[11/10, 12:22 p.m.] 💎Diamond Bhatool 💎: Typing 📲
🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡 (All in a big family 🏠)_ ★TAKUN ƘARSHE★ [Labari/Rubutawa] *Fadimatu Adamu Hassan*💎 *A.k.A Diamond Bhatool* *(Famanté)*
Wattpad: @diamond_bhatool Arewabooks: @diamondbhatool
_Ƙirƙirarren labari mai cike da ƴan'uwantaka, gwagwarmayar rayuwa, makirci, mugunta, hassada, munafurci, rashin tausayi da kuma dauwamammiyar soyayya maras iyaka_
_Creative work of love vs. societal expectations., family bonds and loyalty, Identity and self-acceptance, Hypocrisy and jealousy's destructive power._
*Chapter 1: Zahrah settled down at Abatcha estate*
*PAGE* 0️⃣1️⃣
_Assalamu Alaikum, barkanku masoyana na ɓoye da Kuma zahiri, yau Diamond Bhatool ta fere alƙalaminta tare da sabunta shi don cigaba da rubutun littafin *A BABBAN GIDA*, ina fatan masoya zaku bani haɗin Kai sosai ta hanyar sharing da Kuma sharhi ga duk update da na sake muku. Taku har kullum, ITZ Diamond Bhatool 💎._
_Sannan masu son amfani da littafi na ko buƙatar karanta shi, ƙofa buɗe take bayan samun izini daga gare Ni, na gode._
_Wannan shafin naku ne Angels ɗina da koyaushe nake alfahari da ku, Meenal da kuma shaheedah, love U much 💕 😘_
﷽
“Maaa..ma...dii...diiiiiiiiiii...diiiina...ceeee” Daga haka ta faɗi sume. Da sauri Daddy da kuma Laraba suka yo kanta kowa ransa fal tambayoyi. Daddy da kansa ya ɗaga Hajjaty ya ɗaura ta kan doguwar sofa da ke parlourn. Da hannun yayiwa Laraba alamar ta kawo mishi ruwa. Bayan ta dawo ta bashi, daga nan ya sa ta ta shigar da baƙuwar da basu san sunanta ba ciki, a hannunsa ya shafa ruwa sannan ya shafi fuskar Hajjaty da ke kwance. Ajiyar zuciya ta sauƙe tana buɗe idanunta don ƙara tabbatar da abunda ta gani, Madina ta dawo gare ta. A rarrabe ta furta “Ya...U...dai...ta..ta...da...w'plp00lp0liikp8im00oA ɓangaren Zahrah tun lokacin da tsohuwar ta faɗi jikinta yayi sanyi zuciyarta ta k tun daga lokacin ta ji duk wani ƙarfin guiwa nata ya baje, tsoronta ɗaya ne ma kada su ƙi aminta da zamanta, in dai kuwa hakq ta faru ba ta da madogara sai Allah, daman nan ne hope ɗinta, ta nan ne ta ke san ran zaa nemo Mama, to su ma yanzu ba ta da assurance na zama da su ɗin. Laraba ce ta zo ta kalle ta cike da girmamawa don su al'adar wannan gida haka take, komai ƙanƙantar mutum dole a girmama shi. “Ƴan mata Alhaji ya ce a kai ki masauƙi, ki biyo ni” Miƙewa Zahrah tayi ta bi bayan Laraba, dogon corridor suka bi, bayan sun ƙare suka tsaya dai-dai wata ƙofa, ita dai Zahrah ido ne kawai nata, Laraba da kanta ta buɗe mata ɗakin ta ce “ki shiga ki watsa ruwa ki huta, ni bari na je na kawo miki abun taɓawa” Da kai ta bata amsar tana shigewa cikin ɗakin wanda tana shiga sassanyan iska mai cike da ni'ima da kuma daddaɗan ƙamshi ta bugeta. Lumshe idanuwanta tayi ta ce “Allah yayi duniya da kayan morewa, kamar ba za'a mutu ba!” sai kuma ta ajiye Ghana must go nata a gefe tana ƙara ƙarewa ɗakin kallo, dontunda take bata taɓa ganin ya shi ba a rayuwarta kai ko gidan Ammin Badi'a da take ganinsa mai kyau ko rabin wannan bai yi ba. Ɗan taɓe fuska tayi kamar zata yi kuka. “Allah sarki Mama na ko ina kike?, yaushe zaki dawo gare Ni? Waige-waige Zahrah ta fara tana neman ƙofar da zata Kaita toilet ɗin don ta watsa ruwa kafin nan, ƙofar da ta hango yasa ta nufi wurin.
Ko da ta shiga toilet ɗin da ƙyar ta iya sarrafa bayin saboda bata taɓa amfani da kwatankwacinsa ba, in taƙaice muku dai Zahrah bata fito ba sai da ta taɓa komai na ciki saboda tsantsar curiousity irin nata. Tana fitowa ta nufi Ghana must go nata ta buɗe, cikin kayan da ta kwaso babu laifi suna da kyau musamman na bibalo da ta juyo ta taho da su. A cikinsu ta cire wata riga da skirt na atampa ta saka, ta yafa veil blue Wanda ya shiga da atamfar.
Kamar wacce akai ma albishir na aljanna haka take murmushi babu ƙaƙƙautawa, knocking da taji ana yi yasa ta gyara zamanta a kan gadon tana faɗin “A shigo”, da ƙyar ta gimtse dariyar da ke cinta saboda yadda wai yau ita ke bada umarnin a shigo. Laraba ce ɗaule da tray wanda aka jera food flasks kusan huɗu sai kuma jug da cup a gefe, plate, spoon da kuma fork sai wuƙa.
A gaban Zahrah ta ajiye ita kuwa Zahrah kamar bata gani ba sai da Laraban ta ce “Ga abinci nan Hajiya ” “Na gode” ta tsinci kanta da bata amsa. Sai da taji ƙarar rufe ƙofar Laraba kafin ta tashi daga gadon tana juyawa. Tsawon daƙiƙu biyu tukun ta jawo tray ɗin ta zauna kan carpet ɗin da ke Malale a ɗakin. Ɗaya bayan ɗaya ta buɗe flasks ɗin tana zaro ido tare da lashe baki kamar wata mayya. “Wai wa wai!, yau akwai shagali, Ni Zahrah aka titso ma wannan abinci!” ta faɗa tana riƙe haɓa sai kuma ta gyara zama ta zuba abincin ta fara ci. Sai da ta ƙoshi tukun ta tura tray ɗin gefe sannan ta zuɓa coconut juice da ke cikin jug ɗin a cup ta sha. Ta daɗe bata yi irin wannan cin ba yasa taci tayi nak da ita kafin ta baje sai kuma bacci.
Da azahar ma Laraba haka ta jibgo mata abinci, bayan ta ci ta yi sallah sannan ta kwanta.
**************************
*Toro* *Jahar Bauchi*
“Sannu baiwar Allah, sannu, sha maganin kada ki zubar fa” Tsohuwar ce ke faɗa yayin da take bawa matar da aka tallafo ta alamar dai ba mai lafiya bace musamman yadda ƴan matan biyun suka dago ta daga kwance.
Kamar ta san me aka faɗa mata bata dawo da ruwan maganin ba, ganin ta sha har ya ɗan tsirga mata yasa suka mayar da ita kwance. Tsohuwar ta dubi ƴan matan ta ce “ke Balki ɗakko zani a ɗaki ki lulluɓa wa baiwar Allahn nan kada ƙudaje su takura mata.” “To Inna ” ta bata amsa tana miƙewa tsaye sannan ta wuce ɗauko zanin. Ɗayar da har yanzu ke zaune gefen matar ce ta kyaɓw baki tace “Inna wai don Allah ina kuka samo matar nan?” Harararta tsohuwar tayi tace “Bani waje Nafisa, ke dai ba zaki taɓa canzawa ba shegen gulma kamar uwarki salamatu” zaro ido tayi jin an haɗo da uwarta sai kuma ta tura baki. “Kai Inna ai ba gulma bace, kawai tambaya ce, Allah matar ne ta bani tausayi kuma wallahi na taɓa ganin mai kama da ita” Cike da zumuɗi Inna tace “Matso nafisatu, faɗa min a ina kika taɓa ganinta, wallahi Kinga wannan baiwar Allah mugun tausayi take bani, kinganta wallahi a can wajen kangon nan na layin su Mamuda na ganta kwance, ke nifa na zata aljana ce.” “To Inna shine sai kika ɗaukota?” Balki ta tambaya. Inna tace “Kinga Balki rufa min asiri, bayan na ganta sai na ƙarasa na tambaya mutum ko aljan, shine naji shiru, wallahi haka kawai ta bani tausayi saboda kayan jikinta tsaf tsaf suke kamar dai kurciya aka mata. To da Mamuda yazo wucewa cikin Sa'a na saka shi ya kawo ta gida shine nake bata jiƙe-jiƙenmu na gargajiya, amma nayi magana da Malam Sufi yace zai zo ya duba ta.”
Jugum suka yi suna kallon Inna kowa na jajanta batun baiwar Allahr, gashi kuma tana mugun yi musu kama da wata da suka taɓa gani a social media. Kawar da tunanin suka yi suka ci gaba da hirarsu da kakar tasu.
**********************
*Oxford University of London*
Samari ne biyu zaune kowa na fuskantar ɗan uwansa sai kuma table ɗin da yayi musu shamaki. Kyawawa ne duk su biyun ga kuma tsantsar kama da suke da juna sai dai ɗayan ya ɗara ɗan uwansa kyan fuska da kuma na jiki.
Mai ƙarancin kyau ɗin ne ya dubi agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya ce “Sadauki time ya cika fa, we've to go no, Alhaji Baba yace da mun koma na ƙira shi na haɗa ku tunda kai ka rufe wayar ta ka” Wanda aka ƙira da Sadaukin Kamar ba zai bada amsa ba can kuma sai ya ce “Ok, amma Khalil sanin kanka ne ba don shi na rufe wayar ba ko?” Baki ya kyaɓe yana faɗin “Wannan kuma kai ya dama Sadauki, na riga nayi iyakar iyawa ta ganin ka rage wannan ƙunci da ka yafa wa kanka amma abu ya gagara, to ya kake so kuma nayi maka?, kaga yanzu dai let's get going, in mun je we'll talk”
Ba tare da ya ce komai ba ya miƙe jiki babu ƙwari yana ɗaukar key da kuma tablet ɗin da ke kan table ɗin, daga haka suka wuce zuwa masauƙinsu kasancewar a hostel suke.
Ko da suka isa Khalil ya ɗauko wayarsa kasancewar ba da ita ya fita ba, number Alhaji Baba ya ƙira, bugun fari kuwa aka ɗaga wayar, da sallama a bakinsa kafin ya ce “To na cika alƙawarin tsoho mai ran ƙarfe, ga Shalelen da ya ɓoye maka kansa nan kuyi magana” daga haka miƙawa Sadauki da ke kallonsa ta gefen ido wayar.
Amsa yayi tare da kara ta a kunnensa sai kuma yayi shiru. “Sadauki!” kamilalliyar Muryar dattijon ta bayyana. Shiru Sadauki bai amsa ba, sabo da halinsa yasa tsohon ya ce “Kana ji na ko?” “uhm” ya bashi amsa a taƙaice. “Tun jiya nake famar ƙiran wayarka amma bana samu, na shiga damuwa sosai” sai a lokacin Sadauki ya ɗan saki fuskarsa tare da sanya wani tsadadden murmushi kanta. “Ina lafiya Alhaji Baba, Ka daina damuwa sosai a kai na, zan kula da kaina yadda ya kamata” Alhaji Baba ya ce “Ai ba zan iya ba, musamman da Baban ka ya tuntuɓe Ni da zancen nan, Abinda nake so da kai yanzu shine ka buɗe wayarka, duk wanda ya ƙira ka ka ɗaga wayarsa ka nuna masa babu komai kaji?” “Ok” ya faɗa a taƙaice lokaci ɗaya kuma fuskarsa ta sauya launi zuwa ja kamar wadda aka daka. Jin shirun yayi yawa yasa Alhaji Baba faɗin “Tunda baka son magana da Ni Sadauki bawa Khalil wayar”
Ba kunya sai tsoron Allah haka ya miƙawa khalil ɗin wayar shi kuma ya wuce can cikin ɗakinsa tare da zubewa kan gadonsa.
******************************
*ABATCHA ESTATE*
Jerin motoci ne kusan biyar waɗanda dukkansu suka kasance na kallo suka Turo hancinsu zuwa katafaren estate ɗin, makeken gate ɗin guards suka buɗe, nan suka samu damar shigewa ciki. A mai flat wato ɓangaren tsoffin gidan suka yi parking motocin, nan suka fara fitowa.
Cikin waɗanda suka fara fitowa ne ɗayan su ya buɗewa Alhaji Baba ƙofar motar ya fito. Masha Allah, kyakkyawan dattijon ya tako da taimakon ɗaya daga cikin mutanen wanda ke tsantsar kama da shi. Haka sauran suka biyo bayansu zuwa cikin gidan.
Babu kowa a katafaren parlourn wanda ya kasance mai faɗi da yalwa sosai, Wanda ke riƙe da Alhaji Baba ne ya zaunar da shi kan kujerar sannan ya nufi wani ɗaki wanda ya ƙara tabbatar da cewa ɗakin Hajjaty ne. Ganinta zaune kan sallaya alamar dai sallar maghrib ta idar ya sa ya ƙarasa gunta yana risinar da kai ƙasa. “Sannu da gida Hajjaty” Ɗagowa Hajjaty tayi tana murmushi ta ce “A'ah Muhammad kun dawo kenan!” fuska sake shima ya amsa mata da faɗin “Eh Hajjaty mun iso kuwa yanzu” “To bari na sa Laraba ta kawo muku abinci sai ku ci ko” Ba tare da ya Musa ba suka fito tare da Hajjaty, sauran suma dake zaune ƙass suka miƙa gaisuwarsu ga Hajjaty, fuska sake ta amsa tare da ƙwalla ƙiran Laraba. Abinci ta jera musu kan dogon table da ke ɗauke da aƙalla kujeru hamsin sai kuma ta koma. Ganin lokacin Isha yayi yasa suka wuce masallaci kawai. Suna dawowa kuma suka baje abincin suka fara ciki.
Sai da suka kammala kafin Dattijo ɗazu (Daddy) yayi gyaran murya ya ce “To! Ɗazu fitarku wani baƙon al'amari ya faru har ya kai ga Hajjaty ta suma” sai kuma yayi shiru. Zuciyar Abba har ta fara bugu don tunaninsa ko wani abu ya faru da matarsa ne da take da shegen jarabar tsiya. “Akwai wata baƙuwa da ta kusa sati tana jele estate ɗinnan sai dai bata samu damar shiga ba sai yau. Kar na ɓata muku lokaci dai wannan yarinya kana ganinta ka ga jinin gidan nan, suna mugun kama da ƴar uwarmu ƙwaya ɗaya wacce ta ɓata shekarun baya.”
Zuciyarsu ce ta buga a tare kowa fuskarsa ta sauya musamman Alhaji Babba wanda duk cikinsu ya fi yin sabo da ƴar uwartasa kafin ɓatanta. “Yanzu dai babu wani ɓata lokaci ko jan magana, ina ga za'a iya ƙiranta yanzu a ji daga bakinta daga ina take idan har ta tabbata jinin mu ce sai a haɗa taro gobe in Allah ya kaimu” Kowa yayi na'am da maganar Daddy shi yasa Hajjaty da ɗauki da kuma anxiety suka lulluɓe ta ta ƙwalla ƙiran Laraba, nan ta sanar da ita tana son ganin baƙuwar ne ta ƙira ta.
*Me kuke tunani game da wannan labari mai cike da cakwakiya, ƴan uwantaka, munafurci, soyayya da kuma saran ɓoye (na billyn Abdul)*
*_Yanayin yadda naga kun amshi littafi na biyu ta hanyar yi min sharhi shi zai sa na ci gaba da muku typing babu ƙosawa, mutane na na channel kuma idan bana ganin reactions zan daina kawo muku shi baki ɗaya, sannan kada a mance ake taya Ni sharing zuwa wasu groups ɗin, wannan ma salon ƙauna ne, ina so saƙon ya kai inda ya kamata, ku sani DIAMOND BHATOOL taku ce!🤗😍😘_*
[12/10, 7:56 p.m.] 💎Diamond Bhatool 💎: *_Typing 📲_*
🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡 _(All in a big family 🏠)_ ★TAKUN ƘARSHE★ [Labari/Rubutawa] *Fadimatu Adamu Hassan*💎 *A.k.A Diamond Bhatool* *(Famanté)*
Wattpad: @diamond_bhatook Arewabooks: @diamondbhatool
_Ƙirƙirarren labari mai cike da ƴan'uwantaka, gwagwarmayar rayuwa, makirci, mugunta, hassada, munafurci, rashin tausayi da kuma dauwamammiyar soyayya maras iyaka_
_Creative work of love vs. societal expectations., family bonds and loyalty, Identity and self-acceptance, Hypocrisy and jealousy's destructive power._
*Chapter 1: Zahrah settled down at Abatcha estate*
*PAGE* 0️⃣2️⃣
_Sadaukarwa gare ku masoyan asali, boyayyu da kuma wanda suka bayyana a zahiri, Allah ya bar ƙauna Ameen_
*Masu Neman labarin daga farko kuyi following channel ɗin nan zaku samu:* https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*Join my WhatsApp group 1* https://chat.whatsapp.com/IWQW3ytbVc611XLon2sn66
*Join my WhatsApp group 2* https://chat.whatsapp.com/EKFnHpoI54t1MvodB5HgYB
﷽
Hajjaty da kanta ta ƙwalla ƙiran Laraba da ke kitchen, nan ta faɗa mata saƙon da zata isarwa Zahrah, ko da ta faɗa mata ta ja ƙofar ta rufe mata, wasu zafafan hawaye ne suka gangaro mata yayin da wani irin fargaba da tsoro suka lulluɓe ta. Cike da ƙarfin hali ta miƙe tare da goge hawayen sannan ta nufi ƙofa.
Taron jama'ar da ta gani wanda mafi akasarinsu maza ne kuma da gani manya ne yasa ta ɗan dakata tana dafe ƙirjinta. Kanta ta sunkuyar ƙasa sakamakon jin Muryar Hajjaty tana faɗin “Ƙaraso nan yarinya”. Babu musu ta nufi wajensu zuciyarta ba bugawa da sauri da sauri, Dukkansu kowa idonsa a kanta yake hakan yasa har ƙafarta ta fara harɗewa kamar zata faɗi, a tare zukatansu suka buga sai dai maganar Alhaji Baba yasa duk hankaulansu dawowa gare su.
Hajjaty ne ta nuna mata gefenta sai dai ko da ta ƙaraso sai ta zame ƙasa ta zauna a kan carpet dai-dai ƙafar Hajjaty. Cikin murya mai ɗauke da zallar izza da nutsuwa Alhaji Baba yayi sallama suka amsa masa. Gyaran murya yayi yace. “To ba komai ya tara mu nan ba sai batun da na riska bayan dawowa ta daga tafiya. Ɗan dakatawa yayi tare da mayar da dubansa ga Zahrah wacce kanta ke ƙasa a takure. “Baiwar Allah kin zo cikin wannan ahali da abun al'ajabi sai dai mu nan bamu san ke wacece ba, idan babu damuwa muna son sani.” Ya idasa yana ƙara kallon Zahrah da yake ji kamar ya rungume ta saboda tsantsar kamanninta da ɓatacciyar yarinyar su.
Ba tare da Zahrah ta ɗago ba ta goge hawayen da suka zubo mata tare da jan hanci, “Da farko suna na Zahrah Abdulkarim Kuru, na zo ne tun daga jahar Bauchi saboda saduwa da ku. Ni ɗin a taƙaice ba kowa bace ga wannan ahali face jika!” Gabansu ne ya faɗi jin furucinta, sai dai ita Zahrah murmushi kawai ta yi tunawa da baƙar ranar da aka rasa Mama. “Eh Ni ɗiyar Madina ce, tabbas ita ce mahaifiya ta, tabbacin hakan kuwa shine kamanni na da ita, ban kwaso komai na mahaifi na ba sai yatsu.” Nan dai ta fara basu labarin ɓatan Mama Wanda a ainihi guduwa tayi kamar yadda tayi mata bayani a kwanakin baya, guduwarta zuwa wurin Abbanta, auren su, haihuwarta, mummunan kisan da aka yi wa Abba, daga nan ta hau bada labaron auren Mama da kawu, wanda ya kasance dan uwa ga Abba, irin zaman auren da suka yi, har zuwa ɓatan Mama. Tuni jikinsu yayi sanyi gabaɗayansu. Hajjaty kuka take shaɓe-shaɓe tare da rungume Zahrar a ƙirjinta kamar wacce za'a ƙwace ta daga gare ta. “Ni dama na sani, Madina ta na raye, gashi Allah yayi haɗuwarmu da tsatsonta kafin ita, amma wannan miji nata Allah yayi mugu wallahi sai ya san ya taɓo ƴar asali!” Hanci ta fyace ta cigaba “Garba, Umaru, Usmanu, Gadanga, Muhammadu da kai Yusufu don Allah a ƙara ƙaimi wurin sanar da jama'a da kuma jami'ai har Allah yasa Madina ta dawo gare ni”.
Kowa jimami yake yi kuma jikin kow yayi sanyi sai dai ganin halin da Hajjaty ke shirin saka kanta yasa suka ɗan kawar da damuwarsu duk da cewa yanayinsu dama saisaitacce ne tunda sun samu tabbacin Madinar na raye. Daddy wanda duk cikinsu yafi zafi ya ce “Tabbas wannan miji na Madina ya cutar da ruhikanmu, Wallahi sai ya san ya taɓo jinin ABATCHA, sai ya san ya taɓo ƴar Babban gida!” Dafa shi Alhaji Baba yayi shima yana ƙoƙarin kawar da tasa damuwar “Ya isa haka Umaru, ka kwantar da hankalinka yanzu abu mai muhimmanci shine kau haɗa kai ku bada himma a nemo Madina, shi kuma mijin daga baya ma san yadda zamu yi da shi.
Shawarar da Alhaji Baba ya basu kowa yayi na'am da ita, nan Alhaji Babba ya murmusa ya ce “Yaki yarinyar kirki, zo jikin babban uba ko?” cike da matsananciyar kunyarsu ta taho garesa, rungume ta yayi sannan ya sumbaci kanta kafin ya ce “Photocopyn Madina, Allah yayi Miki albarka Zahra'u.” da “Amin” Zahrar ta amsa kafin ta nufi sauran jama'ar da ke Parlourn suma ta kwashi albarka. Kasancewar lokacin sallah ya ƙarato daga nan aka rufe ɗan ƙaramin zaman da Addu'a, nan mazan suka fice zuwa mosque da ke cikin estate ɗin.
Ko da suka fita Hajjaty da fara'a ta ƙara rungume Zahrar, tsawon wasu daƙiƙu kafin ta sake ta tana tsura mata ido. Cikin ranta tana ƙara tausayawa rayuwar da ahalinta da Kuma bar soyuwarta Madina tayi, sai kawai ta yi murmushi cike da son kawar da damuwarta ta ce “Muje can ɗaki na kiyi Salla Zahrah, idan Laraba ta zo ta kwaso Miki kayanki” Kan Zahrah ƙasa ta ce “To Mama” Hararar wasa Hajjaty tayi mata tana riƙe da hannunta tace “ki ƙira ni Hajjaty kamar yadda kowa cikin estate ɗin nan ke kira na, kinji?” “Eh Hajjaty ” ta bata amsa har lokacin bata sake ba.
Sallarta ta maghrib ta gabatar shimfiɗa ɗaya da Hajjaty, zuciyarsu tana ƙara kusantuwa da juna, bayan sunyi Sallar Hajjaty ta fara ɗauke Zahrah da zance, tun tana bata amsa a kunyace har dai ta sake suna Hira, ko da Alhaji Baba ya dawo, babban Parlourn sa suka wuce kamar yadda Hajjaty ke yi koyaushe. A nan dai Zahra ta saki jiki da ƴan kakannin nata da suka fara mantar da ita duniyar ta hanyar ɗumbun kulawa da so da suke nuna mata cikin sa'o'i ƙalilan.
Wannan kenan.
Lokacin Isha da yayi ne Alhaji Baba ya fita daga gidan zuwa Masjid tare da rakiyar Daddy. Su Zahra a nan suka yi sallar su kowa ya nuna godiyar sa ga Ubangiji, nan suka yi addu'a Allah ya bayyana Mama. Ko sallayar basu naɗe ba Maid ɗin Hajjaty, Laraba, ta shigo hannunta ɗauke da wani dogon tray wanda ke shaƙe da kuloli shaƙe da. Kuma jugs.
Tana gama jerawa ta fice, few minutes ta dawo da wasu kulolin ta jera, ta zo fita Hajjaty ta dakatar da ita “Laraba, in kin fita ki ɗauko kayan zahra ki mayar da su can ɗaki na” Cike da girmamawa Laraba ta amsa mata da faɗin “To Hajiya, yanzu ma”. Daga haka ta fice.
Tsawon wasu daƙiƙu, misalin 7:23pm suka yi sallama zuwa parlourn, saɓanin fitarsu ɗazu su biyu, wannan karan tare da wasu samari kyawawa guda huɗu, Daddy kuma baya cikinsu. Da sallama suka shigo fuska sake. Alhaji Baba zama yayi a kan kujerarsa su kuma suka zauna ƙasa kamar yadda Zahrah da Hajjaty ke zaune.
Cikin samarin ne ɗaya ya kalli Hajjaty fuska sake yace “Barka da dare Hajjaty” Suma sauran suka gaishe ta, kamar yadda yanayin fuskarsu yake haka ta amsa musu tana murmushi “Lafiya ƙalau yaran nan” sai kuma ta haɗe gida kamar ba ita ce ke cikin fara'a daƙiƙu kaɗan da suka gabata ba. “Duk nayi fushi da ku, tsawon jiya shiru shiru babu wanda ya leƙo cikinku, ƴar gaisuwar safiyar nan ma babu wanda ya leƙo saboda kun maida Ni mutuniyar banza” su dai kallon Hajjatyn kawai suke suna kwaɓe fuskokinsu ba tare da sun katse ta ba. “Amma iyayen ku da ke da daraja ai kun shiga kun gaida su ko?”
Gaban Hajjatyn suka dawo tare da durƙusawa ƙasa, fuskar tausayi suka yi cikin haɗin baki suka ce “Haba tsohuwa mai ran ƙarfe, uwar gida sarautar mata a gidan tsoho mai ran ƙarfe, ki yi wa ƴan jikokin ki haƙuri ba zasu kara ba.” Ɗan sakin fuakarta kaɗan tayi ta ce “Ai yau ba zan yi haƙuri ba, nasan da yarin kirkin nan Mahiru na nan da ban shaƙi takaicin ku ba, shi kafin ya gaida iyayensa sai yazo ya duba lafiya ta, Allah sarki mahiru.”
Ƙara kwaɓe fuska suka yi kamar zasu yi kuka, kamar haɗin baki kuma suka kama kunnuwansu suna faɗin “Ayi mana afuwa Hajjatyn mu”. Dariya sosai Hajjaty tayi, su dai da mamaki suke kallonta though sun San halinta, lokaci ɗaya in ta birkice kamar ba zata dawo dai-dai ba, sai kuma kuga ta dawo unexpected. Shiru Hajjatyn tayi tana kallonsu tana murmushi ta ce “Shikenan yaran kirki, kun ci albarkacin yau ina cikin farin ciki na haƙura” fuska sake ta yadda zaka fahimci ainihin farin cikin da suka yi da jin zancenta suka ce “Mun gode Hajjaty tamu abar ƙaunarmu”
Alhaji Baba da ke kallonsu sosai suka burge shi, yana ƙara alfahari da jikokinsa saboda ɗa'a da biyayya da suke da shi, sai kuma ya kai duban sa ga Zahrah wacce kanta ke ƙasa tun shigowar samarin, ganin she's uncomfortable yasa ya buɗe baki zai yi magana sai Muryar ɗaya daga cikin samarin ta katse masa hnazari. “Hajjaty farin cikin menene wannan ya ƙwacemu daga fushinki mu taya ki celebrating?” Kallonta ta mayar ga zaharh da ke gabanta, sai kuma ta jawo ta jikinta, su ma a lokacin idanuwansu ya kai kanta, sai dai sun yi mamakin ganin ƴar matashiyar budurwa tare da Hajjaty.
Hajjaty ta ɗago kan Zahrah tana dubanta, ba tare da t kallesu ba ta ce “Albarkacin jika ta daga gudan jini na Madina” Da mamaki suka kalleta, in basu manta ba kullum sai Hajjaty tayi magana kan Madina da take cewa ɗiyarta ce auta da ta ɓata tsawon wasu shekaru. Ganin rashin fahimta shimfiɗe kan fuskarsu yasa Hajjaty tayi gyaran murya tana faɗin “Ɗiyar Madina ne yau Allah ya kawo ta cikin ahalin nan, Zahra'u” ɗagowa Zaharah tayi tana duban Hajjaty, har lokacin idonta bai kuskura ya kai kan samarin ba. “Kinga ga yayunki nan, ku kuma ga Zahrah ƙanwarku, gobe zaku ƙara saninta, in kun fita ma ku sanar da sauran ƴaƴan akwai taro gobe”.
A tsorace Zahrah ta dube su sai kuma ta sunkuyar da kai saboda kwarjin da suka yi mata, ga kuma kyau da Allah yayi musu kamar me. “Ina yinin ku” ta faɗa cikin rawar murya. Tare suka amsa da lafiya, mai surutun cikinsu ne ya ce “Sannu Zahrah, muna matuƙar farin ciki da dawowarki cikin ƴan uwanki, fatan zaki karɓe mu hannu bibbiyu, mu dai nan muna farin ciki da zuwanki, ɗago ki kalle mu matsayin ƴan uwa na farko da kika fara gani” ya Idasa cikin sigar zolaya. Ɗagowa tayi ganin basu nuna wani ƙyama gare ta ba kamar yadda da tayi zato.
Cikin sakin fuska yace “Suna na Auwab..” “Ni kuma Aufa...” Ni kuma Tajuddeen” sai kuma Ni “Faruq” murmushi tayi tace “Na gane fuskokin ku, sunayenku masu daɗi” cike da zolaya Ya Auwab ya ce “Ke fa bamu san naki sunan ba” “Zahrah” ta basu amsa tana murmushi. Ta matuƙar burge su, ga ta kyakkyawa son kowa, ko maƙiyi ba ya kushe ba, ita ma bata ɓangaren tunanin kirkinsu take tana addu'ar Allah dai yasa sauran family members ɗin su kasance haka.
Ƴar hira suka fara janta da shi saboda ta ɗan ƙara sakewa da su, ganin sun ware kansu yasa Hajjaty faɗin “Ku tashi kuyi dinner Ku bar min jika, daga zuwan ku kuna shirin ƙwace min ita!” Ya Aufa ya ce “Kai Hajjaty ki bar mu mu gana da ƴar uwarmu mana” Danƙwalo ta kai masa ta ce “Ungo nan!, kai Auwabu ka kiyaye Ni, ku tashi nan ayi dinner.”
Gabaɗayansu miƙewa suka yi zuwa dining ɗin kowa ya nemi wuri ya zauna, ita dai Zahrah sai rarraba ido take tana ganin ikon Allah, Hajjaty da kanta ta samar mata waje daga nan ta fara serving nasu, ta can ƙasan idon Zahrah ke dubanta tana kula da yadda take komai. Tunda suka fara cin abincin shiru ya wanzu, ƙarar spoons da ke arangama da plates kawai kake ji. She's not comfortable eating with them shiyasa tana cin kaɗan ta dakata, tatar kallon Ya Taj tayi ganin shima ya ajiye spoon ya yago tissue ya goge baki yasa ita ma tayi kamar yadda yayi.
Hajjaty ta dube ta ta ce “Zahrah ya bakya ci” a hankali don bata son sauran suji bare su ce sai ta ci tace “Naci, har na ƙishi” “kin sha abun shan ne?” Hajjaty ta ƙara tambayarta “A'a Hajjaty” Hajjaty da kanta ta tsiyaya mata zoɓon tasha.
Bayan sun gama ci nan aka ci gaba da hira, tuni Zahrah ta gama sakin jiki da su, meanwhile Ya Faruq ya tura musu saƙon Hajjaty na meeting gobe. Da misalin tara saura su Ya Taj suka yi sallama suka wuce, Hajjaty ma ta ce Zahrah ta taso su kwanta. Sai da suka yi wanka tare da alwala suka yi shafa'i da witri. Hajjaty na zaune kan sallayar ta ta ce ma Zahrah ta je ta kwanta, babu musu ta haye makeken gadon Hajjaty, ita kuma Hajjaty sai da ta gama laziminta ita ma ta nemi wurin bacci.
Safiya mai albarka Zahrah and Hajjaty. Fatann rayuwar farin ciki tare da Abatcha family.
_Sallar Shafa'i da Witri salloli ne da manzon Allah (S.A.W) ya bayyana cewa: « gara a baka damar yin Shafa'i da Witri akan a baka duniya da duk abinda yake cikin ta» , shiyasa manzon Allah kullum yana yin Shafa'i da Witri koda yana halin tafiya yana yin su. Karanta Sunanut Tirmiziy, Hadisi na 425._
_Zaku samu cikakken bayani kan yadda ake yin ta a channel ɗina_
★★★★★★★★★★★★
_Me kuke tunani game da rayuwar wanan ahali?, me ake aikatawa a babban gidan nan ne?, shin kuna ganin rayuwar Zahrah ta samu Salama kenan?, ina Mama ne? Ko da gaske ta mutu?, Amsoshinku na ɗaure da alƙalamin Diamond Bhatool 💎, Diamond Bhatool 💎 taku ce!👍😍_
*Vote, comment, react and share Fisabilillah!* *Vote, comment, react and share Fisabilillah!* [13/10, 12:12 p.m.] 💎Diamond Bhatool 💎: *Typing 📲*
🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡 _(All in a big family 🏠)_ ★TAKUN ƘARSHE★ [Labari/Rubutawa] *Fadimatu Adamu Hassan*💎 *A.k.A Diamond Bhatool* *(Famanté)*
Wattpad: @diamond_bhatool Arewabooks: @diamondbhatool
_Ƙirƙirarren labari mai cike da ƴan'uwantaka, gwagwarmayar rayuwa, makirci, mugunta, hassada, munafurci, rashin tausayi da kuma dauwamammiyar soyayya maras iyaka_
_Creative work of love vs. societal expectations., family bonds and loyalty, Identity and self-acceptance, Hypocrisy and jealousy's destructive power._
*Masu Neman labarin daga farko, kuyi following channel ɗina.**
*Chapter 2: People only managed to smile, nobody know how they're really hurting deep down*
*PAGE* 0️⃣3️⃣
_Sadaukarwa gare ku mutanen channel ɗina *Diamond Bhatool's library*, ina godiya da ƙaunar ku gare ni._ _Ban manta da ke ba Maryam Muhammad, ƙauna ta ta musamman, ina godiya ƙwarai
*1:00 midnight* *Unknown location but a black wilderness*
Cikin ƙasurgumin baƙin dajin wanda tsabar duhunsa ko tafin hannayenka baka iya gani, duhun wannan daji ya wuce misali, ya wuce siffantawa ga tunanin mai karatu, amma zan iya cewa duhu ne da ba lallai bil'adama ya taɓa cin karo da kwatankwacinsa ba.
Cikin ƙankanin lokaci kuma kamar tsafi sai ga haske ya bayyana kamar safiya irin rana ta fara hudowa. Kamar ƙiftawar ido sai hasken ya ɗauke wurin ya koma kamar dai dare, amma akwai haske though bai wadata ba amma mutum kan iya ganin tafin hannunsa. Kamar daga sama kuma wani irin mummunan sauti maras daɗin amo da sauraro ya fara cika jejin, a hankali kuma sautin na ƙara kusantowa i zuwa tsakiyar wani fili wanda ke ɗauke da bishiyoyi biyu a jere, ƙatuwar bishiyar kuka ne sai kuma ta tsamiya a gefenta wacce ke da duhu kamar wani kurmi.
