ban ce da ita ba sai tsaki da na ja saboda mau kallon da Saurayin natan yake bi na da shi na yi ficewa ta. Tun da na fito daga gida na rasa takamanmen inda zan nufa a saye kunun haka na yi gararamba a titi daga ƙarshe da na gaji na nema gefen hanya na zauna na tisa bokatin kunun a gabana na zabga tagumi. Ko dai maganar da Umma take faɗa na cewar ina da matacciyar zuciya gaskiya ce? Tun da gashi tun fitowata daga gida babu wanda ya sayi kunun ko na sule biyar. Sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya ina bin bokitin kunun da kallo har na kai hannuna na taɓa ya yi sanyi ƙalau yanzu kam ina da tabbacin duk wanda ya saya ba zai ji daɗi sha ba.

Sallamar da na yi a tsakiyar kaina ya dawo daga ni duniyar zahiri daga karatu wasiƙar jakin da na faɗa. Na cira kai ina duban matar dake tsaye a gabana tana riƙe da hannun ɗanta da alama daga makaranta ta ɗauko shi don yana cikin cikakken shirgar kayan makaranta har da kulan abinci riƙe a hannunsa. Sai a lokacin na ankara lokaci ya ƙure kuma ina da islamiyya ƙarfe biyu. Kafin ta yi magana ta riga ta.

"Na nawa za a zuba miki?".

Ta kafe ni da ido"ba kunu nake so ba, mai sayar da kwankwan can nake tambaya". Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya kafin na ƙara cewa komai mai sayar da kwankwan ya zo wajen ta juya za ta bi bayan sa bayan ta sanar da shi na adadin kuɗin da take buƙata. Na marairace ina roƙonta tare da yi mata magiya. "Don Allah Hajiya ki saya ko na Naira hamsin ne, wallahi tun safe da na fito ko naira biyar ban yi ba. Ki taimake ni ki yi mini rai". Ta waigo tana duba na kamar ba za ta yi magana ba sai kuma can ta ce"zuba min na ɗari biyar". Ta zaro kuɗin daga jakarta ta miƙa mini, jikina yana rawa na amsa zan zuba mata ta dakatar da ni.

"Ki raba wa waÉ—ancan almajiran".

Na gyaɗa kai ina jeranta mata godiya kamar kyauta ta ba ni kuɗi. Almajiran suka taso su ma suka dinga yi mata godiya. Na zuzzuba musu na zauna zaman jiran su shanye su ba ni kwanon da ludayin. "Ƴan matan me ye sunan ki ne?". Furucin mai sayar da kwankwan ya ratsa kofofin kunnuwana.

"Amatullah".

Na furta a taƙaice da hakan ya ba shi lasisin ci gaba da zuba kamar ƴaƴan magarya. "Kyakkyawan suna sai kuma ya dace da kyakykyawa mai kyawun sura kamar ki. Gaskiya ki godewa Allah". Rai a jagule na cira kai na yi masa kallo guda tare da cewa"kullum cikin gode masa nake yi Malam".

"Ya kamata ki ƙara masa don ba kowacce mace ba ce ta haɗa abubuwan da kika haɗa. Ga kyau ga sura ga kuma cikakken diri". Zumbur na miƙe ina nuna da ƴatsa"Malam ba na son maganar banza, ka ja girmanka in kana son na girmama ka". "Ba Malam nake ba sunana Haruna". Na ja doguwar tsaki ina tattare robina da almajiran suka gama sha na bar wajen zuciyata tana tafasa kamar talgen da ke bisa wuta. Duk da ɓacin ran da nake ciki wani sashin zuciyata yana cike da murna tun da na yi ɗari biyar don a tunanina na yi abun a yana mini har zuciyata tana kwaɗaita mini samun albarka daga bakin Umma abin da tun da na buɗi ido ban taɓa jin ta furta mini ba. A ƙofar zaure na yi kiciɓus da Auwal saurayin Ummi saura ƙiris jikina ya goge shi na yi hanzarin ja da baya .

"A'uzubillahi mini shaiÉ—anir rajim!".

Idanunsa ƙar a kaina ya ce"me ye haka? Kamar wacce ta yi karo da aljani?". Ban ba shi amsa ba na raɓa zan wuce ya sha gabana. "Ka matsa na wuce ba na son Ummi ta zo ta same ni a nan".

"To ta zo mana ai ita ma kanta ta san kin fi ta diri da sura. Amatullah babu lafiyayyan namijin da zai ganki bai ji wani abu a ransa ba". Yanda ya yi zancen yana lumshe idanu shi ya fi komai ba ni tsoro. Ban ƙara firgita ba sai da na ji hannunsa a bisa ƙuguna. Na juye masa kunun a jikinsa na ɗauke sa da mari a kuncinsa. Jikina gabaɗaya yana rawa na kasa cewa komai kamar yadda na gaza motsawa daga wajen. Sautin marin da na yi masa shi ya ja hankulan mutanen gidan suka cika a zauren.

"Amatullah lafiya? Auwal me yake faruwa?". Ummi da zuwan ta kenan ta jefa mana tambayar a haɗe. Na kasa cewa komai don bakina ya ƙi ba ni wannan damar sai Auwal ne ya soma cewa. "Babu abin da ya faru, wai daga ta shigo na ce in ta shiga ciki ta yi min magana da ke ina so na wuce. Shi ne ta fara gaggaya min maganganu da na tsawarta mata ta juye min kunun a jikina". Kowa ya saki salati da sallallami gami da tafa hannu.

Sai a lokacin na sama zarafin magana"Auwal ka ji tsoron Allah. Wallahi Ummi ba haka ba ne ya faru, maganar banza ya tare ni da shi....". Kafin na rufe bakina ta ɗauke ni da wani gigitaccen marin da ya sani ganin baƙin duhu yana gilmawa. Za ta ƙara nuni wani Umma ta iso wajen ta riƙe hannunta. "Kar ki sake ki ƙara yin gangancin marinta. Don wallahi sai kin yi dana sani". Ummi ta fizge hannunta"ai kuwa dole na mare ta har ma da abin da ya ci uwar mari, ko ba ki ga abin da ta yi wa Auwal ba ne?".

"Na gani shi uban waye ya ce ya aike ta ƙiranki? Ko zamansa take yi a cikin gidan da zai aike ba? Yanzu kuke biya kuɗi fa haka muke lalewa mu ma mu biya don haka muna da damar da za mu sakata mu wala a cikin gidan nan. Ke ma mai naman neman magana haka kike so ai, kullum burinki ki hannu cikin tashin hankali. Ƴar iska dantalalliya marar kishin uwarta". Tana dure zancen ta jawo ni kamar za ta fige mini hannu muka shiga ciki, ɗaki ta wurga ni ta hau huce takaicinta a kaina. [6/12, 6:29 PM] iyammaimuna: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

__________________________________

Page 0️⃣3️⃣

Da ƙyar na ƙwaci kaina na koma gefe guda na takure ina ji wani zazzaɓi yana ƙoƙarin rufe ni. "Ni kam ban san ke wacce iriyar yarinya ba ce mai baƙin jinin tsiya. Yarinya kamar ƴar zina ko wacce take da bakin iyaye komai aka yi miki babu alkarba sai ka ce karfa. Kunu abin banza ma ba za ki iya sayar da shi to ina da wani abun na daman, kina gani ganin idonki yadda Amira ta hucewa uwarta Sahura takaici da tallan wainar da take yi a kowacce rana a ƙalla tana yin dubu goma zuwa sha biyar amma ke kamar wacce aka sawa hannu komai aka yi miki babu sa'a. Oh! Ni Hafsatu ina ganin takaicin duniya".

Muryata a raunane na ce"Umma na yi naira ɗari biyar fa". Ta wurga mini watsa uwar harara kafin ta ce"ina ɗari biyar ɗin?". Na soma laluma jikina sai dai wayam babu kuɗi babu alamarsa na yi tsilli-tsilli da idanu iwa kwarton da aka kama a cikin turaka. "Wallahi tallahi billahillazi la iya ha illa huwa Umma na yi naira ɗari biyar sai dai in ya faɗi a zaure". Ba ta ce da ni uffan ba illa kaɗa kanta da ta yi ta juya za ta fice sai da ta kai ƙofar fita kana ta ce"ki yi shirin makaranta". Tana rufe bakinta ta fice ta bar ni da saki sakakken ajiyan zuciya ina ƙara laluma jikina ko zan ga kuɗi.

Har zanina na since amma babu kuɗi babu alamarsa na ƙara tabbatarwa kaina ba ya jikina, na zauna na yi shiru ina faman tunani barkatai. "Za ki fito ki tafi makarantar ko sai na shigo". Na tsinkayo muryar Umma kamar daga sama, zumbur na miƙe ina amsa da faɗin"Umma zan sauya kaya ne".

Kayana na sauya na saka na islamiyya sai da na fito na yi alwala na koma ciki na yi salla kana na ɗauko jakata da sallaya na fito. Umma tana zaune tana ƙula farar aya a leda. "Na fito zan tafi". Ba tare da kalle ni ba ta ce"ki je ɗaki cikin samira ki ɗauki ɗari ki sayi wani abun ki ci, tun da baƙin hali ya hana ki ki sayar da kunun ". Godiya na yi mata na shiga na ɗauko kuɗin na fito sai a lokacin ta ɗaga kai kalle ni. "Ki maida hankali ki yi abin da ya kai ki sannan kuna tashi ki kamo hanyar gida. Ki zo ki kasa min ayar nan a ƙofar gida".

"To in sha Allah". Na amsa da shi yana jin kamar ana yaye nuni wani nauyi daga ƙirjina. Ta inda na sama sauƙi duk zafin Umma da hargaginta gami da son kuɗinta ba ta taɓa gana ni zuwa neman ilmi, a lokuta da yawa ita take kora ni ko da raina baya so. Haka na fice ina zuwa zaure abin da ya faru tsakanina da Auwal ya fara dawo mini sabo a cikin kwanyata sai da na ƙare wa kaina kallon tsaf. Allah ya yi ni mace mai matuƙar diri da kyawun sura wanda ba maza kaɗai ba hatta ƴan uwana mata suna yabon dirin da nake da shi. Duk da ba ni da kyawun fuska amma ina da cikakken zubin diri, shekarata goma sha biyar amma ga wanda bai sani ba zai yi zaton na kai shekaru goma sha tara saboda girman jikin da nake da shi.

Sai da na muka fito sallan asr sannan na sayi awarar ɗari na ci na sha ruwa muka koma aji, ƙarfe biyar daidai na yammaci muka tashi. Muka tsaya tattaunawa batun walimar sauƙar da za mu nan da satikai shida sai da aka tsara komai sannan muka watse. Muka kamo hanyar gida ni da ƙawayena biyu Ammi da Rauda. "Don Allah ku raka ni shagon Abbana na amso cefane". Rauda ta yi zancen cikin kwantar da murna.

"Ni fa Ummata tana jira na na fitar mata da farar ayan da ta yi. Kin ga kuma yanzu lokaci har ya ja". Ta kuma marairace"don Allah ki yi haƙuri mu je ba za mu daɗe ba, kin ga Ammi yanzu za mu rabu da ita ta iso gida". Na jim ina tunani kafin na ce"mu je amma ba za mu daɗe ba". Muka nufin shagon muna tsallake kwalta muka rabu da Ammi ta shige gidansu. Babu daɗewa muka isa shagon muka duƙa muka gaishe shi ya amsa fuskarsa a washe ya ɗauko ledar ya ba ta ta amsa da godiya. Har muka har ƙofar shagon bai daina sa mana albarka ba. Lamarin da ya yi matuƙar burge ƙalbina sai da ta taɓo ni kafin na dawo daga kogin tunanin da na faɗa.

Ta ɗage mini ido guda"tunanin me ye kike yi haka? Ina ta magana kin yi shuru". Na sauƙe ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya mai sauti kafin na sama zarafin cewa" ba zan miki ƙarya ba Rauda rayuwar gidanku yana burge ni, yadda muke mu'amala da iyayenku abin sha'awa. Babu tsangwama balle hantara uwa uba kullum cikin sa muku albarka suke yi da yi muku addu'ar shiriya. Ku kam kun dace". Sai da ta murmusa kafin ta ce da ni"haka kowa yake cewa amma ke ma ai kin dacen mahaifi Amatullah, kowa ya shaida cewar mutumin kirki ne mai ƙoƙarin kiyaye halak da haram. Sannan duk layinku da ke ake kwatance wajen kyawawan ɗabi'u da halayen ƙwarai, ga nutsuwa ga ƙur'ani". Duk mu biyun muka fashe da dariya haka muka ci gaba da tattauna har na iso gida kana muka yi sallama na shiga gida ita kuma ta wuce, layin gabanmu inda za ta iske gidansu.

"Mun rantse da girman zafin Allah ba za ta taɓa saɓuwa ba wai bingida a ruwa. Dole mu ƙwatawa ƴar uwarmu haƙƙinta. Don ba daga sama ta faɗo ba ita ma ƴa ce kamar kowa mai gata da galihu yau sai mun ga abin da ya turewa buzu naɗi".

Kalaman da suka fara sauƙa a ƙofofin kunnuwana kenan yayin da na kutsa kai cikin gidan. Maman Adnan ce tsaye ta sha ɗamara ga kuma wasu jibga-jibgan mata uku masu ƙiran samudawa tsaye a kutsa da ita wanda suka kasance ƴan uwanta ne na jini. Da ƙyar na jan ƙafafuna na ƙariso ƙofar ɗakinmu na rakuɓe jikin Ummata da take zaune tana sauraran rediyo ta yi bakam kamar ba ta san wainar da ake toyawa ba. Na durƙusa kusa da ita ina cewa"Umma wai me yake faruwa ne?".

"Safina ce ta É—ebo Æ´an tashan Æ´an uwantan suka zo cikin nan suke yin tijara. Wai don mijinta ya lakaÉ—a mata É—an banzan duka, yo daman wacce ta mai da kanta jaka kam ai dole ta zama abin jibga a wajen miji a ko yaushe".

Ɗaya daga cikin matan ta yi kukan kura ta yo kan Umma, kallo kawai Umma ta yi mata ta tsaya cak ta kasa gaba balle baya. Na sha jin ana cewa Umma tana kwarjini da cika ido wannan dalilin ya sanya kowa a gidan yake matuƙar shakka da tsoron shiga gonarta ban gama gaskata hakan ba sai yau ɗin nan. Ƙafarta ta ɗaura ɗaya bisa ɗaya tana ƙare musu kallon ɗaɗɗaya"ai ko giwa ta faɗi ta fi ƙarfin kare ya ja ta. Idan ki na ji da rashin kunya da tashanci ne to gidansa kika zo. Da kin ƙariso ai da na nuna miki yadda ake yin wasan".

Maman Adnan ta ɗaura hannu a ka ta fasa ihu tana durƙushewa akan gwiwoyinta"shikenan na shiga uku na lalace wannan matar so take yi ta guntile min igiyoyin aurena. Anti ku taimake so take ta ƙwace min miji, jama'ar gidan nan muna gani kun kasa cewa komai". U Ɗaya daga cikin mata ta ɗago ta tana faɗin"ta yi tsararo ta raba ki da mijinki Safina. Idan taƙamarta sammako da to mu a hanya muka kwana idan ta san wata ai ba ta san wata, sai mun nuna mata faɗa da aljani sai an shirya wallahi kin taɓo tsuliyar dodo". Tana ada aya ta figi hannun Maman Adnan suka wuce ɗakinta raguwar mata biyun suka rufa musu baya. Shewa Umma ta saka har da tafa hannu tana faɗi"ai ni wargi ce daidai ƙugun ko wani ɗan iska, mu zuba mu gani ɗan halak ka fasa".

"Umma don girman Allah ki fita daga harkan mutanen nan ki bar su su zauna lafiya da mijinta..".

Kafin na ƙarisa ta sauƙe mini ƴatsunta biyar a fuskana, a kufule take cewa"ke har me ye kika sani da za ki zaunar da ni kina faɗa min abin da ya dace na yi ko kar na yi. Amatullah ki fita daga idona na rufe daman ina cike da ke ƴar iska mai kunnen ƙashi, ban ce da ke ki dawo da wuri ki fita min da farar ayan nan ƙofar gida ba?". Kaina a sunkuye na ce"mun tsaya tsara yadda walimar sauƙar mu za ta kasance ne". Ba ta ce da ni komai ba kamar yadda ba ta ba ni umarnin tashi ba, haka na ci gaba da tsugunawa akan ƙafafuna don na san idan na tashi ni na san abin da na taro. Sai da aka yi ƙiran sallan magrib kafin na tashi daga wajen na je na yi alwala na shiga ɗaki na yi salla na fito na soma ciki-cikin haɗa wutan dare. Sai da na sha baƙar wahala kafin wutan ya kama na aza sanwa na ɗauko kayan miya na soma yankawa. Ganin mutum tsaye a kaina ya sani hanzari ɗaga kaina ina dafe ƙirjina ganin Ummi ce ya tursasa mini sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya.

"Ummi lafiya? Kika zo kika yi mini tsaye a tsakiyar kaina?".

"Watau har kin manta abin da ya faru ko?". Ta yi ƙwafa kafin ta ɗaura da cewa"ai idan maye ya manta uwar ɗa ba za ta manta ba. Ke har kin mance rashin mutuncin da kika yi wa Auwal ɗazu watau a tunaninki kin ci banza ko?".

"Ni kin ga na har na kanta kimai. Kin ga Ummi ki tsaya mu yi magana ta fahimta wallahi Auwal ƙarya ya faɗa ba abin da ya faru ba kenan, shi ne fa ya tare ni da maganar banza".

Ta doka mini tsawa"dalla! Rufe min baki, ko da Auwal ya kasance É—an iska ai ba kuma kai matsayin da zai tunkare ki da maganar banza ba. Amatullah zan miki gargaÉ—in dab da mari ki fita daga harkan Auwal, don tun ba yau ba ina ankare da ke a duk lokacin da ya zo hira kin ginda shiga da fita kenan kina shawagi a gabansa kina juya manyan mazaunanki don kawai ki ja hankalinsa. To hawainiyarki ta kiyaye rama ta kuma wallahi Auwal dai nan gani nan bari É—umamen maya na gaba ya yi gaba". Sake da baki da hanci nake kallon ta har ta kammala zancen tsabar mamakin da ta ba ni.

"Allah ya ba ku haƙuri ke da shi". Na furta a taƙaice ina mayar da hankalina ga aikin da ke gabana. "Idan ya ba ni ki ƙwace banza shashasha, girman buredi kawai". Ban tanka mata ba har ta ƙarishe tsayiwarta ta gaji ta tafi, tana barin wajen Amira tana isowa ta ja kujera ta zauna.

"Wai me ye take faÉ—a miki ne?".

"GargaÉ—i ta zo ta yi mini akan saurayinta Auwal".

"Cab! Ke kuma kika ce mata me ye?".

"Me ye kuwa zancen da ya wuce na ce ta yi haƙuri".

Ta tafa hannu kafin ta ce"wallahi in ni ce ba ta isa na ba ta haƙuri ba, akan wani saurayinta mai zubin ƴan daudu ga shegen kallon matan tsiya". Ta ɗago kai na yi mata kallo guda kafin na furta"ki rufawa kanki asiri ki yi shuru kafin ta ji ki wani rigimar ya kaure. Kin san ita ba tsohon ta mutu take yi ba balle ta rayu".

Ta tsirtar da tsaki"to sai me ye in ta ji? Ke dai Amatullah Allah ya ƙara miki haƙuri kawai". Taƙaitaccen murmushin gefen baki na yi na amsa da cewa"Amin ya Allah". Mun ɗan taɓa hira kafin ta miƙe tsaye na bi ta da kallo kafin na yi magana ta riga ni.

"Bari na yi shiri fita tallan dare kafin lokaci ya ƙure". "Da kin zauna mun yi hirar mu ke da in kika fita sai mutum ya yi bacci kafin ki dawo". Ta bushe da dariya kana ta ce"dududu ƙarfe nawa nake dawowa Amatullah? Karfe sha ɗaya ne fa zuwa da rabi. Ke dai bari na wuce na san yanzu an gama dafa min awarar a gidan Tasalla". Kasa cewa da ita komai na yi har ta wuce saboda mamakinta da nake yi na rashin tsoro komai dare ba ya hana ta fita talla haka kuma za ta ratso ta dawo gida idan ta gama soya awarar.

Sai da na kammala girkin na kwashe na tattare wajen, na ɗeba nawa na ci a wajen na kai wa Umma na ta kana na ajiye na Abba. Wanka na yi na yo alwala na yi sallan isha'i na ɗauko littattafaina na fito zaure ina nake ƙara wa yara karatu bayan sallan isha'i. [6/14, 11:31 AM] iyammaimuna: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

______________________________________

Page 0️⃣4️⃣

Muna tsaka da karatun Abba ya shigo na miƙe zan karɓa ledar dake hannunsa bayan na yi masa sannu da zuwa. "Zauna ku ci gaba da karatunku". Ya furta fuskarsa washe da annuri, hasken ƙwan fitillan aci bal-bal da na kunna a wajen shi yake ba ni damar kallon fuskarsa har na fahimci yanayin da yake ciki. Ƙarfe tara na sallami yaran kowa ya watse kafin na koma cikin gidan. "Hafsatu na gargaɗe ki da ki fita daga harkan Ibrahim da kuma matarsa amma kin yi kunnen uwar shegu da zantukana. Ki sani kin fara kai ni bango fa, me ye haɗinki da mijin wata bayan kasancewarki matar aure? Da ilminki da komai amma kike takewa wane irin rayuwa ce wannan kika ɗaurawa kanki?. Saboda son zuciyarki da masifar son kuɗi ki ja wa baiwar Allah duka daga wajen mijinki kuma tsabar tsaurin ido irin na ki kika yaɓawa ƴan uwanta magana".

Zantukan Abba kenan da na fara cin karo da shi yayin da na kutsa kai cikin falon. Jikina ya yi sanyi ƙalau kamar kazar da aka jefa da ruwan gishiri, shirib na zauna akan ɗaya daga cikin kujerun da suke cikin ɗan madaidaicin falon na mu da hakan yake ba ni damar sauraron abin da suke tattaunawa daga cikin uwar ɗaka.

"Roƙansa kuɗi na yi ko kuma maula na yi? Da za ka ɗebo tsamin jikinka ka zo kana yi min hayagaga a kaina. Dare ma da ya kasance mahutan Bawa ba za ka taɓa barin mutum ya huta ba".

"Hafsatu ni kike cewa ina yi miki hayagaga?".

"Kai ɗin fa Munniru. Wani irin masifa ce wannan? Kai komai na yi a idanunka ban fita ba. Ka ƙwammace ka goyi bayan matar wani akan ka goyi bayan matarka ta sunna har kake ƙiran ta da baiwar Allah. Duka kuma ba ni na ce ya sake ta ba tashin hankalinta ne ya jaza mata, ƴan uwanta kuma da ta kwaso ba a haifi shegiyar da za ta zo har inda nake ta gaya min magana na ƙyale ta ba. Kuɗi kuwa ko sau dubu sai ɗauka ya ba ni billahillazi sai na amsa ai ba tursasa masa na yi ba shi ya yi niyya, kai ba ka ba ni ba kuma ban ga dalilin da za ka hana ni karɓa ba".

Sai mintuna suka shuɗe kafin Abba ya ce"ki kiyaye harshenki, ki dinga tauna lafazi kafin ki furta shi. Domin da zaran ya fita to ba a iya dawo da shi. Shi yasa Annabinmu da kansa ya ce kuffa alaika haza ma'ana ka kiyaye wannan a gare ka watau harshe, dafinsa ya bi na bakin maciji. Ke komai ya fito daga bakinki za ki yaɓawa mutum ba tare da tunanina ba, Hafsatu ina guje miki ranar da za ki yi dana sani".

"Babu dana sanin da zan yi Munniru, bakinka ya sari guntun gashi".

Ta yi zancen tana banko labulen ɗakin ta fito falo. Kamar wacce aka tsigara wa matsilli haka na zabura na tashi, kallon da ta tsare ni da shi ya sani saurin rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa. "Watau kin na zaune a nan kin kasa kunne kina sauraron abin da muke tattaunawa ko?".

Na girgiza kaina"ban daɗe da shigowa ba ma". Ta doka mini tsawan da ya haifar mini da rawar jiki. "Dalla rufe min baki munafukar banza munafukar wofi. Duk ba ke kika ce ummul abasin faruwar komai ba. Shegiya ƴar iska mai jinin tsiya". Kafin na ce wani abu tunin Abba ya fito falon cikin matsanancin ɓacin ran da ya bayyana ɓaro-ɓaro a bisa kammalalliyar fuskarsa da farin gashi su ka yi masa ƙwawanya a saman harbarsa. Ya nuna ta da ƴar manuniyar ƴatsarsa da hakan yake tabbatar da ya kai ƙololuwan ɓaci rai da faɗa wa cikin tarin takaici.

"Na hane ki da jifan Amatullah da waɗannan munanan kalaman amma kin liƙa wa kunnuwanki gayan tuwo. Shin ashe idan wani ya ce da ita shegiya ko ƴar iska abin ba zai yi miki ciwo ba kenan?. Ke uwa ce ki zama mai tausasa lafazinki akan Amatullah. Ba na son mins sa'in sa dake amma ke kike jan komai".

"Mtscheew".

Umma ta ja dogon tsaki tana yi wa kanta mazauni a kujerar da na tashi daga kanta, jinjina kansa kawai Abba ya yi kafin ya maido da duban sa gare ni yana faÉ—in"Amatullah ki kai min ruwan wanka".

"To Abba".

Na amsa da shi yayin da nake fita daga falon na ɗauki bokiti na cika da ruwa na kai masa bayi. Kana na zo na sanar da shi. A uwar ɗaka muke kwana tare da Umma yayin da shi kuma Abba yake kwana a falo, tun da na yi girma na yi wayo muke yin hakan wannan dalilin ya sa kullum sai na yi addu'an Ubangiji ya buɗa wa Abba ya yi gidan kansa ko da kara ya kewaye mana mu koma. Mu huta da wannan baƙin masifan takuran. Kamar a mafarki haka nake jiyo sautin maganar a tsakiyar kaina na mirgina ina murtsike idanuna tare da buɗe su kana na maida su na lumshe. Duk da haka ban daina jin sautin yana tashi ba dole ƙanwar naƙi na tashi ina yin miƙa daidai lokacin limamin masallacin kusa da gidanmu ya rangaɗa ƙiran sallan assalatun cikin zazzaƙan muryarsa mai sanyi.

Na tashi zan fita falo na jiyo Abba da Umma ne suke magana na koma na zauna, don ba na ƙaunar sauraron abin da suke tattaunawa wanda ina da tabbacin zai iya zama sirrinsu ne wanda bai dace na ji ba. Ina nan zaune Umma ta shigo tana ta bambamin da ban gane takamanmen akan abin da take yi ba, na tashi na fita domin ɗauro alwalan sallan asubahi na tarar da an haɗa wani rigimar a filin tsakar gidan. Maman Rayyan ce take ta surfa masifa Asabe tana taya ta, a nan na tsinci kan zancen wai a daren jiya ne gandaderen ƙato ya shiga har uwar ɗakinta yana shafa jikinta, kasancewar mijinta ba mazauni ba ne ya kan yi watanni biyar zuwa shida ba ya gida. Har hantsi ya fito masifa da bala'in bai lafa ba abu kamar wasa har ya kai gaban mai unguwa da wasu manyan unguwan, ina kwance a ɗaki ina fitan karatun islamiyya Amira ta shigo sai da na kai ayar ƙarshe da nake karantawa na cikin suratul tagabun kafin na rufe ƙur'anin ina duban ta fuskana cike da murmushi.

Kafin na yi magana ta datsi numfashina"karfe goma da rabi na dawo, na san abin da za ki tambaya kenan". Na murmusa kafin na ce"ai ke da kan ki Amira ya kamata ki yi wa kanki faɗa, wannan daren da kike kai wa a waje ba mutuncinki ba ne a matsayinki na ɗiya mace. Ko na miji ne ai duk inda goma zuwa sha ɗaya ta yi daga lokacin ta fara neman hanyar gida balle kuma mace". Ta yatsina fuska kafin ta ce"kin ga ni ba wannan ba ne ya kawo ni. Amshi ki buɗe ki ga". Ta ƙarishe zancen tana ajiye mini wani baƙin leda a bisa cinyata, ta bi ta da kallon mamaki.

"Mene ne a ciki?". Na jefa mata tambayar ina juya ledar a hannuna. "Ke kuwa ki buɗe mana idanunki su gane miki". Kamar yadda ta faɗa hakan na yi na soma ciki-cikin buɗe ledar. Kwalin waya ce sabuwa dal da ita ƴar shafai. Na kwasa ihu ta yi hanzari rufe mini baki da tafukan hannayenta na zame hannunta. "Amira Ina kika sama wannan dalleliyar wayar nan? Ko wani ne ya ba ki ajiye? Ko aka aike ki da shi wani wajen?". Ta saki dariya har da riƙe ciki sai da ta yi mai isharta kafin ta tsagaita gami da faɗin"babu ko ɗaya nawa ce, daren jiya ta zo hannuna". Na watsa mata kallon mamaki da al'ajabi. Cike da son tabbatar mini da sahihancin abin da ta furta ta ɗage mini idonta guda tana zarce wa da cewa"wallahi kin dai ji rantsuwa kenan ko, wayata ce". Na katse ta kafin ta ƙarisa zancen.

"Ina kika sama kuÉ—in sayan wannan wayar Amira? Ita wayar nan ce fa ta cikin shirin film É—in labarina, ta hannun Baban Sumayya. Kuma na san ko riba da jarinki gabaÉ—aya kika haÉ—a ba za su sayi wannan wayar ba". Ta kuma fashewa da dariya kafin ta ce. "Ba ko sisina a cikin kuÉ—in wayan nan Mansur ne ya kawo min ita jiya, tukwuicin amsar tayin soyayyarsa da na yi".

Kamar saƙaho haka na saki baki da hanci ina bin ta da kallo tamkar yau na fara tozali da ita. Sai da na tattaro jarumta na yaɓa wa kaina kafin na iya yin motsin kirki har na iya furta wani abun. "Amira anya kuwa kina da hankali? Haka siddan daga haɗuwa da mutum ya ɗauki wannan wayar ya ba ki kuma ki sa hannu ki amsa". Ta galla mini harara tana fizge wayar daga hannu. "Kin ga Amatullah kar ki ɓata min rai da sanyin safiyar nan, sanin kanki ne a kaf cikin gidan nan da ke kaɗai nake hira har na saki jiki na sanar da ke abubuwan da nake yi". Ganin tana ƙoƙarin ficewa ya sani riƙo hannunta.

"Kar ki ɗauka da zafi mana ke kuwa. Ki yi haƙuri".

"Ke ce ai kike ƙoƙarin ɓata min rai Amatullah". Ta koma mazauninta ta zauna ta murtuƙe fuska. "Haba! Ke kuwa saki fuskar mana ta Mansur". Babu shiri ta ƙyalƙyale da dariya.

Ta gyara zama tana zubo mini bayanai"ban san inda yake ba amma dai a gajerin da nake kai tallar waina muka haɗu da shi ya kawo gyaran motarsa, ya saya waina ya buƙaci lambata na ce da shi ban da waya. A haka kusan kullum sai ya zo gajerin don kawai ta ganni har ya yi min tayin soyyarsa bayan na gara shi shekaran jiya na amince. Daren jiya kuwa ya same ni har ƙofar gida ina soyar awara ya ba ni ita, bayan p yi min juye".

Ƙwala mata ƙiran da mptessghaifiyarta Sahura ta yi mata shi ya hana ni furta zancen da na yunƙuro da nufin yi. Ta tattare kwalin wayar ta miƙe"bari na je na san yanzu Ummata ta kammala wainar, duk sauran ƙarin bayani inna dawo za ki ji shi". Da kallo na raka ta har ta fice na gaza cewa komai saboda giyan mamakin da ta shayar da ni, haka na zauna ina bitar zantukan Amira tare da yi musu tankaɗe da rairaya.

Ƙatuwar ajiyar zuciya na sauƙe ina tallafe kuncina lalle Amira ta kusa ta fi ƙarfina. A kwanakin baya sai da muka daina magana da ita don kawai na gaya mata gaskiya akan irin shigar banzan da take yi in za ta fita talla. Ko da na yi mata magana sai ta kaɗa baki ta ce da ni idan ba ta yi kwalliya waye zai kalle ta balle har ya sayi abin da take sayar wa. Yanzu ga halin biyewa samari da ta tsira.

"To maza malalaciya tashi gari ya waye. Ga kunu can ya kammalu".

Na tsinkayo amon Ummata da ya yi nasarar dawo da ni duniyar zahiri daga karatun wasiƙan jakin da na faɗa.

DAFIN HARSHE

©️ Maimuna Tijjani Iyam _______________________________________

Page 0️⃣5️⃣

Zumbur na miƙe na rarumo hijabina na saka na bayyano waje, tana tsaye a baranda ta cika ta yi him da dukkan alamu ƙiris take jira ta fashe. Na durƙusa a gabanta sai dai tsoron da ya yi mini katutu a cikin ƙalbina ya hana ni furzar da zancen da ya maƙale mini a bakina. "Uban me ye kike jira? Shegiya mai zubin aljanu". Ta doka mini tsawan da ya tilasta mini runtse idanuna ƙirjina yana tsananta bugu. Ta rusunar da kaina ƙasa kafin na soma faɗin"daman tambaya na nawa ne zan yi". Da alama zancen nawa ya yi tasiri wajen ƙara rura wutan da yake huruwa a cikin ƙirjinta, ta yi ƙwafa tsabar takaici. Duk da idanuna suna ƙasa amma a jikina nake jin ni take kallo. "Amatullah kina ƙure ni fa kina tuntsira ni. Ina jiye miki tsoron ranar da zan yi wasan kura da ke a cikin gidan nan. Dan ubanki na dubu ɗaya ne da ɗari biyar, idan kin ga dama ki dawo min da shi yadda na kika fita da shi. Tun da daman ke ba ki gaji abin azurki ba tsinanniya". Babu shiri na ɗago kaina"don Allah Umma ki yi haƙuri in ranki ya ɓaci ki dinga yin shuru. Kullum ana gaya mana a islamiyya cewar ba a son a dinga yi wa ƴaƴa irin waɗannan kalaman".. Kallon da ta tsare ni da shi ya sani yin shuru tare da mayar da kaina ƙasa ƙwalla suna ciko mini kurmin idaniyata. Fahimtar abin da shurunta yake nufi ya sani tashi na naɗa gammo na ɗaura bokitin kunun a kaina, numfashi mai zafi na fesar daga bakina ina ƙarewa layin namun kallo. Don ban ma san inda zan nufa na sayar da wannan kunun ba. Amon muryar Auwal da suka yi wa ƙofofin kunnuwana sauƙan bazata. "Amatullah kenan! Ƴan mata adon gari matar manya, irin ta gaban mota". A tsorace na waigo ina bin sa da kallo cike da son ƙarin haske, kamar ya san abin da yake cikin raina ya ci gaba da magana kansa tsaye ba tare da tsoro ko shayin komai ba. "Allah ya yi miki zubi da tsari uwa uba ga diri kamar ke kika zana kanki, wallahi ba namijin da za ki wulga ta gabansa bai ji wani abu a cikin ransa ba. Ni da sai yanzu ma na fahimci na yi zaɓen tumun dare, sam Ummi ba ita ce kalan matan da nake so ba sai dai ance da babu gwara ba daɗi. Amatullah na yi miki alƙawarin matuƙar kika amshi soyyayata a shirye nake da na yi watsi da Ummi daga cikin zuciyata, daman can ba shiga can ciki ta yi ba". Sakeke na tsaya ina kallonsa raina cike fal da mamakin furucinsa da yadda yake ya wani kanne ido guda ana lashe leɓan bakinsa kamar maye. Na gyara tsayiwata kafin na harhaɗo jarumta har na sama ƙarfin gwiwan iya furta"Auwal babu abun da ya haɗa ni da kai saurayin Ummi ne kai kowa ya shaida hakan, na roƙe ka don girman wanda yake yi mana ruwa da ƙanƙara ka fita daga harkana ko har ka manta abin da ya faru ne? Ba na son na ƙara tsoma kaina cikin wani masifan". Na ƙarisa zancen cikin sigar roƙo da magiya sai da dukkan alamu roƙon nawan bai ɗaɗa sa da ƙasa ba. "Tun ranar da na yi ido huɗu da ke Allah ya ɗaura min sonki a cikin zuciyata, ba yin kaina ba ne ni ma Amatullah. Kuma ina mai ba ki haƙuri akan abun da ya faru, ban yi da wani manufa ba kuma ban yi tunanin lamarin zai yi ƙamari har haka ba, ki yi haƙuri ya ke Sarauniya". Yana rufe bakinsa muka yi ido huɗu da Salmanu ƙanin Ummi ya dawo daga aiken da aka yi masa, ina ganin sa na sha jinin jikina. Don na san na yi shuka ne a idon makarwa tun da ya ganni da Auwal sai ya je ya isarwa Ummi. "Ka ga ni dai babu ruwana. Ina zaman zamana ba za ka ja mini bala'i da masifa ba, ka ga tafiyata". Ina dasa aya a nan na juya na bar ƙofar gidan da sauri har ƙafafuna suna sarƙafewa, sai da na cire daga layin gabaɗaya kana na sauƙe wani wahalallan ajiyar zuciya. Sai da na yi tafiya mai nisa amma ko ciniki naira biyar ban yi ba na nema waje na zauna ina huta gajiyar da na kwaso. Na tallafe kuncina ina bin bokitin kunun da kallo. A ƙalla na yi zaman mintuna ashirin kafin na yi cinikin naira ɗari biyu na kuma yin naira ɗari, har hantsi ya fito ba a ƙara saya ba, hakan ya sa ni tashi na ɗaura a kaina na fara bi gida-gida. Gida guda ne suka saya na hamsin. Cikin fargaba na nufi gida ganin ranar ta fito ta take ta yi ƙwal, da ƙyar nake iya ɗaga ƙafata saboda gajiyar da na yi lis tun daga nisa idanuna suke gano mini wata shirgegiyar mota a fake a ɗan nisa da gidanmu. Na lumshe idona na buɗe don tabbatar da sahihancin abin da suke gano mini. Sai na yi kusa kafin na gane Amira ce da wani tsaye a jikin motar suna fuskantar juna sun ƙurawa junansu idanu kamar za su cinye juna. Kai tsaye zuciyata ta fassara irin kallon da irin kallon da malamin littafin ahalari ya faɗa mana, kallon da addini ya haramta. Gefe guda kayan tallanta ne a kusa da ita. Jikina ya yi sanyi ƙalau ganin har ta sayar da duk tulin wainar da tun fitowa ta alwalan asubahi Sahura take tuyawa. "Amatullah". Ta ƙira sunana yayin da nake gab da shiga cikin gidan, na juyo jikina a sanyaye. Ta yi mini ishara da hannu akan na zo na isa wajen tare da sallama ɗauke a bakina suka amsa na gaishe shi ya amsa yana kallona. "Masoyi ga aminiyata ko ma na ce ma ƴar uwata sunanta Amatullah". Ya jinjina kansa"ma sha Allah, Amatullah sannu". Kafin na amsa Amira ta riga ni faɗin"Amatullah ga Mansur wanda nake ba ki labarinsa". Na ɗago kaina ina satan kallonsa caraf idanunmu suka sarƙafe na yi hanzarin janye nawa kafin na ce"sannu da zuwa, ai kuwa ta na yi mini labarinka. Allah ya wanzar da alkhairi a cikin alaƙarku". "Amin ya Allah". Duk suka haɗe baki wajen amsawa da shi kafin ya ce"ya kuma kika dawo kunun nakin bai ƙare ba?". "Na yi mantuwa ne na zo ɗauka". Na ji bakina ya furta ba tare da ya yi shawara da zuciyata ba. "Amatullah kenan ke dai akwai zurfin ciki. Ba kya son kowa ya san halin da kike ciki". Na wurgawa Amira da ta yi zancen harara kafin na zarce da cewa"kin ga ni ba na son dogon magana. Sai kin shigo, Mansur na bar ku lafiya". Ya washe baki har kunne ya zaro wasu kuɗi daga aljihunsa ya miƙa mini"to ƙawarmu ga wannan a sayi kayan kwalliya". "A'a na gode Allah ya ƙara azurki". Na furta ina juyawa na bar wajen don na gaji da kallon da yake mini, na shige gida daidai sanda ake ƙiran sallan zuhur da Umma muka fara yin kato za ta fita gani na ya sa ta komawa da baya tana ƙare mini tanadin kallo. "Me nake gani haka? Amatullah yaya da haka kuma?". Na sauƙe bokitin daga kaina na miƙa maka cinikin da na yi ina ƙara wa da cewa"Umma an saya fa wallahi, kin ga ma cinikin da na yi". Ta firge kuɗin ta na irga su kafin ta yi magana yaro ya yi sallama ya shigo da kayan tallan wainar Amira Umma ta bi robobin da kallo da ina da tabbacin ganin su wayam babu komai a ciki shi ya fi komai jan hankalinta. Sahura ta fito daga ɗaki tana rangaɗa kuɗa"Allah kai ne abun godiya. Maraba da ke ƴar azurki irin albarka har kin sayar ki dawo". Ta yi furcim sa'ilin da Amira take shigowa tana tafiya ɗaɗɗaya tana taunar cigam da yake ba da sautin ƙas ƙas. "Umma ni ce fa ko kin manta alƙawarin da na yi miki ne? Ai waina ko na dubu hamsin za ki yi min sai na sayar da ita". Ta ƙare zancen tana miƙa mata kuɗin ta irge su a filin tsakar gidan cas ta lale su, lamarin da ya baƙanta ran mutane da yawa ciki har da Ummata da take ta faman ciki tana batsewa. Na tabbatar takaicin da ya zo mata har wuya ya yi mata tsayiwar ƙayan kifi a maƙoshi shi ya hana ta furta ko da baƙi ɗaya illa ƙwafan da ta yi, ta fice daga gidan. Na bi ta da kallo har ta fice kafin na ɗauki bokitin na shiga ɗakinmu na cire hijabina na fito na yi alwala na koma na yi salla nan kan sallayar na zauna don na san yau kam babu batun zuwa na islamiyya tun da Umma ta sa ƙafa ta fice. Ban san lokacin da bacci ya sure ni ba sai da na soma jin ana bubbuga ni tare da ƙiran sunana. Na buɗe idanuna a hankali har suka yi tar akan fuskan Amira da take tsaye a gabana. Da ƙarfi ta miƙar da ni tsaye ta ja ni zuwa cikin uwar ɗakanmu, na fizge hannuna ina murtsike idona. "Wani irin wulaƙanci ne haka Amira? Ina baccina za ki zo ki tashe ni ki wani jawo ni ɗaki". "To jarabu ki yi haƙuri mana taimako za ki yi min". Ban amsa mata ba na ja tsaki na zauna na kafe ta ido. Ledan hannunta ta zazzage akan gadon Umma ta ɗago dogayen riguna biyu. "Ta ya ni zaɓan wanda ya fi kyau da tsaruwa za ki yi a cikin waɗannan. Mansur ne zai zo mu fita shan ice cream". Ta ƙarƙare zancen tana wani lumshe idanunta. Ta kufule na ce"akan wannan shi ne za ki tashe ni ina baccina? To ki saka duk wanda ya yi miki". Na miƙe zan fita ta riƙo hannuna. "Ki tsaya mana haushinki fa nake ji ma in ba ki sani ba, amma duk da haka na zo neman shawaranki". Na ware idanuna akan ta"haushin me ye? To ma me ye na yi miki?" Na ƙwace hannuna daga riƙon da ta yi mini. "Mussamman na zaɓo ki kamar tumu, a yaran gidan nan gabaɗaya ke kaɗai na ba wa damar ganin Mansur amma kika zo kika wani haɗe rai. Har ya yi miki kyauta ki ƙi karɓa don wulaƙanci". "To kuma sai aka ce dole in ya mini kyauta zai na amsa? Na ga dai kar addu'a na yi muku da fatan alheri. To me ye kike so bayan hakan?". "A bar maganar nan, ni dai yanzu ki duba min rigar da zan sa". Na wafce rigunan ina jujjuya su kafin na ce"ki sa wannan shuɗin za ta yi miki kyau sosai". Ta daka tsalle"haka Mansur ma ya ce da ya kawo min su". "Kina nufin shi ya saya miki?". Ta ɗaga mini gira guda"ƙwarai kuwa". Kafin na dawo daga mamakin da na faɗa ta kuma cewa"bari na je na saka na dawo". Ba ta jira abin da zan ce ba ta karɓa rigar ta fice cikin zumuɗi da tsantsan farinciki. Mamaki ya hana ni motsawa daga inda nake har sai da na jiyo sallamar Umma na fito ina yi mata sannu da zuwan da ta yi kunnen uwar shegu da ni. Na ɗauki hijabin da ta cire ina ninkewa na furta"Umma ina kika je kuwa da ranan nan?". Kaman ba za ta amsa ba sai kuma can ta ce da ni"gidan Malam mai laƙanin sa'a na je". Na dakata da abin da nake yi"Umma ke kuwa me ye kika je yi?". "Kukana na kai gidan mutuwa, na je na ƙarbo taimakon buɗewar ƙofar nasara akan sana'ata. Don ina da tabbacin Sahura ma a nan ta karɓo na ta laƙanin".

[7/7, 10:28 AM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

Maimuna Tijjani Iyam

_______________________________________

Page 0️⃣6️⃣

Sakeke na yi ina kallonta kamar doluwa sai da na ja dogon numfashi na fesar daga bakina kafin na sama damar sarrafa harshena da ya cika mini baki ya kuma yi mini nauyin ɗagawa. "Umma wani irin laƙani ke kuwa? Akwai wanda ya isa ya yi abinda Allah bai yi ba ne? Me yasa ba za ki kwantar da hankalinki ba?. Ko ba ki yi sana'ar komai ba ba za mu rasa ci da sha ba haka nan ba za mu tafi tsirara ba, to mene ne na tada hankali har kike ƙoƙarin faɗawa cikin halaka....". Kafin na rufe bakina ta sauƙe mini marin da ya sani ganin gilmawar baƙin dubu a idanuna, na yi tangal-tangal zan faɗi saboda gazawar ƙafafuwa. Sai da na yi sa gaske kafin na iya riƙe kaina na dafe kuncina ruwan ƙwalla suna ciko mini kurmin idaniyata.

"Ke har kina da bakin magana akan wannan matsalar Amatullah? Bayan ke ce matsalata ke ce sila da tushen shiga ta cikin kowani irin damuwa. Me ye amfanin haihuwarki in har ba za ki zage damtse wajen warkar min da raunin da yake cikin zuciyata ba? Me ye amfanin haihuwarki in har ba za ki kashe wutar da take ƙoƙarin ƙona min zuciyata ba?. Kina ganin yadda Amira take yin komai wajen ganin ta farantawa mahaifiyarta, ba ta taɓa yi mata jaura ta dawo mata da shi ba face ta sai ta sayar da shi tas komai yawansa. Shin ke hakan bai ishe ki ishara ba? Ban da rashin zuciya irin naki ke ko wani abu ba kya ji a zuciyarki game da ita?".

Ji nayi kaina ya soma juyawa jiri yana ƙoƙarin kai ni ƙasa. Ban taɓa zato da tsammanin haka Umma ta ɗauki wannan abun azimun ba. Na gaza cewa komai illa hawayen da suka soma gudun famfalaƙi akan kuncina. Da ƙyar na furta"Umma ki yi haƙuri". Na ƙare zancen cikin raunin da ya bayyana har a muryata ina durƙushewa akan gwiwoyina na riƙo ƙafarta. Tsawon wasu mintuna ba ta ce da ni ko kanzil ba sai da na cire tsammani da samun amsa daga gare ta kafin ta furta zancen da ya girgiza ni ainun.

"Babu wani zaɓi Amatullah dole ne ki yi amfani da wannan laƙanin. Ga shi nan kamar yadda kike kallo kwalli ne sai kuma turare, a duk san da za ki fita talla za ki saka kwallin a idanunki turaren kuma za ki turara kayan tallan da su. Malam ya ba ni tabbacin matuƙar kika yi hakan ko talla dubu ɗari kika fita da shi sai ya ƙare tas kamar yadda wuta take cinye auguda cikin ƙiftawan ido. Amatullah idan kina da hankali da hangen nisa yadda Amira ta zama cinye du kaɗai ya ishe ki ishara kuma hakan ya isa ya zaburar da ke wanda ke da kanki za ki ce na je na nemo miki wannan laƙanin".

Tunani gabaɗaya ya tsaya cak bugun zuciyata ya tsananta. Gaɓoɓin jiki gabaɗaya suka yi sanyi na kasa motsa su. Ina ji ina gani ta zare ƙafarta daga riƙon da na yi mata ta bar ni yashe a wajen. Cikin rashin kuzari na tashi na yi sallan asr na kwanta a inda na yi sallan ina jin zazzaɓi mai zafi yana ƙoƙarin rufe ni. Shiga goma fita goma Umma ba ta ce da ni ko kanzil ba har aka yi ƙiran sallan magrib, a zaune na yi sallan na ci gaba da zama a wajen na kafa kai da gwiwa. Ina karanto karantun al'ƙur'ani a cikin zuciyata. Kamar a mafarki na soma tsinkayo amon Umma a kusa da ni, sautin da kunnena yake tantance mini shi ya tabbatar mini da a kusa da ni take zaune.

"Amatullah".

Ta ƙira sunana cikin wata iriyar murya na amsa ba tare da na ɗago kaina ba. Hakan bai ɗaɗata da ƙasa ba ta ci gaba da maganarta. "Ki buɗe idanuki ki kalli abubuwan da suke faruwa a duniyar zahiri. Me ye Amira ta fi ki da shi kyau, diri, sura, asali, zaƙin murya ko kuma sa'a ta fi ki? A bayyane yake duk waɗannan abubuwan da na lissafo kin fi Amira su ban da abu ɗaya shi ne sa'a. Kuma shi ma na yi alwashin sai kin fi ta shi".

Muryata a dushashe na ɗago kaina ina faɗin"Umma da kin fara nazari akan hanyar da Amira take bi wajen sayar da tallanta domin shi ne gaba da komai. Wallahi kin ji na rantse miki samari ne suke yi mata juye kuma su suke ba ta maƙudan kuɗaɗe har wayan da yake hannunta saurayi ne ya ba ta. Babu wani sa'a da take tare da shi haƙiƙanin gaskiya kamun kai ne ba ta da shi". Kallon da ta kafe ni da shi ya tilasta mini mayar da ƙwayoyin idanuna ƙasa ina sauraran abin da yake faɗi a zafafe alamar ta soma fusata ta kuma zo har wuya.

"Yau ina ganin ikon Allah wai na zaune ya faɗi, Amatullah har ke za ki zaunar da ni kina gaya min abin da ya dace na yi?. Ƴar iskan yarinya marar kunya to ko karuwanci za ki yi sai kin kawo min kuɗin tallan kununa babu gara bin zago, wallahi ba zan ƙara ɗaukar asara ba tun da na lura ba mutunci ne da ke ba shegiya mai mataccen zuciya". Duk yadda zuciyata ta so ba ta haƙuri cikin ƙasƙantar da kai bakina ya ƙi ba ni haɗin kai wajen furta abin da yake kan harshena, haka ta gama ta tashi ta shiga kicin. Na kasa motsawa daga wajen gabaɗaya na gaza gane abin da yake yi mini daɗi cikin duniyar. Ina jin sallamar yaran da nake yi wa darasi a ƙofar ɗakinmu amma na kasa amsawa balle har na tashi na ji da me ye suka zo, har Umma ta fito ta fararraƙe su suka tarwatse a haka Abba ya dawo ya same ni na ji jugum kamar majinyaciya. Babu nau'in tambayar da bai yi mini ba amma na ce da shi babu komai da ya matse na ce kaina ne yake ciwo. A daren ta fita kemis ya karɓo mini magani na sha sannan na kwanta. Haka na yi ta juyi don bacci sam ya yi ƙauracewa idanuna suna nan ƙamas kamar na kifin da aka tsoma a cikin ruwan mai aka tsamo. Haka na yi ta juyi har aka ƙira sallan assalatu na tashi da ƙyar saboda mutuwan da jikina ya yi na gabatar da sallan a zaune.

A ɗaki ya na ci gaba da zama saboda ruwan da aka soma yi kamar da bakin ƙwarya bai tsagaita ba har sai ƙarfe takwas saura. A lokacin na yi ƙarfin hali na bayyano waje na haɗa wuta wanda sai da na ci kwakwa kafin ya ruru na ɗaurawa Abba abin kaci. Kunnu na dama na ɗumama sauran tuwon dare ba kai masa har zan tashi ya dakatar da ni na koma na zauna kaina a ƙasa ina sauraronsa.

"Amatullah tun daren jiya na lura da yanayin da kike ciki tabbas akwai wani abun da yake faruwa. Shin mene ne ki sanar da ni komai kar ki yi ƙoƙarin ɓoye min".

Sai da na sauƙe gwauron ajiyan zuciya kafin na sama zarafin cewa"babu abin da yake faruwa Abba, kamar yadda na sanar da kai jiya kaina ne yake yi mini ciwo. Bayan hakan babu komai". Ya kafe ni da kallon da ya fi kama da na tuhuma duk da idanuna suna ƙasa amma tabbas jikina ya tabbatar mini da irin kallon da yake yi mini, shuru ya ratsa wajen kafin can ya zarce da cewa"ba na son kin sanya kanki a ciki damuwa Amatullah. Ki ƙara haƙuri akan wanda kike yi kuma na san ki da shi in sha Allah za ki ga riban hakan ko ba daɗe ko ba jima".

"Ai dole ka zaunar da ita a nan kana biya mata zancen banza da na wofi har da cewa wai ta ƙara haƙuri. Ai dole ka ce ta yi haƙuri tun da cutar da ita nake yi ko kuma ka ga alamar ina gallaza mata. Ka taɓa shigowa gidan nan ka gan ta a wulaƙanci ko ka ga alamar yunwa ko ƙishi a tattare da ita?. Ƴar iska mai baƙin hali ke kuma har da wani zama ki sadda kai ƙasa kina sauraronsa shegiya munafuka kawai". Tsam! Abba ya miƙe akan ƙafafunsa ya yi taku uku ya isa dab da Umma ya nuna ta da ƴar manuniyar ƴatsarsa yana cewa"Hafsatu kar ki ƙara cewa yarinyar nan ƴar iska balle har ki yi gangancin sheganta ta. Ki kiyaye ranar da za ki kai ni bango, na fara gajiya da halinki fa".

"Manniru ban ga dalilin da za ka zaunar da ƴarta kana aibata ni a gabanta ba kuma na zuba ido na yi shuru. Wallahi ka yi tsararo". Cike da takaici Abba yake jinjina kansa"Hafsatu ki kiyaye harshenki Manzon Allah ya ce"kuffa alaika haza" ku kiyaye wannan a gare ku. Ki dinga tauna magana kafin kin furta ta domin masu iya magana sun ce magana zaran bunu ce in har ta fita ba a mayar da ita". Ya sausauta amon muryarsa kafin ya ci gaba da magana"na roƙi ki zubar da waɗannan halayen ki zo mu zauna mu ba wa ƴarmu ɗaya tilo tarbiyyar da ta dace. Na yi muku alƙawarin ba ku kula daidai ƙarfina samun aljihuna".

Dariyar da Umma ta ba she shi ya sanya Abba dakata wa ba don ya gama bayyanar da takaicin da yake cikin ransa ba. "Alamar ƙarfi ai tana ga mai ƙiba Manniru. Na tabbatar ko zuciyar da take dashe a cikin ƙirjinka ba ta yarda da zancen bakinka ya furta ba. Yanzu kai ko wani ne ga tare ka a hanya ya ce kai Manniru za ka iya ɗaukar ɗawaniyyar iyalinka sai ka yarda?. A aikinka na maluntan ne za ka ɗauki nauyinmu?Shekarunmu nawa tare amma har yanzu ko gidan kanka ba ka mallaka ba ban da keke mai kake da shi a duniya?".

"Ni kuwa nake da abubuwa da yawa tun da na rayu da imani da kuma ƙaunar ma'aikinmu. Ina da lafiyar da zan fita na nema halal ɗina ban taɓa aika wani abun alfasha ba. Ba na so muna musayan yawo da ke a gaban Amatullah don haka wani mataki ne na lalata mata tarbiyanta". Tsaki ta buga ta koma ɗaki ta bar shi tsaye a wajen.

Hularsa Abba ya ɗauka zai fita na yi saurin cewa"Abba abincin fa?". Ba tare da ya kalle ni ba ya furta"lokaci ya riga ya ƙure zan tafi kar na yi latti". Yana dure zancen ya fice ya bar ni zaune cikin tarin damuwar da ya yi wa zuciyata katutu.

"To ke kuma munafuka sai ki tashi ki tattare É—akin kafin na gama dama kunnun nan ki fita da shi. Yarinya kamar Æ´ar gaba da fatiha tun da na haife ki ban huta ba har yanzu, oh! Ni kam ina ganin takaicin haihuwa". Ta yi maganar tana ficewa daga É—akin. Dole na tashi na tattare falon kana na koma na gyara É—aki cikin tashin kuzari, wanka kawai na yi na kora kokon da na damawa Abba wanda bai sha ba ya fita. Na fito waje na tarar da Umma zaune ta kammala komai na kunun.

"Umma na fito".

Ta ɗago kai ta ƙare mini kallo kafin ta miƙe ta ja hannuna muka koma falo ta shige ɗaki ta fito. Ta miƙa mini kwalli. "Ga shi kar ɓi ki saka sa a idanunki. Sannan ga can garwashi wuta ki ɗauko ki turare da shi". [7/12, 1:06 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_________________________________________

Page 0️⃣7️⃣

Ban san lokacin da ƙwalla suka wadaci koramar idanuna ba sai jin ɗuminsu na yi suna shawagi a bisa kuncina. Ban share su ba kamar yadda ban yi wani yunƙurin hana su kwaranya ba. Na haɗe hannayena wajen guda alamar roƙo kafin na sa magana cikin rawar murya da sarƙafewar harshe. "Umma don girman ki rufa mana asiri kar mu garin neman gira mu rasa ido, garin neman duniya mu faɗa cikin fushin Ubangiji, wannan abun fa kamar shirka ne. Don yana nuni da cewar ba mu yarda cewar Allah ne mai yi ba, ba mu yarda shi yake kawo kasuwa kuma ya buɗe wa bawa ƙofofin samunsa a duk lokacin da ya so kuma ya ga dama ba. Umma na yi miki alƙawarin ko zan wuni ba zan dawo ba sai na sayar da wannan kunun". Tun da na fara maganar ta kafe ni da idanu tana bi na da irin kallon da mai hankali yake yi wa zautacce, ta taɓe baki kafin ta soma faɗa a fusace.

"Lalle wuyanki ya yi kauri ya isa yanka Amatullah, har ni za ki kalla tsabar idona ki ce zan jefa mu cikin fushin Ubangiji?. In don islamiyyar da kike zuwa ne ko kuma kina ganin kina dab da haddace alƙur'ani ya saki faɗa min waɗannan kalaman, to sai na hana ki zuwa ko'ina. Ko Allah ma ai ya ce tashi na taimake ka ba zai taɓa yiyuwa kana daga kwance ka ga kuɗi suna zubowa daga rufin ɗakinka ba dole sai ka tashi ka neme su. Da ke gwara ƴar zina sam ba kya tausayina balle mu haɗa kai mu samarwa kanmu mafita. Ni kam ina ganin takaicin haihuwa".

Haƙiƙa kauraran kalamanta sun yi nasarar narkar mini da zuciya har su yi sanyaya mini dukkan gaɓoɓin jikina. Kaina ya ɗauki zafi kamar garwashin dake ƙasan tukuban tsire. Kafin na yi magana na tsinkayo amon muryar Anty Sawwama babbar ƴar Abba da take kusa da mu. Na waiga ina kallonta daga yanayin fuskarta na fahimci ta ji abin da Umma take faɗi.

"Yau ina ganin ikon Allah wai na zaune ya faɗi. Yanzu Hafsatu haka abin nakin ya girmama har ta kai ta kawo ki titsiye ƴar cikinki kina jifan ta da irin waɗannan mummunan kalaman? Kar ki manta ke ba uwa ce DAFIN HARSHEnki yana da matuƙar tasiri akan ta kamar yadda duk addu'ar da kika yi mata Allah zai amsa ta don babu hijabi tsakanin addu'ar uwa da Ubangiji". Ta gyara ɗaurin zaninta kafin ta ci gaba da faɗin"tabbas sai yau na ƙara yarda da cewar babu butulu kamar ɗan Adam shi ne mai manta alkhairi cikin ƙiftawan ido. Ashe Hafsatu kin manta tsawon shekarun da kuka shafe da Manniru a matsayin ma'aurata kafin Allah ya azurta ku da samun Amatullah?. Kin manta wahalhalun da kika sha a yayin goyon cikinta har zuwa lokacin haihuwarta wanda dalilin hakan aka cire miki mahaifa gabaɗaya?. Waɗannan dalilai guda biyu ba su isa su sanya zuciyarki karaya ba ba su isa su dasa so da ƙaunar Amatullah a cikin ƙirjinki ba tun da kin sani na sani daga ita ba za ki ƙara haihuwa ba a duniya, amma don kin cika cikakkiyar butulu mai mance ni'imar da Ubangiji ya lulluɓe ta da shi har kike buɗe baki ki ƙira da ita gwara ƴar zina. Hafsatu ina guje miki ranar ƙin dillanci ranar da ido za ta raina fata. Wannan harshen da muke rainawa wallahi yana da tasiri akan ƴaƴanmu".

"Maman Umar ni fa ba ƙaramar yarinya ba ce da za ki wanko ƙafa ki zo har cikin gidana kina gaya min abin da ya dace na yi ko wanda zan bari ba. Ke fa bakinki kika furta na sha wahala a lokacin rainon cikinta har zuwa haihuwarta don haka kuwa kin ga duk wanda zai nuna mata wata soyayya a bayana yake".

"Hafsatu nusarwa ce na yi miki, ke ɗin fa uwa ce duk abin da kika furta akan ta wallahil azim zai bibiyi rayuwarta ne. Kuma ko ba daɗe ko ba ji ma watarana sai abin da kika shuka ya yi tsuro kin girbe sa". Kallon uku saura kwata Umma ta watsa mata kafin ta juyo kaina"fita ki je ki ɗauki kunun nan ki wuce, idan Allah ya kaimu gobe za mu aiwatar da shirin mu". Tana dure zancen ta shige ɗaki ta bar mu a wajen, na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya kafin na tsugunawa har ƙasa ina gaishe da Anty Sawwama. Ta yalwata annuri fuskarta kafin ta amsa da faɗin"lafiya ƙalau uwarmu maganin kukanmu. Baya goya marayu Allah ya sa ki yi gadon halin mahaifiyarmu wanda tun yanzu ma alamomin hakan sun bayyana. Kina da haƙuri da ɓiyayya Allah ya yi miki albarka".

"Amin". Na amsa da shi ina sadda kaina ƙasa a ƙoƙarin tare hawayen idona kwaranya. "Ki je ki ɗauki kunun kar ta fito tun da kin fi kowa sanin halinta". Duk yadda na so tare hawayen idona zuba lamarin ya faskara ba tare da na yi aune ba suka fara gudun famfalaƙi a tsakanin kuncina da saman haɓata. "Anty zan dawo na same ki ko tafiya za ki yi?".

Ta matso kusa da ni ta riƙo hannuna da hannunta ɗaya, yayin da ɗayan kuma ta soma share mini hawayen fuskana da su. "Za ki dawo ki same ni, don zan jira har mahaifinki sai ya dawo akwai maganar da za mu yi da shi". Kaina kawai na gyaɗa mata na zare hannuna na fita na ɗauki bokitin kunun da ragowar robobin na fita.

Ina fitowa na tsaya a ƙofar gida ina kallon gabar da yamma kudu da kuma arewa. Na rasa wani hanya zan bi da sai sada ni nasara a safiyar yau. So nake yi na goge tunanin da yake cikin kan Umma na nuna mata cewar ko da laƙani ko babu idan Allah ya tsara zan sayar da kunun nan babu makawa sai na sayar ko da kuwa a ƙofar gida ne. Ganin tsayuwar da nake yi ba zai haifar mini da ɗa mai ido ba ya sani soma tafiya ƙirjina yana tsananta bugu. Sai da na fice daga unguwar gabaɗaya na fito bakin titin da ya rabu kashi biyu kudu da kuma arewa. Can na hango tawagar wasu masu talla sun haɗo kansu za su wuce na bi su a baya har muka isa wani babban fili da yake a bakin hanya kusa da wani sabon gidan mai. Suka zauna ni ma na nema waje na zauna bayan na ajiye tallana a gabana, duk suka zubo mini idanu kamar sun ga wata baƙuwar halittar da ta zo daga wata duniyar da ba namu ba.

Tabbas wajen fuskar jama'a ne don tun da muka zaune ake ta sayan kayan mussamman awara da wainar fulawa su suka fi ciniki. Raina ya yi fari ƙal nauyin da yake zuciya a hankali na ji ya fara sauƙa kamar an jefa dutsin a cikin ruwa. Farin ciki ya mamaye ni ganin a ƙasa da mintuna talatin na yi cinikin dubu da ɗari biyu. Farin cikin da yake fuskana ya soma dushashewa ganin sauran masu tallan sun yi cirko-cirko a gabana duk sun riƙe ƙugu fuskokinsu kamar a murtuƙe kamar hadarin da ya taso daga gabas.

"Bayin Allah lafiya?".

Na jefa musu tambayar bayan na haÉ—o jarumta na yafawa kaina, É—aya daga cikinsu ta wurga mini wani mungun kallo har da tsirta da miyau kamar ta yi tozali da kashi. "Uban waye ya ba ki iznin kawo talla nan wajen?". Na É—aya iso na yi mata kallo guda kafin na mayar mata da amsa"har sai an ba da izni kafin a kawo tallan? Na yi zaton fili ne kawai dajin Allah kowa ya kawo tallansa in ya sayar ya koma gida....".

Kafin na rufe bakina ɗaya daga cikin da ta fi su fusata ta ɗauke da mari da ya sani jin hajijiya na ƙoƙarin buga ni da ƙasa duk da a zaune nake. Kafin igiyar firgicin marin ya gama sake ni sautinta ya dira a ƙofofin kunnuwana kamar sauƙar ungulu.

"Ke har kin isa Zaina tana magana kina mayar mata, wane ne ubanki a cikin garin nan? Kuma waye ya tsaya miki a nan wajen?". Na dafe kuncina kafin na ce"laifina ne don ta tambaye ni na ba ta amsa?". Ta ƙara fusata ta nufo ni wata ta dakatar da ita. Cikin isa take faɗin"ƙyale ta Zulfa'u akwai buƙatar sai mun yi mata komai a aikace".

"Zaina don Allah ki bar ni na koyawa wannan kucakar yarinyar hankali. Na nuna mata bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne". Wacce ta ƙira da Zainan na bi da kallo da ta yi musu alama da hannu akan a kawo mata kujera cikin sauri aka kawo mata ta zauna tana fuakanta na sosai. Tsawon wasu daƙiƙu ba ta ce komai ba sai can ta soma magana a gadarance.

"Ni ce shugaban masu kawo talla a wannan wajen kuma duk wacce kika gani a nan tana ƙarƙashin iko da isata ne. Ko kara na ajiye babu wacce za ta tsallake shi sannan kafin ki kawo talla nan wajen sai kin zo wajena na yi miki regista sannan a kowacce rana dole ki biya haraji ko kuma ki fuskanci hukunci mai tsauri". Ta dakata kafin ta doka mini tsawa"me ye kike sayarwa?".

"Kamar yadda kike gani kunu nake sayarwa. Kuma duk waɗannan ƙa'idodin da kika gindaya ba za su aiki a kaina ba don daga yau ba za ki ƙara ganina a nan ba. An yi na farko kuma na ƙarshe".

"Kunu? Wannan ne kunun?".

Ta ƙarƙare zancen tana saka ƙafa ta yi kutubol da bokitin kununa. Sam na miƙe Zulfa'u ta doka mini wata tsawar, cikin ba da umarni ta ce"koma ki zauna ƙasƙantacciya, ke har kin isa Zaina tana zaune ki tashi tsaye ki tsaya mata akai". Na cire leɓena raina cike da takaici na bi su da kallon ɗaɗɗaya kafin na ce"ita ɗin wace ce da in zan tashi ko zan zauna sai na nema izninta, ko ba ki ga ɓarnar da ta yi mini ba ne? In ce dai talla ta zo kuma ni ma shi ya kawo ni don haka ba mu da wani bambanci. Kayana kuma sai an biya ni". Suka tashi gabaɗaya suka yi kaina suka cakumo ni kokuwa ya kaure a tsakaninmu. Kafin wani mutum ya zo wajen ya shiga tsakaninmu. Ya janye Zaina gefe guda tana tambayata abin da ya faru.

"Allah ya ja zamaninka wannan yarinyar ce ta zo ta zauna ba tare da ta cike ƙa'idodi ba". Ya juyo yana kallona sosai"ke me yasa kika zo ba tare da kin bi ƙa'ida ba?".

"Ni baƙuwa ce a nan wajen ban taɓa zuwa ba. Shi yasa ban da dokokin ba, maimaikon ta kawo hankali cikin fahimta sai ta sa ƙafa ta zubar mini da kununa". Na kai aya ina yi masa nuni da inda gabaɗaya kunun ya malale. Ya jinjina kansa yana ƙara kusanto ni har yanzu idanunsa suna kaina ya furta"ba a kyauta miki ba kam, ke Zaina me yasa da ta zo ba ki kawo ta wajena ba?".

Sai da ta wurga masa harara kafin ta ce"na ga zan iya shawo kan matsalar da kaina ne, ba tare da mun je teburinka ba". "To yanzun kin shawo kan matsalar ne na zo na tarar da ku haka?". Ta waro idanu waje"Mai aska ni nake maidawa magana haka a gaban kowa? Ko ka manta waye ce a gaban ka?. Zaina ce fa tauraruwarka".

"Zaina na gane ki mana akwai ina sanar da ke kuskuren da kika yi ne. Na sha gaya miki idan irin hakan ya faru ki dinga zuwa kina sanar da ni amma sam na fahimci ba kya jin abin da nake faɗa miki ba". Ta zabura ta kurma wani uban ihu kamar wacce aka watsawa garwashi ta yi kukan kura za ta cakumo ni ya tare ta ya riƙe ta gam. Amma duk da haka ba ta fasa kai mini duka ba. Ganin ba za ta tsaya ba ya sanya shi ɗauke ta marin da ya sanya kowa shan jinin jikinsa duk suka yi tsam kamar ruwa ya cinye su.

"Ke Zaina ke wata iriyar mahaukaciya ce jaka kawai marar lissafi. Ana tare ki har kina wani ƙara dagewa sai kin yi, to ga ta ki duke ta na gani. Wallahi in har kika yi kuskuren ɗaura hannunki a jikinta sai na tabbatar da hakan ya zamo kuskure mafi girma da za ki yi a cikin rayuwarki".

"Wayyo jama'a ku taimake ni ga annoba ta zo. Mai aska yau ni kake gayawa haka?".

"Na gaya miki ɗin uwa ta ce ke? Na ce uwa ta ce ke da ba zan gaya miki magana ba?. Na baki mintuna goma ki tattara kayan tallanki ki bar nan wajen, kuma idan ba ki wasa ba har matsayin da na ba ki sai na ƙwace sa".

Za ta yi wani maganar Zulfa ta hana ta, sai da suka rirriƙe ta saboda yadda jikinta yake karma kafin suka bar wajen. Maganar da ya soma yi shi ya dawo da ni duniyar zahiri.

"Amincin Allah ya tabbata a gare ki ya ke kyakykyawa da kyawun zubi gami da tsari. Mene ne sunanki?".

"Sunana Amatullah".

"Sunan ya dace da ke matuƙa. Shin ko zan iya sanin adadin kuɗin kunun da Zaina ta zubar miki, ina so na biya don na san hatta su kuɗaɗan za su yi farin ciki idan suka shiga hannun kyakykyawar mace kamar ki". Na ɗan yi jim don na fara tsorita da irin kallon da yake yi mini.

"Ina fatan ba za ki hana ni aikata wannan aikin alkhairin ba. Ya ke tauraruwa mai haske duniya". Tuna jarfan da zan tarar da gidan idan na koma a haka babu kuɗin kunu babu kunu a wajen Ummata, ya tursasa mini jam dogon numfashi na fesar daga bakina kafin na sama sararin cewa"dukka dubu uku ne amma na yi dubu da ɗari biyu". Babu musu ya zaro kuɗin ya irga su ya miƙo mini yawansu ya tsorita ni don na tabbatar da sun zarce dubu ukun da na faɗa masa.

"Ka yi haƙuri ba na buƙatar kuɗinka, iya kuɗin ɓarnar da aka yi mini kawai nake buƙata". Bai yi musu ba ya irga su ya ba ni na karɓa sai na miƙa masa dubu daya da ɗari biyun da na yi amma ya ƙi karɓa, na ajiye masa su a wajen na fara tattare kayan tallana. Na kimtsa komai na soma ƙoƙarin barin wajen ya dakatar da ni. "Zan so ki ba ni damar ki yi miki rakiya har gida. Don na tabbatar da tsaronki saboda na san Zaina kamar yunwar cikina ba ta da daɗi ko na misƙalla zarratin za ta iya bin bayanki". Ambatan sunan Zaina da ya yi shi ya tursasa mini amince ya yi mini rakiya, sai dai ban yi zaton rakiyan zai yi tsayi ba. Har bakin layinmu ya yi mini rakiya kuma bakinsa bai fasa magana da yabon girin jikina ba duk da ba na tanka masa, shi yake kiɗansa yake rawarsa. [7/13, 7:23 AM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

________________________________________

Page 0️⃣8️⃣

"Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya tsara halittarki ya kuma busa miki numfashi. Bai bar ki haka ba ya kuma yi miki tagomashin iya magana da iya taku". Cak na tsaya jin kalamanta da suka sauƙa a na'urar naɗar sautina, na juya ina kallonsa don tunin na yi gaba na bar sa sai dai ban yi tunanin tazarar ta kai haka ba. Hijabina da iska ya ɗaga mini shi ta baya na yi saurin gyarawa ina ɗauke kaina daga gare shi. "Rakiyar ta isa haka na gode sosai Allah ya saka da alkhairi. Ya biya maka buƙatunka".