Tsawon wasu daƙiƙu wasu halittu da zasu kai kimanin Goma sha biyar suka bayyana, ko kaɗan basu da daɗin kallo, siffarsu tayi kama da ta goggon biri saboda gashin da ya lulluɓe fatarsu. Tsarin kama ma dai basu da maraba da goggon biri sai dai haƙwarensu zaƙo-zaƙo ne baƙaƙa da su har abun tsoro. Daga cikin waɗannan halittu wanda suke bisa tsari, wani yafi wani girma, haka wani ya fi wani. Babban cikinsu ne ya zauna can nesa da da sauran waɗanda suke hallare a wuri ɗaya, hakan zai ƙara tabbatar maka da cewa shi ɗin na musamman ne.
Wani irin sauti mai rikitar da tunanin bil'adama ne ya fara fitowa yayin da waɗannan halittu suka miƙe tsaye suna jujjuyawa kamar wanda suka shiga filin rawa. Can kuma sai ga wata walƙiya mai mugun gaske da ta haska illahirin dajin. Lokaci ɗaya waɗannan halittu suka nutsu, wasu baƙaƙen kujeru da ba zaka iya tantance da ƙarfe ko roba aka yi su ba suka bayyana a bayan kowa, nan suka zauna damas yayin da wannan halitta ɗaya dake gefe wata narkekiyar kujera ta iso bayanta, ita ma zama tayi, nan dai halittun suka fara wani kuka wanda zamu iya siffanta shi da Yaren da suke yi. Can bayan wasu daƙiƙu shiru ya wanzu.
Kwatsam!, babu zato ba tsammani wannan shugaban da ba zamu iya tantance jinsinsa ba ya fara magana irin ta mutane, abun al'ajabi ma a wurin cikin harshen Hausa. Muryar dai irin ta mutane ce amma tana fitar da wani amo na musamman wanda ke bada sauti bibbiyu kamar dai echo. “Jinjina ga Gutsirito dodon tsafi! Jinjina ga Gutsirito dodon tsafi! Jinjina ga Gutsirito dodon tsafi!!!” A tare su ma suka amsa da “Jinjina! Jinjina!”.
Shiru suka yi sannan shugaban ya ɗaura da faɗin “Ba komai ya tara mu a wannan waje ba sai don wata muhimmiyar sanarwa da nake son kai wa gare ku a matsayi na ta uwargijiyarku!” “Jinjina! Jinjina!!!” suka amsa mata cikin haɗin baki tare da ɗaga hannayensu masu ɗauke da Zara Zaran faratu masu kama da duwatsu baƙaƙe ƙirin da su.
“Akwai wata masifa da ke tunkaro wannan ƙungiya ta Devil Klans 👿, Wanda idan muka yi sake zamu iya rasa dama da ta rage mana, ƙarfin tsafi da muke da shi a duniya zai raunana, zamu rasa ikon mu! Kai mu kanmu in wannan masifa muka barta ta iso akwai tashin hankali! Don kuwa sauran ƙungiyoyi zasu yi ta kawo mana farmaki yayin da mu kuma bamu da ƙarfin kare kan mu, ku sani in dai bamu tsayar da ita ba to kowa zai yi galaba a kan Devil Klans 👿!” Surutunsu ne sama sama ke ɗan tashi yayin da shugaba wacce ta ambaci kanta da uwargijiya tayi tsit tana jira ta ji daga gare su.
Ganin lokaci na ƙure musu gashi babu wanda ya faɗi wani abu yasa ta buga sandar da ke hannunta a ƙasa, wani irin sauti da sandar ta bayar tare da fidda tartsatsin wuta yasa dukkansu yin shiru. Magana ta fara tana faɗin “Ina jira daga gare ku, Ɓurum me zaka ce?” ta idasa tana nuna wanda ke a farko ta ɓangaren hagu.
Ƙasa yayi da kai sannan ya sauƙo tare da sujjada a gabanta kana ya ɗago, cike da girmamawa ya ce “Uwargijiya ki ƙara mana haske a kai, wace irin masifa ce haka ke tunkarar tawagar mu?” Ba tare da ta kalle shi ba tana mai ɗaura jafarta kan ɗaya ta ce “Ɓurum yayi abunda ya dace! Dodon tsafi yana alfari da kai” ta faɗa tana ɗaura hannunta kan goshi. “To bari nayi muku filla filla, ɗazu na gana da Shastuna Aminiya ta wacce ita ma shahararriya ce a duniyar tsafi shine take sanar da Ni cewa haske na ya fara disashewa! Idan nayi wasa kuma kungiyar mu na shirin halaka!.
A tsorace na koma gida bisa mayafin tsafi kai tsaye fada ta da ta kasance ta sirri na shiga, ina buɗe madubin tsafi a nan na tabbatar, akwai wasu haske guda biyu da ke shirin tunkaro mu, sai dai kuma duk hanyar da zan bi na gano jinsin waɗannan haske ya faskara, abun da dai na gano shine ɗaya na ƙarfafan ɗaya ne, kuma waɗannan ruhi biyu suna gab da ƙarasowa gaban mu, idan bamu dakatar da su ba kuma za'a samu matsala, ya kamata tun wuri mu toshe duk wata hanya da zata sada mu da su, mu rufe kowacce kafa da zata basu damar tunƙarar baƙin daji. Dodon tsafi na a tare da mu!” ta ƙarasa tana ɗaga murya wacce sautin ta ke fita kusan takwas takwas from every direction.
“Ye! Dodon tsafi na a tare da mu!” Suka haɗa baki suna bata amsa. Cike da jarumta ɗaya daga cikinsu tace “Tabbas dole mu tsinkayo wannan ruhika guda biyu sannan mu datse gudirinsu ga Devil Klans 👿 cikin ikon Gutsirito dodon tsafi!, amma kafin nan, ya ke uwargijiya!” sai ya yi sujjada gabanta ya tashi “Ki bamu dama mu mu bincika daga nan sai a san yadda za'a ɓullowa al'amarin. Gobe in an fito meeting sai kowa ya faɗi ya yake tunanin zamu yi, in so samu ne ma a ce kowa yayi matsanancin bincike mu gano waɗannan ruhika biyu kafin mu ɗau mataki kan su!”
Cike da gamsuwa uwargija ta furta “Dodon tsafi ya ƙara kasancewa tare da kai Muƙal! Ka cika magajin Devil Klans 👿, Ka ƙara ƙaimi wajen ƙara gina kanka, dodon tsafi zai yi alfahari da kai!”
A haka dai suka kawo ƙarshen meeting ɗin nasu ba tare da wata kafaffiyar matsaya wacce zata ɓulle musu ba. Daga nan kuma wannan duhu ya ƙara mamaye dajin, tsawon daƙiƙu biyar sai ga haske, waɗannan halittu kuma babu su babu alamunsa, they'll disappear.
_wannan kenan!_
*Oxford University of London*
Zaune yake a katafaren room ɗin shi kaɗai, babu abun da kake ji a ɗakin sai sauƙar ajiyar zuciya da yake sakewa lokaci zuwa lokaci kamar karamin yaron da ya gama shan kuka. Saraki kenan!, yayi nisa cikin tunani wanda ya manta cewa a duniyar ma yake.
Cikin ransa babu Abun da yake tunani sai irin badaƙalar da ke cikin gidan nasu,gidan da ya zame masa tamkar baƙin kurkuku, gidan da yake jin ina ma bai kasance ɗaya daga ciki ba. “Shin me yasa ƙaddara ta tazo da haka?, me yasa rayuwa ta ta kasance haka?, na gaji! Na gaji da wannan rayuwar, ina son samarwa Kai na cikakken ƴanci ko ma yaya ne! Ina so nima nayi rayuwa ba tare da wani ciwo ko nauyi a zuciya ta ba.”
Khalil da ke tsaye kansa ne ya jijjiga kansa cike da tausayawa ɗan'uwansa kuma amininsa, how he wish yana da yadda zai yi ya samar masa mafita, but babu!. Cike da kulawa ya durƙusa gabansa ya kamo hannayensa biyu ya haɗa da nasa. Cikin raunatacciyar murya ya ce “Sadauki! Ya kamata a ce zuwa yanzu ka cire wasu damuwoyin cikin ranka, kowa da kake gani da yadda Ubangiji ke jarabtarsa, ka ƙara haƙuri, addu'a ita ce kawai makaminmu mu, ba kai kaɗai abun ya shafa ba Sadauki, mu ma nan duka family ya shafe mu, amma addu'ar da ake fadi kullum dole dai ita ɗin ce zamu riƙe, Allah ya kawo mana sauƙi cikin wannan rayuwa ya kuma sanya salama da nutsuwa cikin ahalinmu”
Runtse idanunsa da suka yi masa jajir kamar gauta yayi, zuciyarsa na wani irin tafasa, cikin rauni da kuma damuwa ya furta “Amin Dude, ina tsoron wata rana wani abun ne ya faru da tsofaffi da yaran da basu ji ba basu gani ba! Ina tsoron wani abu ya faru da su, Khalil in wani abu ya faru da su ba zan taɓa yafewa kaina ba, Ni ne sila Khalil! Mine sila!...” sai kuma ya dafe kansa da hannu ɗaya, ɗayan kuma ya dafe ƙirjinsa da ke masa nauyi da zafi kamar an ɗaura masa karfen da ya shekara cikin razanannnen garwashi.
Da sauri Khalil ya miƙe, a zabure ya fara jijjiga shi sai dai attack ɗin da ya samu ɗin ya hana shi komawa daidai!, rungume shi Khalil yayi yana ƙara jijjiga shi, ya ma rasa me ya kamata yayi a daidai wannan lokaci. Hawaye ne suka fara zubo masa kamar ƙaramin yaro, har a lokacin kuma bai daina jijjiga Sadaukin ba wanda babu alamar numfashi ma a tattare da shi “Don Allah Dude Ka tashi, ka tashi don Allah, kar ka bari baƙin cikinsu ya kashe ka su basu da asara, don Allah ka tashi ka tashi!”
Ganin dai Sadaukin ya ƙi yin ko da motsi yasa ya ƙara shiga wani matsanancin yanayin. Ya rasa ina zai sa kansa ciki ma, ƙarar shigowar saƙo yasa ya tuna da waya, da sauri ya sa hannunsa ya janyo wayar sannan ya shiga nemo numbern Doctor ɗin Sadauki da ke London. Bugu ɗaya kuwa ya ɗaga, cikin harshe Larabci ya sanar da shi halin da suke ciki shi da patient ɗinsa. Bai tsaya bashi amsa ba ya katse ƙiran.
A haka Ya Khalil ke jijjiga Sadaukin har tsawon mintuna goma. Ƙarar doorbell yasa ya zame shi daga jikinsa da sauri ya nufi ƙofar, yana buɗewa ko jiran ganin waye bai yi ba ya koma wurin ɗan'uwansa. Cike da tausayawa Dr. Arƙam wanda ya kasance balarabe ke kallon Ya Khalil ɗin ganin yadda duk ya firgice lokaci ɗaya, ɗaya ɓari na zuciyarsa kuma na ƙara jinjina ƙarfin so da kuma alaƙar jini da ke ɗawainiya da matasan biyu.
Murmushi kawai yayi shima yana mai tunawa da nasa ɓangaren rayuwar sai kuma ya shiga cikin ɗakin da sauri, First Aid kit nasa ya ajiye sannan ya nufi Sadauki da ke kwance kamar gawa. Shi kansa Dr. Arƙam ya gama sarewa da al'amarin patient ɗin nasa, zuciyarsa tayi rauni gani yake kamar zai rasa wannan patient ɗin da tunda ya fara aiki bai taɓa jin so da ƙaunar da yake yi masa ya taɓa bawa wani ba.
Da sauri ya fara fitar da kayan bada agajin gaggawa, CPR yayi ya kai sau biyar amma numfashin Sadauki bai dawo ba, nan shima zuciyarsa ta sare, hope ɗinsa kenan, tunanin me zai ƙara yi yayi amma ya kasa tunawa ga kuma Ya Khalil da ya tsare shi da ido yana jiran yaga ɗan'uwansa na numfashi. Haka dai Dr. Arƙam ya ci gaba da yi masa CPR ɗin amma shiru, tsoron da Dr. Ke ɓoyewa ne ya bayyana har hawaye na silalowa daga idanuwansa.
A tsorace ya Khalil ya riƙo hannun Dr. Arƙam cikin raunin murya yace “Dr. Ka faɗa min me ya faru da ɗan'uwa na? Ya mutu ko?, shikenan nima wallahi bin sa zanyi! Me zan yi a duniyar babu shi?, ka faɗa min Drrrrrrr.!” ya idasa yana jan ƙarshen sunan hawaye ba bin kuncinsa. Cike da ƙarfin hali Dr. Arƙam ya furta “Calm down Khalil, Umar is in need of your prayer now, so stop crying and pray for him, let's get him to hospital now, there's need for a thorough assessment and intervention, fatan mu Allah yasa ya tashi” ya idasa cikin kwaɓaɓɓiyar hausarsa.
Da sauri Dr. Arƙam yayi dialling emergency number, in three minutes time ambulance ta iso bakin apartment ɗin nasu, da taimakon Ambulance committee ɗin guda biyu suka ɗaga Yaya Sadauki wanda ke a halin rayuwa ko mutuwa sannan motar ta tashi cikin wani irin matsanancin sauri.
On the other hand Dr. Arƙam is wishing for life rather than death to his patient, yana fatan conclusion nasa na cewar he's dead ya zama ba haka ba, this time around so da kuma fata yake wani yayi prooving nasa wrong. A ɓangaren Ya Khalil shi baya ma cikin hankalinsa, surutai kawai yake yana faɗin “Wallahi Dude baka isa ka tafi ka bar Ni ba sai dai mu tafi tare, nima mutuwar zanyi wallahi, Ni Khalil ba komai bane in babu kai Sadauki! Shike nan sun ci galaba kan mu kenan idan da gaske zamu bar musu duniyar?, don Allah ka tashi Man!” Sai kuma ya fashe da matsanancin kuka kamar wani jariri.
Cike da tausayawa suke kallon wannan bawan Allah, duk da cewa basu san me Ya Khalil ɗin ke faɗi ba don yayi maganar ne cikin harshen Hausa amma sun fahimci yana cikin matsananciyar firgici da kuma damuwa. A dai-dai nan suka iso gate ɗin hospital ɗin.
**************************
_Readers! Nace my esteem fans! Da Ku dai nake kuna enjoying wannan labarin kuwa?, me kuke tunani game da rayuwar waɗannan matasa?, wace irin ƙaddara ce ke giftawa tsakaninsu da nasu ahalin? Kunji da wasu Devil Klans 👿! Nace su kuma su wanene?, kuna tunanin ƙudirinsu zai cika kuwa?, Su waye kuma waɗannan haske da ake faɗi?_ _Ku kasance da wannan alƙalami na lu'ulu'u (Diamond pen) don cigaba da samun wannan labari mai cike da tsantsar rikitarwa, zanen ƙaddara da kuma gwagwarmayar rayuwa._
_Mutanen channel ɗi na! Ina nufin my esteem Followers 💕 😘, ina ƙaunar ku da yawa da yawa, ina godiya da irin ƙaunar da kuke nuna min, tabbas yanzu na fara yadda cewa kuna a tare da Ni, zaku ci gaba da kasancewa da Ni saboda ƙaunar da ke tsakaninmu daga Allah ce!, i love you so much my esteem followers! Ina ji da Ku! Ku ɗin Ni ce, nima ku ne!._
_For more information, zaku iya tuntuɓa ta ta wannan number, WhatsApp only please: +234, 8143760764, ko kuma 07061707238/09027383866, phone call only._
*Remember that Diamond Bhatool 💎 Taku ce 💕 😘*
[16/10, 10:22 p.m.] 💎Diamond Bhatool 💎: *Typing 📲*
🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡 _(All in a big family 🏠)_ ★TAKUN ƘARSHE★ [Labari/Rubutawa] *Fadimatu Adamu Hassan*💎 *A.k.A Diamond Bhatool* *(Famanté)*
Wattpad: @diamond_bhatool Arewabooks: @diamondbhatool
_Ƙirƙirarren labari mai cike da ƴan'uwantaka, gwagwarmayar rayuwa, makirci, mugunta, hassada, munafurci, rashin tausayi da kuma dauwamammiyar soyayya maras iyaka_
_Creative work of love vs. societal expectations., family bonds and loyalty, Identity and self-acceptance, Hypocrisy and jealousy's destructive power._
*PAGE* 0️⃣4️⃣
Ambulance na tsayawa ma'aikatan suka matso kusa, da sauri Dr. Arƙam ya furta “Wani ya taho da stretcher!” ana kawo stretcher aka ɗaura gangar jikin Ya Sadauki da ke sake, kallo ɗaya mai hankali zai yi ya tabbatar cewa babu numfashi a tattare da shi. Da sauri kuma aka tura stretcher ɗin zuwa cikin asibitin, directly A&E ward suka wuce da shi. Nan likitoci, Malaman jinya da sauran ma'aikatan da ke da ruwa da tsaki cikin kula da lafiyar majinyaci suka taru.
Abun ba'a cewa komai, Shi dai Ya khalil ya zama kamar wani mahaukaci, idanunsa duk faɗa kamar wanda yayi sati yana jinya, haka fuskarsa ta koma ja abunka da farin mutum. Dr. Arƙam kanshi baya cikin hayyacinsa Shiyasa ya yanke shawarar ƙin shiga room ɗin don a firgice yake da al'amarin patient ɗin nasa. Kafaɗar Ya Khalil ya dafa, cikin harshen turanci ya ce “Kayi haƙuri Khalil, muyi masa addu'a shine kawai, ka daina kukan haka ka ji?” Kamar wani dolo haka ya gyaɗa kai, a reception ɗin suka zauna ganin tsayuwar ba yadda zata kai, cikin zuciyoyinsu kuma suna addu'ar Allah ya bawa Ya Sadaukin lafiya.
*NIGERIA* *ABATCHA ESTATE* *MORNING 🌅, 7:00 O'CLOCK*
Tun bayan sallar asuba Hajjaty ta saka Zahrah ta koma bacci wai ta huta da kyau. Ƙarar bedside clock ɗin da ta buga ƙarfe bakwai ya tayar da ita, ɗauke da addu'ar bacci a bakinta ta farka. Tsawon mintuna biyar kafin nan ta miƙe tana mai sauƙa daga kan bed ɗin. Toilet ta nufa tayi wanka, fitowar ta yayi dai-dai da shigowar Hajjaty wacce ta shigo da niyyar tayar da Zahran. Murmushi ɗauke a fuskarta take kallon jikar tata cike da so da kuma ƙauna. Ita ma Zahrah sai ta tsinci kanta da mayarwa Hajjaty martanin murmushin. Tsawon wasu daƙiƙu kamar wacce aka zabura Hajjaty ta nufe ta, ba tare da duba cewa daga wanka take ba ta rungume ta, wani bond ne ya kara ƙulluwa. Cike da farin ciki har haƙwarenta na fitowa ta furta “Barka da safiya kaka ta, fatan daren ki ya kasance mai daɗi” cikin sakin fuska Hajjaty ta amsa mata da “Eh jika ta, ya daren ki?” ta tambaya tana sakin Zahran. “Lafiya Lou Hajjaty, Hakan ta kasance ne da bacci a kusa da ke” wani irin murmushi Hajjaty tayi jin kalaman Zahrah.
“Yauwa Zahrah ga can kaya na sa Ruƙayya ta duba miki cikin kayayyakin Nasreen, anjima bayan kinyi breakfast akwai family meeting da Alhaji Baba yayi magana a kai jiya, yanzu ki shirya ki fito ki karya” “To Hajjaty na gode” ta bata amsa tana ƙarasa zuwa wurin Ghana must go nata. Alhamdulillah ta furta bayan ta zuge ganin wata doguwar rigar Bibalo da ta taho da ita. Cike da kuzari ta shirya zuciyarta tas kamar farin wata.
Tana gama shiryawa ta fito ta tarar da su Hajjaty Zaune kan dining ɗin, da ido ta bisu don ganin su waye, Alhaji Baba ne, sai Hajjaty sai kuma Ya Auwab, ta gane fuskarsa sosai, a hankali ta fara takawa zuwa dining area ɗin, da sallama a bakinta ta ƙarasa tana sunkuyar da kai ƙasa. “Barka da safiya Alhaji Baba ” fuska sake ya amsa mata da “Barka Zahra'u, kin tashi kenan” murmushi kawai Zahrah ke saki har lokacin kanta ƙasa “Ya kuma kwanan baƙunta?” “Alhamdulillah” “Masha Allahu haka ake so, matso kusa da kujera ta ki zauna tunda jiya Hajjatyn ki ta ɗauke ki, matso nan” Alhaji Baba ya faɗa yana nuna mata kujerar da ke gefenta. “A'ah Alhaji Baba yaushe kuma zata zauna kusa da tsoho, kin ga Ƙanwata zo kusa da ɗan'uwanki” Ya Auwab da ke kallon Zahrah yana murmushi ya faɗa “A sit for you sister” Hajjaty Kam kasa magana tayi ganin ikon Allah. Danƙwalon sa Alhaji Baba yayi yana gyara zaman farin gilashin sa wanda ke ƙarawa idonsa ƙarfi kafin ya ce “Ungo nan! Nace ungo Nan Muhammadu! Kai Auwabu ina nuna wa jikata wurin zama shine zaka nuna mata wani daban?” Kwaɓe fuskarsa yayi kamar zai yi kuka har sai da ya kusa sa Zahrah dariya. “Kai Alhaji Baba don kawai na nunawa ƴar'uwata wurin zama shine, to in ban nuna mata ba wa zai nuna mata?” “Usmanu ne! Nace Usmanu ne zai nuna mata!, kai Auwabu ka fita ido na na rufe fa!” Dariya ya Auwab ɗin yayi yana faɗin “Calm down my only grandpa”
Hararar sa Alhaji Baba yayi yana faɗin “Zaka yi bayani ne, bari dai dodonku ya dawo ko na huta da zuwan ku nan kuna caja min kai” Ita dai Zahrah kamar Status haka ta tsaya kallonsu, sun matuƙar burgeta, musamman yadda Ya Auwab ɗin ke tsokalo Alhaji Baba ga kuma yadda yake ƙoƙarin jan ta a jiki, Muryar Hajjaty da ta dafa ta ne yasa ta dawo daga duniyar tunnin. “Kin ga Zahra'u kada ki biye surutun waɗannan don sai kan ki yayi ciwo, samu ki karya ki je ki shiryo, zuwa takwas da rabi kowa zai hallara.
Murmushi tayi cike da jin kunya ta zauna a gefen Alhaji Baba. Ɗago Ido Alhaji Baba yayi yana duban side ɗin Auwab sai aka ci Sa'a ya ɗago suka haɗa ido, fuska kwaɓe ya Auwab ke kallon Alhaji Baba Shi kuma Alhaji Baba sai ya ɗan zaro idanuwansa alamar ya ka ga Ni? “Hajjaty kin gan shi ko?, Allah wannan mijin naki Ni ya takura min” Murmushi kawai Hajjaty tayi tana serving Alhaji Baba sai kuma ta ɗago ta dubi Auwab ɗin da in Ka kalle shi zaka ce ƙaramin yaro ne, yadda yayi da fuskarsa zai matuƙar baka dariya. “Ku kuka fi kusa, anjima kaɗan zaku haɗe kai” ta karasa tana turawa Ya Auwab ɗin plate.
Cike da nutsuwa tare da bismillah suka fara cin abincin hankalinsu kwance, Baka jin komai sai ƙarar spoons da ke colliding da plate. Tsawon wasu daƙiƙu har suka gama ci, kamar yada taga Ya Auwab ya goge bakin sa ita ma ta goge nata da tissue sannan ta furta Alhamdulillah.
Bayan an gama breakfast babu Wanda ya tashi ciki, sai ma wata ƴar hira da suka tayar. Ita dai Zahrah murmushi ne nata idan anyi abun da ya burge ta, idan kuma abun dariya ne ai ta sunkuyar da kanta ƙasa tana rufe bakinta.
Da misalin ƙarfe 7:40 suka miƙe, kowa yayi nasa sashen don fara shirin zuwa Family Hall saboda Taron da za'a yi na family. Duk wani ɗa da ke da alaƙa da gidan kowa ya san da meeting ɗin saboda daren jiya Ya Auwab da Ya Taj sun yi magana a WhatsApp group na family. Nan fa group ya ɓarke da hira ca-ca-ca kawai kake ji, kowa so yake yaji taƙamaimai dalilin wannan unexpected meeting da za'a yi because it's unusual ayi meeting irin haka a family babu wani abu da ya faru.
*****************
*BAUCHI*
A ɓangaren Bibalo jiki ya yi sauƙi sai dai muce Alhamdulillah, lafiya ta samu, surutan da take yi duk ta daina su, hakan yayi wa Baba Amarya daɗi sosai, sai dai babbar damuwarta shine rashin ganin Zahrah a gidan. Duk yadda tayi tunanin a nan iyayen Uwarta suke ta rasa don bata san wacce jaha suke ba. Tun tana neman a hankali har ranta ya fara ɓaci, ta kuma ƙudiri aniyar nemo Zahrah duk yadda take. Alwashin ta darr yake, ba zata taɓa bari Zahrah tayi rayuwa mai kyau ba, kamar yadda uwarta tayi wulaƙantacciyar rayuwa (a nata tunanin) ita ma Zahrah ita zata ɗanɗana. Bata ko tunanin illar hakan duk irin yadda Bibalo ta wahalta gashi kuma babu biyan buƙata.
Kawu ma dai nasa ɓangaren babu sauƙi, cikin kwana biyun nan mugayen mafarkai yake yi da Mama, mostly Kuma yana faɗawa mawuyacin hali ne tana taimaka masa, ya rasa ina wannan mafarki ya dosa, gashi kuma yanzu wata ƙaunarta ke kama shi, ya rasa yaya zai yi cikin kwana biyun nan, a halin yanzu babu abinda ya tsana sama da Baba Amarya, ko da ya shiga gidan ɗakin Mama ya fara nufa. To his suprise sai yaga ƙura alamar dai babu mai rayuwa ciki ga kuma yadda aka barwatsa komai na cikinsa.
Zuciyarsa ce ta buga, cikin ƙarfin hali ya nufi ɗakin Baba Amarya, a tare da Bibalo ya tarar da su suna cin taliyar murji da manja da kuma yaji, Baba Amarya na ganinsa ta miƙe da sauri ta zo gare shi. Kallon da ya jefe ta da shi yasa ta ɗan dakata. “Ina Madina ne?” Sai da ta ɗan yi jim don har ga Allah ba zata ce tana iya tuna wace Madina ba har sai da ya tambaye ta a karo na biyu “Ina Madina ne?” Cikin kame-kame ganin wannan sauyi tattare da Kawun yasa ta ce “Eh ah eh dama haka ne, eh ita da ƴar ta dama dama can sun shirya ne sai suka gudu don cin duniyarsu da tsinke....!”
Dakatar da Ita kawu yayi, shi kansa mamakin dalilin jin wannan zafi yake , a da shi kansa cin kashin da yake mata ko kare ba zai shinshina ba, amma yanzu duk wanda yaji zai faɗi magana kan ta, yana dai-dai ne da dakatar da shi ko ma waye. Juyawa yayi ya fice abunsa tare da barin gidan.
Cike da takaici Baba Amarya ta koma kusa da Bibalo ranta ɓace tace “In dai boka da Malam na nan, cikin su babu wanda ya dakatar da aikinsa, to nima ba zan gaji akan ƙudiri na ba. “Dole ka kasance a tafin Hannayena Idrisu.” ta furta a zahiri tana ɗaura kan Bibalo a kan cinyarta.
**********************
*ABATCHA ESTATE* *FCT ABUJA* *8:05am*
Sai da ta ƙara wanka kafin ta ɗauki wannan kayan da Hajjaty ta nuna mata, cikin wata Black expensive Abaya da ta ji stones wanda ke zuba ƙyalƙyali ta shirya, ba ta yi wata kwalliya ba coz farar powder da ke gaban Mirro ɗin ta shafa, sannan ta shafa wet leaves, ko kwalli bata saka ba ta yafa Black veil da ke haɗe da abayar ta yafa. “Masha Allah ” sosai suka karɓi farar fatarta sai ta fito a ainihin balarabiya amma fa mai jin Hausa 😂.
Hajjaty ma cikin wata atamafar ta ja da baƙa ta shirya, tayi kyau kamar ba ita ta haifi Daddy ba. Ganin ƙarfe 8:10 yasa Hajjaty ɗauko Mayafinta ta yafa “Yi maza ki fito Zahrau lokaci ya kusa cika” Da “To” ta amsa tana ajiye turaren da ta ke fesawa tare da bin bayan Hajjaty da ke ƙoƙarin barin bedroom ɗin.
Basu ɓata lokaci ba kau tsaye suka nufi Family Hall da ke ɗan kusa sosai da ɓangaren Hajjaty. A wannan lokacin kuma da yawa sun iso, saboda su al'adar su babu African time Shiyasa in an saka lokacin taro da wuya ba'a fara shi yadda ya kamata ba.
*Shin kun sa cewa?:* _1. Duk wanda ya tashi daga bacci ba'a so ya miƙe immediately as he wake up?, Ana so idan mutum ya farka daga bacci kada ya miƙe a lokacin, an fi so ya ɗan ci gaba da kwanciya na tsawon wasu daƙiƙu kafin ya miƙe tsaye, hakan zai ƙara improving level of wellness na mutum musamman ta bangaren ƙwaƙwalwa da kuma tunani, psychologically one will be more stable_ _On the other hand miƙewa tsaye da zarar mutum ya tashi daga bacci kan haifar da matsalolin lafiya da dama, ciki yana jawo sauƙar jini (hypotension), yana kawo rashin dai-daiton tunani ta yadda zaka ga mutum a zabure kamar wani abun tsoro ya sako shi gaba. Hakan har ila yau kan iya haifar da matsalolin da suka shafi ƙwaƙwalwar ɗan Adam._ _So You guys should be more careful, in an tashi daga bacci a daina miƙewa tsaye a take, ayi ƙoƙarin jinkirtawa na wani lokaci ko don inganta lafiya._ _Haka nan tashi tsaye bayan dogon Zama, shima yana sanya jinin mutum sauƙa. Ba'a fiye son yin dogon Zama ba saboda gudun hakan, ku sani Sauƙar jini (hypotension) ya fi hawan jini illa, sannan yafi wahalar magancewa fiye da hawan jinin. A kula sosai da lafiya my esteem fans._
_2. Annabi tsira da aminci su ƙara tabbata a gare shi yakan fara kowanne aiki da bismillah_ _Manzon Allah ya kasance yakan ambaci sunan Allah a farkon kowanne abu da zai yi hatta a cin abinci, habibties kada a manta a ke yin bismillah kafin yin kowanne irin abu. Sannan ake yawaita godewa Allah bisa kowacce ni'ima komai ƙarancinta. Allah ya sa mu dace._
*Ku kasance da alkalami na don jin yadda zata kaya, masu cewa kansu ya kulle ku ƙara haƙuri ku ci gaba da bibiyar alƙalami na, komai zaku fahimta ne da sauƙi, ku tuna _A babban gida_ muke, so everything there supposed to be somehow complicated.*
*A karɓa da haƙuri my esteem fans, manage this!, ina ƙara Baku haƙuri in sha Allah komai zai daidaita. I've been busier than before that's why, Amma zan ƙoƙarta komai ya saitu. Make sure that you guys react! React!! React!!! & React har sai na gaji da ganin reactions. I love you guys😘, group members ayi comments Please sannan ayi sharing don Allah, much ƙauna 💕.*
[10/18, 5:24 AM] Diamond Bhatool:
*Typing 📲*
🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡 _(All in a big family 🏠)_ ★TAKUN ƘARSHE★ [Labari/Rubutawa] *Fadimatu Adamu Hassan*💎 *A.k.A Diamond Bhatool* *(Famanté)*
Wattpad: @diamond_bhatool Arewabooks: @diamondbhatool
_Ƙirƙirarren labari mai cike da ƴan'uwantaka, gwagwarmayar rayuwa, makirci, mugunta, hassada, munafurci, rashin tausayi da kuma dauwamammiyar soyayya maras iyaka_
_Creative work of love vs. societal expectations., family bonds and loyalty, Identity and self-acceptance, Hypocrisy and jealousy's destructive power._
*PAGE* 0️⃣5️⃣
_Dedicated to my superhero, father, mentor and role model in person of JS Yakubu, Allah ya ƙara maka lafiya baba._
_Masu neman labarin daga farko kuyi following channel ɗin nan zaku samu_
﷽
Gaban Zahrah ne ya buga suna kaiwa gaban makeken block ɗin da aka maƙala mishi signboard na Family Hall wanda ke ƙyalƙyali da dare kuma ya ke fitar da haske kala kala. Hajjaty da ke riƙe da hannunta ne ta fahimci hakan. Cike da kulawa ta ce “Kin ga Zahrau muje duka ƴan uwanki ne ba wani bare, kar ki ji tsoro kin ji?” Kai ta gyaɗa sannan suka fara takawa izuwa steps ɗin da zai sada ka da hall ɗin. Suna tsayawa glass ɗin ya zuge nan suka shiga ciki.
Mutane ne sosai suka halarci taron, manya da yara, sai dai babu iyaye mata da alama iya mazan ne a ciki. Shigowar Hajjaty yasa hankalin su komawa ga saitin ƙofar, mamaki sosai ya cika su ganin wata baƙuwar fuska wacce ko makaho ya shafa ta zai sai jinin gidan ce, but to them abun ya ɗaure kanunsu. Ko da yake lokacin Alhaji Baba ne kaɗai bai shigo ba sai kuma Daddy yasa suka nemi wuri suka zauna. Few minutes sai ga Alhaji Baba tare da Daddy wanda ke riƙe da shi. Har wurin zamansa aka kai shi bayan ya zauna Daddy ma ya nemi nasa wurin ya zauna.
Babu alamar motsi cikin hall ɗin tun shigowar Alhaji Baba. Kowa yayi tsit yana sauraran me za'a ce, wadanda suka kula da shigowar Hajjaty ma suna jira a kammala su ji wacece wannan kyakkyawar yarinya da suka shigo tare.
Alhaji Babba wanda a kodayaushe in za'a yi wani taro yake fara magana kamar yadda ya kasance babba cikin Abatcha family. Microphone 🎤 ɗin ya ɗauka da fara magana. “Assalamu Alaikum warahmatullah wabarakatouh” Gabaɗaya Hall ɗin ya ɗauka da “Wa Alaikumussalam” Nan ya ɗaura da faɗin “Iyayen mu masu daraja, ƴan uwa na da kuma ƴaƴan mu, barkan ku da wannan safiya mai Albarka” sai ya ɗan tsagaita kafin ya ci gaba “Kamar yadda na gani akan fuskokin ku na ƙara tabbatar wa da kaina cewa kuna mamakin wannan unexpected meeting, so Kai tsaye ba tare da ɓata lokaci ba zamu fara magana akan abinda ya tara mu. Sai dai kafin nan kamar yadda muka saba za'a bude taron da addu'a, Bismillah Qasim”
Wani kyakkyawan saurayi ne ya mike ya amshi microphone ɗin daga hannun Alhaji Babba, fuskar matashin sake wacce da ke nuna zallar kamala da kwarjini ya fara magana, khudhbatul hajah ya fara daga nan yayi addu'o'i sannan ya mikawa Alhaji Babba da ke zaune microphone daga nan ya koma mazauninsa.
Alhaji Babba ya ci gaba da magana “Masha Allah, Allah yayi Albarka Qasim, kai tsaye zan fara magana akan abinda ya tara mu. Idan baku manta ba wasu lokutan zaku ji ƴan uwana wato iyayenku suna magana akan ƴar uwarsu wacce ta ɓata tsawon wasu shekaru masu yawa” sai kuma yayi shiru. Nan hankalin kowa ya ƙara komawa jin me Alhaji Babban zai ce? An same ta ne ko kuma ta mutu ne? They're all earger to know. “Alhamdulillah” Alhaji Baba ya ci gaba “Cikin ikon Allah Ubangiji ya nuna mana gudan jininta, sai dai ta ɗaya bangaren har yanzu dai ita Madina babu labarin ta, saboda haka a ƙara ƙaimi wurin Addu'a Allah ya bayyana ta.”
Nan da nan Hall ɗin ya kaure da hayaniyarsu wannan na cewa kaza wannan kuma na faɗin kaza har ta kai ga Zahrah da ke gefen Hajjaty shan jinin jikinta, tuni wani tsoro ya ɗan kamata kar dai taje she's not welcome by her cousins.
“Ya isa haka!” Alhaji Baba ya. Faɗa da ɗan ƙarfi, nan Hall ɗin yayi shiru kamar ba dai yanzu aka gama cin kasuwa cikinsa ba. “Yanzu ba tare da ɓata lokaci ba kowa zai introducing kansa saboda ta ƙara fahimtar ku, amma ita bari ta fara sanar da ku sunan ta, Bismillah” rass gabanta ya faɗi, hannun Hajjaty ta ɗan ƙanƙame, ƙasa ƙasa Hajjaty ta ce mata “Ki nutsu Zahrah, maza tashi ki je”
It's not her first time to speak in public but this time is different, zuciyarta ne ke tsalle tana kai kawo. A hankali ta miƙe ta nufi stage ɗin, hannunta na ɗan rawa ta ɗau mike ɗin. A hankali zuciyarta Kuma ta fara saituwa, cike da ƙwarewa da magana a cikin mutane ta ce “Assalamu Alaikum, good morning my lovely grannies and parents, good day my esteem sisters and brothers, da farko suna na Zahrah Abdulkarim Kuru, ɗiya ga Madina Abatcha wacce aka riga aka sanar da ku komai game da ita. Naji daɗin shigowa cikin ku kuma ina fatan kuma kun ji daɗin kasancewa ta da ku.” sai kuma ta yi shiru tare da ajiye microphone ɗin. Babu laifi kowa was impressed with her speech, though wasu daga ciki were disgusted by her speech. A nutse ta taka ta koma gefen Hajjaty tana sauƙe ajiyar zuciya.
Alhaji Baba ya ce “Now!, Qasim zo ka ɗau abun magana a fara ta kanka, let everyone introduce himself to her now.” Ya Qasim ne ya miƙe a nutse ya fara magana “wa Alaikimussalam, morning, Ni suna na Qasim Abubakar Abatcha.” daga nan ya miƙawa sauran mutanen, ɗaya bayan ɗaya kowa yayi introducing kansa, daga nan kuma suma iyayen suka yi. Nan Alhaji Babba ya ce gobe za'a zaga da ita ta ga sauran mutanen gidan.
Ya Qasim ne ya rufe taron da Addu'a nan manya suka fara fita kafin maza sai kuma matan kowa na ƙara tattaunawa akan yarinyar.
Wasu Ƴan mata guda uku da zasu kai 24years ne ke tafe suma suna magana akan Zahrah. Ɗaya daga cikinsu wacce fatarta ke da haske sosai ta ce “Ke Rumana Ni fa yarinyar nan ta burge Ni wallahi, see how courageous she's, ga ta kyakkyawa, kina ganinta kamar Hajjaty ce tayi kaki ta tofar. Wacce aka ƙira da Rumana ce ta yamutsa fuska tare da tofar da yawu gefe. “Ke Hibba matsala ta da ke, you're so local, don Allah wannan yarinyar what's that her name!” ta ɗan ɗaga kai sama tana ymutsa fuska sai kuma ta ce “Zahrah take ko wa! Wallahi haka kawai yarinyar bata mun ba, daga gani zata yi rawar kai, ga ta da shegen kyau kamar aljana”
Ɗan taɓe baki ta ukun nasu tayi ta ce “Kya ji dai da wannan banzan halin naki, Ni dai tunda jini na ce dole ba zan ƙyamace ta ba, kyau kuma da kike magana ke ma ai kina da shi, duk cikin familyn nan babu wadda za'a cewa mummuna.” “Faɗa mata kam Jidda, Ni na rasa wane irin hali ne da Rumana, mutum bai Miki komai ba kawai ki ce kin tsane shi” Hibba ta faɗa tana faɗin “Kun ga Ni nayi ciki, sai mun haɗu kuma”. Ta faɗa tana shigewa apartment ɗin su da yafi kusa da na Hajjaty.
Tsaki Rumana ta ja ta nufi apartment ɗinsu ranta duk babu daɗi, tana shigar ta tarar da Mai aiki na mopping Parlour, harara ta cilla mata tace “Ke Jennifer kin gyara min ɗaki na ko?” “E Eh ranki ya daɗe, ta faɗa tana sunkuyar da kai gudun masifar Rumana, tsaki kawai ta ja ta haye stairs ɗin sannan ta shige room nata tana sakin tsaki a kai a kai.
********************
*ABATCHA FAMILY*
Kamar yadda ya gabata Alhaji Baba da Kuma matarsa Hajjaty da marigayiya Khadijatu suna da yara bakwai cur. Alhaji Abubakar Abatcha (Alhaji Babba) shine babban su, matan sa uku ne. Hajiya Ruƙayya, Hajiya Karima sai kuma Hajiya Balkisu.
Hajiya Ruƙayya (Hajiya Babba) na da yara Bakwai. Aunty Madina ita ce babbar ƴarta, yaron ta ɗaya Aamir kuma suna zaune ne a Kaduna ita da mijinta. Sai Ya Haidar shi kuma ba a Nigeria yake da zama ba shi da matarsa Aunty Salma, yarinya ɗaya gare su, Nihal. Sai kuma Ya Khalil wanda shi bai yi aure ba har yanzu, shi a nan Abatcha estate yake da zama, yayi tafiya ne zuwa London. Akwai Aunty Mabruka yanzu haka ta kammala karatun ta a ɓangaren law, ta fara aiki da Court of Appeal. Sai kuma Humaira, Nasreen da kuma auta Fu'ad.
Hajiya Karima yaranta biyar, Ya Qasim shine babba, sai Ya Auwab sai kuma Hibba, Jalal sai kuma Samha.
Hajiya Amina yaranta uku, Meerah, Jidda sai Naufal.
Alhaji Umar Abatcha (Daddy) matansa biyu, Hajiya Laila (Aunty Amarya) da Kuma Hajiya Sughrah (Mommah). Hajiya Sughrah ce babba, yaranta biyar, Ya Junaid, Aliyu, Anam, Nainarh sai kuma Ra'ees.
Aunty Amarya yaranta uku, Fadhwah, Adnan, sai kuma Noor.
Alhaji Uthman Abatcha (Papa) shima matansa biyu, Hajiya Saudatu (Ammie) sai kuma Hajiya Ramla (Mimie). Ammie na da yara biyar, Aufa, Imad, Afifa, Minal, da Kuma Sudais. Mimie kuma yaranta uku, Affan, Muhibbat, da kuma Zakiyya.
Alhaji Aliyu (Abie) na da mata ɗaya ƙwal. Hajiya Rahila, yaransu uku, Ya Tajudden, Rumaysa, da kuma Auta Mahir.
Alhaji Muhammad (Abba) na da mata biyu, Hajiya Baraka (Mami) da kuma Hajiya Na'ima (Small Mom). Mami na da yara uku, Ya Faruq, Kausar, da Kuma Asim. Small mom yaranta biyu, Amna da kuma Aneela.
Alhaji Yusuf (Affa) ma matansa biyu,Hajiya Hauwa (Amma) da kuma Hajiya Hadiyya (Aunty Hadiyya). Hajiya Hauwa yaranta biyu, Feenah da kuma Reedah. Aunty Hadiyya dai bata da yara ko ɗaya amma tana da ciki.
Wannan sune suka yi making ABATCHA FAMILY.
*Back to story*
Bayan kowa ya fice Hajjaty ta kama hannun Zahrah suka wuce zuwa ɓangarensu. A parlour Zahrah ta yada zango tana sakin nishi “Auh! Wallahi har na gaji Hajjaty” “Gajiya kuma Zahrau, Kinga yanzu bari na ƙira yaron nan Auwabu ko Tajudden wani ya kai ki kiyo siyayya sai ku tafi tare da Nasreen ta taimaka miki” Zahrah ta ce “To Hajjaty na gode, amma da mun bari sai yamma fitar zai fi daɗi” Cike da gamsuwa Hajjaty tace “Eh kuma fa haka ne, yanzu ki huta abunki ”
Ƙara miƙewa Zahrah tayi akan sofa ɗin tana lumshe idanunta tare da tariyo moment ɗin da take ciki, tun daga zuwan ta estate ɗin zuwa yanzu. “Mamah” ta furta har lokacin idanuwan ta na a lumshe. “Yanzu matsala ta kenan! Ita ɗaya ta rage min, ubangiji ka bayyana min ita” Duk maganar da take yi cikin ranta ne, bata san maganar ta fito fili ba sai da taji an ce “Amin ya Rabbi” a ɗan tsorace ta buɗe lumsassun idanuwanta tana ɗaura su kan wanda ya amsa tambayar.
Wasu kyawawan ƴan mata ne waɗanda ba zasu wuce tsarar ta ba a shekare sai dai bata iya banbance cikinsu wace ce tayi maganar. Murmushi suka yi mata hakan yasa ta ƙara lumshe idanunta sannan ta buɗe ita ma ta mayar musu da murmushin tare da miƙewa zaune tana nuna musu gefenta. “Thank You”, ɗayarsu ta furta. Murmushi tayi tana ƙara kallonsu sai dai ta kasa tuna sunayensu duk yadda ta so tunawa cikin sauƙi.
Bayan sun zauna, Ɗayarsu wacce ganin fari zaka tabbatar da surutun ta tace “Zahrah, gamu mun biyo ki” Murmushi tayi tace “Sannun ku da zuwa” Daga cikin su wata ta ƙara cewa “We're glad that you're back, Barka ƴar uwa!” “Na gode” zahrah ta bata amsa tana haɗa hannayensu tare.
“Suna na Nasreen” mai surutun ta faɗa “Ga kuma...” “To wa ya saka ki?” ɗayar tayi saurin katse ta “Mu ma muna da baki”. Ɗayar ce tayi murmushi tace “Ni kuma Nainarh” Ɗayar ta ce “And I Zakiyya” Ni kuma Rumaysa”. Da ido take binsu tana ƙara nazartar fuskokinsu fuakarta ɗauke da murmushi. “Thank You so much sisters, pleased to meet you all!” “You are welcome ” suka faɗa su ma suna murmushi.
*LONDON* *Sadauki*
Sun shafe kimanin Awanni biyu a emergency room ɗin kafin aka samu damar ceto numfashinsa, nan Nurse ɗin tayi masa allura tuni bacci yayi awon gaba da shi.
Dr. Arƙam ne yayi saurin tunkarar ma'aikatan yana mai tambayar su ya ake ciki, ɗaya daga cikinsu ne ya dafa kafaɗarsa yana faɗin “Calm down doctor, we're able to rescue his breath, now an mishi allura. In sha Allah he'll be stable but.... let's get inside please” “Ok” Dr Arƙam ya bashi amsa tare da bin bayansa zuwa office. Nan Dr ɗin ya ƙara shawartar Dr. Arƙam game da patient ɗin nasa. Daga nan ya fice ya koma wurin Ya Khalil da ke reception cike da zullumi da damuwa, nan yayi ta kwantar masa da hankali, jin ya farka tukun hankalinsa ya ɗan kwanta.
Nan ya laluɓa wayarsa don ya ƙira Gida ya sanar. Jin bata jikinsa yasa ya tuna cewa ya bar wayar ma can gida yasa ya ɗan kawar da kansa gefe yana cije leɓe. Cikin ransa kuma ya riga ya gama yanke shawarar abun yi, don ba zai bari rayuwar abokinsa kuma ɗan uwansa ta salwanta a banza ba, dole ne su koma gida ko yaya ne abun zai fi zuwa da sauƙi.
*Wannan kenan!* *Na san har yanzu zuciyar readers cike take da ƙaulani! To kada ku damu yanzu ne zamu fara labarin, zuwa yanzu na san kun fahimci wasj abubuwan, yanzu dai mun san babban gida da kuma ahalin by names, da sannu alkalami na zi warware muku komai! Ga Ya Sadauki da. Kuma Ya Khalil! Ku dai ku kasance da Ni kawai don jin yadda zata kaya.* *Jama'ar Channel ku da nake yaba ko yaushe ku ma kuna son bani kunya, yanzu reacting ɗin ma ba sosai ba, idan baku jin daɗin labarin nd lemme know please* *Reacting ƙasa da 20 means na daina yin update.*
*My esteem fans a nuna min ƙauna ta hanyar reacting please, Ina son ku da yawa da yawa, kada ku mance ni ɗin taku ce 🤗 😍 😘 💕*
[10/20, 6:12 PM] Diamond Bhatool: *Typing 📲*
🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡 _(All in a big family 🏠)_ ★TAKUN ƘARSHE★ [Labari/Rubutawa] *Fadimatu Adamu Hassan*💎 *A.k.A Diamond Bhatool* *(Famanté)*
Wattpad: @diamond_bhatool Arewabooks: @diamondbhatool
_Ƙirƙirarren labari mai cike da ƴan'uwantaka, gwagwarmayar rayuwa, makirci, mugunta, hassada, munafurci, rashin tausayi da kuma dauwamammiyar soyayya maras iyaka_
_Creative work of love vs. societal expectations., family bonds and loyalty, Identity and self-acceptance, Hypocrisy and jealousy's destructive power._
*PAGE* 0️⃣6️⃣
_Dedicated to Moonlight writer's Association_
_Masu neman labarin daga farko kuyi following channel ɗin nan zaku samu_
﷽
Hira suke sosai abunsu, tuni Zahrah ta saki jiki kamar ba ita ba. Suna cikin hirarsu Nasreen ta ce “Zahrah ajinki nawa ne yanzu?” Sai a lokacin Zahrah ta tuna da batun wata makaranta. Cikin raunin murya tace “Eh da ina zuwa lokacin da Mama na nan, mun kai SS 2 kuma sai na daina zuwa sosai, amma dai ban gama ba?” Fuskar Nasreen ɗauke da ayar tambaya tace “Ban gane ba Zahrah?” Kau da kai gefe Zahrah tayi tana faɗin “Mance kawai Nasreen” Sauran da basu faɗin komai tun bayan introducing kansu suka haɗa baki wurin faɗin “Haba Zahrah, a mance kuma”
Haka kawai ta ji wani iri ganin sun nuna concern Nasu a kanta, At least sun cancanci su san komai nata. “Kinyi shiru” Nainarh ta ƙara fada fuakarta fal damuwa. “Eh am dama fita nayi a makarantar” Dafa kafaɗarta Zakiyya tayi tace “Feel free, mu nan duka ƴan uwa ki ne Zahrah ” Rumaysa ta ƙara da faɗin “Ki ɗauke mu kamar yadda muka ɗauke ki Please, mu dukkanmu ƴan uwa kuma ƙawaye muke gare ki, don Allah Zahrah ki faɗa mana” Zuciyarta ne ta karaya da yadda suke maganar, hakan yasa ta basu labarin Dalilin barinta makaranta.
Sun tausaya mata sosai. Nasreen ta ce “Kada ki damu Zahrah, zaki koma makaranta, makarantar ma wacce ba'a yi tsammani ba, kiyi haƙuri kin ji?” kai ta gyaɗa sai Nainarh ta ce “Ni fa Zahrah wallahi kin matuƙar yi min kama da wata yarinya wacce da take trending a social media, what's that her name?, Rumaysa kin gano yarinyar nan da kwanaki muka ga video nata tana speech lokacin muna JSS three ne kamar dai” Rumaysa ta ce “Ƙwarai kuwa Nainarh, nima na fuskanci hakan, sunan ta Zahrah ne kamar dai?” Zakiyya ta ce “Kai wallahi inaga wannan Zahrahn ce, kun san me yasa?” Duk suka jijjiga kai banda Zahrah da ke binsu da ido.
“Kun tuna lokacin da muka ga news na best in BECE a Bauchi State a parlourn Alhaji Baba?” Kansu suka ƙara gyaɗa mata. “To wallahi lokacin nan sai da Alhaji Baba yace anya wannan ba jininsa bace?, amma ke Zahrah daga wane gari kika taho?” “Bauchi” ta basu amsa a gajarce. Baki haɗe suka ce “Wallahi ke ce yarinyar nan!” Ɗan harararsu tayi tace “Sannu manya” Dariya dukkansu suka yi. Nainarh ta ce “Kada ki damu Zahrah Kinga muma a SS 3 muke yanzu, Kinga sai muyi paper tare kawai, nasan zaki iya ko don irin yadda kwanaki muka ga kina trending a media da gani ke gifted ce” “Uhm ba wani nan fa” “Da gaske wallahi ” Zakiyya ta faɗa.
Haka suka yi ta hirarsu nan Zahrah ta basu labarin makarantar su ta da, da yadda aka yi ta fara zuwa. Yadda ta fara haskawa da kuma yadda ta bar makarantar. Sun matuƙar jinjina mata kuma sun mata alƙawarin kasancewa kamar Ƙawarta Badi'a a gare ta. Sosai suka ƙara jin ƙaunar junansu duk da cewa cikin ransu kowa tsoro yake, don zasu iya cewa a iya sashen Hajjaty ne suke samun wannan kusanci da kuma tattaunawa da juna.
****************
Hajiya Babba ce zaune a parlourn ta cikin shiga ta alfarma wacce ke ƙara bayyanar da kwarjininta a idanun mutane. Sallamar Affan ne tasa ta ɗago idanuwanta tana kallonsa. A gaban ta ya zauna yana faɗin “Barka da safiya Hajiya” “Barka” ta bashi amsa a gajarce. “An gama meeting ɗin kenan?” “Eh Hajiya an gama” shiru na ɗan wani lokaci ta ce “Masha Allahu, a kan me aka yi zaman ne?” Fuska dauke da murmushi ya ce “Hajiya kin san wannan ƴar uwar su Alhaji Babba wacce ta ɓatan nan?, Aunty Madina yauwah kamar dai haka sunan yake!” “eh me ya faru da ita to?” ta faɗa cike da son sanin abunda ke faruwa. “Hajiya ai ƴarta ce ta dawo, amma ita ɗin an ce ta ɓata ba'a san yadda take ba.”
Cikin halin ko in kula ta ce “To Allah ya bayyana ta.” Affan ya ce “Amin Hajiya, kin san mene Hajiya?” Kai ta jijjiga masa “Yarinyar kina ganinta sai ki ce Hajjaty ce ta haife ta.” Ba tare da ta ɗago ba ta ce “Ayya, ina Nasreen ne?” Dariya Affan yayi kafin yace “Hajiya ai ƙafar Zahrah ƙafar Nasreen, tana can part ɗin Hajjaty” Daga haka bata ƙara ce masa komai ba hakan yasa shima ya tashi ya nufi bedroom ɗinsa.
************** Su uku ne zaune a katafaren Parlourn da alamu dai suna tattauna wani muhimmin zance ne. Mommah ce ta kalli Ammie da Mami ta ce “Nifah ina cikin matsanancin tashin hankali kwanan nan!” Ido zare Mami ta ce “Lafiya Hajiya Sughrah?” “To lafiyar dai, kin san har yanzu Aliyu baya ɗaga kira na?, hankali na ya gama tashi, shi ma wannan yaron Khalil bana samun numbersa, Abu ƙarami Aliyu ya ɗauke shi babba.” Gyara zama Mami tayi ta ce “Kai Ni na rasa wane irin yaro ne wannan, mutum sai shegen taurin zuciya, gaskiya ina ga da sa hannu akan al'amuran sa fa, dole a duba al'amarin nan.” Jimm kaɗan Mommah ta ce “Gaskiya ina tunanin hakan, Amma ko yaya za'a yi ai bai ƙarfi na ba, Ni na haife shi, zai dawo ya same ni ne, gabaɗaya kwanan nan da ciwon kai nake kwana, ga BP na ma ya hau wallahi.” Mamie ce tayi gyaran murya ta ce “Ai kuwa Ni ne fara zargin anya ba Bakin Hajiya Babba cikin wannan al'amari kuwa?”
“Nima na fara zargin haka, ban san yaushe Hajiya Babba zata bar kowa ya shana da ƴaƴansa ba a gidan nan, duk ta bi ta maƙalƙale kowa kamar nata. Gaskiya dole muyi kyakkyawan shiri akan wannan al'amari” Ammie ta ƙara a kai, murmushi Mami tayi ta ce “Ni na rasa wane irin boka take bi haka, kiga fa abokan zaman ma kamar tsoronta su ke yi!” “Yo ba dole ba!” Mommah ta faɗa “Ai dole su ji tsoronta, gadararta fa ita aka fara aura a gidan, ke su ma Hajjaty da Alhaji Baban ba haka ta bar su ba, duk irin yadda take tsula tsiyarta basa magana.” “Mtss Allah dai yayi mana tsari da ita, ke Ni fa na fara zargin anya ba ita ce da yaranta ke zagon ƙasa ga Abatcha Automobiles ba?” Mami ta faɗa fuska ɗaure wanda ke nuna tsantsar takaicin abunda ke faruwa.
Kwanaki an saci billions of Naira daga asusun Companyn, sannan an saci motoci Masu tsadar gaske da bikes gashi duk binciken da za'a yi an kasa ganowa waye ya ɗauke su.
Haka suka ci gaba da hirarsu sai ga Nainarh ta shigo parlourn, kamar zata yi kuka ganin Mamie da Ammie a part ɗin su. Ta rasa me yake kawo su wurin Mommah ko yaushe, su zo suna zancen waccar masifaffiyar Hajiya Babbar.
Fuska ɗaure ta ƙarasa, ƙasa tayi da murya alamar bata so ta ce “Ina yinin ku” Baki washe Ammie ta amsa da “Lafiya ƙalau Nainarh, an dawo kenan”. Baki taɓe Nainarh ta ce “Eh” tana ƙoƙarin wucewa. Muryar Mamie ce ta tsayarta tana faɗin “Zo mana Nainarh kamar wacce ake kora?” kamar zata yi kuka ta juya tana faɗin “Gani” Murmushi Mamie tayi tace “An gama meeting ɗin ne?” “Laa Kinga Ni har na manta ma da batun meeting ɗin” Ammie ta ƙara. Kamar bata so ta ce “Eh an gama” Cike da ƙosawa da tambayar ta ce “Zan ɗan shiga toilet ” Baki washe Ammie ta ce “Babu komai shiga ki fito mana”
Daga haka Nainarh ta nufi bedroom ɗin ta tana sakin ajiyar zuciya. Tunani sosai take akan rayuwar wannan family nasu, a haka zaka ga kamar cikin farin ciki da ƙaunar juna suke amma a gaskiya babu duka biyun, a da yadda taji ana bada labari ƙalau ake zaune, amma tun wani lokaci da ya shuɗe zaman lafiya ya ƙauracewa wannan family, ga dai duniyar ta samu sai son Barka, abu ɗaya suka rasa shine zaman lafiya da kwanciyar hankali don kuwa daga Wannan sai wancan
Kullum cikin cases ake, yau wannan gobe wancan, an rasa gane ina gaskiya take, saran ɓoyen da ake a gidan ya fara wuce misali. Kowa na zargin kowa, cikin matayen gidan ma babu wata jituwa mai kyau, gidan Alhaji Babba dai suna zamansu ƙalau, amma sauran gidajen kam ba'a magana, wasu kansu haɗe musamman amaren hakan iyayengidajen ma.
Idan muka koma ɓangaren yara kuma Alhamdulillah yawancin su kansu haɗe yake, sai dai wasun ba haka bane. Wasun sun tashi ne kuma an raine su da ƙiyayha da kishin juna, yayinda wasu kuma ke zaune cikin farin ciki da sauran.
A ɓangaren su Mommah tun shigar Nainarh bedroom nata suka ci gaba da hirarsu. Ammie ce ta ce “To yanzu ke Hajiya Sughrah meye hukuncin da kika yanke kan shi Aliyun?” Gyara zamanta tayi tace “Ni me na San zan yanke ne? Gabaɗaya kai na ya kulle, na tura masa messages ma Bana tunanin ya gani, na ce masa yayi haƙuri ya dawo gida za'a shawo kan matsalar amma ya ƙi.” ta idasa cikin raunin murya. “Gaskiya ban ji daɗin abinda ya faru ba, shi ma Aliyu me ya kai shi ga neman ƴar gida a cikin gida?,gashi yanzu ba'a san ma wane hukunci Alhaji Baba zai yanke ba.” Ammie ta faɗa cike da kulawa. “Abun da na gani kenan Hajiya Saudatu, sai dai wani hanzarin ba gudu ba, tunda yanzu dai muna hasashen irin hukuncin da Alhaji Babba dai yanke, ina laifin kawai mu haɗa aurensa da Kausar idan ya so Kinga dole Alhaji Baba ya dakatar da wannan hukunci!” Mamie ta faɗa tana son ƙara nunawa Mommah muhimmanci wannan shawarar sai dai Ammie ji take kamar ta ƙwale ta don ta mata shigar sauri.
Jimm kaɗan Mommah tayi tana tunanin yadda abun zai kasance, idan har tayi wasa da wannan damar za'a samu matsala, amma wani ɓangare na zuciyarta na nuna mata illar hakan, musamman in ta tuna da halin Mazan nata, sai kuma Wani ɓangare na zuciyarta ta ce mata “Cikin ku waye ya haifi wani ne kam?” Tabbas dole yanzu ta nunawa Ya Sadauki iyakarsa, babu yadda ya iya, dole ya bi wannan sharaɗin nata, tunda gashi ƙiri da muzu dai so ake kowa ya tsane shi a gidan. Kullum tana da burin sanin waye ke musu wannan Zagon ƙasa (Khadija candy). Har yau har yanzu ma bata gamsu da cewar Ya Sadaukin zai aikata abinda aka tuhume shi a kai ba.
Ganin shirun da Mommah tayi yasa Ammie jin daɗi ganin dai alamar ƙorafin Mami bai karɓu ba. Ɓangaren Mami ma ras gabanta ya buga, fatan ta dai Allah yasa kar ta bayyana hakan gaban Hajiya Saudatu. “Kinyi shiru Hajiya Sughrah ” Wata nauyayyar ajiyar zuciya Mommah ta sauƙe tana faɗin “Gaskiya ne Hajiya Baraka, ina ga shawarar ki ta yi, amma kuna tunanin kuwa Sadauki zai amince da wannan haɗi?” Cike da son ƙarfafa mata guiwa Mami ta ce “Ƙwarai kuwa ai dolensa ya amince Hajiya Sughrah, ke ce uwar ko shi?” “Ni ce mana”. Mommah ta bata amsa. “Idan kuwa ta tabbata hakan ban ga abun tashin hankali ba, yanzu dai amincewar ki kawai nake jira.”
Hararar gefen ido Ammie ta jefawa Mami don ji take kamar ta shaƙo wuyanta ko zata huta, sai dai kawai sai ta danne gudun kada a gani wacece ita ɗin “Ki amince kawai Hajiya, in ba haka ba kuma ki shirya haɗa zuri'a da Hajiya Babba, ta ƙara samun damar mallake ko da ɗan naki tare da dukiyarsa fiye da da .” Ammie ta faɗa yayinda zuciyarta ke ƙuna.
Murmushi Mami tayi jin yadda Ammie ta sauƙaƙa mata plan ɗinta. “Ina sauraron ki Hajiya Sughrah ” Kamar zata yi kuka tace “Babu komai, yanzu dai Allah yasa ya dawo gidan, in ya dawo ko baya so dole ne ya amince da auren nan, don wallahi ban isa ba haɗa zuri'a da dangin Mayu masu mallake zukatan jama'a ba ”
Cike da farin ciki Mami ta ce “Kar ki wani damu Hajiya Sughrah, akwai malamin da yake min addu'a, gobe goben nan zan samu na je wurinsa, cikin kwana uku zaki ga Sadauki ya dawo gida” fuska sake Mommah ta ce “Da kuwa kin samu kyauta mai tsoka matsayin tukuicin ki.” “Baki da damuwa Hajiya, Ni dai tunda kin amince zan kula da komai.”
Ammie ce ta fara miƙewa da niyyar wucewa, Mani ta ce “Hajiya Saudatu ki ɗan jira Ni don Allah sai mu wuce” Fuska sake Ammie ta ce “To kin san ina so ne naji yaya akan me suka tattauna yau, fata na Allah yasa ba batun Sadauki bane ”
Ɗan ƙaramin tsaki Nainarh da ta fito daga bedroom ɗinta tayi, steps ɗin takalminta Ammie ta ji hakan yasa ta waiwayo don ganin ko Hajiya Baraka ce. Ganin Nainarh yasa ta washe baki tana faɗin “Nainarh, kin fito gashi zamu wuce, ko zaki biyo NI ki karɓi kunun gyaɗar ne?, na riga na gama Shiyasa amma na ajiye miki sanin yadda kike son abun.” Fuska sake Nainarh ta ce “Kai Amma na gode sosai , bari kawai na bi ki na karɓo” “To kiyi sauri.” Daga nan Nainarh ta bi bayan Ammie zuwa shashen ta.
_Don Allah masoya ayi reacting, masu complain cewa basu ganin update kuyi haƙuri don Allah, zan rage ɗaura abu bayan update saboda kuna gani, idan baku samu ba kuma zaku iya yi min magana na tura muku ta 08143760764. Please ayi reacting sannan a taya Ni sharing, zan ƙara yawan update a rana in har na ga sauyi, at least 100 reactions nake son gani._ _Thanks my esteem fans, Love you loads.._
[11/9, 11:45 AM] Diamond Bhatool💎:
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
*PAGE* 0️⃣7️⃣
﷽
Bayan tafiyar su Nainarh ya rage sai iya zahrah wacce ta lula izuwa duniyar tunani, tabbas yanzu ne zata fara gina rayuwarta, amma kuma matsala ɗaya da ta gagara kawar da ita daga ƙwaƙwalwarta shine rashin Mama. Fatanta kullum Allah ya bayyana ta. A wani ɓari na zuciyarta kuma haka kawai take jin wani baƙon yanayi na ziyartarta tun shigowar ta wannan gida, har ta kai ga ta fara tunanin kamar ƙaddarar rayuwarta na shirin canzawa, sai kuma wani abu da ta lura da shi a ƴar hirar da suka yi da cousins nata, amma sai ta kawar jin abun na shirin kai ta wata duniya ta daban.
*****************
*LONDON*
Alhamdulillah zamu iya cewa don a halin yanzu, jikin Ya Sadauki yayi sauƙi sosai, kulawa kam ya same ta daga Ya Khalil da kuma likitansa DR. Arƙam. Abu ɗaya da har yanzu ya kasa fahimta shine tsawon jinyarsa da Ya Khalil yayi bai taɓa ce masa komai ba, idan ya gama masa abunda ya dace a matsayinsa na majinyaci baya ƙara cewa komai, tun yana sharewa saboda miskilanci irin nasa har ya dawo abun ya fara damunsa don tsawon rayuwarsu hakan bata taɓa faruwa ba, sun tashi ne cike da so da ƙaunar juna duk da cewa babu wata alaƙa mai kyau tsakanin iyayensu mata, a irin hali na Ya Khalil, Ya Sadauki kansa ya san shi ke hakuri da shi.
Ganin ba shi da wata mafita kuma hakan na ƙarawa zuciyarsa nauyi yasa yayi niyyar tunkarar ɗan'uwan nasa ya ji wani irin babban kuskure ya tafka haka ne har ya iya fushi da shi, fushin ma irin wadda bai taɓa yi ba. Lumshe fararen idanuwansa yayi yana sauƙe wata nauyayyar ajiyar zuciya.
Shigowar Ya Khalil ne yasa ya buɗe lumsassun idanuwansa da sauri yana kai dubansa gare shi, sai dai abunda ya ƙara bashi mamaki shine yadda Ya Khalil ɗin ya kauda kan sa gefe. Kujerar da ce gefensa ya ja zauna fuskar nan tamau kamar an aika masa da labarin mutuwa. Kamar zai bar maganar sai sun koma sai kuma ya daure, a hankali cikin Muryar da ke nuna cewa mallakinta lafiya bata wadace shi ba ya ce “Dude!”.
Ɓangaren Ya Khalil ya ji sarai sai ya ƙara ɗaure fuska ba tare da ya juyo ba. Zuciyar Ya Sadauki ne ta ɗan karye sai kuma ya tsinci kansa da ƙara ƙiran Ya Khalil ɗin. “Dude!” nan ma ya Khalil bai amsa ba. Hakan ya ƙara tabbatarwa Ya Sadauki irin fushin da ɗan'uwansa yayi da shi. Tunanin yadda za'a yi ya sanyaya zuciyarsa yake amma ya rasa. Karo na farko da murmushi ya sauƙa kan kyakkyawar fuskarsa, alamar dai ya tuna da wani abun ne da ya saka shi nishaɗi.
Lokaci ɗaya kuma ya sarƙafe da tari ba ƙaƙƙautawa, a zabure Yaya Khalil ya miƙe ya nufi yadda yake. “Man! Man!!!, lemme call the Dr.” sai ya juya zai fice a rikice. Dakatawa yayi jin an riƙe shi, tuni ya waigo yana duban Ya Sadaukin da yayi kalar ban tausayi da fuskarsa. Haɗe fuska Ya Khalil yayi kamar ba shi ya gama nuna kulawarsa ga yanayin ɗan'uwan nasa ba. “Ya dai Malam, let go off me!” A sanyaye Yaya Sadauki ya ce “Why Dude?” ya idasa cike da raunin murya. “Why all these please?, idan ka juya min baya haka ina ganin babu amfanin cigaba da rayuwa ta, kar ka manta kai ɗaya ne bayan Alhaji Baba Ka kasance garkuwa gare Ni, kada ka yi min haka, idan wani abun nayi maka we need to talk, ba wai ka sauya min ba.” dafe kansa yayi yana gama faɗar hakan tare da lumshe idanunsa.
A sanyaye Yaya Khalil ya juyo yana fuskantar ɗan'uwansa cike da so da kulawa tare da tausayawa rayuwarsa, sai kuma ya ji a ransa cewa bai kyauta ba kan abunda ya aikata, he should haven't act in such a way, but it's not too late. Fuska sake ya riƙo hannun Yaya Sadauki tare da haɗe su wuri ɗaya da nasa. “I'm sorry man!, I shouldn't have not done such, duk irin yadda muka kasance but I can't hold it more Shiyasa nayi fushi da kai, don Allah Man, ka sanyaya ranka, ka ƙara haƙuri da jajircewa, ƙungiyarku na shirin durƙushewa saboda yadda ka raunana, don Allah ka koma Sadaukin da Abatcha Family ke alfahari da shi, kada ka bari maƙiya suyi dariya, ka koma kan aikinka Sannan ka koma ga Ahalinka, a cikinsu akwai waɗanda suke cikin ƙunci da rashin ka, be linient with them please, Ka koma don Allah, na maka alƙawrin kasancewa by your side.”
Shiru ne ya wanzu tsawon wani lokaci kowa da abunda yake saƙawa cikin ransa, Yaya Khalil na addu'ar ubangiji ya bashi sa'ar kwantar da wannan raunananniyar zuciya shi kuma Yaya Sadauki na addu'ar Allah ya sauƙaƙa masa al'amarin.