"Amin tauraruwa, amma zan so na kai ki har ƙofar gidanku don na sauƙe nauyin tsaronki da yake kaina".

Cikin ƙosawa da sauraronsa na ce"Malam na ce maka ya isa na gode, to kuma me ye kake so da ni? Don Allah ka bar ni ka koma wajen sana'arka". Ya yi wani irin shu'umin murmushi yana takuwa a hankali ya zo gabana. "Ai tun da na yi tozali da ke zuciyata take wajabta min ya zama dole na ba ki kariya da kuma kulawa ta mussamman. Babu wani aikin da ya sha gaban hakan a yanzu". Taɓe baki na yi na ƙara yi masa godiya na ci gaba da tafiya ganin har yanzu yana bi na ya sani ɗaga ƙafa kamar wacce aka jefo haka na faɗa cikin gida ina waige-waige. Saura ƙiris na yi karo da Ummi da Auwal da suke zaune a zaure suna hira, cikinmu babu wanda ya ce da wani ko kanzil na yi wucewa ta cikin gidan. Duk matan gidan suna waje yayin da Sahura mahaifiyar Amira take baza shewa ta baje a ƙofar ɗakinsu tana irga cinikin da Amira ta yi yau na waina fuskarta kamar gonar auguda.

Kamar wacce aka tsigarawa matsilli haka Umma ta yi wani wawan zabura ta miƙe sa'ilin da ta ganin. Ta iso wajena tana bi na da wani irin kallo kafin ta ce"Amatullah yaya haka nake ganin ƙasa a jikin bokitin?".

"Umma na sayar da shi gabaɗaya, a hanyar dawowa ne bokitin ya faɗa shi ne kika ga haka". Na ƙare zance ina miƙa mata kuɗin ta amsa tana lalle su ɗaya bayan ɗaya, tsakanin mamaki, al'ajabi da farin ciki na gaza bambance takamanmen wanda ya hana Umma yin magana a lokacin sai juya kuɗin take yi a hannunta kafin daga bisani ta ja ni zuwa ƙofar ɗakinmu muka zauna. Tsakin da manaifiyar Amira ta buga shi ya hana ta maganar da ta yunƙuro za ta yi ta kallo ta.

"Ke kuma tsakin na me ye Sahura?".

"Sai kuma aka ce miki da ke nake yi Hafsatu? Lissafi ne ya ɓarce min kin ga kuwa dole na yi abin da ya ci uwar tsaki ma. Babu uban da ya isa ya hana ni don daidai nake da uban kowa a cikin gidan nan yadda ake biyan kuɗin haya haka ni ma nake biya babu raran ko ficika". Shewa Umma ta saka har da tafa hannu kafin ta furta"Allah na gode maka. Daman an ce makashinka yana tare da kai kuma hassada dai aka ce mungun ciwo ce a zuciyar mai ƙula shi. Mu zuba ni da ke Sahura tsakanin ni da ke ɗan halak ka fasa". "Tun da haka kika ce to mu zuba ɗin wallahi sai na tabbatar da in kika zuba ba ki kwashe ba Hafsatu". Sahura ta yi zancen tana miƙe wa tsaye Amira ta riƙe ta tana ba ta haƙuri suka shiga ɗaki, nan Umma ma ta ƙarishi banbamin ta ta gama. Jikina a saɓule na tashi na shiga ciki a falo na tarar da Abba da Anty Sawwama duk su biyun sun yi shuru alamar duk abin da yake wakana a filin tsakar gidan suna saurara, na durƙusa na gaishe su Anty Sawwama ce ta amsa Abba kuma maimako ya amsa sai ya jefo mini tambaya.

"Yau ma kin je tallan ne?".

Kafin na amsa masa Anty Sawwama ta tari numfashina"kunun ma yana tafiya kenan? Daga fitarki har kin dawo ko awa biyu masu kyau ba ki yi ba". Ƙirjina ya harba ɓat! Kamar yadda alburushi yake fita daga cikin bindiga, gabaɗaya na riɗime na daburce na soma kame-kame har izuwa lokacin da na ƙara tsinkayo amon Abba a karo na biyu. "Ina kika kai tallan ya yi saurin ƙarewa haka?".

"Bakin titi ne Abba, masu tafiya makaranta da gona ne duk suka saye". Shurun da ya yi ya tabbatar mini da hashashen zuciyata na cewar bai yarda da abin da na faɗa ba. Zancen da Anty Sawwama ta yi ya ƙara jefa ni cikin kogin firgici har na kasa magana da motsi na tsawon wasu mintuna.

"Ya kamar shatin Æ´atsu ne a fuskarki Amatullah? Ko dai dambatuwa kuka yi a wajen tallan?".

"Ba-ba-ba- ba abin da ya faru, shatin kwanciya ne kawai. Don jiya ban kwanta ana matashi ba".

Ta gyara zamanta tana fuskantar Abba da kyau kafin ta sa furzar da takaicin da yake kwance a ƙasan ranta"Allah ya jiƙan iyayenmu ya sabunta rahama a gare su, tabbas bango Ya faɗi don na tabbatar da ɗaya daga cikin iyayenmu suna raye ba za su taɓa zura ido jikarsu ta yi talla ba komai talauci da matsin rayuwar da muke ciki. Don an shaide su da wadatar zuciya da kuma kare mutunci da martaɓan ƴaƴansu mussamman ɗiyoyinsu mata, har muka girma iyayenmu mata ba za fita ko'ina iyayenmu da yayun maza suke fita domin samar mana da abin da za mu gudanar da rayuwa da shi. Amma yanzu kai Manniru ka ga dacewar wannan tallan da Amatullah take yi? Zankaɗeɗiyar budurwa da ita a ɗaura mata talla tana yawon layi-layi, kororo-kororo, lungu-lungu da sunan neman kuɗi. Wanda ina da tabbacin ba ku rasa ci da sha ba balle suturar da za ku rufe tsiraicinku, ya kamata ka farka daga baccin da kake yi kai ne na miji a gidanka kuma kai kake da alhakin gyara shi da daidaita shi. Ka sani fa akwai ranar Allah zai tambaye ka amanar da ya ba ka a ranar da babu lauyan da zai kare ka". Numfashi mai zafi Abba ya furzar daga bakinsa sai da ya musguta kafin ya ce"wallahi ni ma har cikin zuciyata ba na son wannan tallan da Amatullah take yi......".

"Kar ka wani rantse min Manniru. Kai ne fa namiji a cikin gidanka kuma da Amatullah da uwarta duk a ƙarƙashin ikonka suke, idan suka lalace sai Allah ya tambaye ka don haka zaɓi ya rage gare ka".

"Ba shakka Maman Umar dole ka sa shi a gaba kina yi masa huÉ—ubar banza. Ke ki fara gyara naki gidan auren mana kafin ki wa gidan wasu katsalandan".

"Ke Hafsatu ki iya bakinki idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri. Zan jure komai akaina amma ba zan juri cin mutumci ga ƴan uwana ba. Maman Umar kamar uwa ce a gare ni zan iya ƙarya duk hannun da ya nuna mata ƴatsa". "Dole na furzar da abin da yake cikin raina Manniru, ko yaushe ƴan uwanka gani suke yi kana ɗaukar duk ɗawainiyyarmu bacin ba haka ba ne. Talla dole na ɗaurawa ƴata don na rufawa kaina asiri ina da yaƙinin ko aurenta ne ya tashi babu wanda zai tsinana mana komai daga kai har dangin nakan". A matuƙar fusace Abba ya soma magana kamar zai yi aron baki.

"Ya ishe ki haka kar ki wuce gona da iri. Ki ɓace min daga gani kafin na yi miki abin da zuƙata da yawa za su raunana". Tanadin kallo ta ƙare masa tas kafin ta buga tsaki ta wuce cikin ɗakin bayan ta ba ni umarnin tashi daga wajen a cewarta a daga wajen su nake koyan baƙin hali da gardama. Muna shiga ɗaki ta tsare da ido tamkar mai son gano wani gaskiya a tattare da ni.

"Kar ki ba ri kalamansu su sama matsuguni a cikin kanki balle har zuciyarki ta amshe su. Ke ganau ce ba jiyau ba cikinsu gabaɗaya waye yake taimaka mana da ko da tsinke ne? Ko yaushe gani suke yi kamar duk duniya babu namijin da yake ƙoƙarin sauƙe haƙƙoƙin iyalinsa da wadata su da komai na rayuwa kamar ɗan uwansu don zuzurutun son kai. Dole na yi sana'a haka zalika dole ki je min talla don mu rufawa kanmu asiri".

Tun da ta fara zancen kaina yake ƙasa har ta gama kana a hankali na furta"in sha Allah Umma zan ci gaba da zuwa matuƙar ba Abba ba ne da kansa ya dakatar da ni". Ba amsa mini ba illa ɗauke kanta da ta yi gefe guda, na fito na yi alwala na koma na yi sallan zuhur a ƙuraran lokaci babu jimawa aka yi ƙiran asr na yi su gabaɗaya. Na janyo jiki na zauna a ƙasa kusa da ƙafafunta.

"Umma kin ga ikon Allah ko? Ga shi yau na sayar da duk kunun ba tare da ko sisi ya yi ciwon kai ba. Daman na gaya miki idan Allah ya so kuma ya datar da mu ko ana so ko akasin haka zan sayar da kunun, Umma shi Allah mai nuna iko da isarsa ne akan komai kamar yadda ya nuna mana a yau ko da laƙanin nan ko babu idan ya nufa wallahi ko a cikin gidan nan ne sai kin ga an saye kunun, ina roƙonki da mu haƙura da wannan abun ki watsar da duk zantukan da Malamin bogin nan ya zuba miki a cikin kanki, ni kuma na yi miki alƙawarin zan yi iya ƙoƙarina na ganin ban dawo da kwantan kunun ba".

Tun da na soma maganar take bi na da wani irin kallo da na gaza gane ma'ana da maƙasudin yin sa. Ta taɓe baki kafin ta ce"ki daina ɓata bakinki don babu abin da za ki ce min na fasa aiwatar da abin da na yi niyya musamman yanzu da hassadan Sahura ya fito ƙiri-ƙiri akan mu. Dole ne na tashi na tsaya akan ƙafafuna don na san ba za ta taɓa bari na haka banzan ba".

"Don Allah ki yi haƙuri ki tura mata mungun nufinta".

"Ke Amatullah". Ta doka mini tsawan da ya tursasa mini yi wa bakina linzami nan take. "Kar ki ƙara yi min wannan maganar don na riga da na gama yanke shawara". Haƙuri na ba ta na ja bakina na gimtse har izuwa lokacin Anty Sawwama ta soma shirin tafiya a sa'ilin Abba ya tafi masallaci bai dawo ba. Fuskata ɗauke da annuri nake faɗin"Anty har tafiya za ki yi ga shi ko abinci ba ki ci ba". Kafin ta yi magana Umma ta yi caraf ta amshe zancen kamar jira take yi na ce kule ta ce da ni cas.

"Ai dole ta tsaya jiran abinci tun da shi ɗan uwan natan ya kawo ya ajiye. A kan idonta ya dawo ai haka ya shigo siƙau hannu na dukan cinya, don haka ba abin da za mu ɗaura balle har ta sa tsammanin ci".

Sosai kalaman suka daki zuciya na ji wani ɗaci a bisa maƙoƙarona yana tasowa har izuwa cikin bakina. Satan kallon Anty Sawwama na yi na ga gabaɗaya jikinta ya yi sanyi da alama ita ma zancen ya baƙanta mata ruhi sai dai ba ta bayyana shi a fuskarta ba. "Ba komai Uwata zan tafi, daman na gama abin da ya kawo ni kuma mun yi sallama da shi kafin ya fita masallaci. Kin ga kuwa ai babu abin da ya rage". Ta yi zancen yayin da take miƙewa tsaye kafin na ce wani abu har ta fice daga falon na yi wuf na rufa mata baya muka fito daga gidan tare, har ƙarshen layinmu na yi mata rakiya kasancewar ranar babu islamiyya kana muka yi sallama a dawo gida.

Ganin har lokacin Umma ba ta ce da ni na haɗa wuta ko kuma ga abin da za a girka ba, ya sani shimfiɗa tabarma a ƙofar ɗakinmu na ɗauka jakar islamiyyata na soma tilawa. Kamar faɗuwar aradu haka abin da ya faru da ni ɗazu a wajen talla ya faɗu mini a rai na ja dogon numfashi na fesar ina lumshe idanuna. Na sha jin ana cewa ƴan talla ba su da kunya kuma ba sa tsoron ta mutuwa balle ta yi rayu wanda wasu suke amfani da wannan dalilan suke yi wa duk wata mai talla kuɗin goro. Ban taɓa yarda kalaman da ake faɗa akan su ba sai yau da na ga zahiri ya kuma faru a kaina. Tabbas akwai babbar matsala matuƙar aka ci gaba da tafiya, zuciyata ta harba yayin da na tuno irin musayan kalaman da Zaina da Mai aska suka yi da irin ikirarin da alwashin da ta yi a kaina. Gabaɗaya sai na yi gwiwoyina sun sake zuciyata ta karaya yayin da raunina ya bayyana.

"Amatullah".

Sautin ƙiran sunana da Amira ta yi ya fizgo tunanina da ya yi ƙaura daga gare ni izuwa gangar jikina. Na gyara zamana a ƙoƙarin daidaita nutsuwata. "Amira yaushe kika zo kika zauna a nan?".

"Lokacin da kika yi nisa cikin kogin tunanin da kika faɗa". Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ba tare da na tanka mata ba. "Wai me ye yake damunki ne? Tun da kika shigo na fahimci akwai tsoro da firgici a tattare da ke".

"Ina Ummanki?".

Ta murmusa kafin ta ce"tana cikin ɗaki tana bacci ki kwantar da hankalinki na san abin da kike tsoro. Kafin ta kwanta sai na tabbatar ta manta komai, kuma ina da tabbatar ko musayar alburushi suka yi da Ummanki Ummata ba za ta taɓa hana ni zuwa inda kike ko mu'amala da ke ba, a wajenta laifin wani ba ya shafan wani, don haka ki sanar da ni kawai me yake faruwa?". Tiryan-tiryan na kwashe komai na faɗa mata da ita kaɗai na ji zuciyata ta nutsuwa da ita, ta ƙura mini ido kafin can ta soma maganar da ya ƙara sanya hankali tashin gauron zabuwa.

"Don É—an wannan abun shi ne duk kika bi kika tashi hankalinki? Indai har wannan abun zai É—aga miki hankali to ai ba ki shirya yin talla ba ne Amatullah. Wannan su ne abubuwan da suke faruwa yau da kullum kuma duk wacce ta amsa sunan cikakkiyar Æ´ar talla ya kamata ta san da su ta kuma tanadar wa kanta mafita".

"Kin ga haukan da ta yi kuwa Amira? Ni wallahi ta ba ni tsoro har na yanke shawarar ba zan ƙara zuwa wajen talla ba". Ta hanzarin katse ni"ai kuwa yanzu ma aka fara ɗaura ɗamarar yaƙi da su za ki yi, ki nuna musu duk abin da suke taƙama da shi kin dama su kin shaye. Ki fito a cikakkiyar ƴar tasha ki yi musu hauka da naɗe-naɗanta, hatta shi mai gidan nasun ki yi duk yadda za ki yi ki dawo da hankalinsa gare ki ta yarda za ki gasa musu aya a tafin hannunsu". Sakeke na yi ina bin ta da kallo har ta kai aya kafin na iya magana.

"Wallahi Allah ma ya sani ni kam ba zan iya ba".

"Za ki iya kuma in har kika gwada ina da yaƙinin ke ce da riba. Ai ko a addini ma an ce ka kare kanka daga wanda zai cutar da kai, kuma ai raba cuta ga macuci ibada ne". [7/13, 1:19 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

___________________________________

Page 0️⃣9️⃣

Wuri-wuri na yi ido ina bin ta da kallo tamkar na sama majigi raina cike fal da mamakin zantukanta tsoron da yake cikin zuciyata ya bayyana ƙarara a bisa fuskana. "Ki nutsu ki nazarce abubuwan da na faɗa miki. Don matuƙar tallan za ki yi da gaske to sai kin shafawa idanunki toka kin rikiɗa kin koma ƴar tasha ko ma na ce ƴar bariki. In ya so in kika dawo gida duk ustazancin da za ki yi sai ki yi".

"Ba na ma fatan na ɗau tsawon lokaci ina wannan tallan Amira. Allah ya sani ba zan iya yin waɗannan abubuwan ba". Dariya ta bushe da shi mai matuƙar sauti sai da ta tsagaita kana ta ce"lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan Amatullah amma ina da yaƙinin sanda za ki fara ma ba za ki sani ba".

"Ke Amira a uban waye kike yi wa dariya?".

Muka tsinkayo muryar Ummi kamar daga sama duk mu biyun muka miƙe muna kallon juna. Amira ce ta yi magana don ni kam bakina ya rufu kiruf. "Da uban wanda ya tsarku nake yi. Inda abun da za ki yi kuma to bismillah". "Billahillazi ki fita daga idona Amira ba ni da daɗi, yanzu zan yi wasan kura da ke hakan ba damuwata ba ne".

"Don girman Allah Ummi ki yi min abin da Allah bai yi min ba yanzu-yanzun nan. Idan kin cika Æ´an halak kar ki bar ni da numfashi". Amira tana rufe bakinta Ummi ta cakumo ta da kokuwa suka kaure da faÉ—a kamar ba za su bar junansu da rai ba. Duk yadda na so raba su hakan ya gagara sai da Baban Adnan ya fito daga É—aki ya raba su, duk da hakan Ummi ba ta lafa sai sura take kai wa Amira.

"Malam ka matsa ka ba ni waje yau sai na koyawa yarinyar nan hankali. Sai na nuna mata bakin rijiya ba wajen wasan mahako ba ne kuma wallahi na gaba ya yi gaba na baya sai dai labari".

"Ke mahaukaciya ce wai? Ana raba ku har kina wani cewa a bar ki. To ka ga ki kashe ta in kin ga dama". Baban Adnan ya yi maganar cikin tsananin fusatan da ta bayyana har a kalmominsa. Duk suka yi shuru sun yi zuru-zuru da ido, lokacin har an ca a kan su kowacce mata ta fito daga ɗakinta don ba wa idanunta abinci. "Na lura da ke yarinyar nan Ummi sam ba ki da kunya, har za ki kalla tsabar idona ki ce wai na matsa na ba ki waje ki koya mata hankali?. Ko kin manta wane ne ni? To a matsayina na ɗan sanda ba zai yiyuwa na zuba ido ayi ɓarna akan idona ba".

"Da yake Ummi ce marainiyar wayonka dole ka ce ita ce ba ta da kunya. In shari'ar gaskiya za ka yi ai kamata ya yi ka bar su su fitar da raini a tsakaninsu, ina kuma adalci za ka yi kamata ya yi la fara da tambayar abin da ya haɗa su". Furucin mahaifiyar Ummi kenan yayin da take isowa wajen ta riƙo Ummi kana ta zarce da faɗin"ba fa zai yiyuwa ace duk gidan nan an sawa ɗiyata ido ba. Babu uban da ya isa ya takura mata tun da kuɗi muke biya muna haka muke biya. Daga yau na ba ka damar ki ƙwaci ƴancinki duk wanda ya taka ki kema ki taka shi komai girma, shekaru ko furfurarsa".

"Ai kuwa da kin ba ta lasisin aikata kuskure mafi girma a cikin rayuwata. Don duk ranar da tsautsayi ya sa ta yi wa Baban Adnan tashin kunya ko kallon banza, sai na yi mata raunin da har ta koma ga mahaliccinta rabonsa bai bar jikinta ba".

Maman Adnan ta yi zancen daidai sanda take fitowa daga banɗaki. Ummi ta mayar mata da martani daidai da zancenta. "Billahillazi ko iyayenki ne suka zo gidan nan suka shiga karkata sai na ba su amsa daidai da su, balle kuma wani banza". "Banza? Ummi mijin nawan kike da ƙira da banza akan idona? To yanzu ni zan koya miki hankalin da ke kika gaza koyawa Amira". Tana rufe bakinta ta tunkaru Ummi kafin ta yi aune tunin ta rotsa mata bokitin ƙarfen da ta fito daga wanka riƙe da shi a hannunta. Kan ka ce kwabo jini ya ce sallama alaikum jini kamar an yanka saniya sai zuba yake yi daga gashin Ummi da ta zube a ƙasa tana burburko tare da rausa ihu.

"Wayyo Allah! Jama'a ku kawo min ɗauki za ta kashe min ɗiya. Shikenan ta tsiyayar mata da ƙwayan idonta".Mahaifiyar Ummi ta yi zancen tana fasa ƙara ta riƙo Ummi suka fice daga cikin gidan ko mayafi babu balle takalmi. Nan kuma wani faɗan ya kaure tsakanin Baban Adnan da matarsa. Ta hau masifa tana ikirarin duk abin da ake mata a cikin gidan shi yake ja mata, saboda shishshiginsa da tsoma baki a cikin abin da babu ruwansa a ciki sai ya yi wanka tsarki ya faɗa, sai da ya gaggaura mata mari kafin ta yi shuru. Don shi a gare sa dukan mace akan abin da bai taka kara ya karya ba shi ne abu mafi sauƙi a wajensa wajen aikatawa.

Sai da ƙuran ya lafa kafin na sama damar ba wa Amira haƙuri tana buƙarewa akan za ta jira Ummi ta dawo su ɗora daga inda suka tsaya. Da ƙyar da suɗin goshi na shawo kanta ta haƙura. Sai da aka magarib kafin Umma ta ce na tafasa tafiyar murji kamar yanda ta ce haka na yi na ci nawa na kai mata nata ɗaki na zuba na Abba a kula na ajiye masa. Na yi sallan isha'i na kwaso littattafain da nake koyar da yara da su na fito gidan ya haɗe da gurmi. Don mahaifiyar Ummi ta lashi takori akan sai an bi wa ɗiyarta haƙƙin zubar mata da jini da aka yi ba gaira ba dalili. Ta ƙira Mahaifin Ummi da yake legas a waya tana shaida masa abun da ya faru ya fi sau shurin masaƙi. Tunin na tarar da yaran da nake koyar da su a zaure suna jirana babu ɓata lokaci muka fara karatu har mun yi nisa Abba ya dawo na miƙe tsaye da fara'ata ina yi masa sannu da zuwa sai kafin ya kai ga amsawa wani yaro ya shigo.

"Wai ana sallama da Amatullah a waje".

Daga ni har shi duk muka yi mutuwar tsaye kafin ya tsayar da idanunsa a kaina tamkar yau ce rana ta farko da ya fara ganina. Cikina sai ƙugi yake yi haƙwana suka datse harshena lokacin da Abba yake tambayar yaron da har yanzu yana tsaye bai gusa ba. "Waye yake sallama da ita?".

"Wani ne ya zo akan babur ya ce a ƙira ta".

"Ke waye ya zo neman ki?". Tambayar da ya watsa mini ta sanya hanjin cikina kaɗawa jikina ya soma rawa kamar mazari. "Ba magana nake yi miki ba? Waye ya zo neman ki a daidai wannan lokacin?". Ya kuma maimaitawa a karo na biyu cikin tsantsan buƙatuwar sn jin amsar tambayarsa. "Ka yi haƙuri Abba ni ake nema ba Amatullah ba. Wani ne muka haɗu da shi kuma ya ce min zai zo gidanmu, yanzu ma muka gama waya da shi, ni ce na ce masa sunana Amatullah saboda ya takura min a lokacin".

Da wani irin hanzarin na waigo ina ƙarewa Amira da ta yi maganar cikin takewa da ƙwarin gwiwa kallo haka nan ma Abba shi ma kallon natan yake yi. "Ita ba ta da bakin kare kanta sai ke?". Cikin girmamawa Amira ta amsa da faɗin"Abba ba ta san komai ba ne shi yasa ta kasa cewa wani abu. Amma ina mai ƙara ba ka haƙuri na san yadda kake taka tsantsan da tarbiyyan Amatullah. Ka yafe min akan kuskuren da na yi na ba ta sunanta a matsayin nawa".

Sai da ya yi ɗan jim kamar mai tunani ko nazarin wani abun kafin ya ce"ba komai amma dai a dinga kiyayewa. Ke ma bai dace kina tara samari a ƙofan gidanku ba ki nutsu ki fitar da wanda kike so a cikinsu, don haka ne daraja da kimarki a matsayinki ta ɗiya mace".

"In sha Allah Abba kwana nan zan fita da guda daga cikin su. Ku dai ci gaba da yi mana addu'a Allah ya ba mu na gari". Cike da jin daÉ—i Abba ya ce"Amin amin ya hayyu. Kuma in kin je kar ki daÉ—e Amira, ni sai na rasa ma me ye kuke tattaunawa su yi awanni suna zance".

"Ba zan wuce mintin talatin ba ina sha Allah". Kansa kawai Abba ya jinjina ya wuce ciki sai da na tabbatar ya gama wucewa kafin na fizgo hannun Amira. "Waye kika kika ba shi sunana har yanzu gida nema na?". Ta fizge hannunta"dalla! Ki nutsu mu yi magana. Malama ni babu wanda na ba wa sunanki balle har ya zo gida ne nemanki, na yi haka ne kawai don na ƙwace ki daga tuhumar Abba. Yanzu dai ki zo mu je mu ga ko wane ne kuma da me ye ya zo".

"A'a Amira ni gaskiya babu inda zan je tsoro nake ji". Ta watsa mini harara kafin ta finciko ni muka yi waje muna fitowa muka hango mutum zaune a bisa babur yana latsa wayarsa. "Amira na shiga uku! Idan Abba ya fito ya kalle ni fa?". Na furta muryata tana rawa. "Ki nutsu mu yi abin da ya kamata mu koma gida akan lokaci. Ban da abin ki me ye zai fito da Abba yanzu kuma, ke dai kawai ki nutsu". Tana dasa aya anan ta ja hannuna muka ci gaba da tafiya duk ɗaga ƙafar da zan yi sai ƙirjina ya buga har muka isa wajen mutumin.

Sunan da ya ƙira ni da shi ya ƙara jefa ni cikin firgici. "Tauraruwa Amatullah ba ki tsammanin gani na a ƙofar gidanku ba ko?". Jikina ya soma rawa tamkar wacce ake jonawa wutan lantarki. Da ƙyar na daidai nutsuwata.

"Mai-mai-mai aska kai ne?". "Ƙwarai kuwa ni ne haka kawai zuciyata ta kasa nutsuwa. Na ji ko runtsawa ba zan iya yi ba idan har ban yi kwalli da kyakykyawar fuskarki ba".

"Amatullah wane shi? A ina kika san shi?". Amira ta yi magana a karo na farko. "Amira shi ne wanda na ba ki labarin wanda muka haÉ—u a inda na kai talla yau". Ban jira amsarta ba na juya ina fuskantarsa da kyau na ci gaba da maganata.

"Na roƙe ka da girman wanda yake yi mana ruwa da ƙanƙara kar ka ƙara sako ƙafarka cikin layin nan, me ye kake so da ni? Don Allah kar ka ja mini masifa da bala'in da kaina ba zai iya ɗauka ba".

"Amatullah ba na nufin da masifa ko bala'in face alkhairin Allah".

"Wani irin alkhairi?".

"Ƙauna ce tafe da ni kuma ina fatan za ki amshe ƙoƙon barana". Takaici ya mamaye zuciyata"ba na soyayya kuma ba zan fara akan ba don haka ka yi haƙuri Abbana bai ba ni damar tsayawa da ko wani ɗan namiji ba a hali yanzu". Ina gama faɗin haka na ja hannun Amira muka bar wajen muka shiga zaure ɗalibaina suka zuro mana ido. Nan take na sallame su duk suka watse muka zauna ni da Amira.

"Shi ne za ki tursasa mini fita kuma ki kasa cewa komai a gabansa. Kika bar ni ni kaɗai ina ta magana". Ta ɗan murmusa kafin ta ce"na ga ai ba cutar da ke ya zo yi ba shi yasa na yi shuru. Soyayya ce ta kawo sa kin ga kuma babu yanda za a yi na farraƙa tsakanin masoya".

Babu shiri na kai mata duka ta kauce tana ƙara ƙyalƙyale wa da dariya. Na miƙe tsaye ita ma ta miƙe na naɗe tabarma ina cewa"zan shiga ciki kar Abba ya ce na daɗe. Idan Allah ya kai mu gobe za mu tattaunawa".

"Cab! Ni kuwa kin ga yanzu ma zan je na ƙarbo awarata a fita tuya". Na taɓe baki"Allah ya ganar da ke". Ba ta amsa ba illa dariyar da ta yi muka shigo ciki tare ta yi ɗakinsu na yi namu. [7/17, 1:21 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

___________________________________

Page 1️⃣0️⃣

Kamar ƙadangaruwar bayan murhu haka na shigo ciki ina raɓe-raɓe iwa munafuka ko kuma wacce ta yi wa Sarki ƙarya, na nema waje na zauna a falo kasancewar na jiyo Umma da Abba suna tattaunawa a cikin uwar ɗaka. Kamar ko yaushe muryar Umma ya ɗara na Abba sai hayagaga take yi kamar za ta yi aron baki. "Manniru ni fa ba ƙaramar yarinya ba ce da za ka tisa ni a gaba ka yi min wannan zancen banza da na wofin. Da yake ni ce karkatacciyar bishiyar kuka mai daɗin hawa shi yasa kowa ya ɗebo shararsa sai ya watso min, kai da danginka kun uzura min kun sako ni a gaban akan yarinyar da babu wanda ya taya ni goyan cikinta na tsawon watanni tara balle a kawo min tallafi yayin da nake nishin naƙudanta. Kowa ya ɗebo warin bakinsa zai nufo wai ina ƙoƙarin lalata tarbiyyar yarinyar nan".

"Ni kike kallon tsabar idona ki gaya min wannan zancen?". A kaurare na tsinkayo muryarta tana mayar masa da martani kamar wacce take jira ya ce kule ta ce cas.

"An gaya maka É—in na ce an gaya maka. Manniru ka yi duk abin da ka ga dama ga fili ga mai doki, babu wanda zai dakatar da kai balle ya hana ka wanzar da abin da zuciyarka ta yi niyyar aikatawa, ko ce maka aka yi ina tsoro ko shakkanka ne? Ai wallahi an sha ni na warke kan mage ya daÉ—e da wayewa".

"Ba zan taɓa iya aikata abin da zuciyata ta saƙa min akan ki ba. Allah ya sani kuma shi ne masanin abin da yake taskace a cikin tsokar zuciya kina da girma da matsayi a wajena ta yadda duk abin da kika yi zan jure shi, kuma na yi miki uzuri. Amma kin ga wannan harshen naki Hafsatu ina jiye miki zuwan ranar da zai yi silar fadawarki cikin halaka, DAFIN HARSHE ya fi dafin maciji illa da saurin nakasa sassan jikin ɗan adam". Gama maganar da fitowarsa sun yi daidai da lokacin da ƙwallan da suka wadaci koramar idanuna samun hanyar kwaranya. Ya kafe ni da ido da hakan ya sani yin ƙasa da idanuna. Sai da ya zauna kafin ya ba ni umarnin zama, na nema waje na zaune kusa da kujerar da yake zaune.

"Kukan me ye kike yi Amatullah?".

Na yi saurin kawar da hawaye da suka ɓata mini fuska kafin na sama sararin cewa"babu komai". Ya yi ɗan jim kafin can ya ci gaba da magana. "Har baƙon nakin ya tafi?". Babu shiri na ɗago kaina ina dubansa mamaki da tsoro kwance luf a bisa fuskana ban ƙara shan giyan mamaki ba sai da ya ƙara jefa mini wani tambaya a karo na biyu da ya kusa sanya nokinan kaina suncewa take na soma haɗa gumi duk da sanyi da ni'iman Ubangiji da ya lulluɓe garin.

"Me kuka tattauna da shi?".

Na gyara zamana kafin na iya raba tsakanin haƙwarana da suka manne da junansu kamar mayen ƙarfe aka sanya a tsakanin su. "Abba ba fa waje na ya zo ba. Baƙon Amira ne....". Kafin na ƙarisa ya ɗaga mini hannu alamar baya buƙatar sauraron jin ragowar bayani. "Amatullah". Ya ƙira sunana cikin kaushashshen amon da ya ƙara sanya ni na sha jinin jikina ainun. Kamar kazar da aka jefa da ruwan gishiri na amsa da ƙyar. "Na'am Abba". "Me yasa kike so ki sauya daga yanda na san ku a baya? Shin zuciyar ba ta tausayina akan irin fafutukan da nake yi wajen ganin na inganta tarbiyan, na tsaya kai da fata don tabbatar da cewa ba ki sauƙa daga kan gwadaben da kika taso a kai ba. Amatullah ina sa burin ganin rayuwarki ta inganta na ƙayatar da ita sa ilmi da tarbiyya daga yanzu har izuwa lokacin da zan miƙa ragamar rayuwarki a hannun mijinki".

Take hawaye suka ɓarke mini ban iya cewa komai ba har ya ɗaura daga inda ya yi birki. "Ke ce duk wani buri da fatan da nake da muradin wanzuwansa a bayan ƙasa kafin na koma ga mahaliccina. Ba zan hana ki soyyaya ko na katange ki ɗaga kula kowa ba don yanzu kin yi hankalin da za ki iya tantance abun da zai dace da ke ko akasin haka. Amma a duk lokacin da kika ji a ranki kin fi buƙatar aure akan karatun da kike yi, to kar ki ji nauyin sanar da ni haka. Ni kuma na yi miki alƙawarin aurar da ke a lokacin da kika buƙata domin gujewa afkuwar ɓarna da yin dana sani a gaba".

Wani irin gumjin kuka ne ya zo mini mai ƙarfin gaske, gabaɗaya falon ya ɗauki sautin kukan. Na ja jiki na ƙara matsowa dab da shi na riƙe ƙafarsa gam sannan na kwantar da kaina a jiki. "Abba na tuna na yi nadama, ka ji tausayi na ka yafe miji wallahi ba zan ƙara aikata makamancin irin hakan ba. Na yi alƙawarin ba zan ƙara yin abun da zai ɓata maka rai ba". Bai ba ni amsa ba har sai da na cire tsammani.

"Ko kaɗan ba ki ɓata min rai ba Amatullah. Sai dai na ji ciwon ƙaryan da kika haɗa kai da Amira kuka yi min wanda na san ba halin ki ba ne hakan. A ina kuka haɗu da shi? Tsawon wani lokaci ya ɗaura yana zuwa wajenki? Sannan me yasa Amira ta ce ita ya zo nema bayan sunanki aka ambata?".

Tagwayen ajiyan zuciya na sauƙe da ya tafiyar da kukan da nake yi na koma sauƙe ajiyar numfashi akai a kai, tamkar wacce ta fafata a gasar fidda zakaran gwajin dafi na tseren gudu. Sai da na fizgo numfashina da yake maƙalewa a ƙirji kafin na amsa masa jerin tambayoyin da ya watsa mini a lokaci guda. "Wallahi ban taɓa ganin sa ba sai yau, ɗazu ne muka haɗu a inda na kai talla shi ne muka sama matsala da wasu ƴan mata har suka zubar mini da kunun kuma suka neme ni da faɗa. Shi ya hana su dukana kuma ya biya ni asarar da suka yi mini ya dage akan sai ya rako ni don tabbatar da na iso lafiya saboda sun yi ikirarin tare ni a wani wajen. Abba na rantse maka har da Sarkin da ya halicci sammai da ƙassai bakwai ba tare da wani ko wata ya kawo masa taimaka ko ba wannan shi ne gaskiya yadda muka haɗu da shi. Kuma ko yanzu ma sai da na roƙe sa akan kar ya ƙara zuwa yana nemana na ƙara tabbatar masa ma ba zan ƙara kai talla inda muka haɗu da shi ba. Amira kawai ta taimake ni ne don ta ga yadda gabaɗaya na rikici na kasa magana".

"Na yarda da ke Amatullah ba ni da shakka ko kokonto akan duk abin da zai fito daga bakinki. Ba da son raina ko aminvewata kike wannan tallan ba amma da iznin Allah na kusa kawo ƙarshen abun. Ki kwantar da hankalinki ki dinga taka-tsantsan da mutane don yanzu duniyar ta lalace".

"In sha Allah zan kiyaye". Kansa kawai ya gyaɗa bayan ya tallafo kaina na tashi daga jinginar da na yi a jikin ƙafafunsa. Ya miƙe zai shige ciki na yi hanzarin riƙo gefen rigarsa. "Abba kar ka je ka kwanta da tare da bakinka ya furta kalmar yafiya gare ni ba. Hakan zai jefa ruhina cikin ƙunci da rashin nutsuwa". Kyakykyawar ajiyar zuciya ya sauƙe da har sai da na jiyo sautin fitarsa kafin ya ce da ni wani abun da ya sanyaya sashin ruhina da nake jin kamar ana watsa mini garwashin wuta.

"Ko ban yi amfani da kalmomin baki wajen furta kalmar yafiya a gare ki ba. Zuciya ba za ta yi dogon zango tana dakon fushi da ke ba Amatullah. Na yafe miki kuma daman ba ki ɓata mini ba". Sakakken ajiyan zuciya na sauƙe ina jin kamar an sauƙe mini wani ajiyan da aka yi mini a ƙirjina na kasa magana sai kuka, lallashina ya yi sosai har na dawo daidai kafin na yi masa sai da safe na cike cikin ɗakin. Lokacin Umma har ta yi bacci, ta kwanta a gefenta sai dai sam bacci ya ƙi kawo mini ziyara sai da na raba dare kafin na sama na iya runtsawa.

Washe gari haka na tashi da matuƙar ciwon kai ko kaina ban son ɗagawa balle na buɗe idanuna. Ina kwance a inda na yi sallan asuba, Umma ta ɗago labulen tana ƙira na na tashi na zauna kafin ta fesar da abin da yake tafe da ita. "To ki tashi ki zo ubanki yana ƙiranki". Na tashi na rufa mata baya muka fito tare, na zauna a ƙasa yayin da ita kuma ta zauna a kujerar da Abba yake zaune kusa da shi. Shuru ya ratsa wajen kafin Umma ta buga tsaki.

"Ka tara mu ka ce za ka yi magana, mun zo kuma ka saka mu a gaba kana kallonmu. Idan ba ka da abin da faɗa ne ka sallame mu, don ni ina da abin da ya fi wannan zaman muhimmanci wanda zan yi". Wataƙila da Umma ta sama tagomashin kasancewa cikin mata masu lura da karanta ma'anar shuru da rabe-rabensa da ta fahimci shuru da kallon da Abba ya yi mata, yana bayyanar da ɗacin da maganarta ta yi masa ne. Amma sai dai kash! Ko a jikinta wai an mintsini kakkaura ko gizau ba ta yi ba.

"Na tara ku duka ne domin na sanar da ku wani hukuncin da na yanke wannan yake kamar umarni ne a gare ku". Umma ta katse shi ba tare da ya dire zancen ba"to muna jiranka sai ka tafi kai tsaye ga saƙon da kake son isarwa ai, ba sai ka tsaya kana wani kame-kame ba".

"Ina so na sanar da ku a cikin satin nan za mu tashi daga gidan nan. Don haka tun yanzu ku duk shirin da za ku yi".

Tun kafin ya gama zancen Umma ta yi zumbur ta miƙe tamkar wacce aka yi wa alluran doki, ta yi sakeke tana kallon Abba baki sake. Ta toshe kunnuwanta tana cewa"ban gane abin da kake faɗa ba Manniru? Ka yi bayani da harshen da zan fahimta ƙwaƙwalwata ta gaza amsar sauƙon da kake ƙoƙarin isar mata. Mu bar gidan nan mu je ina? Ina muke da shi bayan nan? Ko kuma kawai so kake ka yi amfanin da ikon da kake da shi a kanmu ka tozarta mu a idon jama'a?". "Yadda kunnuwanki suka jiyo miki haka na faɗa Hafsatu za mu tashi daga gidan nan tashi na har abada. Ki fara shirya kayanki tun yanzu".

"Wallahi ba ka isa ba. Ba zan taɓa zuba ido wannan abun ya faru ba, Manniru anya kana lafiya kuwa ƙwaƙwalwarka ba ta sama matsala ba?".

"Zan ga tsakanin ni dake waye yake auren wani. Na yi rantsu ba zan yi kaffara ba ki isa ki sauya min ra'ayi akan wannan lamarin ba, dole ne mu bar gidan nan don ba zan zuba ido ina kallo tarbiyan ƴata tana lalacewa ba. Duk gini da foundation ɗin da na yi don inganta rayuwarta yana rugujewa ba, ba zan laminta ba". "Da an yi magana ka ce ƴa ƴa kamar ka fi kowa ƴa ko a kanka kawai aka fara haihuwa. Duk mazauna gidan nan ba su ce tarbiyyan ƴaƴansu zai lalace ba sai kai uban masu ba da tarbiyya. Wai tarbiyyan nan kai ne kake yin ta ko taimakon Allah ne? Manniru kar ka biye zuciyarka ka cutar da mu babu gaira babu dalili, ka sani na sani daga kai har ni duk ƙoƙarinmu wajen tarbiyya ba zai iya sa yarinyar nan ta kasance cikin amintattu ba, face sai Allah ya dafa mana. Iyaye nawa ne wanda suka kasance manyan malaman addini amma ƴaƴansu suka fi kowa kangarewa da lalacewa ba. Ga misali nan Manniru Allah ya buga mana akan Annabi Nuhu wanda shi annabin Allah ne ma amma iyalinsa suka kauce hanyar da yake. Shi kuma sai ya ce me ye a Ubangiji?".

Ɗan jim Abba ya yi don ta gama ɗaure sa da jijiyar jikinsa. "Ko me ye za ki faɗa barin gidan nan wajibi ne. Saboda gujewa faruwar abubuwa da yawa don haka na gama magana, kina da zaɓi biyu ko ki haɗa kayanki mu tafi tare ko ki yi zamanki a nan ki ci gaba da ɗaukar nauyin kanki kamar yadda kike ikirarin kina yi". Yana dasa aya a nan ya fice ransa a matuƙar ɓace. Ihu Umma ta kurma kamar za ta yi hauka ta zube ta yi zaman ƴan bori. "Shikenan na shiga uku na lalace! Ni kake yi wa kora da hali Manniru? Dole na tashi tsaye a cikin gidan nan. Na rantse ba za mu taɓa tashi daga gidan nan ba ko za ka haɗiye zuciya ka mutu dare ɗaya......". Ba ta ƙarisa ba na yi hanzari tashi na je na rufe mata bakinta. "Don Allah Umma ki yi haƙuri. Ki dinga yi salati zuciyarki za ta yi sanyi, ba daɗe irin wannan maganar ko kaɗan". Ta ture hannuna kafin ta ce"Amatullah ya ya zan yi da raina? Idan muka bar gidan nan ina za mu dosa? Sanin kanki ne ba mu da wani matsugunin da ya wuce nan, a nan ne kawai asirinmu zai rufu amma ubanki ya dage sai ya tona mana asiri sai ya fallaso sirrinmu ga duniya. Wallahi ba zan taɓa barin hakan ya faru ba tashi ki ɗauko min hijabina na fita".

"Umma ina za ki je a cikin wannan halin da kike ciki?".

"Wajen Malam zan je don shi kaÉ—ai ne zai share min hawaye nan take". [7/18, 11:05 AM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_______________________________________

Page 1️⃣1️⃣

Ganin tana ƙoƙarin tashi ya sani saurin cafko hannunta ina yi mata magiya"don girman Allah Umma ki rufa mana asiri kar ki je ko'ina. Da bakinki fa yanzu ki ka ce Abba yana so ya tona mana asiri amma asalin tonon silili zai faru ne daga loakcin da kika je kika baje wannan lamarin a wani can da daban da yake bakewa da malunta yake aikata abin da ba shi ne ba". Zafin marin da ta sauƙe mini a gefen kuncina na hagu shi ya sani haɗiye ragowar zancen ba tare da na furzo shi waje ba, kafin na yi aune ta ƙara sauƙe mini wani marin a karo na biyu da sai da ya tursasa mini sakin ƙara. Tsabar azaba da zogin da fatar wajen yake yi mini da nake jin tamkar ruwan tafasasshen ɗanyen dalma aka watsa mini.

"Sai yau na tabbatar har yanzu ba ki da hankali Amatullah girman jiki ne kawai da ke amma hankali kam sam babu shi a tattare da ke. Don ya wulaƙanta ni sai da ya ƙira yo ki sannan ya yi wannan ikirarin, ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba wannan duk shiri da tuggun Maman Umar ne kuma sai na nuna mata ina daidai da zamaninta. Manniru kai da ka bar gidan nan wallahi sai dai a cikin makara amma zaman daram yanzu ma aka fara sai mun ga abin da ya turewa buzu naɗi". "Umma ki tuna fa komai ya yi zafi maganinsa Allah shi ne ya ke juya dare zuwa rana. Ya yaye ƙunci ya wanzar da farin cikin a zuciyar da cikinta babu kusuni. Me zai hana ki yi alwala ki yi salla raka'a biyu ki ba shi zaɓi ya zaɓa mana mafi alkhairi". Ba ta ce da ni komai ba illa bangaje ni da ta yi gefe guda ta shiga ɗaki ta ɗauko hijabinta ta fita, zubewa na yi a wajen na kwanta na yi luf ina sakin wani maraya kuka marar sauti.

Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau ji nake yi kamar na tashi na ruga da gudu na je na dakatar da Umma daga abin da yake shirin aikatawa, sai dai gangar jikina ya ƙi ba ni haɗi kai wajen motsa ɗaya daga cikin gaɓoɓina. Har na ci gaba da kwanciya har izuwa lokacin da Amira ta shigo ta iske ni cikin mayuwayacin hali. Cikin tashin hankali ta iso inda nake zube ta ɗago ni sai dai na kasa tashi dole na koma na zauna na kifa kaina akan gwiyoyina ina ci gaba da kukan.

"Amatullah me ye ya faru?". Ta jefa min tambayar muryarta tana rawa, rashin samun daga gare ni bai hana ta ci gaba da tambayar duk abin da take tunanin shi ne sanadi da musabbabin kukan nawan ba. "Ko dai mutuwa aka yi muku ne?". Na jijjiga mata kaina alamar a'a kafin na yi nasarar cira kaina ina duban ta da kumburarrun idanuna da suka rikiÉ—e suka sauya kala zuwa launin ja. "Da abin da yake shirin faruwa ai gwara mutuwar ma Amira. Tun da dai shi wanda ya mutu ya huta daga rikici da fituttunun duniya sai dai ya je ya tarar da abin da ya shuka".

Ta waro idanunta tar a kaina"ke kin san zafin mutuwa kuwa? Ko don har yanzu kina ganin iyayenki biyu kuna rayuwa tare? Billahillazi mutuwa ta fi komai ciwo da raÉ—aÉ—i don har yanzu zuciyata cike take da gurbin rashin mahaifina duk da ya rasu tun kafin na mallakin hankalin kaina. Kuma alhamdulillah Baba Habu mijin Umma bai bar ni na yi kukan maraicin uba ba".

"Wani babban lamari ne yake dab da faruwa ko ina ce warhaka kam komai ya faru".

"Ki sanar da ni me ye yake faruwa don Allah, kar ki bar ni cikin duhu Amatullah".

Dogon numfashi na ja na fesar kafin na zayyana mata duk abin da ya wakana ban ɓoye mata komai haka nan ban tsallake ko da layi guda ba. Ta yi shuru kamar mai tunanin wani abu kafin can ta yi magana. "To amma ke me ye kike tunanin ya sanya Abba yanke wannan hukuncin lokaci guda haka?". "Ban san dalilinsa na yanke wannan hukuncin ba kuma cikinmu babu wanda ya tambaye sa".

Ta gyara zamanta kafin ta soma cewa" Samu gidan hayan a ƙurarran lokaci fa abu ne mai matuƙar wuya gwara ma ina kana da kuɗinka a hannu. Kuma ko da kuɗinka ma ba za ka sama yadda kake so ba, shi yasa gaskiya ni ban ga laifin Umma ba. Me ye amfanin a yi abun da daga baya za a zo ana dana sani?". Mamaki kwance a fuskana nake bin ta da kallo saboda dukan da zantukanta suka yi wa kwanyata. "Kina nufin ba ki ga ma rashin dacewar abin da Umma za ta yi a addinance ba kenan?". Ta riƙo hannuna"har ga Allah ban ga ni ba, don a tunanina haƙƙin kowacce uwa ne samar da daidaito a rayuwar gidan aurenta. Kuma Umma ta fi mu tunani ba za ta taɓa yanke hukuncin da zai cutar da ɗaya daga cikinku ba don haka kawai ki goya mata baya". Na fizge hannuna"kin manta wajen wanda na ce miki za ta je ne Amira? Wannan Malamin ba da yake fakewa da addini yana aikata alfasha. Ta inda mutum kamar ta mai ƙafafu biyu zai taimaka maka bayan shi ma mabuƙaci ne a wajen Allah?".

Taƙaitaccen murmushi ta yi tana kallona da wutsiyar idonta ta furta"amma kin san aikinsa yana tasiri akan ko waye kuma an yi ittifa'i ba a taɓa zuwa masa da kukan da ya kasa gogewa mai shi hawaye ba. Bari na sanar da ke wani sirri ko Ummata da shi ta dogara wajen kankaro mutunci, daraja har da kima a idanun Baba Habu". "Kina nufin Ummanki tana zuwa wajensa? Tirƙashi!". Na yi mata tambayar a rikice. Ta gyaɗa mini kanta"ƙwarai kuwa har ma tana aike na na karɓo mata saƙo daga wajensa". "Innalillahi wa inna ilaihir raji'u! Shikenan mun shiga uku!".

Na furta cikin maɗaukakin tashin hankalin gami da firgicin da yake ƙoƙarin tarwatsa zuciyar da take dashe a cikin ƙirjina. Da mamaki babu ko ɗigo mamaki balle kiɗima a tattare da Amira. "Me ye abun cewa mun shiga uku Amatullah? Ni da wannan kalmar tsinka min zuciya take yi, zamanin ne ya lalace an daina kiwon dabba an koma na mutum. Ba ka damu da mutum ba amma shi yana can yana hana idonsa runtsawa a ƙoƙarin ganin ya ga bayanka kin ga kuwa ai dole ka tashi ka kare kanka, tun da ko Allah ma cewa ya yi sai ka tashi sannan zai taimake ka". Takaici ya zo mini har wuya wani ɗaci ya gauraye da yawun bakina ya jirkita shi gabaɗaya ta yadda sai da na ji kamar na yi amai. Da ƙyar na haɗiye sa ta hanyar wuyana ya wuce kamar na haɗiye ƙarangiya.

"Ai ba irin wannan lamarin ake nufi ba. Ta yaya za ka je wajen wanin Allah kana neman taimakon da shi kasan in ya tsinci kansa a cikin irin halin da kake ciki ba zai iya samarwa kansa mafita ba, kina ganin akwai basira a cikin aikata hakan?". Ta taɓe baki tana jefa da wani irin kallo alamar ta soma gajiya da fahimtar da ni abin da kaina ya gaza ɗauka balle ƙwaƙwalwata ta amshe shi. "Ni kam ban wani irin taurin kai Allah ya zuba miki ba. In da kin fito a cikin mutanen farko irin riƙaƙƙun kafiran nan zai yi wuya ki karɓi musulmci, ga zahiri nan ki na kallo amma kuma runtse ido . Amatullah ya zama dole fa mu amshi abin da zamani ya zo mana da shi, mazan ne yanzu sai da haka sai ana danganawa ga Malamai kafin a shawo kansu. Na rantse miki ba don irin wannan taimakon daga malamai ba da yanzu wani maganar ake yi ta daban mussamman Baba Habu da Allah ya yi wani irin murɗaɗɗan mutum mai wuyar sha'ani, a hakan ma yaya balle kuma an zauna haka nan".

Ni kam shuru na yi don gabaɗaya na rasa me ye zan ce da ido kawai nake bin ta har ta kai aya. Na ja wani gauron ajiyar zuciya na fesar kafin na gyara zamana, na soma ambaton Allah a cikin zuciyata. Ina da tabbacin shurun da na yi ne ya sanya ta ta ture komai ta koma kwantar mini da hankali da kalamai masu taushi da sanyi. Har sau da na ji raina ya sanyaya, na ƙara yarda a duniya bayan iyaye da dangina ba ni da wacce take yi mini irin ƙaunar da Amira take gwada mini wanda babu sirki a cikinsa.

"Yanzu dai ki tashi mu gyara ɗakin nan. Sannan na ba ki wani daddaɗan labari". "Fara ba ni labarin tukunnan". Na yi zancen cikin dauriya ina ƙoƙarin dasa murmushi a fuskana. "Mansur yanzu haka yana hanya. Saura kuma in munje ki ɗaure fuska ki yi ta shan magani". Ta ƙarishe zancen tana galla mini harara.

"Allah ya kawo shi lafiya". "Amin ta hannun dama.Don Allah ki saki ranki ke ba wani shegen kyau kike da shi ba kuma ki zo kina wani ƙara haɗe hanci da gira duk sai ki ƙara muni". Ta ƙarishe zancen tana galla mini harara.

"Ai kuwa a hakan kin san na fi ki kyau sau dubu ɗari". Ta fashe da dariya tana faɗin"kin dai fi mi auki shi ma kuma girman buredi ina gaya miki, amma ni ba ta yau ba ce". Daga haka duk muka saka dariya kamar babu wani abun da ya faru, wannan dalilin yana daga cikin muhimman dalilin da yasa nake jin Amira har ƙasan raina. Don ba ta jure ganina cikin ƙunci duk yanda zai ta yi sai ta yi ta fitar da ni daga halin da nake ciki. Tare da ita muka yi komai har na ɗumama mana ragowar abincin jiya muka ci ita ma ta amso mana waina a wajen Ummanta muka ci muka yi hani'ƙan, sai na ji duk damuwar da na tashi da shi na neme shi na rasa sa. Muna gamawa wayarta ta soma ruri ta hasko mini fuskar wayar tana faɗin"kin ga Mansur ne". Ta ɗaga ya sanar da ita ya zo muka tashi muka fito har mun zo zaure kafin ta soma ba ta labarin yadda muka yi da Abba daren jiya. Ta ja ta tsaya riƙe da kunkuminta tana kallona.

"Kina nufin Abba ya gane gaskiyar komai? Mun shige su". Na gyaɗa mata kaina alamar e. "Wallahi ya gane komai amma na ba shi haƙuri ya ce komai ya wuce sai dai na kiyaye gaba". Ta murmusa kafin ta ce"Allah sarki! Abba wallahi sauƙi halinsa da yanda yake kulawa da tarbiyyanki wani lokacin yana sani kewar mahaifina sai na ji duk duniyar na yi mini zafi".

Na kai mata duka a kafaɗarta"ke dai kam ki godewa Allah don Baba Habu bai rage ki da komai ba". Ta sauƙe numfashin da har sai da na jin sautinsa kana ta ce"Amatullah ba za ki gane raɗaɗin irin ciwon nan. Babu wanda yake maye gurbin iyayen sai dai kawai a kamanta". Tana gama maganar ta yi gaba ta bar ni.

Na fita a baya muka je wajen Mansur yana tsaye a jikin motarsa tana latsa wayarsa yayin da wani abokinsa take kusa da shi, da sallama ɗauke a bakinmu muka isa wajen su suka amsa mana yayin Mansur yake tattara dukkan hankalinsa kan Amira. "Gimbiya kin fito?". "Ai ka san ba zan zo na bar Sarkina a tsaye ba". Ta saki murmushin jin daɗi zai yi magana na katse shi. "Tun da na ga alama idanunka ita kaɗai yake gani, babu amfanina gwada na ja ƙafafuna na koma".

"Afuwan ranki ya daÉ—e. Idanuna sun ganki amma zuciyar ce gabaÉ—aya tana tare da ita. Ya kike ya gidan?".

"Lafiya ƙalau ka zo lafiya". Ya amsa cike da kulawa"lafiya sai dai na tabbatar da zaran na bar nan zan zama majiyanci ne". Amira ta yi masa wani kallo da hakan ya sanya sa cewa"e mana tun da sai na shafe sati guda ban yi tozali da ke ba. Wallahi Amira ba don Alhajinmu ya matsa min akan lalle ni zan wakilce sa a wannan taron ba, babu wani dalilin da zai sa na yi nisa da ke". Jim ta yi gabaɗaya jikinta ya mutu yanayinta ya sauya ta kasa cewa komai illa kallon juna da suke yi.

Ba su dawo duniyar zahiri ba sai da abokinsa ya yi magana"ni ma tun wuri bari na san inda dare ya yi min. Don na ga alama an manta da ni ".

Mansur ya ce"Haba kai kuwa Mukhtar ni na isa na manta da kai. Kawai dai ka san an ce sawun giwa ya danne na raƙumi". Dukkan mu muka fashe da dariya sai da muka tsagaita Mukhtar ya kallo ni yana cewa"kin ga ƙawarmu waɗannan mutanen ba ta mu suke yi ba. Ya fi dacewa mu matsa mu ba su wajen". "Ai kuwa na ga alama". Na yi maganar yayin da nake bin bayansa muka matsa gefe, mun ɗan yi hira jifa-jifa kafin Amira suka yi sallama da Mansur. Da ya buɗe bayan boot ɗin motarsa ya fara sauƙe mata manyan ledodi sai da abin ya ba ni tsoro aƙalla sun kai bakwai a ƙidayen da na yi kuma dukkannisu shaƙe suke da kaya. Har da kukanta da Mansur zai tafi shi ma duk yanayinsa ya sauya haka ya shiga mota ya tafi bayan ya yi mata alƙawarin ƙiran ta da zaran ya isa garin da zai je. Muka kwashi ledodin wanda za mu iya muka shiga da su ragowar kuma muka saka yara suka shigo mana da shi. Ina cikin lallashina Amira a ɗakinsu Umma ta aiko ƙira na na tashi da hanzari na je. [7/19, 7:42 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

______________________________________

Page 1️⃣2️⃣

Tana zaune a falo ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya ta kwantar da kanta a jikin kujera ta lumshe idanunta kamar mai bacci. Gaban ta wani baƙin leda ne a ajiye. Sai da na nema waje na zauna kafin na ce"sannu da dawowa". Ba tare da ta buɗe idanunta ba ta amsa mini tana ci gaba da cewa"ki haɗa wuta ki ɗaura min ruwan kunu". Na ɗan jim kafin na ce"Umma lokacin islamiyya fa ya yi". Sai a sa'ilin ta buɗe idonta tana kallona"ai tun da ba ki da safe ba to tabbas sai kin fita na rana". "Ranan nan ma fa ban sama zuwa, da kin yi haƙuri yau ɗin na je ko da yamma inna dawo sai na fita da kunun". Ba ta ce da ni komai ba ta ta shi ta ɗauki ledar ta shige cikin ɗaki ba ni da zaɓi dole na tashi na fito na huta wuta na ɗaura ruwan da ta umarce ni na zauna na zabga tagumi sai da ruwa ya tafasa na je na sanar da ita ta fito ta dama kunun yayin da na shiga ciki na gabatar da sallan zuhr. Na fito na yi wanka na fara shirin fita idona ya raina fata lokacin da ta miƙo mini kwallin ta ce na saka a idona bayan ta gama turare bokatin kunun da hayaƙi.

Zuciyata kamar za ta tsago ƙirjina ta bayyano waje tsabar bugawan da take yi duk kuka da magiyar da nake yi wa Umma hakan bai yi tasiri ba, dole ƙanwar naƙi na karɓa kwalli na saka a idona. Na ɗaura bokatin a kaina na fita ina tafe ne kawai amma ban san inda nake cilla ƙafafuna ba mussamman da na ga duk layin da na wulga sai jama'ar wajen su bi ni da kallo. Gabaɗaya sai na ji ni duk a takure na kasa sakewa. "Amatullah Mannir". Na tsinkayo amon muryar Malam Suleiman Malamin ajinmu a islamiyya kamar daga sama, a hanzarce na waiga ina kallonsa yayin da shi ma ɗin ni yake kallo kallo irin na mamaki.

"Ina wuni Malam".

Na gaishe shi sai dai maimakon ya amsa sai ya ƙara dawo mini da wata tambayar. "Ina za ki je haka bayan lokacin islamiyya ya yi?". "Yau ba zan sama zuwa ba ne". "Me yasa?". "Zan je talla ne". Ya yi shuru na tsawon wasu daƙiƙu kafin ya furta"waye ya sa ki tallan?".

Muryata tana rawa na ce"Ummata". "To mu je islamiyya sai ki ajiye tallan a staff a wajena ki wuce aji, wataƙila a can sai ya ƙare".

"Malaman ba kayan islamiyya ba ne a jikina da kuma na baro jakata a gida". Ya ɗaure fuskarsa tamau"wuce mu je kafin na sassaɓa miki". Ban kuma cewa komai ba ya wuce gaba ina bin sa a baya har muka isa islamiyyan na ajiye kunun a staff kamar yadda ya ce. Ya ɗauko ƙur'ani ya ba ni ya ce da ni na wuce ajinmu. Haka na wuce ajin na je na zauna muka fara kara karatu, ko da muka fito sallan asr ban yarda mun haɗu da Ammi da Rauda ba don na san zan sha tambayoyi a wajen su, ina yin salla na koma aji na yi zamana ba mu tashi ba sai ƙarfe biyar muna yin addu'a na fito da saurina zan tafi Rauda ta dakatar da ni.

"Don Allah Amatullah ki tsaya".

Sanin girman wanda ta haɗa ni da shi ya sani tsayawa har ta iso gabana hannunta saƙale cikin na Ammi. "Wai me ye yake faruwa ne kwana biyu ba kya zuwa? Yanzu kuma kin zo amma sam ƙi yarda ki haɗa inuwa ɗaya da mu". Ammi ta ci zancen cikin damuwar da ya bayyana har a cikin kalamanta, kafin na ba ta amsa Rauda ta karɓe zancen"kin san Allah yau muka ce idan ba ki zo ba daman za mu ke gidanku mu duba ko lafiya".

Cikin ƙosawa da sauraran zantukansu na furta"lafiyata ƙalau kamar yadda kuke gani ai babu alamar jinya a tattare da ni". "Amma ai akwai alamar damuwa a tattare da ke". "Don Allah Rauda mu bar maganar nan. Tun da yanzu kam na zo ai shikenan ko". Ina dasa aya na sa kai zan wuce wajen Malam Suleiman suka ƙara tsayar da ni.

"Wallahi Amatullah akwai wani abu da yake faruwa ko ma ya riga ya faruwa don ba haka kika saba zuwa ba. Kuma yaya Musbahu ya ce min ya gan ki kina talla a filin taurari, inda duk wata mai tarbiyya da kamun kai ba ta sanya ƙafarta cikin wannan filin. Me yake faruwa Amatullah?".

Ban yi aune ba na ji ƙwalla sun ciko mini kurmin idaniyata sai dai na yi jarumta da ƙarfin hali ban bari sun tsiyaya ba. Na ja dogon numfashi kafin na sama sararin faɗin"zan yi muku bayanin komai amma ba yanzu ba". "Sai yaushe kenan?". Na toshe kunnuwana"don Allah ku yi haƙuri ku bar ni haka. Na ce zan faɗa muku idan lokaci ya yi". Ina gama faɗin haka na bar wajen da matuƙar sauri na nufi staff wajen Malam Suleiman, shi kaɗai na samu duk ragowar malaman sun watse kasancewar lokaci ya fara ƙurewa. Sai da na yi sallama ya amsa kafin na shigo na tsuguna raina ya yi wani sanyi kamar an ɗaura mini ƙanƙara ganin bokitin kunun saura kaɗan.

"Amatullah".

Sautinsa ya dawo da ni cikin duniyar zahiri, na gyara tsugununan da na yi a nutse na ce"na'am Malam". "Me yasa ba kya zuwa makaranta kwana biyu da suka wuce?". "Malam ba na samun dama ne. Idan na fita talla ba na dawowa da wuri kuma idan na dawo da ragowa Umma za ta yi mini faÉ—a".

"Me yasa ba kya fita da wuri?". Na yi shuru don ba ni da amsar tambayar. "Ban hana ki talla ba Amatullah kuma ba ina nufi kar ki yi abin da mahaifiyarki ta sa ki ba. Amma ina mai ba ki shawara da kar ki sake ki yi wasa da damarki, a wannan shekarun ne kawai ki ke da damar yin karatu sosai kafin abubuwa su sauya. Ke mace ce rayuwarki gabaɗaya ƙanƙanuwa ce saura ƙiris ku haɗa hadda ki dage duk runtsi ki na zuwa".

"In sha Allah zan daure ina zuwa". Na amsa a raunane. "Ga kuÉ—inki an saya na É—ari bakwai da saba'in". Na sa hannu na amsa kuÉ—in ina yi masa godiya maimakon na tashi na tafi sai na koma na zauna, hakan ya sa shi zuba mini ido cike da zallar mamakin dalilin da ya sani share waje na zauna.

"Lafiya kuma kika koma kika zauna?". Cike da tsoro na ce"Malam wata alfarma nake nema daga wajenka". Ya tattaro dukkan hankali da nutsuwarsa gare ni"to ina sauraronki". "Malam so nake yi a yi wa mahaifiyata nasiha da kuma tsoritarwa akan wani aikin saɓon Allah da take aikatawa wanda ba zan iya faɗawa kowa ba. Sannan alfarma ta biyu tambaya ce da ni da na daɗe ina buƙatar amsarta na rasa wanda zan tunkara da lamarin. Malam mahaifiyata ta kasance mai kaifin harshe irin mutanen da komai ya fito daga bakinta za ta furzar da shi ga ko waye ba tare da tunanin abin da kan je ya dawo ba. Tun kafin na yi wayo take jefa da mungayen kalamai tsinanniya, shegiya wani lokacin har ta suffata ni da ƴar zina. Kuma ni kaɗai ce ƴarta a duniya balle na yi tunanin son da take yi wa sauran ƴaƴanta ne ya rinjayi wanda take yi mini. Yayin haihuwata ta sama matsala har sai da aka cire mata mahaifa wanda hakan yake nuni da ba za ta sake haihuwa ba bayan ni. Tun abin baya mini ciwo har an kai munzalin da nake kasa bacci saboda damuwa".

Na tsagaita saboda kukan da ya taso mini a lokaci guda na yi na yi son raina ba tare da ya lallashe ni ba kana na ɗaura daga inda na ka burki. "Malam ba yabon kai na sama tarbiyya daidai gwargwado daga wajen mahaifina, ina da kamun kai da nutsuwa. Duk layinmu da ni ake buga misali wajen kyakykyawan hali da ɗabi'un ƙwarai. Amma tsorona ɗaya kar bakin da mahaifiyata take yi mini ya yi tasiri a kaina, ya wargaza duk shiri da tanadin da na yi wa rayuwata. Mahaifina ya sha nusar da ita da fahimtar da ita illar abin da take aikatawa amma kamar ana watsa ruwa a bayan ƙwarya". Jikina ya soma rawa saboda kukan da ya gama galaitar da ni duk da bai ce da ni komai har lokacin amma na ji sanyi a cikin raina. Ko ba komai yau na fitar da damuwar da ta daɗe tana yi mini kai kawo a cikin ƙalbina.

Sai da aka shafa wasu mintuna kafin Malam Suleiman ya ja dogon numfashi ya fesar daga bakinsa da har da na ji sautin fitarsa. Kana ya soma magana cikin jimami da tarin damuwa.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Amatullah ko wani bawa kika ga cikin wannan duniyar yana da tashi irin damuwar. Da za a ba ki tahirin rayuwar wasu mutane sai babu shakka da sai kin yi mamakin yadda aka yi har yanzu suke dariya, rayuwa ce lokaci shi yake warkar da komai. Yanzu kin ga lokaci ya ƙure ki tashi ki je gida gobe idan kin zo sai mu ƙarisa maganar".

Cike da girmamawa na ce"na gode sosai Malam na gode da lokacinka da ka ba ni ka saurare ni". Ina gama maganar na tashi na ɗauki bokitin na ɗaura a kaina zan fita ya tsayar da ni. "Ki cire damuwar komai a cikin zuciyarki. Sannan a duk lokacin da za ki fita talla ki dinga saka hijabi mai girma da zai rufe miki jikinki". "To in sha Allah, na gode Malam". Na amsa cike da kunya ina sadda kaina ƙasa. Lokaci da na fito kowa ya watse daga islamiyyan kafin na iso gida har an ƙira salla, bayan cinikin da Malam Suleiman ya yi mini a hanya na ƙara yin cinikin naira ɗari uku jimillan kuɗin gabaɗaya ya kama dubu ɗaya da naira saba'in haka na koma gida a gajiye ina ajiye bokitin kunun, na yi alwala na yi sallan magrib na fito na haɗa wuta na ɗaura mana abinci kana na koma ɗaki na kai wa Umma cinikin da na yi.

Ban ga damuwa ko tashin jin daɗi a fuskarta ba duk da kuwa ban sayar da kunun gabaɗaya ba. Ki irgawa su ba ta yi ta ajiye su a ƙasan matashi har na tashi zan fita ta ce na koma na zauna na koma na zauna ina sauraronta.

"Mun yi magana da Sahura akan za ki dinga tafiya talla tare da Amira don na ga ta fi ki wayewa da sanin harkan. Da zaran kin kammala haɗa haddarki sai na fara yi miki soyayyar doya da ƙwai kina fita da shi bayan sallan isha'i'.

Na É—aura hannu a ka"na shiga uku Umma. Amira kuma?". Ta gallo mini wata banzar harara"ita ta ko tana da wani aibu wanda ni ban sa ni ba? Da za ki kafa hujja da shi".

"Wallahi inda take kai talla duk maza ne a wajen marasa ɗa'a. Umma kin gan su kuwa? Duk ba su da kamun kai kuma ba sa kunyar haɗa jiki da mace, ko ita Amirar ma ki tambaya za ta faɗa miki". Ta yi sauri katse mini numfashi. "Inna fahimce ki kina so ki ce ita ma kanta Amirar ba ta da kamun kai kenan ko? Idan da kuwa haka take to ina tabbatar miki ke ce ta farko wacce za ta fara gurɓatawa tun da ba ki da wata ƙawa ta kusa sama da ita kullum kuna tare da ita". Na zube ina yi mata rantsuwa"wallahi tallahi Umma kullum muka zauna da ita sai na yi mata nasiha akan abin da take yi ba daidai ba ne".

"Amatullah na gama yanke shawarar dole ki fara bin Amira kuna fita tare har izuwa lokacin da ke ma kanki zai waye". Wani irin zafi da tafasa zuciyata take yi mini na cire leɓena hawaye suna zuba daga idona da ƙyar na iya furta"Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi". Ban jira abin da za ta ce ba na tashi na fita, har na gama girkin hawayen idona bai tsaya ba. Yanayin da nake ciki ya sani sallamar yaran da nake yi wa karatu don babu abin da zai iya aiwatarwa a halin da nake ciki. Ina yin sallan isha'i na kwanta raina gabaɗaya babu daɗi.

Kamar a cikin mafarki na soma jiyo wani tashin sauti da ya sani buɗe idanuna da ƙyar saboda ciwon kan da ya addabe ni. Na laluma gefena ban ji alamar Umma tana kwance a gefe na, na yi zumbur na tashi na jawo tocilan da yake ƙasan matashi na kunna na haska ɗakin ban ga Umma ba. Kuma har lokacin ban daina jin tashin sautin ba.

Haka ya sa na fito falo na haska tocilin daidai inda kunnuwana suke jiyo mini sautin. Babu shiri na yi zaman ƴan bori saboda munin abun da na yi tozali da shi. Umma ce tsaye tana kewaye Abba riƙe da kw turaren wuta tana yi mass hayaƙi, ɗaurin ƙirji ne a jikinta yayin da ta ware kitson kanta ta bar gashin haka ba tare da kallabi ba. Tana wani irin suturai da yaren da tun da na zo duniya ban taɓa jin sa ba balle na san nau'in sa. [7/20, 1:53 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_________________________________

Page 1️⃣3️⃣

Ƙarar faɗuwar tocilan daga hannuna shi ya fizgo hankalinta zuwa gare ni take na ga ta rikice irin rikicewar da tun da ta haiho ni ban taɓa ganin ta cikin makamancin sa ba. Jikinta gabaɗaya ya soma rawa zan iya rantsuwa da Sarkin da ba shi da abokin tarayya ban taɓa ganin ta cikin wannan halin ba, sai dai bushashshiyar zuciyar da take ta shi ya hana ta sa fasa abin da ta yi niyya ba ta dakata da abin da take yi ba har sai da ta gama, wani ƙarin abun mamakin da ya hana ni tashi daga zubewan da na yi shi ne har lokacin Abba bai tashi ba yana nan kwance kamar gawa. Sai da ta ƙara zagaye shi sau uku tana ƙiran sunanta tare da busa masa hayaƙin kafin ta ajiye kwasko a gefe ta nufo ni tamkar kububuwa. Cak ta ɗago ni ta dige ni akan dugadugaina ta finciki hannu kamar za ta raba ta da gangar jikina ta ja ni zuwa cikin ɗaki muna shiga ta cilla ni kam gado ta rufe ƙofar ɗakin kiruf.

"Me ya fito da ke cikin wannan daren?".

Ta watsa mini tambayar babu alamar wasa a tattare da ita yayin da ta dalle mini idona da tocilan da ta ɗauko kafin ta rufe ƙofar ɗakin. Ruɗu da riɗimewar da na yi ya sani kasa cewa komai illa numfashin da nake sauƙewa a wahala. Ta zo dab da ni ta zauna kafin na yi aune na ji ta damƙo gashin kaina da na tufke ta bayan wuyana ta riƙe gam tana gindaya mini sharaɗi.