Lumshe idanuwansa yayi tare da buɗe su lokaci guda sai kuma ya kalli Ya Khalil, kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce “Ok” Da sauri Yaya Khalil ya ɗago ya dube shi jin amsar da ya bashi wondering if amsan da ya bashi yaji da kyau. Tunaninsa ya koma kwacakom ga bai ji da kyau bane. Ganin dai ba ƙara magana Yaya Sadauki zai yi ba yasa yaya Khalil faɗin “Man ka haƙura zamu koma Naija??” kamar ba zai kula shi ba sai ya ɗaga kansa alamar eh. Da sauri yaya Khalil ya miƙe ya rungume Yaya Sadauki, bai yi ƙoƙarin dakatar da shi ba coz he need it, he need someone to hug him ko zai sa damuwoyinsa raguwa. Cike da Farin ciki Yaya Khalil yake faɗin “Masha Allah, thank you so much, Allah ya ƙara maka lafiya.” Cikin ransa ya amsa da “Amin” sai kuma ya janye Yaya Khalil ɗin da ke jikinsa zuwa gefe. Lokaci guda kuma suka shirya, ko da Dr. Ya zo yayi discharging nasu ba su tsaya ba suka wuce bayan shawarwarin da Dr ɗin ya bawa yaya Khalil game da rashin lafiyar yaya Sadaukin.
******************
Ganin duk ƴan matan sun tafi yasa Hajjaty ƙwalla ƙiran Zahrah da ke kwance kan sofa. Da sauri ta miƙe tsaya tana faɗin “Ina zuwa Hajjaty ” a gefen Hajjatyn ta zauna, nan Hajjaty ta fara jan ta da taɗi, sosai suka sha hirarsu Hajjaty na ƙara kula da yanayin Zahrah tana mai ƙara fahimtar ta. Lokacin sallah da yayi Hajjaty ta saka Zahrah gaba suka gabatar da sallar su wanda su biyun suka daɗe a sujjada suna masu faɗawa Ubangiji damuwarsu wacce kusan duk kusan abu ɗaya ne suke roka wurin Ubangiji.
Bayan sun yi sallah suka yi lunch ɗin su, ko tashi daga dining area basu yi ba sai ga Nasreen ta shigo ɓangaren Hajjatyn. Cike da son tsokalo Hajjatyn ta ce “Zahrah samu kiyi wanka tunda kin shirya mu tafi part ɗin mu.” Hajjaty da ke shirin miƙewa ta ce “Kya yi ki gama ai, ko uwarki Ruƙayya bata isa ta zo tace Zahrau tabi ta ba.” dariya Nasreen tayi ta ce “Mai da wuƙar Hajjatyn mu, ba da faɗa min ga na zo ba, na zo ne na ɗauki ƴar'uwa ta mu ɗan huta.” A ɗan fusace Hajjaty ta ce “To ai sai ki ɗauakd ta ko! Ke Nasreen wallahi ki kiyaye Ni, har Ni zaki faɗawa yan'uwan taka? To ki ɗauke ta ku je maza.” Ganin dai da gaske Hajjaty fushi tayi yasa Nasreen kwantar da murya hanmayenta biyu haɗe ta ce “Yi haƙuri masoyiyar kakata wacce babu kamarta, wasa nake kawai na zo na ɗebewa Zahrah kewa ne.”
Kamar ba Hajjaty ke masifa ba sai ta saki fuska yana washe baki “Kai amma naji daɗi sosai Nasreen, Shiyasa kullum nake ƙara yabon ƴaƴan Ruƙayya , Allah dai yayi Miki albarka. ” Sai ta kalli Zahrah da ta miƙe itama tana kallonsu tace “Zahrau kuje bedroom ɗin ki ke da ɗiyar Albarka ko?” Kai kawai Zahrah ta gyada tana mai sakin fuakarta tare da nufar yadda Nasreen ɗin ke kallonta tana murmushi ita ma.
Tare suka ƙare yinin nan sai wuraren 5:25 Nasreen ta ce zata wuce, “Zahrah kiyi wanka kafin na dawo”, “Ok” Zahrah ta bata amsa, daga nan Nasreen ta wuce zuwa part ɗinsu. A hanzarce tayi wanka ta saka kaya, ko kwalliya bata yi ba duk da kasancewar ta gwanar hakan. Wasu EXTRA Kaya ta kwaso ta fito, tana zuwa parlour suka yi kiciɓus da Hajiya Babba. “Eh an Damah Hajiya Zan kaiwa Zahrah ne Yaya Auwab zai raka ta tayi shopping ” kamar zata ce wani abu sai kuma kawai ta yi mata alama da hannunta da ta wuce. Sai da ta sauƙe ajiyar zuciya kafin ta fito da sauri. Ganin Zahrah ta yi wankan ya sa Nasreen miƙa mata kayan. “Ki saka wannan kafin gobe ki yo shopping,”baki Zahra ta buɗe zata yi godiya, kamar Nasreen ɗin ta san me zata ce ta dakatar da ita tana ɗaira index finger nata a kan baki “Dont say thanks, u deserve more.”
Haka Zahrah ta sanya kayan da suka matuƙar amsar jikinta, abun ba'a cewa komai tayi kyau sosai. Nasreen ce ta kalle ta tace “Wow! Kinga yadda kayan suka yi Miki kyau kuwa Zahrah? Abun ba'a magana fah!” Murmushi Zahrah tayi tama faɗin “Lallai kam, babu wani kyau fah, you are just kidding ” In a serious tone Nasreen ta ce “For sure Zaharah I'm telling the fact, kin yi kyau, kina da kyau ma zance” “Ok thank you dear, kema kin yi kyau ai”. Zahrah ta bata amsa cike da son kawar da zancen.
“Kin ga Zahrah, let's get going” Nasreen ta faɗa tana riƙe hannun Zahrah “Ina ne zamu je haka Nasreen?” Zahrah ta tambaya. “Lallai ma Zahrah ” Nasreen ta bata amsa tana harararta. “Ba Hajjaty ta ce zan raka ki ki gaida mutanen gidan ba kuma na nuna Miki gidan ba” “Oh” Zahrah ta faɗa “Wallahi na shafa'a, mu wuce ko” daga haka suka fice har lokacin hannunsu riƙe da na juna suna tafe suna taɗinsu har suka fito daga part ɗin Hajjatyn.
Da Ya Aufa suka ci karo yana ƙoƙarin shiga ɓangaren Hajjaty, da sauri suka gyara masa hanya tare da gaida shi. Tsayawa yayi yana kallon su kamar wasu sababbin halittu, ganin irin kallon da yake yiwa Zahrah yasa duk ta ɗan rikice, gyaran murya Nasreen tayi tana faɗin “Ehm Yaya Aufa mun wuce ko” sai ta ja hannun zahrah suka yi gaba. A ɓangaren ya Aufa sosai ya yaba da kyau da kuma tsarin halitta irin na Zahrah, sai ya tsinci kansa da jin ƙaunarta,zuciyarsa ta ƙara masa ƙarfin guiwa da faɗin “Ƴaruwarka ce ai!” da haka ya ahige part ɗin Hajjatyn cikin sanyin jiki.
Su Zahra na wucewa suka nufi part ɗin Alhaji Babba wanda ya kasance haɗaɗɗe tun daga wajensa, yana da girma da kuma faɗin gaske, kai tsaye Nasreen ta ja hannun ta zuwa cikin part ɗin da ke ɗauke da sassa uku manya manya. A hankali Nasreen ta furta “Nan shine sashen mu Zahrah, ɓangaren Alhaji Babba kenan ai kin gano shi?” kai ta gyaɗa mata daga nan suka tunkari sashen Hajiya Babba, wato sashen sun Nasreen ɗin.
A parlourn suka tarar da Hajiya Babba kwance kan sofa ga kuma Fruits a ɗan basket ɗin da ke table ɗin gabanta. Sunkuyar da kai ƙasa Zahrah tayi ganin matar ita kuwa bata ma san ta shigo ba coz hankalinta na ga labaran da take kallo. Ko da suka isa dai-dai tsakiyar parlourn sai Zahrah ta zauna ƙasan carpet ɗin, Nasreen ce tayi gyaran murya tace “Hajiya Babba!” a lokacin ta ɗago ido tana duban Nasreen ɗin, bata kai ga ɗauke idonta daga gare ta ba taji wata sassanyar murya mai taushin gaske na faɗin “Ina yini”.
A lokacin Hajiya Babba ta mayar da dubanta ga sashen da sautin ya fito, duk da cewa kanta a ƙasa ya ke amma hakan bai hana zuciyarta bugawa ba. Fuakarta babu yabo babu fallasa ta amsa da “Lafiya ƙalau ƴan mata, ya kwanan baƙunta.” Zahrah da kanta ke ƙasa ta fara magana yayin da zuciyar ta ke gudu da sauri da sauri wanda bata san dalilin hakan ba. “Alhamdulillah Mama” Ɗan sakin fuska kaɗan Hajiya Babba tayi tace “Kar ki saka damuwa a ranki, ki ɗauke Ni tamkar Uwar da ta haife ki,ga Nasreen nan zata kasance a tare da ke, amma ki kula sosai!” daga haka tayi shiru. Zahrah ta ce “Na gode sosai, Allah ya ƙara girma” bata ji amsar Hajiya Babban ba amma cikin ranta tana ayyana wasu abubuwa, why take ta haɗe mata fuska ko bata farin ciki da zuwanta ne?, abu na gaba haka ta jinjina mulki irin na Hajiya Babbar har take tunanin anya ita ta haifi Nasreen?.
Muryar Nasreen ce ta dakatar mata da tunanin ta “Mu je gaba kada Maghrib tayi bamu gama zaga gidan ba.” miƙewa tayi ta kai dubanta ga Nasreen ɗin kafin su yi waje tare, Hajiya Babba dai da ido ta bisu har suka ɓace.
Ɓangaren Hajiya Karima suka yi, a nan kam Zaharah ta samu kyakkyawar tarba daga Hajiyar tsakiya. Sosai ta nuna farin cikinta da ganin Zahrah, haka mutanen da ta tarar ma a parlourn, Hibba, da Samha su ma suka yi ta zolayanta sai taji kamar kada su tafi.
Daga nan suka wuce part ɗin Ƙaramar Hajiya, babu laifi nan ma Zahrah ta samu Garba musamman daga Aunty Meerah dake tare da ƙaramar Hajiyar.
Sosai Nasreen taji daɗi ganin yadda suke nuna mata ƙauna, can dama su part ɗin su ba'a faɗa in fact duk kansu haɗe yake Shiyasa ko da ta shiga bata fuskanci wani kallo ko hali na nuna cewa su ɗin abokan zama ne ga mahaifiyarta ba. Hakan yayiwa Zahrah daɗi duk da cewa ta saka Ayar tambaya akan hali irin na Hajiya Babba ɗin.
Daga nan sai da suka yi tafiya mai ɗan tsayi har suka wuce wani ɗan cool down mai ɗauke da flowers masu Kyan gaske, though Zahrah bata tambaya ba amma Nasreen told her that cikin estate ɗin nan akwai kwatankwacin irin wannan wuri kusan guda Ashirin, and its all meant for refreshing minds. Sai dai ta faɗa mata cewa “Wannan kuma da kika gani ba kowa ke zuwa ba saboda na Yaya Sadauki ne! Ko baya gari babu mai gigin zuwa wurin saboda wurin zamansa ne.” Sai da zuciyar Zahrah ta buga da jin sunan though this is the first time da ta ji sunan. Amma sai ta samu ƙarfin halin faɗin “Who is he?” Nasreen ta bata amsa da faɗin “In mun koma I'll let you know who is Yaya Sadauki, zan faɗa Miki!”
_Masn son magana da ni kai tsaye ko suke buƙatar littafin daga farko, ga number na +2347061707238._ _React please, a taya Ni isar da saƙon ta hanyar sharing don Allah, ina ƙaunarku my. esteem fans, Allah ya bar mu tare. Diamond Bhatool taku ce 🤗_
*TALLA! TALLA!! TALLAH!!!*
Ina mata ƴan ƙwalisa! Ina uwar gida sarautar mata!!! Amarya kema ban barki baya ba, Naji da yawa na complain akan yadda fatarsu ta koma saboda rashin samun ingantattun kayan gyaran jiki, fuskarsu ƙuraje da sauran skin infections.
Hohoho! Nesa ta zo kusa fah! Kuyi maza ku garzayo don samun naku kayayyakin gyaran jikin waɗanda basu da wani side effects a jikin mai amfani da su.
*Kayayyakin su haɗa da:* 1. Supplement gummies waɗanda zasu gyara Miki fuskar ki tayi luwai tamkar fatar jariri, ta yadda ko ina kika shiga sai an tambaye ki ina kika samu wadannan kayayyaki masu inganci. 2. Breast enlargement cream Wanda bashi da wata illa ga mai amfani da shi, cikin kwanaki ƙalilan zaki ga yadda yake aiki. 3. Akwai sauran kayayyakin gyaran jiki masu matuƙar inganci wanda babu Algus cikinsu. *Ƴar'uwa matso kusa ki mallaki naki kan farashi mai sauƙin gaske.*
*Kai tsaye ki tuntuɓi wannan number +2347062283256 Kada ku bari ayi babu ku ƴan ƙwalisa.*
[12/7, 9:03 AM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_
*PAGE* 0️⃣8️⃣
﷽
Daga nan suka wuce part ɗin Daddy, kamar koyaushe Mamie, Mommah da Ammie ne ke zaune a katafaren parlourn da ya gaji da haɗuwa wanda shigar su tayi dai-dai da fitowar Nainarh daga bedroom nata. Da gudu ta karaso tare da hugging Zahrah tana faɗin “Irin wannan suprise haka!” sai kuma ta sake ta tare da kama hannunta. “Ina kuma zaki da ita?”Nasreen ta faɗa tana ƴar hararar Nainarh. “Im sorry sis Nasreen wallahi ni ban ma lura da ke ba” “Ina kuwa zaki lura dani tunda Zahrah na rako, silly girl!” ta ƙarasa tana hararar Nainarh wacce ke dariya. Hayaniyarsu ce ta sa mutanen da ke cikin parlourn suka farga da wanzuwar su, Mommah da ta sa idonta kan Nasreen sai ta haɗe rai thinking why is that girl there? Me ta zo yi part ɗin ta. Su ma sauran duk sai suka mika kallon su ga wurin da Mommah ke kalla. Caraf idonsu ya sauƙa kan baƙuwar fuskar da basu sani ba. Da sauri Nainarh ta ja hannunsu tana faɗin “Lets get in” a sanyaye suka bi bayanta har suka kai tsakiyar parlourn yayinda suka lura da kallon banza da ake aika musu wanda hakan ke da nasaba da zuwan Nasreen ɓangaren.
A ƙasa Zahrah ta zube kan guiwowin ta, cikin sassanyar muryarta tafara gaida su, nan suka amsa zukatansu fal da alhinin son sanin wace ce ita, Nasreen ma ta gaida su, sai dai babu wacce ta amsa ciki sai ma kallon Banza da Ammie ta cilla mata. Ganin za'a iya samun matsala yasa Nainarh faɗin “Mommah ga nan jikanyar Hajjatyn da nace miki ta dawo gida, sunan ta Zahrah.” Ɗan murmushi kaɗan Mommah ta saki saying “You are welcome Zahrah” Suma Ammie da Mimie suka faɗi hakan kamar yadda Mommah ta yi.
Nasreen da ke gefe ne ta ɗan taɓo Zahrah, saboda haka suka miƙe, Zahrah na faɗin “Nagode sai anjima”. Daga nan Nainarh tabiyo bayansu suka fice Ita dai Zahrah an cika ta da tunani, ta rasa kan wanne ma zata yi yanzu. Irin yadda taga an yi ma Nasreen ko kuma dai kallon da Ammie ke binta dashi ta ƙasan ido?, Bata san wanne ɗaya ya kamata ta tattauna ba ita da zuriyarta. A haka suka zaga sauran parts ɗin, jiki gajiye suka dawo part ɗin Hajjatyn lokacin ana kiran Sallah a masallacin estate ɗin.
Ko da suka yi sallah nan suka baje babin hirarsu, har kusan Isha Nainarh ta ce zata wuce ɓangaren su. Daga nan suka yi sallama. Ita dai Zahrah dama jira take Nainarh ta fita ta fara baje kolin tambayoyin ta ga Nasreen wacce duk cikin ƴan'uwan nata tafi jin nutsuwa tare da ita. “Yauwah Nasreen what about that Yaya Sadauki da kika ce zaki yi gisting na about him?” “Ai dama na san ba zaki manta ba” Nasreen tabata amsa tana ɗaura hannayenta kan na Zahrah. “Kaɗe kunnuwanki ki ji labarin Sadaukin Abatcha” hararar wasa Zahrah tayi mata saying “See you girl, har wani kaɗe kunne zan, kinga muje don yau inaga anan zaki kwana coz I've so many questions for you.” “Dan ma dai na san the story will be so boring to you, amma lemme start.” Murmushi Zahrah tayi tana mai gyara zamanta kafin ta ce “All ears.”
“Toh Zahrah kamar yadda kika ji nace Yaya Sadauki haka mu muke ƙiransa, amma Aliyu shine ainihin sunansa. Ya samu wannan take ne daga yarintarsa daga wurin Alhaji Baba kamar yadda Hajjaty ta taɓa bamu labari. Yaya Sadauki mutum ne irin masu tsattsauran ra'ayin nan ne da suke rayuwa irin ta kaɗaici kuma basu buƙatar wani ya kutsa cikin rayuwarsu, wanda hakan kuma na da nasaba da tarin damuwoyi da suka masa yawa. Yaya Sadauki miskili ne ajin farko, don zan iya ce miki a rana zaki iya ƙirga words ɗinshi.”
“Idan har kinji maganarsa to shi da Yaya Khalil ne, ko kuma Hajjaty da Alhaji Baba, shima kaso 90 na maganar a hannun su yake.” ta dakata tare da jan wani dogon numfashi alamar tana buƙatar faɗar wata gaɓar da ke da muhimmanci.
“ Zahrah, Duk Cikin estate ɗin nan kai duk faɗinsa babu wani mahaluki da ke da kwarjini irin nasa, babba da yaro kowa shakkar sa yake. Ba wannan ba ma, kin san irin tarin dukiyar da ya mallaka tasa kuwa?, Wallahi Zahrah zan iya ce miki duk estate din nan babu wanda ya kai shi tarin dukiya, shiyasa most yan matan family suka maƙale masa Though shi bai ma san suna yi ba don ana yawan samun fadace fadace cikin gidan nan, ke dai Zahrah zaki ga abubuwa iri-iri, kiyi taka tsantsan wajen mu'amala da kowa, Domin akwai abubuwan da ba sai na miki bayani ba lokaci kaɗai zai nuna miki su.”
Gauron ajiyar zuciya Zahrah ta saki lokaci guda kuma maganganun Nasreen na yawo cikin ranta, and she needs time to think more about them. Shirunta yasa Nasreen murmusawa tana faɗin “Watz wrong Zahrah?” Numfashi Zahrah ta ja tare da fesar da wata zazzafar fuska kafin tace “Nasreen amma ban taɓa kallonsa cikin gidan nan ba.” Cike da kulawa Nasreen din tace “Zahrah In na miki bayani ma ba Lallai ki gane ba, yanzu haka maganar da nake miki baya ƙasar shi da yaya Khalil duk da cewa dama can ba ma'abocin zama bane amma wannan tafiyar ta sha bamban da wacce yake yi”
Cike da ƙaguwa Zahrah tace “gist me please, haka kawai nake jin kamar shi ɗin wani sashe na jikina ne duk da cewa hakan take amma ina jin matuƙar tausayinsa Nasreen”
“Hmm Zahrah nima ina fatan kamar zuwan ki zai sauya abubuwa da dama da suka shige ma ahalinmu duhu”
Jiki sanyaye Zahrah tace “Wallahi tun yanzu naji ina son kasancewa hakan, kuma na saka raina In har na samu damar hakan zan yi yadda ya dace don kawo sauƙi ga radadin da ƴan uwa na suke ciki. Yanzu ki fada min please me ya faru?”
Dogon numfashi Nasreen taja kafin ta ce “Daf da zuwan ki ne abun ya faru _A babban gida_ wanda ya ɗaure kusan kwanyar kowa. A yadda na faɗa miki yaya Sadauki mutum ne da sha'anin mata baya gabansa, bazance gashi yadda abun ya faru ba amma dai naji zancen wai an kama shi ne da shirin raping Aunty Mabruka dai ta gidanmu, idan aka miki bayanin yadda abun ya kasance zaki san cewa shiri ne, don kuwa bayan tafiyarsa ne saboda ɓacin rai su Hajjaty suka farga da hakan, an tsara da gayya na farko don a raba tsakanin sa da Hajiya Babba, na biyu kuma akwai wani boyayyen al'amarin da nake kyautata zaton faruwar sa babu jimawa, Zahrah da ace ina da yadda zanyi ba shakka da tuni nayi don gano gaskiya, Yaya Sadauki don't deserve to be treated that way, duk irin yadda nake fada miki tsaurin sa amma fagen kyautatawa da mutunta na gaba babu ya shi Zahrah, kinga babu jituwa tsakanin Hajiya Babba da Mommah amma Yaya Sadauki baya duba hakan, duk gidan nan babu wadda yake mutuntawa sama da Ita cikin iyaye mata dake cikin ahalin nan, idan tafiya yayi zai dawo, tsaraba baya bambanta wani da wani....”
Kuka ne ya ci ƙarfin ta, cike da tausayawa Zahrah ta fara lallashinta wanda itama ƙarfin zuciya ne kawai. Bayan Nasreen ta dakatar da kukanta shiru ne ya wanzu na wani lokaci kafin Nasreen tayi ma Zahrah sallama.
Ko da Nasreen ta wuce sashen su, Zahrah tunani ne birjik cikin ranta na son samo maslaha ga wannan alhali. Ganin bacci yaƙi ɗaukar ta ya sa ta shiga toilet ta ɗauro alwala, nafila raka'a huɗu ta jera, sannan ta ƙara da witri. Daga nan ta roƙi Ubangiji kan ya kawo mata hasken da zai kasance jagora gare ta wajen saisaita komai cikin sauƙi. Daga nan kuma ta fara raira Alqur'ani, tana cikin yi ne bacci ya ɗauke ta kan sallayar.
Misalin ƙarfe 2:30am ta farka a firgice jikinta na ɓari, da ƙyar ta samu zarrar furta innalillahi wa inna ilaihi rajiuun. Ba komai tayi mafarki ba sai ɗaya daga cikin matan da tarar a parlourn su Nainarh (kamar yadda ƙwaƙwalwarta ta hasaso mata) tana bin ta da matsiyacin gudu hannunta kuma riƙe da wata sharɓeɓiyar wuƙa wacce ke fidda tartsatsin wuta.
Bata kai ga cin mata ba sai ga wani haske mai ƙarfi gaske ya bayyana, tuni Zahrah ta samu nasarar shigewa cikin hasken wanda yayi daidai da isowar matar wajen sai dai ta tsaya tana haki a gaban hasken alamar ba zata iya tunkararsa ba.
Daga haka Zahrah ta farka, nan ta ɗauro alwala ta ƙara jera wasu four Raka'at ɗin sannan ta faɗawa Ubangiji damuwarta cikin sujjadarta. Daga nan ta fara karanta Alqur'ani har alfijir ya keto.
*London*
Tabbas ya Sadauki ya jima bai samu irin baccin da yake yi ba yau, hasali ma zai iya cewa tunda ya zo London bai taɓa yin baccin ba ma saboda tsantsar damuwar da ta cika kogin zuciyarsa, bashi da wani aiki sai tunani, idan daren ma yayi babu abun yi sai tunani, sai kuma in ya gaji ya ɗaura da ƙiyamullayli. Tunda ya rike wannan tsayuwa ta dare kuwa babu makawa Ubangiji zai tsaya masa, zai kuma kare shi daga sharrin makiya sannan zai tabbatar da samar masa da hanyoyin cigaba a rayuwa duk da wasu basu son hakan.
Da misalin 4:20am ya farka ɗauke da addu'ar bacci a bakinsa. Bai miƙe ba yana kwance har bayan wasu daƙiƙu. Ba komai ya ke yi ba sai ƙoƙarin tuna mafarkin da yayi da kuma mamakin ta ya aka yi har bacci ya ɗauke shi bayan tun ba yau ba ya guje masa.
Lumshe idanuwansa yayi, a lokacin kuma komai ya fara dawo masa. Ajiyar zuciya ya sauƙe wondering who's that light? Wane haske ne ya tunkaro shi!? Kuma wace murya ce take wannan amo da yaji? “Ya Allah” ya furta tare da sakin wani gauron numfashi sannan ya miƙe tare da shiga toilet ba tare da ya tashi ya Khalil da ya taya shi kwana ba.
Sai da ya gabatar da raka'atanil fajri sannan ya zauna kan praying mat ɗin yana ambaton Ubangiji. Ganin kamar lokacin salla yayi yasa ya gabatar da tasa, sannan ya karanta azkar ɗinsa kafin ya tashi Yaya Khalil Wanda da ƙyar ya tashi.
Kayansa ya fara haɗawa cikin trolley don ji yake kamar garin ba zai gama wayewa ba, ya ƙosa ya koma gidan da yayiwa rani. Allah Allah yake ya koma domin fara sabon shirinsa, tabbas shine ƙarfin guiwar kansa da ma ahalinsa, sannan kuma ƙarfin guiwar partner ɗinsa da ya gani tana taimaka masa cikin mafarki.
Har yaya Khalil yayi sallarsa bai daina mamakin wannan sauyin na ba zata da aka samu ba. Sauyin da ya matuƙar bashi mamaki tare da alerting nasa cewa something fishy is happening right now.
Cike da mamakin da ya kasa dannewa yace.. “Man! What a sudden change! Allah dai yasa wannan annashuwar da na gani tattare da kai ta dauwama da kai.” sai kuma yayi shiru. Yaya Sadauki bai tanka masa ba sai ma cigaba da haɗa kayansa da yake yi.
“Wai duk zumuɗin na meye?, Mu da zamu bi Flight ɗin 10 shine tun yanzu kake haɗa kaya”
“I'm eager to be home coz finally my strength is home!”
A zabure Yaya Khalil ke dubansa yana son ƙara tabbatarwa kansa cewa shi din ne yayi maganar ko kuma dai wani daban?. Bai tsinke da mamaki ba yaji ya ƙara faɗin. “With my strength! In Allah's name zamu gano komai and dude!” sai kuma ya dakata “I swear by almighty God! Duk wanda muka gano responsible for that wallahi ba zai sha ba” ya idasa in a bitter voice.
Kai Yaya Khalil ya jijjiga yana ƙara jaddada ikon Allah, tare da fatan Alkhairi ma abokinsa, amininsa kuma ɗan uwansa.
“Ehm man za mu faɗawa Alhaji Baba batun dawowarmu ne ko kuwa!?”
Cike da isa da taƙama yace “Don't worry dude!, I'll handle that.”
Shi ma Yaya Khalil shiru yayi don ya san ko ya ja maganar yaya Sadauki ba barinta zai yi tayi tsawo ba. Daga haka ya naɗe praying mat ɗin tare da komawa kan bed ya bar mallam zumuɗiyo sai ha abubuwa yake yi.
*Akwai baƙin al'amura da ke Kunno Kai zuwa rayuwar Zahrah A Babban gida! Fatan mu su zo da Alkhairi* *Ga kuma su yaya Sadauki kan hanyarsu ta dawowa? Ko me zasu tarar a babban Gida? Meye kuma zasu kawo babban Gida?*
*Kuyi share tare da react in har kuna so na ci gaba da update!* *Group members a taimake Ni a gwangwaje Ni da comments don Allah, hakan ne kaɗai zai sa naji ƙarfin guiwar yi muku update gobe.* *I love You my esteem people.*
# diamond_bhatool # Yayasadauki # Zahrah # a_babban_gida [12/8, 8:04 AM] Diamond Bhatool: https://chat.whatsapp.com/Fw6rJSk0GuxKd8IGqbsf35
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_
*PAGE* 0️⃣9️⃣
﷽
Yana gama haɗa kayansa ya zauna bakin gadon yana maida numfashi. It has been long time since he have such beautiful and awesome night ga kuma bright morning da yake hasashen samu. Murmushi yayi a karo na farko wanda ya ƙawata kyakkyawar fuskarsa, (Ni Bhatool sai naji kamar kar ya daina😳) da sauri ya janyo wayarsa yana duba time. Ganin 6:29am yasa ya ɗan ja karamin tsaki, gaba-daya agogon kansa baya masa gudu. Gani yake kamar garin ba zai waye ba.
Kishingiɗa yayi ya kwanta, nan bacci ya kwashe shi unknowingly. A zabure ya miƙe kamar wadda aka tayar. Dage kansa yayi lokaci guda yana tunanin meye matsalar? Da sauri ya ɗauki wayarsa da saƙo ya shigo cikinta a lokacin.
Tsaki ya ja bayan ya karanta saƙon. Kamar koyaushe Rumana ce sending him morning sms, ita ta San ma me take yi coz har yau ko number ta Bata samu arziƙin saving ba, to in zai yi saving bai san waye ɗaya daga cikin ƴan matan gidan ba da suka kasance marasa aji (kamar yadda yake faɗi.)
Ganin 8:10am yasa ya shiga call log nashi, babu wasu important calls, mostly Kiran Mommah ce wanda yawanci ma missed calls ne, scrolling yayi amma bai ga number da yake nema ba.
“Shit!” ya furta tunawa da yayi blocking number kwanakin baya. Da sauri ya danna unblock tare da dialling number. Bayan an ɗaga ya gaida Alhaji Baba cike da mutuntawa
Alhaji Baba ya amsa fuskarsa sake kamar yana ganinsa, farin ciki sosai ya rufe shi ganin yau jikan nasa ya neme shi. Bai tsinke da mamaki ba sai da yaji muryarsa na faɗin. “I'm on my way Alhaji, but don't let anyone know! Iya Hajjaty zaka sanarwa and ka ce mata ta yi min gurasar Nan da take yi mai daɗi. I'll be landing soon.”
Cike da farin ciki Alhaji Baba ya amsa da “Ok babu damuwa sai kun dawo” Nan ya jera nasa addu'o'in a sauƙa lafiya daga nan suka katse kiran.
Duka ya kaiwa Yaya Khalil Wanda ya tashi a zabure. Kamar ba shi yayi dukan ba kuma sai ya make
A harzuƙe Yaya Khalil yace “Why such drum! Kaji zafi kuwa! Gaskiya man Bana son tashi da duka, kayi min magna kaga In ban tashi ba”
Kafada ya dage tare da faɗin “Mallam ka samu ka shirya don Ni ba jiranka zanyi ba” daga haka ya shige toilet ba tare da ya ƙara kallon yaya Khalil ɗin ba.
Baki sake Yaya Khalil yake kallon Yaya Sadaukin har ya banko ƙofar toilet ɗin. Wane sashe na zuciyarsa kuma na farin ciki da sauyin da ɗan'uwan nasa ya samu cikin ƙanƙanin lokaci.
************************************
*Nigeria, FCT, Abatcha estate*
Tun bayan kammala wayar da Alhaji Baba yayi da yaya Sadauki, kai tsaye ya sanar da Hajjaty cewa Allah ya amsa addu'ar ta, jikallenta na hanya. Zo ka ga murna wurin Hajjaty kamar ta taka rawa.
Ba tare da ɓata lokaci ba kuwa ta shiga kitchen da kanta ta duba meye da meye zata bukata!, Sai da ta tabbatar komai da zata yi amfani da shi akwai shi tukun ta shiga Bedroom ɗin Zahrah wacce ke ta kwasar baccinta hankali kwance..
“Zahra'u Zahra'u” “Uhmmm” “Baki tashi ba dama?, Kinga ba sai kun tashi ba dama zan ce miki anjima zaki tays Ni yiwa Yayanku abinci ne, suna kan hanyar dawowa.”
Duk da cewa baccin bai gama sakin Zahrah ba amma kalmar Yayanku da Hajjaty ta ambata yasa taji gabanta ya faɗi sai ta tsinci kanta da tashi zumbur har sai da Hajjaty da ke shirin juyawa ta dara.
“lafiyarki kuwa?” Cikin Muryar bacci ta furta “Kince yaya na zai dawo?” Murmushi Hajjaty tayi ta bata amsa kai tsaye “eh, baccin ya isa ki tashi ki samu ki kimtsa jikinki sai mu samu mu gama da wuri, zaki raka Qasim dauko shi daga airport ai?”
Jiki mace ta tsinci kanta da faɗin “Eh”
Bayan Hajjaty ta fita Zahrah ta sheƙa wankanta sannan ta sanya ɗaya daga cikin kayayyakin da Nasreen ta kawo mata, daga nan ta nufi dining. Sai da tayi breakfast kafin ta nufi kitchen ɗin, ganin Hajjaty bata nan yasa ta nufi Bedroom ɗin ta don ta tambaye ta me zata fara kafin ta zo.
Ko da Hajjaty ta sanar da ita abubuwan da za'a yi sai ta juya zuwa kitchen. Cikin ƙanƙanin lokaci Zahrah ta gasa gurasar, ƙamshinta kuwa har Bedroom ɗin Hajjaty.
Ganin yanayin zafi da ake yi lokacin yasa ta fara haramar dama abun sha, duk da cewa bata san wane yayan nata ne zai dawo ba sai ta ji kamar ta fasa yi ganin akwai drinks iri-iri a gidan ta yadda ba lallai ma abun da ta haɗa ya zama ya samu ko da kallo ne daga garesu ba.
Wata zuciyar ce ta ce mata a'a ki yi, ki da basu sha ba ai kinyi, and zasu ga kin mutunta su. Da wannan shawarar ta samu ta haɗa zoɓo mai kyau wanda ƙamshin sa kaɗai mutum ya ji sai ya so da kuma fatan harshen da ya dandana. Bayan ta gama ta koma ta watsa ruwa sannan sanya wasu kayan.
Tana gamawa ta nufi Bedroom ɗin Hajjaty don sanar da ita cewa ta kammala, sosai Hajjaty ta nuna jin daɗinta sai albarka take saka ma Zahrah.
*Nnamdi Azikwe international airport, FCT*
Ƙarfe sha ɗaya daidai jirgin yayi landing a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe, tsawon wasu daƙiƙu bayan daidaita tsayuwa da yayi passengers suka fara fitowa.
Sanye yake cikin fatan riga kirar Armani, sai kuma p-cap da ya sanya da alamar dai baya son a gane shi ne. Garin three quarter ya saka sai wani farin takalmi say ciki.
Fuskar nan ɗaure ya sauko daga matakalar Benin, biye da shi kuma ya Khalil ne wanda sabanin ya Sadauki shi fuskar sa a sake take.
Wayar shi ya fitar sannan ya kara a kunne alamar dai kira yayi, can kuma ya sauke tare da kallon gefensa. Tun kafin ya ƙaraso Alhaji Baba da ke tsaye ya ƙarasa gare shi tare da rungume shi.
“Nayi kewarka sosai” Ya faɗa can kasan maƙoshi. Sake shi Alhaji Baba yayi jin Muryar ya Khalil yana faɗin. “Tare da Ni fa muke tafe.” Shi wallahi tsabagen farin cikin ganin Sadaukin sa yasa ya manta ma da cewa tare da Khalil suke. Murmushi irin na manya yayi yana faɗin “mu samu mu wuce gida ku huta ko?”
Kai suka gyada, nan ya Qasim da ke tsaye yana kallon su gwanin ban sha'awa ya wuce zuwa wurin da motar su tayi parking, nan yaya Khalil ya shiga front seat, su kuma Alhaji Baba da Sadauki sa suka zauna gidan baya.
Kai tsaye estste ɗin su suka nufa, bisa umarnin Alhaji Baba suka tsaya a ɓangaren su. Bayan sun daidaita parking suka dunguma baki dayansu.