"To billahillazi bari na ja miki kunne, ki manta da duk abin da kika gani ki É—auka tamkar mafarki kike yi kuma har yanzu ba ki tashi daga baccin da kike yi ba. Idan kika sake na ji labarin nan a wani wajen sai kin yi mamakin abin da zan aikata gare ki, ki burne duk abin da kika gani a yanzu don na tabbatar da cewar sai kin fi kowa amfanar abin da na aikata a nan gaba kaÉ—an".

Na buɗe baki zan yi magana ta katse mini numfashi. "Ba na so ki tambaye komai ki dai kawai ki yi abin da na ce da ke". Cikin wani irin yanayi da ya zarce a ƙira sa da tashin hankali ko firgici na ce"in sha Allah". Na ja bargo zan kwanta duk da na san ko da na kwantan ba zan iya baccin ba. "Amatullah idan har kika fallasa wannan sirrin babu shakka sai na tsine miki kuma sai kin biya ni ɗawaniyyar da na yi dake". Zumbur na miƙe tsaye jikina yana wani irin matsanancin rawa duk yanda na so na yi magana amma hakan ya gagara, babu shiri na zube ƙasa sakamakon gazawar ƙafafuna na kifa kaina jikin gadon ina rera wani irin kuka marar sauti. Ko gizau Umma ba ta yi ta haye gado ta yi kwanciyarta ba tare da ta damu da nake ciki ba, babu abin da yake sanya zuciyata tafasa da hana ruhina samun sallama da nutsuwa kamar idan na tuna ban san turaren me ye Umma take yi wa Abba ba.

Tsorona guda kar ta cutar da shi don na tabbatar idan wani abun ya faru da shi ba zan taɓa rayuwa ba ni ma. Ko motsawa ban yi ba har aka yi ƙiran assalatul farko bayan mintuna ƙadan na ji ana bubbuga ƙofar ɗakin na tashi jikina gabaɗaya babu ƙwari ina dafe jiri yana ƙoƙarin buga ni da ƙasa na isa na buɗe ƙofar. Ganin Abba tsaye yana ƙoƙarin saka hularsa ya sani yin mutuwar tsaye hasken tocilar wayarsa da ya kunna a falon shi ya ba ni damar ƙarewa fuskarsa kallo. "Ku tashi asuba ta yi kar lokaci ya ƙure, ni ma masallaci zan tafi yanzu".

Kar ya juya ya fita na kasa cewa komai tsabar giyar mamakin da yake ɗawainiyya da ni. Na ja dogon numfashi na fesar da shi ta bakina ina jeranta hamdala da godiya ga Allah a cikin ruhina. Alwala na fito na yi kana na koma ciki na yi salla na zauna akan sallayan ta zabga tagumi duk damuwar da take kai kawo a cikin ruhina amma bakina ya kasa cewa komai sai dai ina da yaƙinin Ubangijina masanin abin da yake cikin zuƙatana ne kuma babu shakka yana sauraron yaren zuciyata. Har gari ya fara haske Umma ba ta tashi ba balle ta yi sallan asubahi, kuma na yi mini kashedin kar na ƙara tashinta daga bacci kowa za ta kwana da wuni. Don na taɓa yi karon mu da ita a sa'ilin bai yi mini daɗi ba.

Yanayin da nake cikin bai hana ni tashi na haÉ—a wuta na É—aura mana É—umame ba, na zubowa Abba na shi na kawo masa na ajiye a gabansa ina gaishe shi, cike da kulawa ya amsa mini yana bi na da kallo. Zan tashi ya ce na koma na zauna. "Kamar akwai abin da yake damunki ko?".

Na jijjiga kaina"babu komai". "Amma kin san dai a duniya gabaɗaya babu wanda ya san halinki ya kuma karanci dukkan motsinki sama da ni ko?". A sanyaye na furta"haka ne Abba". "To sanar da ni me ye yake damunki Amatullah?". Kafin na kai ga ba shi amsa Umma ta fito daga ɗaki tsam na ga Abba ya tashi tsaye yana faɗin"kin tashi kenan? Ai daman yanzu nake son in mun magana da Amatullah na shiga na tashe ki sai kuma kika fito". Ba ta amsa ba har sai ta zaune ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tana jijjigawa ta ce"Allah ya yi na tashi ko ba ka ji daɗin hakan ba ne?".

"Ni na isa na faɗi haka Hafsatu ni waye? A'a wallahi kawai dai na ga shurun ya yi yawa ne". Banza ta yi da shi hakan ya ba ni damar gaishe ta ta amsa mini a taƙaice ba tare da ta kalle inda nake ba. "Kai kuma za ka zaune ne ko za ka ci gaba da yi min tsayeye a ka, kamar ka haɗiye taɓarya".

Da rawar jiki na ga Abba ya koma mazauninsa ya zauna ko abincin da yake gabansa ya kasa buɗe wa balle ya ci. Hakan ya sa Umma sakin wani ƙayataccen murmushin da har sai haƙwaranta suka bayyana. "Amatullah tashi ki je ɗaki ki fara haɗa mana kaya, tun da Ubanki ya dage akan sai mun tashi daga gidan nan gwara mu fara shirin tun yanzu". Abba ya yi wuf ya karɓe zancen"ranki ya daɗe uwar gida ran gida ai tun lokacin da kika nuna ba kya so na janye maganar tashin. Babu inda za mu je tun da har kika nuna ba kya son hakan". "Manniru ban isa ka watsa min tsaba kaji su bi ni ba, salon ƴan uwanka sun kwanko ƙafa su zo har cikin falon nan su yi min ɗiban albarka su ce na hana ka sauƙe aiwatar da abin da ka yi niyya. Ai tun da ka furta za mu tashi to babu makawa sai mun bar gidan nan".

"Wallahi babu wani daga cikin ƴan uwana da ya iso ya zo ya gaya miki magana ahalin ina ji ina gani. Babu inda za mu har sai lokacin da kika ji zuciyarki ta sama nutsuwa da lamarin". Abba ya ƙare zancen cikin tsatsar biyayya kamar zai yi mata sujjada.

Umma ta gyara zama tana duban sa da wutsiyar idonta"tashi ka zauna a kujerar mana. Ko ka manta ikararin da ka yi na cewar kai ne mai gidan". Da mamaki gami da al'ajabina sai na ga Abba ya tashi ya zauna akan kujerar, zuciyata ta harɓa da wani ƙarfin bala'i take na faɗa tunani. Kenan da Umma ba ta ce ya kau kujera ba a ƙasa zai ci gaba da zama?. "Tashi ki ba mu waje za mu yi magana". Muryar Umma ta dawo ni duniyar zahiri daga tunanin da na yi nisan kiwo a cikinta, na tashi na fita waje ba na jin zan iya cin komai shi yasa ban zuba abincin ba na zauna na zuba tagumi yanayin da na sama Umma daren jiya da abun da ya faru yanzu ya dinga yi mini safa da marwa a cikin kwanyata. Tabbas akwai wani surkulle a cikin hayaƙin da Umma ta yi wa Abba jiya da ya juya masa kafatalin tunaninsa.

"Ke kuma lafiyarki da sanyin safiyar nan kika zagba tagumi?". Muryar Amatullah ya fizgo tunanina da ya yi nisa da gangar jikina, na saki ɓoyayyar ajiyar zuciya ina miƙa mata kujera ta zauna. Maimakon na amsa mata tambayar da ta yi mini sai na sako wani maganar na daban.

"Umma ta ce za mu na tafiya talla tare da ke, ban san ko kin san da maganar ba".

Ta É—an murmusa kafin ta ce"tun jiya Ummata ta sanar da ni. Kuma na ji daÉ—in haka sosai fiye da zatonki". "Amma kin san ni fa ba zan na daÉ—ewa ba saboda zuwa islamiyya". "To na ji ustaziya".

Tana rufe bakinta Abba tana fitowa ta gaishe shi ya amsa yana saka takalmarsa ya fita da sauri, sai da na bi shi da É—ayar takalminsa don haÉ—in gambiza ya yi ba tare da ya sani ba. Na tsaya a zaure na goge hawayen da ya zubo mini kafin na dawo wajen Amira, duk yadda ta so jan hankali da hira ta kasa samun kaina. Haka har Umma ta kammala kunun ta ce da ni na je na saka kwallin kafin ta shigo kasancewar kwallin yana wajena ina ajiye da shi. Ban sa ka ba amma ko da ta shigo ta tambaye ni na ce da ita na saka. Don har cikin raina nake jin ba zan iya yin abin da take so na yi ba. Akan idona ta yi wa bokitin kunun turare har da gammo da zan naÉ—a bai tsira ba, sai da ta gama komai ta ce na É—auka na fita na É—aura a kaina na fito na iske Amira har ta shirya tana jira na.

Ta ci ƙwaras cikin shigar doguwar rigar kamlafa da ya bi jikinta ya fito da surarta a bayyane. Ta yafa mayafi a kafaɗarta bayan ta buga ɗaurin da ake wa take da ture ka ga tsiya a kanta. Har muka fito ban yi mata magana haka nan ma ita ma ba ta ce da ni uffan ba illa latsa wayarta da take yi, kasancewar ita akwai almajirin da yake tura mata kayan tallanta a bairo ya kai mata har inda za ta. Sai da muka yi nisa na ce"wai ina muka nufa ne?".

"Tasha mana".

"Tasha kuma? Haba Amira duk faɗin garin nan mu rasa inda za mu yada zango sai tasha?". Ta cira kai tana kallona"ke dai ba buƙatarki ki sayar da wannan kunun ba?". Na gyaɗa mata kaina da hakan ya ba ta damar zarce wa da faɗin"to ke dai kawai ki biyo ni". Daga haka ban ƙara cewa komai ba har muka isa tashan almajirin ya sauƙe mata kayan ta sallame sa ya juya ya tafi. Kan ka ce kwabo samari sun yi mana rumfa sayar masan suke yi ba ƙaƙƙaurawa. Kafin awa guda ta rufa ta sayar da Masar tas har ana nema, sai dai ta ajiye take away guda biyar ta ƙi sayar wa kowa, ni ma ba laifi na dandani farin jininta na yi ciniki sosai.

Ganin ana ta zuwa neman masan tana cewa ya ƙare ya sani yi mata magana"ke kuwa ki sayar musu da wannan ɗin ma tun da ana ta zuwa nema". "Wannan ba na sayar wa ba ne don a riga da an saye su tuntunin. Wannan da kike gani na Naziru ma Zamani ne kuma ko wani take away ɗaya naira dubu biyar yake sayansa, sai dai shi yana da sharaɗi". Na ware idona tar a kanta"wani irin sharaɗi kuma?". "Har inda yake ake kai masa kuma a taya sa hira". "To a ina za ki same shi?". "A ɗakin mana". Na dafe ƙirji ina maimata abin da ta furta"a ɗakinsa kuma?".

"Ƙwarai kuwa. To me ye abu tada hankali dududu ba kya wuce awa guda ya ba ki kuɗinki ki dawo".

Shuru na yi na kasa motsin arzuki balle na yi furta wani kalma tsabar ruÉ—un da na shiga. Sai da na fizgo numfashina kafin na ce"yanzu kuma Amira sai ki je É—akin nasan?"

"To sau nawa kuwa. Wani lokacin ma da na fito a can nake tsaya wa ya yi min juye. Ke ma kwanan nan zan nema miki wani na jona ku". Na galla mata harara"Allah Ubangiji ya kiyayi gatari da saran shuka. Ke ma ki yi wa kanki faɗa don ke yanzu ba yarinyar ba ce ko a addini alƙalami ya hau kanki. Ya rage na ki ki yi daidai ko akasin hakan". Dariya kawai ta soma yi ta tashi ta ɗauki take away ɗin ta miƙe tsaye.

"Lokacin da za ki fara hakan Amatullah ke ma kanki ba za ki sani ba. Lokaci shi ne sauya komai, mu ma da ba mu tunanin za mu iya ba amma lokaci ya koyar da mu abun da ba mu taɓa tsammanin za mu iya aikata shi ba". Tana dasa aya ta juya ta tafi kai masa take away ɗin. [7/21, 6:16 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

____________________________________

Page 1️⃣4️⃣

Da kallo na raka ta har ta ɓacewa ganina na sauƙe wani gawurtaccen ajiyar zuciya ina zabga tagumi da hannuwa bibiyu. Kafin maganganun da ta yi mini ya soma dawo mini a cikin kwanyata ina yi masa rankaɗe da rairaya. Babu shiri na zame hannuna daga tagumin da na yi ina ji har cikin ƙasan zuicyata ba zan taɓa iya aikata abin da Amira take ikirarin lokaci zai sa na koya ba.

"Ƴan mata me ye kike sayarwa ne?". Muryar saurayin ya dawo da ni cikin duniyar zahiri daga karatun wasiƙan jakin da na faɗa. Na cira kai ina ƙare masa kallon tsaf. Shigar ƙananan kaya ne a jikinsa da su da kansu suke bayyanar da tsadan farashin su, komai na shi tsaf-tsaf alamar baya haɗa hanya da ƙazanta ko mai aikata ta. "Ko ba za ki yi min magana ai za ki tashi daga nan wajen kar zafin rana ya yi wannan kyakykyawan fatarta ki illa". Sai da ya yi maganar na ankara da har rana ya iso inda nake zaune na tashi na matsa gefe na zauna shi ma ya matso. "Don Allah ki yi min magana mana ko da kuwa zagina za ki yi ko cin mutunci. Na tabbatar yanda kike da kyawun jiki da na fuska muryarki ma za ta kasance kamar sarewa a kunne".

A kufule na ce"me ye kake so daga gare ni? Idanunka dai sun gane maka kuma sun isa su ba ka amsar duk wani tambayar da kake tafe da shi. Ba shashashci ba ne ya kawo ni nan sana'a nake yi". Ya murmusa yana ɓalle murfin ruwan roban da yake hannunsa ya kurɓa kafin ya ce"tsarki ta tabbata da Ubangijin da ya tsagawa bayinsa baki kuma ya ba su ikon yin magana. Tabbas ki na da zaƙin murya mai rikitar da ƙwaƙwalwa tun da na hango ki daga nisa na ji zuciyata tana cewa na zo gare ki". "Don Allah Malam ka yi haƙuri".

"A zuba min kunun na dubu biyu". Na ɗaga kai na yi masa kallo guda kafin na kawar da kaina gefe ina faɗin"gabaɗaya sauran kunun bai kai na adadin wannan kuɗin ba". "To yanzu a zuba min na sha sauran kuma sai ki yi yadda kike so da shi". Ban ce da shi uffan ba na zuba masa na ɗari biyu na miƙa masa ya ɗauka ya zauna ya soma sha. "Kin san dai wallahi ita ce ƙarshen rantsuwa ga duk wani ɗan musulmi ko? To wallahi tun da nake ban taɓa shan kunun mai daɗin wannan ba. Don Allah zan roƙi wata alfarma daga gare ki idan ba za ki damu ba". Ba tare da na kalla inda yake ba na ce"don damuwa kam dole na damu. Faɗi na ji wani irin alfarma ce".

"So nake yi a duk lokacin da kika kawo tallan kunu tashan nan, na zama mutum na farko da zan fara sha kafin kowa".

Na galla masa harara"ba zan iya ɗaukar abun da ba zan iya ba ka yi haƙuri". Ina ɗago kaina muka haɗa ido da shi na kuma watsa masa wani harara ina saki gajeren tsaki. "Wallahi idan kina magana kamar kar ki daina. Yadda kike fassara leɓɓanki shi kaɗai ma abin burgewa ne". Ban ce da shi komai ba har ya gama kiɗansa kuma ya yi rawansa bayan ya gama shan kunun ya miƙe tsaye ya tsaro wasu kudaɗe daga aljihunsa ya raba biyu ya ajiye mini kashi ɗaya akan bokitin kunun yana faɗin.

"Ga kuɗin kunun". Ta ƙara ajiye mini ɗayan kashin yana ci gaba da cewa"wannan kuma ni ne na yi niyyan baki saboda gamsuwa da na yi da wannan daddaɗan kunun nakin".

"Malam na ɗari biyu ai kawai ka sha. Don haka iya ɗari biyun nake buƙata domin shi ne haƙƙina". Kafin ya yi magana Amira ta iso wajen hakan ya sani miƙewa tsaye ina kallonta sai dai kafin na yi magana ta riga ni. "Tuba nake yi na bar ki ke ɗaya ko? To yanzu dai ga shi na dawo".

"Kin ga ni kawai ma mu tafi gida na gaji da wajen nan gabaɗaya". Ta yi sakeke tana kallona"ban gane mu tafi gida ba Amatullah? Ta yaya za mu tafi gida bayan kunun har yanzu akwai saura. Ai kawai haƙuri za ki yi mu zauna har ya ƙare".

"Babbar yarinya daman tare kuke da ita? Ai kuwa faɗuwa ta zo daidai da zama da ke zan yi kamun ƙafa". Ta murmusa tana fuskantarsa kafin ta ce"Bash ai ban gane ka ba kai ne haka? Duk ka wani canza ka sama duniya ka manta da mutane. Na ji ma ance wai yanzu babbar mota kake ja. Sai jifa-jifa ake ganinka a cikin tashar". Ya bushe da dariya har da tafa hannu sai da ya tsagaita kafin ya ce"ikon Allah! Ke ma kin sama labari kenan?. Wallahi ina gaya miki yanzu gabaɗaya ba na samun sama". Cike da fara'a Amira ta ce"ma sha Allah ina taya ka murna".

"Ina godiya babbar yarinya. Wannan fine girl ɗin fa?". Ta waigo tana kallona. "Au wai Amatullah? Ƙawata ce ko akwai magana ne?".

"Sosai ma kuwa sai dai ina ta yi mata magana ba ta tanka min. Kin san ba ni ban cika shiga harkokin mata ba amma ita É—in ta yi nasarar yin daidai da ra'ayina, da ita za a tafi". Ta saka dariya kafin ta ce"to wannan kuma ai maganarku ce kai da ita sai dai ko na ba ku waje".

Na haɗe giran sama da ba ƙasa ina watsa mata harara da wutsiyar idona"Amira kin fi kowa sanin ba na son irin wannan wasan". "Allah ya ba ki haƙuri ba ni na kar zoman ba rataya aka ba ni". Daga haka ta nema waje ta zauna ta zaro wayarta tana dandanawa ni ma na koma na zauna. "To babbar yarinya ni dai zan wuce. Ɓarauniyar zuciyata ga kuɗin nan don Allah kar ki ƙi ɗauka". Ya ƙare zancen yana maraicecewa lamarin da ya ƙara tuntsura mini zuciyata ta zo daidai wuya ta yi nuni tsayiwar ƙaryan kifi a maƙoƙaro.

"Malam na ri ga da na gaya maka adadin kuɗinan ai ko? Me zan yi da wannan tulin kuɗin da ka ajiye mini?". Kafin ya ba ni amsa Amira ta yi caraf ta cafke zancen. "Kar ka damu Bashir zan shawo maka kan komai". Ya yalwata fuskarsa da yalwataccen annuri kafin ya furta"ina godiya ƴar gari, yanzu dai ki saka min sha ɗayanki tun da na ga kin ƙara da gari yanzu, kin dantsalo babbar waya". Da murmushi a fuskarta ta karɓa ta sanya masa lambarta ya ƙira a take ya ce ta yi saving kafin suka yi sallama ya tafi.

Ta watsa kuɗin ta irga su kafin ta soma cewa"kin ga dubu dubu huɗu ne dukka. Yanzu me ye za a yi da su?". Raina ya kai ƙololuwar ɓaci na yi mata wani irin mungun kallo ina furzar da takaicin da ta yi silar cusa mini cikin raina. "Sai ki san yadda za ki yi da shi tun da ke kika ɗauke su".

Ganin na ɓata rai ya sanya ta soma faɗin"ki saki ranki Amatullah abun da na yi shi ne daidai. Don idan ba ki karɓa ba ma wata can daban ce za ta ci kuɗin kin ga kuwa ban yi laifi ba don na ɗauka. Su da irin su Bashir kuɗinsu duk a wajen mata yake ƙarewa ba sa tsinanawa kansu komai gwara ma ki kwanki gara ki bar gara a inda kika same shi".

Ban ce da ita komai ba na tashi na na ɗaga gammona zan ɗauki bokitin kunun na ɗaura a kaina ta dakatar da ni. "Haba ke kuwa ina za ki da ragowar kunun? Ai almajirai za ki nema ki yi musu sadaka ki nema albarkar kasuwa". Na kasa cewa da ita komai balle na yi wani yunƙurin haka ina ji ina gani ta rabarwar almajirai kunun har da cewa wai su yi mini addu'a Allah ya sa na shigo tashar da ƙafar dama. Ta tattara kayan gabaɗaya tare da na ta almajirai suka ɗauka mana zuwa gida, suna gaba muna biye da su a baya.

"Amatullah sai fa kin watsar da waɗannan tsauraran ɗabi'un nakin kafin ki iya zama cikin tashar nan har ki ci riban zaman. Kin ga mutanen sai ka musu abin da suke so kafin kai ma ka sama yadda kake so daga gare su". Na yi hanzarin taka mata burki"ban gane sai ka yi musu abin da suke so ba?". "Kwantar da hankalinki kar ki fassara zancena ta wani hanyar daban. Ki dinga sakar musu fuskar kuna yin ɗan hira nan ko da jifa-jifa ne. Matuƙar za ki yi haka to jauranki ba zai taɓa yin kwantai ba, kuma ina tabbatar miki babu wanda ya isa ya taɓa a tashar nan ya kwana lafiya".

Na yi É—an jim ina nazari da lalumen gurbin da zan aza zantukanta. "Amma ai ce mini kika yi garejin mota kike zuwa kai talla".

"Kin manta Mansur baya gari ne? Idan yana gari ne nake zuwa gareji amma idan baya nan tashar nan nake zuwa". "Me yasa?". "Saboda haka kawai na yi ra'ayi". Na ja hannunta muka tsaya muna kallon juna. "Amira ki ji tsoron Allah kin san da cewa Mansur yana sonki sosai kuma yana iya ƙoƙarin sa a kanki na gani ya biya miki duk wata buƙatarki da ta taso ɓangaren ƙudi. Amma me yasa don baya gari za ki nema cin amanarsa ta hanyar kula wasu mazan bayan shi? Ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba na san shi ne ya hana ki zuwa wannan tashar saboda baya son ki yi mu'amala da mazan wajen". Ta fizge hannunta ta fara tafiya na bi ta a baya.

"Shikenan don ina sonsa sai aka ce ba zan yi mu'amala da kowa bayan shi ba. Aure na ya yi ko kuwa ya zo gidanmu an ba shi ni ne da kike yi min wannan maganganun?. Amatullah idan na ce ba na son Mansur na yi ƙarya amma mu'amala da wasu mazan bayan shi ya zama wajibi". Ta yi tsaki daidai lokacin da muke karya kwanan shiga layinmu kafin ta ci gaba da maganan.

"To ma ce miki aka yi su É—in soyayya muke yi ko me ye? Ko ke za ki ba da shaidar babu wanda nake so a cikin zuciyata sama da Mansur". "Ko ba soyayya kuke yi ba amma ai abin da kuke yi bai dace ba. Me ye zai kai ki É—akin mutum ku kwashe tsawon mintuna kuna hira don kawai zai sayi abin da kike talle alhalin ku ba muharraman juna ba ne, me yasa ba zai zo ya saya ba kamar yadda kowa yake yi?".

"Lokacin da lamarin zai juyo kanki, na tabbatar miki a sa'ilin ko kalmomin kare kai ba za ki same su akan tsinin harshenki ba".

Rashin gane inda zancen natan ya dosa ya tursasa mini yin shuru ba don na rasa abin faɗa ba. Haka har muka isa gida cikinmu babu wanda ya kuma cewa uffan almajiran suka shigar mana da kayan har cikin zaure, ta ba su naira ɗari biyu bayan ta ce da su gobe da safe ma su zo su ɗauka mana kayan. Cike muka iske gidan kowa yana tsaye cirko-cirko kamar waɗanda suka haɗiye taɓarya sai da muka ƙarisa shigowa muka gane wa idanunmu abin dake faruwa. Mahaifin Ummi ne a tuɓe a tsakar gidan daga shi sai singilet da gajeren wando tana ta ɓarin zancen da ikirarin sai ya ɗaukar wa ɗiyarsa fansan fitar mata da jini da Maman Adnan ta yi ba gaira ba dalili. Yayin da mahaifiyar Ummin take ƙara rura wutar rikicin. Can ka ce kwabo yaran unguwa da uwayensu sun cika ƙofar gidan har cikin zaure babu masaka tsinke.

Muka shige ɗakinmu tare da Amira muka tarar da Umma tana zaune a falo tamkar ba ta san wainar da ake toyawa a cikin gidan ba. Duk rusuna muka gaishe ta ta amsa mana fuskarta babu yabo babu fallasa. Amira ta yi mata bayyanin mun sayar har mun dawo Umma ta cika da farin cikin mussamman lokacin da ta miƙa mata wannan dubu huɗu ta haɗa mata da bayanin inda muka same su. Lamarin da ya faranta ran Umma har ya kai ta ga rangaɗa guɗa.

"Aw ashe fa gidan ba lafiya? Amira ai irin ki ake so É—iyar azirki irin albarka. Ga Amatullah nan na bar ta a hannunki ki ci gaba da É—aura ta akan hanya".

"Ba ki da damuwa Umma. Yanzu dai bari na je na huta".

"To yarinyar kirki ɗiyar fita kunya, na gode sosai ko". Murmushi kawai Amira take ta baza wa ta tashi ta fita. Ta bar ni da ƙuncin rai don ban yi zaton za ta iya faɗawa Umma yadda aka sama kuɗin nan ba sai gashi ta shafe idonta ta aikata.

"Umma ga cinikin da aka yi, bari na yi salla na yi shirin islamiyya". Na furta yayin da nake miƙa mata kuɗin cinikin da yake wajena. Ta amsa tana washe baki har kunne, ganin ba ta da niyyar ce mini komai ya sani fallasa abin da yake raina. "Umma ni ma ko sau ɗaya ai sai ki sa mini albarka". "To Allah ya yi albarka. In ce dai shikenan ko?". Babu shiri wani ƙayataccen murmushi ya suɓuce mini"na gode sosai". Sallan na yi kana na yi wanka na ci abinci na yi shirin islamiyya na tafi. Bayan mun fito sallan Malam Suleiman ya aiko ƙura na na je na same shi a cikin staff room. [7/22, 6:43 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

________________________________________

Page 1️⃣5️⃣

Shuru ya biyo bayan gaisuwar da na yi masa ya amsa. Sai da aka yi nisa kafin ya kawar da shurun ta hanyar soma faɗin"Amatullah na je na yi nazari akan maganganun da muka fara tattaunawa da ke jiya, mataki na farko da za ki ɗauka wanda babu nadama shi ne ki dage da addu'a, ki dinga tashi cikin dare yayin da kowa ya kwanta ki yi alwala ki yi salla ki yi kuka a Allah ki ƙasƙantar da kanki gare sa. Ki yi tawassali da sunanyensa ɗari ba ɗaya tsarkaka ki roƙe sa mafita. Ki nema wa mahaifiyarki shiriya Allah ya sa ta gane illar abin da take aikata. Sannan ɗabar da nake son na ja hankalinki sosai akan sa shi ne kar ki sake shaiɗan ya yi nasara akanki ki wa mahaifiyarki rashin kunya ko ki raina ta ki daina ba ta girma da kimarta a matsayinta na uwa. Allah ya kan jarabci bawansa ta ko wani fage a rayuwa kamar yadda ya zo a tarihin Allah ya jarabci Annabi Ibrahim ta ɓangaren mahaifinsa wanda ya kasance mushiriki. Daidai da rana guda bai taɓa ƙin aikata masa abin da yake so ba, Annabi Ibrahim har tallen gumaka ya yi don jaddada biyayarsa ga mahaifinsa. Don Allah ina mai jan hankalinki da duk runtsi duk wuya da yadda lamura za su sauya kar ki kuskura ki yi wa mahaifiyarki rashin ɗa'a".

Na sauƙe ɓoyayyan ajiyar zuciya kafin na ce"in Sha Allah Malam zan yi amfani da duk shawaran da ka ba ni. Ba zan taɓa kauce wa daga wannan turban ba". Cike da jin daɗin kalamaina ya ci gaba da cewa"Allah ya yi miki albarka ya kawo miki sauƙi da mafita a cikin dukkan lamuranki. Zan ba ki wasu addu'ar da Annabi ya yi amfani da su kuma ya umarce mu da mu yi amfani da su, a duk lokacin da muka tashi roƙon wani buƙata a wajen Allah. Babu inkari matuƙar ka yi su Allah da kansa ya ce yana jin kunyar wanda zai roƙo sa da wannan addu'ar ba tare da ya ba shi duk abin da ya roƙo ba". "Na gode sosai Malam Allah ya saka da alkhairi ya biya buƙata".

"Amin ya Allah".

Ya amsa yana miƙo mini watar farar fefe da ya rubuta mini addu'ar a jiki, na amsa ina ƙara yi masa godiya. Tun kafin a tashi daga islamiyyar na haddace addu'ar kafin na iso gida ta zauna ɗas a kwanya da saman harshena. Ina isowa gida na wuce ɗaki na sauya kayan da ke jikina na fito kasancewar ban tarar da Umma ba. Ɗakin su Amira na nufi don karanta mata dashin dacewar abin da ta aikata mini ɗazu, tana kwance a cikin kujera a falo ta duƙunƙune waje guda yayin da ta lumshe idanunta tana ƙare matse wayar da yake kunnenta. Da hakan ya hana ta jin sallamar da na shigo da ita ɗauke a bakina.

Ganin ba ta da niyyar saurara ta ya sani na fizge wayar, ta tashi ta zauna tana kallona bayan ta dafe kanta. "Wallahi na san duk gidan nan babu wanda zai yi min wannan wulaƙanci sai ke Amatullah". Na galla mata harara"kin kyauta abin da kika yi min kenan ko?". Cikin rashin fahimta ta ce"da na yi me ye kenan?". "Ya dace ki je ki sama Umma ki sanar da ita inda aka sama wannan kuɗin? Ni da nasan haka ne ma ba zan bari ki ɗauka ba". Ta tuntsire da dariya har da riƙe ciki lamarin da ya ƙara fusata ni na cika na yi fam na zo har wuya.

"Au! Dariya ma maganar ta ba ki kenan?".

"To Amatullah idan ban yi dariya kuka kike so na yi? Me ye don na sanar da Ummar hanyar da muka sama kuÉ—in?. Ince dai ke ce kullum kike jan hankalina da yi min nasiha akan na guji faÉ—ar abin da daidai ba duk runtsi da matsin lambar da za a yi min na faÉ—i iya gaskiyata a cikin ko wani irin yanayi. Cikin ikon Allah kuma yau na faÉ—i gaskiya kin zo kin titsiye ni".

"Ni ba titsiye ki na yi ba amma ai kin san zancen da ya dace a faÉ—a da akasin hakan".

"Ni dalla ba ni wayata ina shan soyyaya da masoyi kin zo ki katse min jin daɗina". Ta ƙare zancen tana fizge wayarta da yake hannu ta koma ta kwanta ta ci gaba da wayarta, yayin da na nema waje na zauna na yi tagumi. Babu abin da yake yi mini yawo da kai kawo a cikin raina face yanayin da na sama Umma jiya da yadda Abba ya sauya a safiyar yau. Duk da Abba yana da sauƙin kai da hakan yake sa mutane da yawa tunanin ya fiye sanyi, amma tsayayye ne kuma jajirtaccen mutum ne akan iyalinsa da ba ya ɗaukar wargi a wannan fanni ko kaɗan. Kamar daga sama na ji an manna mini ways a kunnuna hakan ya dawo da hankali da tunanina da suka yi nisan kiwo gare ni. Na cira kai ina duban Amira.

"Mansur ne za ku gaisa".

Na amshi wayar muka gaisa da shi sannan na yi masa ya hanya ya amsa mini da sun sauƙa, kafin mu yi sallama ya dinga jeranta roƙo akan na kula masa da Amira kafin ya dawo ya ba ni amanarta ya bar ta a hannuna da makamantan su. Sai da na dara sosai kafin na amsa da cewar zai dawo ya same amanarsa yadda ya bar ta da iznin Allah. Da haka muka yi sallama na miƙa mata waya ita ma ɗin sallama suka yi ta ajiye wayar. Na gyara zamana ina kallonta haɗe da cewa"Mansur yana matuƙar sonki ta yadda ba iya ɓoye hakan har a cikin kalaman da suke fita daga bakinsa. Don Allah kar ki ba wa kowa irin damar shiga zuciyarki balle har ya kai inda Mansur yake, kar ki ci amanar bawan Allah nan ko da wasa". Numfashi mai ƙarfi ta sauƙe da har sai da na ji sautin fitarsa kafin ta soma magana a hankali alamar na taɓo mata inda yake yi mata ƙaiƙayi. "Ni ma ina jin sa har ƙasan raina, kuma ina sonki fiye da tunaninki. In sha Allah zan yi amfani da duk shawarwarin da kika ba ni".

Daga haka na daina fahimtar abin da take faɗa sai dai na ƙura mata idanu ina ganin leɓanta yana motsawa da hakan ya tabbatar mini da har yanzu ba ta daina maganar ba. Sai da ta taɓo ni kana na dawo daga karatun wasiƙan jakin da na afka na figigi na ɗaga kai ina kallonta. "Tunanin me ye kike yi ne haka Amatullah? Tun da safe na fahimci akwai abin da yake damunki, amma kika ce min babu komai. Me ye amfanin muna ƙiran kan mu aminai kuma ƴan uwa amma ba ma iya sanarwa junanmu abin da yake damun mu?".

Na ja dogon numfashi na fesar kafin na sama lasisin faɗin"Amira babu abin da yake damuna akwai dai matsaloli ne na yau da kullum, kuma kin san ba'a raba bawa da tunani komai daular da yake cikinta". "Ko kin ɓoye min abin da yake damun ki fuskarki ba zai ƙi bayyanar da labarin zuciyarki ba. Tabbas akwai abin da yake damun ki".

"Babu komai na ce miki babu komai. Ki yarda da ni mana Amira". Ina ƙare zancen na miƙe tsaye na ɗaura daga inda na tsaya"kin ga ni bari na je na duba ko Umma ta dawo". Ban jira abin da za ta ce ba na yi wuf na fice. Kai tsaye ɗakinmu na nufa sai dai kafin na kai ga shiga muryar Baban Adnan ya tursasa mini dakatawa.

"Amatullah ƴan mata, kwana biyu kamar ba kya cikin gidan nan". Maimaikon na ba shi amsa sai na rusuna na gaishe shi na yi wucewa ta cikin ɗaki da mamakina na tarar da har yanzu Umma ba ta dawo ba. Na fito na yi alwalan sallan magrib na zo na yi ina raka'ar ƙarshe Umma ta shigo cikin ɗakin ta zauna tana huce gajiyar da ta kwaso. Sai da na iddar na shafa addu'ar da na yi kafin na yi mata sannu da zuwa ta amsa mini fuskarta babu yabo babu fallasa, so nake yi na tambaye ta inda ta je amma sam tsoro ya yi mini katutu na kasa cewa komai.

"Umma me ye za a dafa ne?"

"Ki tafasa doya".

"To".

Na amsa da shi a taƙaice ina tashi na fita na haɗa wuta na ɗaura ruwa. Yayin da na ɗauko doyar ina ferewa na zuba a cikin tukunyar. Na ɗaukar jakar islamiyyata ina duba litattafaina. Ban tashi daga wajen ba sai da doyar ta dahu ba soya manja kana na shiga ciki na zuba nawa na ci na yi sallan isha'i na fito zaure wajen yaran da suke jirana. Sosai na zage damtse na yi musu karantu duk wani ƙoƙarin manta abin da yake ta'azzaran raina na yi shi. Muna tsaka da karatun Ummi ta fito daga cikin gida ta tsaye mini a kai kamar mai karɓan bashi.

"Ummi lafiya?".

Ta riƙe ƙugunta tana yi mini kallon hadirin kaji ta ce"ku tashi ku nema wani wajen, zan shigo da Auwal". Na cira kai ina duban ta da mamakin rainin wayon da yake tafe da ita. "Ban gane mu nema wani wajen ba? Sanin kanki ne a ko wani daren duniya a cikin zauren nan muke yi karatu a daidai irin wannan lokacin. Sai yau kawai za ki ce mu nema wani wajen don za ki yi zancen, ai kuwa sai dai ke da shi Auwal ɗin ku nema wani wajen". Ta yi poster tana ganina da nake da tabbacin mamakin furucina ne ya hana ta motsawa.

"Lalle Amatullah wuyanki ya yi kauri ya isa yanka. Yau zan bar ki ne kawai amma wallahi gobe ba za ku yi karatu a nan ba".

"Ba gobe ba har jibi da gata ma a nan za mu yi, ki sa hakan a cikin ranki". Ba ta tanka mini ba illa dogon tsakin da ta ja ta fice daga ciki zauren tana shuri da takalmar yaran, na raka ta da kallo har ta fice kafin na ɗauke kaina. Babu jimawa Abba ya dawo na tashi na yi masa sannu da zuwa kana ya shige cikin gida. Ƙarfe tara muka yi addu'a kowa ya watse na naɗe tabarmar na shigo cikin gidan, muka yi kiciɓus da Amira za ta fita daga ni har ita dariya muka sakarwa juna. Na matsa na ba ta waje ta wuce ina faɗin"Allah ya shirya ki ke kam".

Ta bangaje ni"ki sa munjaye Allah dai ya shirya mu". Daga haka ta fice ni ma na ƙarisa ɗakinmu. Cak! Na tsaya na ɗaga ƙafarta ɗaya amma na gaza sauƙe ta sakamakon zancen da suka sauƙa a ƙofifin kunnuwa tamkar sauƙar aradu, take jikina ya soma rawa kamar ana jona mini wutar lantarki. Zuffa ya soma tsatstsafo wa daga dukkan mafitan gashin jikina, tsoro da firgici ya bayyana ƙarara a fuskata. In dai ba matsalar ji na samu ba tabbas muryar Abba na ji yana cewa"Hafsatu na gama ki da girman Allah kar ki yi fushi da ni zuciyata ba za ta iya jura ba, na yarda ki hukunta da ko wani irin nau'in hukunci amma ban da wannan. Na biya ta wajen Maman Umar ne shi yasa ban dawo da wuri ba ban san hakan zai ɓata miki ba da ban tun magriban fari na dawo cikin gidan nan".

"Manniru ni fa ba zan juri wannan cin mutuncin ba. Sati ba ta cika ba tare da matar nan ta wanko ƙafarta ta zo cikin gidan nan ba yanzu kuma kai da ka baro wajen aiki sai ka wuce wajenta kafin ka iso gida. In ce dai tun ƙarfe biyar kuke tashi daga makarantar amma don kuturun wulaƙanci sai ƙarfe taran dare za ka shigo min cikin gida". Cikin wani irin yanayin na tsinkayo muryar Abba yana faɗin" ki yi haƙuri in Sha Allah hakan ba zai ƙara faruwa ba".

"Wai Maman Umar ɗin nan ita ta haife ka ne? Ko ita ta yi naƙudarka sai haka. Ni fa na gaji ba zan ɗauki wannan rainin hankalin ba".

Kamar an jawo ni haka na ji na faɗa cikin ɗakin sai dai na yi nadamar shiga ta saboda yanayin da na iske su a ciki. Umma tana tsaye yayin da Abba kuma yake durƙushe akan gwiyoyinsa ya riƙe ƙafarta.

Zuciyata ta yi wani irin harbawa sai da na ji duniyar gabaÉ—aya tana juya mini a lokacin. Da gudu na shige É—aki na zube akan gado, sai dai sam na gaza yin ko É—igon hawaye duk da suyan da zuciyata yake yi mini. Na sa hannuna na toshe dukkan kunnuwana saboda amsa-kuwwar da zancen da na ji suka yi mini a na'urar naÉ—ar sautina. Har Umma ta shigo cikin É—akin ban motsa daga kwanciyar ruf da cikin da na yi ba, ba ta ce da ni ko kanzil ba ta É—auki abin da ya shigo da ita ta fita. Ba ta dawo ba sai da dare ta raba sosai ta shigo ta kwanta.

[7/25, 11:19 AM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

___________________________________

Page1️⃣6️⃣

Har dare ta raba bacci ta ƙi kusanta na illa juyin da nake yi raina cike da wani irin zogin da raɗaɗin da yake tasowa tun daga ƙasan raina yana mamaye mini dukkan sashin da sassan ruhina. Sai da na tabbatar da Umma ta yi nisa a baccin da take har da munshari kafin na tashi na fito na yi alwala na zo na tada salla. Raka'a biyu na yi na sallame na ɗaga dukkan hannayena sama ina yi wa Allah kirari kafin na soma zayyana matsalolina na ƙarƙare da yin addu'ar da Malam Suleiman ya ba ni kafin na shafa addu'ar cikin sanyi da mutuwar jiki. A zaune a wajen na ƙarisa daren yau sai can gabannin asubahi na runtsa ban yi nisa ba na ji an soma ƙiran sallan asubahi, na yi figigi na tashi ina murtsule idona tare da ƙara kasa kunna don tabbatar da abin da kunnuwana suke jiyo mini. Sai da na tabbatar da cewa lalle sallan ake ƙira kafin na tashi riƙe da kaina da yake matuƙar sarawa, na buɗe ƙofan ɗakin raina cike tal da mamakin abin da ya hana Abba tashi akan lokaci.

Turus na ja na tsaya bayan na kunna ƙwan wuta haske ya gauraye ɗakin. Na hangen Abba kwance a makwancinsa ko tashi bai yi ba, na je na tsuguna a gaban sa na ɗan buga matashin take ya buɗe idonsa ya tashi ya zauna.

"Subhanallahi! Kar dai har an yi ƙiran salla?".

"Tun ɗazu aka ƙira".

"Wallahi gabaɗaya na tara gajiya ne a jikina jiya. Shi yasa tun da na wanka ko juyi ban yi ba". Na jinjina kaina"bari na je na sama maka ruwa a buta". Zan tashi ya dakatar da ni. "Ki fara zuba wa Ummanki tukunnan. Bari na je na tashe ta". Na sakake ina kallonsa har ya tashi ya shiga cikin ɗakin na kasa tashi daga wajen. Sai da na sauƙe gwauron ajiyar zuciya kafin na tashi kamar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki na fita waje. A buta biyu na zuba ruwan kana ni ma na zuba nawa na yi na koma ciki na gabatar da sallan ko da na iddar ban tashi daga kan slalayan ba na ɗauko al'ƙur'ani na soma karantawa a ƙoƙarin dawo da nutsuwar zuciyata. Ban gushe ina yi ba har sai da na jin ɗan sanyi a cikin raina kana na rufe na ajiye na tashi na soma gyara ɗakin na gyara ko'ina kana na ɗaura mana abin kari.

Na kawo wa Umma da Abba na su, ko gama ajiye wa ban yi ba Umma ta soma faɗin"A'a ni kam ba zan ci ma wannan abincin ba ɗauke shi kawai". A hanzarce Abba ya ce"to me ye kike so ki ci?". Ta yatsina fuska"ba na jin sha'awar cin komai". "A'a haka kuma ai ba zai yiyu ba ace kin zauna ba tare da kin ci komai ba. Ki faɗi duk abin da kike son ci ni kuma na yi miki alƙawarin samo miki shi matuƙar dai akwai shi a cikin wannan duniyar da muke rayuwa".

"Gandan shanu nake so ci da matsatstsan ruwan rake". Babu shiri na cira kai ina ganin Abba da ya miƙe tsam yana faɗin"yanzu zan fita neman sa ba kuma ba zan dawo ba har sai na samu miki su". "Abba ka kawo na je na nemo mata, tun da kai ka ga wajen aiki za ka je. Kar ka yi latti ka kawo kawai".

"A'a Amatullah ni nake da alhakin nema mata duk abin da take buƙata. Don haka ki bar ni na je da kaina don sauƙe haƙƙinta da yake kaina".

Yana rufe bakinsa ya fita daga cikin falon da hakan ya yi daidai da sa'ilin da Umma take tuntsirewa da dariya mai ƙarfin gaske har da tafa hannu. "Wa ya faɗa maka borno gabas yake Manniru?. Ai kowa ya ce bai iya kuka ba to uwarsa ce ba ta mutu ba, mu zuba ni da kai ɗan halak ka fasa". Ban san lokacin da idanuna suna fara tsiyayar da ƙwalla ba sai ɗumin su da na ji a bisa dandamalin kuncina suna sauƙa har izuwa tudun wuyana. Har na buɗe baki zan yi magana Umma ta watsa nuni wani hargitsatstsen kallon da ya tursasa mini yi wa bakina linzami. Kalaman da ta yi mini da ƙarfin sanin halinta da na yi suka soma yi mini shawagi a tsakiyar kwanyata. Kif na rufe bakina na juya na fita ban tsaya a ko'ina sai cikin banɗaki na zauna na ci kuka kamar raina zai fita har sai da na godewa Allah.

Na fito na zauna na yi jigum na kasa shiga cikin ɗakin kuma na rasa wanda zan sanarwa damuwata ko da zan ji sanyi a cikin raina. Ko na yi yunƙurin aikata hakan ikirarin tsinuwan da Umma da yi mini idan na yi maganar da kowa sai na ji duk jikina ya yi sanyi ƙalau kamar kazar da aka jefa da ruwan gishiri. "Amatullahi baiwar Allah. Ina fatan dai lafiya ko? Kin zabga tagumi da safiyar nan". Muryar Baban Adnan ya dira a ƙofofin kunnuwana da ya tursasa mini cira kaina ina duban sa yana tsaye a kaina ya zuba mini idanuna kamar yau ya saba kallona.

"Ina kwana".

Na jefa masa gaisuwa maimakon ya amsa sai ta jefa muni wata tambayar ta daban da ba ta da haɗi da zancen da na yi masa. "Murmushi ne ya fi dacewa da fuskarki ba tagumi ba". Ban ce da shi uffan ba na tashi zan shige ɗaki muka yi kiciɓus da Umma za ta fito daga ɗakin na matsa na ba ta hanya ta wuce kafin ni ma na shige ciki. Kai tsaye cikin ɗaki na nufa raina a jagule gabaɗaya na rasa gane abin da yake damuna balle har na iya siffanta shi cikin kalma guda. Duk wani addu'ar da ya zo kaina a lokacin sai na yi sa don kawai na samarwa kaina sauƙin halin da nake ciki na suya da radaɗin zuciya.

Ina kwance akan gado na ji an ɗanna mini dundun a gadon bayana ban motsa ba. Illa runtse idanuna da na yi ina cije leɓena don na san babu wanda zai yi nuni hakan face Amira. Ba tare da na buɗe idona ba na furta"don Allah Amira ki bar ni, ba na cikin yanayin da za ki yi mini irin wannan wasan. Ki bar ni da abin da yake damuna kawai.....". Kafin na rufe bakina na ji ta ɗane kan gado ya na jan ƙafata take faɗin"tashi ki sanar da ni abin da yake damun nan ki". Na ƙare runtse idanuna"don Allah ki bar ni". Na ƙare zancen ina juya mata baya amma hakan bai hana ta aikata abin da ta yi niyya ba.

"Wallahi sai kin tashi ki yi min bayani. Tun jiya na fahimci kina cikin damuwa amma kika ce da ni babu abin da yake damun ki. Amatullah ni da ke fa yanzu mun wuce matakin ƙawayen da zaman gidan haya ya haɗa mu, mun zama tamkar ƴan uwan da suka fito daga cikin ɗaya da ba za iya ɓoyewa junansu komai".

Na ja dogon numfashi na fesar ina tashi na zauna kana na sama zarafin faɗin"tabbas ina cikin matuƙar damuwa amma ba zan iya sanar da ke abin da yake damuna ba. Iya ƙaunar da za ki gwada mini shi ne ki taya ni da addu'a Allah ya kawo mini sauƙi da mafitan halin da nake ciki".

Ta yi ƙuri tana kallona har na kammala zancen ba tare da ni komai. Ta riƙo hannuna ta sa cikin nata tana murzawa a hankali kafin ta soma cewa"in sha Allah zan taya ki da addu'a Allah ya yaye miki duk abin da yake damunki. Amma don Allah ke ma ki cire damuwa daga cikin ranki. Rayuwar nan fa kowa kike gani yana da na shi matsalar, idan kika zauna kika ji damuwa da matsalar wani wallahi sai kin yi mamakin yadda zuciyarsa ta iya ɗaukar wannan abun kuma har take iya yin dariya da walwala. Amatullah haƙuri, juriya da miƙa lamuranka ga Allah su ne kaɗai abubuwan da suke wadata rayuwar ɗan Adam da haske kowa kuwa ƙunci da baƙin ciki ya yi masa katutu".

"In sha Allah zan yi amfani da shawarwarinki Amira na gode sosai". Na ƙare zancen hawaye suna gudu a fuskana, ta sa hannu tana share mini su tana yi mini tsiya. "Daɗina da ke ragwanta abu kaɗan sai kuka, kamar yaron da aka ƙwace wa alawa". Dariyar yaƙe na yi ina kallonta kan ka ce kwabo ta warware mini duk ƙullin da yake ƙasan raina. Ta ja hannuna muka sauƙa daga kan gadon. "Mu je mu ci abinci ga shi can sai mu fita tallan ko?". Kaina kawai gyaɗa mata muka fito daga ɗakin muka shiga na su, muka ci abincin tare tana ta ja na da hira har muka gama. Muna gamawa na yi wanka na shirya ita ma ta kimtsa ta fito lokacin har ƙarfe taran safiya ya wuce amma har lokacin babu Abba babu labarinsa.

Muna fitowa ƙofar gida na hango Abba ya ɓullo daga can ƙarshen layinmu yana turo keken sa hannunsa ɗaya riƙe da leda. Ina ganinsa na ji duk jikina ya mutu murus hawaye suka ciko mini kurmin idanuna ganin yadda yake ta gumi ga takalmin ƙafarsa da ya tsinke yana tafe yana tura keken da yake ƙara gaskata mini hashashen zuciyata na cewa faci keken ta yi. Ba mu gusa ba har sai da ya iso na isa zan karɓa ledan hannunsa ya dakatar da ni.

"A'a Uwata bar shi kawai, ai na iso ma". Cikin wani irin yanayi na karyewar zuciya na furta"sannu da dawowa". "Yauwa sannu. Har za ku tafi kenan? To Allah ya kiyaye ya ba da kasuwa mai albarka". Yana dasa aya ya sa kai zai wuce cikin gidan ko gaisuwar da Amira ta yi masa sama-sama ya amsa.

"Yau kuwa lafiya na ga Abba a wani irin yanayi?". Ta tambaye ni cikin tsantsan mamakin da ya bayyana ƙarara akan fuskanta. Na sauƙe numfashi kafin na ce"yadda kika gan sa ni ma haka na gan shi yau". Daga haka na wuce gaba tana biye da ni a baya. Muna zuwa ƙarshen layinmu na ji ana ƙira sunana, tare muka waiga dukkanmu ni da Amira muna kai dubanmu izuwa idan muke jiyo sautin ƙiran.

Na dafe ƙirjina ina waro idanuna waje"na shiga ukuna! Sarkin Aska". Amira ta bi shi da kallo har ya iso gabanmu ya zube dukkan hannayensa a cikin aljihun wandon jamfan da yake jikinsa yana kallona. "Barka da fitowa yake tauraruwar da take haska duniyata".

"Me ya kawo ka unguwanmu?" Ya saki taƙaitaccen murmushi kafin ya amsa mini cikin faɗin"laifi ne don na zo inda kike? Ko kin manta an ce garin masoyi ba ya nisa. Kusan kullum sai na zo nan na tsaya don kawai na ga wucewar ki hakan ya na taimakawa wajen saisaita bugun zuciyata da daidaita fitar numfashina. Amatullah ke ce sanyin idaniyata, ke ce a cikin tunanina a farke ko a cikin bacci....". Bai gama ba na ɗaga masa hannu alamar ba na ƙaunar jin ragowar zantukan da za a fito daga bakinsa.

"Ya isa haka ya isa. Ban tsaya a nan don ka dinga zayyana mini abin da yake cikin zuciyarka ba. Zan ƙara jadadda maka ka fita a harkata don girman Allah na roƙe ka".

"Ba ni da ikon akan zuciyata balle na sama damar kitsa abin da zai zauna a cikinta ko wanda zai fita. Ina sonki shi ne kawai abin da na sani kuma na yi imanin babu abin da zai sauya hakan komai wuya komai runtsi".

Tsaki mai dogon zango na saka ina wurga masa harara na ja hannun Amira muka bar wajen cikin sauti. Har muka isa tashan raina a ƙuntume kamar wacce aka aikowa da sauƙon mutuwar uwa da ubanta. [7/29, 5:39 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

___________________________________

Page 1️⃣7️⃣

Haka na zauna fuskana gabaÉ—aya babu annuri raina, akan idona Amira ta ware wasu ta away ta ajiye a gefenta ta ce wannan ba na sayarwa ba ne. Dafo kafaÉ—ana da ta yi shi ya fizgo hankalina zuwa jikina na cira kai ina duban ta tare da É—age mata ido É—aya alamar lafiya. Ta yi mini ishara da idonta na bi inda take kallo da ido can na hango Bashir tafe ya nufo inda muke zaune, yana tafe yana washe baki kamar gonar auduga. Tsaki mai dogon zango na ja ina É—auke kaina gefe guda na buÉ—e baki zan yi magana kenan ta riga ni.

"Don Allah kar ki ce komai Amatullah. Ki yi wa Allah ki yi wa annabi ki saki fuskarki a bawan Allahn nan. Ko sau ɗaya ne in ya yi miki magana i masa masa, kin san fa an ce gaida mai gaishe ka ko ba zai amsa ba". "Don girman Allah ki bar ni Amira ki bar ni da abin da yake damuna ma ya ishe ni. Ba sai kin ƙara mini wani ba".

Ina rufe bakina yana isowa wajen ya zauna a kan bencin da yake fuskantar mu. Ya soma zuba kamar bishiyar magarya. "Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da yake da ikon juya dare zuwa safiya. Kuma ya yi mini tagomashin yin tozali da kyakykyawan suranki a matsayi abin mafi kyau da burgewa da na fara gani a wayewar garin yau. Da ke da na kwana a cikin ƙirjina shi yasa yau na yi ƙudurin zuwa na ganki kafin na aiwatar da dukkan ayyukan na ranan yau".

"Kan bala'i! Bash yana kashe wuta ina bin ka da fetur. Irin wannan kalaman tashin kai haka ai ni da nake gefe ma kana sawa na fice daga cikin duniyar balle ita kuma wacce ake yi domin ta".

"Babbar yarinya ke dai ki kawai lamarin ya wuce duk yadda kike tunani da zato a cikin zuciyata. Ban taɓa ɗanɗana garɗin soyayya ba sai yanzu da na faɗa kogin soyayyar Amatullah". Raina ya cika fam zuciyata tana tafasa tamkar talgen da aka aza a bisa wuta, na gaza cewa da su komai illa hararar da nake banka musu a faƙaice. "A zuba min kunun. Don yau na yi wa kaina alƙawarin ba zan sha komai dangin abin sha ba sai na fara shan wannan daddaɗan kunun nakin, ya ke Gimbiyata".

"Na nawa kake so?".

Na furta zancen a zaffafe kamar zai kai masa duka. Hakan ya sanya Amira kallo ni tare da faɗin"Haba! Amatullah ya haka kamar da gaba? Ki tuna wanda ya ce yana sonka fa, komai lalacewarsa ya fi maƙiyi". "To laifi ne don na tambaya na nawa yake so?". Ta jijjiga kanta alamar a'a tana ƙunshe dariyar da yake son kufce mata. "Ban so kika dakatar da ita ba, ko kalmar zagi da cin mutumci ne zai fito daga bakinta ina son na ga waɗannan kyawawan leɓan natan suna motsawa. Ki ba ni na ɗari biyu". Ban tanka masa ba na zuba masa na dosara masa a gabansa. Ya ɗauka yana sha yana ta suturan da sam ba na gane kansu balle gindinsu, da na ga zaman ba zai fishshe ni ba na amshi wayar Amira ina kallon hotuna.

Muna zaune har masan ya ƙare duk wanda ya zo sayan kunun ya yi mini wata maganar ko ya yabi surar jikina, sai na fasa sayar masa na kuma buga masa rashin mutunci. Hakan ya sa ban yi ciniki da yawa ba. "Bari na kai wa Naziru masarsa". Na bita da kallo yayin da take miƙewa tana ɗaukar take away ɗin. Na janye hannuna daga tagumin da na zagba kafin na sama zarafin faɗin. "Ni fa Amira na lura zaman cikin tashan nan ban gishiri a baka manda ne. Sai ka mayar da kanka bolar da kowa ta kwaso jujinsa zau juye akai. Allah ya sani ba zan iya wannan rayuwar ba".

Ta tsaya tana kallona"bari na je na dawo sai mu yi magana. Kar na bar shi yana jira na". Tana dire zancen ta juya ta bar wajen wanda hakan ya yi daidai da sauƙe sakakken ajiyar zuciyar da na yi ina zabga wani uban tagumi kamar wacce aka aikowa da saƙon mutuwa. "Yan mata adon gari idan ba ku gari ya ɓaci idan kuka yi yawa gari ya ɓaci". Kalaman da suka dira a ƙofofin kunnuwana kenan da suka tursasa mini ɗago kaina ina ƙarewa mutumin kallo tun daga sama har ƙasa. Babban mutum ne wanda a ƙalla zai kai sa'an Abbana a kwanakin duniya ya yi shigar kamala cikin cikakken jamfa har ƙasa ga jakar kaya riƙe a hannunsa. "Me ye kike tsayarwa ne ƴan mata?". Ya kuma jefa mini wani tambayar a karo na biyu har lokacin idanunsa ƙar a kaina ba ya ko ƙiftawa.

"Kunu ne. Na nawa za a zuba maka?". "Ga shi kuma ni ba na shan kunu. Sai dai na sha mai tsayar kunun". Tsam! Na miƙe kamar wacce aka tsigarawa alluran doki na tsaya ƙyam akan ƙafafuna duk da rawar da suke yi mini tsabar firgicin da zancen nasan ya jefa ni a ciki. Muryarta har sarƙewa yake yi idanuna yana kawo ruwa na soma faɗin"wani irin banzan magana ne wannan bawan Allah?. Babban mutum ne kai don haka ka ja girmanka don billahillazi idan ka yi gigin zubar da ni babu abun da zai sa ba zan sanya ƙafa na tatttake sa ba. Ni ba iskanci ne ta fito da ita daga gidanmu ba face sana'a". Kafin na rufe bakina na ji ya ɗauke ni da mari kafin na yi aune ya ƙara sauƙe nuni wani marin a karo na biyu na ɗayan kuncina. Na ɗago kaina a gigice sai dai kafin na sama zarafin cewa wani abun tunin ya tari numfashina.

"Ke yarinya kar ki sake ki yi min rashin kunya irin na ku na Æ´aÆ´an zamani. Ni nan da kike gani na shekaruna É—aÉ—É—aya shekaru sittin da biyu a duniya. Jikata da farko yanzu haka tana gidan aurenta har da Æ´aÆ´a, da kina da mutuncin ni É—in nan na matsayin uba ya kamata ki kalle ni".

Na dafe kuncina raina cike da fal da takaici. Ƙirjina yana dakan lugudan tara-tara sau goma sha tara. Ruwan da ya wadaci kurmin idanuna suka kwaranyo akan kuncina. "Ai ba ka riƙe girmanka ba ne shi yasa har na sama fuskar gaya maka ko wani irin magana". Na yi maganar jikina har ɓari yake yi tsabar ɓacin rai da ƙuncin da nake cikinsa. Kafin ka ce kwabo mutane sun cika a wajen kamar kai ka ce kisan kai aka yi a wajen ko kuma wani babban laifi. Girmamawa da mutuntawan da duk wanda ya zo wajen yake yi wa mutumin shi ya fi komai ɗaure mini kai da jefa ni cikin kokonto. Wasu har tsunguwana suke yi har ƙasa kafin su gaishe shi ko ya miƙo musu hannu don su yi musabaha ba sa miƙa nasu.

"Wai me ye yake faruwa ne ya Sheik? Me ye ya haÉ—a ka da wannan yarinyar?". ÆŠaga daga cikin mutanen da suka cika a wajen ya jefawa mutumin tambaya kafin ya amsa masa wani ya amshe zanen ya soma furzar da zancen da yake cikinsa cikin tsananin fusata, tamkar zai kai mini bugu. "Allah dai wadaran naka ya lalace. Yanzu ke don fitsara da rashin kunya ki dubi tsabar idanun wannan mutumin da ya yi kusan jika da ke kina yi masa rashin kunya irin na ku na Æ´aÆ´an zamani. Ke kam alla wadaran halinki hakan ya nuna ba ki sama kyakykyawan tarbiyya ba a gida".

"Alhaji Mamman ka yi haƙuri mana mu ji ta bakinta. Kafin mu yanke hukunci". Ɗaya daga cikin mutanen wajen ya furta kafin ya juyo yana dubana tare da faɗin"ke yarinya me ye haɗinki da wannan mutumin kar kika nema ki yi masa raini da rashin kunya". Duk yadda na so na yi magana lamarin ya gagara hawaye ne kawai suke gudun famfalaƙi akan kuncina na kasa furta ko da kalma guda. Ana cikin haka Amira ta dawo ta tambayi me ke faru aka mayar mata da ba'asi ita ta yi ta masu haƙuri, amma da farko tsayawa suka yi tsayin dakan akan sai sun lakaɗa mini na jakuna. Yayin da manyan wajen suke ta ba wa mutumin haƙuri kamar wanda aka yi mata wani gagarumin zunubi. Da ƙyar Amira ta shawo kansu shi ma sai da taimakon samarinta na wajen da suka sanya baki. Ƙurar tana lafawa na fara harhaɗa kayan tallana, Amira ta riƙe ni tana jijjiga ni"wai Amatullah me ye yake damunki ne? Hauka kika yi ko kuma aljanu ne suka shafe ki?".

Na kawar da hawayen idanuna kafin na sama lasisin faÉ—in"babu ko É—aya kawai tafiya zan yi ne". "To ki tsaya mu nema almajirai su É—eba mana kayan mana". Ban kula ta ba na ci gaba da tattare tattaren da nake yi. Ta nema almajirai suka É—eba mana kayan muka bar wajen har yanzu hawaye ba su daina kwaranya daga idanuna ba.

"Don girman Allah ki nutsu ki daina wannan kukan haka ya isa mana. Ki bari mu je gida mu zauna sai mu tattauna akan lamarin". Na shece majinan kukan da ya zo mini kafin na ce"Amira ba zan taɓa samun kwanciyar hankali ba har sai na san wane ne wannan mutumin, da ya ƙware a munafurci da launa zance". Kafin na gama ta yi saurin kai tafin hannunta ta rufe mini baki.

Kamar mai raɗa ta soma cewa"ke Amatullah ki rufa mana asiri, kar wani ya ji ki kina wannan maganar. Kin san waye wannan mutumin kuwa? To idan ba ki sani ba ki saurara ki ji wannan mutumin sunansa Sheik Dawood Nasarawa babban malamin addini ne a jihar nan da ma kewayenta, ya yi shura sosai a fannin ilimin addini da sanin hukunce-hukuncensa. Sannan kuma malamin jami'a ne a babban jami'in jihar na koyar da kimiyya da fasaha kuma na ji an ce ma ba a iya wannan jahar yake koyarwa ba. Kin gan sa nan babu wani abun duniyar da za a ba shi ta ruɗe sa haka nan babu adadin kuɗaɗen da za a ba shi a rinjayi hankalinsa, kin gan sa nan ko motar kansa bai da shi. Duk wani shugaban da ya yi ba daidai ba ga al'ummarsa ba ya ragar masa fitowa yake ya tsigale shi ba tare da fargaba ko tsoron abin da kan je ko ya dawo ba. Da yawan mutanen suna yi maka kirari da murucin kan dutse ba ka fito ba sai da ka shirya wasu kuma su ce da shi gaskiya dokin ƙarfe".

Ba kaɗan ba kalaman Amira suka daki ƙwaƙwalwata tare da munana ƙalbina. Take yanke zuffa ya soma tsatstsafo wa daga jikina. Na yi maza na cafko hannunta na riƙe gam saboda rawar da ƙafafuna suke yi. "Ki na nufin wannan mutumin shi ne Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe?". Na galla mini harara"ƙwarai kuwa shi ne". Na dafe kaina ina karanto auzila kafin na ci gaba da magana cikin tsananin kaɗuwa da ruɗewa. "Na daɗe da sanin muryarsa babu wani malamin da nake bibiyar wa'azinsa kamar sa. Hatta Abba yana son wa'azinsa saboda yadda yake feɗe gaskiya komai ɗacinta".

Ta zame hannunta daga cikin nawa kafin ta furta"kowa ya san wannan. Don kwanakin baya duk inda kika shiga a garin nan maganarsa ake yi. Mai girma gwamna da kansa ya ba yi masa tayi wani gwagwgwaɓan matsayi a gwamnatance da alƙawarin buɗe jami'a mai zaman kanta a damƙa masa ragamarta kuma a sanya mats sunansa. Ban da alƙawarurrukan zunzurutun kuɗin da abubuwan more rayuwa da ya yi masa, amma duk da haka ya ƙi karɓa".

"Na rantse da girman wanda rayuwata take hannunsa ban san fuskarsa a zahiri ba. Kuma shi ya fara tara ta da maganan banza".

Ta yi hanzarin katse ni"ki rufa mana asiri Amatullah. Ko a mafarki mutumin ba zai taɓa tarar wata mace da maganar banza ba saboda dattakunsa yana ƙoƙarin kiyaye duk wani abun da zai taɓa martaban kimarsa. Ke dai kawai ki tsori ta ne da kalaman Bashir suna yi miki amsa-kuwwa a kunnenki". Na ja dogon numfashi na fesar kafin na ce"wallahi babu kuskure cikin abin da na faɗa miki Amira". "Ki yi shuru haka ya isa". Tana rufe bakinta ta ja hannuna muka ci gaba da tafiya, har muka isa gida na kasa magana kamar gunki tafiyar kawai nake yi ba tare da na san inda nake ajiya ƙafana ba. [8/4, 7:11 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_______________________________________

Page 1️⃣8️⃣

Muna isa na wuce ɗakinmu na yada zango a falo ina mayar da nurfarfashi kamar wacce ta yi gudun ceton rai. Sai Amira ce ta shigo mini da kayan tallan ta juya ta fita bayan ta gama jeranta mini maganar da ban ba ta amsar ko guda daga ciki ba. Yadda na ji falon ya yi shuru ya tabbatar miji da cewar Umma ba ta cikin gidan amma na fi zargin cewar ba ta yi nisa ba tun da ga shi ba ta rufe ƙofa ba. Ina zaune a wajen Abba ya fito daga ɗaki yana saka hula akansa, na maza na tashi na gyara zamana ina yi masa sannu da fitowa. Ya amsa mini yana neman waje ya zauna, mamaki ya hana ni yin wani motsin kirki na shiga duniyar tunanin dalili da ya hana Abba fita wajen aiki, a iya sanina da shi baya fashin zuwa wajen aiki in ba tare da wani ƙauƙauran dalili ba.

"Har kun dawo kenan?". Na gyaɗa masa kaina da hakan ya ba shi zarafin ci gaba da maganar da ya sani daskarewa a wajen, na sha jinin jikina ainun. "Ummanki ce ta fita tun ɗazu ita nake ta jira ni ma shi yasa ban fita ba". Na ɗaga ido ina kallonsa"Abba da ka yi tafiyar ka ai, wataƙila ba nisa ta yi ba". Ya jijjiga kansa kafin ta ce da ni"A'a Amatullah ko na fita hankalina ba zai kwanta ba. Zan fi samun nutsuwa idan na ga ta dawo cikin ƙoshin lafiya". Na yi shuru na kasa yin magana don na ga lamarin ya fi ƙarfin kwanyata, tausayin Abba ya cika mini sashin ruhina har ƙwalla suka ciko mini kurmin idaniyata. "Ya islamiyyarta kun kuwa? Ya batun sauƙanku yaushe ne?".

Na musguta kafin na ce"islamiyya alhamdulillah, Abba nan da sati huɗu ne sauƙar in sha Allah". Ya jinjina kansa"Allah ya nuna mana lokacin, za mu yi magana da Ummanki sai mu ga abin da ya dace ayi". "Ina godiya Allah ya ƙara girma. Bari na sa maka ruwa a buta an yi ƙiran salla". Na ƙare zancen ina miƙewa na fita waje na sa masa ruwan alwala a buta kana ni ma na yi nawa. Na shiga cikin ɗaki bayan na sanar da shi na saka ruwan. Ko da na iddar da sallan na daɗe a zaune na gaza gane me ye yake yi mini daɗi. Ƙur'anin da na ɗauko zan yi muraja'a ma na gaza karanta ko aya guda, ganin wankin hula yana son kai ni dare ya tursasa mini tashi na fara shirin tafiya islamiyya, sauran kunun da na dawo da shi na sha kafin na fito har lokacin Abba bai dawo ba. Don haka na shiga ɗakin su Amira na sanar da ita idan Abba bai dawo ba ta ja mana ƙofar falon.

Ina fitowa daga cikin gida na hango Abba yana dawowa na tsaya har ya iso wajen. "Har kin fito za ki tafi?". Na É—aga masa kaina. "Kin cin abinci ne?".

"Na sha kunu". Cike da kulawa ya ce"kunu ai ba abinci ba ne Uwata, ga wannan naira darin ki sayi ko awara ce ki ci in kin isa". Cikin girmamawa na amsa ina yi masa godiyar da yake amsawa cikin daɗin rai, muna tsaye a wajen muka hango Umma tafe, jikina ya yi matuƙar sanyi ganin yadda Abba gabaɗaya ya gigice daga ganin ta tun kafin ta iso wajen ya ɗauki hanyar zuwa gare ta da rawar jiki ya amshi jakar da yake maƙale a kafadarta. Yana ta yi masa sannu ta yi biris da shi har suka iso inda nake, na yi mata sannu ta amsa mini a daƙile tamkar an yi mata dole.

"Ai ke na tsaya jira ki dawo kafin na fita".

Ta gantsalo masa harara kamar ta yi arba da kashi"ko yanzu da na dawo ɗin uban me ye zan tsinana maka?. Yanzu kam ga ni ai sai ka dafa ni ka cinye, babu dama na motsa ko wani wajen sai ka titsiye ni da tambayoyin babu gaira babu dalili". Ya yi shuru tare da sadda kansa ƙasa ba tare da ya ce komai ba. Ta kuma jan wani uban tsaki kafin ta zarce da faɗin"wuce mu shiga ciki yanzu ko". Ta yi zancen lokacin da yaran gidan da iyayensu maza da suka je masallaci suka nufo inda muke tsaye.

Tamkar raƙumi da akala haka Abba ya bi bayanta suka shiga cikin gida, na yi maza na goge hawayen da suka zubo mini ba tare da na shirya musu kafin na ɗauki hanyar bari wajen. A hankali nake tafiya tamkar wacce aka zarewa laka na shawo layin da zai sada ni da islamiyyar kenan na ji an danna mini horn ɗin mota har sai da na riɗime na rasa inda zan yi na tsaya kawai cak na ɗaura hannuna aka na lumshe idanuna ina jiran na ji da inda motar za ta buge ni.

"Ƴan matan buɗe idonki mana".

A hankali na soma buɗe idanuna kafin har na buɗe su tar akan sai da gabana ya faɗi, saboda kwarjinin da ya yi mini a ganin farko da na yi masa. Na yi saurin ja da baya ina dafe ƙirjina dole na yi ƙasa da idona. "Na razana ki ko? Ki yi haƙora tuba nake yi. Ban lura da ke ba sai na zo dab dake". Shuru na yi ban amsa masa ba sai dai hakan bai hana sa ci gaba da furzar da zancen da ke cikinsa ba.

"Ko sai na durƙusa akan gwiwoyina ne sannan za ki haƙura".

"To ai ni babu abin da ka yi mini ba". Na yi maganar ina ƙoƙarin wucewa ya yi saurin shan gabana. "Na razana ki mana baiwar Allah. Kuma kin san an ce tsorita musulumi haramu ne. Don Allah ki furta ki yafe min raina zai fi samun nutsuwa, don akan hanyar nake zan yi tafiya mai nisa. Ki taimaka min kar na tafi da haƙƙin wani a kaina". Na cira kai na yi masa kallo guda kafin na janye idanuna"kamar yadda na gaya maka ba ka yi mini komai ba, amma tun da ka matsa na haƙura Allah ya kiyaye hanya ya kai ka lafiya". Ina gama maganar na wuce na soma tafiya cikin sauri saboda lokaci ya riga ya ƙure kafin na iso har Malam Suleiman ya shigo ajinmu ana karɓan hadda na shiga na zauna na buɗe ƙur'anina, duk yadda na so biya karatun lamarin ya gagara wai cire wando ta kai, ji na yi kamar ba a taɓa karanta mini wajen ba a kaf cikin rayuwata. Ina ta ƙoƙari haɗa kalmomin amma ya ci tura har aka iso kaina na tashi na isa gaban Malam Suleiman, sai dai na gaza karanta ko aya guda sai faman kame-kame nake yi.

"Amatullah anya ki biya karatun nan a gida kuwa?".

Na yi ƙasa da kaina don ni kaina na san duk abin da zai fito daga bakina a lokacin ƙarya ne. "Malam na yi amma......". Kafin na ƙarisa ya dakatar da ni"koma ki zauna idan an fito salla ki zo ki same ni". "To Malam". Na amsa da shi ina tashi daga wajen na koma mazaunina na zauna, na kwantar da kaina akan desk ban ɗago ba har sai da aka fita sallan asr Rauda ta taɓo ni na tashi muka fito muka yi alwala, muna iddar da sallan na wuce wajen Malam Suleiman.

Yana zaune a cikin staff room na shigo na zauna, sai da ya gama rubutun da yake yi kafin ya gyara zamansa yana fuskanta na da kyau ya soma magana. "Amatullah mene ne yake damunki? Me ye ya yi miki zafi a cikin rayuwar nan?". Kalamansa suka daki ƙwaƙwalwata tare da raunana zuciyata, na ɗau tsawon lokacin wani bai yi mini irin wannan tambayar ba. "Babu abin da yake damuna Malam".

"Kar ki yi ƙarya don fuskarki ta riga da ta bayyanar da labarin zuciyarki. Amatullah dole akwai wani abun, tun da ga shi har ya fara taɓa karatunki, duk wanda ya sanki a makarantar nan ya san ki ne saboda dalilai guda biyu na farko ƙoƙari da mayar da hankalin da kike da shi akan karatu na biyu kuma ladabi da biyayyarki".

"Babu komai akwai dai matsalolin rayuwa ne na yau da kullum, kuma yanzu a rayuwar nan kowa da irin na shi kalan damuwar".

Ya yi ɗan jim kafin can ya yi magana cikin taushin harshe"na fahimta kuma ina fatan haka ɗin ne. Kar ki saka komai a ranki ki miƙa wa Allah dukkan lamuranki don shi kaɗai ne zai iya magance miki matsalolinki, kin ga rayuwar nan kowa da na shi matsalar idan kika ji na wani sai ki ji na ki ko kashi ɗaya bai kai cikin kashi ɗarin nasa ba. Kar ki bari ki ɓata shekarun da kika yi a baya kuma karatu mussamman yanzu da aski ya zo gaban goshi".

Cike da gamsuwa da zantukansa na ce"in sha Allah Malam ina godiya sosai". Haka na tashi na baro cikin staff ɗin jikina duk a sake, na koma aji har aka tashi ban dawo daidai ban tsaya jiran su Rauda ba na yi tahowa ta, ina tafe kaina a ƙasa na ji ana yi mini sallama. Da farko ban amsa ba sai da aka ƙara yi a karo na biyu kafin na amsa tare da waigawa bayana. Na yi turus na tsaya ganin mutumin da muka haɗu da shi ɗazu da zan taho ne kafin na yi magana ya riga ni.

"Na ƙara tsorita ki ko?"

Na jijjiga kaina na juya zan ci gaba da tafiyata ya kuma tsayar da ni. "Har kun tashi daga islamiyyar kenan? Ai tun É—azu nake tsaye a nan ina jiran dawowanki". "Don Allah bawan Allah kar bar ni haka nan".

"Zan bar ki ne kawai idan har na tabbatar da cewar kin isa gida cikin ƙoshin lafiya, ba tare da wani ya ƙara firgita ko tsoritar da ke ba". Na ɗaga kai ina kallonsa ganin ya bar motar ya soma bi na da ƙafa. "Ba ka tsoron a ɗauke motan ka baro ta a can?". Ya murmusa kafin ya ce"na bar ta a hannun Allah, na yarda kuma duk abin da ya zartar babu kuskure a cikinsa".

"To ka koma kawai na gode da rakiyar". Ya ɗan ranƙwafo da kansa ya rage tsayinsa ya ce"don Allah kar ki hana ni aikin lada. Ni ma fa ina da ƙanne mata kuma na san yanayin rarurarsu, yanzu haka a gajiye kike".

Taƙaitaccen murmushin gefen baki na yi kafin na furta"babu alamar gajiya ni kam". "Kar ki faɗa abin da ba shi ne a cikin zuciyarki ba don fuskarki ta riga da ta bayyana gaskiyar da kike ɓoyewa".

"Wai me yasa mutane da yawa suke cewa fuskana yana bayyanar da labarin zuciyata ne?".

Ya ɗage girarsa guda"wataƙila zuciyar ce ba ta son a zarge ta da kasancewa daga cikin maƙaryata". Babu shiri na ji dariya mai sauti ya ƙwace mini na sake ina yi babu ƙauƙƙautawa. Sai da na tsagaita don kaina kafin na ce"kai dai da abin dariya kake". "Ɗabi'ata ce son ganin wani yana farin ciki a sanadina. Yanzu dai mu je na raka ki ko". Ban ce da shi komai ba muka fara tafiya yana ta ja na da hira ina amsa masa har muka isa farkon layinmu na dakata a nan. "To rakiyar ta isa haka kar na ja ka da nisa. Kuma ka ce tafiya ce a gabanka".

"Tafiya ce kam a gabana mai nisa amma na zaɓi na tsaya na fara sauƙe haƙƙin da yake kaina".

Na ɗage masa ido ɗaya alamar ban fahimci zancen ba haka ya ba shi damar ci gaba da zancen"haƙƙin tabbatar da cewar wani bai sake razana ki ba mana". "Da ba ka fasa tafiyarka ni kam babu wani matsala, ni da ko sani na ma ba ka yi ba". "Ina ji a jiki zuwa gaba zan zama ɗaya daga cikin mutanen da suka fi kowa saninki, yanzu dai mun iso ne kika tsaya a nan?".

"Ba mu iso ba amma ga can gidan mu daga nan ma ina hango sa". Na ƙare zancen ina nuna masa gidanmu da ƴar manuniyar ƴatsata. "To tun da kin hana ni aikin lada bari na tsaya daga nan, sai dai har za mu rabu ba ki tambayi sunana ba alhalin ni kuma na san naki". Na ware idanuna"a ina ka san sunana bawan Allah?". "Zuciyata ce ta sanar da ni". "To me ye ta sanar da kai?". Ya juya manyan fararen idanun"Safiyya". Na jijjiga kaina"tun da na ɗan ji tausayinka bari na sanar da kai. Sunana Amatullah".

"Ni kuma sunana Muhammad Taukeeq".

Na jinjina kaina"ina godiya, Allah ya kiyaye hanya". Cike da jin daÉ—i ya ce"Amin na gode, ki fara wuce wa tukunnan". Murmushi kawai na yi na wuce izuwa gida har na isa annuri bai gushe daga fuskana ba. [8/4, 8:52 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_________________________________________

Page 1️⃣9️⃣

Kai tsaye na wuce ɗakinmu ba tare da na mayar da hankali akan tunkoson jama'ar da suke tsaye cirko-cirko a cikin gidan ba. Sauya kayan jikina na yi na fito na soma haɗa wuta saboda wani irin masifaffan yunwan da take ƙwaƙulan hancin cikina da tun suna kukan yunwan har sun saduda. A wajen na tsinci kan zancen wai sata aka shiga ɗakin Maman victor aka yi mata na turamen zannuna da kuɗi. Sosai aka yi dambarwa kamar ba za su bar juna da rai ba, sai da wasu biyu daga cikin manyan dattijan unguwa suka shigo suka tsawatar saboda hayaniyar ya ƙai ƙololuwar yawa. Taliya na tafasa fara na ci na zuba mata mai da yaci na ci nawa na bar wa Umma da Abba na su a kula, ina gamawa na fito na yi alwala na koma ciki na gabatar da sallan kasancewar yau ba mu da karatu da yaran da nake koyar da su, hakan ya sa ina iddar da sallan na ɗauko alƙur'ani na soma karanta ban gushe ina yi ba har sai na haɗa izu biyu cif-cif. Na yi sallan isha'i na fito falo na zauna don har yanzu Umma ba ta dawo ba haka nan ma Abba tun da na shigo ban shi ba, kuma a sanin da na yi masa tun runtsi ba ya wuce ƙarfe taran dare a waje.

Kamar an jefo ta haka Amira ta faɗo cikin ɗakin ta manna mini waya kunne, na bi ta da kallo. "Mansur ne za ku gaisa". Na riƙe wayar ina yi masa sallama ya amsa, haka muka gaisa cikin girmamawa da mutunta juna kafin na miƙa mata wayar, ba su yi wani dogon magana ba ita suka yi sallama. Ta ajiye wayar tana kallona. "Ba ni labari mana?". Na ɗage mata gira"ban gane ba wani irin labari kenan?".

"Kar ki raina min hankali mana Amatullah. Wane ne wannan mutumin da É—azu kuka tsaya da shi a bakin layin nan, kuna ta hira kamar kun daÉ—e da sanin juna".

Fuskana ɗauke da mamaki ƙarara na furta"waye ya sanar da ke wannan labarin?". Ta sheƙe da dariya kafin can ta soma cewa"da idona fa na ganki, na so na je na tutsiye ki a wajen sai kuma na sauya shawara". Na yalwata fuskana da yalwataccen annurin da yake fitowa tun daga ƙasan zuciyata.

"Wallahi ni ma ban san ba ban taɓa ganin sa sai yau ɗin nan. A hanya muka haɗu shi ne ya tsaya jirana har muka taso daga islamiyya, ya dage wai sai ya rako ni gida saboda kar wani ya ƙara tsorita ni kamar yadda ya tsorita ni da horn ɗin motarsa". Na ƙare zancen ina baza murmushi kamar wacce aka yi wa alƙawarin kujerar makka na bana. Sake da baki Amira take kallo na har na gama zancen kafin ta musguta tana faɗin"amma ai ba shi ne mutum na farko da ya taɓa nuna buƙatar yi miki rakiya ba, kika watsa musu ƙasa a idanunsu. Shi wannan me yasa kika amince masa har kika sake masa fuska".

"Wannan ya bambamta da duk wanda na taɓa haɗuwa da su akan hanya". Ta katse ni"me ye ya bambamta shi da sauran?". "Saboda har muka rabu da shi bai yabi sura ko halittan jikina ba. Saɓanin sauran samarin da nake cin karo da su maganar farko da yake fara fitowa daga bakinsu shi ne yabon surana".

"Ki na da gaskiya da wannan fannin. To ba ni labari me ye kuka tattauna?". Na galla mata harara"ban sani ba uwar son gulma da bin ƙwaƙwƙwafi". "Shikenan in ta yi tsami ai za mu ji". Na gyara zamana na kawar da zancen ta hanyar sauya akalar maganar"wai ina Umma ta je ne ga Abba ma har yanzu bai dawo ba?". "Umma ta dawo ta ƙara fita. Shi kuma Abba bai fita ba ma sai da aka yi ƙiran asr".

Na ɓoye mamakina na ce"Abban?". Ta gyaɗa mini kai alamar e tana ci gaba da cewa"me ye wani abin mamaki?". "Babu daman ina so mu yi magana akan wannan malamin da muka haɗu da shi a tasha.......". Ta ɗaga mini hannun na dakata haka.

"Ki rufa mana asiri Amatullah kar wani ya ji ki kina maimaita wannan maganar, ki manta da wannan mutumin ki sa a ranki kamar babu wani abun da ya faru. Wallahi idan kika kuskure wani ya ji ki kina irin wannan maganar sai É—an buzunki".

"Ki saurare ni ki ji abin da zan faÉ—a mana".

"Ina jin ki". Ta amsa mini a daƙile. "Sheikh Dawood Nasarawa yana daga cikin manyan baƙin malaman da za a gayyata a lokacin yaye mu daga islamiyya, saboda ya sama halatta babu irin faɗi tashin da Malam Suleiman bai yi ba. Zuciyata ta cika da wasi-wasi akan sanin da mutanen gari suka yi masa da kuma fuskar da yau nuna mini a tasha". Tun kafin na gama zancen na ga ta haɗe giran sama da na ƙasa ta zuba mini na jiyamunta. A kufule ta soma furzar da takaicin da na yi silar cusa masa a cikin ranta. "Ki yi maza ki cire wannan gurɓataccen tunanin daga cikin ranki kafin ki jefa kanki cikin wata masifar da ba za ki iya cire kanki ba. Kin san fa yanzu duniya ta sauya abu ƙiris za ka yi ko'ina ya ɗauka, yadda malamin nan ya yake kan lokacinsa idan kika ce diddiginsa za ki bi sai kin sama ma su tsigare ki ma daga cikin addinin. Don haka ki rufa mana asiri ki rufawa kanki asiri".

Sallamar Umma shi ya sanya ni haɗiye maganar da na yunƙuro da nufin furtawa, ni da Amira muka haɗe baki wajen yi mata sannu da zuwa ta amsa mana a taƙaice tana wucewa cikin ɗakin. "Kin ga ni bari na je na karɓo awarata, na fita soya". Amira ta yi zancen tana miƙewa tsaye, na yi banza da ita na ƙi kallonta. Fahimtar abin da nake nufi ya sa ta ci gaba da magana.

"Na manta ban sanar da ke ba, ɗazu Bashir ya ƙira ni wai yana son jin muryar sarauniyar mata tauraruwar birnin zuciyarsa....".

Ba ta ƙarisa ba na ɗauki pillown kujerar na jefa mata ta fice cikin sauri tana ƙyalƙyala dariya. Tsaki na ja kafin na tashi na shiga ɗaki wajen Umma tana tsaye tana duba cikin kayanta na iske ta da alama wani kayan take nema. Na tsuguna kafin na ce"Umma ga can abinci na gama a kawo miki nan ne, ko za ki fito?". Kamar ba za ta amsa mini ba sai can kuma ta yi magana kamar wacce aka yi wa dole. "Me ye kika dafa?". "Taliya". Na amsa da shi kaina yana ƙasa.

"Ba na jin sha'awar cin taliya ki je ki cinye kawai. Idan Manniru ya dawo sai ya je ya sayo min fankasau da miya".

"Fankasau kuma Umma? A cikin wannan daren a ina za a samu a nan kusa". Na yi maganar da ban san lokacin da ya fito daga bakina tsabar kaɗuwar da na yi da zancen. Ta bar abin da take yi ta juyo tana kallo na kamar wacce ta yi tozali da wani abun al'ajabi. "Amatullah ba ni da ƴancin cin abin da raina yake so kenan a cikin gidana?". Na jijjiga mata kaina"a'a Umma amma wallahi ba a sayar da irin wannan nau'in abincin a nan kusa. Kuma kin ga Abba idan ya dawo yana buƙatar hutu, don Allah ki yi haƙuri ko awara ce sai na karɓo miki a wajen Amira....".

Kafin na rufe bakina na ji sauƙar mari a kuncina da ya gigita ni da na yi zaman dirshan. Cikin kauraran amo ta soma magana tana nuno ni da ƴar manuniyar ƴatsata. "Na yi miki iyaka da shi shiga abin da babu ruwanki mussamman abin da ya shafi tsakanina da mahaifinki. Duk abin da zan yi a cikin gidana na ki ido ne, idan kuwa kin yi kunnen uwar shegu da zancen ai jiki magayi".

"Ki yi haƙuri Umma ban yi don na ɓata miki rai ba. Don Allah ki yafe mini". Rufe bakina ya yi daidai da sa'ilin da Abba ya shigo cikin ɗakin idanuna suka sauƙa a kansa, da hakan ba wa hawayen da suka wadaci koramar idanuna damar kwaranya kamar an kunna burɗaɗɗan famfon burtsatse.

"Lafiya na gan ku haka duk a hargitse?".

Umma ta buga wani uban tsaki tamkar wacce ta yi arba da kashi, ta juya ta ci gaba da abin da take yi. Na tashi ina yi Abba sannu da zuwa na kai hannu zan amshi ledar da yake hannunsa ya dakatar da ni. "A'a wannan saƙon Ummanki ne". Ya juya yana fuskantar inda take kafin ya zarce da cewa"Hafsatu ga abin da kika buƙata na taho miki da shi".Ta ɗaura hannu aka ta buga salati da sallallami.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Ni kam na shiga tara ma ba uku ba, wai a cikin ɗakina ma ba za a bar ni na huta ba. Manniru me ye kake so da ni ne? Kai ƙaramin yaro ne ko mene ne. Don ka sayo min kilishi shi ne sai na amsa da hannu ko me ye kake so da ni? To ba na cin kilisin fankasau da miya raina yake so".

"Fankasau kuma Hafsatu?".

"Ƙwarai kuwa".

Ya yi shuru yana jijjiga kansa bai ce komai ba ta juya ya fita daga ɗakin. Dole ni ma na tashi na fita na yi sauri na cimma Abba a zaure yana ƙoƙarin fita. "Don Allah Abba ka koma ka huta yanzu fa ka dawo cikin gidan, bai dace ka ƙara fita ko'ina ba. Ka ba ni kuɗin ni zan je na nemo mata fankasau ko a ina ne a cikin garin nan".

Ya tsaya kawai yana kallo hasken farin watan da ya gauraye ko'ina shi take ba ni damar kallon fuskarsa tar. "Amatullah ni ya dace na fita na nemo mata, don haka ki koma ciki ki zauna. Ki kwantar da hankalinki babu abin da zai faru da ni". Zan yi magana ya ɗaga mini hannu"ki koma kawai". Muna cikin haka Amira ta shigo ta gaishe da Abba ya amsa mata a taƙaice da ido na yi mata alama akan babu lafiya. Hakan ya sa tambayar Abba ko lafiya.

"Lafiya lau Amira zan É—an fita ne amma yanzu zan dawo".

"Abba idan wani abun kake buƙata ka ba mu mana sai mu je mu nemo maka..". Tun kafin ta ƙarisa ya taka mata burki"ku shiga gida kawai na ce". "Ko mun shiga hankalinmu ba zai kwanta ba matuƙar muka bar ka fita yanzu. Abba tun safe fa kake aiki kamata ya yi yanzu ka zauna ka huta, yayin da mu kuma za yi maka hidima". Ya yi ɗan jim yana kallon ta sai dai bai ce ko kanzil ba. "Me ye amfaninmu idan ba za mu iya samar maka da nutsuwa ba. Amfanin haihuwar kenan fa Abbanmu, ka sanar da ni abin da za a sayo maka matuƙar akwai shi a cikin garin nan sai na kawo maka shi gabanka kafin ka kwanta bacci".

Ya ja dogon numfashi ta fesar kafin ya ce"to shikenan fankasau da miya nake so, amma kar ku bata lokaci idan ba ku samu ba ku dawo kawai". Ya kai aya yana zaro naira dubu ɗaya daga aljihunsa ya miƙa mata ta ƙarba kana shi kuma ya koma ciki. Tana wucewa ta ja hannuna muka fita waje muka tsaya. "Sanar da ni me ye yake faruwa ne?". "Amira mu fara neman fankasau ɗin tukunna. Yanzu a ina kike ganin za a samu?". Ta yi shuru kamar mai nazarin wani abun kafin can ta ce"zo mu je akwai inda nake da yaƙinin za mu samu".

"To soyar awaran fa?".

"Na gama don yau na fita a sa'a. Tun kafin na fara soyawa aka saye ta dukka". Tana kai wa aya ta ja hannuna da ƙarfi muka bar wajen. [8/10, 3:10 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_____________________________________

Page 2️⃣0️⃣

Tafiya muka soma yi bar cikin layin gabaɗaya muka tsaya a bakin kwalta, zan iya rantsuwa akan cewar tun da uwata ta haife ni ban taɓa fitowa wajen a irin wannan lokacin ba sai ga shi yau ƙaddara ta jayo ni inda ƙafafuna ba su taɓa tunanin zuwa ba. Na cika da mamakin ganin yadda ƴan mata da samari suke ta wucewa daga wajen yayin da wasu kuma suke hira har da masu yin hoto. "Amira yau ina za mu je da muka zo nan muka tsaya?". "Fankasau za mu nema mana Amatullah". Na tsayar da idona akan ta"ban ga alamar abin da abin da kika faɗa ba" Ta fito da wayarta ta soma latsawa tana ƙiran wani layi bugun farko aka ɗaga aka fara magana. "Amira zah big girl yaya aka yi".

"Babe gani a bakin hanya ka fito in kana kusa". "To ranki ya daɗe". Ya amsa da shi a taƙaice yana kashe wayar, mintuna kaɗan tsakani ya iso waje sosai na tsorita da ganin yanayinsa don babu alamar nutsuwa ko kaɗan a tattare da shi balle a yi zaton samun sanin hukuncin addini a tattare da shi. "Bane ya me ye da akwai ne?". Ta shagwaɓe fuska kafin ta soma cewa"fankasau nake son ci a cikin daren nan". Ya waro idanu waje kafin ya fashe da dariya har da tafa hannun. "Fankasau kuma Babe? Yanzu ina zan sama fankasau a cikin daren nan. Ni tukunnan ma me ye wannan fankasau ɗin nan ne da ya ɗag miki hankali cikin daren nan har kika fito?".

"Ni dai wallahi ji nake yi kamar zuciyata za ta fashe idan ban ci fankasau ɗin nan ba". Bai ce komai ba illa dariyar da ya ci gaba da yi yana tafa hannu tare da shafa ƙasuban da ya yi wa fuskarsa ƙawanya. Ta riƙo hannuna ta riƙe gam a cikin nata tana dubansa ta ce"dole ka tisa ni gaba kana yi min dariya ai tun da kana magana da mahaukaciya wacce ba ta san abin da nake yi ba, duk duniya kai ɗaya na zaɓo kamar tumu. Tun ka nuna gazawarka a gare ni na gode Almustapha".

Za mu wuce kawai na ga ya riƙo ɗayan hannun natan ya riƙe. Na cika da mamakin ganin ba ta dakatar da shi ba balle ta yi wani yunƙurin tsawatar masa. "Common Babe ai duk inda fankasau yake a cikin garin nan sai na nemo miki shi. Ina zan tsoma raina na ji sanyi ahalin kina fushi da shi, bari na ɗauko mota sai mu je global delight na san babu abin da za a rasa a nan".

Ta yi banza da shi ba tare da ta tanka masa ba. Ya wuce ya bar wajen da hakan ya ba ni damar furzar da abin da ya tokare mini ƙirjina. "Ke wai ina zamu je har da mota? Ki rufa mana asiri Amira". "Nan kusa ne fa yanzu za mu dawo ai". Kafin na yi wani magana tunin har ya iso wajen da mota ta ja hannuna muka isa wajen muka shiga gidan bayan saboda akwai abokinsa zaune a kujerar mai zaman banza. Muna shiga cikin motar ya fige ta tamkar zai tashi sama ya cilla motar a bisa titi.

"Babe wannan ƙawar takin ba ta magana ne?".

Kalamansa suka dawo da ni cikin duniyar zahiri daga na tunanin da na faÉ—a. "Amatullah ba ta cika magana ba ne shi yasa".

Abokin nasan ya amshe zancen"au sunanta Amatullah kenan? Sunan a dace da ita. Kyakkyawan sunan da kyakykyawar halitta ya dace daman". Ban kula su saboda tsoron da ya gama cika ni duk gudun da yake yi ji nake yi kamar ba sauri, ban ce komai ba har sai da na ga ya tsaya ya faka motar a cikin wani babban fili gefe guda ina hango wani babban wajen da aka rubuta sunan wajen da manyan harrufa suna wani walwal da wuta yana sauya kala daga ja zuwa shuɗi. "To Babe mu je ko". Almustapha ya furta yana ɓalle murfin motar ya fita Amira ita ta fita, ya rage daga ni sai abokinsa a cikin motar. Zuciyata sai bugawa take yi haka siddan na gaza gano dalilin harbawanta fiye da kima.

"Ƴan matan mu yi amfani da wannan lokacin mana kafin su fito".

Saurin ya yi wa ƙofofin kunnuwana dirar mikiyar da ya sani hanzarin kai duba na zuwa ga inda na jiyo sautin. Ban san lokacin da har ya dawo bayan motar ya zauna dab da ni ba har ina iya jiyo fitar numfashinsa ya ƙura mini idanu kamar zan cinye ni ɗanya.

"Malam ka fita tun kafin na kurma maka ihu". Da mamakina sai na ga ya bushe da dariya har da ƙyalƙyalewa, takaici ya cika ni na yi fam babu shiri na soma ture sa daga kusa da ni amma ƙarfina ya gaza don ko gizau bai yi ba balle na haƙata ta cimma ruwa. Mutuwar zaune na yi yayin da na cafko dukka hannayena ya haɗe su waje duka ya riƙe, ya fizgo ni na faɗo kan ƙirjinsa. Na runtse idanuna da mungun ƙarfi hawaye suna kwaranya.

"To yanzu ki yi ihun na ji, kina tunanin ko kin yi ihu anan akwai mai kawo miki ɗauki ne? Ko an samu ma to duk ire-irena ne nan wajen babu wani mutumin kirki da yake ko wucewa ta hanyar balle har ya faka a nan. Ki ba ni haɗin kai kawai mu yi mu gama a wuce wajen, ni ba baƙon zafi ba ne shafa jikin ma kawai ya isa ya gusar min da ishina akan ki".

"Allah ya haramta abin da zake ƙoƙarin aikatawa, ba saduwa ba ce kawai zina akwai hanyoyin aikata zina da dama. Abin da kake ƙoƙarin yi yanzu yana ɗaya daga cikin su, ka cika mini hannayen duk kafin na yi maka mummunan raunin da duk sadda ka gani sai ka tuna da ni".

Da alama bazaranar da na yi masa ba su shige ba, ya ci gaba da cewa"ki yi duk abin da za ki yi. Amma ni dai kam sai na aiwatar da ƙudurina". Kafin ya rufe bakinsa tunin na fizge hannayena daga cikin nasan na soma kai masa yakushi da cizo ta ko'ina har sai na kai shi ƙasa ya kwanta akan seat ɗin, na cire takalmina ina kai masa duka da shi cikin tafasar zuciya da ɗacin rai.

Ina cikin haka na hango Amira da Almustapha sun dosa wajen hakan ya sani furta"ka tashi ka koma mazauninka tun kafin na tona maka asiri". Tsam ya tashi ya zauna ta tsakanin kujerar direba da na mai zaman banza ya wuce izuwa mazauninsa yayin da na kimtsa kaina na zauna. Har Amira ta shigo ta rufe ƙofar Almustapha ya ja motar ban ko kalle ta balle na ce da ita wani abu, tamkar talgen da aka aza bisa wuta haka zuciyata take tafasa ina jin wani ɗaci yana gauraye mini dukkan wani kusurwan bakina yana bi har ta cikin maƙoƙarona. Na daɗe da yi wa kaina alƙawarin ba zan taɓa ba ta kaina wani ya yi amfani da ni alhalin ina cikin hayyacina ba. Sai dai ya yi amfani da abun da zai gusar mini da hankali kafin ya kai ga cimma burinsa a kaina.

Jin motar ta tsaya ya sani dawowa daga karatun wasiƙar jakin da na faɗa. Na ɓalle murfin motar na fito na tsaya ina jiran Amira. "Ki yi min abin da tun da uwata ta haihu ni ba a taɓa yi min irin sa a cikin duniyar bariki ba. Ina mai tabbatar miki da duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha, sai na fanshe abin da kika yi min a lokacin da ba ki da wani abun da za ki kare kanki da shi".

Na cira kai ina kallonsa yayin da yake furta zancen cike da ƙwarin gwiwa yana tsaye a gabana, na galla masa harara kafin na soma furzar da takaicin da yake kwance a ƙasan raina. "Da Allah a dogara kuma na yi imanin duk wanda ya jingina yarda da yaƙininsa zuwa gare shi ba zai taɓa kunyata ba, balle tozarta. Don haka ni kai ɗan halak ka fasa". Na ƙare zancen ina jefa idanuna cikin nasan, na daɗe da yakice wannan tsoron a cikin raina, wannan dalilin ya sanya ko kaɗan kalamansa ba su yi nasarar ɗaɗani da ƙasa ba balle su haifar da tsoro a cikin raina.

Kafin ya yi wata maganar Amira ta iso wajen ban tsaya ɓata lokaci ba ya ja hannunta muka bar wajen har sai muka tsallaka titi kafin na sakar mata hannu, daidai lokacin da ta sama sararin jefa mini tambayar lafiya?. Na yi kunnen uwar shegu da ita na ci gaba da tafiya ita ma ta yi banza da ni har muka iso gida cikin mu babu wanda ya ce ko kanzil. Muna shiga zaure ta riƙo bayan hijabina na juyo a fusace ina kallonta. "Ga shi in kin ga dama ki ɗauka in kin ga dama ki bar shi a wajen. Tun dai ke duk abin da mutum zai yi ba ya yi miki gwaninta". Ta ƙare zancen tana ajiye mini ledar da ke hannunta a gabana, har za ta shige ciki na dakatar da ita.

"Ki yi haƙuri Amira wallahi raina ne a ɓace, da ya kai matakin da har na kasa sarrafa fushina".

"In ce dai ba ni na kar zomon ba rataya aka ba ni ko? Don haka sai da safe". Na yi wuf na sha gabanta tare da zayyana mata duk abin da ya faru, ita ma kanta na hangi mamaki kwance akan fuskarta.

"Amatullah me ye kai sa'in'sa da shi? Irin su fa billahillazi ba a yin ja-in-ja da su yanzu kana zaman zamanka sai su jawo maka wata masifar da babu mai iya fitar da kai. Shin ke ba ki san hanyar da za ki bi ki kuɓuce masa ba sai kin bi wannan hanyar".

"Magana ake fa ta kare mutunci da kimata Amira. Shin na yi laifi don na kaina da kimata?".

"Ba za ki gane ba Amatullah amma ina fatan nan gaba kaɗan ki gane duk karantun da nake yi miki, ba tare da kin nema fassaran su". Na sauƙe gauron numfashi kafin na furta"ba na fatan na gane wannan karatun har duniya ta naɗe". Ba ta ce da ni komai ba illa jinjina kanta da ta yi ta wuce ciki, nima na rufa mata baya bayan na ɗauki ledar.

A ƙofarmu na hango Abba tsaye yana riƙe da tocila a hannunsa kallo guda za ka yi masa ka fahimce nutsuwa da kwanciyar hankali sun yi hijira daga gare sa. Yana ganina ya iso inda nake cikin hanzari. "An samu kuwa Amatullah?".

"E an samu".

Na amsa da shi yayin da nake miƙa masa ledar dake hannunsa, sai da ya sauƙe numfashi kafin ya duba ya gani ya ce"alhamdulillah! Allah ya miki albarka Uwata, wuce mu je ciki". A raunane na amsa da kalmar amin na wuce gaba yana baya na har muka shiga ciki.

Na zauna a falo yayin da shi kuma ya wuce cikin ɗakin wajen Umma. Tun ina lissafin fitowarsa nan kusa har sai na kishingiɗe ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba, sai ji na yi kamar a mafarki ana ƙiran sunana na yi firit na tashi. Kafin na tsinkayo muryar Abba. "Ki tashi ki je ki kwanta dare ta yi". Ban ce komai ba na wuce ciki na kwanta saboda gajiyar da na yi jikina gabaɗaya ciwo yake yi mini, ko sallar asubahi a makare na yi ta bayan na iddar na soma karatun alƙur'ani har lokacin Umma ba ta tashi ba, shigowa huɗu yana tambayar ko ta tashi na ce masa a'a. Har sai da na yi shara na shigo ɗakin na samu a sa'ilin take tashi na tsuguna har ƙasa na gaishe ta ta amsa mini a daƙile.

"Umma me ye za a É—aura?".

Ta yi banza da ni sai can ta ce"ki dafa ko ma mene ne". "To". Na amsa ina ƙoƙarin ficewa daga ɗakin ta tsayar da ni. "Zo ki ɗauki wannan ledar fankasau ɗin ki fitar min daga ɗaki". Kamar yadda ta buƙata haka na yi na je na ɗauki ledar sai jin ta da nauyi alamar ba a ma buɗe ta ya hana ni fita. "Umma ya kamar ba ki ci ba?". "Ba a kawo min ita a lokacin da nake so ba ne".

"Umma da kin yi haƙuri kin ci ko kaɗan ne. Wallahi ba ki ga irin ƙoƙarin da Abba ya yi ba, har kasa kwanciya ya yi sai da ya ga an samu miki fankasau ɗin nan. Ko kaɗan ki ci ai shi ma zai ji daɗi....". Kallon da ta tsare da ni shi ya tursasa mini yin shuru ba tare da na gama furzar da zancen ba. "Ba zan ci ba idan kuma dole ne cin sai kin sani dole na gani". Na sadda kaina ƙasa kafin na ce"ki yi haƙuri". Na fita daga ɗakin na je ƙofanmu na zauna na tisa ledar a gaba na zabga tagumi ina hashasho irin abubuwan da suka faru da ƙoƙarin da muka yi da Amira kafin mu samo fankasau ɗin nan.

"Tunanin me ye kike yi kuma?". Muryar Amira ta sauƙa a kunnuwana. Na bi ta da kallo yayin da take ɗauko kujera ta zauna kusa da ni kafin na yi magana da ci gaba da cewa"wannan ba ledar jiya ba ce?". Ba ta jira na ba ta amsa ba ta buɗe ganin ba ci ba ya sa ta kallona tana faɗin"ya haka kuma Amatullah?".

"Yadda kika gan shi ni ma haka na gan shi, Umma ta ce ba za ta ci ba wai ba a kawo mata shi a lokacin da take buƙata ba". "To Abba kuma ya ya ya yi?". Na zame hannuna daga tagumin da na zagba kafin na ce"ya ya zai yi kuwa? Dole shi ma ya haƙura ai". Ta saki dariya mai matuƙar sauti da hakan ya sani kafe ta da ido. "Mata masu duniya, lalle Umma ta na sha'aninta. Tana gara Abba kamar ƙwallon tamula wallahi shi yasa wani lokacin har cikin raina take burge ni don mazan yanzu sun zama zuma dole sai da wuta". [9/21, 10:16 AM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_______________________________________________

Page 2️⃣1️⃣

Harara na bi Amira da shi da ta yi furucin tana sheƙewa da dariya gami da tafa hannu. "Ke Amira ba na son rainin wayo fa, me ye hakan kuma? Yanzu wannan abun ne ya zama abin dariya a wajenki?. In ce dai da ke muka sha wuyar nemo wannan fankasau ɗin na yi tunanin ai za mu haɗu ne mu taya juna jimami da takaici, amma sai ki bige da dariya". Na ƙare zancen a kulefe don ba ƙaramin cusa mini takaici dariyar tatan ta yi ba. "Ki yi haƙuri ƙawata, me ye laifin maganata fisabillillahi? Ai ni ina ga hakan ma abin alfahari ne gare ki da tunƙaro. Ko a gaban waye za ki tinƙaho ki bigi ƙirji domin mahaifiyarki sarauniya take a cikin a wajen mahaifinki kuma tana iya juya gidan kaman waina a bisa tanda". Na bi ta d irin kallon da mai hankali yake yi wa zautacce kafin na furta"yanzu ke a irin tunaninki wannan abin wayewa ne?".

Ba tare da shakkan komai ba ta ce"ƙwarai kuwa, ai duk wacce kika ga mahaifiyarta ta isa da gidansu ta huta gaba da baya kuma ta wuce raini". Na jijjiga kaina tsabar takaicin da ya zarge muni wuya ya haifar nuni da wanzuwar ɗaci a cikin maƙoƙarona. "Wani lokacin idan kina yin magana sai ki jefa ni cikin tunani, na yi ta hashashen anya kina amfani da ilmi da hankalinki kuwa wajen haɗa kalmomin da bakinki zai furta. Amira ina wayewa a cikin wannan lamarin? Yanzu fa in gaya miki gaskiya samari sun waye ko aure za su nema sai sun tabbatar da cewa uban yarinyar ya isa da gidansa, kuma yana da cikakken ikon zartar da ko wani irin hukunci ta yadda ko kara ya ajiye babu bai ƙetare shi".

"Wannan kuma ra'ayinki ne. Kin faɗi naki ni ma na faɗi nawa, don haka kowa sai ya riƙe na shi".

Tana ƙare zancen ta soma cin fankasau ɗin zallarta ba tare da ta haɗa da miyar ba. Ban ƙara cewa da ita komai ba har izuwa lokacin da Umma ta fito daga cikin ɗaki, Amira ta gaishe ta ta amsa fuskarta babu yabo babu fallasa kafin ta juyo gare ni.

"Wai ina mutumin nan ya shiga ne?".

Cikin rashin fahimta na ce"Umma waye fa kenan?". "Waye kuwa ban da wannan lalatacceb uban nakin. Ina magana kin wani tsare ni da ido shegiya tanbaÉ—aÉ—É—iyar yarinya wacce ba ta yi gadon abin azurki ba".

Kalamanta suka sanya jikina yin sanyi ƙalau har da na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa, muryata a shaƙe na furta"tun safe da ya fita har yanzu bai shigo ba".

"Haba! Ke kuwa baiwar Allah ki dinga sasauta harshenki mana akan yarinyar nan. Wallahil azim bakin uwa guba ne ga Æ´aÆ´ansa wanda da yawan uwaye ba su san hakan ba".

Furucin ustazun gidan kenan wanda bai daɗe da kama hayar ɗakin da yake kusa da na Naman Vector ba, daga shi sai matarsa amarya wanda a cewarta aure su wata huɗu kenan. "To fa! Ɗankari manƙari har da su kaza acin ɗanko?. Wanene kake da suna?".

Ya yi hanzarin faÉ—in"Abdulwahab nake".

Umma ta gyara tsayiwarta kafin ta ci gaba da furzar da zantukan dake kan harshenta masu nauyin gaske, wanda kunnuwa ba za su yi mararin ƙara sauraran su ba ko da bisa kuskure ne kuwa. "Zan ɗaga maka ƙafa ne kawai don kai baƙo ne a cikin gidan nan, amma wallahi bacin haka babu abin da zai dakatar da ni daga yaga maka rigar mutumci a tsakar gidan nan a gaban kowa. Don ni da kake gani na ɗin nan abun kunya gaba na ba shi ba baya ba. Ka jira tukunnan idan ka sama naka ɗiyar sai ka yi yadda kake so da ita amma ba yanzu ba, Amatullah ƴata ce babu wanda ya fi ni ƙarfin iko akan ta".

Cike da takaicin zantukan Umma, Ustaz ya jijjiga kansa tare da sadda kansa ƙasa. "Allah ya kyauta, Allah ta yi mana mai kyau". Ya furta yayin da yake ficewa daga cikin gidan ba tare da ya ɗago kansa ba. "To ku kuma munafukai masu kunnuwan son jin gulma da tsegumi, sai ko wacce ta ja jikinta ta bar nan". Umma ta yi zancen tana wurgawa Maman Adnan da Asabe da suke yi cirko-cirko a ƙofar ɗakunansu harara, kafin ta ja dogon tsaki ta shige ɗaki. Ban san sa'ilin da ƙwalla suka soma tsere a bisa kuncina sai ɗuminsu na ji suna sauƙa a saman haɓarta, daidai lokacin da Amira ta dafo kafaɗuna tana doge mini hawayen da suka ɓata mini fuska. Ta ja hannuna zuwa ɗakin su a nan ta dinga lallashina da kalaman masu kwantar da hankali da haifar da nutsuwa a cikin rai da ruhi.

Wayarta ta soma ruri ta É—aga ta sanya a kunnenta, hankalina baya gare ta hakan ya sa ban ci abin da take faÉ—a ba har sai lokacin da na ji ta duga ihu gami da tashi tsaye ta daka tsalle. Na fita da kallo ba tare da na ce da ita ko kanzil ba har sai da ta gama wayar kafin ta kallo ni, fuskarta kamar gonar auguda bakinta har kunne ta soma cewa"albishirinki Amatullah".

"Goro".

"Fari ko ja?".

Na juya idanuna kafin na ce"fari ƙal kamar haƙwaranki". "Yau Mansur zai dawo kuma ya yi min alƙawarin yana shigowa garin nan a ƙofar gidan nan zai tsaya. Saboda ya yi wa kansa alƙawarin da ni zai fara tozali da zaran ya dawo".

"Allah ya dawo da shi lafiya, Allah kuma ya bar ƙauna".

Cike da annuri ta furta"Amin na gode". Ta ƙare maganar tare da rungume ni. Mun ɗau lokaci muna tattaunawa har Ummanta ta gama toya waina ta zubo mana muka ci, na baro ta akan za ta shiga wanka. Na iske Umma har ta kammala dama kunnun na yi mata sannu da aiki ta yi banza da ni, sai da na jira Amira ta fita kana ni ma na shiga na yi wanka muka shirya muka fita muka yada zango a inda muke zama a tasha.

Kan ka ce kabo mutane sun yi mana rumfa sanyan waina da kunun ake yi babu ƙauƙautawa, tun daga nisa da na hango Bashir na fara haɗe fuskata ban bar wata ƙofar da zai iya yi mini kowacce iriyar maganar ba. Ya iso ya zauna suka gaisa da Amira suka ɗan taɓa hira ina jin su ban soma baki ba. "Bari na kai wa Naziru masarsa kafin ta yi sanyi". Na tsikayo muryar Amira. Na bi ta da ido don na san da gayya ta yi maganar, na yi tsam na riga ta miƙewa ta kafe ni da ido alamar son ƙarin bayani.

"E mu je na raka ni, tun da muke tashar nan fa kin san babu inda na taɓa zuwa a cikinta".

"Kin san ke ma ai hakan ba zai yiyu ba. Kayan kuma a waye za mu bar wa". Na saurin tarar numfashinta" ba ga Bashir yana zaune a wajen ba, sai mu bar mi shi". "Bashir kuma?".

"Ƙwarai kuwa, Bashir ko kana da wani uzurin ne?". Na yi zancen cikin sanyin murya mai cike da taushi gami da jawo hankali mai sauraro. "Kin san ance ai sayon giwa ya take na raƙumi, ko ina da wani uzurin ai ya sama dole na zauna na jire muku kaya tun da Gimbiya da kanta ne ta buƙaci hakan". Ya yi zancen yana washe baki kamar wanda aka yi wa kyautar kujerar hajji da umra. Ta yi masa fari da ido kafin muka bar wajen tafiya ce mai ɗan nisa muka yi kafin muka iso bakin wasu shagona biyu. "Ki jira ni anan bari na shiga na kai masa".

Na yi wuf na riƙo hannunta"Amira shiga za ki yi? Kamar ɗaki ne fa?". "Ba ma kama ba ne ɗauki ne, ke dai kawai ki jira ni yanzu zan fito". Ba ta jira abin da zan ce ba ta fizge hannunta ta shige ta bar ni tsaye a wajen ina kallon ikon Allah buwayi gagara misali. Tun ina tsaye akan ƙafafuna har sai da suka gaji Amira ba ta fito ba, ɗakin da yake kusa da wanda Amira ta shiga aka buɗe ƙofar aka fito, wata mai tallan awara ne ta fito daga ɗaƙin riƙe da roban awaran a hannunta yayin da wani mutum yake bayanta daga shi sai singileti da gajeren wando.

Ya miƙo mata kuɗi yana faɗin"yau fa ba irin farashin kullum zan biya ba, don ba ki yi min yadda nake so ba don haka ga wannan ki je ki rage zafi". Ta yi masa wani mungun kallo kafin ta amsa kuɗin" kawo ai an ce raba arne da makami ibada ne". Ta kai aya tana kwafce kuɗin daga hannunsa.Ya ɗaga hannu zai maka duka ta yi hanzarin kaucewa. "Matsalan ƴaƴan matsiyata kenan kana son su da azurki kuna ɓokarewa. Da ni kike zance yarinya". Ya yi zance a kufule yana yin ƙwafa. Daidai sanda zai shige ɗakin muka haɗa ido da shi ya yi mini ɗagowa, da hakan ya sanya ni sauri rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa, kafin kakkauran muryarsa suka dira a ƙofofin kunnuwana.

"Ke dan ubaki me ye kike yi a nan? Kuma me ye kika tsaya kina kallo?".

Na ji maganar ƙarshen a kusa da ni na cira kaina na gan shi tsaye a gabana. Gaba ɗaya na ruɗe hakan ya sani gaza cewa komai. Har Amira ta fito ta same mu a haka. "Amatullah me ye yake faruwa? Me ye ya haɗa ki da shi?".

"Babban yarinya daman kin san ta ne?".

"Ƙwarai kuwa tare muke da ita".

Ya gyara tsayinsa yana kallona tun daga ƙasa har sama kafin ya ce"ga ta kuwa ƴar ɗas da ita komai na ta cif-cif. Cikakken ƙirji ga kuma faffaɗan ƙugu". Take na ji wani jarumta ya zo mini ruɗewan da na yi lokaci guda na neme shi sama ko ƙasa na rasa shi, na nuna shi da ƴar manuniyar ƴatsata idonuna har sun soma ƙanƙancewa don masifa. "Ahir ɗinka ko kai maye ne sai dai ka ci kanka". Ina ada aya anan na figi hannun Amira kamar zan raba shi da gangar jikinta muka bar wajen, ba mu tsaya ko'ina ba sai wajen kayanmu na zauna a mazaunina ina jin zuciyata tana tafasa tamkar talgen da aka ɗaura a bisa wuta.

"Har kun dawo kenan?". Bashir ya tambaya.

Na yi buga masa wani mungun kallon da bai ƙara yin gigin kallon inda nake ba balle ya yi nuni wata magana. Sai Amira ce ta ba shi haƙuri ta ce gobe ya dawo, muna gama sayar da kayanmu muka haɗa su almajiran da suke kwasar mana suka ɗeba suka yi gaba muna biye da su.

"Don Allah ki dunga É—aukar abubuwa a hankali Amatullah. Rayuwar nan fa sai ana kai zuciya nisa". Na galla mata hararar"babu wanda ya isa ya yi nuni maganar banza ba tare da na mayar masa da martani ba".

Ta sheƙe da dariya mai isarta kafin ta ce"ai kuwa duk mazan yanzu haka suke, maganar batsa ya zama ruwan dare a wannan zamani tsakanin samari da ƴan mata. Sai dai in ba za ki yi soyayya ba balle aure don duk maza halinsu ɗaya ne. Musamman ke da Allah ya bai rage ki da komai ba kina da kyawun sura da diri ina yaƙinin babu namijin da zai ganki bai yabi surarki ba, Amatullah surarki jikinki kawai ya isa namiji ya so ki. Shi yasa kowa ya ganki sai ya yabe ki".

Na ja dogon numfashi na fesar"Amira akwai na tabbatar akwai. Akwai namijin da muka rabu da shi bai yi mini magana akan kyawun sura na ba. Shi ne mutum na farko da na taɓa haɗuwa da shi har muka rabu bai yi mini maganar banza ba".

"Amatullah ƙarya kike yi in akwai kuma ki faɗa min wanene wannan? Ni kuma zan tabbatar miki da a cikin biyu dole akwai ɗaya, ko dai ba shi da cikakken lafiya ko kuma idanunsa ba sa aikin su yadda ya kamata".

Na tsaya cak a inda nake ina kallonta cike da yaƙini na ce da ita"ki yarda da duk abin da zai fito daga bakina, tabbas akwai".

[9/28, 9:31 AM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_____________________________________

Page 2️⃣2️⃣

Tsare ni ta yi da ido tana bi na da irin kallon da mai hankali yake yi wa zautacce, ta jijjiga kanta alamar duk abin da na furta bai sama matsuguni a cikin kwanyata ba. Balle har zuciyarta ta aminta da shi. "Kin ga Amatullah ki zo mu tafi mu bar wannan maganar". Ban ce da ita komai ba ta yi gaba na bi ta a baya babu abin da nake yi illa saƙe-saƙe a cikin raina, kalamanta suna yi mini yawo a cikin ƙwaƙwalwata. Har muka kai gida cikinmu babu wanda ya ce ko kanzil muka shigo da kayayyakinmu ciki.

Har na nufi hanyar ɗakinmu ta dakatar da ni ta hanyar faɗin"kar ki manta yau Mansur zai dawo kuma komai dare a nan zai fara tsayawa. Don haka akwai shirye-shiryen da zan yi wanda ina buƙatar taimakonki". Sai da na sauƙe numfashi mai nauyi kafin na iya raba tsakanin haƙwarana da suka manne da juna na ce da ita" zan je islamiyya fa amma....".

Ta katse ni"idan ba dole ba ne ki haƙura mana da zuwa na yau ne fa kawai". "Ki yi haƙuri Amira ya zama dole ne, kin ga sauƙarmu fa wasa gaske sai ƙara matsowa yake yi. Amma na yi miki alƙawarin zan dawo da wuri". Ta faɗaɗa annurin fuskarta"yauwa to jiran ki". Muka sakarwa juna murmushi kafin kowa ya shige ɗakinsu, Umma na iske a falo ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tana sauraron rediyo, na yi sallama ta amsa mini kamar wacce aka yi wa dole na durƙusa na yi mata sannu ba ta kula ni ba, na ajiye mata kuɗin cinikin da na yi.

"Umma ga kuÉ—in na sayar da shi tas ban dawo da ragowa ba".

Ba tare da ta kalle ni ba ta ce"kin kyautawa kanki". Daga haka shuru ya cika ɗakin na wani lokaci kafin na gusar da shi ta hanyar faɗin"Umma daman ina ta so na yi miki magana akan bikin sauƙarmu da yake ta matsowa, akwai ankon atamfa da hijabi da zamu yi shi ne nake son idan Allah ya hore miki ki yi mini ko da hijabin ne kaɗai". Sai a sa'ilin ta cira kai ta kalle ni.

"Saura kwana nawa ne yanzu sauƙar nakun?".

Cike da farin ciki na gyara zama na soma zubo mata bayani daki-daki wani na bin wani. "Yanzu dai saura kwana ashirin da biyar cif sati uku kenan Æ´an kai".

"Allah ya kaimu lokacin".

"Amin ya Allah, me ye za a ɗaura?". "Ki dafa iya abin da za ki ci". "To". Na amsa mata da shi ina jin raina ya yi mini ƙal zuciya ta washe ta yi tas. Taliyar murji na tafasa na ci da manja da yaji. Wanka na shiga tun ina banɗakin nake jiyo hayaniya har ana dukan ƙofar banɗakin hakan ya sani saurin zura zumbuleliyar hijabinta da na shigo da ita, ina gama sawa ana bankaɗo ƙofar tamkar za a karya ta.

"Na rantse da Allah sai kin fito don ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa". Furucin Ummi kenan da suka sauƙo a ƙofofin kunnuwana tamkar sauƙar aradu ta finciko hannuna ta yi waje da ni. Tsabar ɓacin rai da baƙin ciki da takaicin da suka yi wa raina rakon dangi ban san lokacin da idona ya makance ba na sauƙewa Ummi mari a kuncinta. Marin da ya jawo hankulan sauran mutanen zuwa gare mu.

"Ubara uban can! Ni za ki mara Amatullah? Ai kuwa kin taro balbalin bala'in da babu ranar mutuwarsa. Daga nan har yanzu lokacin da mahadi zai bayyana".

"Na mare ki ɗin na ce na mare ki Ummi ki yi duk abin da za ki yi. Wani irin wulaƙanci ne wannan ina banɗaki ina wanka za ki buɗe mini ƙofa, shin ba ki yi tunanin a wani irin halin za ki riske ni ba?".

Ta yi hanzarin katse mini numfashi"babu ruwa da ko wani irin hayaniya zan same ki, ai kina ganin ruwana a ƙofar banɗakin kika shiga don haka ban ga dalilin da zai hana ni fiddo da ke waje ba ko da kuwa tsirara kike". Baƙin cikin kalamanta ya tursasa mini runtse idanuna ina jin rai da zuciyata yana wani irin tafasa kafin na yi magana Amira ta iso wajen ta nema jin ba'asin me ke faruwa Ummi ta yi caraf ta amshi zancen tamkar jira take yi.

"Ruwa na ajiye zan shiga banÉ—aki tana gani amma don tsaurin ido ta riga ni shiga shi ne ni kuma na shiga na fiddo da ita".

Tsabar mamaki Amira ta riƙe ƙungunta"kanbu! Kika shiga kika fito da ita? Ke kuma Amatullah kina tsaye duk aka yi wannan abun?".

"Ai in gaya miki Amatullah ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, sai da ta ɗauke Ummi da mari in ni ma kaina sai da na ji raɗadinsa balle ita kuma da aka sauƙe shi akan kuncinta". Furucin Maman Vector kenan cikin gurɓatacciyar hausarta da har yanzu ba ta hau hanya ba. "Tabbas kin cika cikakkiyar ƴar halak, Wallahi da ba ki ɗauki wannan hukuncin ba Amatullah takaici da baƙin ciki sai ya hana ni motsawa daga nan wajen".

"Na rantse da Sarkin dake dake busa min numfashi ban zan yarda ba. Ko sama da ƙasa za su haɗe sai na rama marin da kika yi min, tun da ni ba jakar uwarki ko ubanki ba ne kuma ba cin azurki na zo yi cikin gidan nan ba. Yadda kuke biyan kuɗin haya haka mu ma muke biya". Ummi ta yi ikirarin tana tankaɓar da ruwan da yake cikin bokatin ƙarfe da za ta shiga wanka da shi ta sure shi ta nufo ni gadan-gadan da nufi rotse mini goshi.

Ƙam na tsaya a inda take tsaye kusa da Amira na riga da na ƙudurce a raina cewar duk abin da zai faru sai da ya afku. Ba zan matsa ba balle na yi ƙoƙarin guduwa in ta fasa yin abin da ta yi niyya ma ta raina iyayen da suka yi silar kawo ta duniya. Kafin ta iso gare ni muka ji tas sautin sauƙar mari duk muka jiyo da hakan ya yi daidai sake wani gigitaccen ihun da Ummi ta saka tare da zube a ƙasa tana yin burburku. Duk muka tsayar da idanunmu akan Baban Adnan da yake tsaye a wajen cikin tsananin fusata ya yi cilli da bukatin da ya amshe daga hannun Ummi.

"Wannan wani irin fitina ce haka? Babu dama mutum ya yi aikin kwana ya dawo gida ya kwantar da haƙarƙarinsa ya huta sai kun ɗaga sa. Kar ku sake ku kai ni bango a cikin gidan nan don idan har hakan ya faru to kowa ba zai ji daɗi ba daga babba har yaro, ko wani bala'i daga gare ki yake fara ɓullowa Ummi". Ya ƙare zancen tamkar zai kai wa Ummi da take yashe a ƙasa duka. "To wallahil azim yau kam ba zan yarda da wannan cin kashin da ake mana, babu dama abu ya haɗu yaran nan sai ka yi wankan tsarki ka tsunguma ciki ka yi kane-kane ka juya zancen ka ba wa Amatullah gaskiya, don ita ce ta gaban goshi". Furucin Maman Ummi kenan yayin da take ɗaura ɗamara tamkar mai shirin tafiya filin yaƙin duniya na biyu.

"Idan ba ki rufe min baki ba yau sai na nuna miki iyakarki a cikin gidan nan, yanzu waya kawai zan ɗaga kawai na ƙira azo a kwashe ku a kai ku bayan kanta".

Tsam Maman Ummi ta sha ruwan jikinta ta koma yin wasu ƙananan maganan, ta zo ta ɗaga Ummi suka wuce ɗaki suna cin alwashi akaina. Kaina kawai na jijjiga har yanzu ban sauƙo daga dokin zuciyar da na hau ba na wuce ɗaki, na wuce Umma ba ta ce da ni komai ba shiryawa na yi na fice islamiyya.

Kaina a ƙasa tun da na fito daga gida har na isa islamiyya ban ɗago ba, raina cike da takaicin da kuktun abin da Ummi ta yi mini. Babu shiri na saki wata doguwar tsaki mai matuƙar sauri tunawa da na yi zancen Abba na barin mu gidan izuwa yanzu kam ya sha ruwa. Ban yi aune ba na ji dirar wata baƙuwar murya a cikin dodon kunnena da ya tursasa mini tsayawa cak tamkar gunki. "Ke uban waye kike yi wa tsaki?".

Na bi mutumin da kallo cike da tsoron da ya yi wa birnin zuciyarta dirar mikiya. Muryata a shaƙe na ce"ba da kai nake yi ba bawan Allah". Ya yi ƙwafa"Allah ya taimake ki". Daga haka ya ja zugan ƙafafunsa ya bar ni cike da tarin mamaki da al'ajabin da ya tsaya mini a rai. Lalle sai yau na ƙara gaskata cewa mafi yawan mutane yanzu a fusace suke ainun.

Haka na wuce islamiyyar na samu har Malam Suleiman ya shiga ajinmu, da hanzari na ƙarisa na shiga na zauna na ciro alƙur'anina na soma karatu. Haka muka fito salla muka koma ajinmu har mun fara karatu Malam Suleiman ya aiko ya ce duk ƴan ajin sauƙa su je filin salla yana son ganin su. Duk muka ɗauki jakakkunanmu muka nufi filin kasancewar an kusa tashi ma a lokacin, ba mu daɗe da haɗuwa ba ya zo shi tare da Malam Aminu, Malam Suleiman ya fara yin jawabi mai kama hankali.

"Mun tara ku ne a nan akan sauƙarku da kullum yake ƙara gabatowa, akwai abubuwan da makaranta ta shirya yi muku domin taya ɗalibanta murnar haddace littafi mai tsarki. Cikin abin da makaranta ta shirya har gayyato manyan malaman domin su zo su yi muku nasiha da nusar da ku hanyar da za ku yi amfani da ilmin da kuka samu ta hanyar da ta dace, hukumar makaranta ta zauna ta yanke hukuncin turawa Sheik Dawood Gaskiya dokin ƙarfe a matsayin babban malamin da zai halarci walimar sauƙan ku".

Ras! Na ji gabana ya yanke ya yi wani mummunan faÉ—uwa. Babu shiri na É—ago kaina ina kafe Malam Suleiman da idanu tamkar magiji ko kuma yau ce rana ta farko da na fara yin tozali da shi a cikin rayuwata.

"Sheik Dawood Gaskiya dokin ƙarfe".

Na maimaita a cikin raina zuciyata cike da tarin fargaba. Babu shiri na dafe ƙirjina da dukka hannayena saboda tsananin bugun da yake yi, take na ji zuffa ya soma keto mini. Idanuna suna hasko mini zanen hotonsa tar ina gani tare da wassafa kalamansa da ya furzo mini a cikin kwanyata. Maganar da Malam Suleiman ya ɗaura da shi shi ya yi silar fizgo hankalina da ya yi nisa daga gangar jikina zuwa gare ni. "Babban mutum ne a ƙasan nan da ma nahiyar Afrika gabaɗayanta. Mutumin kirki ne ƙwarai da gaske kuma mutunci da dattakunsa sun kai matuƙa ba ya wasa da duk wani lamarin da ya shafa addininsa komai uzurin da yake cikin idan aka yi masa irin wannan gayyatar haƙiƙa yana amsar ta. Ta yadda ko mai sama damar halalta ba ya kan wakilta ɗansa ɗaya tilo namiji ya zo a madadinsa, sai da ku kun yi sa'a shi da kansa zai zo walimar yaye ku ba aike zai yi ba, don haka muna son ranar ku fitar da mu malamanku da kuma makaranta da kanta kunya".

Take wajen ya rikice aka soma yin kabbara babu ƙauƙatawa, ni dai ina zaune inda nake rungume da jakata ko motsin kirki na gaza yi balle na bi ayarin masu yi kabbaran. "Za mu ware ɗalibai uku da za su yi karatun littafi mai Tsarki a ranar daga cikinku, wanda kuma suka kasance masu ƙwazo ne da basira haɗi da mayar da hankali akan karatunsu. A cikinsu kawai Al'amin Yakubu, Aliyu Shehu sai kuma Amatullah Munnir". Ras! Na ji gabana ya yi wani mummunan faɗuwa da hakan ya haifar mini da runtse idanuna, wajen ya ɗau shewa abokan karatunmu suna cike da farin ciki don a ganin su wanda aka zaɓa ɗin duk sun cancanta. Na buɗe idanuna a hankali ina kallon maza biyu da suka fito suka tsaya kusa da Malam Suleiman wanda ni ko sanin fuskokinsu ban yi ba, kasancewar ajin maza daban haka nan ma na mata, wajen alwala da salla ma nasu daban da na mu ba ma haɗuwa da su sai in an tashi yayin tafiya gida.

"Amatullah ki tashi mana ki je ke ma".

Na tsinkayo amon Ammi yayin da take zare jakata daga runguman da na yi mata, tamkar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki haka na tashi duk jikina babu ƙwari na fita na tsaya wanda hakan ya ba wa Malam Aminu ɗaurawa daga inda ya dakata. "Waɗannan su ne ɗalibai uku da za su yi karatu yayin walimar yaye ku, kuma a cikin su muke saka ran samu na ɗaya, na biyu da kuma na uku". Kan ka ce kabo wajen ya ƙara kaurewa da kabbara ni dai ina tsaye ne kawai a wajen amma hankali da nutsuwata ba sa tare da gangar jikina.

Kafin a watse Malam Suleiman ya ce gobe yana buƙatar ganin mu da wuri kafin a shiga aji, muka amsa da to. Kafin ta sallame kowa har muka fito daga cikin makarantar babu abin da ake tattaunawa sai batun zuwan Sheikh Dawood. Ko jiran Rauda da Ammi ban tsaya yi ba na yi tafiya don ji nake tamkar ba zan isa gida ba, ina so wa kuwa kai tsaye na wuce ɗakin su Amira na iske Ummata zaune a ƙofar ɗakin na tsuguna har ƙasa na gaishe ta kafin na shiga ciki.

"Amira na shiga uku".

Na furta a razana cikin rawar murya da take bayyanar da tsoron da ya yi wa ƙalbina naɗin huhun goro. Tsam ta tashi daga inda take zaune ta kamo hannuna muka shiga uwar ɗaka. "Sanar da ni me yake faruwa Amatullah? Rasuwa aka yi?". Na girgiza mata kaina alamar a'a. "To me ye faru?".

Tiryan-tiryan na kwashe duk abin da ya wakana na sanar da ita daga farko har ƙarshe, ba tare da tsallake ko da jimla guda ba. Dogon tsaki ta saka kafin ta soma furzar da takaicin da na yi silar cusa mata.

"Yanzu akan wannan abun ne kika bi duk kika É—aga hankalinki?".

"Dole hankalina ya tashi Amira ko kin manta yadda muka yi da shi, a tasha ne?".

Ta musguta kafin ta furta"ban manta komai ba, amma yadda malamanku suka suffanta muku kirki da mutumcinsa a ido duniya shin hakan kaɗai bai isa ya wanke zargin da zuciyarki ta ɗisa miki akan sa ba?. Ya kamata fa izuwa yanzu ki manta da duk abin da ya faru, babban mutum ne a ƙasan nan kuma yana da girma a idanun mutane, ko zuwan da zai yi walimarku ma ai ya isa ya sa ki ji kin nutsu akan kasancewarsa mutumin kirki".

"Amira babu wani zancen da zai sauya abin da na gani da idanuna kuma na ji da kunnuwana. Tabbas akwai wani ɗabi'a da mutumin nan yake aikatawa a ƙarƙashin ƙasa wanda ba ya son duniya ta sani, ko kuma in ce yana amfani da girmamawan da mutanen suke yi masa wajen lulluɓe wannan sirrin".

"Wani mutum kuke magana akai? Kuma wani sirri yake ɓoyewa?".

Zancen Umman Amira suka yi wa ƙofofin kunnuwanmu dirar mikiya. Duk muka cira kai muna dubanta tana tsaye a ƙofar ɗakin ta kafe mu da ido tana jiran amsan tambayoyinta. "Umma ba fa wani abu ba ne, wai wani malamin islamiyyansu ne fa ta gani tare da wata budurwa anan bayan layin nan suna tsaye. Shi ne fa duk ta bi ta tada hankalinta wai ta ji an ce yarinyar ba ta da halin ƙwarai".

Ta ɗan yi jim kafin ta ce"Allah ya kyauta, ki tashi ka ga gawayin an kawo sai ki ɗaura girkin kafin ya iso". "To Umma yanzu zan fito". Ba ta ce komai ba ta juya ta fita hakan ya ba wa Amira daman faɗin"yanzu dai ki tashi ki je ki cire kayanki ki zo mu yi wa Mansur girki, don ya kusa isowa". Ban iya amsa mata da kalmomin baki ba illa gyaɗa mata kai da na yi na tashi na fita. [9/29, 3:41 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

____________________________________

Page 2️⃣3️⃣

Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka nake ɗaga ƙafafuna da ƙyar tamkar wacce ke tsoron taka ƙasa, kamar daga sama na ji an jawo hijabina ta bayana ya zarge mini wuya har sai da tari mai ƙarfi ya sarƙafe ni. Babu shiri na waiga don ganin wanda ya aikata hakan a gare ni bayan na yi kici- kicin fizge hijabina da aka damƙe. Na yi turus ganin Ummi tsaye a bayana ta sha ɗamara a ƙudunta tana cika tana batsewa kamar saniya za ta kai bugu, sai da na yi ƙoƙarin daidai nutsuwa da numfashi da yak tsaya mini a ƙirji kafin na iya harhaɗo kalmomin da bakina ya furta cikin tsananin takaicin da ta yi sanadiyar cusa mini.

"Ummi lafiya? Me ye na yu miki haka?".

Ta galla mini wata uwar harara kafin ta furta"aw! Wai har kin manta kenan? To ba ri na yi miki tuni wallahil azim duk wanda ya ci tuwo da ni sai na tabbatar masa da cewar miya ya sha, tun da har kika yi kuskuren shiga cikin gonata sai kin yi kuka da idanunki". Raina ya harzuƙa zuciyata ta soma tafasa take jikina ya soma rawa saboda tsabar ɓacin rai da kalamanta suke jefa ni, idanuna suka soma cikowa da ƙwalla.

"Ummi magana ta riga da ta mutu a tsakaninmu, don haka ki bar ni haka na sarara. Babu ni babu ke babu ruwan biri da gada".

Ta tafa hannu gami da tsarin shewa kafin ta ce"ai kuwa magana tana nan daram har sai zuwa lokacin da na rama irin É—iban albarkan da kika yi min a cikin gidan". Na buga tsaki na juya zan tafi ta koma cakumo ni daga lokacin da Abbanmu da Baba Habu suka shigo cikin gidan suka buga salati kafin Abba ya nema jin ba'asin abin da ya afku, na kwashe komai na sanar da shi.

"Yanzu ke Ummi tun da an gama magana me ye amfanin tayar da shi yanzu?". Tambayar da Baba Habu ya jefa mata kenan kafin ta amsa Ummanta ta yi caraf ta amshe zancen. "Ko sama da ƙasa za ta haɗe sau Ummi ta ɗauki fansar abin da Amatullah ta yi mata".

Kansa kawai Abba ya yi kafin ya furta"Uwata wuce ɗaki, ga salla ma yanzu ake ƙira".

"To Abba".

Na amsa da shi a taƙaice ina jin wani takaicin a cikin raina da ta tokare mini ƙirjina. Ban san sa'ilin da hawaye ya zubo daga idona ba yayin da nake shigewa ɗaki kai tsaye na wuce na je na sauya kayana, na fito na ɗau alwala na zo na yi salla. Sai a lokacin na lura da cewa Umma ba ta cikin gidan don haka na wuce wajen Amira ta ɗauke fuskana na yi mur don ba na so ma ta tare ni da wani zancen, tare muka fara aikin abincin da ita fried rice muka yi da soyayyar kazar da muka yi mata miya ta sha kayan lambu. Haka muka yi muka gama duk jikina babu ƙwari kuma na ƙi ba wa Amira fuskar da za ta yi mini wata tamnayar. Ina zaune a ɗakinsu ina latsa wayarta ta shigo ta dire plate ɗin abincin da ta shigo da shi a gabana, tare da fizge wayar tana faɗin"to Madam Bismillah mu ci abinci".

Na sauƙe gwauron ajiyar zuciya kafin na sama zarafin cewa"wallahi kin ga ni kam ko yunwar ma ba na ji". Ta watsa mini harara"saboda me ye?". Kafin na ba ta amsa ta ɗaura da faɗin"kin ga Amatullah in zan ba ki shawara ki ɗauka to tun wuri ki cire damuwar komai daga cikin ranki. Kar ki je ki ja wa kanki wani matsalar na daban akan wasu mutane can daban, yanzu dai ki daure ki ci abincin sai mu yi magana daga baya".

Ban ce da ita uffan ba na saka hannu muka soma cin abincin har muka gama ban yi magana ba, duk da yadda take ta ja na da ita, da uhm ko umm kawai nake amsa mata wani sa'ilin kuma na saki taƙaitaccen murmushin da iyakar sa leɓena. Haka muka gama cin abincin na baro ta akan za ta shiga wanka don sun yi waya da Mansur ya ce ya ma shigo garin, wajenta kawai zai nufa. Sakakken ajiyar zuciya na sauƙe lokacin da na shigo ɗakinmu na iske har yanzu Umma ba ta dawo ba wanda ban san inda ta je ba, alwala na fito na yi na koma na yi salla ko da na iddar na gaza tashi daga inda na yi sallan na zaune na zagba tagumi da hannu bibbiyu tamkar wacce aka aikowa da saƙon mutuwar uwa da ubanta.

"Uwata lafiya kuwa ina ta sallama ki zauna kin yi tagumi, ko amsawa ba ki yi ba?".

Tamkar a cikin mafarki na tsinkayo amon Abba a tsakiyar kaina, da hakan ya tilasta mini cira kaina ina dubansa na miƙe na amsa baƙar ledar da ya shigo da ita ina yi masa sannu da zuwa. Na kawo masa ruwa ya sha kana na ce"ba ri na ɗaura maka girki kafin Umman ta dawo". Ya yi saurin faɗin"ba na jin yunwa sai dai ki dafa iya cikinki, Ummanki kuma na san ko ta dawo ba lalle ba ne ta ci wani abu". Tsimi-tsimi na koma na zauna kusa da ƙafafunsa tare da sadda kaina ƙasa, shuru ya ratsa wajen na tsawon wasu mintuna kafin Abba ya kawar da shi ta hanyar faɗin"walimar sauƙanku tana ta gabatowa ko?".

"E akwai Æ´an kwanaki ma yanzu kam suka rage".

Ya yi ɗan jim kafin ya ce"kuma za ku yi wasu hidimomi ko?". "Hijabi ne kawai sai ankon da za mu yi. Kuma Umma ta ce za ta yi mini hijabin". "In Sha Allah kafin lokacin ma zan yi iya ƙoƙarin na ga na yi miki ankon, su makarantar takun me ye suke shirya muku na ga ana gayyato mutanen". Sai da na haɗiye wani miyau mai kauri daga bushashshen maƙoshina kafin na sama lasisin faɗin"Sheikh Dawood za a gayyato".

Tun kafin na gama maganar ya tari numfashina"kai! Ai kuwa ya zama dole na halacci wannan taron nakun ko don na yi ido huɗu da Sheikh Dawood. Amma gaskiya sun yi ƙoƙari da suka gayyato shi don a malaman yanzu da wuya a sama kamarsa, mai ƙoƙarin hidimtawa addini da ziyartar duk wani wajen taron addini".

Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri, na yi shuru kamar wacce ruwa ya cinye ta. Ban ƙara cewa komai don na gaza samun abin da harshena zai sarrafa. Sallamar Amira shi ya dawo da ni cikin hayyacina daga duniyar tunanin da na yi nisan ciwo a cikinsa, na amsa mata kana ta shigo ta durƙusa har ƙasa ta gaida Abba tare da yi masa bayanin zan raka ta ƙofar gida ta amsa saƙo.

"To kar dai ku daÉ—e kuma ku lura, ni ba na son wannan hirar daren nakun wallahi".

Amira ta fashe dariya har da rufe fuskarta saboda kunya kafin ta ce"Abba saƙo ne kawai za mu karɓa". Ya murmusa tare da cewa"to na ji, Allah ya kiyaye sai kun dawo". "Amin mun gode". Muka haɗe baki wajen amsawa kana muka tashi muka fita a zaure muka dakata ina ƙarewa Amira da ta sha doguwar rigar shuɗin kamfala an mata wani masifaffen ɗinkin da ya fito da duk wani suran jikinta. Ta kashe ɗaurin ture ka ga tsiya yayin da ta watsa sumarta zuwa bayan wuyanta.

"Ma sha Allah! Wallahi kin yi kyau kamar a sace a gudu. Anya kuwa in Mansur ya ganki zai iya motsawa".

Cike da matuƙar jin daɗi ta yi fari da idanunta gami da buga tsalle. "Na gode ta kusa da ran". Ta amsa da shi tana jan hannuna muka fita wajensa, yana tsaye a inda ya saba tsayuwa inda ya zo a jikin motarsa da duk da duhun dare hakan bai hana sheƙin da take yi ɗaukar ido ba. Da sallama muka isa wajen bai amsa ba illa kafe ta da idanu da ya yi wanda ita ma ɗin shi take kallo.

"Barka da fitowa tauraruwata hasken idaniyata, filitar dake haskaka birnin zuciyata da kewaye. Na yi kewarki yadda ba ki ba zai iya misaltawa ba, wasu lokutan har ji nake yi kamar na yi tsuntsuwa na zo don kawai na gan ki sai dai hakan ba mai yiyuwa ba ne".

"Ni ma nan kullum da kewarka nake kwana kuma nake tashi a cikin raina Masoyi".

Na naɗe hannayena tsam a ƙirjina ina kallon su"to masoya tun da ba a gani ba babu amfanin tsayiwata a wajen. Don na ga alama iya junanku kawai kuke gani". Murmushi Mansur ya yi yana haɗe hannayensa waje guda alamar ban haƙuri. "Afuwan ranki ya daɗe, mun yi kewar juna ne irin sosai ɗin yadda baki ba zai iya furta wa ba". Na taɓe baki ina cewa"to har shekara dubu nawa kuka yi ba ku ga juna ba?".

"Ai duk kwana guda jin sa muke yi tamkar shekara muka yi ba mu ga juna ba". Amira ta yi furucin fuskarta tamkar gonar auduga. "To sannu masoya yanzu kam ai ga ki ga shi. In kun ga dama ma ku cinye juna ƙarshen soyayya". Dukkan su suka tuntsire da dariya kamar waɗanda aka ba su wankan gardi, sai a lokacin muka sama damar gaisawa da Mansur na yi masa sannu da dawowa mun ɗan taɓa hira na wani lokaci kafin na ce zan shiga ciki, Amira ta yi tsalle ta dige akan babu inda za ni. Dole na tsaya ba don raina yana so ba jifa-jifa nake soma baki a cikin hirar tasun kafin can na hango Umma ta doso gida. Da alama ba ta gan mu ba don kai tsaye ta wuce cikin gidan ba tare da waiwaye ba.

"Amira kin ga Umma ta dawo bari na wuce gida".

Ta galla mini harara"babu inda za ki je yadda muka fito tare to haka za mu koma. Sai ka ce cizon naman jikinki ake yi a nan ɗin". Ban ce komai ba illa murmusawan da na yi, ba su ja hirar da yawa ba don hatta shi kansa Mansur ɗin ya fahimci cewar na ƙosa na bar wajen, ya zagaya ya buɗe bayan motarsa ya fito da wasu manyan ledodi biyu ya zo ya dire su a gabanmu.