Babu kowa a parlourn hakan yasa duka baje kan kujerun da ke parlourn yaya Khalil na korafin wai ya gaji Alhaji Baba da ya Qasim sai dariya suke masa. Hayaniyarsu yasa Hajjaty fitowa da sauri don tabbatarwa kanta cewa su din ne.
Ganin da gaske su ɗin ne yasa ta ƙarasa wurin nasu tana sakin kukan farin ciki na ganin shalelen jikanta. Da sauri duka suka juyo suna kallon ta. Cike da zolaya yaya Khalil ya ce “Ya da kuka kuka Hajjaty, gaskiya zan sa ɗan'uwa na gaba mu koma tunda baki farin ciki da zuwan mu”
Dariya dukkansu suka yi banda Hajjaty dake hararar Ya Khalil ɗin sannan ta ƙaraso gefensa ta zauna tana faɗin “To ja'iri ku koma mana”
Yaya Khalil ya ce “Ai don ina tausayin halin da zaki shiga ne In na ɗauke miki shi da kin ga aiki da cikawa ” Ya idasa yana mata gwalo.
Danƙwalon sa tayi tana faɗin “ kaga Ni ban Don kai na fito ba” sai kuma ta mayar da kallonta ga ɓangaren da Yaya Sadauki ke zaune fuska babu yabo babu fallasa “Ga don wanda na fito ”.
Nan suka kwashe da dariya bako dayansu , daga nan kuma aka fara gaisawa. Sai a lokacin Hajjaty ta tuna da Zahrah da ke kunshe can a Bedroom dinta. “Zahra'u Zahra'u” dim dim zuciyarsa ta buga jin bakon sunan da Hajjaty ta ambata sai kuma ya waske yana tunanin ko sabuwar mai aiki ce.
Ɓangaren Zahrah ta ji shigowar su har ta mike zata fito sai kuma ta gargadi kanta ta koma yayin da zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri. Ko da Hajjaty taji karar rufe kofar sai kawai tace “Ki kawo ma su Yayanku abun sha ko?”
Ta gefen ido yake kallon mai fitowa daga wannan dakin, haka kawai yaji gabansa na faduwa da fitowar ta sai kuma yake ji a ranar yana biɗar kallon wannan sabuwar mai aiki. Tunanin sa ya katse nr jin kalaman Hajjaty na Yayanku, sai kuma zuciyarsa ta fara raya masa ko dai cikin ƴan matan gidan ne.
Tunanin sa ya katse ne yayin da sallamarta wurin ta rike dodon kunnuwansu. Zuciyarsa ne ta bada Wani sauyi Na daban sai dai a zahiri ba zaka fahimci hakan ba saboda hankalinsa kwacakom ya mika shi ga wayar da yake dannawa.
A ɓangaren yaya Khalil shi ma abun da ya faru kenan, sallamarta yasa yayi saurin ɗagowa don ganin wacece, shi dai iya tsawon rayuwarsa bai taɓa jin makamanciyar wannan Muryar ba a fadin estste ɗin su.
Kan ta ƙasa ta ƙaraso tana ajiye babban jug ɗin da ta zuba zoɓon da ta yi dazu. A sanyaye ta furta “Sannun ku da hanya, ina yini”
Baki sake yaya Khalil ke kallonta yayin da zuciyarsa ke tunanin wacece wannan, sai dai kamarta da ya gani ya sa ya tabbatarwa kansa cewa jininsu ce. Ɓangaren yaya Sadauki ma haka abun take, sai dai shi babu wanda zai san cewa kallonta yake yi.
Yaya Khalil ne yayi ƙarfin halin amsa mata da “Yauwa sannu, lafiya kalau.” Without minding his response ta fara zuba zoɓon a cups Tana Mika musu. Sai da ta sakawa kowa har su Hajjaty da Alhaji Baba kafin tayi yunkurin zuba nasa taji Muryar yaya Khalil yana fadin “Ki ɗaukowa man drink coz ba lallai ya iya shan wannan ba.”
Da “To” ta amsa tare da ajiye cup din hannunta tana kokarin juyawa muryarsa ta daki kunnenta “No bar shi, serve me wannan ɗin.” Ba iya Zahrah ba Kowa na parlourn kallon mamaki yake masa don iya saninsu dai baya son home made drinks shi kuwa ganin haka yasa ya kara maida hankalinsa ga wayarsa sai dai shi ma he's eager to know who is this lady don ya tabbatarwa kansa cewa ba mai aiki bace ganin yadda take zubi da famoly members don musamman Hajjaty, zai iya cewa photocopyn ta ne.
Kai kasa Zahrah ta juyo sannan ta dauki cup ta zuba tare da mika masa, tsawon wasu daƙiƙu tana shirin kara ce masa ga shi ya miƙo kyakkyawan hannunsa ya amshi cup din. Tana shirin komawa Hajjaty ta dakatar da ita “Ina kuma zaki je Zahrah?” “Zan koma ne ina karatu ne” ta bata amsa kai tsaye.
Alhaji Baba ya ɗago ya kalli Zahrah kafin ya ce “Dawo ki zauna ƴa ta gari, ga ƴan uwanki sun zo kuma shine zaki koma ciki”
Yaya Khalil who's tired of hearing ƴan uwanki ya ce “Hajjaty Ni ban ma gane Zahrahr taki ba, sai wani sunkuyar da kai take kamar mu ɗin sirkanta ne.”
Dariya suka yi baki dayansu, Ita dai Zahrah ta kosa ne amma haka ta dawo ta samu wuri a kasa ta zauna yayin da duk wani motsin ta yake kan idonsa.
Murmushi Hajjaty tayi sai kuma ta hade rai alamar she wanna say something important. “Yanzu Halilu wai baka san Zahrah'u na ba kake nufi?, Dama shi wancan kam ba a magana” kai yaya Khalil ya gyada yana maida kallonsa ga Zahrah wacce ke zaune ƙasa. “Da gaske Hajjaty ban san ta ba”
“Gaskiya ne, ba lallai ku san ta ba dama” Ya Qasim ya faɗa yana kallon su duka biyun sai kuma ya ce “To Hajjaty sai ki musu bayani amma ya kamata a ci tararsu.”
“Haba Yaya na Allah (kamar yadda suke kiransa su biyun) ka sa baki Hajjaty ta sassauta mana.”
Dariya Hajjaty tayi sannan ta ce “Ai babu sassauci tunda baku san shalelen jikanya ta ba, yau babu ku a girki na, kai wanda yayi muku ma ba zan baku ba, Qasim In ka tashi tafiya zan baka Gurasa ka wuce da ita.”
Da sauri kuwa yaya Qasim ya amsa da to. Ba shiri Yaya Khalil ya sauko har kasa yana faɗin “Haba Hajjaty, ai babu wannan magana, ke Zahrah je ki jera mana gurasar a dining”
Mikewa Zahrah tayi tana nufin zuwa ta jera ta tsinkayi muryarsa da tun shigowar ta bata ji ya ce komai ba tun bayan cewa ta saka mishi zoɓon. Cikin ranta tana kara tabbatar da zancen Nasreen.
“Idan kin jera, ki ajiye sauran a kitchen anjima zan sa ki haɗa min shi” daga haka kuma ya make kamar ba shi yayi maganar ba, ita kam Zahrah kadan ne ma ya hana ta dariya saboda yadda taga yayi maganar yana wani shan kamshi kuma ya make kamar ba shi ba. “He's damn amazing” ta faɗa cikin ranta.
Hajjaty ne ta dakatar da ita da faɗin “Koma Zahrah, ai hukunci na yanke musu” Zahrah sai ta koma ta zauna tare da daura kanta a cinyar Hajjatyn tana jiran ganin karshen wannan drama ta su Hajjaty. Cikin ranta kuma tana yaba yadda suke mu'amalarsu da juna, abun ya matuƙar burge ta ya kuma kara karfafa mata guiwa kan ƙudirinta.
*React and comment please, yau fa In ba a gwangwaje Ni da reactions ba zan daina update gaba-daya sai kuma kun ji Ni, ah to , Ina matuƙar son ku my esteem fans da yawa da yawa din nan 💔🦋*
[12/24, 6:57 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
https://www.facebook.com/profile.php?id=61570606515077
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 1️⃣0️⃣
_Not edited_
﷽
Hajjaty ta ce “Babu abun da ya shalle nikam, ba dai Wai ba ku San Zahrah'u na ba ku ka ce?” hmm” sai Kuma ta yi shiru. Yaya Khalil da ya kosa da son sanin wace ce wannan Zahrahr ya sa ya ɗan kwaɓe fuska kamar zai yi kuka ya ce “To Hajjaty ki faɗa Mana please” Sosai Zahrah ta so darawa sai da babu dama musamman yadda wannan sarkin izza ya haɗe girar sama da ƙasa dhi ala Dole bai son raini.
Gyara murya Alhaji Baba ya yi sannan ya ce “To ni bari na yi magana tunda ita ba faɗa muku za ta yi ba...” Kafin ya ƙarasa Yaya Khalil ya katse shi da “Yauwa Tsoho Mai ran ƙarfe, Allah ya ja kwana.” Cikin ran sa ya amsa da Amin sannan ya ce “Idan ba ku mance ba akwai yarinyar mu Madina wacce ba zan ce ɗayanku ya San ta ba sabisa rasa ta da muka yi” sai ya ɗan ja numfashi ya ce “A taƙaitace dai wannan Zahrahr ɗiyarta ce, Amma ita a halin yanzu ba a San yadda ta ke ba”
Murmushi Yaya Khalil yayi yayin da Master Kuma ya dake kamar bai ji me ake magana a Kai ba Amma can ƙasan ransa ya tausayawa yarinyar ga Kuma su Hajjaty da ke tsananin kewar ɗiyarsu musamman da ta kasance tilon ya mace. Kallonsa ya Kai ga wurin da ta ke ita kuma lokacin ta sa hannu ta goge hawaye. Lokaci ɗaya tausayin yarinyar ya lulluɓe shi and he's eager to know how all these happened.
Ya na Shirin janye idanuwansa su ka haɗa ido sai Kuma kowa ya kasa janye nasa daga na ɗan'uwansa yayin da kowa ke saƙa wani abun cikin ransa. A ɓangaren Zahrah kwarjini sosai ya yi mata sai da ta gagara ɗauke idanuwanta, cikin ranta ta na ayyana irin kyan da Rabbi ya yi Masa. A nashi ɓangaren shi Kuma tsantsar tausayin yarinyar ya tsaya masa a rai and cikin idanuwanta Yana hango wasu exceptional abubuwa da bai jin ya taɓa gani tattare da wata halitta. Ko da ya dawo hankalinsa ganin kallonsa Zahrahr ma ke yi yasa ya ƙara haɗe fuskar Nan tare da zaro mata idanuwa, ai da sauri ta janye nata tana mai ƙara lafewa jikin hajjaty. Yaya Sadauki kuwa sai da ya murmusa ganin kallo ɗaya da yayi mata ya furgita ta.
Duk wannan zare idon hankalin Alhaji Baba Kansa yake lokaci ɗaya Kuma ya murmusa Tare da faɗin “Hajiya ki yi haƙuri ki sallami Sadauki don sai zarewa jikar ki ido yake saboda kin Hana ta haɗa Masa ɗa'ami” Sosai kowa ya kwashe da dariya ban da Yaya Sadauki da ya ƙara haɗe fuska jin yadda Alhaji Baba ya ke Shirin yaga shi gaban yarinya, ita kuwa Zahrah sai da ta murmusa sannan ta ɗago tana Kai dubanta ga Hajjaty, fuska shagwaɓe ta ce “Allah Hajjaty da gaske kin ga har haka yayi min” sai ta shata wuyanta da yatsa alamar yanka.
Tashin hankali Wai ba a sa Masa date, Yaya Sadauki kamar yayi Yaya saboda yadda yaji Sharrin da ta ƙulla Masa sai kuma ya murmusa cikin ransa yace “Atleast zan ci favorite bayan wani lokaci” yayin da a zahiri Kuma fuskarsa ke ɗaure ta ke sai ma Danna wayarsa da yake.
Sai a lokacin Hajjaty ta sa Zahrah ta haɗo Musu gurasar, ba Musu ta Wuce kitchen ta haɗo ta Kai dining. Ta gefen ido Yaya Sadauki yake kallonta har ta dawo ta zauna wurin zamanta ta ce “Na gama haɗawa”. “Ki kawo Mana Nan!” ya faɗa in an authoritative way Ba Musu ta koma ta kwaso ta kawo Musu Nan suka Fara ci. Ko da suka gama suka dawo ba su tarar da Zahrah a parlourn ba, hakan yasa kai tsaye suka nufi bangaren Hajiya Babba. A can suka zauna salla kawai ke fitar da su, abun mamaki kuma har zuwa lokacin Babu wani mahaluki da ya San da dawowarsu.
Bayan sallar isha suka koma part din Hajjaty kamar yadda ya saba dama wurin zaman sa ne. Zahrah da kanta tayi warming gurasar sannan ta hada ta coz a yadda ta fahimta he too much like gurasa. Fahimtar cewa a nan din zai ci yasa ta jera a dining.
Tana fitowa ta wuce bedroom dinta jin alamar kiran salla, wanka tayi kana ta dauro alwala sannan ta gabatar da sallar ishar ta.
A lokacin da su Yaya Sadauki suka shigo ita da Hajjaty na parourn, nan fa aka baje a parourn ana hira. Yaya Kalil da bai da jimurin yunwa ya kwaye baki sai hamma yake saki. Harararsa Yaya Sadauki yayi shi kuma sai ya kwashe da dariya. “Haba Man, irin wannan kallo sai ka sa Sis Zahrah ta tsorata.” Takaici kamar ya kashe Yaya Sadauki jin yana so ya kawo raini tsakanin su nan take ya tamke fuska. “Sorry Man! Ka cewa Hajjaty yunwa nake ji please” ya fada kasa-kasa. Hararar da ya balla masa wannan karon kamar idon zai cire, a daidai lokacin kuma Zahrah ta dago kanta sai aka yi rashin sa'a idonta ya sauka kansa. Kun san Zahrah da wata dabi'a tata na rashin iya kunshe dariya ai kuwa sai ta kece da dariya.
Nan da nan hankalin kowa ya dawo kanta including Yaya Sadauki wondering why is this girl laughing kamar mahaukaciya, on the other hand Yaya Kalil already ya gano kan me take dariyar coz a kan idonsa ya ga lokacin da Zahrarhr ta zaro idanuwa waje.
“Zahra'u lafiya?” Hajjaty ta tambaya. Kafin ta tsayar da dariyar har ta yi tunanin bawa Hajjaty amsa tuni Yaya Kalil ya yi caraf ya CE “Wallahi Hajjaty ita da Man ne!” AI Babu shiri Zahrah ta tsayar da dariyar tana kunshe baki sai zaro idanuwa take jin tereren bankadar da Dan'uwanta yayi Mata yayin da hanjin cikinta suka juya har cikin Na bada sautin kuuuuu. “Wallahi ba haka bane!”ta fada a kidime.
Yaya Khalil da ya dago ta sai da ya murmusa kasa-kasa don yana so shirin sa yayi aiki a kansu. Wani kallo Yaya Sadauki ya aika Mata tuni ta Kara shiga hankalin ta. Ganin yadda ta tare wuri guda yasa Alhaji Baba yin magana. “Ya dai Zahra'u? Me kike wa dariyar ne?” Cikin rawar murya ta ce “Alhaji Baba Babu komai fa kawai Na tuna da Bibalon Aunty Amarya ne lokacin da suke duka na sai nake kwatanta Ina ma a ce yanzu ne da Na koya Mata hankalin.”
Ran Yaya Sadauki ne ya baci jin yarinyar na son raina masa wayo bayan kuma Dude dinsa ya sanar da shi cewa da shi take. Fuska daure ya maida kallonsa gare ta tare da zaro kwalakwalan idanuwansa waje sai dai Bai kai GA furta komai ba Alhaji Baba ya ce “Rabu da ita Sadauki ba da kai take ba.” Wai wai wai, tashin hankali ba a sa masa date, wai yau Yaya Sadauki aka rainawa wayo a gidan nan? The whole Sadaukin Abatcha? To ai ko manyanta ba za su masa irin haka ya share ba talkless of tiny her!, he must deal with her.
Abun ka da miskilin mutum sai ya waske ya ce “Okay” daga haka ya gimtse bakinsa. Yaya Khalil dai dariya ya yi kasa-kasa yana kuma Kara jaddada wayon yarinyar cikin ransa and he feel good about her, ko ba komai yau ta harzuka Man din sa, he's always hoping for change, yana so ya koma ainihin Sadaukinsa.
A haka dai aka shashantar da zancen aka koma wani batun sai dai har lokacin zuciyar Zahrah bata daina tsalle ba GA firgicin da ya kasa barin fuskarta. Bangaren Yaya Sadauki kuma ya yi shiru ne kawai saboda baya son musu amma fa deep down his heart ya kudirikudiri aniyar saita yarinyar nan.
“Uhm jama'a ni fa hakuri Na ya riga da ya kare, tun dazu Na ji shiru, mai son Allah dai ya biyo mi dining mu ci kafin Na sume muku” Jin batun nasa sai da kowa ya dara Banda Yaya Sadauki da ransa ya yi tsananin baci ganin dai da gaske Yaya Khalil raini yake son jawo musu, fisabilillahi gaban yarinya karama! Kai this is unfair of him, tirr.
Alhaji Baba ne ya fara tashi fuska sake sai kuma sauran ma su ka Mike ban da Yaya Sadauki da ya hade girar sama da kasa alamar ma ba ya son wargi. Bayan sun zauna Zahrah ta yi serving kowa sannan ta zuba ma kanta, har ta kai spoon din farko bakinta ta tuna da shi, sai ta tsinci kanta da karewa dining din kallo, ganin ba ya nan yasa ta ji wani iri. Hakan Sam bai Mata dadi ba sai take ganin kamar laifin ta ne, ba ta ci wani mai yawa ba ta Mike tare da nufar flask din da ta hada gurasar tare da daukar ta, ta juya zata nufi kitchen Hajjaty ta dakatar da ita da fadin “Ina za ki je ne Zahra'u?” Wuri-wuri ta yi da ido tayi kana ta sunkuyar da kai sai shafa flask din take da hannunta. Ganin ba ta da abun fadi yasa Hajjaty ta ce “Maza dawo ki zauna Ina gani ba ki ci Na kirki ba.” “A'a Hajjaty ki bar ta, hala kunya ta take ji, in Na tashi probably ta dawp ta ci” cikin ransa yana addu'ar Allah yasa dai kar su Hajjaty su ce a'a coz ya riga ya dago jirginta don dama can Yaya Khalil ba dai sa ido ba. Wani sanyi ne ya ratsa zuciyar Zahrah ta San ko ba komai Yaya Khalil ya cece ta har tana tunanin tsaftace aika-aikar da ta yi.
Jin Hajjaty ba ta ce komai ba ya sa Yaya Khalil murmusawa sannan ya mayar da duban sa ga Zahrah wacce har lokacin kanta ke kasa yace “Je abun ki sister, anjima zan tashi sai ki dawo ki ci tunda kunya ta kike ji.”
Jikinta har rawa yake ta nufi kitchen, tana shiga ta sauke ajiyar zuciya a bayyans ta furta “Allah na gode maka da ka tseratar da ni.”
Basket ta dauka ta hada komai da zai bukata a ciki kana ta ajiye sai ta fice ta backdoor ta zagayo zuwa parlourn dauke da sallama a bakinta yayin da ya amsa kasan makoshin sa ba tare da ya kalli inda sallamar ta fito ba sai ma maida hankalinsa da ya yi kan phone dinsa da yake latsawa.
Jikinta sanyaye ta karasa cikin can kasan ranta kuma tana addu'ar Allah ya bata nasarar wanke laifin ta, sai a lokacin ita ma take nadamar abun da ta yi, deep down her heart she's apologizing and hoping that her apology will be put in to consideration.
*Mommah's Pov*
Gabadaya Mommah ta fara zabgewa saboda damuwar rashin nagartaccen danta tana Kara tabbatar da zancen su da Hajiya Baraka da kuma Hajiya Saudatu. Babu shakka Hajiya Babba tana cutar da su amma Babu komai zata San matakin dauka.
“Amma batun shawarar Hajiya Baraka fa?” Lokaci guda tayi na'am tare da gyara zamanta kan sofa, amma kuma sai ta tuna da dabi'un Kausar din nan take ta jijjiga kai, ba zata yi wa danta fatan samun mace irin sa ba, amma dai zata yi mai yiwuwa ta ga ya auri wata ko da kuwa a wajen Ahalin ne.
*Na rage tsayin update yau saboda Na tabbatarwa kai Na cewa kuma tare da ni, hakan zai faru ne idan Na GA reactions din kuitanen kirki. ILYSM* _Be with my pen to know what will happen next, shin plan din Kawayen Mommah zai yi aiki?, me zai faru tsakanim Zahrah da Yaya Sadauki? Idan kun yi reacting sosai da safe zan yi update._
[12/25, 11:36 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©️Diamond Bhatool*
https://www.facebook.com/profile.php?id=61570606515077
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 1️⃣1️⃣
_Not edited_
﷽
Shi fa har ga Allah bai ma San da zamanta ba sai da ta ɗan bige ƙafarsa garin zuba gurasar a plate tukun ya San da mutum kusa da shi, a hankali ya mayar da dubansa ga wurin da ƙafarsa take, mamaki fal cikin ransa ganin mutum, mutum ɗin ma yarinyar da ta gama raina sa, a fuska ɗaure ya kalleta sai dai ita ba ta san da hakan ba sakamakon yadda ta maida hankalin ta ga zoɓon da take zuba masa.
Tashin hankali Wai ba a sa masa date! Zahrah ba mugun ƙoƙari ta yi ba, bayan ta kammala sai ta ja gefe tare da tsugunnawa gabansa sai Kuma ta kama kunnuwanta biyu.
“I'm sorry Yaya, ka yafe min, I don't meant to hurt you, please ka Yi haƙuri ba zan maimaita ba.” Ko ɗagowa yayi ya kalle ta bata samu ba talkless of ta sa ran zai amsa, hakan ya sa guiwarta yin sanyi.
“Yaya ga gurasar I prepare it to you myself, don Allah ka ci kada ka kwana da yunwa, I won't forgive myself if you didn't eat, don Allah Yaya.....”
Hannu ya ɗaga mata alamar ya isa sannan ya nuna mata ƙofa da hannunsa. “Out of my sight!” Ai da sauri har tana harɗewa ta bar parlourn sai bedroom ɗinta. Duk Wannan ban haƙuri da take bashi yana jinta, and temper da ya hau ya sauƙo musamman yadda ta iya lanƙwasa harshe ta bashi haƙuri. Shi a da yana da wani stereotype game da mata that Suna da girman Kai but karo na farko kenan da yayi proving kan shi wrong.
Abun da ya fu burge shi da yarinyar bai Wuce yadda yadda nuna concern ɗinta kansa ba, he really appreciated it Amma cikin ransa fa, ganin tunanin babu yadda zai Kai shi yasa ya ja tsaki tare da furta Bismillah sannan ya fara cin gurasar yana lumshe idanuwa, cikin ransa ya furta “This sister is unique”
Bai Kai ga kammala ci ba yaji muryar su Hajjaty, idanuwa ya zaro sai Kuma ya gyara Zama ya ci gaba da cin gurasar sa hankali kwance. Ko da suka dawo babu Wanda yayi wa ɗan'uwansa magana sai Yaya Khalil da ɗan banza tsokalarsa ya ce “Man wa ya kawo maka gurasa kuma?” Ya ƙarasa yana ƙura Masa ido, gogan naka bai ce komai ba ya ci gaba da Kora zoɓo abun sa. Sauran jama'a babu wadda yace uffan game da hakan.
Alhaji Baba ne ya miƙe don ya Wuce ɗakinsa ya kwanta, Sallama ya Musu sannan ya nufi bedroom ɗinsa, Nan Yaya Sadauki ya bi bayansa ya rage iya Hajjaty ce Sai Yaya Khalil. Hajjaty ta kalli Yaya Khalil ɗin tace “Ni Halilu wa ya kawowa Sadauki abinci Nan?”
“Ina ga Zahrah ce fa”
“Zahrah kuma?”
“E Hajjaty, ni fa akwai abun da nake hasasowa and Ina fatan ya tabbata, you people will be Happy with it.”
“To Allah ya tabbatar da alkhairi.”
“Amin” ya and.
A ɓangaren Yaya Sadauki da Kansa ya kaɗewa Alhaji Baba shimfiɗa kana ya taimaka Masa ya zauna bakin gadon Shi kuma ya Nemi waje ya zauna kan carpet din dake shimfiɗe a bedroom ɗin. Ganin hakan yasa Alhahi Baba fahimtar cewa da abun da yake so.
“Ya dai Sadaukin Abatcha? Akwai damuwa ne?” “A'ah Alhaji Baba, it's all about that case.” ya faɗa cikin ƙunar rai.
“I believe in you Sadauki, bayan tafiyar ka na Yi bincike and it's found that akwai wadda ya haɗa wannan Abu, a matsayinka na jami'in tsaro da bincike ina roƙon ka da ka faɗaɗa binciken don na ƙosa da ire-iren abubuwan nan.”
Tun da Alhaji Baba ya fara bayani zuciyar Yaya Sadauki tayi sanyi ƙalau, tsoro da fargaban da yake ji all disappeared. Cikin ransa yana faɗin “It's now the game will be started.” Murmushi ya yi yana faɗin “Alhamdulillah, na ji daɗin bayyanar gaskiya, Allah ya tsare gaba.” “Sai dai Sadauki akwai wani hukunci da na yanke game da hakan, Dole za ka auri Mabruka in ba Haka ba ba zamu taɓa gano miyagun cikin familyn nan ba.”
“What? Alhaji Baba aure fa ka ce?”
“Eh Sadauki, aure dai na ce, auren Mabruka dai ƴar'uwarka, ko da Haka ba ta faru tsananin ku ba a tunani na in nace ka aure ta zaka yi babu jayayya but now da aka kawo wannan batun ko cikin family none of your brothers will marry her get my point Sadauki. Yanzu ba mu da wani evidence da za mu wanke ta da Kai kanka idon mutane, but I'm hoping that we'll get one soon.” ya ƙarasa a raunane.
His heart is beating faster to extent that yana ji kamar zata fasa chest ɗinsa ne ta for. He's speechless and soft, ko da was baya jin cewa zai iya ƙetare umarnin Alhaji Baba ba coz he's his everything, he's more than a Granny but someone qualified to be called a Father.
Abu na gaba kuma shi ne matsawar ya amince da wannan haɗin zai cutar da rayuwarsa da Kuma ta baiwar Allahr da Bata ji ba Bata gani ba, sannan shi a tsarin rayuwarsa ma babu saki bare ya ce in gaskiya ta bayyana zai sallame ta, hakan zai Zama babban cin fuska ga Hajiya Babba wacce ta ɗauke sa tamkar ɗanta Khalil.
Nooo ba zai ƙi amincewa da umarnin Alhaji Baba ba ko Dan samarwa Mabruka ƴancin ta Amma ya ɗau alwashi in ya binciko ko uban waye ke da sa hannu sai ya ɗanɗani kwatankwacin ɗacin da ya ji.
“Ka Yi shiru Sadauki, ya ka gani?”
Da ƙyar ya furta “Babu komai Allah yasa hakan shi ne mafi alkairi”
Murmushinsa irin na manyan mutane yayi sannan ya ce “Allah yayi maka albarka Sadauki, Allah ya baka iyalan da za su Yi maka biyayya kamar yadda kake Yi Mana.”
Can ƙasan maƙoshi ya amsa da “Amin”
Shiru ɗakin kamar babu kowa tsawon wasu daƙiƙu, cike da ƙarfin Hali tare da son ɓoye damuwarsa ya ce “Alhaji about that girl ...ehm your granddaughter.” daga haka yayi shiru. Alhaji Baba yayi murmushi sannan yayi gyaran murya.
“Tun dawowar ta nake famar nemanka ba na samunka and it's about her issue....dama Ina son ka taimaka min ne after telling you how it happened.” Nan ya bashi full labarin Madina tun tana a tare da su zuwa ɓacewarta.
Ransa ɓace ya ce
“Why Alhaji? Why ba za a ɗau mataki kan wannan mugun mutumin da ya cutar da Momy Madina ba? Wallahi sai ya San ya taɓo jinin Abatcha. Wallahi ba Dan ƙyale shi ba Kuma sai ya fito da ita ko ma Ina ya Kai ta!.”
“Halinku ɗaya da Mahaifinka, zafin nama da ɗaukar zafi, wannan ba maslaha bace, mu fara Nemo ta kafin mu koma Kansa.”
Wata zazzafar iska ya fesar.
“Ka je kun gaisa da mutanen gidan ne?”
Kamar ya tsala ihu ya ce “Sai da safe tukun” Nan fa Alhaji Baba ya fara mass faɗa Wai meyasa ba zai shiga ya gaida Mahaifiyarsa ba ko da ba zai duba kowa ba?
“Bana son irin Haka Sadauki, ba irin rainon da Rukayya tayi maka ba, yanzu ba sai gobe ba ka tabbatar ka shiga wurin Sughrah ka Kuma Bata haƙuri ka ji ko?”
Kai ya gyaɗa kamar zai Yi kuka ya ce “To”
“Mu kwana Lafiya ni zan kwanta.” “Allah ya Bamu alkairi”
Daga Haka ya fice zuciyarsa na ƙuna. Ba tare da ya je ɓangaren Mommah ba ya Wuce bedroom ɗinsa da ke part ɗin Hajiya Babba, ba Wai ya ƙi bin umarnin Alhaji Baba ba ne, sai dai baya son a Yi ba daidai ba musamman da yake sama, ya Kuma riga ya San halin birkitacciyar Mahaifiyarsa shiyasa kawai ya zaɓi ya huta Idan ya so da safe ya shiga.
Yana shiga yayi wanka sannan ya ɗauro alwala don yin shafa'i da witri kamar yadda yadda Saba coz yana jin yau ba lallai ya iya tashi don ya riga ya faka damuwar jama'a a gefe, in ya tashi daga baccin ya saɓa ko ya ɗuura ta a baya.
*Zahrah's POV*
Da sauri ta bar parlourn sai Kuma bedroom ɗinta. Kan bed ta faɗa tana maida numfashi
“Ya Allah! Allah dai yasa ya ci abincin kada ya kwana da yunwa.” she said so openly sai Kuma ta yamutsa fuska “To Ina ruwa na da shi in ya ci in bai ci ba?” “Kin manta kin ce Zaki taimaka wurin dawo da rayuwarsa daidai, it's part of your job.” “Yea Haka ne! Amma meyasa nake jin sa mutum na musamman a rayuwata?” “Saboda shi ɗin ɗan'uwanki ne.”
Kamar mahaukaciya Haka take ta surutu ita ɗaya. Kamar an ce ta nutsu sai ta tura bankinta gaba tare da cakumo blanket ɗin dake shimfiɗe kan bed ɗin saying “Ke Zahrah relax! Relax! Relax please.”
Lokaci ɗaya ta kwashe da dariya “Wallahi yau na Zama mahaukaciyar gaske, please lemme control myself!” Sai Kuma ta Fara juyi kan bed ɗin. Tunawa da Bata Yi salla ba yasa ta diro da sauri ta nufi toilet, sai da tayi wanka tukun ta ɗauro alwala, bayan ta yi salla ta haye bed don ta fara tsara ta Ina zata Fara. Ganin kamar an toshe brain ɗinta yasa ta yanke shawarar gobe sa zanta da Nasreen kawai. A Haka dai har bacci ya ɗauke ta.
*Devil Klans’ POV, 1:13 Midnight, in an unknown dark area full of long canopies and trees.*
Guguwa ce Mai ƙarfin gaske ta tashi kamar duniyar zata kife lokaci ɗaya Kuma ta ɗauke yayin da wani irin duhu ya mamaye farfajiyar wajen tsawon wani lokaci Kuma sai ga Haske yana bayyana kaɗan kaɗan har ya gama mamaye wurin.
Halittun Nan na kwanakin baya da za su Kai goma Sha biyar suka bayyana shugabansu kuma na zaune ƙafarsa ɗaya kan ɗaya. A yau dai Kam na gama tabbatarwa da Kai na waɗannam matsafa ne ko Kuma cultists waɗanda ke amfani da jinin mutane da wasu dabbobin Suna shayar da baƙaƙen shaiɗanu don Samar ma kanunsu da wani ƙarfin iko na sihiri, ɗaukaka ko Kuma dukiya.
A yau ma kamar ibada sai da suka gabatar da karatun dalasimansu da suke cewa addu'a kafin su Fara tattaunawa kan abun da ya Tara su.
“Kamar yadda na sanar da ku a taron mu da ya gabata, waɗannan Haske fa sun haɗe da juna Kuma Suna gab da Fara kawo Mana farmaki, yanzu lokacin aiki ya yi, kowa ya shirya don ba zamu bar kowanne mahaluki ba da zai kawo Mana cikas cikin tafiyar Devil Klans ba, babuai dakatar da mu har sai mun gama cimma ƙudirorin mu a doron ƙasa, har Sai mun tabbatar mun mulki duniya gabaɗaya tare da yin arziƙi na ban mamaki.” Uwargijiya ta faɗa tana sauƙe numfashi kafin ta ci gaba.
“Saboda Haka nake roƙon kowanne a cikin ku yayi sadaukarwa ga dodon tsafi ta yadda ƙarfin mu zai ƙaru fiye da na da har ta Kai kowa na fargaban tunkarar mu. Zamu mulki duniya gabaɗaya tare da yaƙar duk wani maƙiyi.”
Ihu sauran su ke Suna faɗin wasu maganganu da babu su cikin harshen hausa Idan Kuma har akwai to zan iya danganta hakan da yaren tsafi ne.
“Dole kowa ya sadaukar da jinin makusancinsa domin dodon tsafi ya fi buƙatar irin waɗannam jini, sannan kowannen mu zai Yi sadaukarwccar baƙaƙen karnuka da aladai da Kuma jakkai, zai haɗa da ɓaƙaƙen kuliyu da jarirai da kuma samari goma-goma each.”
“Sai mun Yi! Sai mun Yi!!” They said it in a chorus.
“Abu na gaba kuma shine kowa yayi kaffa-kaffa da na kusa da shi, ku Kula da sirrin warakarku don matuƙar wani ya gano shikenan taɓarɓarewa zata tabbata gare ka, zaka rasa ikon ku Kuma ku rasa nutsuwa cikin gamagarin mutane, hakan Kuma Jan iya jawo rauni ga Devil Klans Wanda ni ba zan jura ba, ku Yi yaka tsantsan don duk Wanda ya bari sirrinsa ya bayyana bayan rasa ikonsa za mu yi sadaukarwa ne da shi ga dodon tsafi.”
“Yea! Yea! Yea!!!”
“Jimjina ga Gutsirito Mai iko, kowa ya kiyaye ya Kuma Yi taka tsantsan. let's disappear!”
Kamar ƙiftawar ido suka ɓace wurin Kuma ya koma wani fili kamar dai football field ne ma.
_To jama'a yanzu mun fara wasan, yanzu ne ya Kamata ku kasance da ni don jin ya zata Kaya. Reactions da comments kawai nake buƙata daga gareku, thank you 🦋_ _I'm sorry for not updating my esteem fans matsalar caji ya sa hakan, Amma ga wannan a karanta._
*Don Allah a Yi reacting sannan a taya no sharing, wannan ita ce ƙaunar da zaku nuna min, Diamond Bhatool taku ce.*
[12/26, 9:59 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 1️⃣2️⃣
_Not edited_
﷽
*Sadauki's POV*
Ya so ya Samu isasshen bacci Amma hakan ya gagara sakamakon tarin damuwoyin da suka addabi zuciyarsa waɗanda with time yake hasashen matuƙar ba su bar shi ba ba lallai ya iya ci gaba da ɗaukar su ba. Wannan ma is part of his triumph and courage. Ganin baccin ba zuwa zai yi ba yasa ya miƙe tare da ɗauro alwala, Haka dai Daren Nan ya ƙare yana Kai kukansa ga Allah. Fatan sa Allah ya bashi ikon ɗaukar komai da ya jarabce shi da shi.
Safiyar ranar bai samu zuwa breakfast part ɗin Hajjaty ba saboda baccin da ya ɗauke shi bayan ya dawo daga masjid.
Cikin baccin sa ya fara jin hayaniya sama-sama. Juyi kawai yayi ya ci gaba da baccinsa. Can kuma ya ji hayaniyar na ƙara ƙamari hakan ya sa ya buɗe idanuwansa yana mai karanta addu'ar tashi daga bacci. Tsaki ya ja tare da ziraro ƙafafunsa ƙasa sannan ya nufi toilet, wanka ya yi sannan ya shirya cikin wasu light Armani brand masu taushi sannan ya fesa turaren sa mai mugun daɗi.
Tsaki ya ƙara ja a karo na biyu don har ga Allah hayaniyar nan ta ishe shi, fuska ɗaure ya fito yana mai taka staircase ɗin a hankali. Sai da ya kusa sauƙowa ya hango fuskokin da yake gani as useless. “Ko me ya kawo su nan?” ya tambayi kansa.
Yana ƙarasa sauƙowa Mommah ta cillawa Hajiya Babba Harara tare da faɗin “Kuma ina dawowa.”
Da sauri ta nufi inda yake tsaye yana kallonsu cike da takaici while cikin ransa yana tunanin sai zuwa yaushe mutanen gidan nan zasu yi hankali ne. Bai ji zuwan ta ba sai da tayi hugging ɗin sa, cikin wata raunananniyar murya take faɗin
“Haba son! Sai zuwa yaushe ne za ka bar zuciya ta ta zauna cikin salama? Ka kwashe ka tafi and ka dawo ma sai dai naji a bakin jama'a? Haba son, ka rasa ma ina zaka tare sai nan, ɓangaren matar da ke shirin raba Ni da kai? Why son?”
Yes, ya san at times bai kyauta mata amma ita ma da gudunmawarta ga hakan ai, yanzu irin wannan zubda girman da tazo ta yi a nan ai bai dace ba, ta gefen ido ya kalle su fuskar su sake suna riƙe da ƙugu tuni ya ji ransa ya ƙara ɓaci hatta Mommahn ma haushin ta yake ji na mu'amala da wadannan mutanen da sam basu son zaman lafiya a rayuwarsu.
Jin ya yi nata mata shiru yasa ta ɗan ƙara kwantar da murya tare da sakin sa “Mu je my son” Har cikin ransa ya tausaya mata amma yayi alƙawarin dole ta fahimci kuskuren ta ta rabu da mutanen nan da take wa kallon masoya.
Dubansa ya kai ga Hajiya Babba wacce bata ce komai ba duk abunda ke faruwa sai ma karatunta da ta cigaba da yi. Bai ji daɗin abun da Mommah ta yi mata ba amma ya ji daɗin ganin yadda Hajiya Babban ta share su.
“Ka yi shiru son, mu je ko?”
“I'm going no where Mommah, sai zuwa yaushe ne zaki gane mutanen da ke tare da ke kai ji suke su baro ki?, Ahbeg Mommah, ki ja mutanen ki ku koma zan zo yanzu.” ya faɗa cikin ƙunar rai.
“Kin ji ko? Kin ji shi ko Rukayya? Na rantse da Allah ki sake min yaro na ya isa haka!” Ta faɗa a fusace tana nuna Hajiya Babba da yatsa.
Abun nema ya samu, Ammie da Mami suka matso kusa da ita duk da cewa suna shakkar dizgawar Yaya Sadaukin.
“Ai tun ba yau ba nake faɗa miki Hajiya Sughrah, Rukayya ta riga ta mallake miki ɗa, ba iya shi ba kusan duka gidan ta mallaki kowa. Gaskiya dole ki tashi tsaye.”
Yaya Sadauki da ransa ke ɓace bai san lokacin da ya kalli Mami ba ya Wulla mata wani kallo da yasa ta shiga taitayin ta.
“Matar da kuke zagi duk ta girme ku amma gashi ta banzatar da ku, hakan kaɗai ya isa ya tabbatar muku da cewa ita ɗin ba tsararku ba ce, Mommah!”
Ya faɗa yana riƙe hannunta “It's now time da ya kamata a ce kin gane masoyanki, na roƙe ki da Allah ki ja mutanen nan ku tafi zan zo na faɗa miki.”
“Ai gashi nan, kin ji me yake faɗi ko Hajiya Sughrah, to gaskiya dai Allah ya sa ka gane hanya, ina ga dai....”
“Gaskiyar ki Hajiya Saudatu, wallahi burin ta bai wuce ta samu tsohon can ya hana auren ɗan nan da ƴar ta Mabruka ba ganin ta yi kwantai kuma.....”
“Ya isa haka Baraka!”
A zabure suka juyo ganin Alhaji Baba ne da kansa kuma fuskarsa babu alamun sauƙi, nan kowacce ta shiga taitayinta suka sunkuyar da kanunsu ƙasa kamar wasu munafukai.
“Kun gama? Nace kun gama?”
“Haba Alhaji ya za a yi a daki mutum a hana shi kuka? Fisabilillah komai Hajiya Babba tayi cikin gidan nan bata da laifi?” Hajiya Saudatu ta faɗa tana riƙe kunkumi kamar wata yarinya.
“Ban ce ki yi magana ba, Rukayya Allah yayi miki albarka, ki ci gaba da haƙuri da su har lokacin da za su yi hankali.”
Murmushi Hajiya Babba tayi wanda ake cewa ya fi kuka ciwo sannan ta amsa da Amin ba tare da ƙara cewa komai ba.
Alhaji Baba ne ya fuskance su sannan yayi murmushin takaici “Kai Sadauki wuce ɗakin ka, ke kuma Bāraka ba wasa da gaske kuwa sadauki zai auri Mabruka sai dai ki mutu, me ma ya kawo ku nan..?”
Taran numfashinsa Mommah tayi kamar zata haɗiyi zuciya saboda baƙin ciki. “Don Allah Alhaji Baba kada ka yi haka, wallahi sharri aka yi wa yaron nan ka san ba mutumin banza bane, ka taimaka kada ka masa auren dole, ga nan Kausar ta wajen Hajiya Baraka ina laifin a yi haɗin da ita?”
“Ba shawarar ki nake nema ba Sughrah, auren Sadauki da Mabruka babu fashi sai dai in bana numfashi. Ku kiyaye shiga sabgar Rukayya wallahi, duk ranar da na kuma ganin ku ɓangaren ta kun zo yi mata cin fuska wallahi sai na sa mazajen ku sun mayar da ku zawarawa tunda ku baku san mutunci ba.” Daga haka Alhaji Baba ya nuna musu kofa da hannunsa. Simi-simi kamar munafukai suka fice zuwa ɓangarensu, Alhaji Baba ya ƙara bawa Hajiya Babba haƙuri kana ya wuce abun sa.
A ɓangaren su Mommah ko da suka fita ɓangarenta suka wuce, nan suka fara zage-zage a kan rashin adalcin da ake yi musu a gidan (amma fa a nasu ganin.) Nan suka ƙara zuga Mommah kan kada ta yadda a mata fin ƙarfi a kan ɗanta ko da kuwa hakan zai yi sanadiyyar barin ta gidan. Wannan shi ne abun ta hau kuma ta Zauna.
*Yaya Sadauki's POV*
Ko da ya shiga Bedroom ɗinsa ji yayi kamar ya sanya kuka saboda yadda abubuwan ke shirin dagula masa lissafi. Abun da ya faru ya sa ya ji ya ƙara aminta da auren Mabruka musamman da ya tuna irin tarbiyyar da Hajiya Babba ke bawa ƴaƴanta har da na mutane, shi kansa abubuwan da ya koya masu kyau daga gare ta Allah ya yi yawa da su.
Jin shiru yasa ya fito jiki sanyaye, har lokacin kuma Hajiya Babba na zaune yana karatunta. Jiki mace ya tsugunna ya ma rasa me zai ce mata. In a cool voice ya ce “I'm so sorry Hajiya, I don't mean it to happen, ban ji daɗin abubuwan da Mommah tayi miki ba, kullum ina ƙara nuna mata hanya amma ta kasa fahimta, don Allah ki yi haƙuri, sannan kada ki biye maganar Ammie da Mami ki ce zaki hana aure na da Mabruka, Allah meant it to happen, kada ki hana don Allah.”
Murmushin su na manya tayi kana ta shafi fuskarsa tace “Kada ka damu son, ban isa na ja da hukuncin Alhaji Baba ba, sannan batun Sughrah ban taɓa ɗaukarsa da muhimmanci ba saboda na san ba yin kanta ba ne, fata na ka taya ta da addu'a Allah yasa ta gane da wuri.”
Dattaku irin na Hajiya Babba kullum ƙara burge shi yake, murmushi yayi sannan ya ce “Bari na je na duba ta, addu'a In Sha Allah muna kan taya ta.” Daga haka ya wuce yana ƙara godewa Allah da ya sa abun da ya faru babu wani yaro duk suna school, Mabruka kuwa yana kyautata zaton ta wuce court abunta.
Abun da ya tarar a can ai ya dama wadda ya gabata, duk irin huɗubar da suke wa Mommah cikin kunnensa ne, duk shaiɗancin su bai taɓa zaton za su yi mata irin wannan huɗubar ba duba da yadda suke nuna cewa suna tare da ita, ya za a yi su ɗaura ta kan ta kashe aurenta akan abunda ta san ba Mai sauyuwa bane?.
Makewa yayi ya wuce tare da gyara murya, tuni suka miƙe suna yi wa Mommah sallama, shi dai da kallo ya bi su yana musu addu'ar shiriya cikin ransa kuma yana ayyana barin Mommah ta yanke ne ya dace da ita, In ta zaɓi kashe aurenta fine, zata koyi darasi ne ai.
Rungume shi tayi tana kuka kamar wata yarinya “Son kana ganin irin cin mutuncin da aka min gaban idon ka ko? Ko tausayi na ma baka yi ko?” Hankalinsa ne ya tashi don baya son kuka musamman na ɗiya mace, macen ma wacce tayi silar zuwan sa duniya. Sanyaya murya yayi kana ya ƙara hugging nata tightly, he so much love her, yana son mahaifiyarsa ko yaya take, amma kuma ɗabi'unta kawai yake so ta gyara.
“Ba haka bane Mommah, ina jin zafin abun da ke faruwa indeed na ma Fi ki jin zafi amma ke har yau kin kasa fahimtar cewa masu zuga ki kina aikata ire-iren abubuwan nan wallahi ba son ki suke ba illa iyaka son su ga mutuncin ki ya zube.”
Ba tare da ta yadda ba sai dai kawai tana tsoron wannan damar ta kuɓuce mata yasa ta ce “Is alright sit down let's talk.” ba musu ya zauna gefenta kamar yadda ta umarce shi. “Na ji wata magana da Alhaji Baba yayi ɗazu amma ina so ka tabbatar min ba haka bane”
Tsaf ya fahimci a kan me take magana amma sai ya kame ya ce “Me kenan Mommah?”
“He Said that zai haɗa auren ka da yarinyar nan da tayi kwantai har take bin maza don na tabbata abun da ya faru ma shirin ta ne” Kamar zai yi kuka yake kallon Mommah. Tabbas wanda yayi nisa ba ya jin kira amma sai ya kame ya ce
“Yea haka ne Mommah, akwai matsala ne?”
“Tambaya ta ma kake akwt matsala Haidar?” ta faɗa a ɗan zafafe.
Ba tare da ya ce komai ba ya riƙo hannunta ya haɗa da nasa.
“Mommah Please understand, ba Wai Alhaji Baba ne ke da laifi ba, hakan da yayi adalci ne, ki ƙiyasta a ce Nainarh ce haka ta faru da ita kuma kawai sharri aka mata, kina tunanin zata samu wadda zai aure ta ne? No Mommah kada ki ce zaki ja da wannan hukunci, Ni na riga nayi accepting ma kawai kema ki share, and Zan faɗa miki wani abu da baki sani ba wallahi Mommah mutanen da ke ɗaura ki hanya ba mutanen kirki bane, kuma ki sani abinda ya faru ma suna daga cikin waɗanda suka shirya shi, ki yi tunani a kai.”
Cikin rasa Madafa ta ƙara duban yaya Sadauki sannan tace “Ba wai bana son ka yi auren nan bane, yarinyar da aka Baka ne, ɗiyar Hajiya Babba fa, matar da ke ƙwace duk wani abu da zan mallaka, kai kanka ƙoƙarin raba Ni take da kai son, Ina ga in ka auri ɗiyar ta, get something here son, in ma zaka yi auren ka auri ɗiyar masu ƙauna ta mana, ga ƴaƴan Hajiya Baraka da Saudatu amma sai ƴaƴan Hajiya Babba?”
“Mommah, ki fahimci wani abu, Hajiya Babba ba ta nufin ki da sharri ke ce ba ki fahimce ta ba saboda huɗubar da ake miki, Mommah don Allah ki gane gaskiya ki gane masu son ki tun kafin ki yi nadama lokacin da babu amfani.”
Ita fa duk iri wahalar da ta bashi na yin doguwar magana bata gamsu ba da saboda ta riga da ta yi nisa. Cikin ransa yake mata addu'ar Allah ya sa ta fahimci gaskiya.
Daga haka ya miƙe yace bari ya je ya bawa Alhaji Baba haƙuri, Bata Hana shi ba duk da bata so hakan ba, sai ta amsa da to amma ya dawo Please za ta gyara masa Bedroom ɗinsa. Shi har mamaki yau ta bashi, wai yau shi ne yake samun irin wannan kulawar daga Mommah? Lallai ta yi laushi kam.
Shi kam murmushi yayi sannan ya nufi kofa zuwa ɓangaren Hajjaty ya bar ta parlourn tana saƙawa da warwarewa.
_Mu haɗu gobe don jin yadda zata kaya, yanzu muka fara wasan fata na dai zaku bani haɗin kai mu kammala tare da ku ta hanyar reacting, commenting da Kuma sharing. Na gode_
*Comment, react and share fisabilillah*
[12/27, 8:06 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 1️⃣3️⃣
_Not edited_
﷽
Hajjaty ce sai Zahrah a parlourn, Alhaji Baba Kuwa yana can Bedroom ɗinsa tun da ya baro part din Hajiya Babba ya dawo bai ƙara leƙowa. Saƙawa da warwarewa kawai yake game da family crisis da ke samu.
“Assalamu alaikum” Zahrah ta amsa masa tare da sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da ƴaƴan yatsunta. Lura da yadda ta suƙure da shigowarsa sai yaji babu daɗi amma hakan bai sa ya saki ransa ba sai ma ƙara haɗesa da yayi.
Ita ta fara gaishe shi kanta ƙasa, bata ma yi tunanin zai amsa mata da ta tuna da korarta da jiya yayi. Jin ya amsa yasa ta ɗan turo baki wanda caraf a kan idon sa ne, bai ce uffan ba ya zauna gefenta Hajjaty sannan suka gaisa.
“Ai na ɗauka ka tafi yawon naka da naga shiru baka zo ka yi breakfast ba.”
Harara ya bankawa Zahrah ai ba shiri ta miƙe, cikin ransa yace “Wannan da ganinta zata yi rashin kunya sai dai kuma tana da shegen tsoro da alama”. Ganin ta bar wajen yasa yace “Ina nan, ban samu bacci bane jiya shi yasa ban fito da wuri ba.”
“Ayya, baka karya ba ma kenan?”
“Uhm”
“Bari Zahrah tazo ta haɗa naka wani abu Mai sauƙi...” bata kai ga kiran Zahrahn ba ya yamutsa fuska yana faɗin “Haba Hajjaty yarinyar nan ne za ta min girki ai sai dai jagwalgwale, ki bar shi na ci lunch kawai.”
Baki riƙe Hajjaty ta ce “Sannu Sadauki, to bari ka ji, girki jiya zan iya cewa ita tayi tunda gurasar ka ma ita tayi ta haɗa maka, Zahrah! Zahrah”
“Na'am, ga Ni nan zuwa. Ga Ni Hajjaty”
“Zaki ɗan haɗawa Yayanku abun karyawa ne mai ɗan sauƙi”
“Tooo Yaya me za a yi?”
“Something simple” ya faɗa a saman laɓɓansa. Nan Zahrah ta wuce kitchen don Samar Masa breakfast shi kuma ta bar shi suna ɗan taɓa hira da Hajjaty wacce duk rabin hirar nasiha da jan hankali take masa.
Within 10minutes Zahrah ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da good flask da kuma thermoflask, tana gama ajiye masa a dining table dawo parlourn looking at his innocent face tace “I'm done yaya.”
Shiru can kuma ba tare da ya ɗago ya kalle ta ba yace “You wait for me there ko Ni zan yi serving Kai na?”
Kai ta jijjiga sannan ta koma dining area Tana jiran zuwansa. Ya share kusan 3minutes kafin ya zo ya zauna. Serving nasa fried potatoes with egg tayi sannan ta fara ƙokarin zuba bread ɗin da ta soya da ƙwai cikin wani bowl. Hannu ya ɗaga mata hakan yasa ta tsaya tana jiran umarni.
“Have You taken yours?” ba ƙaramin mamaki taji ba jin tambayarsa amma sai tayi ƙoƙarin ɓoye hakan ta girgiza kai.
“Oya serve yourself now!”
Babu yadda ta iya ta zuba nata sai dai ta kasa ci saboda kunyarsa da kuma nauyinsa da take ji but can ɓangarensa hankali kwance ya ci abun sa yana korawa da shayin da ta haɗa masa.
Bayan ya gama ya goge bakinsa da tissue sannan ya ɗan kai dubansa ga ɓangaren da take. Ganin ba a sake take ba yasa ya murmusa kana yace
“Why Are You not eating?, Ain't you hungry?”
“Ina....Ina ci fa Yaya.” ta faɗa a rarrabe. Wani iri yake ji idan ta ƙira shi da Yaya, ji yake kamar yadda take faɗa ba kamar yadda sauran family members ɗin ke faɗi ba ne.
“Alright, ajiye zamu yi magana In na tashi sai ki ƙarasa.”
Ƙirjin ta ne ya bada sautin dimm jin maganar sa. Da sauri ta ture bowl ɗin gefe kana ta sauƙar da kanta ƙasa tana wasa da hannunta, hakan kuma ya zama mata ɗabi'a matsawar zata magantu da wani babba.
“Me yasa jiya kika min dariya?”
Shiru tayi tana zaro idanuwanta.
“Bana so ina ina magana ana shiru musamman magana mai muhimmanci.”
Cikin sanyin murya tace
“A'a ba da kai nake ba Yaya, Ina tuna Bibalo ne fa...”
Hannu ya ɗaga mata yace “Ba na magana sau biyu, kuma ba na maimaita tambaya, just tell me the truth.” Tsoro ne ya ɗarsu cikin ranta ai kuwa sai taji kawai faɗan gaskiyar ne alkairi.
“Dama Yaya...dama zare idonka kayi kana hararar Yaya Khalil shine fa.”
“Dama kallo na kike kenan?” Tambayarsa tazo mata a ba zata. Cikin in'ina tace “A'a e a'a dama iya lokacin ne na ɗago.”
Fuska kame yace “Is alright kada ki ƙara, bana son ina waje ma ake yin dariya, Thank God kin bani haƙuri jiya wallahi I'll have smash you into pieces.”
“Kayi haƙuri Yaya, ba Zan ƙara ba.”
“Is alright, Deal?” Kai ta gyaɗa Masa
“In ina magana ba a amsa min da kai, ko ke kurmiya ce?”
“A'a, na yi”
“in kin ƙara na miki me?”
“Punish me.”
“Ok, now about the issue of your Mom. Ina so ki faɗa min yadda komai ya faru.”
Hawayen da suka fara wanke mata fuska ta share, ta buɗe baki zata yi magana ya dakatar da ita “Na duka ki ne?” da kai ta bashi amsa.
“Ba kya jin magana, ba na ce bana son a amsa min magana da kai ba?”
“I'm sorry” ta faɗa da sauri.
“Ina jin ki.”
Nan ta bashi labari tas har da ƙara wasu abubuwan da ta manta bata faɗa wa su Hajjaty ba. Cike da tausayawa yake kallon ta musamman yadda take kuka tana magana cikin raunin murya.
“Is ok, wipe your tears” ya faɗa yana miƙa mata handkerchief ɗinsa wadda kamar an yi masa wanka da ruwan turare ne. Amsa ta yi ta goge kana ta miƙa masa.
Kai ya jijjiga mata yana faɗin “No, ki riƙe shi a tare da ke, believe In me Zahrah.” sai da ta ɗago ta kalle shi jin ya ambaci sunan ta. “In har Mamah na raye zan yi iyakar iyawa ta na binciko ta, kuma zan ɗauki hukunci a kan mutanen da suka cutar da ku da sannu. Ki daina kuka kinji? Ki zama jaruma kamar ni, na fi ki tarin damuwoyi amma ba na bari a fahimci hakan a tattare da Ni.”
“Is he that simple?” ta tambayi kanta, a zahiri kuma tace “In sha Allah Yaya, Thank you”
Without minding on her appreciation yace “Alhaji Baba ya yi magana a kan karatunki ma, aji nawa kike?”
“S.S.S 2 ne sai na daina zuwa.”
“Ok zaki koma kin ji? Ki shirya gobe da safe I'll be taking you to school, Zaki koma final year ne kiyi SSCE.”
Jin maganar sa yasa Zahrah jin wani irin daɗi cikin ranta tana faɗin ashe haka ɗan'uwa yake?.
“Thank You so much Yaya, zuciyarka tana da kyau, kamar yadda ka faranta min Ubangiji ya yaye maka damuwoyin ka kaima ka rayu cikin farin ciki.”
“Amin” daga haka ya fara ƙoƙarin miƙewa. “Yaya Thank you.”
Murmushi yayi wanda ya jefa ta cikin mamakin dama yana yi? Ganin kallonsa da take yasa ya ce “Ki kula da kan ki, In kina da damuwa feel free ki same ni, and I promise to be there for you.”
“In Sha Allah, thank you.” daga haka ya bar dining ɗin ya koma parlour, ita kuma Zahrah na tsaye tana mamakin how simple he is tare da yaba kyakkyawar zuciyarsa. Murmushi tayi tana shafa fuskarta kana ta koma dining ɗin taci abincinta hankali kwance sai murmushi take yi.
Tana gamawa ta fito parlourn, lokacin har Yaya Sadauki ya tafi iya Hajjaty je zaune, murmushi tayi tana mai ƙarasawa jikin Hajjatyn ta kwanta.
Hajjaty ma murmushi tayi tace “Zahrah'u Yayanku yace a faɗa miki da yamma ki shirya zai miƙa ki ki yi shopping.”
Zaune ta miƙe tana duban Hajjaty da mamaki. Ganin hakan kuma yasa Hajjatyn ƙara faɗaɗa murmushinta tace “Dama na ce miki shi nake jira ya dawo ya kai ki, ban ma masa maganar ba ya tunkare Ni, yana son ƴan'uwansa shi kam, Zahrah naga wasu abubuwa tattare da shi game da ke, Please be with him, ki kula da shi kuma ki ƙarfafe shi a kowanne hali ok?”
Kai Zahrah ta gyaɗa daga nan suka ci gaba da hirarsu wacce yawanci Zahrah ke bawa Hajjaty labarin Mamah da kuma tsohuwar rayuwar su, haka kawai take jin daɗin hakan duk da ba labarin jin daɗi bane amma tana enjoying when narrating it to others, atleast yana rage mata damuwar rashin Mamah duk da cewa yanzu ma bata rasa komai ba, she's sorrounded by supporters everywhere. Fatanta Allah ta bayyana Mamah itama ta rayu da ahalinta.
Sun daɗe suna hirarsu har lokacin azahar, yau dai Zahrah ba a shiga kitchen girkin Rana ba. Ko da suka yi sallah bata fito ba sai da ta watsa ruwa. Bayan ta dawo parlourn bata ga Hajjaty ba sai ta bi ta Bedroom ɗinta. A lokacin kuma Hajjaty ta ajiye wayarta alamar dai ƙira ta amsa.
“Ƴar halak ga ki nan ma, dama Yayanku ne yace wai ki taimaka ki masa girki amma ba yanzu ba sai around 3:00pm zai shigo.” “To Hajjaty.” Bayan sun yi lunch Zahrah ta ɗan kwanta, bata yi aune ba taji hayaniyar su ai kuwa ta miƙe da sauri tana dirowa sannan ta nufe su da gudu tana rungume su.
“Kai sisters, daga school duk sai ku daina nema na?, Na yi fushi ma.” ta faɗa tana zame jikinta daga nasu lokaci ɗaya.
“Haba sister, ba haka bane wallahi, yanzu dai mu zauna sai ki hukunta mu.” Zakiyya ta faɗa tana kwaɓe fuska har sai da gabaɗayansu suka dara. “Ke dai Zakiyya ba kya rabuwa da ban dariya wallahi.”
“Ba wannan ba dai, tun da na sanya murmushi kan fuskarki na cancanci Ni kaɗai ki yafe min, kowa ta sa ta fisshe shi.” ta faɗa tana ƙara sakin dariya.
Dukan wasa suka kai mata ai kuwa Zahrah ta tare tana faɗin “Kwa dake ta kuma? Kowa tasa ta fisshe shi. Jama'ar nan dan kun koka school sai ku mance Ni?”
“Sorry Zahrah kin san ko kowa ya manta da ke Ni ba zan manta da ke ba, ina matuƙar ji da ke shalelen hajjaty.” Nainarh ta faɗa ita ma tana addu'ar Allah yasa ta kauce. Ƴar harara Zahrah ta banka mata kana tace “Kin ci Sa'a ina ji da ke ai.” Dariya ita ma tayi ta dawo ɓangaren da Zahrah da Zakiyya suke tana yi wa su Nasreen gwalo.
“Yanzu Sis Zahrah kina gani har gwalo Nainarh ke min saboda mun ɓata, dom Allah mu bawa maraɗa kunya.” Nasreen ta faɗa tana ɗagewa Zahrah gira.
“Kin ci Sa'a kema.” Zahrah ta faɗa tana janyo hannun Nasreen zuwa ɓangarensu ya rage iya Rumaysa wacce ta kwaɓe fuska tace “Shikenan tunda Ni kaɗai ce ba a so, bari na koma kawai.” ƙofa ta nufa kamar zata fita, caraf dukkansu suka taho suka rungume juna. “We're sorry” suka kama kunnuwansu “We all love you.” “I love you too my sisters.” Duk sai suka kwashe da dariya.
Haka suka yi ta shirmensu, buɗe idon da Zahrah zata yi kan wall clock taga 2:16pm, a zabure ta miƙe tana faɗin “Innalillahi, ashe akwai aiki gaba na” Da mamaki suke kallonta Nainarh ta ce “Aikin me kuma?” Duk sai suka mayar da kallonsu ga Zahrah seeking for more explanation.
Kanta ta kauda gefe tana faɗin “Forget it kawai, maza ku tashi mu shiga kitchen.”
“Tab, daga dawowarmu daga school ko hutawa ba muyi ba?” Nainarh da Zakiyya suka faɗa.
“Naga dai ku ne kuka tsayar da Ni da yanzu na gama, Please muje ku taya Ni.” Babu yadda suka iya haka suka nufi kitchen ɗin, tare suka toya masa sannan suka haɗa miya wacce taji nama sai mitar wai ma ake wa girkin suke, ita dai Zahrah bata ce komai ba illa iyaka ta kalle su ta kauda kai.
Bayan sun gama suka Kai dining suka jera sai ƙorafin sun gaji suke. Daga nan ta ce to su koma su huta abun su ita kuma ta nufi kitchen ɗin ta haɗa Masa fruit salad. Tana gamawa ta kai ta ajiye sannan ya koma Bedroom ɗinta.
A can ta tarar da su sun baje sai hayaniya suke, ita kuwa ta shige toilet ta sheƙa wankanta ta fito. Bata bi ta kansu ba har sai da ta shirya tukun ta zauna. Hala suka yi ta shirmensu har lokacin da Laraba tazo kiran Zahrah.
A lokacin har Yaya Sadauki ya dawo ashe yana jiran a zo a bashi abinci. Da kanta tayi serving nasa sai surutu take masa shi kuwa ba abun da yake cewa sai dai murmushi ko uhm ko kuma a'a. Cikin ransa kuma yana ƙara yaba mata don girkin nan da yake ci dawowarsa ya tabbatar ba masu aiki ke yi ba kuma ba Hajjaty ba saboda ya san girkinta. Addu'ar sa Allah ya bashi ikon dawo da Mama don kuwa ba ƙaramar gwarzuwa bace, renon da tayi wa ƴar ta ya burge shi musamman ta ɓangaren girki, zai iya cewa cikin familyn nan da wuya a samu wacce ta iya girki ma har manyan ƴan matan gidan.
_Bari na dasa aya a nan, Please kuyi reacting sannan ku taya Ni sharing saboda Allah, in kun yi reacting sosai anjima zan ƙara update. Ina ƙaunar ku my esteem fans._
[12/28, 11:25 AM] Diamond Bhatool: *🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 1️⃣4️⃣
_Wannan shafin kwacakom ɗinsa sadaukarwa ne ga Maman Tajuddeen da kuma Maryam Muhammad, alkhairin Ubangiji ya kai gareku mutanen kirki. Ina matuƙar jin daɗin comments ɗinku wallahi, ILYSM_
﷽
Yana gama ci ta tattare Wurin ta ɗan gyara, nan yace in ya huta zasu fita. Cike da farin ciki ta koma Bedroom ɗinta, har ga Allah ta manta da su Nasreen da ke ciki yayin da murmushin saman fuskarta ya kasa gushewa.
“Ehn Zahrah why this smile?” Nasreen asked
Ba tare da ta kalle ta ba tace “Nothing, kawai yau ta kasance rana ta farko da zan fara fita ne.”
“Da wa zaku fita? And where are you guys going?” Rumaysa ta tambaya tana kafe ta ido.
“Ehn knowing where is not important Amma in na dawo zaki gani. Ni da waye shima ban sani ba, Hajjaty dai yanzu take faɗa min cewa in shirya.”
Abayar da Nasreen ta kawo mata ta saka sannan ta fara ƙoƙarin gyara fuskarta, ko da ta gama ta juyo gurin su hannunta riƙe da veil suka tsira mata ido. She look so awnn and breathtaking. Ganin ta Yi Shirin fita yasa Zakiyya faɗin “Bari na je na ɗan huta Please, xan dawo anjima kafin nan kun dawo.”
“Nan ɗin ba wurin hutawa ne sai kin koma can?” Zahrah ta tambaya.
“Tsaya muje Zakiyya nima zan wuce, Mommah ta ce min Yaya Sadauki ya dawo, In ya koma bai tarar da Ni ba zai hukunta ni.”
Nan suka wuce suna ɗagawa Zahrah hannu “Ki kawo mana tsaraba kuma.”
Nasreen da Rumaysa zamansu suka yi nan Bedroom ɗin Zahrah ita kuma ta fito parlour tana jiransa. Few minutes sai ga Yaya Sadauki cikin takunsa na ƙasaita, sanye yake cikin wata back expensive T-shirt gaban an rubuta SPORT sai Kuma blue-black jeans Wanda ya ɗan kama shi kaɗan. Black takalmi ne a ƙafarsa, taku yake kamar wani basarake yayin da ƙamshin turarensa ke isa wuri kafin shi.
Agogonsa da ke ɗaure a tsintsiyar hannu ya duba ganin da sauran lokaci yasa kai tsaye ya nufi Bedroom ɗin Hajjaty ya mata sallama kan sun tafi. Ko da ya fito bai ce mata uffan ba sai yayi waje, ta riga ta gane cewa miskilanci a jininsa ne hakan yasa ta miƙe tabi bayansa.
Motar da ya nufa ta ƙarewa kallo tana ƙara yaba kyanta, horn ɗin da yayi mata yasa ta Zabura ta nufi motar, gidan baya ta buɗe da niyyar shiga ta tsinkayi muryarsa yana faɗin. “Ni drivern ki ne?” ai tuni ta rufe ta koma front seat ta Zauna.
Wani makeken shopping mall ya nufa da ita yayinda kowannensu ya ƙunshe bakinsa in Banda sautin karatun Minshawiy babu abinda ke tashi yayin da Zahrah ke ɗan satar kallonsa time to time tana ayyana irin nutsuwarsa.
15minutes suka share kafin suka isa, bayan ya daidaita parking ne ya juyo gareta
“Let's go” daga haka ya buɗe side ɗin da yake haka nata ɓangaren ma. Tunda duka fito mutane ke kallonsu musamman Yaya Sadauki da ya shahara a faɗin ƙasar ba don saboda tarin dukiyar da yake da shi ba sai don ƙwazo da ubangiji yayi masa, he's the head as well as founder of NIC, mutumin da ya samu ƙwarewa a fannin bincike sannan kuma the whole CEO of Abatcha Automobiles Wanda ke ji da kuma tashe da samartaka.
A tare suka nufi entrance na makeken mall ɗin, wasu na faɗin “Anya wannan ba ALIYU UMAR ABATCHA ba ne?” others are worried about the lady he's with Suna fatan ba aure yayi ba, wasu ƴanmatan kuma na faɗin ai ko ya yi aure suna son shi, mathna wa thulatha wa rubā', wasu kuma na faɗin maybe ƙanwarsa ce don da gani ba aure tsakaninsu. To shi ya ma san suna yi ne?”
Kallon Zahrah yayi bayan sun shiga yace “Go round and pick anything you like, kada ki damu da ya yake just pick it ok?”
Kai ta gyaɗa Masa daga haka ta nufi ciki, tsawon mintuna amma ta kasa zaɓar komai, kamar ya sani kuwa sai ya bi bayanta, ganin babu abunda ta ɗauka yasa ya ɗan ja ƙaramin tsaki.
Komawa yayi sai ga shi tare da ɗaya daga cikin ma'aikatan wurin, pointing ma Mai aikin Zahrah yayi wacce ke tsaye still ko uban me take. Ban ji me yace masa ba sai ga Zahrah ta dawo wurin sa da zuwan mutumin. Daga nan Yaya Sadauki yace su fito su jira a mota.
Ba musu tabi bayansa suka koma. Kusan 10 minutes sai ga mutumin nan da wasu masu irin kayansa sun fito su uku yayin da hannuns kowannensu ke ɗauke da akwati. Motar su Yaya Sadauki suka nufa, dama booth a buɗe yake, so basu sha wahala ba suka ajiye kana mutumin yazo ta saitin da Yaya Sadauki yake ya miƙa masa ATM card ɗinsa, har ya karɓa mutumin na shirin juyawa ya tsayar da shi sannan ya miƙa masa wasu kuɗaɗe masu ɗan yawa. “Thank you” mutumin ya fara godiya kenan Yaya Sadauki ya ɗaga masa hannu. Nan ya basu hanya su kuma suka wuce abun su.
Ba tare da Yaya Sadauki ya kalli Zahrah ba yace “Why didn't you pick anything? Ko babu abun da ya burge ki a wurin ne?”.
Har ta jijjiga kai ta tuna da ba ya so, da sauri ta buɗe baki tace “A'a ban san ya kuɗin abubuwan zai kasance ba, kada na ɗauki masu tsada da yawa na karar maka da kuɗinka.”
Statement ɗinta na ƙarshe ne ya bashi dariya har sai da ya murmusa ita kuma sai kallonsa take ganin yadda wani sihirtaccen kyau ke fitowa daga gare shi cikin ranta ta furta “Tabarakallahu Ahsanul Khaliqin”.