"To Babe ga tsarabarki".

"Ranka ya daɗe ba na so ka na wahalar min da ajihunka". Amira ta yi zancen cikin karya harshe da sausauta amonta. "Rufe idonki ki miƙo min hannunki". Mansur ya furta a dake don kar ma ta kawo masa wargi. Kamar yadda ya buƙata hakan ta yi, ni dai ina tsaye ina kallon ikon Allah buwayi gagara misali. Ya ciro wani kyakykyawan agogo daga ajihunsa ya ɗaura mata a hannunta kana ya ce ta buɗe idonta. Ta cika da farin ciki da murna yayin da ta ya tozali da agogon ta dinga jeranta masa godiya wani na bin wani ni ma ina taya ta. Haka suka yi sallama ya tafi mu kuma muka shigo gida kai tsaye na wuce dakinmu don haka kawai na ji ƙirjina yana bugawa fiye da kima a kimiyance. Babu kowa a falon don haka na wuce uwar ɗaka na yi turus bisa tozali da mummunan ganin da na yi, take ƙafafuna suka soma rawa suffa ta soma keto mini daga dukkan mafitan gashin dake jikina. [9/30, 7:07 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_____________________________________

Page 2️⃣4️⃣

Tabbas indai ba idanuna ne suka sama matsala ba ko kuma suka daina aikin su yadda ya dace, to babu shakka Umma na ga ni tana tsaye a kan Abba da yake kwance a bisa gado yana bacci huce gajiyar da ya kwaso, ƙaramin almakashi ne a hannunta tana yadda gashin gemunsa tana zubawa a cikin wani kwalba. Ban yadda ta ganni ba na yi wuf na koma don da farko ban ya ma tunanin cewa Abba yana cikin ɗakin ba da ba zan shigo ba, zama na yi a ƙasa dirshan na tallafe kuncina yayin da numfashina yake sarƙafe mini a ƙirjina, zuffa ya soma jiƙa miji jiki lajaf tamkar wacce aka juyewa bokatin ruwa a kanta. Na dulmiye cikin kogin tunanin dalilin abin da Umma take yi, sannan me ye za ta yi da gashin gemun Abba da take yadda take sanyawa cikin wannan kwalban?.

"Amatullah".

Na tsinkayo muryar Umma a tsakiyar kaina, na yi figigi na miƙe tsaye ina goge ƙwallan da ya ɓata mini fuska wanda ban san lokacin da suka zubo ba. "Ki samo min garwashi".

"Umma ai ba a hura wuta ba ma. Amma me ye za ki yi da garwashi a daren nan?". Kallon da ta tsare ni da shi ya sanya ni rusunar da idanuna ƙasa jikina a sanyaye tamkar jinjiran kazar da ruwan sama ya yi wa ɗan banzan duka. "Ba na son yawan tambayoyi ki wuce kawai ki nemo min abin da na buƙata". Ban kuma cewa komai ba na fice jikina gabaɗaya babu kuzari kamar wacce aka zarewa laka. Ko da na fito na gaza assala komai na tisa munkubarin a gabana na zagba tagumi tunani kala-kala babu wanda bai kawo wa ƙwaƙwalwata ziyara ba.

"Ƴar uwa lafiya kika zauna kika zagba tagumi haka?".

Babu shiri na ɗago kaina saboda ba kaɗan ba sauƙar furucin a ƙofofin kunnuwana ya razana ni, Anty Amarya ce matar ustazu Abdulwahab ta yi maganar tana tsaye kusa da ni. Ganin ban amsa mata ba ya sanya jan kujera ta zauna kusa da ni tana ƙara faɗin"ko dai akwai wata matsalar ne wanda kike ganin bai dace kowa ya sani ba, ba zan matsa miki sai kin faɗa min sirrin zuciyarki ba amma in Sha Allah zan taya ki addu'a. Allah ya kawo miki mafita ta inda ba ki taɓa zato ba balle tsammani".

"Amin na gode". Na amsa da shi a taƙaice kasancewar tun da suka shigo gidan ba mu taɓa wani dogon magana da ita da ya wuce gaisuwa ba. Har ta tashi za ta tafi na yi hanzarin dakatar da ita ta hanyar faɗin"don Allah na ga kamar girki kike yi ko?". "E girki nake yi yau na yi dare ban gama ba".

"Don Allah garwashin wuta nake so ko guda biyu ma. Za mu sa turaren wuta". Ta faɗaɗa fara'ar fuskarta kafin ta ce"ba damuwa ina kaskon na zuba miki". Na ji kamar an sauƙe mini wani ƙaton dutse daga kaina, na tashi da sauri na shiga na ɗauko mata kaskon na ba ta. Ta karɓa ta je ta ciko mini shi na karɓar ina ta zuba mata godiya kafin na yi mata sai da safe na shiga ciki. A falo na iske Umma na ajiye kaskon a gabanta.

"Umma ga garwashin".

Ba ta tanka mini ta ɗauka ta shiga cikin uwar ɗaka, babu jimawa ta fito mini da abun shimfiɗi ta ce na yi shimfiɗi na kwanta a falon na amsa tare da yi mata sai da safe wanda ba ta ko amsa ba ta yi shigewarta ciki. Shimfiɗi na yi na ɗauko alƙur'ani da tocila a kusa da ni na zauna, sosai na mayar da hankalina kacokam ga karatun don so nake yi na hana kaina faɗa cikin tunanin da yake addaban kwanyata. Na daɗe ina karatun don aƙalla na yi awa guda ina yi ban gushe ina yi ba har sai da na yi wani sanyi ya soma ratsa sashin ruhina kana na rufe alƙur'anin. Na kwanta akan bayana ina kallon rufin ɗakin da ya zamo shamaki tsakanin ganina da sararin samaniya, ajiyar numfashi na koma sauƙewa wani na bin wani tamkar wacce ta yi gudun ceton rai tunanin abun da na ga Umma ta yi shi ya tsaya mini a rai kwatankwacin yadda ƙayan kifi yake tsayiwar ƙiƙam a maƙoƙaro.

A bayyane na furta"Ya Allah ina roƙonka tare da tawassali da sunayenka tsarkaka guda ɗari ba ɗari da ka shirya mini Ummata ka dawo da ita kan hanya madaidaiciya mai ɓulewa. Ka kuɓutar da Abbana daga dukkan abin da take shiryawa ka kuma tsaretar da shi daga dukkan ƙullin da take ƙullewa".

Cikin wani irin yanayi na mutuwar jiki na ƙare zancen ina jin wasu tsiraran hawaye masu ɗumi suna bin gefe da gefen fuskana. Haka na ƙarar da kusa rabin daren ban runtsa ba abubuwa da dama sun taron sun yi mini yawa sai da na yi sallan asubahi kana na sama runtsawa. Hayaniyar da nake ji kamar a cikin mafarki shi ya yi silar farkawa na ba don baccin ya ishe ni ba. Na soma buɗe idona a hankali kafin na buɗe sa tar ina ƙarewa ɗakin kallo, tashi na yi na zauna ina murtsike idanuna tare da ambaton addu'ar tashi daga bacci kamar yadda addinina ya tanada.

Ƙananun maganganu nake yi suna tashi daga ɗakin wanda ina da tabbacin Abba da Umma ne suke magana, numfashi na sauƙe mai karfi kafin na tashi na soma tattare shimfiɗana. Don na yi wa kaina alƙawarin indai ba bisa kuskure ba ba zan taɓa sauraron zancen da suke tattaunawa a tsakaninsu ba, ko da kuwa ya shafe ni. Tattare falon na yi tsaf na yi shara na kimtsa ko'ina na fito na haɗa wuta na ɗaura farar shinkafa, ina girkin ina duba alƙur'anina ina ƙara tisa karatun da aka yi mana jiya. A haka Amira ta zo ta same ni ba ta katse ni ba har sai da na kai ƙarshen ayan da nake karantawa na rufe ƙur'anin, kana muka gaisa da jin lafiyar juna.

"Wannan ledar fa?".

Na jefa mata tambayar ina jawo ledar da ta ajiye a gabanta na soma buɗewa, atamfa ne guda biyu da sarƙa da ɗan kunne. "Wai har kin manta kenan? Tsarabar da Mansur ya kawo ne". Na yi mata kallo guda ina fiddo da atamfar ina ƙare musu kallo. "Ai kuwa ga su ma sha Allah! Allah ya saka masa da alkhairi ya ƙara buɗi. Amma dai wannan ɗawainiyyar ta yi yawa kar ki manta fa ko gabatar da kansa bai yi a gaban magabatanki ba".

"Amin! Matsalata da ke kenan ba a yi miki gwaninta ko kaɗan. Bawan Allahn duk ƙoƙarin da yake yi a kaina in ba a sa masa albarka ba ai bai dace a kushe sa ba, ke yau da safen nan ma da muka yi waya cewa ya yi na kusa na daina fita wannan tallar sai ɗauka dukkan ɗawaniyyata da ta mahaifiyata".

Babu shiri na ware dukkan girman idanuna a kanta tare da sake leɓɓe ina bin ta da kallon mamaki, kafin na yi magana muka jiyo sallamar Anty Sawwama da hakan ya tursasa mini haɗiye zancen da na yunƙuro da nufin furtawa. Muka haɗe baki da Amira wajen amsa sallamar muna yi mata martaba da zuwa, falo muka shiga muka zauna kana muka gaishe ta ta amsa fuskarta ɗauke da yalwataccen annurin da ya ƙara taimaka wajen fito da tsatsar kaman jinin da suke yi da Abbana. " Na yi muku sammako ko?". Na yi murmushi tare da girgiza kaina alamar a'a hakan ya ba ta damar ci gaba da maganar. "Ina son na yi magana da Abbanki ne shi yasa na yi wannan sammako don kwana biyun nan da damuwar nan nake kwana nake tashi a cikin raina. Ina dai suna ciki ko?".

"Ga mu me ye muka yi ake nemanmu da wannan farar safiyar?".

Martanin da Umma ta mayar mata kenan cikin kakkauran murya tana isowa cikin falon ta zauna tare da ɗaura ƙafarta ɗaya bisa ɗaya. "Hafsatu kenan kun tashi lafiya, Mannirun yana ciki kuwa?".

"Da ba mu lafiya ba ai ba za ki zo ki tadda mu haka ba. Manniru kuwa yana ciki amma na yanzu zai fito ba sai ki jira shi". Gabaɗaya ji na yi jikina ya yi sanyi ƙalau na sadda kaina ƙasa ina jin zafin furucin da Umma ta yaɓawa Anty Sawwama. Fitowar Abba ya sani ɗago kaina ina bin sa da kallo har ya zauna haka kawai na ji tausayinsa ya cika mini raina ba tare da na san dalili ba.

"Maman Umar ke ce tafe da safiyar nan? To ya gidan ya kuma yaran?".

"Wallahi ni ce tafe gida da yara kuma duk lafiya lau. Daman na zo mu tattaunawa wata magana ne da kai shi yasa na yi sammako kar na zo na iske ka fita wajen aiki".

Shewa Umma ta saka har da tafa hannu kafin ta ce"su aiki manya, yo wannan aikin har wani abun ne? Aikin da ba ya tsinana masa komai shi kansa balle kuma wanda suke kewaye da shi". Ƙwalla suka ciko mini kurmin idaniyata cikin rauni na ce"don Allah Umma ki yi haƙuri mana".

Amira ta riƙo hannuna tana faɗin"Amatullah mu je daga waje mu ba su waje su tattaunawa". Ban yi mata musu na tashi muka fita muna fita wani kuka mai ƙarfi ya kubce mini na kifa kaina a bisa gwiwa ina rero sa cikin durshashewar murya. Duk ƙoƙarin da Amira ta yi na ba ni haƙuri da lallashina na gaza sarrafa kaina kukan ne kawai nake jin yana yi gaban kansa yana fitowa. Har sai da Ummanta ta fito ta nema jin ba'asin me yake faruwa Amira ta yi mata bayani ita ma ta lallashe ni sosai ganin ba ni da niyyar tsagaita kukan hakan ya sanya ta jan hannuna zuwa ɗakinsu, ta umarci Amira da ta ƙarisa girkin da na aza bisa wuta.

Ko anan ɗin ma hawayen sun kasa tsayawa da ƙyar Umman Amira ta lallashe ni ta zubo mini wainar da take toyawa sai dai na kasa kai ko da loma guda cikin bakina. Haka har Amira ta zo ta iske ni .

"Don Allah ki kwantar da hankalinki babu komai fa,Anty Sawwaman ma fa yanzu na ga ta fito za ta tafi".

Na zabura na miƙe zan fice Amira ta riƙo hannuna ta riƙe gam" ina kuma za ki je?". "Zan je wajen ta ne kafin ta tafi mana". Ta gizgiza mini kanta"bai kamata ki je yanzu ba Amatullah. Idan maganar da suka tattauna ta shafe ki to ko ba ki je ba za a ƙira ki, amma tun da kika ga ba a neme ki to maganar ba ta shafe ki ba ne ta kowacce fuska".

Cikin sanyin jiki na koma na zauna tare da buga wani uban tagumi, ganin yadda Amira ta dage ita da Ummanta wajen kwantar mini da hankali hakan ya sani dole na saki fuskata ba don na daina jin raɗaɗi da zogi a cikin raina ba. Haka kawai na ji gabaɗaya zaman gidan ya ishe ni har yunƙurin ƙiran Anty Sawwama na so yi da wayar Amira sai dai ban haddace lambarta a kaina ba haka dole ina ji ina gani na haƙura. Umma ta soma ƙwala mini ƙira tana shelanta mini na fito na gama dama kunnun, sai da na yi wanka na shirya kana na ɗauki tallan muka fito tare da Amira yayin da almajirin da yake tafiya mana da kayan ya yi gaba. Inda muka saba zama kamar kullum yau a nan muka yada zango, ba mu yi awa guda cikakken ba muka sayar da komai.

"Bari na yi sauri na je na kai wa Naziru masarsa kar ki gaji da zaman".

Amira ta yi zancen tana miƙewa tsaye, taɓe baki na yi ina faɗin"ni yau gabaɗaya ma wallahi ba na sha'awar komawa cikin gidan nan. Don tashin hankalin cikinsa ya fi komai yawa". "To Amatullah ya ya za mu? Tun da ƙaddara ta jefo nan kam ai haka za mu yi haƙuri". Haka kawai na ji wani sanyi a raina da na hango Bashir yana nufo wajen har sai da na kasa haƙuri na fito da abin da yake raina, wanda ni ma kaina ban taɓa zato da tsammanin bakina zai iya furta makamancin irin wannan kalamin ba.

"Yauwa! Ga can Bashir ma yana tahowa, za mu yi hira da shi kafin ki dawo don na lura mutumin akwai shi da barkwanci".

Sakeke Amira ta yi tana kallona hakan ya sani ankara da fahimtar cewa na kwafsa, sai dai ban bari na bugo jirgin nawan da wuri ba na yi wuf na gyara maganan. "Malama ni fa ba wani abu nake nufi ba don na ga kina ƙoƙarin fassara ni ta wani fuskan daban". Ta sheƙe da dariya mai isarta sai da ta tsagaita kafin ta ce"a yi dai mu gani in tusa tana hura wuta".

"Ni fa ba abin da kike nufi ne a cikin raina ba. Kawai ba na son komawa gidan nan yanzu gabaɗaya shi yasa". Ta yarfa hannayenta alamar babu abin da ya shafe ta da abin na furta, daidai lokacin da Bashir ya iso wajen bakinsa har kunne. [10/1, 1:48 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_______________________________________

Page 2️⃣5️⃣

"Barka da warhaka yake tauraruwar da ke haska ilahirin birnin zuciyata. Ban san yadda zan kasancewa a duk lokacin rana ta fito ta faɗi ba tare da na yi tozali da wannan kyakykyawan fuskarta kin ba, da ke nake kwana a cikin raina haka zalika da ke zan farka ƙunshe a ƙirjina, zan so ki ba ni dama don na nuna miki ainihin yadda nake yi akan ki Amatullah". Na tallafe kuncina ina kallonsa tare da cewa"to wani irin dama kake buƙata daga gare ni ya kai bawan Allah?". Da alama maganar tawa ta haifar masa da wanzuwar farin ciki a cikin ransa da har sai da ya bayyana ɓaro-ɓaro a bisa fuskarsa.

"Ki ba ni dama shiga cikin zuciyarki ni ma na yi miki alƙawarin wadata da dawwammen farin ciki kuma ba zan taɓa sanya ta yi dana sanin zaɓina ba". Na saki taƙaitaccen murmushi kafin na sama damar cewa"ga shi kuma babu abin da yake zama dawwammen a cikin duniyar gabaɗaya, face ikon Allah". Ya ɗan rusunar da kansa ƙasa yana sosa ƙeyarsa haɗe da cewa"to na ji amma na ba ki tabbacin ba za ki taɓa yin kuka ba idan ina kusa da ke".

"Ikon Allah sai kallo wai na zaune ya faɗi. Amatullah ke ce dai wacce na sani ko kuma gizo idanuna suke yi min?". Amira ta yi furucin cikin zallan mamaki da al'ajabina. Na yi fari idanuna kafin na furta"wai daman ba ku tafi ba ne? To dai ki yi sauri don ba zan tsaya jiranki da yawa ba". Ta sheƙe da dariya haɗe da cewa"wannan kuma zance kike yi". Tana dasa aya a nan ta juya ta tafi kai wa Naziru masarsa. "Ina so ki ba ni dama a yau domin na fallasa sirrin zuciyata izuwa na ki zuciyar. Don so nake yi na tabbatar mata da cewar ta sama abokiyar rayuwa na har abada wacce ba ta san komai ba face so da ƙaunarta".

Kalaman Bashir kenan da suka yi silar dawo da idanuna kansa. Har yanzun fuskarsa ɗauke da maɗaukakin annuri haka kawai na ji na tsinci kaina da kallon fuskarsa da take zagaye da kwantaccen saje baƙi wuk da shi har wani sheƙi yake tamkar yana shafa masa mai. "Tafi kanka tsaye wajen isar da saƙon da yake ƙunshe a cikin zuciyarka".

Da alama ya ji daɗin zancen nawan, ya gayara zaman yana fuskanta na da kyau kafin ya soma zubo jawabi babu ƙakkautawa. Yi kawai yake yi ina ji da sauraronsa yayin da na gaza ɗauke idona daga gare sa har ya kai aya wanda hakan ya yi daidai da canzuwar bugawar zuciyata da hakan ya haifar mini da runtse idanuna. "Tauraruwata lafiya kuwa? Na ga gabaɗaya yanayinki ya sauya". Na furzar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakina kafin na ce"ba komai". Ya yi hanzarin katse ni"ai kuwa yanayin ki ya nuna cewar akwai wani abu da kike ɓoyewa. Sanar da ni mene ne? Don yanzu zuciyata da taki sun zama aminan juna babu abin da za mu ɓoyewa junanmu".

Ya ƙare zancen yana ƙara matso da bencin da yake zaune a kai kusa da ni, na cira kai na yi masa wani irin kallo da ya sanya sa shan jinin jikinsa. "Na ce maka babu koma ko za ka yi mini dole ne?". Na yi zancen fuskata a ɗaure mur tamkar magribar ɗinya. "Ki yi haƙuri ba nufina kenan na ɓata miki rai ba". Ban tanka masa ba na miƙe na soma harhaɗa kayanmu, ina cikin aikata hakan Amira ta dawo. "Har kun gama hirar da ku kenan? In kuma ba ku gama sai na koma na ba ku waje".

Na wurga mata harara da wutsiyar idona"in za ki zo mu tafi ki zo. In kuma ba yanzu za ki tafi ba sai ki sanar da ni". Maimakon ranta ya ɓaci bisa yanayin da na yi mata maganar sai ma murmushin da ta saka ta ce"daɗina da ke saurin hawa Amatullah. To haɗa kayan sai mu tafi". Muryar Bashir ta katse ni daga tattare kayan da nake yi na tsaya cak.

"Ki yi haƙuri idan ni na ɓata miki rai, na roƙe ki har ki azabtar da zuciya da ruhina ta wannan hanyar".

Haka kawai na ji gabaɗaya ilahirin jikina ya yi sanyi ƙalau na ja dogon numfashi na fesar kafin na waigo, na yi turus ganinsa durƙushe akan gwiwoyinsa. Na runtse idanuna ina faɗin"don Allah ka tashi kar mutane su ganka haka". Ya marairaice murya"ba zan tashi ba har sai kin tabbatar min da cewar ba ni na yi silar canzuwar yanayin fuskarki ba Amatullah".

Banza na yi da shi ba tare da na ce da shi uffan ba na ci gaba da aikin gabana sai da na haɗa kayan tsaf, almajirin da yake ɗauka mana kayan ya zuba su a wheelbarrow ya yi gaba da su. Ganin Amira ba ta da niyyan tafiya hakan ya sani jan hannunta muka bar wajen har mun yi nisa sai na ji ta tsaya cak ba ta tafi, na ja hannunta ta ƙi motsawa hakan ya sani waigowa don ganin abin da ya hana ta tafiya. A zafafe na soma cewa"me ye hakan Amira ina jan ki kina turjewa? In ba tafiya za ki yi ba ai sai ki sanar da ni". Ta jijjiga mini kanta alamar duk abin da na faɗa ba su hau gwadaben dalilin da ya hana ta tafiya ba.

"Amatullah don Allah ki duba lamarin Bashir, na yi wa masa farin sani kuma duk wanda zai ba ki labarin halinsa to a bayana yake. Ban taɓa jin ya furtawa wata mace kalmar so ba a kaf cikin tashar nan sai ke, ina da tabbacin da dukkan zuciyarsa yake sonki. Duba ba fa ki ga tun ɗazu yana kan gwiwoyinsa bai tashi ba".

A faƙaice na juya na kalle shi har yanzu yana durƙushe akan gwiwoyinsa bai gusa ba. Tagwayen ajiyar zuciya na sauƙe ina dafe goshina saboda sarawan da kaina yake yi mini tamkar zai tsage gida biyu. Ban ce da ita komai ba na koma wajen Bashir na tabbatar masa da cewa ni bai yi mini komai ba. "To indai har ki na so na yarda da duk abin da kika furta sai ki yi min wani alƙawarin guda".

Na ware idanuna"wani irin alƙawarin ne haka? Faɗi ko mene ne matuƙar bai fi ƙarfina ba zan yi maka shi Bashir". Sai da ya gyara tsayiwarsa kafin ya ce"ina so yi min alƙawarin gobe za ki ba ni lokacinki don mu tattaunawa". Ba tare da tunanin komai ba na tsinci kaina da faɗin"in Sha Allah na yi maka wannan alƙawarin". Cike da jin daɗi ya amsa da cewa"to ina godiya, mu je na yi muku rakiya ko?".

Na jijjiga kaina"ba buƙatar hakan, kai dai kawai ka koma wajen sana'arka". "To shikenan yadda kika ce haka za a yi ranki a daɗe". Murmushi kawai na sakar masa na bar wajen muka ci gaba da tafiya tare da Amira. Har mun yi nisa da tashar na tsaya. "Lafiya kuma kika tsaya?". Amira ta jefa mini tambayar cikin zaƙuwar son jin amsa daga gare ni.

"Wallahi da zarar na tunkaro hanyar gidan nan sai na yi gabana yana faÉ—uwa. Haka nake jin ba na son komawa cikin wannan gidan saboda tashin hankalin da zan tarar a cikinsa ko na sakan guda ba na samu farin ciki".

Ta riƙo hannuna dukkan biyun ta sanya cikin nata kafin ta soma magana da laulausan amon mai ratsa ƙalbi. "Amatullah sai fa kin cire damuwar komai daga cikin ranki, kin ga rayuwar nan kowa da irin na shi ƙaddarar da kuma ƙalubalen rayuwarsa". Na yi saurin tarar numfashinta"Amira ni fa ba dogon magana nake son ji ba. Kawai ba na son komawa gidan nan ne a yanzu na fi so sai lokacin tafiya islamiyya ya gabato kafin na koma, ni wallahi gwara mu koma tashar ma mu yi zamanmu". A tsorace ta waro idanunta ta buɗe su tar a kaina"tasha kuma Amatullah?". Ba tare da tsoro ko shakkan komai ba na ce"ƙwarai kuwa, zaman cikin tashan nan ya fi mini kwanciyar hankali fiye da zama cikin gidan nan".

Ta riƙe haɓa cike da mamaki tare da faɗin"tirkashi! Lalle lamarin ya girmama. Amatullah yau ke ce da bakinki kike furta kin fi son zaman tasha fiye da gida". Na yi shuru na gaza ba ta amsa don na rasa ƙwarin gwiwar buɗe bakina. Take wani tunanin ya faɗo mini a rai tamkar faɗuwar aradu na yi caraf na ce"ko dai mu je gidan Anty Sawwama ne?". Ta yi sakeke kawai tana kallona kafin can ta yi magana a taƙaice. "Indai har za ki sama nutsuwa a can ɗin, to mu je mana". Murmushi muka sakarwa juna kafin na ja hannunta muka fice daga layin, tudun nabawa muka nufo da yake bayan layinmu, tun daga zaure muke zabga sallama har muka isa cikin gidan, gidan wayam da alamun Umar ya tafi makaranta don daman shine mai zama a gida.

"Wa alaikussalam sannunku da zuwa".

Muka tsinkayo muryar Anty Sawwama daga bayan mu da hakan ya sa mu juyawa dukkanmu. Anty Sawwama ce da alama daga banÉ—aki ta fito ta ajiye bautar da ke hannunta kafin ta yi gaba muka bi ta a baya har cikin É—akinta. Sai da muka zazzauna kafin muka gaishe ta ta amsa mana fuskarta babu yabo babu fallasa. "Daga ku kuwa kuke da wannan ranar?".

"Daga wajen tallla muke". Na amsa mata a gajarce, sai dai na lura da yanayin fuskarta ta sauya gabaɗaya ta yi ɗan jim kafin ta can ta ce"Allah dai ya kyauta, ki je kitchen ki ɗauko muku by ragowar abincin safe ku ci". "To". Na amsa da shi yayin da nake tashi na nufi kitchen na ɗauko Mana abincin na ajiye mana muka ci tare da Amira sai da muka gama ci tas, kana na tambayi ko akwai wani aikin da za mu yi mata ta ce sai dai mu haɗa mata wutan abincin rana. Kamar yadda ta buƙata haka muka fito muka fara aikin, na soma haɗa wuta yayin da Amira ta ɗauko doyan ta soma ferewa. Sai da muka haɗa komai har ruwan ya tafasa muka zuba doyan kana na tashi na shiga ciki wajen Anty Sawwama yayin da na bar Amira tana zaune tana waya da Mansur.

"Sannu da hutawa Anty Sawwama".

Ta gyara kwanciyarta daga gishingiɗan da ta yi kafin ta amsa muni cikin faɗin"yauwa uwata sannunku da aiki". "Anty daman na zo ne musamman don na ba ki haƙuri akan abin da ya faru tsakaninki da Umma ɗazu da safe. Ina mai ba ki haƙuri a madadinta kuma ina so ki yi mata uzuri". Ta jinjina kanta tana sakin taƙaitaccen murmushi kafin ta ce"tabbas albasa ba ta yi halin ruwa ba. Uwata ba komai ai ya riga da ya wuce, kin ga ni har na manta ma ai".

"To amma Anty me ye kuka tattaunawa haka da ya ki tafiya da wuri? Ko sallama fa ba mu yi ba sai fito na yi na iske har kin tafi".

Ta sauƙe tagwayen ajiyar zuciya mai matuƙar sauti da har da kunnuwana suka ji yo mini sautin. "Uwata ba wata magana ba ce da za ki tada hnakalinki, daman na je na roƙi alfarman Manniru da ki dawo wajena da zama saboda yanzu kin girma ke ba yarinya ba ce, sannan a can gidan falo ne kawai ne da ɗaki dole ne wani lokacin iyayenki suna buƙatar yin sirri a tsakaninsu wanda babu damar yin hakan. Da a tunanina na ce idan ki gama haɗa haddarki sai ki dawo idan kin ga nan ɗin ma bai yi miki ba sai ki koma wajen yayarki Zulaihatu". Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya mai nauyin gaske, duk wasu gaɓoɓin jikina suka yi sanyi ƙalau. Anty Zulaihatu ita ce babbar ɗiyar Anty Sawwama sa take aure a cikin gari, kuma ita ɗiya ɗaya tilo mace sauran ukun duk maza ne. Yaya Alhassan shi ne yake bin bayan Anty Zulaihatu wanda yanzu haka yana aiki a ma'aikatan shinfaka yana samu sosai don hatta gidan da suke ciki shi ya saya musu, daga shi sai Yaya Walid wanda ya ci sunan Abbana aka ɓoye masa suna ana ƙiran sa da Walid wanda yanzu haka yake karatu jami'ar jiha sannan autansu Umar wanda tazarar tsakaninmu da shi kaɗan ne. Kalaman da ta ɗaura da su su suka yi silar dawo da ni izuwa duniyar zahiri daga na tunanin da na dulmiya a cikinsa.

"Amma tun da Ummanki ba ta amince da shawarar da na je da ita ba. Daman shawara ce ba komai ba".

"To Anty ki bari zuwa bayan kwana biyu mana sai ki ƙara komawa ki sama Abba shi kaɗai, ko a wajen aiki ne wataƙila ya amince". Na ƙare zancen cikin marairaice murya yayin ƙwalla suke ciki mini kurmin idaniyata. Kafin ta yi magana muka ji yo sallamar Yaya Alhassan muka amsa masa kafin ta shigo ciki na tashi na amsa ledar da yake hannunsa kana na gaishe shi. Ya ɗauke kansa gefe kamar bai ganni ba yana cewa"ai ni kam na yi fushi Amatullah. Na ma yi tunanin ko kin manta hanyar gidan namun ne ai".

Na girgiza kaina"Yaya Alhassan wane ni na manta hanyar gidan nan, akwai kwanakin nan ba na samun zama ne saboda sauƙarmu ta gabato". Ya faɗaɗa annurin fuskarsa tare da faɗin"haka Umma take sanar da ni, yaushe ne sauƙar takun?".

"Yanzu sai saura sati uku". Ya jinjina kansa"Allah ya kaimu lokacin kafin lokacin ma kuma sai ki zo ki ƙara sanar da ni". Cike da jin daɗi na ce"to in sha Allah, bari na je na duba girkin na bar Amira ita kaɗai a waje". Har zan fice Yaya Alhassan ya dakatar da ni.

"Ai kuwa na zo a daidai ba zan tafi ba sai na ci girkin ƴar ƙanwata".

"Lalle kam! Yaushe rabon duniya da ayyaraye Alhassan? Ni ba zan iya tuna ranar da ka ci abincin rana a cikin gidan ba ko an ce ka saurara ka ci za ka kawo uzurin cewar kana sauri. Amma yau da yake Amatullah ce ta girka ko tayi ba a yi maka ba za ka tsaya". Furucin Anty Sawwama kenan tana kafe Yaya Alhassan da ya sadda kansa ƙasa da ido, ni kam murmushi kawai na yi na fice. Har yanzu Amira wayar take yi na je fizge na kashe muka soma gyara kayan miyan da Yaya Alhassan ya kawo kan ka ce me ye tunin har mun ɗaura miyan akan wuta. Bai ɗau lokaci ba ya kammala muka sauƙe a lokacin Umar ya dawo daga makaranta.

"Ke yarinyar nan yaushe kika zo?".

Na wurga masa harara"ban sani ba É—an rainin yawo kawai, kuma da kake ce mini yarinya ka san dai da cewa na girme ka ko".

"Never wannan kuma zancen ne. Me ye kika jagwalgwala mana haka?". Ya ƙare zancen yana sunkuyawa ya ɗauki doyar da na sauƙe, na kai masa bugu ya zame ya yi ciki da gudu. Na kwafa na ci gaba da zubawa Yaya Alhassan abincin na kai masa ciki. Ya buɗe ya soma ci.

"Zan dawo na same ki a nan ne?".

"A'a ni kam yanzu ma tafiya zan yi, don zan je islamiyya". Ya É—ago kansa ya yi mini kallo É—aya kafin ya mayar da idanunsa kan abincin ya ci gaba da magana. "To yaushe za ki dawo?".

"Sai an kwana biyu".

Ya yi shuru bai ce da ni komai ba sai can ya ce"ina son zuwa gidanku ko don na dinga ganinki ina kuma gaishe da Abba. Amma ba na jin daɗi abin da Umma take yi a duk sadda na je wannan dalilin ne ya sa na ɗan ja baya da zuwa". Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya kana na furta"halin Umma ai sai haƙuri". "Amma dai in Sha Allah zan yi ƙoƙarin na zo kafin lokacin sauƙanku sai mu tattaunawa akan abin da ya dace a yi muku".

"To". Na amsa da shi na fito na yi alwala muka shigo tare da Amira muka yi salla, kafin mu iddar tunin Yaya Alhassan ya kammala cin abincin har ya Yaya Alhassan ya koma wajen aiki, a gurguje muka ci abincin muka fara yin haramar tafiya Anty Sawwama ta ba mu dubu ɗaya ta ce mu hau napep ina ji Yaya Alhassan muka karɓa da godiya, tare muka fito da Umar ya rako har bakin hanya hana shi ma ya wuce wajen sana'arsa ta ɗinki. Tun muna shawo kwana muke cin karo da taron jama'a har muka iso ƙofar gidan, muka iske mutane a cike maƙil ko hanyar wucewa babu. [10/3, 1:12 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

______________________________________

Page 2️⃣6️⃣

Mutanen ta ko'ina babu masaka tsinke, ba mu sama damar shiga cikin gidan ba muka soma jiyo jiniyar motar ƴan sanda ta nufo wajen, hakan ya sa mutanen wajen suka soma darewa. A ƙofar gidan motar ta faka wasu ƴan sanda biyu suka fito diro daga bayan motan yayin da Baban Adnan ya fito daga gaban motar. Kai tsaye cikin gidan suka nufo hakan ya ba mu damar bin bayan su muka shiga tare, filin tsakar gidan ma ya cika da mata. "Ina wacce aka watsawa ruwan zafin?".

Tambayar da Baban Adnan ya yi kenan da ya sani kai dubana gefen da na ka an fi cika, idanuna suka sauƙa akan Asabe da take yashe a ƙasa tana fitar da numfashi a wahale, cikinta ya yi jajir tun daga wuyanta har zuwa gadon bayanta ruwan ya ƙona ta, rigar dake jikinta ya manne a fatarta tamkar tare suka zo. Babu shiri na runtse idanuna sakamakon rawar da jikina ya soma yi tsikar jikina yana tashi. "Duk taron yawan nakun nan a rasa wanda zai iya kai ta asibiti tun lokacin da abin ya afku, sai dai ku cika gidan ku yi cirko-cirko akan ta". Furucin Baban Adnan kenan cikin zallar takaicin da ya cika masa birnin zuciyarsa, kafin kowa ya yi magana Maman Adnan ta yi caraf ta amshe zancen tamkar wacce take jira ya ce kulle ta ce cas.

"To kai ina ruwanka? Waye ya aike ka balle ya ga daÉ—ewanka?. Kai ka san abin da ita Asaben ta yi ta yi mata haka?".

Ba ta ƙarisa ba sakamakon marin da Baban Adnan ya sharara mata, daman an yi masa shaida a kaf cikin unguwan nan da kewayenta babu wanda ba ya shakkan dukan matarsa fiye da shi. Ko a gaban waye ba ya shakkan kai mara bugu ko da dalili ko akasin hakan. "Ki bar ni na yi aikina yadda ya dace wannan ba abin da ya shafe ki ba ne". Furucinsa ya sanya kowa shiga tarairayinsa, tunin ya ba da umarnin a wuce da Asabe da take kwance magashiyan rai a hannu Allah zuwa asibiti. Ita kuwa Maman Vector da na ji an ce ita ta yi aika-aikan aka maka mata ankwa suka tisa ƙeyarta. Mutuwar tsaye na yi don har aka fice da ita na gaza motsawa daga inda nake tsaye balle na yi wani yunƙurin barin wajen ban dawo daidai ba har sai da Amira ta dafo kafaɗuna.

"Ki je ki huta. Don matsalar gidan nan ba mai ƙarewa ba ne". Kaina kawai na iya ƙarfin halin jijjiga mata kafin na soma jan ƙafafuna da nake jin su tamkar ba sa cikin sassan jikina haka na isa ɗakinmu ba tare da na san inda nake cilla ƙafata ba, na iske Umma ba ta nan ko wanka ban yi ba na sauya kayan jikina zuwa na Islamiyya don lokaci ma ya riga da ya ƙure na fito na yi wa Amira sallama na tafi, sauri nake yi tamkar zan kife akan karan hancinsa ina isa cikin islamiyyan ana fara tarar masu zuwa latti ko aji ban wuce ba na nufi wajen Malam Suleiman a makare. Tun kafin na iso na hango Aliyu Shehu ya fito daga cikin staff room ɗin malaman muna haɗa ido da shi ya ƙara murtuƙe fuskarsa daman can ba shi da annuri ko kaɗan kullum fuskarsa a haɗe take tamkar magribar ɗinya. An yi ittifa'i a duk cikin islamiyyan babu wanda yake ji da kansa da tunƙaho da fariya da ilminsa kamar sa.

"Dalla malama ki ɗago ƙafa, kin san ai ke kaɗai ake jira amma kike wani tafiya a hankali kamar ba ki san ana jiran ki ba".

Ya yi zancen cikin ɗaga murya ta yadda zan ji, na ƙara saurin da nake yi ina sowa wajen ya juya ya koma ciki na bi shi a baya har cikin staff room ɗin, da sallama na shiga wanda ta amsawar Malam Suleiman da na Malam Aminu sai kuma Al'amin Yakubu. Sai da na zauna kana na gaishe da su suka amsa. "Amatullah ya ya aka yi kika makara haka?". Tambayar da Malam Aminu ya jefo mini kenan da ya tursasa mini sadda kaina ƙasa saboda tuno munin abin da wakana, sai da na aro jarumta na yafawa kaina kafin na iya faɗin"Malam a yi haƙuri".

"Ba batun haƙuri ba ne Amatullah yanzu gabaɗaya kina ƙoƙarin komawa baya akan lamarin karatunki. Ga shi kuma aski ya zo gaban goshi". Jikina ya ƙara yin sanyi ƙalau na kasa cewa komai sai Al'amin ne ya kare ni da kalamansa. "Malam in ba za ta faɗi gaskiyar abin da ya faru ba ni zan faɗa maka". Na yi hanzarin ɗago idona ina kallonsa sai dai ya ƙi yarda ya haɗa ido da ni, maimakon hakan ma sai ci gaba da ya yi da maganarsa.

"Malam na haÉ—u da ita a hanya kafin na iso, wata yarinya mai talla ce abin da take sayarwa ya zube shi ne ta tsaya ta taimaka maka. Kuma ta rakata har gida gudun kar a yi wa yarinyar faÉ—a".

Murmusawa kawai Malam Aminu ya yi tare da cewa"to Allah ya kyauta". Duk muka haɗe baki wajen amsawa da amin kafin Malam Suleiman ya soma jawabinsa. "Mun tara ku anan ne saboda maganar zuwan baƙonku Sheikh Dawood bikin walimarku. Bayan shi akwai sarakuna da masu muƙamai a jihar nan da za su halacci wajen don aka mu na ku nutsu ku yi karatu mai kyau, domin tabbatar da ingancin karatun da kuka samu daga islamiyyar nan. Sannan kamar yadda muka sanar da ku a tsakaninku ne za a cire gwarzon shekara, ɗalibi mafi ƙwazo da kuma wanda ya zo na ɗaya". Tun kafin ya gama maganar Aliyu Shehu ya soma murmushi tare da cewa"Malam ai ba za mu ba ku kunya ba, kuma in sha Allah wannan shekarar ma ni zsn cinye dukkan waɗannan kambun".

Kalaman Aliyu suka sani ɗago idona na saci kallonsa, mutum ne shi ma matuƙar son ganin ya kewa kowa akan komai. Shekara uku kenan a jere shi yake lashe kambun ɗalibi mafi ƙwazo a islamiyyar gabaɗaya, a bikin yaye wasu ɗaliɓan ma ya kan yi majinta balle kuma nasa, wannan dalilin ya sanya ni cire duk wani buri a raina.

"Amatullah kasancewar ki mace É—aya a tsakaninsu dole idanu za su dawo kanki don haka ina so ki yi karatu mai kyau kuma cikin nutsuwa". "In Sha Allah Malam".

Dariya Aliyu ya fashe da shi da hakan ya ja hankalinmu zuwa gare shi, Malam Suleiman ya tsawatar masa. "Dariyar me ye kake yi?".

Ya ladabtar da murya"tuba nake yi Malam, wani abun na tuna".

"Za ku iya tafiya mun sallame ku".

Godiya muka gabatar musu muka tashi za mu fita Malam Aminu ya ƙira suna na juyo ina sauraron abin da yake faɗa. "Ki shiga aji huɗu ki karɓa haddansu. Yau Malama Khadija za ta sama zuwa ba". Cikin girmamawa na ce"to Malam". Na juya na fita har na yi ɗan nisa na jiyo muryar Aliyu na tsaya har ya iso gabana ya tsaya har da naɗe dukkan hannayensa a ƙirjinsa.

Na bi sa da kallo tun daga ƙasa har sama, ƙal-ƙal uniform ɗinsa yake ya sha goga ga ƙamshin wani sanyayyan turare da yake tashi daga jikinsa, hularsa taɓa ni ka sha hadisi fara sol sai sheƙi take yi.

"Tunanin me ye kike yi?".

Na yi masa wani kallo guda na ɗauke kaina tare da cewa"tunanin me ye kuwa zan yi?". Ya murmusa kafin ya ce"tunanin yadda za mu fafata da ke mana, tun wuri ki sauƙaƙawa kanki yawan damuwa don ba za ki taɓa cin nasara akan Aliyu Haidar ba, tun shigowata islamiyyar ni nake yi na ɗaya kuma na lashe kambun ɗalibi mafi ƙwazo a duk shekara, na yi bajinta a shekarar wasu ma balle shekarar walimarmu. Har na bar Islamiyyar nan babu abin da zai sauya wannan tarihin don haka ma kar ki sa a ranki".

Taƙaitaccen murmushi na saka kafin na sama zarafin cewa"Aliyu kenan!. Ai kai ya fi dacewa na ba wa shawarar ka cire tunani daga cikin ranka don da dukkan alama kai hakan ya dama. Ina yi maka fatan nasara a ko yaushe ni ka ga tafiyata". Ina ƙare faɗin haka na bar wajen na nufi aji huɗu domin karɓan haddarsu kamar yadda Malam Aminu ya umarce ni, har na yi na gama raina a ƙutume na yi musu ƙari na fito lokacin har an tashi sallan asr don haka kai tsaye na wuce wajen alwala na zauna na zabga tagumi abin duniya duk ya fi ya ishe ni. "Ke lafiyarki kuwa? Yau ki haɗuwa ba mu yi ba".

Na tsinkayo muryar Rauda a kusa da ni na zame hannayena daga tagumi da na rafza ina saki tagwayen ajiyar zuciya wani na bin wani. "Wallahi na fara gajiya da abin da Aliyu yake yi mini a ciki islamiyyar nan". Ta kafe ni da ido alamar son ƙarin bayani"wani Aliyu kenan?".

"Aliyu Shehu mana".

Ta taɓe baki kafin ta soma cewa"kin san Allah Amatullah wannan Aliyun sonki yake yi, matuƙar so ma kuwa. Ke in taƙaice miki bayani mazan ajinsu sun taɓa kama sa yana rubuta sunanki jikin ƙur'aninsa". Wani kallo na watsa mata da ya sanya ta haɗiye sauran zancen ba tare da furta su ba. "Wani irin banzar magana ce haka Rauda? Sanin kanki ne babu wanda ba ya ƙaunar ci gaba na a cikin islamiyyar nan kamar Aliyu. Ko wani abun bajinta na yi sai ya ƙalubalence ni akan hakan ki na nufin wanda ma duk cikin so ne kamar yadda kika yi ikirari?". "Ko waɗannan ba su kasance alamomin so ba to tabbas akwai soyayyarki mai ƙarfi a cikin zuciyar Aliyu. Shin ke ba ki lura da wani abu, duk yadda ƴan matan islamiyyar nan suke yi masa shishshigi baya kula su amma ke ko kina so ko ba kya so sai ya nema hanyar da zai yi magana da ke ko da kuwa baƙar magana zai faɗa miki".

Na miƙe kafin na furta"Rauda mu bar wannan maganar don hankali ba zai taɓa ɗaukarsa ba". Ban jira abin da za ta kuma cewa ba na tafi na soma yin alwala na zo na yi salla har iddar tana zaune a cewarta tana fashin salla a lokacin tare muka koma aji muka soma muraja'a cike da shauƙi da soyayyar abin da muke karantawa. Har sai da aka tashi ba mu sani ba sai da muka zo daidai inda muke son tsayawa kana muka yi addu'a kowa ya fito domin tafiya gida.

Tsaye a ƙofar fita na hango Al'amin yana tsaye muka sakarwa juna murmushi yayin da muka haɗa ido, na riƙo hannun Ammi ina cewa"raka ni na je na yi wa Bawan Allahn can godiya". "In kuka daɗe ni kam tafiyata zan yi don yunwa nake ji". Rauda ta yi zancen tana neman waje ta zauna tana jiran mu, ba mu amsa mata ba illa darawa da muka yi dukkanmu. Da sallama muka isa wajen Al'amin ya amsa mana yana ƙara yalwata annurin fuskarsa.

"Na yi tunanin ai ɓacewa kuka yi a cikin makarantar". Na murmusa tare da cewa"mun tsaya yi karatu ne". "Na dai lura ajin matan nan kun dade sosai".

Na ƙara murmusawa a karo na biyu kana na ce"daman na zo na yi maka godiya ne. Tabbas ka cece ni daga tuhumar Malam Aminu".

"Ya zama dole ne hakan Amatullah babu wanda bai san tambayoyin titsiye irin na Malam Aminu ba".

"To ni dai ina godiya matuƙa".

Har yanzu fuskarsa ɗauke take da murmushi ya ce"to yanzu dai mu je na raka ku ko?". Ammi ta amshe zancen"mu muka ce maka muna buƙata". Ya harare ta"yau dai ba zan kula ki don masifarki sai dai ki ci kanki". Ban tsoma musu baki ba illa murmushin da na yi muka soma tafiya muka isa wajen Rauda sai dariya muke yi mata don duk ta sauya Ammi sai tsiya take ya mata wai kamar ba ta yin azumi yunwar lokaci guda ta jigata ta har haka. Har muka rabu da Ammi da Rauda, Al'amin bai daina ja na da hira ba har farkon layinmu ya raka ni, muka rabu cikin girmamawa da mutunta juna.

Ina doso ƙofar gidanmu na ji gabaɗaya raina yana ɓaci zuciyata tana tafasa sosai. Haka kawai na nema dukkan nutsuwata na rasa ƙirjina ya tsananta bugu. Sai da na tsaya a zaure na ja dogon numfashi na fesar kafin na ƙarisa cikin gidan, har yanzun Umma ba ta dawo ba don haka wanka na yi na sauya kayana na tattare wasu abubuwan kana na ɗaura mama girki tuwo na yi da miyar bushashshen kuɓuewa na juye a kula, na je wajen Amira don ba na son zama shirun.

Babban dalilin ma shi ne ina son jin haƙiƙanin abin da ya faru tsakanin Asabe da Malam Vector da ya kai su ga raunana juna, kiciɓus na yi da Ummanta za ta fito na matsa na mata hanya ina yi mata addu'ar a dawo lafiya bayan ta shaida mini za ta je wajen Sa'ade uwar adashe ta kai zubinta. A falo na tarar da Amira tana kallo a wayanta na zauna kusa da ita tare da fizge wayar, ta bi ni da kallo"har kin dawo?".

"Har ne ma? Watau don ba ke kike zuwa ba dole ki faɗi haka. Amira na yi na yi dake mu shiga islamiyyar nan amma kin ƙi, ina guje miki ranar da wannan damar za ta kuɓuce miki".

Ta gyara zamanta tare da cewa"tun da dai na sama na salla ya ishe ni". Kaina kawai na jijjina na kawar da maganar ta hanyar cewa"wai ni kuwa me ye faru tsakanin Asabe da Maman Vector, Umma ba ta nan balle na tambaye ta".

"Kin san Baban Vector ya dawo daga Benue shi ne Maman Vector ta kama shi da Asabe a cikin É—akinta suna hira, kin sa ta da shegen kishin tsiya tana ganin haka ba ta wata-wata ba ta É—auko tafasasshen ruwan zafi ta shiga ta juyewa Asabe a jikinta".

Na dafe ƙirji"na shiga uku. Amma kuwa Maman Vector ba ta kyauta ba ai kamata ya yi ta fara jin dalilin shigarsa ɗakin Asabe".

"Ko ni ce fa zan yi fiye da abin da Maman Vector ta yi, wani dalilin ne zai sanya su keɓe da juna bayan su ɗin ba muharraman juna ba ne".

"Amira kenan. To ai in haka ne ma laifin Baban Vector ne tun da shi ya je har cikin ɗakinta". Ta taɓe baki"koma dai mene ne ni kam Maman Vector ta yi min daidai". Ta gyara zamana ina fuskantan da kyau kana na soma cewa"ni zuwa na yi ma na tambaye ki, ko akwai in da za ki je ne yanzu ko zuwa bayan sallan isha'i?".

Ta yi mini wani kallo kana ta ce"yau ko toyar awara ba zan fita ba amma lafiya kike tambaya?". Na yi ɗan jim kafin na ce"wallahi ba za ki gane ba ne ba na son zaman cikin gidan ne, ko Bashir za ki ƙira mini a waya to mu gaisa?". Tun kafin na rufe bakina na ga ta tsare ni da wani irin kallon mamaki da al'ajabi. [10/4, 12:16 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️Maimuna Tijjani Iyam

__________________________________

Page 2️⃣7️⃣

Sake da baki da hanci take kallona tamkar wacce ta ga wani sabon halitta, mamakinta ya kasa ɓoyiwa har sai ta furzo shi waje. "Bashir kuma? Yau da bakinki kike cewa na ƙira miki Bashir?". Na sauƙe sakakken ajiyar zuciya mai nauyin gaske kafin na sama zarafin faɗin"Amira ke fa ko yaushe kike nusar da ni cewar wanda ya nuna yana sonka a rayuwar nan ya gama maka komai, to yanzu laifi ne don na buƙaci ki ƙira mini shi kawai mu gaisa". Ta jinjina kanta"ba laifi ba ne kawai ban yi tunanin za ki buƙaci hakan da wuri ba ne, bari na ƙira miki shi". Murmushi kawai na sakar mata ina miƙa mata wayarta da yake hannuna ta karɓa ta soma lalumo lambarsa, haka kawai na tsinci kaina cikin wani irin yanayi wanda ni kaina ba zan iya fasalts ainihin takamammen abin da nake ji ba, na dai don kawai na sauya daga Amatullah ɗin da nake a can baya.

Manna mini wayar da ta yi a kunne da sauƙar sallamar Bashir a cikin kunnuwana su suka yi nasarar dawo da ni izuwa duniyar zahiri daga na tunanin da na afka. Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya kafin na amsa sallamar, jin muryata ya sanya sa sakin wani nishaɗantaccen murmushin da har sai da na ji ilahirin gaɓoɓin jikin sun amsa. "Tabbas na cika cikakken mai sa'a tun da har Sarauniya da kanta ta ƙira ni yau. Da ina da ikon buɗe ƙirjina da na yi hakan don na gwada miki irin farin cikin da nake ciki a yanzu".

"Uhmm! Daman na ƙira ne don mu gaisa. Kuma na ba ka haƙuri akan abin da ya faru ɗazu".

Tun kafin na rufe bakina ya katse ni"babu abin da za ki yi min a cikin duniyar wanda yake buƙatar sai kin ba ni haƙuri Amatullah, ni ɗin bawanki ne mai hidimta miki kuma zan yi alfahari da hakan a ko'ina kuma a gaba ko waye. Ina da tabbacin ba zan taɓa yin dana sanin sonki ba har abada ki ba ni dama don na gwada miki ƙarfin son da nake yi miki". Gabaɗaya na ji jikina ya mutu murus na gyara zamana kafin na ce"na ba ka dama". Ina faɗin haka na miƙawa Amira wayar ina rufe fuskata da tafukan hannayena saboda kunyar da yi wa raina mamaya. Babu abin da Amira take yi face dariya a haka dai suka yi sallama da Bashir bayan na ji da kunnena ya na faɗin ya damƙa amanata a hannunta. "Lalle ikon Allah! Ashe akwai ranar da za ki ba da kai bori ya hau Amatullah?. Haƙiƙa Bashir ya cika mai sa'a kamar yadda yake faɗa".

"Ban san me yasa ba ban san dalilin da ya sa har na ba shi dama ba Amira. Na dai fahimta kawai ina buƙatar wanda zai dinga kwantar mini da hankali ne wanda zai dinga saurara damuwa da matsalolin rayuwarta, wanda a duk lokacin da nake cikin damuwa zan tsaya a tare da ni. Tun da kin ga Umma ko yaushe ba ta zama a gida babu shaƙuwa a tsakaninmu ba ta da lokacin sauraran damuwata". A raunane na ƙare zancen ƙwalla yana ciko mini kurmin idanuna. Cike da kula ta Amirka take furta" ko ba ki da wata matsala ma yanzu kin kai muzalin da za ki buƙaci wani a kusa da ke, rayuwar nan sai da farin ciki. Farin ciki kuma ba ya samuwa daga wajen masoyi na haƙiƙa". Na furzar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakina kafin na sama sararin cewa"indai har na fahimci yana da ɗabi'un ƙwarai zan buƙaci ya gabatar da kansa a wajen Abba, don ni ba zan tsaya yin dogon soyayya da mutum ba".

"Ina da tabbaci akan son da Bashir yake yi miki gangariya ce".

Ban ce da ita komai illa gyaɗa mata kai da na yi alamar na gamsu da abin da ta furta, na jingina bayana cikin kujerar da nake zaune tare lumshe idanuna ina jin kaina kamar ba ni ba don ban taɓa tsammanin a nan kusa ko nisa zan iya amincewa wani saurayi ba. Shuru ya ratsa wajen kafin na kawar da shi ta hanyar cewa"wai a gida za ki zauna ne yau ba inda za ki je?". Na yi zancen har yanzu ban buɗe lumshashshun idanuna ba.

"Wai lafiyarki kuwa Amatullah? Sai ka ce wacce take zaune akan wuta a cikin gidan".

"Ba za ki gane ba ne Amira wallahi har raina yanzu ba na ƙaunar zaman cikin gidan nan, indai ba ya zama dole ba". Ta yi ɗan jim kafin ta ce"to ki dai yi a hankali". Na zabura tamkar wacce aka tsigarawa matsilli na buɗe idona tare da cewa"to ko dai gidan Ta salla za mu je?".

"Wai ke lafiyarki kuwa?".

Ta yi saurin katse mini hanzari kallon da ta tsare ni da shi ya tursasa mini yin ƙasa da kaina ina jin wani iri a rai da ruhina. Tashi ta yi ta shiga ciki ta ɗauko hijabinta ta dawo. "Tashi mu je don na fahimci in dai ba fita muka yi hankalinki ba zai kwanta ba".

Zumbur na yi na miƙe har na riga ta fita daga cikin ɗakin, ina sanya ƙafata na fita daga cikin gidan na ji wani sanyin daɗi yana ratsa ruhina. Nauyin da ƙirjina ya yi mini yana warwarewa a hankali-hankali, gidan Ta salla muka nufa wacce take dafawa Amira awara. Cike muka iske gidan da samari da ƴan mata, gefe guda wasu sun baje hajarsu yayin da Ta salla take zaune akan garduma gabanta da manyan kulolin abincin da take sayarwa a gida, kusa da ita muka zauna ta bi mu da kallo har muka zauna muka gaishe ta ta amsa tana zarcewa da faɗin"Amira wannan fa ina kika samo ta?". Ta kai ƙarshen zancen tana nuna ni da ƴar manuniyar ƴatsarta.

"Au! Wannan É—in ce ba ki gane ta Hajiya? Amatullah ce fa ta gidanmu".

Ta tafa hannu gami da rafza salati ta riƙe haɓa cikin mamaki ta ce"lalle girman ɗan mutum ba shi da wuya yanzu Amatullah ɗin Hafsatu ce ta girma har haka? Lalle muna da ƴan mata a unguwan zankaɗa-zankaɗa sai mu yi fatan Allah ya baku mazaje na gari". "Amin ya Allah". Muka haɗe baki wajen amsawa, sai a lokacin na sama damar ƙarewa tsari da zubi gami da irin mutanen da suke cikin gidan, a ƙalla mutane za su kai ashirin muka iske a gidan kowa yana harkan gabansa daga fahimtar da na yi ma wasu a gidan suke kwana.

"Har yanzu muna gidan nan nakun ashe? Ciki da falo ne kaman ai ko?". Tambayar da Ta salla ta jefo mini kenan da ya dawo da ni daga cikin karatun wasiƙan jakin da na faɗa. Na sadda kaina ƙasa na ce"e ciki da falo ne kawai, ai duk ɗakunan gidan ma haka ne".

"Ai kuwa wannan akwai takura a ciki yanzu haka kuke cakuɗuwa da iyayen nakun duk a ɗaki ɗaya?". Kunya ta hana ni cewa komai yayin da Amira babu abin da take yi face dariya har da ƙyalƙyalewa. Tashin samun amsa daga gare ni ya ba ta lasisin ci gaba da cewa"ai kuwa gwara tun wuri ku nemawa kanku mafita. Ga ku ƴan mata da ku amma ace har yanzu kuna raba ɗaki da iyayenku. Ai gwara ku ɗinga zuwa nan kuna kwana".

"Kwana kuma a nan Hajiya?". Na furta babu shiri ina ware girman idona akan fuskarta da ta gaji da jin man bleaching har ya saduda ya daina amsar man, ta yi jajir da ita tamkar ƙosan da ya ji jawa. "Ƙwarai kuwa ƴan mata nawa ne akan layin nan suke kwana a cikin gidan nan. Kai wasu ma gabaɗaya rayuwarsu a cikin gidan nan suke gudanar da ita". Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina satan kallon Amira na ga hankalinta ba ma a kanmu yake ba. Sai da na haɗo jarumta kafin na iya furta"Hajiya haka dai za mu ci gaba da haƙuri har Allah ya kawo mana mafita, ko kuma mazaje mu yi aure mu tafi gidajenmu".

Ta taɓe baki"to Allah ya kyauta".

"Amin".

Na amsa da shi a taƙaitacce, ba ta ƙara cewa da ni komai illa mayar da idonta kan Amira ta yi ta umarce ta da ta tashi ta ɗauko kwana ta zubo mana abinci na ce na ƙoshi da ƙyar ta tilasta mini akan sai na ci na saka hannu na ɗan caccakala abincin sai da muka yi sallan isha'i kafin muka fito za mu tafi. Cike ƙofar gidan yake da masu jaura babu wani nau'in abincin da ba a sayarwa a wajen, ƴan shaye-shaye sun yi bataliya a wajen sai cin karensu suke yi babu babbaka. Gabaɗaya jikina ya yi sanyi luƙus haka har muka isa gida jikina babu kuzari ba mu iso gida sai kusa ƙarfe tara da wasu mintuna na dare. Muna shiga gidan tun daga zaure na fahimci Abba ya dawo gaba ya soma faɗuwa har muka ƙarisa ciki. A ƙofar ɗakinmu na hango Abba yana tsaye ya naɗe hannayensa a bayansa idanunsa akan hanyar shigowa take na sha jinin jikina na kasa ɗago kaina. Ko gaisuwar da Amira ta yi wa Abba bai amsa ba ya juyo ya shige ciki ya bar ni cikin tarin fargaba.

"Amira na shiga uku, me ye zan cewa Abba?".

Na yi zancen a rikice muryata har yana shaƙewa tsabar rikicewar da na yi. Ta riƙo hannuna saboda gabaɗaya jikina rawa yake yi tamkar wacce aka jonawa wutar lantarki. "Ki kwantar da hankalinki mana komai zai zo da sauƙi. Idan ya tambaya ki ce raka yi kika gidan Sa'ade mu kai zubin adashen Ummata".

"Amira ke ma kin san ai dole ne ya tambaya".

"Ki nutsu kawai don in dai kika shiga a wannan yanayin duk abin da za ki faɗa ba zai shiga kansa ba". Kaina kawai na jinjina mata alamar na ji muka yi wa juna sai da safe kafin na shiga cika. Sai na da na aro jarumta da ƙarfin hali na yafawa kaina kafin na sama ƙwarin gwiwan shiga ciki bakina ɗauke da sallamar da sai na yi baki biyu kana a yunƙuri na uku na ji Abba ya amsa mini tare da ba ni iznin shigowa. Tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka na shigo cikin falon kaina a ƙasa kamar wacce ta ƙullawa Sarki sharri na zo na zauna ina yi masa sannu da zuwa maimakon ya amsa mini sai ya jefo mini tambaya.

"Daga ina kuke?".

"Na'am".

"Na ce daga ina kuke a cikin daren nan?". Ya kuma maimata mini tambayar a karo na biyu cikin tsawar da ya haifar mini da runtse idanuna.

"Abba ka yi haƙuri".

Na furta hawaye masu ɗumi suna gangarowa daga kurmin idaniyata. "Ba abin da na buƙata ba kenan. Amatullah daga ina kuke kuma waye kika tambaya kafin ki yi?". Sosai jikina ya ɗauki kyarma don duk ranar da Abba ya ƙira sunana kai tsaye to tabbas magana ce mai girma zai yi da ni ko kuma ransa ya kai maƙura wajen tunzura.

"Wai me yake faruwa ne nake jin ka na ta ɗaga murya?". Furucin Umma kenan yayin da take fitowa daga cikin ɗaki ta iso cikin falon ta zauna, Abba ya irge mata komai da ya wakana. "Don ta fita shi ne kake ta tada jijiyoyin wuya haka Manniru? So kake yi mu garƙame ta a cikin gidan mu dafa ta mu cinye kenan?. Ni fa ba zai yiyuwa ka tisa min ƴa a gaba kana ɗaga mata murya ba ba zai yiyuwa. Kai ba ka bar ni ba ƴan uwanka ma ba su bar ni ba, da wanne kuke so na ji ne?".

"Hafsatu ki bar ni da yi iko da ƴarta don ni Allah ya ɗaurawa nauyin kula da tarbiyanta. Ba zai yiyu na zuba ido ina ji ina gani ta lalace ba, wani abu ne zai fitar da ita da dare wanda ba ta yi sa ba tun ido na ganin ido?. Daga yau sai yau idan na ƙara dawowa ban tarar da Amatullah a cikin gidan nan daga ke har ita sai na saɓa muku saɓawa mafi muni".

Tsam Umma ta miƙe tamkar kububuwa jikinta har wani rawa yake yi ta nuna Abba da ƴatsarta haɗe da cewa"Manniru ba ka isa ba wallahi ka yi tsararo". "Ai kuwa yau zan nuna miki cewa na isa a gidana". Ya yi zancen shi ma yana miƙewa akan ƙafafunsa cikin tsananin ɓacin rai.

Ta matsa kusa da shi tana nuna kanta"ni kake ɗagawa murya? Ni kake kallon tsabar idona kana furta min duk abin ya fito daga bakinka? Tabbas ka kyauta kuma na gode". Tana dasa aya ta juya ta shige cikin ɗaki tare da turo ƙofar ta murza masa makulli. Cikin wani irin sauri kamar mayan ƙarfe haka Abba ya bi bayanta ya soma dukkan ƙofan yana magana. "Hafsatu ki yi haƙuri ki buɗe ƙofar nan ki fito mu zauna mu fahimci juna. Kar ki kwanta da baƙin cikina a cikin ranki hakan sai ya fi komai ƙona min rai". Har ya yi ya gama jawabinsa Umma ba ta tanka masa ba balle ta buɗe ƙofar, haka ya yi ya gaji ya komo ya zauna ya zabga tagumi.

Na ja jikina na matso na riƙe ƙafafunsa ina kuka don yadda na so na yi masa jawabi na rasa wannan ƙwarin gwiwan, saboda kukan ya gama cin ƙarfina ainun. Da dukkan ƙarfina nake kuka da take jikina ya ɗauki zafi kaina ya yi mini wani irin nauyi tamkar an ɗaura mini dutsen dala na jihar Kano a tsakiyar kaina.

"Ki daina wannan kukan komai ya wuce ki je ki kwanta. Dare ta yi yanzu".

Ya yi zancen yana zare ƙafarsa daga riƙon da na yi masa. Ya miƙe tsaye na yi wuf na ƙara riƙe sa sai a lokacin na sama damar yin magana. "Abba to ina za ka je?".

"Zan je masallaci na kwana, kar ki manta ki rufe ƙofar".

Yana gama faɗin haka ya fice ba tare da ya jira abin da zan ce ba. Na daɗe zaune a wajen ba tare da na motsa ba ina kuka kafin na tashi na lallaɓa na fito waje na yi alwala na koma ciki na gabatar da salla raka'a biyu. A falon na kwanta bayan na rufe ƙofar na kashe wuta, gabaɗaya na rasa gane mai yake yi mini daɗi idan na tuna Ni ce silar faruwar duk abin da ya faru sai na ji zuciyata ta ƙara karyewa hawaye sun soma ambali a kuncina. Maganganun Hajiya Ta salla ta soma dawo mini cikin kwanyata tabbas da yanzu ina da wajen kwana da Abba ba zai fita ya kwana a masallaci ba. [10/6, 3:36 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_____________________________________

Page 2️⃣8️⃣

Haka na ci gaba da juyi na kasa runtsawa har aka yi ƙiran sallan asubahi, da ƙyar na tashi saboda nauyin da gabaɗaya ilahirin jikina ya yi mini na fito na yi alwala na koma ciki na gabatar da zauna. Sosai kaina yake yi mini ciwo tamkar zai faɗo ƙasa ko zai rabu zuwa gida biyu, runtse idanuna na yi ina jin yadda ɗakin yake juya mini ina jin rufin ɗakin tamkar zai rikito a kaina. Na kifa kaina akan gwiwa ina karato farkon suratul Maryam ban gushe ina yi ba har sai na ji sauƙin lamarin na zame ns kwanta akan sallayan babu jimawa wani bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ni.

Tamkar a cikin mafarki na ji ana ƙiran sunana na buɗe idanuna da ƙyar ina jin ciwon kan ma tamkar ƙaruwa ya yi maimakon raguwa. Na tashi na zaune dafe da goshina da jijiyon kaina suka fito suka yi ruɗu-ruɗu ina kallon Umma da take tsaye a kaina dishi-dishi. Na yi ƙarfin halin jefa mata gaisuwa sai dai ko gizau ba ta yi balle ta amsa illa kallo na da ta ci gaba da yi tamkar yau ta soma tozali da ni. "Ba ki da lafiya ne?".

"Kaina ne yake yi mini ciwo sosai". Na amsa mata da shi cikin dauriya da halin da nake ciki. Ta yi ɗan jim kafin ta furta"ki tashi ki je ki ɗeba kunnu ga shi can na dama, sai ki dawo ki kwanta. Na san yadda zan yi da kunun tun da na ri ga da na dama shi". Na yi zumbur na ce"A'a Umma ai zan iya zuwa tallan ma". Kallon da ta katse ni da shi ya sani hanzarin haɗiye ragowar zancen ba tare da na gama amayo da shi waje ba. "Ki fita daga idona na rufe Amatullah, in ba haka ba kuwa yanzun nan zan yi wasan kura dake a cikin gidan nan ƴar iskan yarinya mai halin dangin ubanta". Jikina ya yi sanyi ƙalau na sadda kaina ƙasa ina jin gabaɗaya jikina ya ɗauki zafi tamkar naman da yake wuta ake sulala shi.

"Ki tashi ki je ki yi abin da na saka ki".

Ban ce komai ba na tashi na fita na je na wanke bakina kafin na ɗeba kunna na zauna a ƙofar ɗakin ina sha a hankali, da ƙyar yake wucewa ta maƙoshina tamkar wacce take haɗiyar ƙarangiya. "Amatutun Mama". Na ji yo muryan Amira ta tsakiyar kaina yayin da take jan kujera ta zauna kusa da ni. Ta bi ni da kallo"ya kamar ba kya jin daɗi? Na ga duk yanayinki ya sauya". Na lumshe idanuna da babu komai a cikin su face bacci da gajiya kafin na buɗe su tar akanta ina faɗin"wallahi kar ki so ki ji yadda kaina yake yi mini wani masifaffen ciwo. Ko juya kaina ban so na yi balle wani motsi mai ƙarfi". Ta jinjina kanta cikin kulawa kafin ta furta"Ayya! Sannu Allah ya ba ki sauƙi".

"Amin na gode". Na amsa da shi a taƙaice ina kurɓan kunun da ko kaɗan ba na jin danɗanonsa a bisa harshena. "Amma yau kam ba za ki sama zuwa tasha ba ko? Don na ga jikin nakin ba ƙwari". Na caraf na mata amsa har ina neman ƙwarewa tsabar sauri. "Me zai hana ni zuwa kuwa Amira?. Yanzu ma tashi zan yi na je na shirya na fito mu tafi". Ta kafe da wani kallon da ya fi kama da na al'ajabi don ya zarce a misalta shi da kallon mamaki.

"Ke Amatullah kin san komai sai da lafiya ake yin sa. Mene ne don yau kawai kin zauna a gida kin huta? In kin sama lafiya ai za ki je".

Na katse mata hanzari"ni fa babu abin da zai hana ni zuwa, bari ki ga tabbaci". Ina dasa aya na tashi na É—eba ruwa na shiga banÉ—aki na yi wanka na fito duk tana zaune a wajen na wuce ta na shige É—aki na sako kaya, na fito falo inda na wuce Umma tana zaune.

"Umma na fito zan tafi".

"Zuwa ina kenan?".

Na saci kallonta kafin na ce"wajen talla".

"Har kin ji sauƙi kenan haka da wuri?". Na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa kafin na ce"ban ji sauƙi sosai ba amma duk da haka dai zan iya zuwa". Ta jinjina kanta ba ta amsa mini ba har sai da na cire rai da samun amsa daga gare ta kafin ta ce da ni"Allah ya kiyaye".

"Amin sai na dawo".

Na amsa da shi annuri yana wanzuwa a bisa fuskata tsam na tashi na fita na faÉ—a É—akin su Amira na iske ta har ta shirya tana É—aura É—ankwali. Daga ni har ita babu wanda ya yi wa wani magana na jira ta ta gama muka fito tare tunin almajiran da suke É—auka mana kaya suka yi gaba muka bi su a baya.

"Daga jiya zuwa yau na gaza gane kanki Amatullah".

Na ware idanuna akanta"me ye kuma na yi?" Ta ja dogon numfashi ta fesar kafin ta ce"ke ma kanki kin san kin sauya ba kya buƙatar sai an sanar da ke hakan". Na matse yatsun hannuna waje guda na matse su har sai da suka ba da wani ɗan sauti kafin na sama zarafin cewa.

"Amira ba za ki gane ba wallahi ni ma kaina ban san me ye yake damuna ba. Haka kawai nake ji na a matuƙar takure a cikin gidan indai ba fita na yi ba na taɓa samun kwanciya hankali balle nutsuwar zuciya". "Ina tsoron abin da hakan zai iya jawo miki. Don haka ina mai ba ki shawara tun wuri ki nema wa kanki mafitar da ta dace dake da kuma tsarin rayuwarki".

"Shikenan kuma ni ba ni da Æ´ancin jin daÉ—i ko kasancewa da waÉ—anda za su samar mini da farin ciki a cikin rayuwarta?".

"Amatullah kenan! Lokaci ne kaɗai zai ba ki amsar waɗannan tambayoyin nakin". Ban ce da ita komai daidai lokacin da muka karyo kwanar da za ta sada mu tashar har muka shiga muka zauna a wajen zamanmu ban daina jin ciwon kan ba, sai dai na gwammace da zauna a nan ɗin da na koma gida. Aƙalla mu shafa biye da mintuna arba'in amma ko wulgawar Bashir ban ga ni ba hakan ya sani furta abin da yake ƙunshe cikin raina ga Amira, da hakan ya ƙara jefa ta cikin mamaki.

"Amira kin lura kuwa yau ko wulgawar Bashir babu a cikin tashar nan?".

"To me ye abin mamaki a cikin hakan? Ke ma kanki kin sa direba ne to wataƙila an yi masa lodi ya tafi bai dawo ba". Na jinjina kaina tare da yi wa bakina sakata ba wai don na gamsu da abin da ta ce ba. Haka muka ci gaba da zama duk da azababben ciwon kan da yake ta'azzara na bai gani waige-waige ba ko zan yi tozali da Bashir. Lura da yanayin da na shiga ya sanya Amira soma furucin da ya yi silar jawo hankalina. "Amatullah ba na buƙatar sai kin faɗa min da kalmomin baki yanayinki kawai ya nuna min cewar kin faɗa cikin soyayyar Bashir, sai dai kin yi zurfi da yawa. Tun yanzu har kin fara irin wannan abu to ina kuma idan soyayyar ta yi ƙarfi a cikin zuciyarki. Ina gudun abin da zai je ya dawo".

Ban san dalili sai kawai na ji na fashe da kuka mai matuƙar ƙarfi na kifa kaina da gwiwana ina rure shi da dukkan ƙarfin iyawana. "Na shiga uku! Kuka kuma Amatullah? Me ya faru me ye aka yi miki?".

"Amira ni ma kaina ban san me ye ya faru, kuma zan fi kowa son jin abin da ya faru ɗin. Wallahi ni ma kaina ina ji a jikina cewar na sauya sai dai babu yadda na iya. Zuciyata tana gaya mini cewar ba ni da wani zaɓin da ya wuce na amshi tayin soyayyar Bashir, ko don farin cikina tun da kin ga Umma ba samun lokacinsa take yi ba balle har ta ji damuwar da yake cikin raina".