“An ce miki kuɗi na zai ƙare ne for common shopping da zaki yi? Ai ko mall ɗin zan siye babu wani giɓi da kuɗaɗe na zasu samu.”
A ba zata ta furta “Ka ji daɗin ka”
“Ke ma kina son kuɗin ne?”
Dariya Zahrah ta kwashe da ita jin ya mata wata irin tambaya har sai da dimples ɗinta suka lotsa, duk irin yadda yaso ya kauda kansa kasawa yayi, sai ya tsinci kansa da faɗin “Kina da kyau” tukun ya mayar da dubansa ga titi.
“Kai Yaya ai kuwa ka fi Ni, duk duniyar nan ban taɓa ganin kyakkyawa kamar ka ba, da ina cewa Yaya Ishaq ne amma tun da na ganka na tabbatar babu ya kai.”
Kalamanta sun masa daɗi ta ɗaya ɓangaren kuma sun bashi dariya amma a wannan karan dariyarsa yayi ga yadda fararen haƙwarensa suka bayyana, Zahrah kam kasa daina kallonsa tayi.
“You're funny Zahrah, Wai kina nufin na fi kowa da, to ina batun Indian”
“Allah Yaya ka fi su musamman when you smile, sai ka ƙara kyau.”
“Uhm” kawai yace ganin sun doso katafaren gate na estate ɗin su. Bayan sun iso yayi parking a apartment ɗin Hajjaty. A hankali ya furta “You can go, Ni zan wuce part ɗin mu, Please in baki gaji ba cook something for me.”
“Ok Yaya thank you, may God bless your wealth and Grant you jannah.” Ya ji daɗi sosai da addu'arta har sai da ya murmusa sannan yace “Amin Lily, Zan sa a shigo da kayanki yanzu, take care.” “Ok bye” ta faɗa tana waving hand ɗinta sannan ta shige ciki shi kuma ya ja motarsa zuwa part ɗin su.
Ashe duk abun da ke faruwa a idon Rumana ne wacce ta kusa mutuwa don mamaki da tsananin kishi, wai a wannan yarinyar Yaya Sadauki yake wa murmushi? Yaushe ma yazo?, Tsabagen yadda zuciyarta ke tafasa da gudu ta tafi tana kuka har part ɗinsu without minding the distance.
Ita kuwa Zahrah tana shiga ta tarar da Hajjaty na zaune ita da Ya Auwab, Ya Taj, Ya Aufa da kuma ya Faruq, kan ta ƙasa ta ƙarasa. Fuska sake Hajjaty tace “A'a Zahrah'u an dawo kenan, ina shi Sadaukin?”
“E Hajjaty ya wuce part ɗin Mommah.”
Shaye da mamaki Ya Auwab ke kallon Hajjatyn kana yace “Hajjaty wane Sadaukin? Wai Yaya dodon mu?” Sosai Zahrah ta dara duk da cewa she's not comfortable being in-between them saboda yawan kallo irin na Ya Auwab.
“Shi dai, ai tun jiya ya iso shi da Halilu.” Zahrah dai wucewa tayi zuwa Bedroom ɗinta, kamar yadda tayi zato none of them was there. Wanka ta Yi ta ɗauro alwala, tana idar da Sallah ta yi zikirorinta sannan ta nufi kitchen don haɗawa Yaya Sadauki abinci.
*Yaya Sadauki*
Lokacin da ya isa ma an fara kiraye-kirayen sallah, hakan yasa ya haye sama don yin alwala, kamar yadda Mommah tayi alƙawari ta sa na gyara masa Bedroom ɗinsa. A gaggauce yayi wanka sannan ya ɗauro alwala, yana saka kaya ya fito sai sauri yake jin an shiga sallah a masallaci.
Bai wani tsaya ba da aka idar kuma bai bi su Alhaji Baba ba sai ya juya zuwa ɓangarensu don samarwa mahaifiyarsa lafiya. Ita ma lokacin tana parlourn ita da Nainarh sai kuma auta Ra'ees. Da gudu Rarrashi ya nufi Yayan nasa yana ihun murna “Oyoyo Yaya, oyoyo Yaya.”
Hugging nasa yayi shima yana murmushi coz he so much adore that little creature. Tare suka ƙarasa. Cike da farin ciki Nainarh ta gaishe shi tana faɗin yaushe ya dawo?, Kallon da ya aika mata yasa ta miƙe tsaye ta nufi Bedroom ɗinta. Kallon Ra'ees yayi yace “My Man, maza ka bi Aunty Nainarh ka ce ta koya maka karatu.” A shagwaɓe Ra'ees ɗin yace “Yanzu Aunty Nainarh duka na zata yi, da ba ka nan ma kullum sai ta je wajen Aunty Zahrah da Mommah ta hana naje na ganta,kuma Aunty Nainarh tace kyakkyawa ce, wai haka ne Yaya?”
“Uhm, yanzu kace Ni na aiko ka ba zata dake ka ba kaji.” daga haka Ra'ees ɗin ya wuce shi kuma ya maida dubansa ga Mommah. Cike da girmamawa ya gaida ta ta amsa fuska babu yabo babu fallasa.
Suna gama gaisawa tace “Aliyu ya zancen aurenka da yarinyar can? Ka samu ka shawo hankalin Alhaji Baba?” dariyar takaici yayi cikin ransa yana ƙara nema mata shiriya.
“Mommah ai babu fashi auren nan, nima ina so fa” A zabure tace “Uban me suka ba ka Aliyu, yaushe ma kake kula matan ballantana har ka ce kana son ta, wallahi ƙarya kake kuma baka isa ka auri ɗiyar Hajiya Babba ba.”
Ganin yadda ta ɗau zafi yasa ya kwantar da murya yace “I'm sorry Mommah, calm down please” tea ɗin da ke ajiye kan Centre table ya miƙa mata “Shikenan mu bar zancen tunda baki so, mu yi wani daban.” Haka suka sha hirar su daga nan kuma ya fice saboda lokacin salla da yayi. Bayan an idar kuma ya wuce da Alhaji Baba.
Shi da kansa ya shiga da akwatinan da ya manta bai sa an miƙa mata su ba tun ɗazu. Laraba da ta Ganshi da sauri ta karɓa nan ya faɗa nata inda zata kai. Dayan ya koma ya ɗauko sannan ya nufi ciki.
Nan suka yada zango a parlourn ana ƴar hira. Sallamar Yaya Khalil ne ta dakatar da su daga maganar. Bayan ya shigo gefen Man ɗinsa ya zauna, suna gaisawa da Hajjaty da kuma Alhaji Baba aka ci gaba da hira.
“Nifa abinci ne ya kawo Ni nan bayan gaida tsofin nan, a tashi a ci abinci Please.”
“To foodie, you'll never change.” Dama aikin Yaya Khalil ne In dai an fara hirar nan shi ke tuna musu da abinci. Babu musu kuwa Hajjaty ta ƙwala ƙiran Zahrah.
Ita tayi serving ɗin su ganin bata sakawa Yaya Sadaukin ba yasa Yaya Khalil faɗin “Ke Zahrah abun naku har ya kai haka? Ni na haƙura da nawa ki miƙawa Sadauki.” Ƴar bazawarar dariya tayi har sai da sautin ta ya fita.
“Haba Yaya Khalil, ci naka kawai, na Yaya na ai daban yake da na kowa.” ba iya Yaya Khalil ba har Yaya Sadauki sai da ya kafe ta da ido. Su dai tsofin abincinsu suka ci gaba da ci. Ganin yadda suka kafe ta da ido yasa ta ɗan kau da kanta gefe sannan ta buɗe foodflask tayi serving nashi.
Nan Yaya Khalil ya tubure ala dole shima wancan zai ci, Yaya Sadauki yace ai ba wannan zance kowa yaci nasa. Da ƙyar dai ya bari Zahrah tayi serving Yaya Khalil ɗin karo na biyu sannan ita ma ta zauna tana ci. Ko da suka gama Yaya Khalil sai mitar wariyar da Zahrah ta nuna yake, ita kam abun ma dariya yake bata.
*React and Comment Please, Diamond 💎 Bhatool 🦋 taku ce.*
[12/28, 9:19 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 1️⃣5️⃣
_Gabaɗaya sannan shafin sadaukarwa ne ta musamman gare ku mutanen channel ɗina ~Diamond Bhatool Reading Club (DBRC)~ alkairin Ubangiji ya kai gare ku a duk inda kuke. Ku sani ina matuƙar godiya da yadda kuke nuna min ƙauna, wallahi ina don ku irin da yawan nan. ILYSM🦋💞_
﷽
Sai da kowa ya tashi a wurin ga rage iya Yaya Sadauki ne da Zahrah wacce ke jira tayi masa godiyar kayayyakin da ya sa aka jida mata. Fahimtar hakan yasa ya ɗago ya kalle ta yana goge bakinsa da tissue.
“Ehn” yace yana ɗage mata gira. “Yaya, thank you so much, words ain't enough to express how much deeper I appreciated, you are not only a brother but a father himself. Jazakallahu khairan Yaya na.”
“Uhm Ameen Babu komai, bana son godiyar nan ma, all I did na Yi ne saboda Allah, and you indeed deserve it. Thanks for the food.”
Tura baki tayi tace “I don't like the thank you also, Nima na Yi ne saboda Allah and you deserve the tasty and handsome food from me.” (Kun ji wai handsome food😳🤣)
“Ey? Who say your food is tasty? Wai ma handsome, hhhhh I'm only managing to take it saboda kar ki ji babu daɗi, amma sam baki iya girki ba.”
Zaro ido Zahrah tayi tana kuma shagwaɓe fuska lokaci guda “To In haka ne nima ka biya ni kuma ka daina ci tunda ba daɗi ai su Hajjaty zasu ci.”
“Waye ya ce miki zasu iya ci?, Tab! Lallai baki san duk wanda ya kai girkin nan naki bakinsa ba lallai ya iya ƙara sha'awar abinci ba har ya mutu?.”
“A'a a'a wallahi I know that I prepare the tasty and delicious meal you ever tasted, you're only beating around the bush, Kuma daga yau ban ƙara yi maka.” ta faɗa tana miƙewa tsaye bakin nan gaba kamar shantu, shi abun nata ma dariya ya bashi. Buguzum ta ja kujerar baya tana shirin ficewa taji ya dakatar da ita cikin murya mai cike da umarni.
“Don't You dare add a step in ba Haka ba sai na ɓalla ƙafar, come back.” Juyowa tayi kamar zata yi kuka saboda takaici.
Muryarsa ya sanyaya yace “I'm sorry Lily, kin ga wasa nake, girkin ki ba dai daɗi ba, Mamah dai ta yi raino mai kyau don duk ƴanmatan gidan nan babu wanda zai iya irin girkin nan naki.”
Lokaci guda Zahrah ta saki wani murmushi tana faɗin. “Ai dama na sani, Babu wadda zai ci girkin Zahrahn Mamah bai yaba ba. Thank you Yaya na.”
“Uhm nace ba”
Hankalinta kwacakom ta mayar gareshi
“In na yi aure zan ɗauke ki kike mana girki Ni da mata ta.”
Dimm! Zuciyarta ta buga, sai kuma ta zaro ido gudun kar ya gano ma ta tsoratan nan.
“Tab ɗin, Zahrahn Mamah ce zata muku girki?, Allah ya sauwaƙe Barrister Zahrah ta muku girki?” Ido waje shima yake kallonta musamman yadda tayi kici-kicin da fuska.
“Do You mean ba Zaki yi min ba kenan har kike faɗin Allah ya sauwaƙe?” baki ta turo bata ce komai ba
“Shikenan tunda ba zaki min ba ai. Tun yanzu Gara na daina ci kada na saba kuma daga baya na sha wahala.” Da sauri tace “Ni fa ban ce haka ba Yaya, kawai dai sai nayi muku girki kai da wata gardiya?”
Ido ya zaro yana kallonta musamman yadda hankalinta kwance take magana babu wani shakkar sa kamar yadda sauran mutanen gidan ke ji.
“Me kika ce?”
“Wallahi suɓutul kalam ne Yaya na, ai matarka kam ƴar suwalwala ce kamar yadda kake ɗan suwalwali.”
Ɗan suwalwalin da tace ya sa shi dariya sai da ya dara, yana ƙara mamakin yadda take. Lokaci ɗaya kuma ya dakatar da dariyar da yake yi ya kalle ta. “Lily? Are You that talkative?” Da hannunta ta ƙunshe bakinta tana dariya.
Wayarsa da tayi ringing ya fitar, ganin Yaya Khalil ne yasa ya ɗan ja tsaki, sai a lokacin ya tuna da cewa a dining area suke, kallonsa ya kai ga parlourn babu kowa sai Hajjaty da Yaya Khalil, Alhaji Baba already ya shiga ciki. Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da katse kiran. Kallonsa ya mayar gare ta yana faɗin.
“Ni zan wuce Lily, kar ki manta gobe zan kai ki school and I dislike African time.”
“Zan shirya da wuri in Sha Allah, Bye Yaya na.” daga haka ya wuce ita ma ta nufi Bedroom ɗin ta.
Nan ta fara buɗe kayayyakin da ya sa aka kwaaa mata wanda tunda take bata taɓa tsammanin ko rabinsu zata samu ba a rayuwa. Sosai ta yaba da kyansu tana ƙara godewa Allah tare da addu'ar Allah ya bayyana Mamah, Thank you thank you kam Yaya Sadauki ya sha ta, tunda ta fara buɗewa take faɗa har ta gama. Tana gamawa ta fitar da kayan kwalliya ta jera kan mirror, masu buƙatar a kai su toilet ma ta agaza Musu zuwa masauƙinsu.
Nan ta fito kayan ta jera cikin closet, sannan ta ware waɗanda zata saka gobe tare da takalmi da handbag. Toilet ta faɗa tayi wanka sannan ta saka night dress daga cikin sabbin da tayi daga nan ta faɗa gado tana Allah Allah gobe tayi. (Sweetest dreams Zahrah.)
A nasa ɓangaren ko da ya ƙarasa parlourn bai bi ta kan Yaya Khalil ba saboda ya san halin kayansa, yanzu zai tusa shi gaba da zolaya. Gefen Hajjaty ya zauna yana faɗin “Tsohuwar nan ina mijinki ne?”
“Ungo nan” tayi masa daƙuwa
“Ai yau ba wajensa kazo hira ba.”
Harara ya bankawa Yaya Khalil da yayi magana kana ya ce “Hajjaty daga tambaya kuma? To bari na tafi kawai.”
Hajjaty tace “Ai dama ba wurin mu kazo ba yau kam, Allah ya tsare hanya.”
Kwaɓe fuska yayi yana kallon Hajjatyn wacce ta haɗe rai, shi dariya ma ta bashi Wallahi. “Tuba nake, kaina bisa wuya, a yafe min sarauniya ɗaya a gidan Alhaji Muhammad Abatcha, tsohuwa mai ran ƙarfe kuma.”
Lokaci ɗaya Hajjaty ta fashe da dariya tana faɗin “Allah ya shirye ka Sadauki, kwanan nan naga alamar ka fara barin mugayen ɗabi'unka na miskilancin, ai yafi maka ma. Ni kaga bacci ma nake ji, bari na wuce sai da safe.”
Dariya shima yayi yace “To a tashi lafiya Hajjaty”
“Kai kuma...” ya faɗa yana jefawa Yaya Khalil wani mugun kallo mai bayyana zuwa haɗu daga haka ya nufi Bedroom ɗin Alhaji Baba. Yaya Khalil kuwa dariya ya yi daga nan shima ya wuce zuwa part ɗinsu.
Lokacin da Yaya Sadauki ya shiga ciki Alhaji Baba har ya gaji da jiransa ya fara gyangyaɗi. Sallamarsa ne tasa ya wartsake. Yau basu daɗe ba sosai coz tattaunawar gaba ɗaya ta ta'allaƙa ne ga batun auren Yaya Sadauki da Aunty Mabruka, Nan Alhaji Baba ya ƙara gaining consent ɗin Yaya Sadaukin lokaci ɗaya shima ya nuna goyon bayansa tare da fatan Allah yasa hakan shine mafi alheri garesu. Fatansa dai a yanzu bai wuce ya maida hankali wurin gano masu yiwa ahalin zagon ƙasa da kuma ƙulla sharruka ba.
Ganin dare ma ya fara yasa yayi wa Alhaji Baba sallama kana ya ja masa ƙofa. Alhaji Baba har cikin ransa yayi farin ciki da abunda yake shirin ƙullawa ganin yadda Yaya Sadauki ya nuna goyon bayansa ɗari bisa ɗari, wani sashe na zuciyarsa kuma na ƙara tausaya masa.
*Flash back* Bayan wannan ƴar tarzoma da aka yi a ɓangaren Hajiya Babba, kowacce mijinta ya ja mata kunne akan kada ta ƙara shiga sabgar Hajiya Rukayya balle su kai mata raini, ita ɗin ba sa'ar su bace, abun ya ƙonawa kowaccensu rai har ta kai ga kowa ta ɗauki alwashin samarwa kanta maslaha game da hakan. Haushin su bai wuce ma yadda mazajen nasu ke matuƙar ba wa Hajiya Rukayya girma ba, ko faɗa suka yi ba sa bin bayansu sai na Hajiya Rukayya, that's what make them took a pledge to destroy her.
Ɓangaren Mommah ta ƙudiri aniyar hana auren da Alhaji Baba ke shirin ɗaurawa ko da kuwa zata yi yawo tsirara ne ba wai iya rasa aurenta ba sakamakon huɗubar shaiɗanci da ƙawayen ta suka yi mata ita la ta hau kan keken ɓera.
*Ci gaba*
Kai tsaye ɓangaren su ya wuce don ya samu ya huta, har ya fara taka staircase ɗin ya juyo jin Mommah na ƙwalla ƙiransa.
Juyowa yayi sai a lokacin ne idon sa ya sauƙa a kan Daddy. Ƙarasawa yayi yayi hugging Daddyn yana faɗin “Daddy na, yaushe ka dawo?”
“Wato ma ina maka magana Aliyu ka tafi wurin ubanka saboda Ni bani da muhimmanci a wurinka ka bar Ni Ni ga mahaukaciya ko?”
Dafe kansa yayi yana faɗin “I'm sorry Daddy, Ina yini ya hanya?”
Fuska sake Daddy ya masa da “Alhamdulillah Lafiya ƙalau.” sai kuma ya haɗe fuska har ya zartawa Yaya Sadauki a iya kamewa. Kallon Mommah da ke haki yace
“Wuce ki shiga ciki ki jira Ni, Aliyu go and rest”
“Ok Daddy, bye Mommah, bye Daddy.” Ya keɓe ta zai wuce da sauri ta tsayar da shi “Ba kiranka nake ba?” ta faɗa a harzuƙe.
“Let him go Sughrah in ba Haka ba you'll see the other side of me, ALIYU go.”
Ya ɗaga ƙafa zai tafi Mommah ta ƙara tsayar da shi. “Other side of yours na nawa, nace na nawa Daddyn Ra'ees?, Aliyu if you dare go sai na saɓa maka.”
Ransa ne ya fara ɓaci da abunda Iyayen nasa ke yi a gabansa, shiyasa baya spn zaman part ɗin su tunda yayi wayo. Fuskarsa ɗaure sai kuma ya kwantar da murya yace “Haba Mommah, why kike son rigima ne ke kam? DADDY na miki Magana kin ƙi bin umarninsa how do you expect me to obey your orders?, Mommah not me alone in baki daina musu da Daddy a gaban mu ba har su Ra'ees sai sun daina bin maganar ki. Please calm down ki bi umarnin DADDY.”
Ba ƙaramin tasiri kalaman sa suka yi a ranta ba, hakan yasa ta sake hannun Yaya Sadaukin ta wuce zuwa Bedroom ɗin nata. Sai da yaga shigewarta tukunna yayi wa Daddy sai da safe.
Bai ɓata lokaci ba kamar kullum yayi wanka ya saka kayan bacci sannan ya fashe jikinsa da turare, daga nan ya shinfiɗa praying mata yayi shafa'i da witri kana ya nufi bed ɗin sa yana mai kashe bedside lamp ɗin da ya kunna. Ya so bacci ya ɗauke shi amma tunanukan da suka yi wa zuciyarsa ƙawanya sun ƙi barin hakan, bahaguwar rayuwar da iyayensa ke yi ya fara isar shi coz tunda ya tashi yayi wayo bai taɓa ganin an yi zaman arzikin a gidan ba, Mommah ko kaɗan ba ta daraja Daddy shiyasa ma ya Hajjaty ta nema masa auren Aunty Amarya.
Moreso, tunanin sakamakon rayuwarsa yake, ya zata kaya yaya zai yi? Ga kuma auren sadaukarwa da yake shirin yi saboda Hajiya Babba da amininsa kuma ɗan'uwansa, ga kuma tunanin ƴar'uwarsa Zahrah da ya rasa dalilin da yasa ya kasa manta ta daidai da na second ɗaya ne, amma ya alaƙanta hakan da kyautatawarta gare shi. A haka a haka dai har ɓarawo bacci ya sace shi. (Good night Yaya Sadaukin mu).
*Other side of the house, Hajiya Babba's apartment.*
Yammacin ranar bayan Aunty Mabruka ta dawo daga court Hajiya Babba ta titsiye ta gaba akan al'amarin da ya faru a karo na ba adadi. Hawayen da Aunty Mabruka ke yi yasa Hajiya Babba daka mata tsawa har sai da Nasreen ta Zabura ta fito parlourn.
“Ki faɗa min gaskiya Mabruka in ba haka ba ranki zai ɓaci.”
Tsabar takaici da ya tokare mata maƙogwaro yasa ta kasa cewa komai sai zubar da ƙwalla da take.
“Don't let me repeat myself Mabruka, can Dama akwai wata alaƙa tsakanin ki da Sadauki ne har kike bashi damar shiga ɗakinki? Allah yasa dai baki bashi kanki ba ma.”
A zabure Mabruka ta buɗe baki ta fara magana har wa lokacin kuma hawaye bai daina zuba kan fuskarta ba.
“Haba Hajiya, idan kowa bai shede Ni ba ai ke kika haife Ni kuma kika raine Ni, kin san me zan yi kin san meye ba zan yi ba. Shekarata yanzu ashirin da bakwai a duniya, duk da cewa bani da aure hakan bai sa ina bin maza ba, ke kan ki kin san bana mu'amala da su ko da kuwa a lokacin da nake ji da tashen balagar tsuntsaye ban aikata hakan ba sai da nayi hankali? Ku duba al'amarin Hajiya Babba, kullum amsar da zan baku ba zata wuce babu abunda ya faru tsakani na da shi ba, hasali ma shi kansa akwai abinda aka bashi in ba Haka ba ke kanki kin san Yaya Sadauki ko kallo ban ishe shi ba.”
*Some of you will wonder why all these is happening, menene dalilin mutanen gidan na tsanar Hajiya Babba kuma meyasa ita da abokan zamanta suke zaman lafiya.?* *A tunanin ku za a yi auren nan ko kuwa? Kuna tunanin ƙiyayyar da uwar miji ke nunawa? Anya Hajiya Turai zata amince? Leka see.* *Duk amsoshinku na tare da ni, ku ci gaba da kasancewa da ni don jin yadda zata kaya.*
[12/29, 10:16 AM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 1️⃣6️⃣
_This page is dedicated to my troublemaker and joy giver (Rouhy🦋). ILYSM🦋💞_
﷽
“Abun da ban fahimta ba kenan, tabbas al'amarin nan akwai sarƙaƙiya and whoever is behind this akwai target ɗin shi kan ki Mabruka. ”
“Hajiya In Sha Allah duk wanda ya nufe ni da sharri ma kansa zai koma.” ta faɗa a raunane, duk irin biris ɗin Hajiya Babba yau she shows her empathy on her daughter, for the first time ever.
“Haka ne, ki shirya jin sakamako daga Alhaji Baba, though ni ba lallai na aminta da zaɓin ba.
*Ina Rumana?*
Tunda ta isa part ɗinsu ta iske Ammie a parlour, tashin hankali ƙarara a fuskar ta, ɗan kukan da take ƙoƙarin riƙewa ne ya ƙwace mata nan ta faɗa cinyar Ammir.
“Ke Rumana lafiyar ki kuwa? Me ya faru?” Ammie ta tambaya cikin tashin hankalin ganin ƴar ƴar'uwarta da take matuƙar so da ƙauna cikin yanayi na damuwa. Shiru Rumana bata amsa ba sai ma ƙara volume ɗin kukanta da tayi.
“Kin ga Rumana ki nutsu ki sanar da Ni damuwarki, wani abun ya faru ne?” ajiyar zuciya Rumana ta sauƙe tana rage sautin kukanta.
“Ina jin ki Rumana, hankali na gaba ɗaya ya tashi, don Allah ki faɗa min ne ya faru?” cikin wata raunananniyar murya Rumana tace “Ammie kin dai san yadda nake son Yaya Sadauki...” dakatawa tayi saboda kukan da yaci ƙarfin ta.
“Talk Rumana, me ya samu Sadaukin?”
“Ammie kin san wannan yarinyar? Jikar Hajjatyn nan yanzu na gan su tare alamun daga wani wurin suke, Ammie Ni fa ko kallo bai ishe Ni ba, wallahi na tsani yarinyar nan kamar mutuwa ta.”
Cikin tashin hankali itama Ammie ɗin tace “Wai Zahrah kike nufi?” kai Rumana ta gyaɗa. “Ki kwantar da hankalin ki daughter, ko ana ha maza ha mata ke ce matar Sadauki, burin mu Ni da ke sai ya cika, yanzu dai ki share zancen yarinyar nan don maganar da nake miki Alhaji Baba....”
Nan ta bata labarin halin da ake ciki. Tashin hankali wai ba a sa masa date! Rumana dai har da sumarta jin wata na shirin wuf da abun harinta. (Allah Sarki Rumana...)
*MORNING.......*
Yau ma dai Zahrah ce ta girkawa Yaya Sadauki breakfast sauran Kuma Laraba ce tayi, Hajjaty sai ɓaɓatu take mata wai tana sakalta Yaya Sadauki, idan ta fara zuwa school ta ga yadda zai yi ai. Ita dai Zahrah dariya kawai tayi tace “Hajjaty ai duk abinda zan yi wa Yaya ban faɗi ba, ya cancanci fiye da hakan.” kyaɓe baki Hajjaty tayi tana faɗin “Ai sai ki yi.”
Bayan sun yi breakfast ya shigo looking so breathtaking and awesome, hairstyle ɗin shi kawai ya sauya amma wani irin kyau da ya ƙara ba a magana. Cike da girmamawa suka gaisa da Hajjaty, ita ma Zahrah ta gaida shi, ba tare da yace uffan ba ya nufi dining, zugum-zugum Zahrah ta bi shi. Tana serving nashi ta wuce don shiryawa.
Wanka ta ƙara yi a gurguje daga nan ta shirya tsaf cikin wata Maroon Egyptian cotton Abaya wacce ta matuƙar amsar farar fatarta, gashinta ta tufke before ta saka Black hula sai kuma tayi rolling black veil na abayar. Sosai ta fito kamar ba ita ba, In ka hanta ba ka yi zaton ɗiyar hausawa bace, sai ta fito sak a balarabiya....black wristwatch ta Sanya wadda kana ganin sa ka san ba na wasa bane kana ta janyo Black handbag da kuma takalmi ta saka.
Ma sha Allah, kiran da Hajjaty ta ƙwala mata yasa ta fesa turare a gaggauce kuma ta fice parlourn.
“Yayanku ya fita” Da sauri Zahrah ta bi shi tana farin cikin yau zata koma karatu bayan wani dogon zango. By the time ta fita da sauri ta ƙarasa motar ta buɗe gidan gaba ta zauna. Nan motar su ta fice daga estate ɗin.
Ganin shirin ya yi yawa yasa Zahrah ta saci kallon Yaya Sadaukin, and to her observation, he looks so worried...
“Yaya” ta faɗa a hankali, ba tare da ya kalle ta ba yace “Uhm”
“You look so worried, wani abu na damunka, ko ba ka da lafiya ne?” Abun da mahaifiyar sa bata taɓa fahimta a tattare da shi kenan, bata san damuwarsa ba ba kuma ta damu da damuwar tasa ba sai ma tsananin son kai da take da, always putting her priority over na wasu, amma yau ga yarinya ƙarama har takan iya fahimtar yana cikin wani hali. Ko ba komai kulawarta gare shi yasa ta ƙara samun matsuguni cikin zuciyarsa.
“Yaya...” ta faɗa kamar za ta yi kuka. “Babu komai Lilyn Yaya, bacci ne bai ishe Ni ba kawai.”
“Kai yaya” ta faɗa Yana kwaɓe fuska. “Wallahi a'a, akwai abun da ke damunka kawai dai Ba ka so na sani ne, but always believe in Allah Yaya, zai magance maka damuwoyin ka, I'm always praying for you tun ban taɓa ganin ka ba.” ɗagowa yayi ya kalle ta sai kuma ya maida kallonsa ga hanya.
“You look so beautiful Lilyn Yaya.” “And you look more handsome than...” Bata ƙarasa ba ganin an wangale musu gate ɗin school ɗin. Ba su wani daɗe ba ya kammala duk wasu matakai na ganin ta zama cikakkiyar ɗaliba, a lokacin kuma ta amshi uniform da littattafai, daga nan aka wuce da ita Form 3...same class da su Zakiyya. Ihun murna suka saki ganin Zahrah suna kuma mamakin ba zatar da tayi musu. Nan suka yi introducing Bata ma sauran ƴan ajin, daga nan fa Zahrah ta ɗame kamar ba baƙuwar ba, har ta yi abokin wai shi Nu'aym, shi ne kuma class rep ɗin su.
Ko da lokacin tashi ya yi ta fito za su tafi da su Nasreen ta hango sayyarar Yayan ta, da sauri ta juya za ta wuce. Nainarh ta dakatar da ita “Where do you think you're going, an Zo ɗaukarmu fa.” pointing motar Yaya Sadaukin tayi sa hannu, nan Nainarh ta zaro ido waje tana mamaki, In ba ƙarya tayi ba wannan motar da Yaya Sadauki yau ya fita da ita ne. Bata aune ba ta ga Zahrah har ta kai ga wurin motar, babu yadda ta iya ta nufi motar Baban Salaha. Ko da su Nasreen suka tambaye ta ina Zahrah sai tace musu ai ta tafi. Basu matsa mata da tambaya ba ganin yanayin fuskarta da haka suka wuce gida.
Can wajen Zahrah tana shiga ya ja motar. “Yaya shi ne ka baro aikinka ka zo, ai da zan koma da su Nainarh.” shiru ya mata bai ce komai ba can kuma yace “Na san da motar can ɗin ai nazo, kullum kuma Ni zan kai ki na maida ki, don't say anything again....” shiru babu wanda yayi magana har suka isa. Yana daidaita parking ta fito, wannan karon kuma a idon Mami wacce motarta ke shirin barin estate ɗin.
Ko da Yaya Sadauki ya shigo Zahrah ta zo ta tambaye shi ko za ta masa girki? Yace mata a'a zai ci wancan ɗin shima and ta shirya in zai fita zai kawo mata uniform na Tahfiz wacce take cikin estate ɗin.
A islamiyyar suka haɗu, nan suka tusa ta gaba da tambayar waye ya mayar da ita gida, shiru tayi musu, da ta gaji kuma tace musu ai motar su Nu'aym ne, ba tare da sun yarda ba suka ƙyale ta amma suka ce mata kada ta ƙara bin wata motar in ba haka ba sai sun faɗawa Alhaji Babba. Bayan sun keɓe da Nainarh ne ta kawo zancen ta kuma yi mata jan ido kan ta san waye ne a motar.
“Ya Allah, Sis Nainarh Yaya Sadauki ne fa ba kowa ba, kinga Dama shi ya kawo Ni, ya riga ya gan Ni, In na wuce na bi ku ba zai ji daɗi ba.”
“Then meyasa kika ɓoye min da farko? Ko kina tunanin ba zan so na ganki da shi ba? Ke ma ƴar'uwarsa ce ai.”
“Ba haka ba ne Nainarh...”
“Don't say anything Zahrah, kawai dai na baki amanar Yaya na, don na ga ke ta musamman ce gare shi, ki kasance da Yaya kina ɗebe masa kewa ko damuwoyinsa za su gusa. Nan ta bata labari kamar yadda Nasreen ta bata. Ita dai Zahrah mamaki take, ko me suka ɗauke ta da ta kasance da shi?
Bayan an tashi daga islamiyyar a gajiye ta koma, amma duk da haka she prepare dinner for him. Lokacin da ta shiga wurin Alhaji Baba ne taji ana zancen aure, amma bata fahimci na waye ba. Ko da ta dawo sai ta ji ta rasa sukuni amma haka ta daure, a yau kam ba su yi wata hira ba da Yayan ta, tana gama serving nasa ta wuce ba tare da ita ta yi dinner ɗin ba.
*Washegari*
Kamar yadda ya faɗa ɗin shi ne ya kai ta school da kansa, haka kuma ya ɗauko ta. A hanyarsu ta dawowa ya kawo mata zancen aurensa. Dim ƙirjin ta ya buga, amma sai ta masa Allah sanya alkairi duk da bata ji daɗin zancen ba, amma ta ta'allaƙa hakan ne da sanin ba son auren yake yi ba saboda ta san mata ba sa gabanta.
A sukwane ta ƙarasa yinin ranar, ko a islamiyya sisters ɗin ta babu tambayar da basu mata ba amma tace babu abinda ke damunta kawai gajiya ce. Bata fasa masa hidima ba tayi masa dinner. Bayan ta yi sallah ta ɗan kwanta kan sallayar ta da niyyar ba zata ma fita waje ba coz ji take kamar ta rausa kuka haka take ji idan ta tuna da maganar. (Yarinya don't know that she's in love....).
Tsawon sati guda tana bin motar gida gudun kada su haɗu, In an tashi ma da wuri take kaɗe ma su Zakiyya hankali su wuce, cikin satin nan ba ƙaramar rama ta yi ba, and bata Zama a parlour ma gudun kada su haɗu da kowa, she's always fund of isolating herself saboda ta fi jin daɗin hakan, duk yadda ƴan uwanta suka matsa mata da tambaya ko uffan ba ta cewa sai ma ta basu waje.
Ɓangaren Yaya Sadauki kwana biyu in ya zo sai Hajjaty tace masa Zahrah ta bi su Nasreen saboda kada ta makara, a rana ta uku ya bar mata sallahun lallai lallai ta jira shi da safe gobe coz zaman part ɗin Hajjaty ma daina shi tayi ta koma Part ɗin Hajiya Babba.
Babu wadda ya fahimci dalilin Zahrah na sauyawarta daga yadda take zuwa Silent Zahrah. Allah sarki Yaya Sadauki ya fi kowa damuwa da rashin ganinta, ta riga ta sabarwa zuciyarsa da rayuwa da shi and yanzu take gudunsa, ya Yi tunanin har ya gaji kan me ya mata amma ya kasa fahimtar komai. Lokacin ya fara fahimtar cewa ita ɗin ƙarfin guiwarsa ce, dole ta dawo gare shi don cikar burinsa da ya ɗauri aniyar cimma su.
Alhamdulillah ya fara aiki kan neman Mama, an kama kawu wanda ke hauka tuburan daga ƙarshe dai aka sake shi ganin ba information ɗin da za a samu wurinsa. Baba Amarya da ɗiyarta Bibalo Are no where to be found. Yadda yadda so abun ya zo masa sai yake ƙoƙarin ba shi wahala and supporter ɗinsa ta guje shi, ba shi da wata maslaha da ta wuce ya dawo da ita gare shi.
Yau juma'a kuwa ya ƙuduri aniyar sanya ta a idonsa ya kuma tanadi tambayoyin sa da zai mata, dole ta amsa masa su kuma in ba haka ba.....