Ina iya jiyo sautin ajiyar zuciyar da ta sauƙe kafin cikin sanyin murya ta soma cewa"na fahimce ki amma fa dole sai kin iya sarrafa kanki, kar ki bari zuciyarki ta dinga sarrafa maimakon ƙwaƙwalwarki. Ko da ya ke zan yi miki uzuri guda na cewar wannan ne karo na farko da kika fara soyayya". Ban iya cewa da ita komai illa kukan da na ci gaba da shi jikina har yana rawa tsabar kukan ya gama galaitar da ni ban gushe ba na ji ta furta kalmar da ya sani saurin ɗago kaina babu shiri.

"To ai ga can Bashir É—in ma yana zuwa".

Na kafe shi da idanuna da suke tsiyayar da ƙwalla har ya iso wajen. "Subhanallahi!Kuka kuma, me yake faruwa ranki ya daɗe?". Ya watsa mini tambayoyin a rikici yayin da yake ƙoƙarin zama akan bencin da yake kusa da ni.

"Yauwa! Na gode wa Allah da ya kawo ka a wannan lokacin. Tun ɗazu nake yi da ita amma ta ƙi jin lallashi balle lallami, ka ta ga ka kai m sai ka gwada taka sa'ar bari na je na dawo".

"Me ya same ta ne? Za ki tafi ba ki yi min bayani ba". Ta yarfa hannunta alamar ita ma ba ta sani ba, ta ɗauki masar Nasiru ta tafi kai kai masa. "Don ki yi haƙuri ki tsagaita da wannan kukan da kike yi billahillazi ba ki ji yadda nake ji wani abu yana tasowa daga ƙasan ƙirjina yana sukan raina ba. Ki taimaka ki sanar da ni abin da yake damunki". Na kai hannu na share ƙwallar da suka ɓata mini fuska kafin na furta"ba komai". Ya jijjiga kansa alamar bai gamsu ba.

"Kar ki ɓoye duk abin da yake cikin ranki, ni kuma na tabbatar miki da cewa indai bai fi ƙarfina zan magance miki shi". Na kafe da idanuna ko ƙiftawa ba na yi"Bashir ka tabbata inna sanar da kai za ka iya magance mini ita?".

Cike da tabbatarwa ya ce da ni"ƙwarai kuwa matuƙar bai fi ƙarfina ba, indai kuɗi ko ƙarfi suna magani to tabbas zan tsaya miki". Na cije leɓena kana na ce"kulawa nake so". Ya ranƙwafo da kansa saitin fuskana"kin tabbata shi kaɗai kike buƙata, bayan shi ba kya buƙatar komai Amatullah?".

"Ba na buƙatar komai bayan hakan".

Ya yi gyaran mury kafin ya soma cewa"to na yi miki alƙawari ba za ki taɓa yin kuka alhalin kina tare da ni ba. Kuma zan tabbatar da cewa ba ki yi dana sanin amsar soyayyata, ina so ki ba ni dama na nuna miki tsantsan son da nake gwada miki".

Ya ƙare zancen yana marairaice murya tare da lumshe idanunsa yana yi muni wani irin kallon da na ji dukkan jikina ya amsa, da hakan ya tursasa mini sadda kaina ƙasa. Ya saki murmushi kafin ya ce"ki ɗauko kanki ko kuma na ɗago shi na goge miki hawayen da suka ɓata wannan kyakykyawar fuskar". Babu shiri na ɗago kaina ya miƙo mini wani ƙyale da ya zaro daga aljihunsa na amsa na goge fuskata.

Kamar ko yaushe na zuba masa kunun a roba na miƙa masa ya miƙo hannu zai ƙarba, kwatsam ya cafko da ƴatsun hannuna ya riƙe. Jikina ya yi wani irin yarfawa na same hannu babu shiri sai dai da mamakina ko gizau ban ga ya yi ba balle ya ji wani iri kamar yadda ni na ji. Har ya gama shan kunun ya ƙarishe surutunsa na gaza sake jikina, muka yi sallama aka zai je ya dubo ko an gama masa lodi ya dawo. Wani numfashi mai nauyi na fesar daga bakina ina jin ƙirjina ya yi mini wani irin nauyi tamkar an yi min ajiyar dutsi. Kamar daga sama na ji an rumgume ni ta baya tare da faɗin"babbar yarinya, yarinya mai lokaci na yi kewar kasancewa tare da ke". Take jikina ya soma rawa tamkar wacce aka jonawa wutar lantarki na yi ta maza na ƙwace jikina tare da miƙews tsaye duk da rawar da ƙafafuna suke yi da ya taimaka wajen ƙara dahuwar jikina ina jin zafin har cikin jiki da jijiyata.

"Malam lafiyarka kuwa me ye hakan?".

Na yi maganar har yanzu jikina bai bar rawa ba, shi ma da alama mamaki ne ya hana da motsa balle ya ce wani abun illa kallona da yake yi. Sai da ya dafe goshinsa kafin ya ce"ki yi haƙuri don Allah na yi zaton Amira ce, amma ki yi haƙuri".

"Ba komai".

Na amsa da shi a gajarce ina komawa na zauna, amsar da na ba shi ya ƙara gaskata mini abin da Amira take sanar da ni na ce na sauya. Tabbas da da ne sai na ko farcena ya riƙe bisa kuskure sai na yi masa wankin babban bargo tare da tara masa mutane su yi ca a kansa. "Don Allah ke ƴar uwar Amiran ce?" Na tsinkayo muryarsa a karo na biyu na yi masa kallo guda tare da kawar da kaina gefe. "E".

"Ta yi nisa ne?"

"E za ka iya tafiya in sauri kake yi".

Bai ce da ni komai face murmushin da ya saka wanda na gaza gano manufar yin ta. Ya ja bencin ya zauna tare da fito da wayarsa yana latsawa, babu jimawa Amira ta dawo lokacin har na soma tattara mana kaya ina haÉ—a su a wajen guda.

"Mafarki nake yi ko kuma a farke nake? Sayyid kai É—in ne ko kuwa gizo idanuna suke yi min?".

Amira ta yi zancen cikin zallar mamakin da har sai da ya bayyana a cikin kalymanta yayin da take isowa wajen. Ya tashi ya tsaya yana murmushi wanda na lura kamar hakan ɗabi'arsa ce. "Ni ɗin ne dai babbar yarinya, yau da asuba na doro garin". Ta dafe ƙirjinta"na shiga uku! Kai da aka ce an fashi sun tare motaku sun tafi da ku".

"To yanzu dai ai idanunki sun gane miki gaskiya. Ya wannan cikar Æ´ar uwarki ce?". Ta kallo ni kafin ta ce"e ga shi kuma ka zo za mu tafi". Ya É—age kafaÉ—unta"ba matsala gobe za mu haÉ—e. Dole mu magantu da ke".

"Sayyid manyan gari, to shikenan sai gobe za mu haÉ—u". Da haka suka yi sallama almajiran suka yi gaba da kayan yayin da mu ma muka fito. Har mun yi nisa kafin na yi magana.

"Amira me ye haÉ—in ki da wannan mutum?".

"Wa? Wai Sayyid? Abokina ne da harkan azurki ya haÉ—a mu da shi".

"Ki dai yi hankali da shi, har ta rumgume ni ya yi cikin rashin sani wai ya yi zaton ke ce. Hakan ya nuna kenan kuna yin irin hakan a tsakanin ku".

Ta ja tsaya"kar ki gaya min Amatullah. Amma lalle Sayyid ya ƙaro wulaƙanci". Daga haka ta fashe da dariyar da ya ƙular da ni har na kasa cewa da ita komai har muka isa gida, cinikin da na yi na damƙawa Umma na yo alwala na gabatar da salla na ci abinci kana na watso ruwa na soma shirin tafiya islamiyya. Ina ta so na tambayi Umma shin ko Abba ya dawo amma ban ga fuskar hakan ba. Haka na fito duk masallatan unguwan sai da na rage ƙafa inda na iso wajen kon zan ga Abba amma babu shi babu alamarsa. Haka na isa islamiyyar raina duk babu daɗi ina zuwa Malam Aminu ya ce na aji huɗu na yi musu ƙari na je na yi musu na koma ajinmu, sai da muka dawo daga salla kana Malam Suleiman ya shigo ajinmu ya yi mana ƙari tun da muka soma ba mu dakata ba har sai da aka tashi, ya yi mana addu'a kowa ya watse.

Hatta Rauda da Ammi sai da suka fahimci ba na jin daɗi amma na musanta musu na fir na ƙi yarda, haka muka rabu da su kowa ya yi layinsu. Tun da doso ƙofar ɗakinmu nake jiyo tashin muryar Umma har na doso ƙofar ƙirjina bai daina sakan lugudai ba. [10/15, 11:05 AM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_________________________________

Page 2️⃣9️⃣

Gabana ya ci gaba da bugu yana jin wani irin tsananin faɗuwar gaba, sai dai hakan bai hana ni ƙara tunkarar ɗakin ba. Ciki-ciki na yi sallamar da ya tsaya iya kan leɓena yayin da nake zura ƙafafuna cikin falon na tsaya cak yayin da na yi tozali da Abba, Yaya Alhassan da kuma Umar ƴaƴan Anty Sawwama ƴar uwa ɗaya tal ga Abba. "Da ku har mahaifiyar takun da take ikirarin ɗan uwanta ne uban me ye kuke tsinana min?. Ko yaushe kuna sintikin zuwa gidan nan ba za a bar ni na huta a cikin gidana na sakata na wala ba, wacce iriyar bala'i wannan?". Zafafan kalaman Umma kenan da suka fara dira a kunnuwana da ya tilasta mini yin mutuwar tsaye ina kallon su ɗaya bayan ɗaya. "Anty Hafsatu mu fa da ki gan mu ba tashin hankali ba ne ya kawo mu ehe. Ziyara muka zo wajen kawunmu kuma dai ba za ki taɓa raba hanta da jini ba. Ko kin ƙi ko ƙin so shi namu ne muma na sa ne". Umar ya yi zancen yana miƙewa tsaye fuskarta ta yi kici-kici, daman duk ƴaƴan Anty Sawwama babu mai zafin zuciyarsa da saurin fushi.

"Lalle Umar wuyanta ya isa yanka, ba shakka uwar taka ce kenan ta kitsa maka ka zo ka yi min wannan ɗiban albarkan. Manniru kana gani wannan yaron da aka haifa akan idona yana kallon tsabar idona yana gaya min abin da ransa ya ke so amma don mutuwar zuciya irin naka ka gaza taɓuka komai. Allah wadaran naka ya lalace".

Cikin sanyin murya Yaya Alhassan ya amshe zancen cikin faɗin"don Allah Anty Hafsatu ki yi haƙuri, ki hukunta Umar akan duk abin da ya yi miki amma na roƙe ki da kar ki jingina wautar da ya yi da mahaifiyarmu......". Kafin ya rufe bakinsa Umma ta katse shi. "Dalla can rufe min baki kai da shi ɗin me ye bambamcinku? Duk ƙwaryar sama ce take dukan na ƙasa. Don Allah zan ba ku sallahu ku kai wa ita uwar takun ni wargi ce daidai nake da ƙugun ko wani ɗan iska".

"A'a Anty ki dinga sausauta kalamanki don ba za mu jure wani abun ba....". Umar ya yi furucin cin zallar ɓacin ran da ya bayyana har a bisa harshensa, yana rufe bakinsa Yaya Alhassan ya ɗauke sa da mari. "Umar ka yi hauka ne ko kuma wani abun ka sha? Ko manta wacece a tsaye a gabanka da har take faɗa kake mayar mata ita ɗin tsararka ce? Ko me ye za ta yi ta ci daraja da kimar Kawu mana, maza yanzu ka ba ta haƙuri kafin na sassaɓa maka". Dafe kuncinsa Umar ya yi yana wani irin huci ba a kufule ya ce"Anty ki yi haƙuri". Yana dasa aya anan ya fice daga falon fu kamar iska ina da tabbacin ɓacin ran da yake ciki ya makantar da idanunsa daga ganina tsaye a kusa da ƙofar. Sai a lokacin muka haɗa ido da Yaya Alhassan sai dai ya ɗauke idonsa ya yi tamkar bai ganni ba ya ci gaba da maganar daga inda ya ja burki.

"Kawu don Allah ka yi haƙuri ba nufin mu kenan mu zo mu tada maka da hankali ba, mun zo ne don mu sada zumunci mu kuma tattaunawa da ƴar uwarmu Amatullah akan batun sauƙanta da yake gabatowa. Amma ba mu sama ganawa da ita ba". Ya juyo yana kallona kana ya zarce da faɗin"Amatullah don Allah duk wani abun da kike buƙata kar ki yi ƙasa a gwiwa ki garzayo ki sanar da ni, duk wani abun da ake yi wa ko wacce yarinya a irin wannan lokacin zan yi miki shi". Taɓe baki Umma ta yi tana jan wani dogo tsaki mai dogon zango, Abba kam ƙasa ya yi da kansa ya kasa ɗagowa balle ya ce wani abun har Yaya Alhassan ya juya zai tafi.

"Sai ki ƙariso ai ƴar iska tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba alkhairi ba".

Munanan kalaman da Umma ta yaɓa mini kenan da ya tursasa Yaya Alhassan tsaya cak ya kasa gaba ya kasa baya, ya runtse idanunsa cike naman leɓensa alamar ya ji zafi da ɗacin kalaman Umma matuƙa. Ina iya jiyo ajiyar zuciyar da ya saka daidai sa'ilin da yake buɗe idanunsa ya fita na yi wuf na bi bayansa ina ƙiran sunansa cikin kuka da tsananin damuwar da ya sanya ƙirjina yi mini wani irin nauyin gaske. Bai amsa mini ba kamar haka nan bai waigo ba ya ci gaba da tafiyarsa har sai da muka zo zaure kana na yi nasarar shan gabansa. Na haɗe dukkan hannayena waje guda alamar roƙo ina wani irin kuka mai matuƙar ciwo da cin rai, duk yadda na so ce da shi wani abu na gaza samun wannan damar saboda galabaitar da ni da kukan ya yi jikina har rawa yake yi tamkar ana jona mini lantarki.

Babu shiri na durƙushe akan gwiwoyina sakamakon gazawar ƙafafuna ban gushe ba ina yin kukan don a halin da nake ciki shi kaɗai ne abun da nake yi na ji sanyi a raina, bayan ambaton Ubangijina. Na ja dogon numfashi na fesar kafin na sama zarafin faɗin"don Allah kar ka tafi".

Ya tsuguna akan ƙafafunsa a gabana kansa a ƙasa gabaɗaya shi ma jikinsa ya mutu murus. Zan yi magana ya ɗaka mini hannu. "Ba sai kin ce komai ba Amatullah ba ki da laifi kuma ba ki yi mana komai ba. Anty uwa ce a gare mu baki ɗaya dama su iyaye wani lokacin sai ana haɗawa da haƙuri, ko kaɗan ban ji ciwon abin da Anty ta yi ba kuma ke ma ina so ki cire damuwar hakan daga cikin ranki, ki daina wannan kukan laifinmu ne don mun zo ba tare da mun sanar ba".

Na jijjiga kaina alamar ban gamsu da kalamansa ba"ina mai ba ku haƙuri a madadin Ummata. Don Allah ki yi mata uzuri...". Kafin na gama maganar ya ɗaura yatsansa a saman leɓena alamar na yi shuru. "Normal ne fa don haka kar ma ki damu. Yanzu dai alfarman da za ki yi min shi ne ki goge fuskarki ki daina wannan kukan har tsakiyan kaina nake jin sa".

Ya ƙarƙare zancen yana zaro handkerchief ɗaga aljihun farin jamfan da yake jikinsa ya soma goge mini fuskana da shi, na koma sauƙe ajiyar zuciya wani na bin wani tamkar wacce ta yi aikin fasa dutse. Tamkar daga sama muka ji an sheƙa mana ruwan sanyi duk muka yi mutuwar zaune na wucen gadin, sanyin ruwan na ji ya ratsa har jini da jijiyoyin jikina na daskare a wajen na kasa motsa gaɓoɓin jikina illa idanuna da nake sarrafa su daga wannan gefen zuwa wani. Ummi da mahaifiyarta ce tsaye a kanta sun riƙe ƙugu suna jefanmu da wani irin kallo da na gaza gano manufarsa.

"Bayin Allah lafiya? Za ku yi mana wannan aika-aikan?".

Yaya Alhassan ya jefa musu tambayar yayin da yake miƙewa tsaye yana kakkaɓe jikinsa da ruwan ya yi masa lajab. "Ahayye! Yau ina ganin iskanci da wasalinsa. Ai kamata ma ya yi idan ka dawo cikin hankalinka ka yi mana godiya".

Cikin rashin fahimta ya ce"godiya kuma? Na meye kenan?".

"Aw tambaya ma kake yi? To bari ka gani". Take Umman Ummi ta soma kurma shewa kan ka ce kwabo ta tara mana mutanen gidan manyansu da ƙanana suka cika akan mu suna rige-rigen kallon mu tamkar jinjirin watan Ramadana.

"Wai me ye yake faruwa ne?". Baba Habu ya tambaya, Ummi ta yi caraf ta ce"ga su nan kama su muka yi suna aikata baÉ—ala sun fita daga cikin hayyacinsu. Har sai da muka watsa musu ruwa kana suka dawo cikin hayyacinsu". Take wajen ya ruÉ—e da salati da sallallami kowa sai tofa albarkacin bakinsa yake yi ba tare da su ba mu damar cewa komai ba. Cikin tururuwan mutanen ban ga Ummana ba amma Abba kam tun da Ummi ta yi jawabin da ya hargitsa wajen bai ce komai ba, illa dafe kansa da ya yi cikin wani irin yanayin da kalmomin baki sun yi kaÉ—an wajen siffanta su.

"Me kuke jira? Ba za ku taru ku lakaÉ—a musu É—an banzan duka ba".

Na jiyo maganar ta gefen inda nake yashe sai dai na kasa tantance mai muryar, kafin na yi yunƙurin tashi na jiyo muryar Abba a karon farko. "Ku yi haƙuri su ɗin dukkan su ƴaƴana, a ba ni damar ganawa da su kafin yanke ko wani irin hukunci". Aka wani ƙananun maganganu kafin a hankali-hankali aka fara watsewa daga wajen.

"Kawu wallahi wallahi sharri suke yi mana, ba mu aikata abin da suke zarginmu da shi ba. Amatullah Æ´arka ce ka fi kowa sanin irin tarbiyan da ka yi mata ni ma kuma ka san halina, ka san abin da za mu yi iya aikatawa da akasin hakan. Kawu ka yarda da ni sharri ne kawai.....".

Abba ya ɗaga masa hannu alamar ba ya ƙaunar jin komai daga gare sa. "Alhassan ka wuce ka tafi, ina roƙanka da ka ɗauke ƙafarka daga zuwa gidan nan har sai wannan ƙurar ta lafa".

"Kawu don Allah ka saurare ni na yi maka bayani...".

"Alhassan ka wuce ka tafi ka tafi na ce, zan zo gidan na same ka". A tsawace Abba ya yi zancen har sai da zauren ya amsa. Cikin sanyin jiki da na murya Yaya Alhassan ya ce"shikenan Kawu na gode mu kwana lafiya".

"Amin".

Abba ya amsa da shi ciki-ciki bai ko kalle inda nake ba ya juya zai bar wajen, daidai sa'ilin da Amira ta iso tamkar an jefo ta sai da ta matsa kana Abba ya wuce. Ta iso inda nake yashe ta ɗago ni tsaye sai dai na kasa tsayiwa akan ƙafafuna.

"Wai me yake faruwa ne Amatullah? Tun ina wanka nake jiyo tashin hayaniya, na fito kuma na zo na tarar da taron mutane". Na kasa cewa da ita komai illa kukan da nake yi tamkar raina zai fita, ƙafafuna suka fara rawa alamar sun gaji da ɗaukar nauyin sanƙararren gangar jiki da ba shi da maraba da bishiyar da ta baza jijiyoyinta a ƙarƙashin ƙasa. Na kwantar da kaina a saman kafaɗunta saboda jiri da hajijiyan da yake kwasa ta yana ƙoƙarin buga ni da ƙasa. Haka har muka iso cikin ɗakinsu muka yada zango a falo har izuwa lokacin hawaye ba su bar kwaranya daga idanuna ba. Take jikina ya ɗauki zafi gau zazzaɓi mai ƙarfi ya rufe ni babu shiri na soma rawar ɗari tamkar jinjirin kazan da ruwa ya yi masa ɗan banzan duka.

"Don Allah ki yi haƙuri ki daina wannan kukan. Ki nutsu ki yi min bayanin abin da ya faru"

Amira ta yi zancen cikin damuwar da ya bayyana har a kalamanta. Na ja dogon numfashi na fesar daga bakina ina kafe ta da rinannun idanuna da suka sha kuka har suka saduda. "Sharri suke yi mana, wallahi ba mu aikata ba".

"Sharrin kuma? Su waye suka yi muku sharrin kuma ke da waye?".

"Yaya Alhassan".

Ta maimaita sunan kafin ta zarce da faɗin"wani irin sharri? Kuma waye ya yi muku sharrin?". Sai da na cije leɓena saboda takaicin da ya cika mini raina kafin na sama zarafin cewa"Ummi da mahaifiyarta, su yi mana sharrin aikata baɗala ni da Yaya Alhassan. Lamarin da ya fusata Abba matuƙar har ya juya baya a Yaya Alhassan, Amira zuciyata bugawa take yi wallahi". Na ƙare zancen cikin rauni haɗe da ƙara fashewa da wani irin kuka mai cin rai da ruhi, na riƙo hannunta na ɗaura a saman ƙirjina da nufin ta ji yadda yake bugawa fiye da kima a kimiyance. Duk ƙarfin hali irin na Amira sai gabaɗaya jikinta ya yi sanyi ƙalau ta kasa cewa da ni komai balle ta iya furta kalaman rarrashi a gare ni illa kallo na da ido tamkar majigi.

"Amira zan je na yi Abba bayanin duk abin da ya faruwa. Zan je na goge zargin da ya ɗarsu a cikin ransa". Na ƙare zancen tare da yin zumbur zan miƙe ta riƙo hannuna gam. "Kar ki je kar ki je yanzu, ki bari sai ya huce tukunnan kafin ki je masa da kowani bayani". Na girgiza kaina"ba zan iya jira ba don hankalina ba zai taɓa kwanciya ba". Na yi kai aya ina ƙoƙarin fizge hannuna daga riƙon da ta yi mini sai dai ban yi nasarar yin hakan ba.

"Amatullah ki nutsu mana. Ba ki da kalmomin da za ki yi amfani da shi a yanzu wajen fahimtar da Abba ya fahimce ki saboda ransa ya riga da ya ɓaci. Ki yi haƙuri ko zuwa gobe da safe ne sai ki yi masa magana".

Na gaza cewa komai na faɗa jikinta ina ƙara sakin wani kukan mai matuƙar sauti, haka na ci gaba da yi duk lallashin da take yi mini bai yi amfani ba. Har sai da mahaifiyarta ta shigo ta sanya baki haka na lafa ta tashi ta shiga cikin uwar ɗaka ta bar mu. "Yanzu za ki tashi ki je ki kwanta ne ko kuma? Don kin ga Baba Habu yana gari ni zan je gidan Ta salla ne na kwana....".

Na ji caraf na katse ta"daman kina zuwa wani wajen kwana ne?". "Ban taɓa zuwa ko ina ba yau ne dai zan fara. Don ko Umma ba ta fito ta faɗa min ba na lura akwai takura a zaman, na yanke shawarar in dai Baba Habu yana gari zan dinga zuwa kwana sanda baya nan sai na kwana a gida".

"Waye ya ba ki wannan gurguwar shawarar Amira?. Duk wata Æ´a mace fa kwana a cikin gidan mahaifinta ko da kuma filin taku É—aya ne shi ne cikar darajarta".

"Ya kamata ki fahimce ni Amatullah don ke ma a cikin wannan yanayin kike. Ki na gaji dai gidan kowa É—aki ne da falo gare shi, in dan Baba Habu ya dawo shi da Umma suna cikin É—aki ni kuma ina kwanciya a falo amma hakan bai hana ni sauraron duk abin da suke yi kamar a gabana suke aiwatarwa ba, hatta idan suna raya sunna ina ji yi sumbatun da suke yi. To da hakan ya ci gaba da faruwa ai gwara na nemawa kaina mafita ko?".

Kalamanta suka sanya jikin mutuwa murus, tabbas indai zan yi wa zancenta adalci da duba irin na hankali haƙiƙa hukuncin da ta yanke shi ne daidai. "Haka ne kam ki na da gaskiya".

"Ke ma kuma zan so ki bi hanyar da na bi". Murmushin ƙarfin hali kawai na sakar mata kafin na ce"sai Abba ya sauƙo tukunnan, amma kema da kin yi haƙuri yau dai mun kwana tare a nan tun da kin ga halin da nake ciki. Wallahi ba zan iya komawa ɗakinmu alhalin na san Abba yana fushi da ni ba".

"Ba matsala kin san ina son duk abin da zai sanya ka farin ciki ai".

Murmushi kawai na sakar mata, muka yi salla ta kawo mana abinci sai dai na kasa kai koda loma guda cikin bakina haka na kwanta. Raina cike fal da tarin damuwa da fargabar abin da gobe za ta haifar. [10/16, 12:34 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

______________________________________

Page 3️⃣0️⃣

Haka na ji ta juye- juye a bisa shimfiɗan bacci ya gagari idanuna, ya bushe ƙamas kamar soyayyen fikin da aka zuba a cikin mai. Ina jin Amira ta na ta hira da masoyinta Mansur a waya cikin nishaɗi da walwala. Sun daɗe suna wayar har sai da dare ta raba kana suka yi sallama, na juya ina kallon ta duk da duhun da ya mamaye ɗakin na furta"masoya kun yi sallama kenan? Na yi tunanin ai yau soyayyar za ta hana ku bacci". Ta murmusa kafin ta ce"ai ba mu ƙi mu kwana muna wannan wayar ba, wallahi idan ina tare da Mansur ko a waya ne sai na ji duk na manta duk wani damuwar da yake addaban raina. Ina samu nutsuwa sosai daga gare shi".

Na taɓe baki"kuma duk kin san da hakan amma kika kasa sakan kowa ki kama shi. Duk da nutsuwar da kike samu daga gare shi hakan bai hana ki ganin wasu mazan ba har alaƙar soyayya ta gifta a tsakaninku". Ta sauƙe numfashi mai zafin da har sai da na jiyo sautinsa kafin ta sama lasisin faɗin"duk na san da hakan Amatullah amma kin sa komai na rayuwar nan sai ana yi ana lissafi, sama da saurayi ɗaya ai tsautsayi ne babba idan ya juya min baya lokaci guda kuma ya ya zan yi ni ƴasu". "Amira kenan! Ki na raina ikon Ubangiji kenan? Allahn da ya ba ki Mansur a lokacin da ba ki yi tsammani ba shi zai kawo miki wani a lokacin da ba ki yi zato ba. Ki tsarkake zuciyarki kawai ki so mutum guda in sha Allah ba za ki kunyata ba".

"Ki kwanta ki huce gajiyar da kika kwaso wa jikinki Amatullah, don wannan maganar takin ba ta da matsuguni a cikin kwanyanta". Ta yi zancen tana gyaran kwanciyarta, taƙaitaccen murmushi kawai na yi ina sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya mai nauyin gaske. Duk yadda na so baccin ya zo mini lamarin ya gagare ni wai ƙoƙarin cire wando ta kai, haka na ci gaba da juyi ina sauƙe numfaffashi tamkar wacce ta yi aikin fasa dutse. Runtse idanuna na yi da ƙarfin gaske ina karanto ƙarin da Malam Suleiman ya yi mana yau, har aka yi ƙiran assalatu ban runtsa, ladanin yana ƙwala ƙiran sallan farko na tashi na zauna tamkar a daidai ƙofar kunnena ya ƙwala.

Na tashi Amira muka fito muka yi alwala, muka koma muka yi sallan, ina kammala azkar ɗina na miƙe Amira ta bi ni da kallo. "Ina kuma za ki je?".

"Zan je wajen Abba ne. Don wallahi daren jiya ko runtsawa ban iya yi ba tsabar firgicin da zulumin da ya cika mini zuciya". A sanyaye ta ce"to ki dai nutsu kar ki je ki tsaya kuka kawai maimakon bayani. Kuma ki je ki dawo ki same ni don Ummi ba za ta ci banzan ba billahillazi". Ban ce da ita komai ba don na fahimci ko na furta ba za su shiga cikin ƙoƙon kanta ba. Ina fitowa Baba Habu tare da Abba suna shigowa sun dawo daga masallaci, na tsaya a inda nake cak har sai da Abba ya wuce ɗakinmu Baba Habu ma ya nufo ƙofar su kaina a ƙasa na gaishe shi ya amsa tamkar wanda aka yi wa dole tana ɗaure fuskarsa tamau, ajiyar zuciya na sauƙe mai ƙarfi don tun daren jiya na lura tamkar bai so kwanan da na yi tare da Amira ba, kawai dai da yake Umman Amira ta fi shi ƙarfin faɗa a ji ne a zamantakewar su, shi yasa ya saduda.

Tamkar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki haka nake ɗaga ƙafafuna da nake jin su tamkar ba a a jikin gangar jikina, na iso ƙofar ɗakinmu na raba tsakanin haƙwaraina da ƙyar kafin na shiga doka sallama, sai da na yi baki uku ana huɗu na jiyo muryan Abba ya amsa. Haka kawai na tsinci kaina cikina matsanancin faɗuwar gaba yayin da nake shigowa cikin ɗakin, da ya gauraye da hasken rana tocila.

Na zaune a ƙasa zan nesa da shi kaina a ƙasa na gaishe shi fuskarsa babu yabo babu fallasa. Sai da na aro jarumta na yafawa kaina kafin na soma magana cikin sarƙafewar harshe. "Abba wallahi sharri Ummi take yi mana ba mu aikata abin da suke zargin mu ba da Yaya Alhassan. Hasalima na bi shi waje ne don na ba shi haƙuri akan abin da ya faru, shi ne ya zaro handkerchief daga ajihunsa......". Ya ɗaga mini hannu alamar na dakata.

"Ni ma na san ba ku aikata ba Amatullah, tun kafin a haife ki na san wane ne Alhassan na kuma san ɗabi'u da halayansa baki ɗaya. Amma dole ya janye ƙafafunsa daga zuwa gidan nan na ɗan wani lokaci ko da kuwa wannan abun bai faru ba ma, ko don rashin fahimtan da suka samu da mahaifiyarki". Na ja jikina na iso gabansa na haɗe hannayena waje guda alamar roƙo ina cewa"Abba ka yafe mini na san jinya ka kwana da ɓacin raina a cikin zuciyarka, wannan dalilin ne ya sa na kwana a ɗakin su Amira don ba zan iya fuskantan ka a irin wannan yanayin ba".

"Uwata ba ki yi min komai ba da har za ki nema gafarana, kuma ban kwana da baƙin cikinki ko takaicinki a cikin raina ba. Babban damuwata ma shi ne yadda ran Ummanki ya yi maƙurar ɓaci". Jikina gabaɗaya ya yi luƙus jin abin da Abba ya furta na zame na yi zaman dirshan ina ci gaba da sauraron jawabin da ya ɗaura da shi.

"Allah ya jarabce ni akan mahaifiyarki har cikin raina na tsani duk wani abun da zai sosa mata rai. Na ƙi jinin duk wanda zai tsaya a gabanta ya yi furucin da zai baƙanta mata rai ko wane ne shi, kuma komai girman alaƙar dake tsakanin mu da shi zan iya yanke alaƙa da shi".

Na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya kafin a sanyaye na ce"in sha Allah komai zai wuce Abba, amma su Yaya Alhassan kam ai ni da su mun zama abu guda a gare ka. Idan har zuciyarka za ta iya yafe mini to tabbas su ma sun cancanci hakan". Ya yi hanzarin taran numfashina"akwai bambanci ke a ni kika yi wa laifi yayin da su kuma ran Hafsatu suka baƙanta. Zan iya yafe duk girman laifi amma ban da wannan". Ban iya cewa komai ba saboda zallar ruwan mamakin da zantukansa suka shayar da ni, na tashi na fito na soma shara ina jin ciki tamkar an yi yasa don rabo na da abinci tun jiya da rana.

Sai da na gama na hura wuta na ɗaura girki ina kammalawa na ɗeba nawa na ci a wajen kana na shigarwa Abba na sa ciki. Kamar ƙaramin yaro haka ya ke cin abincin hannu baka hannu ƙwarya na yi sakeke ina kallon sa raina cike da tarin tausayinsa don na tabbatar shi ma rabon sa da abinci tun jiya, hawaye suka zubo daga idanuna na yi hanzarin kawar da su.

"Uwata tunanin me ye kike yi haka kin yi shuru?".

"Babu komai Abba, Umma ba ta tashi ba ne?".

"Ba ta tashi ba, amma Uwata tabbas akwai wani abun da yake damunki. Ki saki jikinki ki sanar da ni ko mene ne, shin ki na da wanda ya kai ni ne a gare ki?". Na jijjiga kaina cikin sanyin jiki da hakan ya ba shi damar ci gaba da cewa"to mene ne haka a ranki kike wannan dogon tunanin?".

"Abba ina so na roƙi wani alfarma ne a wajen ka". Ya kai lomar da ya ɗauko kafin ya ce"faɗi kanki tsaye in har ina da halin yi miki to ki sa a ranki kin riga da kin samu". Na ɗan ji jim kafin na ce"daman akwai wani gida ne a nan bayan layin, matar mijinta ya rasu daga ita sai ƴaƴanta biyu kuma duk samari ne ba sa zaman gidan. Shi ne Amira za ta na zuwa gidan ta na kwana saboda Baba Habu ya dawo, zaman cikin da falon akwai takura".

Ya kare ni kafin na isa inda nake son tsayawa"yanzu dai me ke kike so?". Na sadda kaina ƙasa kafin na sama zarafin ci gaba da cewa"shi ne nake roƙan alfarma a wajenka inda ka amince sai na dinga bin ta muna zuwa can muna kwana tare". Ya yi shuru kamar bai ji ni ba hakan ya ƙara sanyaya mini dukkan jikina, bai amsa mini ba ya ci gaba da cin abincinsa har sai da ya gama cin abincin tas ya kwance hannunsa ya yi hamdala bayan ya ɗaura da ruwan da na kawo masa. Na tashi na tattare kwanukan na fitar wajen na wanke su kana na ɗaura ruwan zafin dama kunu, na koma ciki da nufin duba ko Umma ta tashi har yanzu Abba yana nan zaune a inda na bar shi bai ko motsa ba.

Na yi masa sannu ya amsa zan shige ya ƙira sunana na dawo na tsuguna a gabansa. Ya kafe ni da ido yana faɗin"na yi nazarin maganar da kika faɗa na duba na ga dacewar hakan, sai dai wani gida ne za ku na zuwa kwanan?". Na yi caraf na ce"nan ne gidan Ta salla matar marigayi Alhaji Bashiru mai kwanuka". Ya yi ɗan jim kamar mai nazarin wani abun kafin can ya ce"shikenan za mu magana da Ummanki, Allah ya sa ta yarda don in ba ta yarda ba. Ba zan yi mata dole ba, zan kuma yi bincike akan gidan ita Ta sallan".

A sanyaye na ce"na gode Allah ya ƙara girma". Kafin ya kai ga amsawa Umma ta fito tsam Abba ya miƙe zai je gare ta, ta buga masa wani uban hararan da ya tsaya sa tsayawa cak har sai da ta iso ta zauna kana shi ma ya koma mazauninsa ya zauna, yana yi mata sannu da fitowan da ko amsa masa ba ta yi ba. Na gaishe ta ta amsa fuskarta babu yabo babu fallasa.

"Ranki ya daɗe daman wata alfarma muke nema a wajen ki". Abba ya yi zancen cikin matuƙar ƙanƙan da kai da girmamawa. "Ina jin ka". Umma ta amsa da shi cikin isa da gadaran da ya haɗe da tsantsan izza.

"Daman ɗiyarki ce ta zo da wani batun da na yi na'am da shi, ta ce tana so su na zuwa gidan Ta salla suna kwana tare da Amira saboda yanayin ɗakunan namun. Ga shi kuma kullum yaran ƙara girma suke yi akwai abubuwan da bai dace sun ji ko suna gani ba, gare ni kam babu matsala na yarda sai dai duk yadda kika ce haka za a yi ranki ya daɗe".

Ta yi banza da shi na tsawon wasu mintuna da har sai da na ji daman ban zo masa da zancen ba, wataƙila da ban ja masa wannan abun ba. Sai da muka cire rai da samun amsarta kana ta buɗe baki ta yi magana.

"Ka san ƴar uwarka ma ta zo da makamancin wannan zancen amma ban amince ba. Duk da ba na son abin da zai sa Amatullah ta yi nisa da ni amma ina ji zan iya amincewa da wannan ko don na nunawa ƴar uwarka cewar na isa da gidan aurena kuma ina da ƙarfin gwiwan juya komai". Cikin sanyin jiki da na murya Abba ya ce"yanzu dai ki na nufin kin amince kenan?".

"Na amince".

"To muna godiya sosai ranki ya daɗe. Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai amfani, Allah ya bar mana ke ki yi tsawon rai ki yi shekaru irin na dabino". Abba ya yi kalaman tamkar zai yi mata sujjada tsabar ƙanƙan da kai da biyayya. Ni ma godiya na gabatar mata ta ce na je na dama kunun don yau ba ta jin daɗin jikinta.

Na fito waje na ja kujera na zauna na zabga tagumi, ban yi aune ba na yi an watsa mini ruwa a fuskana. Ko gizau ban yi ba don na san babu wanda zai yi mini hakan face Amira. Ta ja kujera ta zauna kusa da ni tana faɗin"me ye kuma ya faru kika zo kika zabga tagumi haka?". Na ƙi na kula ta amma hakan bai hana ta ci gaba da faɗin abin da yake ranta ba. "Ya ya kuka yi da Abban?". Na zame hannuwana kafin na kwashe duk yadda muka yi na sanar da ita hatta da maganan zuwa na kwana gidan Ta salla da muka yi, ta yi ta murna tana zantuka cikin jin daɗi. Haka na dama kunun na gama komai na kashe wutar ina wanke tukunyar Ummi ta fito daga ɗakinsu ta ci kwalliya tana zaunar chew gum ƙas ƙas. Amira ta yi wuf ta sha gabanta.

"To tauraruwa mai wutsiya dilallalan sharri ke da uwarki. Kun yi tunanin kun yi mata sharri kun ci banza kenan ko? To wallahi bashi kuka ɗauka sai na nuna muku bambamcin dake tsakanin ruwa da wuta, sai na haɗa miƙa gurmin da duk danginku ba za su iya kawo ƙarshensa ba. Sai kin zubar da hawaye kin yi kuka fiye da yadda Amatullah ta yi".

"Ahayye nanaye. Har da su kaza a cin danƙo? Ai ko giwa ta faɗi ta fi ƙarfin kiyashi su ja ba. Sanin kanki ne ni Ummi na yi muku nisan da har a naɗe duniya ba za ku iya iske ni ba". Amira ta bushe da dariya har da tafa hannu kana ta furta"to ina abin yake wai maye ya ci jajiri, ai ke ma kin san cewa ruwa ba sa'an kwando ba ne. Kuma ko da girgiza kurna ta fi magarya zaƙi, Ummi ga fili ga mai doki mu zuba ni dake sai mu ga wanda zai kwashe. Haka za ki ƙare da saurayi guda ɗaya mai jaraban nacin tsiya babu ko sisi a aljihunsa don lalacewa ma kwanon abincin safensa, rana da dare duk yana gidanku. Ban da rashin sanin ciwon kai". Da alama maganar ya yi matuƙar girgiza zuciyar Ummi don sai ta gaza cewa komai illa cizon ƴatsan da take yi cikin takaici. Ganin mutane sun fara fitowa daga ɗakunansu ya sani tashi na je na janye Amira ina ba ta haƙuri sai ba ta fasa zazzago zancen ba har sai da Ummi ta fice.

"Ban san yaushe za ki dinga É—aukar abubuwa a hankali ba Amira. Yanzu dai ki je ki shirya ki zo mu tafi". Harara ta banka mini ta yi shigewarta É—akinsu ta bar ni tsaye. Sai da na gama duk abin da nake yi na shiga ciki na tambayi Umma ko za a kawo mata abinci ta ce ba yanzu ba don haka na shiga É—aki don na ga alamar kamar akwai abin da suke tattaunawa.

"Hafsatu ki yi wa Allah ki yi Manzon da ya karɓo mana sallalo biyar da muke yi a yini. Ki cece ni sau sausauta wannan hukuncin da kika yanke ya yi min tsauri, Maman Umar kamar uwa take a gare ni kuma ta yi ɗawainiyya da ni da tun ina yaro, ta sadaukar da abubuwa da yawa da suke mallakinta domin ji daɗina. Ta kan iya kana cikinta abinci ta ɗauka ta ba ni tana son duk wani abun da nake so ko da kuwa ita a ranta bai yi mata ba. Ta kan saurare ni ta ji damuwata kuma ta magance min ita, ba taɓa zuwa wajen da wani buƙatar da ta gaza biya min ita ba. Ta ya ya kike tunanin zan iya kallon tsabar idonta na ce da ita kar ta sake zuwa gidana don matata ba ta buƙatarta?". Daidai lokacin da nake shiga cikin ɗakin na ji zancen Abba ya sauƙa a kunnena, na shiga daga jiki na tsaya a jikin labule ina ci gaba da saurara don ba kaɗan ba zancen ya ja hankalina.

"Ai kuwa sai dai ka zaɓa ko ni ita Maman Umar ɗin. Don duk ranar da ta ƙara zuwa cikin gidan nan, to ka ƙaddara a ranka cewar a ranar a gidanmu zan kwana".

A raunane tamkar mai shirin yin kuka na jiyo muryan Abba yana cewa"kin san ko da wani mahaluki aka haɗa aka ce na zama ke zan zaɓa Hafsatu akan kowa da komai. Amma ki dubi girman Allah ki janye wannan ƙudurin nakin, na yi imanin wannan abun da ya faru ma zai sa ta taƙaita zuwan da take yi ba sai na je mata da wannan zancen ba".

"Manniru idan ba za ka iya ba ni ba, ni ka ba ni iznin na wanke ƙafafuna na je na iske ta har gida na sanar da ita". Da hanzari Abba ya furta"A'a ba sai kin je ba zan je da kaina na sanar da ita". Sulalewa na yi zuwa ƙasa na durƙushe akan gwiwoyina ina kuka marar sauti, jin motsin za a shigo ya sani na yi wuf na tashi na ɗauko kayana na fito banɗaki na shiga na yo wanka na saka kayan da na shiga da su. Don tun ranar da Baban Vector ya bankaɗo ƙofar banɗakin Ina wanka na fara shiga da kayana inna gama wankan sai na saka su na fito abin na tsaf.

Sanda na fito na iske Abba har ya fita na shirya, na yi wa Umma sallama na fito na tarar Amira har ta shirya ni kawai take jira. A zaure muka tarar da Ummi da Auwal suna zancen muka wuce su bayan Amira ta buga musu wani uban tsaki tamkar ta ga kashi. Har muka bar cikin layinmu ban ce komai hakan ya sanya Amira cewa"ke kuma lafiyarki Madam?".

Na ja dogon numfashi na fesar kafin na ce"Amira a iya sani na a bisa addini da al'adarmu na Malam Bahaushe mace ita take yi wa mijinta biyayya. Bai dace ta É—aga murya ga mijinta ba amma gabaÉ—aya Umma ba haka take ba. Yanzu Abba har shakkan ta yake yi idan zai yi mata magana har jikinsa ruwa yake yi".

"To ke me ye matsalarki da hakan?".

Na yi mata wani kallo"a ganinki hakan ya dace ne Amira?". "Ko mai dace ba to ke ina ruwanki da rayuwar da suke yi a tsakanin su? Ke yanzu babu dama mace ta zauna da mijinta lafiya sai ki yi wani tunani na daban Amatullah. Ai so da ƙauna gami da zaman lafiya shi yake kawo hakan in ba ki sani ba na gaya miki". Ban kuma cewa da ita komai har muka isa tashan duk da kuwa yadda ta yi ta ja na da hira, ranar Bashir ma bai sama kaina ba muna barin tashan na ce Amira ta raka ni gidan Anty Sawwama ta ce kar na je yanzu na bari abubuwa su lafa tukunnan. Ta shawarce ni akan ko zan je to gwara na je wajen aikin Yaya Alhassan na same shi mu yi magana, na amince da hakan.

Kamar yadda na yi zato ban sama Umma a gida ba Amira ta kawo mana abinci muka ci kana na soma shirin tafiya islamiyya, don so nake yi kafin na wuce na tsaya a wajen aikin Yaya Alhassan duk da hanyar ba ɗaya ba ne. [10/18, 1:53 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

__________________________________

Page 3️⃣1️⃣

Ban É—au lokaci ba na isa wajen aikin Yaya Alhassan na gyaran shinkafa, na tsaya a waje ina ta hange-hange kafin can na hango wani saurayi yana fitowa daga cikin wajen na yi hanzari na isa gare sa bakina É—auke da sallama. Ya amsa yana kafe ni da idanuna. "Don Allah wani taimako nake nema". "Ina jinki".

"Ina so ayi mini magana da wani ne a ciki, sunansa Alhassan". Ya yi ƙuri yana kallona kafin can ya furta"a wani sashi yake aiki? Kin san akwai ɓangaren masu zuba ita shimkafan a buhu akwai masu ɗinke bugun sannan akwai masu lissafi". Na yi shuru ina cizon ɗan ƴatsa, kafin na kai ga furta wani abun ya katse mini hanzari. "Mu je ciki sai na saka a duba miki shi. Amma me ye haɗin ki da shi Alhassan ɗin?".

"Yayana ne". Ya jinjina kansa yayin da ya yi gaba ina bin sa a baya muka bi ta wani ƙaramin ƙofa mun ɗan yi tafiya mai nisa kafin na tsaya saboda ganin wajen shuru babu gilmawar mutane. "Malam wai ina za mu je ne?". "Ina kike tunani?". Na yi zancen yana riƙo gefen hijabina na fizge ina nuna sa da ƴar manuniyar ƴatsata. "Kar ka sake ka yi kuskuren taɓa jikina, don ina mai tabbatar maka da cewar hakan da za ka yi shi ne kuskure mafi girma da za ka yi a rayuwarka".

Da mamakina sai na ga ya fashe da dariya yana ƙara matso ni. Na sa dukkan ƙarfina na hankaɗe sa ya faɗi sai dai kafin na yi wani yunƙuri tunin ya tashi ya finciko ni ya ɗaga hannu da nufin zabga mini mari. Na yi saurin runtse idanuna cike da tsoro ina jira na ji ta wani ɓangare zai sauƙe mini marin, jin shurun da na yi na sanya ni buɗe idona a hankali. Tagwayen ajiyar zuciya na sauƙe bisa ganin Yaya Alhassan da na yi tsaye a wajen ya riƙe hannun mutumin da ya ɗaga da nufin zuba mini mari. "Halilu ashe har yanzu ba ka sauya wannan halin nakan ba?. Ina maka nasiha da ka tun kafin lokaci ya ƙure mata ka sauya zuwa mutumin kirki wanda iyaye da al'umma za su yi alfahari da shi".

Yana gama faɗin hakan ya sakar masa hannunsa, cikin rawar jikin da borin kunya mutumin ya bar wajen tana ta muzurai tamkar wanda ya yi wa sarki ƙarya. "Amatullah me ye ya kawo ki wajen nan?".

"Wajen ka na zo Yaya Alhassan". Ya murtuƙe fuskarsa tamkar bai taɓa yin dariya ba"me ye kawo ki? Me ye da ba za ki iya zuwa gida ki same ni ba. Yanzu da ya yi galaba akan ki fa, ki wuce ki tafi islamiyyarki in kun tashi zan zo na same ki a can".

"Don Allah Yaya Alhassan ko minti biyu ne ka ba ni, ka saurari abin da na zo da shi".

"Ki wuce ki tafi". Cikin tsare gida ya yi zancen da hakan ya hana ni cewa komai haka na wuce na tafi har na isa islamiyyar ina ji na wani iri, ina shiga aji na kifa kaina akan benci ina kuka marar sauti ban gushe ina yi ba har sai da Malam Suleiman ya shigo ajinmu kana na ɗago kaina fuskana ya kumbura ya ya tsimtim yayin da idanuna suka yi ƙulu-ƙulu tamkar za su faɗo ƙasa.

Har aka fito salla jikina gabaɗaya babu ƙwari tamkar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki. Ko tambayoyin da Rauda da Ammi suke haɗe suna yi mini ban amsa musu ko guda ba ko da suka matsa mini cewa na yi da su ba ni da lafiya ba, dole suka rabu da ni bayan sun yi mini addu'ar samun sauƙi. Tun kafin mu fito daga cikin aji na hango Al'amin da alama ni yake jira haka kawai na ji raina yana ɓaci ba tare da wani dalili ba. Ko da aka shafa fatiha mun tattaunawa sosai akan walimar sauƙarmu da yanzu ya rage saura kwanaki ashirin cif, an tsara komai yadda zai gudana domin abubuwa su tafi yadda ake so a kuma fita kunyar baƙin da aka gayyata.

Muna fitowa daga ajin na yi wa su Rauda sallama na ɗauki hanyar har na yi nisa na ji ana ƙiran sunana. Ya tsaya ina dafe goshina don muryar Aliyu ce, ban motsa ba har iso gabana. "Saurin me ye kike yi haka? Tun da kuka fito nake ƙiran sunanki amma ba ki waigo ba".

"Aliyu yau ba na jin daɗi ne so nake yi na tafi gida da wuri". Cike da kulawa ya furta"Ayya! Sannu ai ban sani ba da ban tsayar da ke ba. To amma don Allah ina neman alfarma ina son gobe idan kin shigo akwai maganan da za mu yi da ke". "To ba matsala sai goben". Na furta ina barin wajen ba tare da na jira abin da zai ce ba. Ina shawo kwanan layinmu na hango Yaya Alhassan akan mashin ɗinsa yana zaune yana latsa wayar hannunsa. Na ƙara sautin da nake yi na isa gare shi bakina ɗauke da sallama sai dai duk jikina ya bi ya yi sanyi ganin yanayin da ya amsa mini sallamar fuskarsa babu walwala balle annuri. "Sai yanzu aka tashe ku?". Na yi ƙasa da kaina"mun tsaya mun tattaunawa akan walimarmu ne shi yasa na ɗau lokaci". Ya jinjina kansa yana kallo ya furta"gani kin ce za mu yi magana".

Kunya gabaɗaya ta yi mini dabaibayi na yi ƙasa da kaina"daman na je na ba ka haƙuri ne akan abin da ya faru". Ya ɗaga mini hannu alamar na dakata. Ya cira kai yana kallo na tare da faɗin"ba ki yi min komai abin da ya faru kuma ai ƙaddara ce wacce ba ta wuce rana da sa'ilin ta. Don haka ki ma manta da abin da ya riga ya faru, damuwata ma shi ne kar hakan ya sa Abba ya yi fushi da mu".

"Abba bai yi fushi ba. Don ya fahimci mu sosai kuma ya yi imanin cewar ba za mu aikata abin da suke zarginmu da shi ba". Ya yi ɗan jim kafin can ya ce"amma gaskiya mutanen nan sun ba ni matuƙar tsoro. Na sha jin ana cewa ka guji sharrin mace ai ranar na ga zahirinta". "Yaya Alhassan sharri ai dodo ne mai shi ya kan ci". Ya jinjina kansa cike da gamsuwa"haka ne kam. Yanzu dai ya batun sauƙan nakun me da me ake buƙata".

Na lissafa masa komai da komai da za mu yi. Bai ce komai har sai da na gama lissafin ya É—ago ido ya kalle ni"shikenan ko akwai sauran wasu abubuwan?". Na waro idanuna"kai! Yaya Alhassan to waÉ—annan É—in ma da na lissafo ba dole sai na yi su dukka ba. Hijabi daman Umma ta ce za ta yi mini ko atamfar ma ka yi mini wallahi ta isa".

"Ko atamfar ma ka yi mini wallahi ta isa". Ya kwaikwayi muryata da hakan ya sani murmusawa ina rufe fuskana. "Duk abin da kika lissafa da ma wanda ba ki saka su cikin lissafin duk sai na yi miki su Amatullah. Gobe idan kin taso daga islamiyyar ki bi ta wajen Anty Zulaihatu zan ajiye miki a can sai ki karɓa".

Na turo baki ina furta"kar ka ɗaurawa kanka nauyi da yawa fa". "Ke ɗin ce za ki zama min nauyi? To ashe in haka ne ni ma wataran zan gaji da ɗaukar nauyin kaina da kaina. Amatullah ke ƴar uwata ce kuma ba zan gaji da yi miki ɗawainiyya ba har abada, yanzu dai ki wuce gida magriba ta kusa". Godiya na gabatar masa sosai kana muka yi sallama ya wuce yayin da ni kuma na ƙariso gida, ina shigowa ana ƙiran sallan magriba don haka sai da na yi alwala kana na shiga ciki na yi salla, na sauya kaya na fito na haɗa wuta na ɗaura girki. Ina girkin ina biya karatun da aka yi mana haka Amira ta zo ta iske ni har sai na kai ayan da na ɗauko kana na kallo ta tare da cewa"yau ba za ki ke tallan taren ba ne?".

Ta dafe ƙirji"ni jikar mutum huɗu rufa min asiri. Ai wataƙila in dai ba wani ikon Allahn ba kuma na daina tuya awarar dare".

"Me yasa?".

"Mansur ya ce ba ya so iya na safen da nake zuwa na ya isa. Ya ce na yi masa lissafin abin da nake samu a toyar awarar a kullum zai na ba ni, kin ga kuwa ai kakata ta yanke saƙa".

Na tallafe kuncina ina kallon ta"to Allah ya saka masa. Amma ni kam da wannan kashe miki kuÉ—in da yake yi É—in nan ai gwara ya fito ayi maganar aurenku. Tun da dai alhamdulillah yana da rufin aisirinsa daidai gwargwado".

"Yana so sai ya gama gininsa ne kana ya zo gida. Yau ma zai zo mu haɗe a gidan Tasallah za mu fi sakewa a can, kin san gidan nan da tsegumi da sa ido shi yasa duk nacin son zuwa hirar dare irin na Mansur na shata masa layi, ban isa ayi min sakiyar da babu ruwa ba, yadda ƴan matan gidan nan suka ƙware wajen ƙwacen saurayi ban isa ba. Don tabbas idan Mansur ya juya min baya ko ban bar duniya ba sai na zama marar amfani ta yadda ba zan iya amfanin kaina ba balle wani".

"To ya dai kamata iyaye su shiga cikin zancen gaskiya". "Kar ki damu in Sha Allah ban da wani na mijin da ya wuce Mansur a duniya da lahira". Na bushe da dariya kafin na yi magana Abba ya shigo muka haÉ—e baki wajen amsa sallamar da ya shigo da ita, muka yi masa sannu da zuwa ya amsa ba tare da ko kalle inda muke ba.

"Wai har an yi isha'i?".

Amira ta tambaya, na gyaÉ—a kaina"ga shi kuwa tun da kika ga Abba ya shigo". "Bari na yi je na yi salla kafin kin gama girki sai mu tafi".

"Wallahi Amirka yanzu kuma sai na ji gabaɗaya hankalina bai kwanta da zuwa gidan Tasallan nan ba, ina jin kamar ƙaddarar faruwar wani mummunan abu ne zai kai ni".

Ta dafo kafaɗata cikin son kwanta mini da hankali ta soma cewa". Amatullah ki haƙurƙantar da zuciyarki daga ni har ke ba mu da yadda muka yi iya shi yasa. Kina ganin dai irin rayuwar takurar da muke yi muka iyayenmu duk muna rayuwa ne a ɗaki guda, dole za ta sa mu zuwa ba wai don son ranmu ba". Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya kafin na furta"haka ne Amira to Allah ya kawo mana mafita cikin sauri".

"Amin ya Allah".

Ta amsa da shi tana tashi ta koma É—akinsu. Ina gama girkin na zubawa Abba na shi na kai masa ciki na ajiye masa a gabansa na fito na ci na wa a waje, na san Umma yanzu sai ta yi niyya take cin abinci don haka na juye ragowar a cikin kula. Na É—auro alwala na shigo ciki har yanzu Abba yana nan inda na bar shi da alama ko buÉ—e abinci bai yi ba balle ya ci. Na tsuguna a gabansa ina faÉ—in"Abba lafiya kuwa ka zauna ka yi shuru? Ko dai akwai wani abun ne?".

Ya saki sakakkiyar ajiyar zuciyar da har sai da na ji sautin ta kafin ya soma magana. "Na daÉ—e ban shiga cikin matsanancin tashin hankali irin na yau ba, na daÉ—e ban ga Maman Umar cikin irin yanayin da na gan ta a yau ba. Tun muna yara mace ce mai fara'a da sakin fuska mace ce mai son nata akan komai da kuma son É—abbaka zumunci. Amma yau a dalilina har hawaye sai ya taro a idanunta Amatullah".

Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau" Abba wani abun ne ya faru tsakanin ku?". Ya goge zuffa da ta taru masa a saman goshi kafin ya ce"na je na sanar da ita saƙon mahaifiyarki na cewa ba ta son ci gaba da ganin ta a cikin gidan nan. Haƙiƙa lamarin ya jijjiga ta amma sai dai ba ta bar ni na fahimta. Ba ta ce da ni komai ba illa fatan ɗaurewan lafiya da ta yi a gare mu, ta kuma ƙara da cewar idan har hakan zai samar mana da kwanciyar hankali babu matsala don tana maraba da duk abin da zai haifar da zaman lafiya a tsakaninmu".

Lokaci guda na daskare a wajen ina jin kamar ana ɗauɗare mini dukkan gaɓoɓina. Ban yi zaton Abba zai iya zuwa ya sanar da Anty Sawwama wannan lamarin kai tsaye haka ba. Ban yi aune ba na ji hawaye sun ciko mini koramar idanuna. A raunane na ce"Allah ya daidaita tsakanin ku".

Ya amsa da amin yana É—aurawa da"yau za ka fara tafiya gidan kwanan ko?". Na gyaÉ—a kaina da hakan ya ba shi damar ci gaba da maganar.

"Nasiha ɗaya zan yi miki shi ne ki ji tsoron Allah Amatullah. Ki sani cewa duk in da kike da duk abin da kike aikatawa Allah yana kallonki ko da kuwa mu kin ɓoye mana, ki kiyaye mutumci da kimarki a duk kika tsinci kanki sannan tarbiyyarki ta bayyana a cikin aikinki, Allah ya kiyaye ki ya kuma tsare ki da tsarewar sa a duk inda kika kasance".

"Amin ya Allah. Abba in Sha Allah ba zan ba ka kunya ba".

"Allah ya miki albarka". Na amsa da amin ina tashi na shiga cikin ɗakin na tarar da Umma tana bacci na yi sakeke ina kallonta don ina da tabbacin ko sallan magrib ba ta yi ba balle isha'i. Kayana na ɗauka na fito na shiga wanka na dawo na tarar a lokacin ta tashi muka yi sallama da ita na fito. Na tarar da Amira ma ni take jira tun da muka fito take waya da Mansur tana yi masa kwantacen gidan Tasallan har muka isa. Kamar yadda na yi zato haka muka iske ƙofar gidan cike da masu jaura muka kutsa kai zuwa cikin gidan, inda muka iske Tasalla zaune a bisa tabarma ta ba za hajarta a gaban ta, muka isa muka zauna a kusa da ita bayan mun gaishe ta Amira ta yi mata bayanin komai.

Ta riƙe haɓa"tirƙashi! Ga shi kuma yanzu babu ɗaki duk da mutane a cikin sa, daman na yi tunanin zuwan nakun zai kai gobe ne hala ko jibi don zuwa lokacin akwai wacce za ta tashi".

"To Hajiya yanzu ya ya za a yi ke nan? Ko za mu je kawai sai goben to?".

"A'a bari na ƙira Ƴar gold na ji ko kwana za ta yi a can inda ta je ɗin, in kwana za ta yi sai ku yi amfani da ɗakin kafin na gyara muku waje zama" Tana ƙare zancen ta ɗaga waya ta shiga latsawa, ba ma ji abin da ake faɗa daga ɗayan ɓangaren mun dai ji sai amsawa take yi da to to har ta zare wayar daga kunnenta.

"Za ku iya amfani da ɗakinta don ita ta yi nisan zango, dawowanta sai wani sati ta tafi can ƙauyen su saboda batun auren da ya taso. Sai ki tashi mu je ka ga can ɗakin sai na kai ku". Haka kuwa aka yi ta tashi ta kai mu har ɗakin kuma ta sa aka sayo mana maganin sauro ta kunna mana, muna zaune wayar Amira ta yi ruri ta kalle ni"tashi mu je Mansur ne ya iso".

"Sai dai ki je ki don babu inda zan iya zuwa yanzu". Ba takura mini ba ta tashi ta fita bayan ta buɗe wayarta ta bar mini ita da nufin ta ɗebe mini kewa. Mahanjar shafukan alƙur'ani na shiga na soma karantun. Sai ƙarfe sha ɗaya Amira ta shigo na galla mata harara ina faɗin"na yi tunanin ai a can za ki kwana".

"Har kin fusata kenan? Yanzu dai bari na yi je na yi fitsari na zo na ba ki labari". Ban kula ta ba illa lasje wutar É—akin da na yi na ja bargo na yi kwanciyata a bisa katifar. Tamkar daga sama na ji an yaye bargo na yi zumbur na tashi ina lalumar inda na ajiye wayar Amira don na kunna haske na ga an dalle mini idanuna da haske tocila. "Watau aure za ki yi ki bar ni ko? Kin sama wanda ya fi ni shi ne za ki juya min baya. To billahillazi ba ki isa duk gyaran da kika yi sai na buÉ—e ki sai dai a kai ki gidan nasan a haka".

Take jikina ya soma rawa na fara kuka ina masa magiya, cak numfashina ya tsaya bayan da na jin ƙarar rufe ƙofa da hakan ya yi daidai da lokacin da aka kashe tocilar. "Wallahi ba ita ba ce don girman Allah ka yi mini rai kar ka cutar da ni....". Ban ƙarisa maganar ba na yi an sa wani abu mai kauri an ƙulle mini bakina da hakan ya hana sautina fita, na sanƙare lokacin da na ji yana ƙoƙarin raba ni da kayan jikina, na so kai masa duka, yakushi da cizo ya falla mini marin da sai da na ji bakina ya cika da ruwa wanda nake kyautata zaton jini ne, ya hankaɗe ni gefe guda kaina ya bugu da ginin ɗakina. Da wani irin ƙarfi na ji ya yage rigar jikina na yi saurin kai hannu na rufe ƙirjina, ina ƙoƙarin tashi ya jawo ni, tun daga lokacin ban ƙara sanin inda kaina yake ba saboda zafin buguwan da na ji da ya ratsa har tsakiyar ƙoƙon kaina.

[10/19, 3:30 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

___________________________________________

Page 3️⃣2️⃣

Tun daga lokacin ban ƙara sanin inda kaina yake ba, numfashina ya ɗauke na wucen gadi na gaza motsa ko da ƴatsan hannuna balle sarrafa sauran gaɓoɓin jikina. A hankali na soma buɗe idona da suka yi mini nauyi wasu hawaye masu zafi da ɗumi suna gangarowa ta gefe da gefen idanuna suna wanke mini fuska da nake jin sauƙar su bisa fatana tamkar tafashashshen ɗanyen ruwan dalma, na yi yunƙurin motsa jiki amma na kasa saboda wani zafin da na ji ya ratsa dukkan ilahirin jikina tun daga ɗan ƴatsan ƙafata har zuwa tsakiyar kaina.

Jin wani abu na bin tsakanin cinyoyi yana gudu zuwa ƙafafuna ya tilasta mini runtse kumburarrun idanuna ina sakin wani irin kuka marar sauri haɗe da cin rai. Na ji an buɗe ƙofar ɗakin an fita babu jimawa na ga an kunna wutar ɗakin haske ya gauraye ko'ina. "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Na shiga uku ni Amira me zan gani haka? Me ye ya faru Amatullah?". Na tsinkayo muryar Amira cike da damuwa tana nufo inda nake yashe tamkar gawa ban da idanuna babu abin da nake iya sarrafa a cikin jikina.

"Amira ki taimaka ni ki É—aga ni na zauna".

Ta kamo kafaɗana da nufin ɗago ni na calla wani uban ƙaran da babu shiri ta maida ni na koma na kwanta. Duk inda ta latsa a jikina ciwo nake ji yana yi mini. "Amatullah wai me ya faru ne? Waye ya yi miki wannan ɗanyen aikin?".

Na gaza magana illa kukan da ya ɓalle mini na ke yin sa tamkar da bakin ƙwarya. Ji nake yi gabaɗaya duniyar tana juya mini ina ganin rufin ɗakin tamkar zai rikito a bisa kaina, na yi nadama ainun na kuma ƙara yin da na sanin kasancewa ta a raye har zuwa wannan lokacin da wannan ƙaddarar ta afka mini a bisa turban tsautsayi. "Amira jikina gabaɗaya ciwo yake yi mini, jini zuba yake yi daga jikina. Amira mutu zan yi mutu zan yi". Na furta zancen cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa cikin kalmomin da baki kan iya furtawa, ji nake ji tamkar ba zan iya ƙara ko da sakon ɗaya a raye ba saboda tsananin azaba da masifar azababben ciwon da nake ji a cikin jikina.

"Ba za ki mutu ba Amatullah, bari na je na sanar da Hajiya abin da ya faru". Amira ta yi zancen tana lulluɓa mini mayafi a jikina da ya taimaka wajen ɓoye tsiraicina da ya bayyana. Ta tashi ta fice daga cikin ɗakin cikin hanzari babu jimawa suka dawo tare da Hajiya Tasalla da ta na shigowa ta soma zagba salati da sallallami ganin mungun halin da nake cikinsa. "Amatullah tashi ki yi min bayanin abin da ya faru? Waye ya yi miki haka? Waye ya shigo cikin ɗakin nan ba tare da sanina ba? Alhalin tun ɗazu ina zaune a filin tsakar gidan nan ban ga shigowar kowa ba balle fitar wani".

"Hajiya ku kai ni asibiti wallahi mutuwa zan yi". Na yi zancen cikin tsananin zafin ciwo da takaicin halin da na tsinci kaina, da kuma sauyawar da rayuwata za ta yi daga wannan lokacin. Ta dafe ƙirji tare da waro idanunta waje"asibiti kuma Amatullah ai hakan daidai yake da tonuwar asirinki, na iyayenki da kuma ni da kaina. Bari na je na tafasa muka ganyan magarya da lalle ki ci shiga ciki za ki ji daɗin jikinki". Ba ta jira abin da za mu ce ba ta tashi a hanzarce ta fice tamkar za ta kife akan hancinta. "Na shiga uku ni Amira yanzu da wani idon zan fuskanci Abbanki da wannan zancen, bayan ya damƙa amanarki a hannuna. Ya yarda da ni tare da yaƙinin matuƙar kina tare da ni ba zan taɓa bari wani abun ya cutar da ke ba". Furucin Amira kenan da ya ƙara saka ni kuka daga ni har ita kukan muke yi da dukkan ƙarfinmu, tamkar wanda aka aiko da saƙon mutuwar iyayensu uwa da uba tare da dukkan ahalinsu.

Har Hajiya Tasalla ta dawo ba mu daina kukan ba, ta je ta rufe gidan ruf a cewarta kar wani ko wata ya shigo ya tarar da abin da ya faru asiri ya tonu, ta kuma sallami duk masu kwanan ranan suka tafi. Tare da Amira suka cicciɓe ni zuwa waje na shiga cikin ruwan ɗumin wani azababben zafi na ji ya ratsa ƙoƙon kaina na yi zumbur zan tashi Hajiya Tasalla ta maida ni. "Ki yi haƙuri ki koma ki zauna a cikin ruwan nan, domin shi ne samun lafiyarki a yanzu". Haka ina kuka ina cije leɓe na koma na zauna na aƙalla mintuna talatin kafin na fito ta kai mini ruwan ɗumi banɗaki na yi wanka na fito ina ɗingisa ƙasa. Wani kayan ta ba ni na saka na kifa kaina da gwiwa ina ci gaba da kukan tausayin kaina da iyayena da nake yi. Amira ma ta zo ta jona ni muna yi tare. Cikin durshashewar murya da sarƙafewar harshe na ce"Amira gida zan tafi ba zan iya kwana a nan ba, ki taimaka ki mayar da ni gidan. Ko mutuwar ce ma na fi so ta ɗauke ni a can".

"Amatullah ki yi haƙuri yanzu idan muka koma gida ai asirinmu ya gama tonuwa a idon duniya. Dole mu tsara yadda lamarin zai tafi". Ban tanka ba na miƙe tsaye ina cije leɓe na yunƙura zan fice daga cikin ɗakin ta sha gabana tana yi mini magiya. "Don girman Allah Amatullah ki yi haƙuri ki rufa mana asiri kar ka fita cikin wannan daren". Runtse idanuna na yi ina jin wasu hawayen da na gaza samun ikon akan su suna kwaranya daga koramar idanuna.

"Ya na ganku duk kuna tsaye cirko-cirko?". Na tsinkayo amon Hajiya Tasalla na buɗe idona ina kallon ta da wutsiyar idanuna, ji nake yi tamkar na yi tsalle na je na shaƙe mata wuya. Ta dire wannan abinci da kofin da ta shigo da shi kana ta zo ta riƙo hannuna za ta taɓo jikina na zame. Ina ci gaba da kukan da nake yi.

"Ki yi haƙuri mana ke kuwa abin da ya faru ai ta riga da ya faru, sai dai a kiyaye gaba". Na galla mata harara kamar idanuna za su faɗo. "Hajiya an cuce ni a cikin gidanki ai dole ki ce mini haka. Me yasa tun farko ba ki sanar da mu cewar kowa yana da ikon shiga kowani ɗaki ba a kowani lokaci? Me yasa kika bari aka cutar da ni cutarwa mafi muni da raɗaɗi da zai ci gaba da bibiyar rayuwarta har zuwa ranar da numfashi zai yi bankwana da gangar jikina?. Hajiya me na yi masa ya aikata hakan a gare ni?". Na ƙare zancen ina sulalewa ƙasa saboda gaza ɗaukana da ƙafafuna suka yi na durƙushe ina kuka da tun sautinsa yana fita har ya dishashe.

"Amatullah ki tambayi kowa a cikin unguwan nan zai faɗa miki cewar gidana akwai tsari da kuma dokoki daki-daki. Na fi zargin kin taka sawun ɓarawo ne kawai domin nan ɗakin Ramlatu ƴar gold ne sai dai in wani jagwal ɗin ta haɗo kai kuma ya faɗi akan ki. Tabbas Ramlatu ƴar hau ce ta bugawa a jarida". Na yi zumbur na miƙe tamkar wacce aka tsigarawa matsilli. "Wace ce Ramlatun? Don yanzu haka tana ina?". Ta ja dogon numfashi ta fesar kafin ta ce"ita ce mai ɗakin nan kuma yanzu haka tana can ƙauye amma bari na ƙira ta a waya". Tana ƙare zancen ta shiga latsa wayarta bugu biyu aka ɗauka ta soma magana.

"Kina ina ne?". Daga ɗayan ɓangaren aka amsa da"ina ƙauye mana. Bashi ko tara kike yi min waɗannan tambayoyin?". "Ramlatu akwai wanda kuka yi da shi za ku haɗu ne, a cikin ɗakinki?". Ta ɗan yi jim kafin can ta ce"babu wanda muka yi da shi, amma na san ko an zo nema na ma ba zai wuce Mus'bahu ba. Kin san shi kaɗai ne yake zuwa har gida ai kuma ba shi da shamaki da ɗakina".

Ta ɗaura hannu a ka"shikenan Musbahu ya cuce mu ya tona mana asiri. Duk abin da kike yi ki bar shi da asussubahin gobe ki dawo, don wata wuta ce ta kunno kai". Daga haka ta datse wayar duk muka zauna jigum-jigum, zaman dirsham na yi kukan ma na gaza samun ƙarfin yin sa balle wani motsi mai ƙarfi ina jin numfashina yana sama yana ƙasa. Take na ji kaina yana juyawa duk da ina zaune ne sai da na yi lu zan faɗi Amira ta yi saurin riƙo ni na faɗo jikinta.

"Hajiya ya kamata fa mu kai ta asibiti. Don wallahi ni kam lamarin nan ya fara ba ni tsoro, kin ga fa jijjiga take yi".

"Ƴar nan ai ba zai yiyuwa a kai ta asibiti a wannan yanayin, da zaran mun saka ƙafa mun fita to asiri fa ya tonu mutumcinta da na iyayenta ya zube. Kin kuma san ance mutumci madara ne in ya zube ba a iya kwashewa, akwai wani likitan da zan ƙira zai zo har gida ya duba ta". Ta ɗaga waya ta yi ƙira babu jimawa ta fits ta je ta shigo da mutumin, lokacin gabaɗaya na cire rai da ci gaba da numfashi a doron duniya, na fidda rai ga rayuwa. Da taimakon Amira na tashi na zauna bayan ta sa mini matashi na zauna a kai likitan ya duba ni kana ya soma jero mini tambayoyi.

"Da alama wannan ne karon farko da kika taɓa saduwa da wani ɗana miji a rayuwarki ko?". Na ji tambayar ta tsaya mini a rai kwatankwacin irin tsayiwar da ƙayan fiki yake yi a maƙoƙaro. Na haɗiye wani miyau mai kauri kafin na sama zarafin gyaɗa masa kaina alamar e da hakan ya ba shi daman ci gaba da tambayoyi. "Hajiya ba wani babban abu ba ne da zarar ta juri shiga cikin ruwan ɗumi kuma tana samun ishashshen huta, za ta dawo daidai. Sannan zan rubuta wasu magunguna sai a daure a neme su tabbas su ma za su taimaka".

"Likita ka tabbata za ta warware?". Ya gyaɗa kai"za ta warware Hajiya wataƙila ma nan da zuwa safiya duk ciwon jikin da take ji zai yi sauƙi. Ga maganin sai a nemo mata su". Ya ƙare zancen tare da miƙa mata wata takarda ta karɓa jikinta har rawa yake yi, ya fita ta bi shi a baya.

Har ta je ta dawo ban gusa daga inda nake ba ta zo ta durƙusa a gabana. Na runtse idanuna don ba na ƙaunar ko da ganin fuskarta balle sauraren zantukanta. "Amatullah ina mai ba ki haƙuri na san an cutar da ke, amma babu yadda muka iya ƙaddararki ce ta zo a haka babu yadda za mu yi mu sauya ta. Ina mai roƙon ki da ki rufe wannan maganar a nan inda ta faru kar ki bari kowa ya sani ciki kuwa har da iyayenki". Babu shiri na ware idanuna tar akan ta cike da son ƙarin bayani.

"Ƙwarai kuwa hatta iyayenki kar su ji wannan labarin don in suka ji to har su koma ga Allah wannan tabon ba zai bar cikin zuciyoyinsu ba. Sannan babu wani ɗa na mutunci zai dai fito neman aurenki, ko ya zo ma ƴan gulma za su tsegumta masa abin da ya faru. Ki rufa wa kanki asiri ki rufawa iyayenki".

Wasu tsiraran hawaye suka soma rige-rigen fitowa daga idanuna suna sauƙa har izuwa tudun wuyana. Na ji ta riƙo hannayena na yi saurin zamewa.

"Hajiya wace ce Ramlatu kuma me ye tsakaninta da shi Musbahun? Me ya sa zai aikata wannan abun a zuwan cewa akan ta ya yi?".

Ta ja dogon numfashi ta fesar kafin ta soma cewa"Ramlatu ƴar ƙanina ne da iyayenta suka rasu tun tana jaririya, ni ce na raine ta da hannuna har ta girma kuma na ba ta mummunan tarbiyan da yanzu haka take kan gwadabensa. Mus'bahu wani saurayinta ne da ya yi hidima da ita tun zamanin ƙuruciyarta har ta riƙa ta zama cikakkiyar budurwa sun yi soyayya da shi na bugawa a jarida kafin daga bisani masu hannu da shuni suka soma danno gare ta, a lokacin ne hankalinta ya karkata zuwa gare su har ta zaɓo ɗaya daga cikin su ta tura shi can ƙauye ya magantu da manya. Tun daga wannan lokacin ta fara wasan ɓoya da Mus'bahu don ya yi ikirarin cewar idonsa idonta sai ya lahanta ta ko kuma ya gurgunta mata rayuwa, sai dai ban taɓa kawowa a raina cewar yana da wannan mungun nufin a cikin ransa ba. Amatullah ƙaddara Ramlatu ce ta faɗa akan ki". Wani zazzafan kuka mai sauti na fashe da shi tabbas na yarda ƙaddarar bawa ba ta wuce ranarta sai dai ban taɓa tunanin ta wa ƙaddarar za ta zo a irin wannan siffan mai muni ba. Duk su biyun suka haɗu suna rarrashina amma na kasa tsayar da kukan da nake yi, tausayi da tunanin halin da Abba zai shiga shi yake ta kai kawo a cikin birnin zuciyata yana yi mini yawo a cikin kwanyata.

Haka muka kwana da idanunmu har aka yi ƙiran assalatu Hajiya Tasalla ta ƙara dafa mini ruwan zafi na shiga na yi wanka, tun kafin gari ya gama wayewa na zara hijabi na kallo Amira da ta buga tagumi na ce"ki tashi mu tafi in kuma ba yanzu za ki tafi ba. To ni kin ga tafiyata".

Ta yi sauri ta riƙo ni"don girman Allah ki yi haƙuri ki bari tukunnan mu ƙara ganin yanayin jikin nakin zuwa nan da gari ya yi haske". "Amira ki bar ni na tafi kawai". Na yi zancen ina fizge jikina daga riƙon da ta yi mini. Na durƙushe a ƙasa ina hawaye tare da sumbatu.

"Amira da kin san yadda nake ji a cikin zuciyata da ke ce mutum na farko da za ki fara taimaka mini da hanyar barin cikin gidan nan. Ashe akwai irin wannan baƙar ranar cikin ranakun rayuwata? Ashe duk yadda nake tattali da killace mutumcina wani wanda shari'a ba ta mallaka masa ni ba zai rusa mini dukkan tanadin da na daɗe ina yi a rayuwata. Amira da wani idon zan kalla Abba?".

"Ai ba za su taɓa sanin abin da ya faru ba ma har abada". Na kafe ta da ido don na kasa cewa komai sai da na fizgo numfashina da yake maƙale mini a ƙirji kafin na zama zarafin faɗin"ke ma kin goyi bayan abin da Tasalla ta faɗa kenan?".

"Ba wai ina goyan bayan ta ba ne ina dai goyan bayan abin da zai siya miki mutunci ne Amatullah. Haƙiƙa idan maganar nan ta fita ba ke hatta ni ma na kaɗe balle kuma iyayenmu don shiga cikin jama'a ma sai ya gagare su, an dinga yi musu zumɗe kenan ana nuna su da baki tamkar watan Ramadana. Ki yi haƙuri ki karɓa ƙaddarar da ta faɗa miki, na tabbatar ko a wajen Allah ba ki da laifi don ba son ranki hakan ya faru ba. Kowani bawa da irin na sa salon ƙaddara ke ma kuma ta wannan fannin Ubangiji yake son ya gwada ƙarfin imaninki".

"Ko zan ɓoyewa kowa ba zan iya ɓoyewa iyayena ba". Ta zo dab da ni"za ki iya matuƙar kika sa a ranki cewar za ki yi hakan. Yanzu dai ki bari gari ya ƙara waye wa sai mu tafi". Na gaza cewa da ita komai illa kukan da na ci gaba da ni, a haka Hajiya Tasalla ta shigo ta same mu ta kawo mana abincin karin kumallo sai dai gabaɗayamu mun kasa cin komai, da kanta ta je ta sayi maganin da aka rubuta ta kawo mini, da ƙyar Amira ta lallaɓa ni na sha maganin muka fito za mu tafi, har zaure Hajiya Tasalla tako mu tana jeranta mini sannun da ko kallon arziki ba ta ishe ni ba balle na amsa mata.

Muna shawo kwanar da za ta sada mu da gidanmu muka hango Abba tsaye a ƙofar gidan, sai waige-waige yake yi. Cak na tsaye ina lalumo hannun Amira yayin da hawaye suka ciko mini kurmin idanuna. [10/21, 5:05 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

____________________________________

Page 3️⃣3️⃣

Amira ta riƙe hannuna gam"don girman Allah Amatullah ki nutsu kar ki tona mana asiri, kar ki bari ya gane da wani abu". "Na shiga uku kin ga fa Abba ne tsaye". "To don Abba ne sai me ye? Ki nutsu dai kawai ke kam kar ki yi abin da zai gane cewar wani abu ya faru". Ban kuma cewa da ita komai ba na goge fuskana da hawaye suka ɓata mini shi kana mu ka ci gaba da tafiya har zuwa lokacin hannuna yana cikin nata. Muna doso wajen muka haɗa ido da Abba ya sauƙe wani ƙatuwar numfashi yana kafe mu da idanu.

"Uwata sai yanzu kuka dawo, a ina kuka tsaya?". Kafin na yi magana Amira ta yi hanzarin karɓe zancen cikin faɗin"Abba ba sa buɗe gidan da wuri ne shi yasa. Don a cewarta babu wanda zai fita sai gari ya yi haske ido na ganin ido". Ya yi ɗan jim tamkar yana nazarin wani abun kafin can ya ce"shikenan tun da kun dawo cikin ƙoshin lafiya alhamdulillah, amma dai ku daina tsayawa a ko'ina. Ku wuce ku shiga ciki".

"To in sha Allah". Muka haɗe baki wajen amsawa, muka soma tafiya ina jan ƙafana a hankali saboda ciwon da gabaɗaya jikina yake yi mini. Cak duk mu biyun muka tsaya bisa zancen da Abba ya furta da ya kusa tarwatsa zuƙatanmu.

"Uwata lafiya na ga ki na tafiya kina ɗingisa ƙafa?". Take gumi ya keto mini jikina ya soma rawa cikin in'inar da ban san ina yin ta na soma cewa"daman-daman-daman Abba...". Ban ƙarisa ba Amira ta yi caraf ta amshe zancen cikin hanzari. "Abba zamewa ta yi a banɗaki shi ne ta bugu". Cike da tausayi da jin ƙai Abba ya furta"subhanallahi! Sannu ba ki dai ji ciwo ba ko?". Na runtse idanuna a ƙoƙarin hana hawayen da suka ciko mini koramar idanuna samun damar kwaranya.

"Ban ji ciwo ba Abba akwai bugu na yi a ƙuguna". Na yi zancen cikin sanyin jiki da na murya. "Allah ya kiyaye na gaba. In sha Allah in zan dawo zan taho miki da magani sai ki sha kin ji?". Kaina kawai na sama damar gyaɗa masa na yi masa fatan a dawo lafiya ya tafi yayin da mu kuma muka shige ciki. Muna shiga zaure na sulale a ƙasa saboda wani ƙarƙarfan kukan da ya yanko mini, Amira ta dafo kafaɗuna haɗe da faɗin"don Allah Amatullah ki yi haƙuri wannan kukan da kike yi fa ba shi zai gyara abin da ya riga ya afku ba. Ki nutsu mu yi tunanin hanyar da za mu ɓullowa lamarin nan".

"Allah in wani laifin na yi maka ka jarabce ni ta wannan hanyar, Allah na tuba ka yafe mini". Na yi furucin cikin ƙanƙan da kai da jingina dukkan lamurrana ga Sarkin da ba shi da abokin tarayya wanda bai haifa ba kuma ba a haife shi ba. Cikin lanƙwasar da murya da rarrashi ta soma yi mini magiya da ban haƙuri. "Don Allah ya ya kike so na ya miki ne Amatullah? Na ba ki haƙuri na ƙara ba ki haƙuri amma kin ƙi fahimta ta, abin da ya faru fa ya riga da ya wuce sai dai a kiyaye gaba, yanzu idan wani ya fito daga cikin gidan nan ya gan ki a haka ai shikenan asirin mu ya gama tonuwa". "Amira kin san yadda nake ji a cikin raina kuwa?". Ba ta bar ni na ƙarisa ba ta katse numfashina ba tare da na dire zancen ba.

"Duk abin da kike ji a cikin ranki ina jin makamancin sa a cikin raina Amatullah. Don Allah ki yi haƙuri ki tashi mu shiga ciki". Tana rufe bakinta muka jiyo sautin muryar Auwal saurayin Ummi ya buga sallama. Zumbur na miƙe ina karkaɗe jikina tare da goge hawayen da suka ɓata mini fuskata.

"Ƴan mata adon gari, Hajiya Amatullahi manyan gari ashe ana ganin ku a cikin duniyar nan?". Ta buga masa harara ina sauƙe numfarfashi na ja hannun Amira muka shige ciki, har muna na ƙoƙarin cin karo da Ummi yayin da take fitowa ta ja gefe ta tsaya tana bin mu da ido tare da riƙe haɓa.

"To ikon Allah! Wai na kwance ya faÉ—i ku kuma fa lafiyarku?".

Cikin mu babu wanda ya tanka mata har ta yi ta gama. Sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin na sama ƙarfin gwiwan shiga cikin ɗakin mu bayan Amira ta gama ƙara mini ƙarfin gwiwa da ƙarfafa ni. Da sallama na shiga ɗauke a bakina kaina a ƙasa saboda nauyin haɗa ido nake da Umma ma balle kuma Abba da tausayinsa ya gama ragargaza mini zuciyata. Na durƙusa har ƙasa na gaishe ta ba ta amsa mini ba illa mayar da hankalinta da ta yi akan ci gaba da irga kuɗin da take yi. Na tashi zan shiga ciki na je na kwanta don gabaɗaya ba na jin daɗin jikina ga wani azababben zazzaɓin da yake ƙoƙarin rufe ne lokacin guda. Har na fara tafiya zan doshi hanyar ɗakin ta dakatar da ni ta hanyar faɗin abin da ya gigita dukkan nutsuwar da ya yi saura a gangar jikina, hanta cikina ya haɗa yayin da kaina ya juya jikina ya ɗauki rawa tamkar wacce akan jona wa wutan lantarki, haƙwarana suka datse harshena, yawun bakina ya ɗauke cak kamar rijiyar da ruwan cikinta ya kafe ya tsawon zamani.

"Me ya same ki na ga yanayin tafiyarki ya sauya?".

Take zuffa ya soma tsatstsafo mini daga dukkan mafitan gashin da yake jikina, sai da na aro jarumta na yafawa kaina kafin na sama damar sarrafa abin harshena da ya cika mini bakina. "Umma zame wa na yi a banɗaki na faɗi. Shi ne ƙuguna ya bugu". Ta ɗago ido tana ƙare mini tanadin kallo har sai da na tsargu na rusunar da kaina ƙasa.

"A ina kika zame É—in? Wannan kayan kuma fa na jikinki?".

"A gidan Hajiya Tasalla, kayan kuma ita ta ba ni na sauya don nawa sun jiƙe na shanya su". Sai da ta salwantar da wasu mintuna kafin can ta ce"Allah ya sauwaƙe ki je ki kwanta". Ban ce da ita komai ba na wuce cikin ɗakin ina shiga na fire hijabin kaina na yi jifa da shi kamar jaka haka na zube akan gado ina wani irin matsanancin kuka mai matuƙar cin rai da haifar da zogi da ƙaiƙayi a cikin zuciya. Na cire kallabin kaina na tusa a cikin bakina a ƙoƙarin hana sautin kukan nawan fita, har sai da na ji numfashina yana ƙoƙarin sarƙafewa kana na tashi na zauna na zabga tagumi ina tunanin makomar rayuwata, tabbas ɗan Adam baya taɓa gujewa ƙaddararsa amma na yanke hukuncin ba zan ƙara zuwa gidan Tasalla da sunan kwana ba, na gwammace na kwana ko da a soron gidanmu ne don sai na fi samun kwanciyar hankali da nutsuwar ruhi. Take na ji jikina ya ɗauki zafi zazzaɓi ruf-ruf ya rufe ni na koma na kwanta ina ta rawan ɗari.

A cikin wannan yanayin Umma ta shigo ta iske ni, ta kai hannunta saman goshina ta ji zafi gau hakan ya sa ta faÉ—in"Ke Amatullah lafiyarki kuwa? Mene ne yake damunki haka?".

"Kaina ne yake ciwo".

"To ki tashi ki sha magani mana sai ki kwanta da ciwo haka ba tare da kin sha magani ba". Na tashi ta fito falo inda ake ajiye maganin na duba na ɓalle paracetamol ƙwara biyu na fito waje na ɗebo ruwa na afa ina jefa ƙafana a cikin falon na ji jiri yana ɗeba tare da ƙoƙarin nanayi da ƙasa. Na yi hanzarin dafe kaina da yake juyawa tamkar sitiyarin mota a hannun ɗan koyo. Ban yi aune ba na ji ni shirib na zube a ƙasa na yi warwas, ina jiyo amon Umma ta zo kaina tana tambaya ta ko lafiya amma na gaza samun bakin da zan ba ta amsa. Daidai lokacin Amira ta shigo ɗakin suka haɗu ita da Umma suka ɗago ni suka kwantar da ni a bisa kujera suna yi mini fiffita don fankan da yake aiki a cikin falon bai hana ni fitar da gumi b ya yi mini lajab kamar wacce aka watsawa ruwa.

"Ki tashi ki daure ki ci wani abu sai a kai ki chemist ɗin Halilu ya yi miki allura. Don zazzaɓin bana sai an tare shi tun da wuri in ba haka ba sai ya tsotse mutum tsaf". Furucin Umma kenan da ya sanya hawaye zubowa daga idanuna ina jin a raina ina abin da take tunani ne watau zazzaɓi ba wannan abun ba. Amira ta taimaka mini na tashi na zauna Umma ta dama mini koko da ƙosai kunun kawai na iya zuƙa na koma na kwanta na yi luf, Umma ta ce Amira ta raka ni chemist ɗin Halilu ya yi mini allura. Haka muka fito tare da ita tana riƙe da hannuna muka wuce Ummi da Auwal zaune a zaure suna hira, suka zaro mana idanu lamarin da ya fusata Amira har ta furzar da takaicin da yake cikinta.

"Wannan kallon fa bayin Allah? To sai dai ku ci kanku wallahi mu kam nan gani nan bari É—umamen mayya".

"To ma me ye za mu gani a jikinku? Har ina abin yake wai maye ya ci jariri?". Ummi ta mayar mata da martani a zafafe. Amira ta yunƙura za ta tanka mata ta kwaɓe ta, sai da muka doso chemist ɗin Halilu na ja na tsaya, Amira ta juyo tana kallo na alamar lafiya. "Anya kuwa ba a gane abin da ya faru ba? Ni fa duk a tsorace nake". Ta jijjiga mini kanta"babu wanda zai gane matuƙar ba ke kika faɗa ba". Tana dire zancen ta ja hannuna muka shiga ciki chemist ɗin Amira ce ta yi masa bayanin wai zazzaɓi ne yake damuna da kuma ciwon kai, ya rubuta mini magunguna sannan ya yi mini allura ya ce da dare na dawo a yi mini. Har muka iso gida ban ce da Amira komai ba, duk da kuwa yadda ta dage tana lallashina da roƙona akan kar na faɗa kuma kar na bar kowa ya gane halin da nake ciki. Koda muka dawo ɗakinmu na shige na kwanta lamau ba tare da na yi aune ba nake jin wasu tsiraran hawaye suna kwance mini fuskata. Ina jin ƙirjina yana yi mini wani zafi tamkar ana watsa mini garwashin wuta. Ban san sa'ilin da wani wahalallen bacci ya yi awun gaba da ni ba.

Kamar daga sama na jiyo muryan Umma tana ƙiran sunana tare da bubbuga matashin da kaina yake kai. Na yi figigi na farka ina sumbatu. "Don Allah ka yi mini rai ka taimake ni kar ka raba ni da......". Muɗuk na haɗiye ragowar zancen yayin da idanuna suka washe a bisa fuskar Umma, jikina sharaf da gumi saboda mungun mafarkin da na yi da ya gigita ni ainun. "Ke lafiyarki kuwa sai ka ce mai shafar aljanu? Ki na bacci kina ta battutuwa". Sai da na daidaita nutsuwata kafin na yi ƙarfin halin faɗin"lafiya ƙalau Umma, yanzu ƙarfe nawa?". Sai da ta ƙare mini kallon tsaf kana ta ce da ni a taƙaice.

"Ƙarfe biyu saura".

"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!".

Na furta ina dirowa daga oan gado na fito waje na yi alwala na koma ciki na yi salla, duk yadda Umma da Amira ta suka matsa mini akan na ci abinci kasa ci na yi, da ƙyar na sha kunu shi ma bai wuce ludayi uku na yi ba. Ranar ko islamiyya ban je ba duk son da nake yi mata kuwa, haka na wuni a ɗaki inna fito waje to alwala zan yi ina kammalawa nake koma na kwanta tun ina hawayen har suka daina tsiyaya. Tun da na kwanta nake ta biya karatun alkur'ani a cikin zuciyata har wani baccin ya kuma ɗauka na, ba ni na tashi ba dab ana ƙiran sallan magrib na fito na shiga banɗaki da nufin yin wanka amma na fi mintuna talatin ina durƙushe ina kuka, da ƙyar na yi wankan na fito na ɗauro alwala na koma ciki na yi salla, ban tashi daga kan sallayan ba har sai da na yi sallan isha'i ina zaune Amira ta shigo lokacin Umma ta fita.

"Ya jikin nakin?".

"Da sauƙi".

Na amsa mata da aa taƙaice da hakan ya ba ta damar ci gaba da magana. "Ki tashi mu je ayi miki alluran daren daga nan kuma sai mu wuce ko?". Na ware dukka girman idona akan ta"mu wuce zuwa ina ke nan Amira?". "Gidan Tasalla mana". Baƙi ciki da takaici ya hana ni cewa komai illa bin ta da kallo da na ci gaba da yi ina cije leɓena. Ta riƙo hannuna na zame.

"Na san abin da kike tunani a cikin ranki Amatullah, amma idan kika ce kin daina zuwa to ina tabbatar miki da cewar kin kafawa kanki alamar zargi kenan. Dole su Abba su bincika dalilin da ya sa kika ce ba za ki koma ba alhalin ke da kanki kika zo masa da buƙatar". Ta sauauta amon muryarta kana ta ci gaba da cewa"ki ɗauri abin da ya faru a matsayin ƙaddara".

"Na yarda da ƙaddara mana Amira na yarda da ƙaddara. Amma ba zan iya komawa gidan nan ba". Na yi zancen cikin raunin da yake fitowa tun daga ƙasan zuciyata. "Ni ma ba wai na ce ki ci gaba da zuwa ba ne, na ɗan wani lokaci kawai saboda mu kawar da zargi. Ki daure ki rufa mana wannan asirin". Na fashe da kuka ina faɗin"Allah na tuba idan laifi na yi maka ka jarabce ni ta wannan hanyar. Allah na tuba ka yafe mini".

"Ki yi haƙuri ki daina wannan kukan Amatu ya isa haka. Kar ki ja wa kanki wani ciwon na daban don Allah".

Kafin na amsa mata muka tsinkayo sallamar Abba, na yi zumbur na miƙe ina gyara ɗaurin zanin da yake jikina na goge fuskana da bakin hijabin da yake jikina. Na fito falon Amira tana biye da ni. Muka haɗe baki wajen yi masa sannu da zuwa ya amsa yana tambayata ya ya jiki na ce da shi da sauƙi. Ya ba ni wani magani ya ce ma sha na ciwon jiki ne, a take a wajen na ɓalla na sha ba mu tafi ba sai da Umma ta dawo muka yi mata sallama muka tafi. Sai da muka tsaya a wajen Halilu mai chemist ya mini alluran kana muka tafi. Ko kallon azurki ban yi wa Hajiya Tasalla ba duk da kuwa kulawar da take ba ni don tun da muke je ta kasa zaune ta kasa tsaye sai hidima take yi da mu har sauya mana ɗaki ta yi.

"Hajiya ina ita Ramlatun ta dawo?". Na yi tambayar fuskata a ɗaure kamar hadarin gabas. Ta soma inda-inda"ki yi haƙuri an yi rasuwa ne a can ƙauyen shi yasa. Ni ma saboda na san za ku zo ne shi yasa ban je ba. Amma in Sha Allah da zaran an yi sadakan bakwai za ta dawo ku yi haƙuri".

Ban ce da ita komai ba na tashi da sauri na har ina harɗewa na shige ciki ina tare hawayen da suke ƙoƙarin zubo mini daga idanuna. Amira tana shigowa muka rufe ɗaki na ciki na amsa wayarta na buɗe application ɗin alƙur'ani ina karantawa tun Amira tana zaune har sai da ta kwanta bacci ya soma fizgan ta don daren jiya ba mu runtsa ba.

Na daɗe ina karatu kafin na ɗaga hannuna sama sai dai na kasa cewa komai illa kukan da ya kubce mini. Na kifa kai da gwiwa ina rero shi. Yadda na ga rana haka na ga dare don ko ya ya na rufe idanuna sai na ga kamar abin da ni jiya ne zai ƙara maimata kansa. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya lokaci yana shuɗe wa tun ina kwana na tashi cikin fargaba da zulumin abin da zai je ya dawo har tunanin hakan ya fara raguwa, daidai da rana guda Umma ba ta taɓa fahimtar halin da nake ciki ba balle ta lura sauyawar yanayin jikina. Haka har sati cif ya cika lokacin ya rage saura sati biyu sauƙarmu komai ya kankama, tun ina saka rai da dawowar Ramlatu kamar yadda Hajiya Tasalla take faɗa har na miƙa lamarin ga Allah na kuma yi yaƙinin dukkan abin da ya zartar a kaina shi ne daidai. Cikin ƙanƙanin lokacin na rame na zabge na yi baƙi kowa ya ganni sai ya ce na rame. Duk wanda ya tambaye me ke faruwa na kan ce da shi karatun sauƙanmu ne kawai na sa a gaba shi yasa. Na yi duk yadda zan yi na haɗu da Ramlatu ko shi Mus'bahun amma lamarin ya ci tura duk da kuwa irin naci da bibiyar lamarin da nake yi daki-daki. Komai nawa ya sauya hatta a karatun islamiyya ƙoƙari na ya ja baya. Har gida Anty Zulaihatu ta aiko mini kayan da Yaya Alhassan ya saya mini kasancewar ban sama nutsuwar zuwa gidan ba balle na amsa, Umma ta daka tsalle ta dire ta ce ba zan yi amfani da kayan ba. Babu yadda muka iya daga ni har Abba, haka muna ji muna gani aka mayar da kayan, na ci kuka har na godewa rabbana. Ana saura kwana uku sauƙan mu a wani yammaci Malam Suleiman ya zo gidan mu ya yi sallama da Abbana, tun da na ji sunan wanda ya zo neman Abba na tsinci kaina cikin faɗuwar gaba. [10/22, 7:02 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_____________________________________

Page 3️⃣4️⃣

Tun da Abba ya fita ganawa da Malam Suleiman na kasa zaune balle tsaye, haka kawai na tsinci kaina cikin tsananin faɗuwar gaba da kuma tsinkewar zuciya. Amir ya bankaɗo labulen ƙofar falon da hakan ya sani miƙewa zumbur na miƙe akan ƙafafuna ina sauraren abin da yake faɗi cikin tsiwa. "Wai ki zo in ji Abbanki suna zaune".

"Ni kuma?". Na jefa masa tambayar cikin ruɗewa. Ya taɓe baki kafin ya ce"e ke ɗin fa malama". Yana dasa aya anan ya saki labulen ya juya ya fice yana wasu ƙananun magana. Jikina a sanyaye na fito ina tafi kamar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki na iso cikin zauren bakina ɗauke da sallamar da ta sama amsawar Abba da Malam Suleiman.

"Abba ga ni an ce kana nema na". Ya yi ɗan jim kafin can ya furta"Uwata wai me yake faruwa ne? Ga malaminku nan ya kawo min ƙorafin cewar yanzu ba kya mayar da hankali akan karatunki". Na rusunar da kaina ƙasa ina faɗin"Abba babu komai". Ya yi saurin datsen numfashina"Uwata akwai wani abun mana ai da ba haka kike ba".

"Abba kawai jinyar da na ɗan yin nan ne cikin kwanakin nan shi yasa". Malam Suleiman ya but caraf ya karɓe zancen"Amatullah akwai abin da yake damunki duk yanayinki ya sauya, kin daina mayar da hankali akan karatunki bayan kin san cewar kina ɗaya daga cikin ɗaliban da za su yi karatu a ranar taronmu. Ki cije damuwar da ke cikin ranki ki fuskanci abin da yake tunkaro rayuwarki". Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau kamar wacce aka zarewa laka, hawaye suka ciko mini koramar idanuna hakan ya sa na yi hanzarin rutsunar da idanuna ƙasa da hakan ya ba wa hawayen da ke cikin idanuna kwaranyowa. Cikin sanyin murya Abba ya ce"Amatullah me yake faruwa ne?".

"Babu komai Abba".

"Kar ka matsa mata Malam Munnir, amma zan so ki ƙara mayar da hankalinki akan karatunki sosai. Don ba zan ɓoye miki ba ke ce hope ɗinmu gabaɗaya Amatullah, duk ƙoƙarin da za ki yi ba iya kanki zai tsaya ba har mu malamanku da makaranta abin zai shafa".

"In Sha Allah Malam na gode sosai Allah ya saka da alkhairi". Duk suka haÉ—e baki wajen amsawa da amin, suka ba ni iznin tafiya na tashi na koma ciki É—akin su Amira na nufa na iske ta tana waya da Mansur na zauna a gefenta na buga uban tagumi tamkar mai takaba. "Ke kuma fa lafiya?".

"Amira wai ya ya zan yi na dawo yadda nake ne a baya? Ni kaina na san na sauya irin sauyawar da ba zan taɓa dawowa daidai ba". Ta sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya da har sai da na ji sautinsa kafin ta sama zarafin cewa"komai fa sai a hankali zai dawo daidai ba zai yiyuwa a lokaci guda ba. Yanzu kuma me ya faru sanar da ni". Na kwashe duk yadda muka yi da su Abba na sanar da ita ta yi shuru na tsawon wasu mintuna kafin can ta ce"sai ki mayar da hankali kan karatunki tun kafin su fara zargin wani abun. Na san abin da nauyi Amatullah amma ya ya muka iya da ƙaddara". Na fashe da kuka kamar wata ƙaramar yarinya har jikina yana rawa tamkar mazari. Ta riƙo hannuna na kwantar da kaina a bisa cinyarta.

"Amatullah wai me kike so ki mayar da kanki ne? Ko so kike yi ki jawa kanki wani ciwon na daban?. Tun ranar da abin nan ya faru kullum sai kin yi kuka fiye da sau biyar a yini guda, Haba Amatullah abin da ya faru fa ya riga da ya faru damuwa da wannan kukan ba shi zai gyara abin da ya wuce ba".

"Allah na tuba ka yafe mini kar ka hukunta ni akan laifin da na aikata a bisa rashin sani....". Ban ƙarisa ba Amira ta rufe mini baki"kar ki ɗaura wa kanki laifin abin da ba ki da ikon sauyawa shi ko hana faruwar sa, kowa fa da kika gani a cikin duniyar nan da irin na shi salon ƙaddaran. Kuma yarda da ƙaddara tana daga cikin cikar imanin mumini". Ban ce da ita komai ba har lokacin da wayarta ta soma ruri ta ɗaga suka yi magana da Mansur sai da suka yi sallama kana ta ce"tashi mu je ga can Mansur a ƙofar gida".

"Ki je kawai". Na furta a taƙaice numfashina yana cushewa waje guda. "Kar ma mu fara gardama da ke Amatullah, ki tashi kawai mu tafi don na tabbatar da zaran na gusa daga nan wajen kukan dai za ki ci gaba da shi". Ban tanka mata na tashi gabaɗaya jikina babu ƙwari muka fita tare da ita muka tarar da Auwal da Ummi a zaure suna hira, ta banko mana harara Amira ba ta yi wata-wata ba ta maida mata. Muka iso wajen Mansur da yake tsaye a jikin motarsa kamar ko yaushe yana latsa wayarsa tare da jijjiga makullin motarsa.

"Barka da fitowa Tauraruwar birnin zuciyata, hasken da yake haska ƙalbina ta yadda zan yi tafiya ko babu sandan jagora". Lumshe idanunta Amira ta yi cike da jin daɗin zantukansa ta soma cewa"maraba da zuwa Sarki mai sarautar dukkan zuciyata. Ban san da wasu kalmomi zan yi amfani da su wajen nuna maka yadda na yi kewarka ba Ya masoyin raina". Wani murmushi mai laushi suka soma sakarwa junansu mai ɗauke da wani ɓoyayyan saƙonni.

"Ni kam bari na koma ciki kafin kun gama". Na yi zancen da ya yi silar dawo da su cikin duniyar zahiri tare da figzo hankali da nutsuwarsu zuwa ga gangunan jikkunansu. Mansur ya haɗe hannayensa wajen guda alamar roƙo yana faɗin"afuwan ranki ya daɗe babban ƙawa, sam ban lura da ke ba ne ayi min aikin gafara". Na taɓe baki"idan ina da zuciya ni ma dai ya kamata na daina rako ta. Kullum sai an ce da ni ba a lura da kasancewata ba a wajen". Duk suka saka dariya kafin Mansur ya ci gaba da magana. "Tuba muke yi a yi mana afuwa. Kuma mussamman zuwan don ke aka yi ta ba na zo duba ki don ta ce da ni ba ki daɗi tsawon kwanaki".

Na jinjina kaina"ai na ga ana ƙoƙarin yi mini kora da hali ne". "To yanzu dai ya ya jikin?". "Da sauƙi alhamdulillah". "Sai dai sauƙin musulunci aminiyarmu, amma ban ga alamar sauƙi a tattare da ke ba. Ga shi duk kin faɗa kamar kin yi shekara kina jinya". Na yi ƙarfi hali na murmusa kafin na ce"kuma fa da sauƙi sosai fiye da lokacin baya ne, ka san ciwo ne yake shiga lokacin guda amma warkewa ko samun sauƙi sai a hankali-hankali".

Ya jinjina kansa alamar gamsuwa da furucina kana ya ɗaura da cewa"haka ne kam. Allah ya ƙara sauƙi da lafiya mai amfani". "Amin ya Allah". Muka haɗe ni da Amira waje amsawa, mun ɗan taɓa hira kafin Mansur ya ce mu shiga mu fito ya sauƙe mu a gidan Hajiya Tasalla. Muka shiga ciki muka yi wa Ummana da Umman Amira sallama muka fito, ba don raina ya so ba muka shiga motar Mansur ya kai mu gidan. Ya fito da wasu manyan ledodi guda biyu ya ajiye su a gabana da bi ledan da ido kafin na sauƙe idona akan sa alamar son ƙarin bayani. "Wannan naki ne ranki ya daɗe, Allah ya ƙaro sauƙi". Zan yi magana ya katse ni"don Allah kar ki ce komai kuma kar ki hana ni aikin alkhairin da na yi niyyan aikatawa. Ke fa Malama ce kin san cewa ba kyau mayar da hannun kyauta baya".

"Gaya mata dai wataƙila ta ji nakan". Amira ta yi zancen tana ƙunshe dariyar da yake ƙoƙarin kwace mata. Na galla mata harara kafin na yi wa Mansur godiya suka yi sallama da Mansur na ɗauki ledar muka shiga ciki. Muna shiga cikin gidan na ji gabana ya yanke ya faɗi lamarin da ya tilasta mini runtse idanuna ina karanto duk addu'ar da ta zo bakina. Sharau muka tarar da gidan don masu kwana ba su fara zuwa ba a wannan lokacin, sai sun gamo sharholiyar su kafin suke dawowa cikin gidan idan dare ya tsala. Muka tarar da Hajiya Tasalla tare da wata matashiyar budurwar da fatarta ta sha bleaching har ta gaji ta yi jajir da ita duk fatan fuskar ya taƙushe waje guda tamkar an yi ɓarin garwashin wuta. Tun da na ɗaura idona akan ta na yi bugun zuciyata ya tssnanta. Har muka iso muka zauna ban ɗauke idona daga kan ta ba, muka gaisar da Hajiya ta amsa ta yi mana tayin abinci muka ce mun ƙoshi, haka nan kawai na ji zuciyata ta kasa nutusuwa don haka na tashi zan shige ciki.

"Hajiya ko wannan ce wacce tsautsayin ya faÉ—a mata?".

Cak na tsaya bisa sauƙar furucin a na'urar naɗan sautina. Kafin na waigo na ji Hajiya ta ba da amsa da faɗin"uhmm! Ke dai ki bari kawai ita ce ina gaya miki".

"Hajiya ita ce Ramlatun?". Na watsa mata tambayar hawaye suna ciki mini koramar idanuna. "Ita ce, ita ma tun da tazo take tambayar ki". Take na ji jikina ya soma rawa duk yadda naso na furzo da zancen da yake ci min rai bakina ya ƙi ba ni haɗin kai wajen aiwatar da hakan. Jikina ya ci gaba da rawa ƙafafuna suka nuna gazawar su wajen ɗaukar nauyina sai da Amira ta taso ta riƙe ni, na fizge jikina na shiga ɗaki da gudu. Shirij na zube akan katifa ina kuka tamkar raina zai bar gangar jikina.

Na ji an dafo kafaɗuna haɗe da cewa"Amatullah kike ko wace ce?". Na ya banza da ita ba tare da na ce da ita komai ba, hakan ya ba ta damar ci gaba da maganar. "Hajiya ta sanar da ni duk abin da ya faru kuma na ji baƙin ciki matuƙa musamman da ta sanar da irin kamun kanki da ƙoƙarin ki wajen ganin kin killace mutumcin kanki da kiyaye kima da martaban gidanku. Ki ɗaga hannu ma ki godewa Allah da ya kasance ba ke kika kai kanki ba ƙaddara ce ta faɗa miki wacce ba ta wuce ranar ta. Ko kin zo gidan nan ko ba ki zo idan Allah ya nufa faruwan hakan babu makawa sai ya faru a gare ki, Mus'bahu cikakken namiji ne na tabbatar ke ma kin ji daɗin kasance da shi...". Kalamanta na ƙarshe suka daki zuciyata tare da baƙa mini ruhina. Na yi zumbur na tashi na zauna tare da buge hannunta daga jikina.

"Ki na matsayin mace kike furta wannan maganar? Shin ko kaɗan ba ki ji tausayina ya ɗarsu a cikin ranki ba? Wallahi don babu yadda na iya ne ba ni kuma da wani zaɓi balle mafita amma da tunin na daina zuwa gidan nan. Ba zan ce da ke komai kuma ba zan nema jin wani abu daga gare ki na yarda ƙaddarata ce ta zo a haka kuma ina neman sauƙi a wajen wanda yake da ikon sausauta lamurana".

Tun da na soma maganar take kallona har na akai aya, ta yi dariya ta ce"ba nufi na baƙanta miki rai ba ne baiwar Allah. Sai dai zan so na yi miki wata tambaya guda, a yadda kike da diri da kyawun suran nan ki na nufi babu wani na mijin da ya taɓa kusantark....". "Ki tashi ki fita tun kafin na idanuna su rufe na illata ki ko kuma na yi miki raunin da har ki koma ga mahaliccinki ba zai bar jikinki ba".

Ya miƙe tsaye ta riƙe ƙugu tana ƙare mini kallo kafin can ta ce"zan fita kamar yadda kika buƙata, amma kafin na tafi zan ba ki wani shawarar da nake da yaƙinin cewar za ta amfane ki. Na ji an ce kina neman Mus'bahu to ba za ki taɓa samun sa don na tabbatar tun ranar da ya aikata wannan abun ya haɗa jakarsa ya bar garin nan wataƙila yanzu ba ya ƙasan nan". Tana gama faɗin haka ta fice daga cikin ɗakin ta bar ni da sakin wani gigitaccen kuka mai raunana zuciyar mai saurare. Ban gushe ina yi ba Amira ta shigo ta dinga rarrashi na, na amshi wayarta na soma karatun aƙur'ani da shi sai da dare ta raba kana na ajiye wayar na yi dogon addu'a na shafa a nan wajen bacci ya yi nasarar ɗauka ta sai dai ban yi nisa ba na farka a zabure. "Lafiya kuwa?". Amira ta jefa mini tambayar cikin damuwar da ya bayyana har a cikin furucinta, maimakon na ba ta amsa sai kawai na fashe da kuka.

"Amira an ya ba haukacewa zan yi ba kuwa ni kam?".

Cikin sanyin murya ta soma cewa"babu abin da zai faru da ke in Sha Allah". Ta jawo ledar kayan da Mansur ya kawo ta fito da kayan ciki kayan marmari ne sai kuma wasu manyan cakuleti masu sanyi sa'annan lemonka gora har kala biyar. Ta matsa mini akan sai na ci wani abu ba don raina ya so ba na sha lemon da wasu daga cikin kayan marmarin. Washe garin ranar a islamiyya Malam Suleiman ya aiko aka ƙira ni ya zaunar da ni ya dinga yi mini nasiha tare da ba ni wasu shawarwari, ban iya daurewa ba har sai da na zubar da ƙwalla. Ko da a fito daga wajen Malam Suleiman lokacin har an tashi ban ga su Rauda da Ammi don daman sun ce daga islamiyyar wajen ɗinki suka nufa za su je su karɓo ɗinkin ankon waliman. A hankali nake tafiyar tamkar wacce take jin tsoron taka ƙasa na fito daga cikin islamiyyar, zan tsallaka titi na ji an ƙira sunana na waiga da sauri.

"Yaya Alhassan". Na furta kalmar cikin mamaki don ban yi tsammanin ganin sa a wannan lokacin ba. [10/24, 10:06 AM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_______________________________________

Page 3️⃣5️⃣

Da saurina na iso inda yake tsaye a jikin mashinsa ɗin tare da wani abokinsa da tun ina tahowa idanunsa yake kaina har na iso wajen bakina ɗauke da sallama. Suka haɗe baki wajen amsawa kana na gaishe su suka amsa. "Kun tashi kenan?". Na gyaɗa masa kaina ina zarcewa da faɗin"daman ma ina so na je gida wajenka na ba ka haƙuri akan abin da ya faru game da waɗannan kaya...". Ya yi saurin ɗaga mini hannu alamar ba ya son sauraren ragowar zancen. "Abin da ya faru ai ya riga da ya wuce sai dai a kiyaye faruwarsa a gaba, na ji wai ba ki da lafiya tun lokacin nake so na zo na duba ki amma ina gudun abin da zai je ya dawo shi yasa ma ban zo ba, shi ne na zo islamiyya. Me yake damunki ne haka Amatullah? Duk kin rame kin faɗa tamkar ba ke ba, me ya yi zafi haka?".

Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya kafin na sama zarafin faɗin"zazzaɓi ne kawai sai kuma yanayin karatu". "Amatullah kar ki faɗi saɓanin abin da yanayin fuskarki ya riga ya nuna. Tabbas akwai wani abun da yake faruwa ko in ce akwai abin da yake damunki". Na yi shuru ba tare da na ce komai tare rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa. "Alhassan don Allah kar ka yi sanadin zubar hawaye daga fuskar wannan kyakykyawar halittan". Furucin abokinsa kenan ya ƙara sausauta amon muryarsa ya ci gaba da cewa"ƙanwata me yake damun ki?". Na ɗaga idona na yi masa kallo guda na janye a hankali na ce"babu komai". Yaya Alhassan ya amshe zancen"shikenan ba zan matsa miki amma ko ma mene ne ina miki fatan samun mafita cikin gaggawa, ranar yaushe ne walimar takun".

Na yi murmushin ƙarfin hali"gobe ne da ƙarfe tara na safe". Ya jinjina kansa"me kike so na taho miki da shi, tun da Umma ta hana ni yin wancan aikin alkhairin da na yi niyya".

"Zuwanka ma kaÉ—ai ya wadatar da ni ba sai ka zo mini da komai ba".

Ya tsuke fuskarsa"idan ba za ki faɗa ma ba ai kuwa duk abin da na yi niyya shi zan saya na kawo miki, in ya so in kin ga dama inna ba ki ki watsar ko ki kyautar wannan kuma ra'ayinki ne". Na saki taƙaitaccen murmushi"to shikenan na bar maka zaɓi duk abin ka taho mini da shi ina maraba da shi". "Ni ma da za a yi na'am da nawa kyautar da na yi " Furucin abokinsa kenan da ya sani ɗaga idona na yi masa kallo guda na mayar da idanuna. Na kawar da maganar ta hanya cewa"yaya Alhassan don Allah ka sanar da Anty Zulaihatu ma don ban sanar da ita ba".

Ya riƙe haɓa"ai duk dangi babu inda ban shelanta cewar ƙawata ɗaya tilo za ta yi sauƙa ba. Don haka ki kwantar da hankalinki gayya guda za ki gan ma ranar, yanzu dai ga wannan ki wuce ki hau abin hawa ki wuce gidan na ga magriba tana kawo kai". Ya ƙare zancen yana miƙo mini naira ɗari biyar ɗin da ya zaro daga cikin aljihunsa, na amsa tare da yi masa godiya sai da na tsallaka titi na shiga napep kana na ga sun tafi. Ina sauƙa a layinmu na hango Amira tsaye da Bashir a ƙofar gida duk suka zubo mini na jiyamunsu, na sa kai zan shige cikin gida tamkar ban gan su ba Amira ta dakatar da ni.

"Amatullah ba ki ga kin yi baƙo ba ne?".

"Amira don Allah na gaji don Allah ki bar ni".

Ina ƙare zancen na shige ciki ta rufa mini baya tare da shan gabana. "Me yasa kike haka ne Amatullah? Ai ko ba za ki ce da shi wani abu ba ya dace ki saurare shi ki ji da abin da yake tafe. Wanda ya damu da ke da halin da kake ciki da ai a tunanin ya wuce wulaƙanci a gare ka".

"Wai da wani yare kike so na yi miki bayani ki fahimta ne? Na gaya miki ba na son ganin wani alaƙa ta ƙara haɗa da wani ɗa na miji ko da kuwa ta gaisawa ce matuƙar shi ɗin ba wai ya kasance muharramina ba ne". Na yi zancen ina ƙoƙarin wuce ta riƙo hannuna gam ta riƙe. "Kar ki manta fa ke kika ba shi dama. Kar ki zama mai ƙarya alƙawari mana". Na ɓanɓare hannunta daga jikina"ki je ki ba shi haƙuri don ba zan iya sauraren sa, ina ji a jikina ma kamar wannan ce haɗuwar mu ta ƙarshe da shi". Ban jira abin da za ta ce ba na ya wucewa ta ciki kai tsaye na nufi ɗakinmu bakina ɗauke da siririyar sallamar.

Na tsuguna har ƙasa na gaishe da Umma da na iske zaune a falon tana irga wasu kuɗaɗen masu yawa, ba ta amsa mini na har na gaji da tsayiwar na tashi zan shiga ɗaki kana ta yi magana a gajarce.

"In kin shiga ɗaki akwai saƙon ki akan katifa".

"To".

Na amsa dashi duk da kuwa ina buƙatan ƙarin bayani sai dai sam ban ga fuskar yin hakan ba. Na wuce cikin ɗakin ina shiga fige hijabina na ajiye na suri ledar da na gani akan gado na buɗe. Hijabi ne a ciki sai kuma ɗinkin doguwar rigan da aka watsawa stone ya fito ya yi ɗasar da shi, wani ihun daɗi da farin ciki na saka a lokaci guda ina faɗawa kan gadon ina tsalla tsabar murnar da na tsinci kaina a cikin sa. Na rumgume hijabin ina ta washe haƙwara tamkar wacce aka biyawa kujerar hajji, tabbas Umma ta faranta mini don na daɗe da cire tsammanin cewa zan yi ankon hijabi da atamfar walimarmu tun bayan abin da ya faru lokacin da Yaya Alhassan ya kawo mini waɗannan kayan. Sai da na ƙarishe murnata na fito na yi wa Umma godiya bakina har kunne, rabon da na tsinci kaina cikin makamamcin irin wannan farin cikin tun kafin wannan iftila'in ya faru da ni. Sai dai kalaman da ta tare ni da su suka sanyaya mini jikina matuƙa.

"Ki dai maida hankali akan karatunki sosai da sosai. Daga ni har mahaifinki mun yarda da ke ne shi yasa muka tura ki wanga islamiyyar, Amatullah...". Kafin ta ce wani abu na tuntsire da kuka har jikina yana rawa. Ta yi sakake tana kallona kamar ba ta taɓa ganina ba. "Kukan kuma na me ye ne? Ki tashi ki ba ni wani waje idan ba za ki rufe min baki ba". Haka na ci gaba da kukan har aka yi ƙiran sallan magriba tun Umma tana mamakina har ta tashi ta bar ni wajen. Na tashi da ƙyar na je na yi alwala na dawo na gabatar da salla tun kafin na yi iddar nake jin wani zazzaɓi mai zafi yana ƙoƙarin riƙe ni. Ina iddar da sallan na ɗauko alƙur'ani na soma karanta cike da shauƙin abin da nake karanta haɗe da sanin fassaransa, haka kawai ranar na tsinci kaina cikin wani irin matsanancin kwanciyar hankali da wanzuwar nutsuwar ruhi. Ji nake yi kamar gari ba zai waye ba balle har mu taro a filin walimar, ranar mitsitsi na kafe akan ba zan je gidan Hajiya Tasalla ba saboda shirye-shiryen walimar man gobe.

Abba ya kawo wake kwano biyu da wasu kayan miyan ya ce a yi alala na sauƙan, sannan ya ba ni naira dubu biyu ya ce na yi zoɓo. Duk yadda na so hana Amira sanar da Mansur labarin walimar sai da ta zagaya ta sanar da shi. A daren ranar ya zo shi ya yi mana siyayya sosai sannan ya ce zai halacci walimar da iznin Allah. Haka muka surfa wanken muka shanya sa muka je muka sayo kayan haɗin zoɓon, ba mu kwanta ba sai ƙarfe sha ɗaya saura na yi wanka na ɗauro alwala na zo na gabatar da salla raka'a biyu, na dinga zagba godiya ga mahaliccina a cikin sujjadata na ƙarshe. Ina ɗagowa na ɗauko alƙur'anina na buɗe na soma karanta ban dakata ba har ƙarfe biyun dare kana na rufe alƙur'anin. Duk yadda na so na runtsa bacci ya gagari idanuna haka na yi juyi har aka ƙira sallan assalatu, ladanin yana ƙwala ƙiran sallan na yi zumbur na tashi na zauna. Na fito na yi alwala ina ƙoƙarin koma ciki Amira ta fito ta dalle mini idanuna da hasken tocilan wayarta tana yi mini tsiya.

"Hafiza Amatullahi".

Na murmusa ina kare hannuna daga hasken tocilan haɗe da faɗin"in za ki yi sallan dai ki yi ki fito mu zo mu yi aiki". "An gama ranki ya daɗe" Ta amsa da shi ban tanka mata ba na koma ciki na yi sallan sai da na ƙara tilawar karatun da zan gabatar a wajen taron kana na fito, muka wanke waken tare da Amira muka kai niƙa muka dawo muka soma ƙulƙulawa kafin garin ya yi haske tunin ya dahu, muka ɗauko lemukan da Mansur ya kawo muka sassaka a leda muka alalen bibbiyu, sai da muka sama leda hamshin da uku.

Muka ƙula zoɓon ma, Amira ta ce tun da mun saka lemo a ledan na bar wannan na ba wa baƙina. Zoɓon kuma nawa da na ƙawayena na yarda da hakan, muna cikin aikin zoɓon Baban Adnan ya fito cikin shigar kayan aikinsa yana karkaɗe hularsa yayin da matarsa take biye da shi tamkar jela. Amira ta taɓo ni"ga mutanan fa. Wallahi sai na ya masa magana ko don na ƙular da ita da safiyar nan".

"Ki rufawa kanki asiri dai". Ba ta ji abin da na ce da ita ba don sai da ta aikata abin da ta yi niyya. Ta lanƙwashe murya tana faɗin"Barka da fitowa Baban Adnan, har an fito ke nan? Allah dai ya saka muku da alkhairi don wannan aikin nakun ba kowa ba ne zai iya yin sa". Take ya washe baki kamar gonar auguda" barka dai Amiratuwa ku na ta aiki ke nan da safen, biki kuke da shi ne ko suna?".

"Au! Wai daman ba ka sani ba? Amatullah ce za ta yi sauƙa yau".

"Sauƙa dai irin wacce na sani na izu sittin ko kuwa?". Ta gyaɗa kanta"ƙwarai kuwa shi fa". Zai yi magana Maman Adnan ta amshe zancen"ya dai kamata ka wuce ka tafi aikin gabanka". Ya juyo ya wurga mata wani mungun kallon da ya sanya ta saurin yi wa bakinta limzami.

Ya zaro wasu kuɗi daga cikin aljihunsa ya irgo guda biyar ya miƙawa Amira"ga wannan to ku ƙara ayi hidima, don ina da aiki da yawa ne ma da zan halatta amma yanzu ma dai bai ɓaci ba sai a yi hotuna a kawo mana mu kashe ƙwarƙwatan idonmu". Kafin Amira ta kai ga amsar kuɗin Maman Adnan ta yi wuf ta kai hannu ta wafce.

"Wallahi ba za ku yi amfani da kuɗi nan ba, me ye haɗin kifi da kaska da har za ta ɗauki kuɗi ka ba su...". Tana rufe bakinta ya wanke ta da mari. "Ba ta kuɗin nan tun kafin na tattaka ki a nan wajen". Babu girma babu azurki ta miƙawa Amira kuɗin ta koma ɗaki tana kuka da faɗin magauta sun shiga tsakanin ta da mijinta. Tun da aka fara dramar har aka ƙare ta ban tsoma bakina a ciki ba har sai da Baban Adnan ya fita kana na ce"yanzu me ye amfanin abin da kika yi kenan? Suna zaman zamansu ki haddasa musu rigima". Ta sheƙe da dariya kafin ta ce"ko banza dai mun sama dubu biyar a ɓagas kuma ta yi asarar hawayenta a banza". Na jinjina kaina cikin takaici ba tare da na ce da ita komai ba.

Haka Ustazu Abdulwahab ya fito ya same mu muka gaishe sa Amira ta shelanta masa cewar yau za mu yi walimar sauƙan alƙur'ani, ai kuwa ya nema waje ya zauna ya soma zubo mini ruwan addu'o'i da yi mini fatan alkhairi. Ya kuma nema da na yi masa kwantacen islamiyyar in Sha Allah amaryarsa za ta je na yi masa. Kafin ƙarfe takwas mun kama komai har na yi wanka na kimtsa cikin sabuwar atamfa da hijabina da ya amshe ni sosai. Abba ma sai da ya yaba da shigar da na yi na ɗauko niƙab na ɗaura a kai, tare muka tafi da Amira abincin kuma su Umma za su taho da shi idan za su zo.

Muna isa cikin islamiyyar Malam Suleiman ya aika aka ƙira mu ni da Al'amin da Aliyu da suka suka sha ankon faran shadda da rawani sai sheƙi da ƙamshi suke bazawa. Sai da muka yi bitan karatun da za mu yi a wajen su, suka gyagygyara mana inda ya kamata kana muka fito lokacin waje har ya ɗau harama. Filin makarantar ya sha ado an kafa rumfuna da kujeru babban taro aka shiyar mana kasancewar an haɗe murnar waliman namun har da na bikin murnan cikar islamiyyar shekaru goma da kafuwa. Muka zazzauna a inda aka tanada domin su masu ɗaukan hoto sai hasko muke yi, na ji kaina ya sara jikina ya ɗauki zafi tsabar zumuɗi ko abincin ban tsaya ci ba haka na taho.

Lokaci guda na ji wajen ya ɗauki kabbara ana faɗin isowan Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe tare da shaƙiƙin ɗansa na miji ɗaya tilo. Duk yadda na so ganinsa cincirindon mutanen da suka kewaye sa sun hana ni ganinsa. Sai da Malam Aminu ya yi magana cikin lasifika kana wajen ya nutsu, ya ƙira Rauda Salisu a matsayin ɗalibar da za ta buɗe taro da addu'a. Sai a lokacin idanuna suka sauƙa akan Sheikh Dawood take ƙirjina ya buga na ƙura masa idanuna, tabbas shi ne wanda na ga ni a tasha har ya yi mini maganar banza da ƙoƙarin taɓa jikina. Haka zalika yanzu ma shi ne zaune cikin kamala da nutsuwa, duk wanda zai gaishe shi sai ya durƙusa har ƙasa.

"Ga can Anty Sawwama da su Yaya Alhassan sun iso, Abba ma ya iso tun ɗazu. Umma ma su a hanya tare da Ummanta mun yi waya da ita ta ce sun kusa isowa". Na tsinkayo amon Amira ta yi zancen a daidai saitin kunnena, na yi kamar zan tashi na je wajen su Malam Suleiman ya yi mini ido akan na koma na zauna, babu yadda na iya haka na koma na zauna. Sai aka gabatar da jawabi sosai sarakuna da ƴan siyasa suka tashi suka yi nasu jawabin kana Malam Aminu ya fara ƙiran Aliyu a matsayin wanda zai fara gabatar da karatu. Ya tashi ya yi karatun cikin tsantsan nutsuwa da fitar da haƙƙin ko wani harrafi, wajen ya ɗauki kabbara aka ayyana shi a matsayin wanda ya zo na uku kuma ya kasance ɗaliba mafi ƙwarzo na shekara. Aka ƙira wani basarake ya ba shi kyautarsa da makaranta ta tanada masa sannan shi ma ya ƙara masa da kyautar zunzurutun kuɗi har naira dubu ɗari tare da fatan alkhairi da addu'o'in da ya dinga yi masa. Har na yi shiri don na sa a raina cewar ni za a ƙira a matsayin ta biyu, haka nan ma sauran ɗaliban don duk sai waigowa suke yi suna kallona. Kwatsam muka yi an ƙira sunan Al'amin jikin kowa ya yi sanyi, hatta shi Al'amin ɗin da kansa don bai fito ba har sai da aka ƙara maimata sunan a karo na biyu kana na tashi. Ya je ya yi karatun jikinsa gabaɗaya babu ƙwari, shi aka ayyana a matsayin wanda ya yi na biyu aka ƙira dan takaran kansilan yakinmu da ba shi kyautarsa da makaranta ta tanada domin shi aka yi musu hoto. Daga haka ya dawo ya zauna gabaɗaya yanayinsa ya sauya.

"Amatullah Munnir".

Malam Aminu ya ƙwala ƙiran sunana a cikin lasifika take zuffa ya keto mini ina ɗago kaina muka haɗa ido da Abbana. Fuskarsa a washe cikin tsantsan farin cikin da har sai da na hawaye a idanunsa. Na tashi na isa kan munbarin ina karantu auziya da bismillah wajen ta kaure da kabbara na ci gaba da karatun suratul Maryam cikin sanyin murya wajen ya yi shuru ina cikin karanton na hango shigowar Umma da Umman Amira. Sai da na karance suran tas kana aka yi kabbara da alama hatta su Malam Suleiman sun ji daɗin karatun da na yi fiye da na sauran.

Aka bayyana ni a matsayin wacce ta yi na ɗaya. Aka ƙira wani basarake ya ba ni kyautata ya kuma ba ni wasu kuɗaɗen da ban san adadin yawansu, zan tafi aka ce na tsaya aka kara ayyana ni a mashin gwarzuwan shekara kuma ɗaliba mace ta farko ta yi sama iri wannan nasarar cikin shekaru goma da kafa islamiyyar. Sannan aka ayyana ni a matsayin ɗaliba mafi hazaƙa a cikin ajinmu. Malam Aminu ya ɗauko kyautar da za a ba ni ya ƙira sunan Sheikh Dawood a matsayin wanda zai karrama ni da kyauta ya taso cikin shirgar alfarma, tun da ya taso nake bin sa da kallo har ya iso wajen. Ya karɓa lasifikan ya soma jawabi.

"Yau na cika da murna da farin ciki ganin yadda aka yaye ɗalibai masu yawan gaske kuma duk sun haddace littafi mai tsarki. Ina jinjinawa malamanku ƙwarai da gaske da suka tsaya kai da fata wajen tabbatar da sun sama ilmi mai inganci. Wannan ɗalibar da ta yi na ɗaya kuma ina yi mata fatan alkhairi da addu'ar dacewa a cikin rayuwarta. Sannan idan mahaifi ko mahaifiyarta yana wajen wannan taron ina so a taso ya hau kan munbari domin na yi masa wani albishir". Aka dinga kwarara kabbara har Abba ya iso wajen suka yi musaba kana Sheikh Dawood ya ci gaba da jawabinsa.

"Bawan Allah da farko ina taya ka murna domin Allah ya yi maka arzikin da ba kowa ne yake dacewa da irin sa. Wannan É—iya taka zinariya ce a cikin zinaru, idan akwai wani karatun da take yi ko kuma za ta fara to na É—auki É—awainiyyarta daga yanzu har ta gama shi, idan kuma daga nan aure za ta yi to na É—auki nauyin yi mata kayan É—aki da duk wani abun da ake yi mace yayin bikinta. Zan karrama ta cikin alkyabba mafi daraja da tsada".

Wajen gabaɗaya ya ruɗe ya sa aka ɗauko wata alkyabba mai tsananin sheƙi da ƙyalle wanda ko da daga kallo guda ka san cewa mai tsada ce balle kuma ace ka murza jikinta. Ya ɗaura mini ita a kaina idanumu suka sarƙafe cikin na juna, take na ji raina yana tafasa sakamakon wani irin kallon da yake yi mini da na kasa gano ma'anarsa. Abbana sai godiya yake zuba wa yana yi yana ƙarawa, ɗan takarar kansila da sarakuna duk suka gaisa da shi tare da yi mini kyaututtuka masu tsoka.

"Ina taya ki murna matuƙa kuma ina addu'ar Allah ya sanya albarka a karatunki".

Da sauri na ɗago kaina don tabbatar da mamallakin wannan muryar da ta kasa gogewa daga cikin kaina. Caraf idanuna suka sauƙa akan sa yana tsaye a gabana fuskar ɗauke da maɗaukaki murmushi. Hannunsa riƙe da alƙur'ani da aka yi ado da wasu irin zare masu jan hankali. Ya miƙo sai dai mamaki ya hana ni karɓa balle na ce da shi wani abu. Sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin na ce"Muhammad Taufik ko?". Ya sakar mini da murmushin yana faɗin"karɓi mana kin tsaya ki na ta kallo na". Jikina a sanyaye tamkar kazar da aka kwararawa ruwan zafi na kai hannu na amsa alƙur'anin.

"Ina taya ki murna Allah ya albarkacin karatun da aka yi. Kafin ku tafi zan neme ki". Kaina kawai na girgiza masa kafin na ce wani abu Malam Aminu ya iso wajen ya ƙira gefe. "Amatullah mu je Sheikh yana son magana da ke". Take na ji ƙirjina ya buga ya yi gaba ina bin shi a baya har gaban Sheikh na durƙusa a ƙasa, ya ƙura mini idanu kamar zai cinye ni ɗanya ya ɗauko wasu littattafai ya miƙo mini na miƙa hannu zan karɓa caraf na ji ya riƙe hannuna gam. Babu shiri na ɗago idona ina kallonsa sai dai ko a jikinsa sai murza mini hannuwa da yake, sai da na sa ƙarfi kafin na kwace hannuna. Na yi zumbur zan tashi wani jiri ya ɗauke ni duk yadda na so tsayiwa akan ƙafata lamarin ya ci tura, Malam Aminu da yake kusa da ni ya yi saurin karɓan alƙur'anin da yake hannunsa da sauran kyaututtukan.

Luu na yi baya na faɗi a ƙasa ina jin kaina yana juyawa jikina gaba ya sake, mutane suka cika a kaina ina ganin su dishi-dishi. "Amatullah lafiya kike kuwa?". Muryar Yaya Alhassan kenan da ya kasance abu na ƙarshe da na ji kafin hankalina ya gushe, aka ɗauke ni ridi-ridi sai asibiti. A hankali na soma buɗe idanuna da na ji sun yi mini matuƙar nauyi ina ƙarewa ɗakin da nake cikinsa kallo. Sai da na ƙarewa ɗakin kallo na tabbatar da cewar asibiti ne. Ummata, Umma Amira, Anty Sawwama da kuma Amira, Anty Zulaihatu su kenan a cikin ɗakin. Suka fara jeranta mini sannu wani na bin wani kafin na kai ga amsawa Abba, Yaya Alhassan, Umar da Malam Suleiman suka shigo cikin ɗakin cikin wani irin matsanancin firgici da tashin hankali, na lura idon Abba har da hawaye ya kafe ni da idanuna kamar ya ga wata sabuwar halitta.

Kafin na yi aune ko na ce wani abu tunin Abba ya wanke ni da mari, ina ɗagowa ya ƙara wanka mini wani marin. Su Umma duk suka tattaso suna tambayar ko lafiya. [10/25, 8:15 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_______________________________________

Page 3️⃣6️⃣

"Munniru lafiya kuwa? Za ka ɗauke yarinya da mari alhalin tana gadon asibiti cikin jinya". Ta juya tana duban Yaya Alhassan da tun da suka shiga kansa yake ƙasa ya gaza ɗago ido balle ya kalli kowa. "Alhassan wai me ye likitan ya shaida muku ne? Me yake faruwa da Amatullah ɗin?". Bai ɗago kansa ya kalle ta ba kamar yadda bai amsa mata ba.

"Ba fa zai yiyuwa a tisa min ɗiya a gaba da duka ba akan wani dalilin? Tana cikin jinya idan ba a lallashe ta ba ai ba za tada mata da hankali ba, wallahi ba za ta saɓu ba wai bindiga a ruwa". "Hafsatu ki rufe min baki tun kafin na yi sassaɓa miki a nan wajen nan. Kin cuce ni kin cuci rayuwar ƴarki. Hafsatu kin wargaza min duk tanadi da shirin da na yi wa rayuwar Amatullah, kin jefa ni cikin kunya da tsoron haɗuwa da mutane balle har na shiga cikin su na yi mu'amala da su, tsakani na da ke Allah ya isa ban yafe miki". Gabaɗaya wajen ya ɗauki salati da sallallami Umma ta hau hayagaga ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, sai da Umman Amira ta taso ta riƙe ta tana ba ta haƙuri da tunatar da ita cewar a asibiti fa muke. Kuka nake yi da dukkan ƙarfina jikina gabaɗaya yana rawa tamkar mazari haƙwarana suna karabɗiya da juna kamar jinriran kazar da ruwa ya yi wa ɗan banzan duka. "Don Allah ku ba mu waje ina son ganawa da Amatullah ita kaɗai". Abba ya yi zancen cikin tsantsan tashin hankali da ruɗewan da ya bayyana har a cikin muryarsa.

"Ai ba kai kaɗai ka haifa yarinyar ba Manniru don haka babu inda zan je, komai a gaba na za ku tattaunawa. Ai ni ma ina da iko akanta kamar yadda kake jin kai ma kana da cikakken iko akan ta". Umma ta yi zancen cikin isa da izgilanci da ƙyar Umman Amira ta shawo kanta ta yarda ta fita daga cikin ɗakin, ya rage daga ni sai Abba a cikin ɗakin har zuwa lokacin kuka nake yi duk da ban san abin da yake faruwa ba amma na yi imanin duk abin da zai sanya Abba shiga makamancin irin wannan tashin gami da furta zafafan kalamai ba ƙaramin abu ba ne.

Ya zauna a kusa da ƙafafuna ya kafe ni da ido lamarin da ya ƙara sanya jikina yin sanyi ƙalau don bai taɓa yi mini irin wannan dogo kallon ba. "Amatullah".

"Na'am Abba". Na amsa muryata a kashe tamkar wacce aka sanya igiyar kirtani aka shaƙewa wuya tamau. "Amatullah ki na ɗaya daga cikin jerin matan da na yarda da su a cikin rayuwata kuma na yi imanin ba za su taɓa cin amanata ko su kunyata ni ba. Tun ranar da kika zo duniya aka cirewa mahaifiyarki mahaifa sakamakon irin wahala da azabar da ta sha tun daga rainon cikinki har izuwa lokacin haihuwarki. Ya tabbatar ba za ta sake haihuwa ba a duniya haka ni ma inda ba wata macen na aura to ba zan sake haihuwa ba tun da an raba ta da mahaifa, tun daga lokacin na yuƙurce a raina cewar zan tarbiyyartar da ke na ba ki kula na ba ki ilmin addini ta yadda za ki zame mini madadin ƴaƴa goma a gare ni, kuma alhamdulillah haƙiƙa na cika da farin cikin a yau ganin kin haddace littafin alƙur'ani akan ki babu abin da zan ce Allah sai dai godiya. Amma me yasa kika zaɓi ki jirkita min wannan ranar ta farin ciki zuwa ta baƙi ciki da kasance rana mafi muni a gare ni?".

Bai ba ni daman cewa wani abu ba ya ci gaba da cewa"Allah ne shaidana domin ba ya bacci yana ganin duk abin da yake na zahiri da na baɗili. Ya san na kula da amanarki da ya ba ni daidai da rana guda ban taɓa barin ki kin sauƙa daga tafarkin addinin da Manzon ya zo mana da shi ba. Amma Amatullah me yasa kika zaɓa ki saka min ta wannan hanyar? Me yasa kika zaɓa ki shayar da zuciyata raɗaɗin baƙin cikin da ba zai taɓa bari na yi rayuwa cikin farin ciki da walwala ba?". Na tuntsire da wani irin kuka mai ƙarfi numfashina har ɗaukewa yake yi.

"Amatullah likita ya tabbatar mana da cewar ki na ɗauke da ciki a jikinki na tsawon sati biyu, Uwata wa ya yi miki ciki?". Mutuwa zaune na yi don cak numfashina ya ɗauke na wucen gadi na dawo da ni da gawa ba mu da maraba. Na ji duniyar gabaɗaya tana juya mini ban dawo daidai ba sai na ji sauƙan wani abu mai zafi a fuska da ya ratsa dukkan sassan jikina wanda ina da tabbacin ruwa Abba ya watsa mini a fuska. Na ci gaba da wani irin kuka wanda ya yanayin da irin zafin da nake cikin a ƙirjina ba na jin akwai kalmomi da za su wadatar wajen fassaruwansa. Duk yadda na so na yu magana baki ya ƙi ba ni haɗin kaina furta abin da yake yi mini ƙaiƙayi a cikin raina. Hankalina ya kai ƙololuwan tashin ganin hawaye suna zuba daga idanun Abba ya sukunyar da kansa ƙasa ba tare da ya ƙara cewa da ni komai ba. Tun ina yin kukan idanuna suna zubar da ƙwalla har sai na da idanuna suka kafe tsiyayar da komai.

"Abba". Na furta cikin wani iriyar muryar mai cike da rauni haɗi da maɗaukakin tashin hankalin da ya jirkice da rashin nutsuwa, shuru bai tanka mini na ƙara ƙira a karo na biyu nan ma shuru ina jijjiga shi na ga ya faɗi a ƙasa idanunsa sun kakkafe bakinsa ya koma gefe guda. Na ɗaura hannu aka na fasa ihun da ya sanya su Umma faɗowa cikin ɗakin tamkar an jefo shi. "Innalillahi wa inna ilahirin alaihir raji'un! Me ya same shi?". Anty Sawwama ta jefa mini tambayar da na gaza amsa wa illa kukan da nake ji jikina yana rawa.

Yaya Alhassan da Malam Aminu suka ɗaga shi suka kwantar da shi akan gadon da na tashi, Umman Amira ta fita ta ƙira likita ya shigo ya umarce mu da duk mu fita. Sai dai ni kam na kasa motsa ƙafafuna daga inda nake tsaye duk da jan hannuna da Amira take yi kamar za ta fincike shi daga gangar jikina. Ganin halin da nake ciki ya san likitan da kansa cewa a ƙyale ni haka suka fita suka bar ni a wajen, na ja saƙararran gangar jikina na isa na durƙusa gaban gadon da Abba yake kwance na riƙe hannunsa ina murzawa a hankali. Likitoci suka rufu akan sa suna ta ƙoƙarin ceto rayuwarsa domin har jijjiga ya fara aka ɗauko wani abu kamar dutsin guga ana danna masa a ƙirjinsa.

Sun ɗau lokaci a haka har sai da komai ya daidaita aka maƙala masa roban numfashi. "Ki yi haƙuri ki tashi ki fita waje, in sha Allah zai sama lafiya kamar yadda kike gani ma ai yanzu da sauƙi". Likitan ya furta cikin sanyin harshe da sassauta amonsa. Na cira kai ina kallonsa"don Allah zai tashi kuwa?".

"Me zai hana shi tashi? In sha Allah zai tashi ya sama lafiya ya ci gaba da gudanar da rayuwarsa tamkar babu wani abun da ya taɓa faruwa".

Ban ce da shi komai ba na kuma fashewa da wani kukan ina murza hannun Abba da yake cikin nawa. Lokacin guda har fuskarsa ta faɗa tafin hannunsa ya yi sanyi ƙalau kamar wanda aka ɗaurawa ƙanƙara. Aka bankaɗo ƙofar ɗakin na waigo ina ganin Umma da ta faɗo cikin ɗakin a fusace tamkar kububuwa tsoro ya mamaye mini ƙalbina, kafin na yi wani yunƙuri na ji ta rufe ni da duka da ko'ina ana ƙoƙarin raba ni da numfashina. Ta buga kaina a jikin ƙarfe gadon take jini ya ce sallama Alaikum ya fara malala kamar da bakin ƙwarya. Da ƙyar likitotin suka ɓanɓare ta daga jikina duk da hakan bakinta bai fasa furta mini mungayen kalmomi ba.

"Allah ya isa tsakanina da ke Amatullah. Da haihuwarki irin ki gwara na rayu har na koma ga mahaliccina ba tare da na yi ko ɓatan wata ba, da na san haka za ki zame min annoba da tun ranar da kika zo duniya na murɗe miki wuya kin mutu kowa ya huta, na tsane ki na tsani kallon ki. Da wannan abun kunyar da kika ɗauko mana gwara a kawo min gawarki a gaba na hankalina sai ya fi kwanciya".

Na rarrafo na zo na riƙe ƙafafunta"don girman zatin Allah Umma ki yi haƙuri kar ki furta mini kalmar da za su jirkita tunanina. Umma ki ba ni dama na yi miki bayani wallahi ƙaddara ce ta faɗa mini...". Tun kafin na ƙarisa ta sa ƙafa ta yi bol da ni na faɗi gefe guda, babu shiri na saki ihu saboda zafin da na ji ya ratsa har cikin ƙoƙon kaina. "Ke ba ki da hankali ne? Idan kika ji mata ciwo fa? Ko me ta yi ai kamata ya yi ki bari sai kun je gida ko kin manta cewa nan asibiti kuma a cikin ɗakin majinyaci kuke kike wannan hayaniyan. Ku tattara ku fita waje don ba ma buƙatar hayaniya da ɗaga murya a nan".

Likitan ya yi zancen cikin ƙololuwar ɓacin rai da takaicin abin da Umma ta aikata, Umman Amira da Anty Sawwama suka shigo suka fitar da Umma Amira ta ɗago ni likitan ya ce na fito a bar Abba ya huta muka je wani waje a cikin asibitin aka yi mini dressing ɗin goshina da yake zubar da jini. Ana gamawa Anty Sawwama ta ce mu tafi gida Yaya Alhassan zai zauna a wajen Abba kafin a ga abin da hali zai yi.

"Anty don Allah ku yi haƙuri ku bar ni a nan...". Kafin na rufe bakina ta katse ni"kar ki yi gardama da ni Amatullah ki wuce mu tafi". Ban ƙara cewa komai don ban ga fuskar hakan daga gare ta ba. Malam Aminu da Yaya Alhassan da Muhammad Taukif suka iso wajen a tare duk su ukun suka jefo mini wani matsanancin kallo. Ba kamar Malam Aminu da har cije baki yake yi, shi ya fara tafiya bayan Anty Sawwama ta zabga masa godiyar ɗawainiyyar da ya yi.

"Anty na ga kamar ku ma tafiya za ku yi ko zan sauƙo a gida. Daga nan ni ma sai na wuce". Muhammad Taufik ya yi zancen idanunsa akan Anty Sawwama. "A'a ɗan nan tun da lamarin nan ya faru kake ɗawainiyya da mu, kai ka kawo mu asibitin nan mai tsada a cikin motarka sannan ka biya kuɗin komai da komai, ɗawainiyyar ai sai ta yi yawa ka yi tafiyarka kawai za mu hau motar hanya".

"Mahaifina ya umarce ni da na tsaya akan lamarin wannan baiwar Allahn nan har sai na tabbatar da cewar komai ya warware. Don haka ina roƙonki da ki taimaka mini wajen cika umarnin mahaifina". Shuru Anty Sawwama ta yi kawai tana jijjiga kanta kana ta ce"shikenan to mun gode". Suka yi sallama da Yaya Alhassan bayan sun yi musayar lambar wayan juna ya yi gaba muna biye da shi a bayan, a Umma da Umman Amira tunin sun tafi gida. Kamar motar gawa tun da muka shiga babu wanda ko tari har muka isa gidan, Anty Sawwama da Amira suka yi masa godiya ni kam na kasa cewa komai illa kallon juna da muke yi ni da shi.

Muna sanya ƙafarmu a cikin filin tsakar gidan Umma ta tare mu tamkar daman jiran shigowarmu take yi. "Kar ki sake ki nufo ɗakin nan shegiya tsinanniya kawai. Amatullah kin ja min abin magana da yamaɗiɗi a cikin gari ki jawo min abin kunya, kar ki matso inda don babu makawa matuƙar muka haɗa wajen zama da ke zuciya za ta iya ɗiba na na murɗe miki wuya".

"Subhanallahi! Haba Hafsatu idan hankali ya gushe ai hankali ake sawa a nemo shi. Ki yayyafawa zuciyarki ruwan sanyi sai a zauna a nemo yadda za a ɗinke wannan ɓarakar da ta same mu gabaɗaya".

Kalaman Anty Sawwama kamar aka fusata Umma suka yi ta cika ta yi fam. "Maman Umar ki fitar da yarinyar nan daga cikin gidan duk kafin na biye zuciyata na aikata abin da daga ni har ke za mu zo muna cizon ɗan tsaya daga baya". Anty Sawwama ta dafe kai"innalillahi wa inna ilahirin raji'un". Idanuna suka daina gano mini komai illa gilmawar baƙin duhu duk da haka na ja jiki na isa gaban Umma na riƙe ƙafafunta.

"Umma idan ba ki rufa mini asiri ba waye zai rufa mini asiri a cikin duniyar nan. Umma ki ba ni dama na yi miki bayanin abin da ya faru wallahi ba laifina ba ne ƙaddara ce ta Ubangiji ta faɗa mini". Ta sanya kafa ta yi kutufol da ni sai da na yi tanbulin goshina da aka yi wa dressing ya bugu da ƙasa, jini ya soma zuba da goshi da hancina. Anty Sawwama ta yi saurin ɗago ni sai dai na kasa tsayiwa akan ƙafafuna sai da ta riƙe ni kam. Duk rashin tausayin mutanen gidanmu a ranar sai da na tausayina kwance a fuskarsu. Matar Uszatu ta ce na je ɗakinta na zauna Umma ta daka tsalle ta dire a duk wanda ya ba ni wajen rakaɓewa sai ta yi masa ɗiban albarka mai wasali, haka Anty Sawwama ta riƙo ni ina kuka ita ma tana yi haka nan ma Amira da ƙyar aka ɓanbare ta daga jikina muna kuka wiwi muka fito daga cikin gidan.

Muna fitowa idanuna suka sauƙa akan Muhammad Taukif ya na ganin mu ya yi saurin fitowa daga cikin motarsa ya fito. "Hajiya lafiya na ga kun shiga kun fito?". Maimakon ta amsa masa sai ta ƙara jefa masa wata tambayar"kana nan ba ka tafi ba?". "Yanzu nake son tafiya sai kuma na ga fitowarku. Lafiya kuwa?".

"Lafiya ƙalau yanayin jikin natan ne ƙawa babu daɗi, shi ne za mu je gidana da ita".

"To ku shiga na kai ku mana".

"A'a kar ka damu za mu nema abin hawa". Da hanzari ya katse ta"Hajiya umarnin mahaifina nake cikawa, don yana girmamawa da mutunta duk wanda ya haddace littafin mai tsarki yana musu hidima da ƙarfinsa da kuma aljihunsa. Don Allah ku shiga na kai ku".

Ba ta musu ba ta ja hannuna muka shiga cikin motar har muka isa kuka nake yi, mu fito za mu shiga cikin gidan nan na ji ya ƙira sunana na tsaya cak.

"Amatullah".

Na waigo muna kallon juna"Allah ya ba ki lafiya". Na kasa amsawa da kalmomin baka sai a cikin zuciyata na amsa. Na muka ƙarisa shiga cikin gidan ina shiga cikin ɗakin na zube akan katifanta ina ta kuka. Anty Zulaihatu ta shigo ta yi mini dukkanin lallashin duniya amma na kasa daina kukan, Anty Sawwama ita ma ta shigo.

"Amatullah tashi ki zauna mu yi magana".

"Anty ba zan iya tashi ba".

Cikin kakkauran murya ta furta"Amatullah waye ya yi miki ciki?". Numfashina ya tsaya na lokaci guda saboda cakwakiyar da yake cikin tambayar da ta yi mini. Wanda ni ma kaina ban san wanda ya aikata mini hakan balle na sama kalaman kare kaina. Abu na sani kuma na yarda da shi shi ne ƙaddarata ta zo a haka babu yadda zan yi na guje mata. [10/26, 3:09 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_______________________________________

Page 3️⃣7️⃣

Numfashi nake ta sauƙewa wani na bin wani ga jinin da yake sauƙowa daga goshina yana wanke mini fuskana, cikin taushin murya na ji ta ƙara faɗin"Amatullah ki taimaka ki sanar mu wanda ya yi miki ciki. Ki dubi halin da mahaifinki yake ciki, a cikin rayuwarsa kina ɗaga daga cikin abin da yake matuƙar alfahari da su tun da kika zo duniya ya kalle ki har kika girma farin cikinsa ya ninku. A lokuta da yawa darajarki mahaifiyarki take ci yake ɗaga mata ƙafa akan dukkan abubuwan da take yi, domin a cewarsa ita ma ta taka rawar gani ta haifa mata ɗiya sannan a dalilin hakan aka cire mata mahaifa yana ganin inya rabu da ita bai yi mata adalci ba. Amatullah iyayenki sun yi ɗawainiyya da ke irin ɗawainiyyar da fi ƙarfin baki ya suffanta shi cikin kalmomi, mahaifiyarki ta sha wahalar rainon cikinki lokacin haihuwarki ta yi dogon naƙudan da har sai da muka cire rai da cewar za ta rayu. Mahaifinki ya yi wahala da ke tun ki na ciki har kawo girmanki ya yi duk mai yiyuwa wajen ganin ya tanada miki more rayuwa daidai ƙarfin aljihunsa, ya ba ki ilmi har sai da yau aka wayi gari kin kammala haddan alƙur'ani. Amma ki rasa da me ye za ki saka musu sai da wannan abun shin sun cancanci hakan ne daga gare ki?".

"Wallahi ƙaddara ce ta faɗa mini ba da son raina ba, Anty ki yarda da ni ba zan taɓa wofantar da tarbiyyan da kuka har ni ko na sauƙa daga kan gwadaben da kuka ɗaura ni akai ba". Ta katse ni"waye ya yi miki ciki?".

"Ban san shi ba ban taɓa ganin sa hasalima shi ma bai sanni ba, bai taɓa ganin fuskata ba". A fusace ta miƙe irin fusatar da tun da uwata ta kawo ni duniya na girma na yi hankali ban taɓa ganin ta cikin makamancinsa ba. "Wani irin magana ce haka wanda hankali ba zai ɗauke shi ba? Kamar ya ya ba ki san shi ba?".

"Wallahi tallahi ban san shi ba ba mu taɓa ganin juna ba ni da shi".

"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!". Ta furta cike da damuwa tana dafe kanta, Anty Zulaihatu ta tashi ta riƙe ta don tana ƙoƙarin faɗuwa. Ta zaunar da ita tana faɗin"don Allah Umma ki yi haƙuri a bi komai a sannu. Son samu ma a bar ta kar kowa ya ƙara yi mata maganar har sai ta dawo cikin hayyacinta nutsuwarta ta daidaita lamuran sun dawo daidai". Numfashinta ne ya soma sama da ƙasa na fita waje da sauri na ɗebo mata ruwa zan kai mata muka yi kiciɓus da Umar ya shigo gidan. Ya sha gabana"ina za ki je?".

Cikin rawan jiki da na murya na ce"ruwa zan kai wa Anty numfashinta sai sama-sama yake yi". Ya kwace kofin ruwan yana jifa na da wani matsiyacin kallo na bi bayan sa da sauri, muka shiga cikin ɗakin. Anty Zulaihatu ta karɓa kofin ruwan ta yi tofin addu'o'i ta ba ta sha ragowar kuma ta shafa mata a jikinta take ta koma sauƙe ajiyar zuciya wani na bin wani tamkar wacce ta yi gudun ceton rai. Anty Zulaihatu ta gyara mata zamanta ta kwantar da ita cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya ɗauke ta. Duk muka sauƙe ajiyan zuciya muna hamdala da lamarin ya zo da sauƙi haka don tana da hawan jini mai sarƙarƙiya gefe guda kuma tana cutar numfashi.

"Anty wai me ye wannan take yi a cikin gidan nan ne?". Umar ya yi zancen cikin haÉ—e rai da zafin zuciya. "Amatullah ce fa ko ba ka gane ta ba ne? Nan kamar gida ne a gare ta ai, tana da ikon zuwa a duk sanda take so kuma ta yi niyya".

"Anty a da kenan ba yanzu za ta watsa mana ƙasa a idanunmu ba. Cikin shege fa Amatullah waye ya yi miki ciki? Me ya sa za ki yi mana haka?". Fayau Anty Sawwama ta ɗauke shi da mari ta nuna shi da ƴar manuniyar ƴatsarsa"Umar ba ka yi hauka ne ko kuma shaye-shaye ka fara yi ba mu sani ba?. Ashe ba za ka iya rufawa ƴar uwarka asiri a bisa ƙaddarar da ta same ta ba". Ya dafe gefen kuncinsa da ta watsa masa marin"Anty ƙaddara? Ƙaddara fa kika ce? Amatullah ba yarinya ba ce ta ba wa shekaru goma sha biyar baya. In ma ƙaddarar ce me yasa tun lokacin da abin ya faru ba ta sanar ba har sai da ciki ya ɓullu a jikinta?".

Tana ada aya a nan tashi ya fice daga cikin ɗakin fu cikin saurin kamar mai tafiyan akan iska. Anty Zulaihatu ta dafe kanta"innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Allahuma ajirni fi musifati". Kasa motsa na yi daga inda nake zauna izuwa yanzu kam ma kukan ma na daina illa kukan zucin da nake yi mai matuƙar ƙuna da raɗaɗi. Ina nan zaune har Anty Zulaihatu ta tashi ta fita babu jimawa ta dawo ta zauna a kusa da ni.

"Ki tashi ki je ki yi wanka, ki gyara jikinki. Ki sauya kaya sannan ki zo ki ci abinci sai ki kwanta ki huta". Na ɗago rinannun idanuna ina kallon ta da shi sai dai bakin ya kasa furta komai. Ta dafa kafaɗata" Amatullah ki yi haƙuri na san ba zan iya kwatanta girman damuwar da kike ciki ba, amma tabbas ni ma ina cikin damuwa domin duk abin da ya same ki haƙiƙa kai tsaye ni ma ya shafe ni. Ki miƙa lmauranki ga Allah ki daidaita nutsuwarki sannan ki tanadi bayanan da za ki yi wa iyayenmu". Da taimakon ta na miƙe tsaye ta riƙo ni ta kai ni har ƙofar banɗakin na shiga. Na durƙushe a gaban bokatin ruwan da ta kai mini ina kukan zuci kaina har wani ciwo yake yi mini idanuna suka kumbura tsumtim.

"Allah na tuba ka yafe mini. Allah ya kawo mini ɗauki da mafita. Ya Allah na yarda babu kuskure a cikin hukuncinka kuma ba ka ɗaurawa Bawa abin da ba zai iya ba, Ya Ubangijin sammai da ƙassai bakwai ya Ubangijin talikai da dukkan wasu halittu ina roƙon da ka tashi kafaɗun Abbana ka ba shi lafiya, kar ka bari baƙin ciki ya yi silar faɗawarsa cikin wani irin yanayi".

A raunane na ƙare zancen cikin dushashewar murya, da ƙyar na miƙe akan ƙafafuna saboda rawar da suke yi na yi wanka na fito sai da na yi alwala kana na shiga cikin ɗakin. Anty Zulaihatu ta ba ni zani da riga t-shirt na saka kasancewar gidan babu ɗiya mace wannan ma a cikin kayan Anty Sawwama ta binciko mini. A zaune na yi sallan saboda ba zan iya tsayiwa ba, na daɗe a sujjadata ta ƙarshe ina kuka kafin na ɗago na ɗaga hannayena dukka biyu sama sai dai na kasa cewa ko kanzil. Ko buɗe abincin da Anty Zulaihatu ta kawo mini ban iya ba na kifa kaina da gwiwa ina ta sauƙe ajiyan numfashi.

Haka na wuni cikin wani irin mungun yanayin da ban taɓa tsintar kaina a cikinsa ba tun da na zo duniya sai bayan sallan la'asar Anty Sawwama ta farka. Anty Zulaihatu ta kai mata ruwa ta yi wanka ta zo ta gabatar da salla ita ma ta kasa cin abincin sai cewa ta yi a ƙira mata Alhassan, Anty Zulaihatu ta ƙira shi ta miƙa mata wayar bayan ta sanya ta a amsa-kuwwa.

"Alhassan ya mai jikin?".

"Da sauƙi dai kawai za a ce Umma, amma tabbas Kawu yana jin jiki wallahi. Bayan tafiyarku ma sun mayar da shi emergency sannan sun hana kowa ya shiga ya gan sa, sun ce zuwa safiya idan babu wani ci gaba dole za su tura mu asibitin dake maƙwabciyar jihar nan, wanda su daman masu irin laluransa kawai suke dubawa".

"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Wai me ye suka ce yana damunsa ne haka?". Ya yi ɗan jim kafin can ya ce"Umma gefensa ɗaya ne ya shanye sannan zuciyarsa ta kumbura. Dole akwai buƙatar a yi masa gashin ƙashi da aiki a zuciya". Tun kafin ya ƙarisa zancen muka saka salati wani kuka marar control ya ƙwace mini na so ma yin sa da dukkan ƙarfina. Anty Zulaihatu ta karɓa wayan" in mun zo za mu sama ganin sa ne?".

"Babu wanda ake bari ya gansa likitotin ne kawai suke shiga, kuma sun dawowa za mu yi don sun ce su a tsarin su ba a kwana a tare da majinyancin da aka kai emergency. Suna da ƙwararrun ma'aikata da kuma masu kula da majinyanta". A rikice Anty Sawwama ta furta"ku kuka shi da waye za a bar shi?".

"Umma ki kwantar da hankalinki fa babu wani abun da zai same shi. Idan na dawo sai mu gama maganan". Da aka suka yi sallama duk muka zauna jimgum-jimgum kamar masu karɓan gaisuwar mutuwa. Sai bayan sallan isha'i Yaya Alhassan da Amir suka dawo suka ƙara yi mana bayanin halin da Abba yake ciki, ni dai ina rakuɓe a gefe guda ina jin na wanin zazzaɓi mai zafi yana ƙoƙarin rufe ni.

Anty Sawwama ta umarce mu da mu tashi mu je mu alwala kowa ya karanta alƙur'ani iya yadda ya sawwaƙa mu yi tawassali da hakan wajen nemawa Abba lafiya a wajen wanda babu abin da ya gagari ƙarfin ikonsa. Hakan muka yi ba mu kwanta ba sai ƙarfe ɗayan dare, daga Yaya Alhassan har Amir tun da suka shigo cikin su wanda ya ce mini ko kanzil haka nan ba su buƙacin jin dalilin kasancewata a gidan ba. Yadda nake jin jikina a wannan daren ban taɓa zaton za a wayi gari da ni cikin rayayyu ba, gaba ɗaya na cire tsammani da rayuwa na saddaƙar da komai na miƙa wuya ina jiran yadda Ubangiji zai yi da ni. Don na yadda duk abin da ya zartar hakan shi ne daidai kuma babu kuskure a cikin sa. Yadda na ga rana haka na ga ban runtsa ko na sakon guda ba. Daga masallacin sallan asubahi Yaya Alhassan da Amir suka wuce asibiti wajen Abba.

Wajajen ƙarfe goma Anty Sawwama da Umar suka shirya za su tafi asibitin na dage akan zan biso na je na ga Abba amma ta hana ni babu yadda na iya dole na haƙura muka zauna da Anty Zulaihatu zaman jiran tsammani. Ba su daɗe da tafiya ba Amira ta zo ta ina jin sallamarta na zabura da sauri na fito filin tsakar gidan, muka rumgume juna muna wani irin kuka mai ban tausayi da ƙyar Anty Zulaihatu ta lallashe mu muka tashi muka cikin ɗakin.

"Amira kin ga yadda rayuwa ta yi da ni ko? Ni kuma tawa salon ƙaddarar kenan". Ta riƙo hannuna ta sanya cikin nata cike da tausayi ta soma cewa" komai yana da lokaci Amatullah komai watarana zai zo ƙarshe zai zama labari har ya shuɗe. Don Allah ki cire damuwar komai a ranki". "Ta ya ya kike tunanin zan iya cire damuwa daga cikin raina? Ba ni da wannan ikon Amira, ba ni da wani buri yanzu da ya wuce na ga Abba ko da kuwa shi ne abu na ƙarshe da idanuna da su yi tozali da shi kafin rai ya yi bankwana da gangar jikina". Ta kai tafin hannunta ta rufe mini bakina ruf.

"In sha Allah ma babu wanda zai mutu. Kuma komai zai zo ƙarshe".

Na kasa cewa da ita komai illa kukan da na fashe da shi ina yi ita ma tana yi babu mai lallashin wani a tsakaninmu. Duk ƙarfin halin Anty Zulaihatu ma sai ta yi kukan haka muka sha kukan har muka gaji. Na ɗago idona ina kallon Amira da ita duk damuwa ya bayyana a fuskarta.

"Umma ba ta neme ni ba ko Amira?". Ta É—an yi jim ba tare da ta ba ni amsa ba. Shurunta ya sani cewa"ba ta neme ni ba ko? Na kan ji ana cewa uwa ita ce majingina kuma mafaka a wajen Æ´aÆ´anta, na sha jin a cikin labarun hikayoyi cewar uwa ce kaÉ—ai ba ta juyawa Æ´aÆ´anta baya ita ce kaÉ—ai take rufawa Æ´aÆ´anta asira komai munin abin da suka aikata. Amma me yasa tawa uwar ta bambamta da sauran?".

"Umma ta na son ki Amatullah ke ma shaida don ta yi abubuwa da yawa da bayyanar da hakan. Ki yi mata uzuri akan abin da ta aikata ki ba ta lokaci ta huci sannan ku yi magana". Amira ta yi kalaman cikin sigar son kwantar mini da hankali. Haka muka zauna har sai bayan sallan asr Anty Sawwama da Umar suka dawo cikin wani irin yanayi na sanyin jiki. Nan suke shaida mana cewar an tafi da Abba asibitin ƙwararru dake maƙwabtaka da jiharmu ta kuma ƙara bayyana mana cewar yana buƙatar addu'armu, lamarin da ya ƙara gigita nutsuwar da ta yi saura akan jikina kuka nake yi tuburan jikina yana rawa tamkar mai shafan iskokai sai Anty Zulaihatu da Amira suka rirriƙe ni suna yi mini tofi kafin na lafa na kwanta na yi lamau. Sai dab da magrib Amira ta tafi mijin Anty Zulaihatu ma ya zo ya ɗauke akan gobe da safe za ta dawo ta ƙara duba jikin nawan. Haka na ƙara kwana cikin wannan yanayin kafin gari ya waye zazzaɓi ya rufe ni ko idona ba na iya buɗewa, na firgita na ruɗe bisa mummunan mafarkin da na yi da Abba, wai na je wajen sa a asibiti ya ce kar a bar ni na shiga wajensa ba ya son ganina.

Wajajen ƙarfe takwas Yaya Alhassan ya ƙira waya ya shaida mana cewar ga su a hanya suna dawowa. Tsam Anty Sawwama ta miƙe"alhamdulillah! Lafiya ta samu kenan? Ina shi Mannirun haɗa da shi". "Umma ba zai iya magana ba, sai dai mun iso ɗin kawai". Yanayin da ya ƙare zancen da kashe wayar da ya yi ba tare da an gama maganar ba, ya samu ɗaura ayar tambaya akan sa. Haka muka dinga ƙiran wayar amma baya ɗauka daga ƙarshe ma ya kashe ta, daga shi har Amir muka daina samun wayoyinsu. [10/27, 5:30 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

___________________________________________

Page 3️⃣8️⃣

Haka muka kasa tsaye balle zaune duk muka yi jigum-jigum da mu cikin mu babu mai walwala. A zaune na yi sallan zuhr saboda yadda ƙafafuna suke rawa ji nake yi tamkar ba sa cikin gangar jikina, ina zaune a wajen na zagba uban tagumi ina tunanin makomar rayuwata da yadda komai ya sauya mini cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. "Abba ka yafe mini Allah ya tashi kafaɗunta. Na san kai kaɗai ne za ka fahimce ni a kaf cikin faɗin duniyar nan. Abba kai ɗaya ne kake fahimtar shuru na kuma ina da yaƙinin kai kaɗai ne za ka yi mini uzuri akan abin da ya faru. Na yi kewarka ina son ganinka sai dai ba zan iya jure ganinka cikin yanayin da na yi silar jefa ka a ciki ba. Abba ka yafe mini ka yafe mini".

Na yi zancen cikin karyarwan zuciya wasu hawaye suna rige-rigen fitowa daga cikin rinannun idanuna. Na ji wani abu ya tokare mini ƙirjina numfashi ma da ƙyar nake fitarwa tamkar mai lalurar cutar numfashi. Kamar daga sama na tsinkayo sallamar su Yaya Alhassan take na ji fada na ya yanke ya faɗi zuciyata ta buga irin bugun da har sai da ya tilasta mini runtse idanuna. Anty Sawwama da Anty Zulaihatu suka miƙe a tare suka fita amma ni kam ko gizau na gaza motsawa daga inda nake zaune, sai dai ina zaune ina jiyo abin da suke tattaunawa. "Alhassan ya ya na gan ku haka? Ina shi Mannirun? An sallama ku ne daga asibitin?". Duk jerin tambayoyin da Anty Sawwama ta jefa masa bai amsa ko guda ba.

"Wai kurame kuka zama ne ko kuwa? Cikinku babu wanda zai amsa min tambayoyina". Anty Sawwama ta ƙara buga musu wani tambayar muryarta har ta na harɗewa waje guda. "Umma ku shiga ciki za a shigo da shi". Ina yin wannan furucin na Yaya Alhassan na zabura tamkar wacce aka tsigarawa alluran doki. Na miƙe har ina ƙoƙarin faɗuwa na fito waje daidai lokacin da wasu maza biyu suka shigo da mutum cikin lulluɓi farin ƙyale, Amir ya ɗauko tabarma ya shimfiɗa suka kwantar da shi, mazan suka fita ya rage daga m sai ya mu.

"Wane ne wannan Alhassan? Alhassan kar ka ce min gawan Manniru ne kwance a nan. Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Daman da kuke cewa za ga ku nan za ku dawo ɗin gawarsa za ku dawo da shi". Anty Sawwama ta yi kalaman cikin tsananin ruɗani da kaɗuwa, Anty Zulaihatu kam ta kasa magana sai kukan da nake yi, ganin yadda na tsaya a waje ɗaya na kasa gaba balle baya ya sa ta iso gare ni ta riƙo ni. "Amatullah sai dai mu yi haƙuri". Tun kafin ta gama maganar na fizge jikina daga riƙon da ta yi mini kamar mai aljanu ko iskokai haka na ƙanƙame ta ƙam ta gaza motsawa balle ta yi wani yunƙurin ƙwacewa. "Abba bai rasu ba, ba shi ba ne bari na buɗe miki ki gani ba shi ba ne fa Anty Sawwama ku daina wannan kukan".

Na kai aya ina jan ƙafafuna da nake ɗagawa da ƙyar na je zan buɗe gawan Yaya Alhassan ya riƙe hannuna jikina har wani jijjiga yake yi tamkar mazari. "Kar ka hana ta Alhassan ka bar ta ta buɗe". Anty Sawwama ta furta dole yaya Alhassan ya cika ni na je na durƙushe a gaban gawar haka kawai tun kafin na buɗe na ji ƙirjina yana tsananta bugu tamkar zai faso allon ƙirjin ya bayyano waje ya daka rawar disko. Duk yadda hawaye suka wadai kurmin idanuna ƙarfi hali da bushewar da zuciyata ta yi ya hana sa zuba, don ba na son na gaskata abun da su Anty Sawwama suke yi wa kuka. Jikina gabaɗaya yana rawa na kai hannu na buɗe dirsham na zame na yi zaman ƴan bori hawayen da nake riƙewa suka zama lasisin yin gudun famfalaƙi a bisa fuskata.

"Abba don girman Allah ka tashi kar ka tafi ka bar ni a cikin wannan yanayin. Abba kar ka yi mini haka ni kuwa ina zan tsoma kaina idan na waiga ban ganka a kusa da ni ba, don Allah ka buɗe idanunka ka tashi kar ka tafi". Na kifa kaina a saman ƙirjinsa ina kuka ji nake yi numfashi yana cushewa tamkar an ɗaure mini wuyana da ya kasance hanyar shiga da fitan numfashina. "Amatullah haƙuri za mu yi Kawu kuma lokaci ya yi wanda ya fi mu sonsa ya karɓe rayuwarsa. Sai dai mu yi masa addu'ar Allah ya kyautata makwancinsa idan lokacin mu ya yi mu kuma Allah ya ba sa mu cika da imani".

Raɗau na ji maganar a na'urar naɗan sautina sai dai na kasa tantance waye mamallakin murya. Kukan kawai nake yi duk da hawaye ba sa fita daga idanuna amma ina jin zafi a cikin ƙirjina tamkar ana watsa mini garwashin wuta, na ji an ɗago ni sai dai na kasa tsayiwa akan ƙafafuna ana ɗago ni nake faɗuwa, aka Anty Zulaihatu ta riƙe ni muka shiga cikin ɗaki take numrashina ya soma ɗauke wa. Jikina ya soma jijjiga sai da ta dafa kaina tana karanto karatun suratul baƙara tana tofa mini a hankali na soma yi kamar an warware mini tirniƙin da ya zarge mini maƙoshina. Na koma kamar gunki babu wani gaɓa a jikina da yake motsawa face idanuna da suka kafe babu ɗigon baƙi a kaɗan a cikinsa ya juya zuwa launin fari fat. Sai da ta nem ruwa ta yi tofi a ciki ta shafa mini a jikina da ya sake ba shi da maraba da bishiyar da ta baza jijiyoyinta a ƙarƙashin ƙasa. Ba ta gushe ta na yi mini har sai da na ji nauyin da ƙirjina ya yi mini ya taguwa har na iya tashi da kaina na zauna. Na kasa kuka da hawaye illa na zuci da nake yi. Anty Sawwama ta shiga tararradin yadda za a sanarwa Ummata labarin rasuwar Abba, daga ƙarshen dai aka yanke shawarar aika Umar ya je ya ƙira ta. Babu jimawa suka dawo tare Anty Sawwama ta zaunar da ita ta yi mata dukkan nasiha cikin sigar mai jan hankali kafin daga ƙarshe ta sanar da ita labarin rasuwar. Ban ga tsananin kaɗuwa a fuskarta ba illa miƙe wa da ta yi ta nufo ni, na yi zaton runguma na za ta yi na ji ɗumin jikinta ko zan ji sauƙi yanayin da nake ciki sai dai na ci karo da saɓanin tunani da hashashena.

Ta wanke ni da wani mahaukacin marin da har sai da ɗan kunnena ya faɗi ƙasa na dafe kuncina. "Amatullah shikenan hankalinki ya kwanta kin yi silar mutuwarsa. Ya tafi ya bar miki duniyar sai ki yi yadda kike so....". Na riƙe ƙafarta ina kuka mai haɗe da magiya. "Don Allah ki taimake ni ki taimaki rayuwata kar ki yi silar rugujewan ta gabaɗaya". Ban ta ce da ni komai ba ta zare ƙafarta daga riƙon da na yi mata ta juya tana fuskantar Anty Sawwama.

"Ku yi zaman makokinku anan ni ma zan je na yi nawa a can."

"Haba Hafsatu me ya yi zafi haka shi ba wuta ba?. Me zai hana duk mu zauna a nan tunda nan É—in ma ya fi fili". A zafafe Umma ta mayar mata da martani"in kun ga dama ku tafi bangon duniya ku yi na ku zaman makokin amma ni a É—akina zan yi. Babu dalilin da zai sa na zo na tare a gidanku tun da wanda ya haÉ—a ya raba".

"Haba! Anty Hafsatu ki yi haƙuri mana da nan da can ɗin ai duk ɗaya ne. Kar ki manta fa ga Kawu can a kwance ko kai sa ba ayi ba kike wannan maganar". Amir ya yi zancen hawaye suna ciko masa kurmin idaniya, tsaki Umma ta buga bayan ta gama jifan mu da harara ta sa kai za ta fice, Yaya Alhassan ya dakatar da ita ta hanyar faɗin" za ki tsaya dai ku yi bankwana da shi ki yi masa kallon ƙarshe tare da addu'o'i".

"Zan iya masa addu'a daga duk inda nake kuma ta iske shi har cikin kushewarsa". Tana dasa aya a nan ta yi ficewar. Kalmar innalillahi wa inna ilahirin raji'un kawai Anty Sawwama take ta maimata jiri ya ɗebe ta za ta faɗi Amir ya riƙe ya zaunar da ita. "Umma a ina za a yi jana'izar kenan?".

"Amir ya ya muka iya dole mu yi yadda take so, tun da a wancan unguwan aka san shi kuma a can yake zaune aje can kawai a yi masa salla a ƙofan gidan. Allah ya jiƙanka Manniru Allah ya kyautata makwancinka halinka na gari ya fita".

"Amin ya Allah" .

Duk muka haɗe baki wajen furta, Yaya Alhassan da Amir suka fita suka nemo mota aka tafi da gawar can unguwanmu Umar ya sanar da dangi labarin rasuwar, muka bi bayan su mu ma zuwa can unguwanmu. Muna karyo kwanar gidan na ga an kafa rumfuna har guda uku a ƙofar gidanmu ga mutane maƙil a wajen wasu suna zaune, wasu suna alwala wasu kuma su na tsaye jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau. Ban taɓa zaton haka mutuwa take da zafi ba sai yau da ta raba ni da jigon rayuwata. Muna shiga cikin gidan muka tarar da taron mata, yau ne rana ɗaya tal da na ga nutsuwa a tattare da matan gidan kowacce tana zaune a ƙofar ɗakinta cikin jimami har da masu kuka wiwi da hawaye don a tsawon shekarun da muka yi a gidan Abba ya zauna da kowa lafiya cikin aminci da girmamawa.

Amira ta taso muka rungume juna muna kuka kowa sai da ya tausaya mana, aka ce mu shiga cikin muka shiga ɗakin Ummanta don ɗakinmu ya cika da mutane babu masaka tsinke. Mun daɗe muna kukan har sai da na kasa buɗe idanuna saboda yadda suka kumbura ji nake yi tamkar ni ma ba zan kai zuwa yamma a raye ba. Umman Amira ta shigo ta ce mu zo mu yi wa Abba addu'a za a tafi da shi, ko da na fita na kasa taɓuka komai illa kwantar da kaina da na yi a jikin makaran, bakina ya kasa cewa komai addu'ar ma a cikin zuciyata na dinga yi masa.

Da ƙyar aka ɓaɓɓare ni daga jikin makarar, ina da ilmin cewar mamaci ba a nuna masa ƙauna da hanyar yi masa kuka. Wannan dalilin ya sanya yi ƙarfafa zuciyata na dinga karatun duk wani addu'ar da ya zo bakina a lokacin ina yi. Ban yi aune ba na ji an rufe ni da duka ta ko'ina tun ina kare kaina har na sadadu na baje a ƙasa. Idanuna suka soma gano mini Umma da ta kau saman ruwan cikina tana ta jibga duk da yadda mutane suka yi tururuwa suna janye ta amma ba ta fasa abin da ta yi niyya ba.

"Ku bar ni na kashe matsiyaciya wacce ba ta yi gadon abin azirki ba. Ku bar ni na kashe ta don babu amfani rayuwarta gwara na kawar da ita".

Da ƙyar mutane suka taru suka janye Umma daga kaina, lokacin har na fita daga cikin hayyacina na ji ɗumin wani abu mai ruwa yana bin tsakanin cinyoyina yana sauƙar har izuwa dugadugaina. Aka ɗaga ni na kasa tsayiwa na lu na faɗi. Tun daga sa'ilin nan ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai farkawa na yi na ganni a gadon asibiti da Anty Zulaihatu da Amira a kusa da ni, ina buɗe ido suka soma yi mini sannu wani bin wani kana Amira ta je ta ƙira likita ya zo ya ƙara duba ya kuma tabbatar da cewar babu wani damuwan.

"Amira me ye ya faru da ni ne ki sanar da ni. Ganin komai na ke yi tamkar a cikin mafarki, don idan mafarki nake yi ki taimaka ku tashe ni tun kafin na zauce".

"Babu abin da ya faru da ke Amatullah faɗuwa kika yi aka kawo ki asibiti kuma yanzu kin ji ai da kunnenki cewar babu wata matsala. Sai dai kuma wani abu....". Ta yi shuru ba tare da ƙarisa ba suka haɗa ido da Anty Zulaihatu take na ga duk su biyun sun fashe da kuka, hakan ya ba ni tabbacin cewar akwai wani abun da suke ɓoye mini.

"Don Allah Anty Zulaihatu kar ku ɓoye mini komai ku sanar da ni abin da ya faru da ni komai munin sa, babu abin da zai same ni yanzu babu wani labarin da zai tayar mini da hankali fiye da rasuwar Abba. Don Allah ku sanar da ni". Na ƙare zancen cikin karyewan zuciya. Sai da suka ɓata wasu mintuna kafin Anty Zulaihatu ta riƙo hannuna ta sanya cikin nata tana murzawa a hankali ta ke faɗin.

"Amatullah kin shiga cikin jarabawa da yawa wanda sai mai ƙarfin imani ne kawai zai iya jure su ba tare da ya rasa tauhidinsa ba. A yanzu ma ina so ki yi haƙuri da abin da za ki ji daga gare ni". Na gyaɗa mata kaina alamar ina sauraran duk abin da take faɗa da hakan ya ba ta damar ci gaba daga inda ta tsaya.

"Sakamakon dukan da Ummanki ta yi miki cikin da ke jikinki ya bi rariya". Na ware dukkan girman ƙwayan idona"ya zube kenan?". "Babu yadda za mu yi Amatullah haka Allah ya ƙaddara". Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya na rasa a tsakanin farin ciki ko baƙin ciki wanne ya fi dacewa da ni a yanayin da nake ciki. Yaya Alhassan yana zuwa asibitin aka sallame mu sai dai maimakon mu wuce can gidanmu sai na ga sun wuce gidan Anty Sawwama. Na yi kuka iya kuka har sai da idanuna suka kafe, na ji gabaɗaya duniyar ta ishe ni babu abin da yake yi mini daɗi a cikinta. Wai ace mahaifina ya rasu amma ba ni da ikon zuwa wajen makokinsa ni kam ba san abin da ya fi wannan ciwo da raɗaɗi ba. [10/29, 10:08 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

________________________________________

Page 3️⃣9️⃣

Haka na kwana na tashi da zazzaɓi a jikina garau kamar garwashin wuta ake watsa mini a cikin jikina. Ji nake yi tamkar a mafarki wai yau Abba ba ya raye cikin duniya ya rasu ba tare da na sanar da na kore masa kokonton da share masa zargin na aikata abin da ake zargina da shi. Ban taɓa sanin haka mutuwa take da matuƙar zafi da ciwo ba sai yanzu da ya juyo kaina, ji nake yi kamar ni ma ba zan yi tsawon rai a duniya ba ko da kuwa na yi to haƙiƙa zan zauce ne na fita daga cikin hayyacina. Tun ina yin kukan da hawaye har suka daina zuba ƙirjina ya yi miji nauyin gaske tamkar an yi mini ajiyan dutsin dala ta Kano a saman ƙirjina, idanuna har sai da suka daina buɗuwa saboda tsabar kumburan da suka yi. Kafin gari ya waye ko magana ba na iya yi haka nan ba na gane wanda yake tsaye a kaina sai dai kawai na tantance muryan.

Ina kwance tamkar ruwa don ko ƴatsan hannuna ba na iya motsawa jikina ya yi lamus ko kaina ban iya ɗagawa, ranar da aka yi sadakan ukun Abba yayin da Anty Sawwama ya ce a haɗa har na bakwai kowa ya watse aka kuwa yi hakan. Aka bar mu daga mu sai ya mu sai kuma halinmu, har zuwa wannan lokacin Umma ta Antyaihatu ta shigo cikin ɗakin ta zauna a kusa da ni ta ɗaura hannunta a bisa goshina da ya ɗau zafi gau. "Ya subhanallahi! Amatullah jikin ne haka? Don Allah ki tashi ki ci wani abun ko kaɗan ne sai ki sha magani". "Anty Zulaihatu mutuwa zan yi ni kam ba zan rayu ba mutuwa ni ma zan yi". Na zaro maganar da ƙyar saboda yadda numfashina yake cukurkuɗewa waje guda kamat mai lalurar cutar numfashi.

"Amatullah duk wanda kika ga ya mutu ai lokacinsa ne ya yi. In sha Allah ba za ki mutu ba sai lokacinki ya yi, za ki ci gaba da rayuwa har ma ki yi dariya ki yi mu'amala kamar kowa. Don Allah ki kwantar da hankalinki komai ya faru da Bawa muƙaddari ne daga Allah ne kuma Bawa baya wucewa ƙaddararsa balle ya guje mata".

Na ɗaya kaina ina ganin ta dishi-dishi ga numfashina yana sama yana ƙasa na yi ƙarfin halin faɗin"Anty Zulaihatu rayuwata ta zo ƙarshe ni kam". Ban ƙarisa ba ta rufe miji bakina da tafukan hannayenta. "Don Allah ki daina faɗin irin wannan maganar babu wanda ya san gobe sai Allah". Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya mai ɗumi ina lumshe kumburarrun idanuna da kamar za su faɗo ƙasa. Sama-sama na soma jiyo amon Yaya Alhassan a masarrafan naɗan sautina, kafin na ji muryar dab da ni.

"Amatullahi".

"Na'am". Na amsa a taƙaice da hakan ya ba shi damar ci gaba da maganan da yake yi. "Wannan damuwar duk na mene ne haka ƙanwata? Abin da ya faru ai riga da ya zama tarihi sai dai ayi ƙoƙarin gyar gaba. Kawu yanzu addu'armu yake buƙata ba wannan koke-koken ba, na san abin da ciwo amma ina so ki daure ki yi ƙoƙarin cire komai daga cikin ranki ki fuskanci rayuwarki ta gaba ka shagala wajen ingantata".

"Yaya Alhassan ni kuma me ye ya rage mini a duniya ai rayuwata kam ta gama rushewa ta rugurguje".

"Har yanzu ki na da sauran daman da za ki ɗinke ɓarakar da ya ɓullo a cikin rayuwarki. Amatullah rayuwa jarabawa ce mai girman gaske, duk munin halin da kike ciki idan kika ga wani ko kika ji halin da wani yake ciki sai kin ji tamkar ke ɗin ki na cikin gidan aljanna ne". Na yi lamau na kasa cewa da shi komai zuciyata tana turara kamar talgen masarar da aka aza bisa murhu. "Tashi mu yi magana".

"Ba zan iya tashi ba".

Muryarsa babu alamar wasa ya furta"tashi ki zauna magana za mu yi da ke". Na cije leɓe na tashin na zauna saboda duk inda na motsa a gaɓoɓina ciwo yake yi mini. Shruu ya ratsa ɗakin kafin ya kawar da shurun ta hanyar faɗin"Amatullah da waye kika keɓe har ciki ya shiga cikinki?". Zuffa ya jiƙa mini jikina tsam jikina ya soma rawa sai da na fizgo numfashina da ƙarfi kafin na iya faɗin"Yaya Alhassan wallahi ba laifina ba ne ƙaddara ce ta faɗa mini...... ....". Na irge masa komai duk abin da ya faru tun daga faru har ƙarshe.

Ya zabga mini wani gigitaccen marin da ban san lokacin da na sake ihu ba. Ya tashi tsaye yana cije leɓansa tare da kai wa iska naushi. "Amatullah me yasa kike ɓoye faruwar wannan abun? Shin ba kya kishin kanki da har wannan abun zai faru amma duk da haka ki zaɓi ki ɓoyewa kowa hatta iyayenki da ƴan uwanki. Wanda kika san cewa duk wuya duk tsinki suka rufa miki asiri. Ina ma kin sanar tun a lokacin da lamarin ya afku da duk abin da ya faru bai faru ba". Ya ƙarishe zancen cikin matuƙar takaici daidai lokacin da Anty Sawwama take shigowa ɗakin cikin tsananin damuwa da alamar ta saurari duk abin da na muka faɗa.

"Allah ba ka jarabtan Bawa da abin da ba zai iya yi. Ya Allah don ƙarfin zari da ikonka ka ba mu juriya da haƙurin jure wannan jarabawan da ka jarabce mu da shi".

"Amin ya Allah".

Duk suka haÉ—e baki wajen furtawa amma ni kam sai a zuciyata na amsa don bakina ya kasa motsawa. "Umma yanzu ya ya za a yi?". Anty Zulaihatu ta tambaya muryarta tattare da tarin damuwa.

"Dole mu je mu yi magana da mahaifiyarta don yadda ta yi watsi da Amatullah a wannan yanayin da take ciki abin yana damuna matuƙa. Zuwa yamma in sha Allah za mu je gabaɗayanmu mu same ta". Duk suka yi na'am da abin da Anty Sawwama ta furta ni kam na yi shuru tamkar wacce ruwa ya cinye ta. Zuwa bayan sallan asr suka sauƙa daga napep a ƙofar gidanmu. Na waiga na hango masallacin da Abba yake salla kuma yake yawan zama a bakin wajen, na ga tarin dattawa zaune a wajen sai dai duk cikin su babu Abba, mutuwa kenan mai raba zumuci da daɗaɗɗan alaƙa.

Sai da Anty Zulaihatu ta ja hannuna kafin na ja ƙafafuna muka shiga cikin gidan, yara da manya suka taru suna ganina kamar ba su taɓa ganina ba kaina a ƙasa tun da muka shigo amma hakan bai hana su magana ba. "Wannan ce annobar kenan? Ni kam da haihuwar irin wannan ai gwara ka zo duniya har ka gama rayuwarka ba tare da ka haihu ba". Cak na tsaya bisa sauƙan furucin da na ji a kunnuwana da ya damalmala mini dukkan lissafina ya farraƙa nutsuwa da gangar jikina.

"Amatullah ke ce haka duk kika lalace kamar mai cutar ƙanjamau?". Maman Adnan ta yi zancen tana iso ta tsaya a gabana kafin na ba ta amsa ta ci gaba da zancen tana taɓe baki. "Ai daman ƙarya fure take yi ba ta ƴaƴa kuma komai nisan daren dole gari zai waye haske ya mamaye ko'ina, ashe duk sintirin da kike yi da sunan da zuwa islamiyya fakewa ake yi da guzuma a harɓi karsana to an yi walƙiya mun gan ku".

"Malama idan har kin san cewa bakinki ba zai furta alkhairi ba, to zai fi dace ki yi shuru". Anty Zulaihatu ta mayar mata da martani a zafafe tana jan hannuna muka shige cikin ɗakinmu, muka tarar da Umma tare da wasu mata biyu muka yi sallama sai dai cikinsu babu wanda ya amsa mana muka shigo muka zauna, ina satan kallon Umma sai dai ko kaɗan ban ga ta yadda na yi tsammanin ganin ta ba. Na yi zaton kamar yadda mutuwar Abba ta girgiza ni haka ita ma lamarin zai taɓa zuciyarta sai dai kash! Ashe kallon kitse nake yi wa ruwa hange dala nake yi wanda ya ke ba shiga cikin birni ba ne.

"Hafsatu ya muka ji da haƙuri?".

"Alhamdulillah". Ta amsa da shi tana yatsina fuska. "Na zo mu yi magana da ke ne amma na ga ki na da baƙi, na ce ko za mu shiga cikin uwar ɗaka?".

"Babu inda zan motsa daga idan kuka riske don haka duk abin da za ki faɗa ki faɗe ta a nan. In ba za ki iya ba kuma ki wanke ƙafafunki ki koma inda kika fito ba lalle ba dole ai".

Lamarin ya ƙullar da Anty Zulaihatu har sai da ta tanka"Maman Amatullah izuwa yanzu kam ai na yi tunanin komai ya wuce, ya kamata mu bayar da hankali mu fuskanci abin da yake gabanmu. Mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen nemawa yarinyar nan nutsuwa da farin cikin ko don daidaituwar rayuwarta". Umma ta gyara zamanta tana fuskantar Anty Sawwama da kyau tare da faɗin. "Ku yanzu har ku na tunanin cewa a cikinku akwai wanda ya fi ni son Amatullah ne, na fi kowa son ganin rayuwarta ta gyaru shi yasa nake yi duk waɗannan abubuwan. Wallahi duk daren duniya ba na iya runtsawa saboda baƙin cikin abin da wannan yarinyar ta aikata, ni kaɗai na sa irin son da nake yi wa Amatullah ko har kun manta irin wahalar da sha yayin raino da haihuwarta".

Kalamanta ya sanya idanuna kwaranyowa da hawayen da na daɗe ban tsiyayar ba, na ja gwiwoyina na gurfana a gaban Umma na ɗaura kaina a bisa kan cinyoyinta. "Umma na tuba ki yafe mini wallahi ni ma shaida ce na san cewa ki na yi mini irin soyayyar da babu wanda zai yi mini kwantan-kwacinta a cikin duniyar nan. Amma zan so ki zauna ni dama na yi miki bayanin abin da ya faru wallahi ba laifina ba ne ƙaddara ce ta faɗa mini Umma kin san da hankali da tunanina ba zan aikata wannan abun ba, don Allah ki sassauta mini ki ba ni mafaka na sama sassauci a wajenki".

"Amatullah na riga da na cire ki daga cikin raina, tun ranar da abin kunyar da kika aikata ya bayyana na sallamar da ke a duniya......".

Da hanzari Anty Sawwama ta katse ta"kar ki yi mata baki Hafsatu ki saurare abin da za ta ce da ke don Allah". "Babu wani abun da ya yi saura wanda za ta sanar da ni da ban ji shi a bakin al'umman gari ba. Amatullah na sallamar da ke ga duniya daga yau ni Hafsatu ba ni da wata ɗiya a duniya, don haka ki tashi ki bi su kar ki ƙara zuwa inda nake balle ni ma baƙin cikinki ya kashe ni kamar yadda ya yi silar mutuwar ubanki".

"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Allahumma ajirni fi musibati. Ya Allah ka kawo mana sauƙi wannan lamarin".

Wani irin kuka nake yi mai raunana zuciyar mai saurare babu shiri na É—ago kaina sakamakon dukan da na ji kalaman Umma sun yi mini. Duk yadda na so na yi magana na kasa yin haka sai ma tashi da na yi da sauri har ina haÉ—awa da gudu-gudu na bar cikin É—akin kai tsaye É—akin su Amira na nufa na zube akan kujera ina ci gaba da kukan.

"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Amatullah me ya faru kuma? Tun ɗazu nake so na je ɗakin nakun sai kuma Ummata ta ce ai da baƙi a ciki shi yasa na dakata". Na tsinkayo muryar Amira cike da kulawa yayin da take zama kusa da ni tare da ɗago kaina. Ta soma goge mini hawayen da suka ɓata mini fuskana.

"Amira me yasa munanan abubuwan suke faruwa da ni? Da farko an yi mini fyaɗe ciki ya bayyana a jikina, Abba ya mutu da baƙin cikin da na yi silar cusa masa sannan yanzu Umma uwar da ta haife ni ta furta cewar ta sallamar da ni ga duniya ba ta buƙatar gani na a kusa da ita. Amira ya ya ake so na yi rayuwata? Allah ma fa da kansa mu na yi masa laifi ya yafe mana to me ya sa Umma ta kasa fahimta na akan wannan lamarin balle har ta dube ni da idon rahama, jin ƙai tare da tausayi. Wallahi zuciyata ta soma saƙa mini wani mungun tunani, duk abin da na aikata kar ku ga laifina wallahi na rasa mafita ne".

Na yi zancen cikin wani irin yanayi mai wahalar fassaruwa cikin kalmomin baki, Amira ma kanta sai da hawaye suka zubo mata daga idanunta. Ta kasa lallashina illan kukan da muka haɗu ni da ita mu na yi. "Duk laifina ne Amatullah ni na fara kawo shawaran zuwa gidan Tasalla. Kuma bayan abin da ya faru ya faru na goyi bayan a ɓoye lamarin. Komai ya faru ni ce sila ina ma a kaina wannan abun ya faru ba ke ba Amatullah ina ma....". Ba ta ƙarisa ba sakamakon kukan da ya ƙwace mata mai ƙarfin gaske muka haɗu duk mu biyun muna yin sa. Ummanta ta shigo ta tsaya a kanmu na tsawon lokaci kafin ta yi magana. "Haƙuri za ku yi don duk abin da ya faru kuka ko shiga tsananin damuwa ba ya gyara shi. Ƙaddara ce da ta riga fata cikin mu babu wanda zai iya guje mata". Ta dafa kaina kana ta ci gaba"Amatullah ki yi haƙuri na san cewa ke mai haƙuri ce da juriya da kuma tawakkali. Duk layin nan da ke ake buga misali da kwatance idan za yi maganar tarbiyya, kamun kai, hankali da kuma nutsuwa kuma ina da tabbacin kowa zai shaide ki cewar hakan ba halinki ba ne. Ki tashi ki share hawayenki ki fito ku tafi ga su can suna jiranki a waje".

Na kuma fashewa da wani kukan mai tsuma zuciya ni nake yi zuciyata tana yi mini hura. Muka fito har zaure hannuna saƙale cikin na Amira suna fitowa waje muka ga dandazon mutanen unguwa ƙwansu da ƙwarƙwatansu wai duk su zo kallona.

"Dube ta simi-simi kamar na Allah ashe kura ce lulluɓe da fatan akuya. Allah dai wadaranki da kuma mungun halinki, ga shi yanzu ki kashe mahaifinki har lahira Allah sarki! Malam Manniru bawan Allah da ya san irin annobar da zai haifa kenan na tabbatar da ya gwammace ya rayu har ya koma ga Allah babu ɗa babu jika".

Kalaman da suka sauƙa a na'urar naɗan sautina kenan da ya gigita ni numfashina ya soma sama da ƙasa, ashe kowa zargina yake yi da akan mutuwar Abba?. Da ƙyar na isa wajen napep ɗin Anty Zulaihatu ta tsayar na shiga na zauna. "Amatullah don Allah kar ki aikatawa abin da zai cutar da ke ko ya jefa mu gabaɗaya cikin wani ruɗanin. Ki yi ƙoƙari ki cire damuwa a cikin ranki in sha Allah gobe da sassafe ni ma zan zo, kuma Mansur ma ya ce a yi miki gaisuwa kafin ya zo da kansa". Kaina kawai na jinjina mata muka rabu, ko da muka isa gidan Anty Sawwama su Yaya Alhassan sun hi matuƙar baƙin cikin abin da ya faru Umar sai da ya yi kuka tsabar takaici.

A daren ranar sai da aka ƙara mini ruwa leda biyu aka yi mini allurai da sauran magungunan da na sha. Ina kwance a ɗaki kamar gawa Yaya Alhassan ya shigo ya yi mini sannu na amsa can ƙasa maƙoshina.

"Amatullahi ki cire damuwar komai daga cikin ranki in sha Allahu duk wanda ya yi miki wannan abun sai na nemo sa ko ina ya shiga a cikin duniya sai kuma na tabbatar da cewar an hukunta sa, bisa tanadin doka. In sha Allah farin cikinki zai dawo za ki rayu cikin nutsuwa da walwala kamar yadda kike a baya".

"Yaya Alhassan ni da samun farin ciki mun yi hannun riga". Ya yi hanzarin katse ni"zan dawo miki da farin cikinki zan tabbatar da cewar duk matsalalolinki sun kau. Amatullahi ki ba ni dama in har kin aminta da ni kuma ki na jin za ki iya rayuwar aure da ni to zan iya ki".

Take na wartsake na tashi na zauna ina kallon sa cikin son tabbatar da abin da kunnuwana suka jiyo mini. "Ƙwarai da gaske ni zan aure ki don ba zan ba ri aure ya kai ki inda za a wulaƙanta ki ko a yi miki gori bisa ƙaddarar da Allah ya ɗaura miki ba".

"Yaya Alhassan rayuwarka tsarkakkiya ce babu wani mummunan abu a cikin tarihinka. Don Allah kar ka gurɓata tarihinka ta hanyar haɗa jini da ni".

"Ko a gidan karuwai kike rayuwa Amatullah zan iya aurenki. Balle kuma ke ɗin ƴar uwata ce ta jini. Sai dai ba zan yi miki dole ba don yanzu farin cikinki shi ne abin da na fi so don haka ki je ki yi tunani da zuciyarki". Na sunkuyar da kaina ƙasa kafin na ce"Anty Sawwama ta san da wannan zancen?". "Sai da na fara tinkarar ta da maganar kafin na zo wajen ki". Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya ban iya cewa wani abun har ya tashi ya fita daga cikin ɗakin, ji nake yi kaina yana juya tamkar ba a cikin duniyar nake ba ga wani jirin da yake ɗeba ta don da kasancewar a zaune nake. Na koma na kwanta hawaye suna tsiyaya ta gefe da gefen idona. Tabbas Yaya Alhassan mutumin kirki ne mai ƙoƙarin kame mutuncin kansa da kuma na ahalinsa a ko da yaushe, mutum ne mai nutsuwa da sanin ya kamata me yasa Anty Sawwama za ta amince masa akan auran watsatstsiyar da ta yi cikin shege ta kunyatar da iyayenta da duk wani wanda ya yarda da ita a idon duniya. Hatta mahaifiyarta ta nuna rashin buƙatata a kusa sai ita ce za ta buƙaci ɗanta ya kasance a tare da ni?.

Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya ina gyara kwanciyata, ba zan zama silar rugujewar rayuwar Yaya Alhassan ba. Don haka na gwammace na tafi can wani wajen da ban san kowa ba ni ma ba sanni ba na je na yi rayuwata. Ko zan sama kwanciyar hankalin da na rasa a yanzu. Gwara na shiga duniya kamar yadda Umma ta yi ikirarin ta sallama ni gare ta. [10/30, 4:03 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

______________________________________

Page 4️⃣0️⃣

Haka na kwana ina tunani da saƙa da warwara cikin raina, ganin bacci ya ƙi kawo mini ziyara hakan ya sani tashi na fito na ɗaura alawa na koma ciki na gabatar da salla raka'a biyu. Na ɗaga hannayena dukka biyu sama sai dai na kasa magana rawa kawai jikina yake yi. Na kifa kaina a bisa gwiyoyina ina rero kukan marar sauti. Ban runtsa ba har sai da aka yi ƙiran sallan asubahi Anty Sawwama ta shigo da nufin tashi ta iske ni zaune ta dalle mini idanuna da haske tocila.

"Lafiya na gan ki a zaune kamar ba ki runtsa ba?".

"Na runtsa kawai na tashi ne da na ji ƙiran salla". Ba ta ce da ni komai ba ta juya ta fita na bi bayan ta alwala na yi na zauna na buga tagumi a gaban botan har Yaya Alhassan, Amir da Umar suka fito domin tafiya masallaci. "Amatullah lafiya kuka zauna kika zagba tagumi?". Na tsinkayo muryar Amir a tsakiyar kaina na yi figigi na dawo cikin hayyacina. "Lafiya ƙalau ina kwananku". Suka haɗe baki wajen amsawa kana suka fita, na tashi na koma cikin ɗakin na shimfiɗa sallaya a zaune na yi sallan don ji nake yi tamkar ƙafafuna ba za su ɗauke ni ba tun ina raka'an farko nake kuka har na yi sallama na ɗaga hannayena dukka biyu zama ina kirari ga Ubangijina.

"Ya Allah kai mai ikon akan kowa da kuma komai. Ya Allah kai ne masanin sirrin dake taskace cikin tsokar zuciyar dake a ciki ƙirji, Allah ka kawo mini mafitan halin da nake ciki. Zan tafi na je can wani wajen da ba a sanni ba ni ma ban san kowa na je na ci gaba da rayuwa a can, don na fahimci zama a nan shi ma wani matsalan ne. Tun da har Umma ta furta ba ta buƙata ta ta sallamar da ni ga duniya zan tafi can wani wajen na je na yi rayuwata, ba zan zama matsala ga rayuwar wasu ba. Ya Allah ya dubi lamarina ka kawo mini komai da sauƙi ka ba ni ikon cinye wannan jarabawan da ya faɗa mini. Allah kai mai rahama ne Allah ya lulluɓe Abbana da rahamarka, Ya Allah kai mai gafara ne Allah ka gafarta masa".

Na shafa addu'ar cikin sanyi da mutuwar jiki wasu hawayen suna gangarowa daga idanuna, na ji ƙarar buɗe ƙofar hakan ya sa na yi saurin komawa na kwanta ba tare da na cire hijabin da na yi sallan ba. Aka shigo aka zauna kusa da ku dab har ina ji sautin ajiyan zuciya da take sauƙewa akai-akai. Ta dafa goshina tana shafawa har zuwa kaina"Amatullahi Baiwar Allah ina son rayuwarki ta inganta ina don ganin ki cikin farin ciki. A yanzu ba ni da burin da ya wuce na gan nutsuwarki ya daidaita kin sama kwanciyan hankali da walwala ki yi rayuwa kamar kowa cikin sakewa wannan dalilin ya sa nake son Alhassan ya aure ki. Don hankalina ba zai kwanta ba matuƙar kika yi aure a wani wajen kika shiga cikin wasu dangin da wataƙila su goranta miki akan abin da ya faru da ke ko ma su wulaƙanta ki. Amatullah tun ranar da aka kawo mini gawar Manniru a gaba babu rai a tattare da shi na yi wa kaina alƙawarin ba zan taɓa barin abin da ya haifa ta wulaƙanta ba bayan ransa, zan yi tsayiwan tsayin daka wajen tabbatar da cewar rayuwarki ta inganta. Ina da yaƙinin ko bayan babu raina Alhassan ba zai taɓa bari ki wulaƙanta ba".

Ta ƙare zancen tare da gyara mini Kwanciyata ta ja hijabin ta lulluɓe mini ƙafafuna da shi, ta fita rufe ƙofan da ta yi ya yi daidai da bugawan da zuciyata ta yi tamkar za ta ɓalle allon ƙirjina ta fito waje ta daka rawan disko. Tausayin kaina da na ahalina ya mamaye mini ruhina hawaey suka jiƙa mini fuska lajab kaina ya sara ƙirjina ya ci gaba da tsananta bugu.

A bayyane na furta"Anty ki yafe mini wallahi ba zan iya zama ba. Gwara na fi can inda ba a sannin ba kuma ban san kowa ba sai na fi samun kwanciyar hankali". Na ƙarƙare zancen ina tashi na zauna daɓas na leƙa ta taga na ga har gari ya soma yin haske na buɗe ƙofar ɗakin har na saƙalo ƙafata waje na hango su Yaya Alhassan suna shigowa da alama sai yanzu suka dawowa daga masallaci na yi wuf na shanye ƙafata na tura ƙofar ina leƙan su, zuciyata ta harba ganin Yaya Alhassan ya nufo ɗakin yayin da Amir da Umar suka shige ɗakinsu. Ban san abin da ya tuna ba sai kuma na ga juya ta ya bi bayan su Amir, na sauƙe ɓoyayyan ajiyan zuciya ina dafe ƙirjina da yake bugu. Sai da na ɓata a ƙalla mintuna biyu ina tsaye kafin na buɗe ƙofan a hankali na fito, filin gidan wayam babu kowa don ranan Anty Zulaihatu a gidanta ta kwana, na riƙe takalmana a hannu kamar ƙadangaruwan bayan tullu haka nake yin tafiya saɗaf-saɗaf na yi sa'a su Yaya Alhassan da suka shigo ba su rufe ƙofar ba. Na ja na fita waje layin babu kowa da alama daga masallacin sallan asubahi kowa gida ya shiga saboda yanayin hunturu da ake yi, sanyi ya lulluɓe ko'ina ga wani iska mai daɗi da yake haɗawa da hakan yake alamta sauƙar ruwan sama a ko wani irin lokacin.

Sai da na ƙarewa ko'ina kallo gabar da yamma kudu da arewa kafin na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya mai nauyin kasa na soma lafiya. Sai da na bar cikin layin gabaɗaya kafin hango titi na miƙe, na dinga tafiya har sai da gari ya yi haske sosai mutane suka fara wucewa jifa-jifa domin gudanar da lamuran yau da kullum kamar yadda aka saba. Tun da na soma tafiyar ban tsaya ba sai da na iso babban tasha da ta fi wacce muke kaiwa talla girma da kuma mutane. Na tsaya cak na kasa gaba na kasa baya illa bin mutanen da ido nake yi ina ganin yadda suke ta zirga-zirga.

"Malama ki kauce daga kan hanya kin zo kin tare ma waje".

Na yi an yi zancen a zafafe kafin na matsa aka bangaje ni saura ƙiris na faɗi. Na ja ƙafafuna na je kasan wata itaciya na zauna na zabga uban tagumi. "Baiwar Allah lafiya kuwa kika zauna kika yi shuru? Ko dai ba lafiya ne?".

A tsorace na ɗago kaina sakamakon furucin da suka yi wa ƙofofin kunnuwana dirar mikiya. Na firgita sosai da ganin yanayin wanda ya yi zancen, matashi saurayi ne da fuskarsa ta sha ɗinki kamar bayan ƙwarya ya shigan da sam babu tsari a cikinta ga jakan kayan da yake rataye a kafaɗunsa. Ban gama dawowa daidai daga giyan mamakin da ya shayar da ni ba na ƙara jin sautinsa a karo na biyu. "Baiwar Allah ko dai da kurma nake magana ne?". Na girgiza masa kaina alamar a'a.

"To na ce lafiya kuwa na ga kin saɓe daga cikin al'umma kin zo gefe kin raɓe".

"Lafiya ƙalau".

"Wannan kuma zance ne kawai kike yin sa wataƙila don ki ji daɗin bakinki. Amma duk wanda ya gan ki ya san da cewar akwai damuwa a tattare da ke".

"Babu komai".

Ya ɗage kafaɗunsa alamar babu abin da ya sha masa "to shikenan Allah ya raba mu da babu". Ya sa ya yi wucewansa ya bar ni a wajen haka na ci gaba da zama har rana ta ƙwalle ban gusa daga wajen ba, motocin da aka yi wa lodi suka fara tashi. "Baiwar Allah zai fi kyautuwa ki sauya wajen zama tun da na ga kamar zaman ne yake yi miki daɗi. Don rana ya fito kuma ya na gasa ki".

Na saci kallonsa da gefen idona kafin na tashi daga wajen kamar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki na sauya wajen zama ya biyo. "Motar wani gari za ki shiga ne?".

Na soma zazzare idanu kamar shege a rabon gado, kamar daga sama na ji wani karan mota yana shelan sauran mutum uku motar garin jafari. Da sauri na furta "garin jafari zan je". "Ai kuwa faÉ—uwa ta zo daidai da zama ni ma garin jafari na nufa sai ka tashi kawai mu shiga mota".

Na sadda kaina ƙasa"kuɗin motan ne ya faɗi a hanya ta ta zuwa nan". "Ba komai kar ki ji kin damu mu shiga ba zai gagara ba". Ban kuma cewa komai ya yi gaba ina bin sa a gaba kamar raƙumi da akala har cikin motar babu jima aka sama ciko mutum ɗaya motar ta cika. Karan motan ya zo ya karɓan kuɗi riƙe da wani takarda a hannunsa in ba ka da kuɗin sai ya ce ka sanya lambar wayan wani nata ta yadda ko da na Allah ya kasance ba fata ake yi ba za a tuntunɓe sa. Ko da aka zo kaina na rasa lambar wayan wanda zan saka ƙarshe da tunanina ya ƙore na saka lambar wayar Abbana ina rubutawa hawaye suna jiƙa littafin haka har na gama, na yi saurin goge su don na ga yadda mutumin ya kafe ni da ido kamar majigi.

Tun da motar ta ɗau hanya na ji gabaɗaya hankalina ya tashi nutsuwata ta yi nisa da gangar jikina. Tun da nake a rayuwata ban taɓa jin sunan garin jafari ba balle har na yi tunanin zuwa cikinta, ban san kowa ba amma yau ƙaddarata ta ja ni zuwa gare ta. Tafiya ce mai nisan gaske don a hanya muka sallan zuhur da kuma Asr dab ƙiran sallan magriba muka iso kowa ya fiffito, nan fa idona ya raina fata don ban san inda zan nufa ba. Tsoro da firgicin da nake ciki ya ƙara hauhawa tashin hankalina ya ninƙu.

"Baiwar Allah ke kuma haka ake yi za ki fito ba tare da kin jira ni ba". Na yi ƙoƙarin ɓoye firgicin da nake cikin kafin na furta"a'a ba haka ba ne ina sauri ne shi yasa". Ya ƙare mini kallon tsaf kafin ya ce"ina kika nufa daga nan? Kuma ke da za ki yi wannan doguwar tafiyar nan na gan ki ko jakan kaya babu". Na daburce na kasa cewa komai ina ta inda-inda da na kamo bakin zaren maganan sai ya zille. Ya ƙara taku uku ya matso kusa da ni"tun kallon farko da na yi miki na ga ne akwai damuwa da firgici a tattare da ke amma kika nuna min ba komai. Tun da na gan ki babu ko jaka na dasa alamar tambaya akan ki don na san nisan tafiyar jafari da irin lalacewar hanyarta da wuya mutum ya ce a wuni guda ya dawo a ranar. Kin gan ni nan da kike ji da gani na ga abubuwa da yawa a cikin wannan duniyar, na ga ƴan mata kala daban-daban na yi mu'amala da mutane iri-iri. Tun daga yanayinki na yi zargi biyu wanda ciki dole ɗaya ya tabbata ko dai cikin shege kika yi kika gudu daga gida kike neman mafaka ko kuma iyaye ne suka wofartar da rayuwarki".

Kalamansa suka sanya hawaye suko mini kurmin idaniya da hakan ya ba shi daman ci gaba da maganan. "Wannan hawayen da kike yi ya ƙara tabbatar min da abin da nake zargi akan ki". Na haɗe hannayena waje guda"don Allah ka taimaka mini da inda zan zauna. Da zaran na sama inda zan zauna zan kama sana'a ko na aikatau ne na biya ka kuɗinki gidan hatta kuɗin motan da ka biya mini". Da mamakina sai na ga ya bushe da dariya.

"Kowacce yarinya da irin kalaman nan take fatawa Æ´an mata. Indai wajen zama ne to kin sama akwai inda zan kai ki ki zauna kuma cikin mata Æ´an uwanki".

"Na gode Allah ya saka da alkhairi".

Bai amsa mini ba ya zari jakarsa ya rataya ya kafaɗa ya tari adaidaita muka shiga ba a yi wani tafiya mai nisa ba muka tsaya a ƙofar wani gida ya fito ni ma na fito ya sallami mai adaidaitan. Kana ya yi gaba ina bin sa a baya har cikin gidan. Tun daga shigar mu na sha jinin jikina, don wasu garke ƴan mata da samari muka iske manne da juna suna ta busa hayaƙin sigari gefe guda kuwa mata ne sun tsuke cikin shigar da bai taimaka da komai wajen rufe tsiraicinsu ba sun zage sai buga caca suke yi. Ya shiga wani ɗaki ya je na jira shi a waje.

Ina tsaye na yi an kwanto a gadon bayana na yi saurin zamewa cike da tsoro. "Ke Lawisa wai me yasa kike yi min haka ne?". Ya yi zancen cikin maye yana ƙara nufo ni, duk tarin jama'ar da suke zaune a yalwataccen filin tsakar gidan babu wanda ya kawo mini ɗauki. Na kurma ihu yayin da na ga yana ƙoƙarin kai hannunsa saman ƙirjina. Lamarin da ya jawo hankalunsu zuwa gare ni sai dai babu wanda ya taso, mutumin da ya kawo ni ya fito daga cikin ɗakin yana tambayar abin da ya faru na irge masa komai. Bai ce komai ba ya ce mu shiga cikin ɗakin ya yi gaba na bi shi a baya.

Wata dattijuwar mace muka iske a ciki tana zaune da ɗaurin ƙirji a jikinta, duk da ban san giya ba amma ba ni da inkari akan cewa kwalban da take kwankwaɗa giya ne. Na tsuguna har ƙasa na gaishe ta amsa tana kallona kafin ta mayar da idanunta kansa. "Aminu wanna ita ce baƙuwar takan?".

"Ƙwarai kuwa Hajiya Babban ita ce, to ya ya kika gan ta?".

"Ba laifi komai ya yi akwai kuma yiyuwan da za sama riba akan ta".

Na gaza gane abin da suke faɗa illa rarraba idanun da nake yi, ta ƙira wata ta zo ta ce da ita ta kai ni wannan ɗakin da babu koma a cikin sa, na tashi na bi bayanta. Ta kai ta cikin ɗakin babu komai a ciki face tabarma. Za ta fice na yi saurin cewa"don Allah ko zan sama rufa na yi alwala na yi salla?". Ta yi sakeke tana kallona kafin ta ce"ruwa? Ai sai dai ki cire kuɗinki ki saya don duk abin da idanunki ya gane miki a cikin gidan nan na sayarwa ne". Tana gama faɗin haka ta fice ta bar ni tsaye cikin matsanancin mamaki na daɗe a tsaye kafin na ja kafafuna na zauna akan tabarma na kifa kaina da gwiwa ina tunanin makomar rayuwata.

Sallamar da na ji an yi ya sanya ni ɗaga kaina, na ga Aminu ne ya shigo da wasu ledodi guda biyu a hannunsa ya ajiye su a gabana ya zauna. "Ga abinci da wasu kayan amfani na kawo miki, don na san za ki buƙace su".

"Don Allah nan ina ne ka kawo ni?".

Ba tare da shakkan komai ba ya ce"nan da kike ganin gidan masu zaman kansu ne". Babu shiri na miƙe tsaye"gidan ba masu zaman kansu kuma? gaskiya Allah ya sani ba zan iya zama a cikin wannan gidan ba, gwara na fita a cikin daren nan na nema inda zan kwana".

"A cikin garin nan dai ina da tabbacin babu inda za ki samu mafaka da ya wuce gidan nan. Amma idan ki na ganin za ki iya samu ba zan hana ki ga ƙofa nan sai ki bi ta inda muka shigo ki bita. Na san ba ki da ko sisi balle ki je ki kama wani wajen, kuma ma inda za ki kama ma ɗin ki na tabbacin za ki sama tsaro a can? Ki na tabbacin in kin je can ɗin kin tsira?".

Ya miƙe tsaye yana ci gaba da maganar"nan ne ya fi dacewa da ke don haka ki na mai ba ki shawarar za ki guje masa. Ga abinci da sauran kayan amfani in ki na buƙata za ki iya ci. Sauran bayanin kuma sai gobe kafin kin yanke shawarar zama ko tafiya". Yana dasa aya a nan ya fice ya bar ni tsaye kamar gumki. Shirif! Na zube akan taburman ina kuka na ciro ɗan kwalina na cusa a cikin bakina a ƙoƙarin hana sautin fita. Rayuwa juyi-juyi wai kwaɗo ya faɗa a cikin ruwan zafi, ban da ƙaddara me ye zai kawo ni gidan masu zaman kansu balle har na yi rayuwa a ciki su?.

Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah!

A nan na kawo ƙarshe littafin DAFIN HARSHE littafi na ɗaya. Shin ya ya rayuwar Amatullah za ta kasance a cikin wannan gidan? Shin za ta tsira da mutumci da tarbiyyan da ta zo da shi? Wani irin rayuwa za ta faɗa? Wani irin tashin hankali Anty Sawwama da iyalanta za su shiga idan aka wayi gari ba su ga Amatullah ba? Ta ina za su fara neman ta? Sannan daga ƙarshe wani irin gwarama za a yi tsakanin Anty Sawwama da Hafsatu idan ta ji labarin ɓacewar ɗiyarta?. Duk amshoshin waɗannan tambayoyin suna cikin littafi na biyu wanda za a posting ɗin sa daga ranar 10 November 2025 in Sha Allah, akan kuɗi naira N500 kacal babu ragi babu ƙari. Ga mai buƙata ƙarin yana iya tuntuɓata ta wannan lambar kamar haka 07038908713 Abin lura: ba complete document ba ne posting za a dinga a paid group daily har mu gama.

End of current loaded text.