*Allah sarki little Zahrah Kuma Lilyn yayanta an zurma tun kafin a je ko ina, anya kuwa za ta samu cikar burin ta a yadda ta sanya damuwa cikin ranta? Kai jama'a....team Zahrah kuna ina? Yau reactions ɗin ku kamata yayi ya zo da emojin 😥 nan. Ni dai ina taya Yaya Sadauki murnar samun mace wayayya kamar Barrister Mabruka. Ko ba komai za mu yi anko, ke kuma Zahrah ki kashe kanki tunda baki da hankali....Ina team Rumana? Ku ma an doka ku, haka team Kausar ku ma ana shiri.* *Ko wanne shiri su Mami ke yi, sun ma san me ake ciki kuwa?* *Allah Sarki Rayuwa, Allah ya kawo ma kowa sauƙi.*
*Kada a mance for any inquiries ga number ta +2347061707238, ƙofar gyara a buɗe take.*
*Please react and share fisabilillah.*
# LilynYaya # YayanLily # Kausar # Rumana
[12/29, 9:56 PM] Diamond Bhatool: https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 1️⃣7️⃣
﷽
*ZAHRAH*
Baiwar Allah daren juma'a dai bacci gagararta yayi, ta rasa ina zata jefa kanta, ga shi yanzu magana ma wahala take bata bare a zo gandun hira, Nasreen ma ta yi ta gaji, har kuka sai da ta yi wa Zahrah amma ƙyam ta ƙeƙashe idanun ta. A haka har bacci ya ɗauke Nasreen ɗin.
Haka ta yi ta jera sallolints har dare ya tsala, cikin daren ta fara jin ihu sama-sama, a hankali kuma ihun ke ƙaruwa har ya kai ga ya fara damun kunnuwanta. A hankali ta miƙe tare da switching bulb Amma ba abun da ta gani, siɗaf-siɗaf ta buɗe ƙofa ta fice parlourn tana waige-waige kamar tsohuwar munafuka.
Still dai babu kowa a parlourn amma ihun nan didn't disappear. Cike da tsoro ta nufi entrance door ɗin ta buɗe ta a hankali bakinta ɗauke da addu'ar neman kariya a wurin ubangiji. Hararbar gidan ma dai babu kowa, sannan har wa lokacin nan tana jin ihun kamar a cikin kunnenta.
Ba ta gushe ba tana mai ambaton sunan Ubangiji a haka ta fara takawa tana kewaya ko'ina but nothing to be found. Da ta gaji da zagayawar kuma kunnenta ya ƙi ya daina jiyo ihun kawai ta yanke shawarar fita waje ta duba.
Duk irin tsoron da take ji haka ta kawar da shi ta murɗa lock ɗin jikin ƙofar a hankali, Allahn da ya so ta kuma ƙofar ba ta yi ƙara ba, ajiyar zuciya ta sauke tana mai ƙara ninka addu'o'in tsari bisa harshen ta. A haka ta fice ba tare da takalmi ba tana tafe tana waiwaye.
Kamar wacce aka ce wa tsaya sai ta tsaya cak da tafiyar tana mai lashe kunne don gano direction ɗin da sautin ke fitowa wanda a yanzu ya sauya amo i zuwa wani irin abu maras daɗin ji ko sauraro.
Wurin da take tsammanin daga nan sautin ke fitowa ta nufa har lokacin zuciyarta ba ta daina lugude ba amma ambaton sunam Ubangiji da take yi yasa take jin ƙarfin tunkarar wurin wanda fili ne tarwal sai kuma bishiyoyi da ciyayi masu tsayi da suka gama cike wurin.
Dakatawa ta yi tana zaro ido saboda hango wasu mutane da tayi daga nesa, mamaki sai da ya so kashe ta, ko su waye ne? Ta faɗa cikin zuciyarta. Cike da ƙarfin hali ta fara takawa cikin sanɗa har ta kusa isa ga mutanen sai kuma ta kwanta cikin ciyayin da suka fara bushewa ai kuwa wani sauti ya ɗan bayyana. Nan ta rufe bakinta da tafin hannunta tana roƙon Allah yasa ba su ji ta ba, sai dai kash sun riga sun ji.
Nan take suka waiwayo a tare. Nan take wurin yayi shiru kamar ba a wurin ake zabga wannan ihun ba. Daga can ta ji ana faɗin
“Motsi nake ji, da alama someone is here.” Sauran ma suka amsa da “Muma mun ji.”
“A kewaya a bincika, idan har hakan ta tabbata ko waye yake mana laɓe zan yi sadaukarwa ga Gutsirito don ƙara samun ƙarfin iko na samu na kammala aikin da nake kai.”
“Maza a nemo ko waye” Tunda Zahrah ta ji waɗannan maganganu hankalin ta yayi mummunan tashi, tsoro da fargaba suka yi mata dirar mikiya, banda rawa babu abun da jikinta ke yi har ta kai ga bakinta ba ya iya furta komai bare ta yi addu'a, haƙwarenta na sama da ƙasa sai karo suke ci da juna suna bada sautin ƙaƙas-ƙaƙas.
Lokaci guda mutanen da za su kai kimanin su goma suka tunkaro wurin da suka ji sautin ai kuwa nan take suka ja da baya. A dai-dai lokacin Zahrah ta sauƙe ajiyar zuciya tana faɗin “Alhamdulillah” sakamakon ƙwarin guiwar tunkarar mutanen da ta samu, lokaci ɗaya ta furta “Allahu Akbar” da ƙarfi ta yadda duk wanda ke kusa zai iya jin sautin hakan. Nan kuma ta miƙe tsaye tana ƙara maimaita kabbarta, a lokacin mutanen suka fara ja da baya saboda furucin ta na kabbara.
*(Me ya dakatar da mutanen su tunkari Zahrah a lokacin da suka gano maɓoyarta?)*
Abun da ya faru shi ne, suna tunkaro wurin da take wani irin haske mai ƙarfin gaske ya yi musu Shamaki da ita har ya kai ga idanunsu ba sa iya ganin komai sai hasken.
“Ku ƙarasa gare ta!” Wata murya ta faɗa, lokacin kuma mutanen suka yunƙuro da nufin su ƙara tunkaro ta sai dai wannan karan gani ta yi an cilla su baya kamar wasu duwatsu, ba kuma su faɗa ko'ina ba sai gaban mai ba su umarnin.
Duk da haka Zahrah ba ta yi shiru ba, duk Ayar da ta zo bakinta karanta ta take, tsoron da take ji kuwa kamar an ɗauke mata shi. Ƙara ƙarfin karatun tayi saboda jin umarnin da aka kuma basu na su yi amfani da ƙarfin ikonsu.
Ai kuwa nan suka fara furta wasu dalasimai irin wadda matsafa ke yi, ganin haka ita ma sai ta fara rairo Alqur'ani. Ƙaf suka ji na su ya tsaya saboda ita Allah ke a tare da ita ba kamar su ba. Haka suka kwashe kusan mintuna Ashirin amma abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, a harzuƙe mai bada umarnin ita ma ta zo amma hasken da ta gani yasa gabanta ya faɗi, ganin nasara na shirin kuɓuce musu ga shi kuma faɗuwa na tunkaro su yasa ta fara gwada Tata basirar sai dai ina abun fa ya ci tura.
Wannan dakikin yasa Black-devil ta fara tariyo abun da ta gani cikin madubin tsafinta wasu kwanakin da suka gabata. “Haske biyu!!” ta furta tana mai dage ƙirji, kar dai a ce duk sadaukarwa da suka yi don daƙile su ba su yi aiki ba?.
Cikin zafin rai ta umarci mutanen ta da su dawo kada ƙarfin ikon su ya ragu don fafatawa da irin waɗannan kan iya jawo hasara mafi ƙolo'uwa ga ƙungiyarsu. Bayan sun dakata ta dubi wurin da babu alamar bil'adama sai haske tace.
“Ya Isa! Mun janye makamin mu”
Cike da jarumta Zahrah tace “Shi ke nan, su waye ku? Kuma me kuke taƙama da shi? Me kuke yi cikin gidan nan?”
“Keeee! Ya isa haka, ke ko kai waye da zaki ki za ka mana wannan tambaya?”
“Kai tsaye ki kira Ni da mace, Ni ɗin baiwar Allah ce wacce tayi imani da cewa Allah ke bayarwa, ku ma ku bani amsa ta.”
“Kin ci Sa'a da yau sai na ƙwamushe ki, na sha wani kaso daga jikinki na kuma sadaukar da sauran ga Dodo na, amma duk da haka ba zan ƙyale ki ba, ke ɗin ba kowa bace Ni nan Black-devil sai na nuna miki ke banza ce.”
“Haka kika ce ko?, To mu zuba, ko ke wacece Nima Zan gano ki da kuma ƙudirin ki! Sai kuma na san dalilin da ya kawo ku gonar mutane kuna shuka sharri!”
“Dakata!” Matar ta faɗa a tsawace. “Kar ki ƙara faɗin abun da kika faɗa, Ni Black-devil ba gonar wasu nazo ba, nan ɗin masarauta ta ce! Kuma ki ajiye sai na sadaukar da jininki na gasa naman jikinli mun yi watanda da ke tunda kika ruguza min wannan rana!” Daga faɗin haka kuma gaba ɗaya mutanen suka ɓace kamar ba a halicci komai a wurin ba, banda kukan tsuntsaye da ke tashi kuma ba ka jin komai sai sautin numfashin Zahrah wanda ke fita da sauri da sauri.
Ikon Allah! Sai a wannan lokacin Zahrah ta fara jin wani tsoro na kama ta, tana kuma tsoron ta ya zata koma ɓangarensu. Wani tsumtsu ne ya wulga ta gefen ta yana tsi-tsi tsi-tsi, a yadda ta zo a tsorace haka ta fara takawa a tsorace har ta kai bakin gate ɗin, ganin ƙofar still a buɗe bai rufe ba yasa ta sauƙe ajiyar zuciya, daga nan kuma ta shiga bakinta ɗauke da addu'a. A hankali yadda kowa ba zai ji ta ba ta koma Bedroom ɗin su wanda har lokacin Nasreen baccinta take sheƙawa hankali kwance.
Ajiyar zuciya Zahrah ta sauƙe sannan ta nufi gadon ita ma don ta kwanta sai kuma kiran salla ya dakatar da ita. Nan ta wuce toilet ta Yo alwala ta zo ta hau sallaya, bayan ta yi raka'atanil fajri ma ba ta koma ba sai ta kama tasbihi har aka shiga salla tukun ta miƙe ta yi Tata sannan ta tayar da Nasreen ma tayi. Daga nan wani mahaukacin bacci ya kwashe ta.
*MORNING*
Kamar kullum Yaya Sadauki ya ɗau wankansa sannan ya fito daga Bedroom ɗinsa, da Mommah suka ci karo wacce ke shirin shiga ta tayar da shi ya yi breakfast.
“Good morning Mommah”
“Morning son, ba dai fita zaka yi ba ko?”
“Sauri nake Mommah, akwai meeting ɗin da zan shiga by 8:00 ne”
Kamar za ta yi kuka tace “Ok, to bari na sa maka breakfast ɗin sai ka wuce da shi.” Tsabagen mamaki ma kasa ce mata a'a yayi. Bayan ta haɗa ta bashi, nan yayi mata godiya ya fice. Haka kawai zuciyarsa bata ba shi ya ci ba don haka da ya fita sai yayi discarding gabaɗaya set ɗin including bottle water ɗin cikin bin, daga nan ya wuce part ɗin Hajjaty.
A can yayi breakfast ɗinsa, bayan ya gama ya miƙe har zai fita sai ya tuna da she's off today, ba sa zuwa Fridays, hakan yasa ya janyo wayarsa, Numbern Hajiya Babba ya nemo, take ya doka mata ƙira sai dai bata yi picking ba, kamar dai yayi kuka haka ya ji, amma a yadda yake ji ko me za a yi sai ya magantu da ita kafin ya cigaba da gudanar da al'amuransa.
Vibration ɗin da wayarsa ta yi yasa ya duba, ganin Hajiya Babba yasa ya katse kiran sannan ya kira ta, ko da tayi picking suka gaisa cike da girmamawa, nan yake tambayarta Zahrah. Ce masa tayi tana bacci.
Har zai datse kiran yaji ta ce “Akwai wani abu ne?”
“A'a dama Hajjaty ce tace In ta tashi a ce da ita tana neman ta.”
Hajiya Babba ta amsa masa da “To bari na tayar da ita tunda Hajjaty ke kiran.” Daga haka yayi mata godiya tare da datse kiran.
Hajiya Babba da kanta ta shiga ta tayar da Zahrahn wacce har lokacin bacci bai bar idonta ba.
“Zahrah, ki yi wanka ki karya, Hajjaty na neman ki ” Cikin Muryar bacci tace “Tooo, sai na tashi” Nan ta fara ƙoƙarin komawa baccin, fuska ɗaure Hajiya Babba tace “Am I not talking to you? Zaki miƙe ne ko kuwa?” Da sauri ta dira daga Bed ɗin ta nufi toilet.
Bayan ta yi wanka ta yi wanka ta shafa mayukanta da ta tattaro wasu ta taho da su, tana gamawa ta saka wata light blue fitted gown wacce ta matuƙar amsar jikinta, daga nan ta saka hula don ko da wasa ba ta sakaci da saka kwali ko don dukan sa tasha wurin Mamah. Sai da ta fesa turare tukun ta fito parlourn. Babu kowa sai Nasreen wacce ke kallon maimaicin series film na Habibaty man takun2 Wadda ake haskaka a mbc Bollywood.
Ba tare da Zahrah ta bi ta kanta ba ta nufi dining tayi breakfast ɗin ta, tana gamawa tayi Hamdala tare da miƙewa, sai da tazo fita ta kalli Nasreen ɗin tace “Sister, na wuce part ɗin Hajjaty. Idan Aunty Mabruka ta Zo fita tace Ina wayarta yana bedside drawer, bye!” ba ta jira amsar ta ba ta fice.
Tana fita kai tsaye ta nufi part ɗin Hajjatyn zuciyarta na bugawa musamman in ta tuna da yadda lokaci ɗaya tayi musu ƙaura sai lokaci lokaci take shigowa ta gaida su tsawon kwanaki kusan goma, karo na farko da taji bata kyauta musu ba kuma nadama ta sauƙa mata.
A hankali ta fara takawa har ta zo kusa da makeken get ɗin, kamar an ce ta kalli gefe kuma taga motarsa a gefenta, idanuwa ta zaro tana rufe bakinta da hannunta, cikin ranta kuma tana faɗin “Shi kenan ai!”
Har ta juya zata koma idan ya so bayan ya tafi ta dawo sai wata zuciyar tace “Why kike nesanta kanki da garkuwarki ne Zahrah?, Saboda zai yi aure?”
“A'a” ɗaya ɓangaren na zuciyarta ta faɗa “Bana buƙatar kusanci ne da shi saboda kada...”
“A'a Zahrah, baki yiwa kanki adalci ba In kika ce haka, meet him and apologize! That's all!”
Da wannan shawarar ta juya ta nufi ɓangaren zuciyarta na bugawa da sauri da sauri kamar za ta fasa ƙirjinta ta fito don ba shakka in ka Kura wa chest ɗin ta ido za ka ga yadda yake hawa da sauka, an indication of anxiety!
*Good night my esteem fansa, a yi bacci da minshari, saura kuma ku yi mafarkin Black-devil, babu ruwa na!* *Reat and share Fisabilillah!*
[12/30/2024, 4:31 PM] Diamond Bhatool: https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 1️⃣8️⃣
﷽
A Haka dai ta daure ta shiga ciki, lumshe idanuwanta tayi tana ƙara shaƙar ƙamshin parlourn tare da sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ganin babu kowa a parlourn...
A hankali ta fara takawa i zuwa ciki, daidai Bedroom ɗin Hajjaty ta ku, daddaɗan ƙamshin turarensa da ke kwantar da hankalin mai shaƙar sa ta jiyo, Waigawa tayi amma bata ga alamar existence ɗin wata halitta ba.
Gently ta buɗe ƙofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Hajjaty ta amsa mata fuska ɗaure.
“Ina kwana Hajjaty” “Lafiya” daga haka ta yi shiru. Ganin Hajjatyn ma kamar fushi take da ita yasa ta fara aikin lallami, da ƙyar Hajjaty ta haƙura da sharaɗin za ts tattaro kayayyakin ta dawo. Da haka Zahrah tace “Yanzu ma zan ɗauko masoyiya kakata.”
“Ke kika sani dai, wato za ki lallame ni ki sa na haƙura, ai ban gama fushin ba Zahrah'u.” ya faɗa tana cilla mata hararar wasa. “Haba uwargidan Alhaji Baba, naci albarkacin kasancewa ta ɗiyar tilon ƴar ki mace.” daga haka ta fita da sauri da nufin ta kwaso kayanta, bata aune ba taji ta ci karo da mutum. Ƙamshin turarensa tabbatar mata da cewa shi ne.
Da sauri taja baya tana dafe ƙirji yayin da idanuwanta ke zare kamar ta ji karo da zaki. Yadda ta ja bayan ne ya bashi dariya har sai da ya murmusa.
“I'm...i'm... I'm sorryyyy” ta faɗa a rarrabe tare da jan sorry ɗin. Ba tare da ya kalle ta ba ba kuma ta sa ran zai kalle ta ɗin ba.
“Follow me!” ya faɗa a zafafe sannan yayi gaba ita kuma ta bi bayansa zuciyarta na bugawa. Kan ɗaya daga cikin sofas ɗin yayi ma kansa mazauni. Jiki sanyaye ta zauna kan lallausan carpet ɗin don ko giyar wake ta sha ba zata zauna ba whole shima yana zaune ba.
Ta kai mintuna biyar zaune bata samu arziƙin ko da kallo ba. Ganin ƙafarta ta fara gajiya da zaman yasa ta ɗan gyara tare da faɗin “Yaya ga ni” Banza yayi da ita har lokacin kuma idanuwansa na lumshe kamar mai bacci. Har ta fara sarewa ga amsawar sa taji ya ce. “Ai bana gani” Hannunta biyu ta haɗe tana zaro idanuwa waje fahimtar gatse yake mata.
“I'm sorry, ina kwana.”
“Ashe kin iya gaisuwa.” ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba. Cikin ranta kuma tana ta mamakin yadda ya sauya mata lokaci ɗaya. “Is he that tough?” she asked herself.
Sai da ya gama shan ƙamshinsa tukun ya gyara zamansa. Kallonta yayi yana mai nazartar ta, ganin yadda ta rame sai ya ɗan tausaya mata yana kuma tunanin ko bata da lafiya?. Ba mai bashi amsa hakan yasa yace “What's wrong with you?” in a pitiful voice., Lokaci ɗaya ta ɗago tana kallonsa jin a irin yanayin da yayi maganar tana kuma ƙara mamakin sauyawarsa kamar ba shi bane ya gama cakume fuska ba.
“Kin san ba na maimaita magana.”
A ɗan kiɗime tace “A'a eah a'ah ai lafiya ta ƙalau me ka gani?” kallon da yayi mata yasa ta sunkuyar da kanta ƙasa.
“Idam lafiyarki ƙalau why do you look so emaciated?”
“Eh dama karatu ne shiyasa”
“Karatun ne ya ramar da ke?” ya faɗa sounding so intensed.
“E Yaya ka san an wuce ni and I want to catch up” ta ba shi amsa a shagwaɓe, yanayin yadda tayi maganar sai da yayi melting heart ɗin sa, a hankali yace “Is ok....ba wannan ba, me yasa kika raina ni ne Lily?”
“Ni!?” ta nuna kanta da yatsa tana ƙwalalo ido waje...harararta yayi yace “A'a Ni!”
Shagwaɓe fuska ta ƙara yi tana faɗin “Am sorry Yaya, wallahi ban raina ka ba, Niii Ƴar Madina na isa?” Dariya sosai ta bashi fot her last statement Amma ya dake.
“Ga shi nan kuwa In na saka miki doka ba kya bi?, Kin mayar da Ni sa'an wasanki ko?”
“Don Allah Yaya ka yi haƙuri, wallahi ba zan ƙara ba.”
“You will repeat it Lily!” ya faɗa a ɗan kausashe.
Kamar za ta yi kuka tace “Allah Yaya na tuba na bi Allah, ba Zan ƙara ba.” “Is ok” ya ba ta amsa “Zan yi haƙuri ne only on a condition.” Kafin taji condition ɗin ta amsa da “Ko mene ne na yadda”
“Is alright, the condition is....” sai Kuma yayi shiru. Ina an excited tone tace “All ears”
Gyara zamansa yayi kana ya fara magana. “Why na saka miki dokar jira na nayi dropping naki school sannan na ɗaukoki kika mayar da Ni mahaukace? 2. Why kika gudu daga nan ɓangaren zuwa can ɓangaren Hajiya Babba?”
Gabanta ne ya bada wani irin sauti, haɗuwarsu ta yanzu har ta manta damuwarta sai yanzu da yayi maganar, cikin ranta kuma tana gabza muhawara kan ta faɗa masa ne ko a'a? Daga karshe dai ta yanke shawarar binne abun a ranta.
“Don't let me repeat myself Lily.” ya faɗa sounding intensed
“Allaj Yaya ban Yi duk abubuwan da ka lissafo da wata manufa ba, infact na tattara na koma can ne to study harder as I told you earlier?”...
“Abi?” “Da gaske Yaya!” ta bashi amsa kamar za ta yi kuka. “You must be very silly Idan har an faɗa miki cewa zan yadda don karatu kika gudu! Na riga na san dalili.” Yaya Sadauki ya faɗa don ya tsoratar da ita. Idanuwa waje take kallonsa cikin ranta tana addu'ar Allah yasa ba da hatske ba ne. Zuciyarta tace “Da gaske ne tunda ya riga ya faɗa.”
Ai kawai sai Zahrah ta kwaɓe fuska sai ga hawaye shaaaa.
Tooo, tashin hankali wai ba a sa masa date. Cike da mamaki yake kallonta yana tambayar kansa me ya same ta, ko ba ta da lafiya ne?”
“Look Lily!” Ɗagowa tayi ta kalle shi da idanuwanta da suka fara ja “Na duka ki ne?” ta jijjiga kai “Da kai kile ba Ni amsar?” “A'a” “Ok tell me, me aka miki” “Nothing” ta ba shi amsa tana sunkuyar da kanta
“Lily” Ya kira sunanta, ta ba shi amsa da “Na'am” “Look In to my eyes” gagara haɗa ido ta yi da shi don a tunanin ta yanzu kam ta gama ƙare mata tunda Yaya ya gano saboda ya ce mata zai yi aure ta gudu, a lokacin ne ma ƙwaƙwalwarta ta fara aiki daidai, “To meyasa ma zata ji haushi? ” ta tambayi kanta.
“Don't let me repeat myself Lily” ya faɗa a karo na biyu sounding so authoritative. Babu yadda ta iya haka ta ɗago but she can't look straight into his eyes, who's she to do so?”
Ganin dai she's not stable yasa ya sauƙa ƙasa kusa da ita har yana iya jiyo sautin numfashin ta da ke fita da sauri da sauri. Hannunta ya riƙo ya haɗa da nasa, cike da kulawa yace “Lily tell my me ya same ki please, in ba ki faɗa min ba waye za ki faɗawa?” tabbas ya faɗi gaskiya ba ta da wanda a yanzu za ta ɗora kanta a kafaɗar sa tayi kuka, shi ɗin dai shi ne wanda zuciyarta ta saba da shi cikin ƙanƙanin lokaci, ta ya ma za ta buɗe baki ta faɗa masa yadda take ji. Nooo that's impossible.
Haka suka share kusan mintuna 15 suna fafatawa, shi ya ce ta faɗa masa damuwarta ita kuma ta nace kan babu abinda ke damunta, yadda ya nuna concern ɗinta a kanta ne yasa ta fara tausaya masa.
“Ba ki ɗauke ni yadda na ɗauke ki ba Lily shiyasa kike ganin ban kai na san damuwarki ba” “Ya yi kyau” daga haka ya miƙe da nufin wucewa. Bata san lokacin da ta riƙe ƙafafuwan ba tana faɗin “A'A Yaya, wallahi ka wuce kowa, Zauna zan faɗa maka.” murmushin gefen baki yayi kana ya koma mazauninsa tare da zuba mata shasshanyun idanuwansa. “I'm All ears, tell me what's eating you inside!”
Kanta ta sunkuyar sannan tace “Yaya dama batun Mama ne, ina tsananin kewar ta da tunanin ta.” Nan ya sa ta gaba da lallashi kan Mamah ta kusa dawowa wajensu tayi hakuri, he's still working on it. Daga haka dai aka bar zancen nan aka koma hira cikin farin ciki. Laraba dai lokaci zuwa lokaci ta kan leƙo su ta koma tana dariya tana faɗin sun dace kuwa (ba ta san ba soyayya suke ba hala?)
Har lokacin azahar yayi suna tare, Zahrah sai zuba ake shi kuma ɗan Mulkin yana murmusawa. Ganin lokacin salla ya yi yace mata zai je Masjid ya dawo, saura ya tarar ta ƙara guduwa. Dariya tayi tace “Ai ba zan ƙara ba tunda Yaya na baya so.” Murmushi yayi yana faɗin “That's good part of you!, Bye!” daga haka ya wuce masjid. Har ta yi hanyar shiga Bedroom ɗin ta kawai taji gwanda ta fara kwaso kayanta. Da haka ta wuce part ɗin Hajiya Babba, Thank God ba ta parlour iya Nasreen ce ke zaune tana aikin kallo tun safe, ba ta bi ta kanta ba ta wuce ciki, tana gama parking ta fito, har lokacin Nasreen ma kallonta hankali kwance. Ita kuwa Zahrah tana fitowa taci karo da Mami wacce da alama ɓangaren Hajjatyn ta nufa, suna haɗa ido gaban Zahrah ya bada wani irin sauti amma sai ta kauda kai sannan ta ƙarasa kusa da ita.
“Sannu Mami, Ina yini.” Duk da cewa Mami ba kallon ƙurulla tayiwa Zahrah ba amma sai da gabanta ya buga, tsoronta Allah tsoronta kada kayan Zahrah ya ɗebi Sadauki yace da ita za a yi aure don tuna ranar da tagansu tare ranta ke ƙuna ganin yarinya ƙarama na shirin yi mata katanga da abun harinta.
“Mami” Zahrah ta faɗa a karo na biyu. Da yake wasu matan akwai iya ɓoye abu sai ta fara murmushi tana faɗin “A'ah Zahrahn Hajjaty ne? Ina kika je haka?” Zahrah ta bata amsa da “Na je ɗauko kaya ne daga ɓangaren Hajiya Babba.” sai kuma ta nuna mata kayan da ke hannunta.
Cike da son gulma tace “Kayan na waye” Zahrah ta amsa mata da “Na Nasreen ne Hajjaty tace ta bani” “Na gode Allah” ta faɗa a ranta a zahiri kuma tace “Hala ba ki da kaya da yawa ne har sai sun baki?” duk da maganar ta ba ta haushi amma sai ta dake don tana buƙatar ƙara fahimtar matar. Dariya tayi tana faɗin “E wallahi Hajjaty ta ce dai za ta sa a ɗinko min amma na karɓo waɗannan ɗin.”
An zo wajen, Mami ta murmusa tana faɗin “Kin ga ki ɗauke Ni kamar Maman ki Zahrah, kina da buƙatar abu ba za ki samu Ni ba?” shaye da mamaki Zahrah ke kallonta tana kuma tunawa in dai ba mantawa ta yi ba first contact ɗin ta da matar nan a part ɗin Mommah kallon tsanatake mata amma da yake mata iyayen kaidi ne ji abinda take faɗi.
Zahrah na da wayo duk da ƙarancin shekarunta amma kuma in ta sa abu gaba sai ta yi. Saboda haka ita ma sai ta sunkuyar da kai kasa tana faɗin. “Na gode Mami, Allah ya ƙara girma.” Murmushin cin nasara Mami tayi tana amsawa Zahrah da “Amin” Daidai lokacin kuma suka iso part ɗin Hajjatyn. Daga nan kuma Mani tayi shiru bata ƙara cewa komai ba. Ko da suka shiga direct bedroom ɗin ta ta wuce ta ajiye kayan sannan ta fito don ganin sauran scene ɗin Mami.
Ganin Yaya Sadauki bai dawo ba yasa ta koma kusan Mami ta Zauna fuskarta sake. Sai da Mami ta juya taga babu kowa tukun tace “Saura kuma naga ba kya zuwa wurin nawa.” Kan ta ƙasa ta amsa da “Zan zo In Sha Allah Mami.” Daga haka hirar ta tsaya saboda fitowar Hajjaty.
Nan suka gaisa cike da girmamawa kamar ba Mami ba, Hajjaty dai mamakin ta bai ɓuya ba ganin abun da bata saba ba. Zahrah kuwa ƙimis tayi ta ƙi ba su wuri, tana so a yi kai gabanta, she wants to feel that she's one of them.
*Afwan My esteem people, Kuna ta jiran update ban yi ba sakamakon ayyuka da suka sha kaina. I'm sorry ga shi nan na yi muku, a taimaka a taya Ni sharing tare da reacting.* *Na gode da ƙaunarku gare Ni and I appreciated it, thank you so much, love you irin sosai ɗin nan.* [12/31/2024, 2:31 PM] Diamond Bhatool: https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 1️⃣9️⃣
﷽
“Hajjaty dama na yi dahuwar kaji ne kuma na ga kina so shi ne nace bari na kawo miki.” Mami ta faɗa tana miƙewa tsaye tare da miƙewa Hajjaty food flask ɗin har da rusinawa kamar ta Allah.
“To madallah, sannu da ƙoƙari Baraka, Allah ya saka.” Mami ta amsa da “Amin”. Hajjaty na shirin ficewa Mami ta dakatar da ita “A'a Hajjaty wurin ki fa nazo.” “To bari na kai abun nan kitchen.” “Hajjaty ai ga Zahrah ki ba ta kawai, ke Zahrah karɓi ki kai, Babba ba ya aiki in da yaro kusa kin ji?”
Kai Zahrah ta ɗaga daga nan ta wuce kitchen kamar yadda Mami ta so. Tana ajiyewa ta juyo da sauri. Isowar ta ya yi daidai da lokacin da Hajjaty ta yi magana. “Ban gane ba Baraka” Ƙasa-ƙasa Mami ta Yi maganar ya yadda Zahrah ba ta iya jin komai. Kamar za ta fasa ihu haka ta koma Bedroom ɗin ta tana cije baki.
Shigowarsa kenan ya ci karo da fuskar Mami a tare da Hajjaty kuma, nan ya fara tambayar kansa ko me ya kawo ta? Har ya yi nufin juyawa wata zuciyar ta hana shi, gyaran murya ya yi wacce ta yi indicating presence na shi.
Kama wata tsohuwar munafuka Mami ta fara zaro idanuwa. “A'a Aliyu ne?” ta faɗa tana washe baki. Ba tare da ya kalle ta ba yace “Good afternoon” Bai jira amsawarta ba ya wuce zuwa Bedroom ɗin Hajjaty tunda abokin hirar tasa ba ya nan. Cikin ransa har yanzu ganin matar nan ya buge shi, ko wanne munafurcin take ƙullawa oho mata.
Da hararar Zahrah ta raka Mami da za ta fita daga nan kuma ta ƙarasa wurin Hajjaty tana faɗin “Hajjaty dama Mamin su Ya Faruq tana shigowa nan? Ko gaisuwa ban taɓa ganin ta shigo ta miki ba”
Murmushi irin na manya Hajjaty ta yi kana ta ce “Zahra'u ashe kema kin iya sa ido ban sani ba?,”
A shagwaɓe Zahrah tace “Ba wani nan Hajjaty, ai dole na sa ido kan duk wani mai zuwa tun da dai noma I belonged to the place.”
“Za ki yi bayani ai, kin ga shiga ciki ki kira Yayanku ya zo ya yi lunch.”
“Yaya kuma? Ya shigo ne?”
“Ban sani ba, kar ki cika Ni da surutu, wuce ki je”
Daga haka Zahrah ta wuce tana tura baki wai Hajjaty ta nata faɗa, lokacin da ta shiga ba ta yi sallama ba ganin yana kwance kamar bacci yake, murmushi tayi tare da juyawa, taku ɗaya biyu ya dakatar da ita
Juyowa tayi tana kame kame “Dama ba bacci kake ba Yaya? E Hajjaty ce tace ka fito ka ci abinci”
“Ok wait for me”
Tare suka yi lunch ɗin su daga nan ya mata sallar zai wuce office ɗinsa.
Tun bayan tafiyarsa Zahrah ke tariyowa abun da ya faru da ita a daren jiya, gani take kamar mafarki tayi amma tunawa da alwashin matar da ta kira kanta da Black-devil yasa ta ƙara tabbatarwa kanta a zahiri abun ya faru. Tunaninta a yanzu ya ta'allaka ne ga don gano wacece wannan Black Devil Kuma meme ne ƙudirin ta ga ahalin nan, amma me? She need someone that'll support her.
A da ta yi tunanin Nasreen sai kuma ta fasa, haka ta yi ta ɗaura mutanen da ta sani kan mizanin amma babu wadda ta ga ya cancanci wannan matsayi na sa rayuwarsa a kasada musamman da ta gano abun Black-devil na da alaƙa da Cultism. “No!” ta faɗa a zahiri “I won't put any one's life in danger, I'll support myself ko da zan mutu sai na gano wace ce ita!”
“Amma ai a'a buƙatar wani ya san al'amarin nan, amma za a gaskata Ni kuwa? If yes waye zai yadda da Ni?”
Zuciyarta ta na ta amsa da “Yaya Sadauki” Idanuwa ta zaro kamar dai tana gabansa ta maimaita sunansa da zuciyarta ta ambata. Cike da karfafa mata guiwa zuciyarta tace “Yes Zahrah! Yaya Sadauki ne kaɗai zai iya yadda da ke ka ya zamo garkuwarki har ki cimma nasara a muradun ki, ina tabbatar miki he'll be there for you kamar yadda yake faɗa.”
Safe kanta ta yi jin shawarar da zuciyarta ke ba ta, kan ta ta gyaɗa alamar na'am sai kuma ta fesar da wata zazzafar iska. “Feel free Zahrah! Calm and relax” Nan ta ja numfashi ta fesar. “Yes! Zan mishi magana” ta faɗa a bayyane. Ganin dai tunanin nan ba barinta zai yi na ga shi kuma ƙwaƙwalwarta na shirin fashewa saboda tunani yasa ta miƙe ta nufi parlour tare da kunna kallo, this is her first time to sit in the parlourn da niyyar kallo. Ko da ta kunna na ba fahimtar komai take ba coz her mind was taken away.
Da yamma Alhaji Baba ya dawo dama ya je wurin makoki mara abokinsa da ya rasu yau ɗin. Ko da ya huta ya a Hajjaty a ƙara yawan dinner without telling her the exact reason.
*BAUCHIN YAKUBU, ƘARAMAR HUKUMAR TORO*
Alhamdulillah za a ce, sauƙi ya fara samuwa ga matar da Inna ke kula da ita tare da ƴan jikokin ta. Yau ma kamar kullum zaune suke su uku, Asma'u, Inna sai kuma Maras lafiyar da ke bin su da ido suna hira, yanayin yadda yake kallon su zai tabbatar maka da cewa ba abinda take fahimta a ciki sai dai kuma suna sanya ta cikin hirar saboda ita a yadda Inna fahimci ciwon Amina (Sunan da suka laƙana mata.) Bai wuce gushewar tunanin ta da kuma hankali ba wanda ke da alaƙa da sihiri ko sammu.
Balkisu tace “Inna har yau dai Malam Sufin bai zo ba, ina tausayawa Baba Amina wallahi, gaskiya Inna me zai hana mu ku ta can ɗin la'alla shi ba shi da lokacin zuwa, ko ya kika ce Asma'u?”
“E wallahi Inna, gobe mu shirya kawai muje can ɗin.” kalaman su sun taɓa zuciyar Inna, hakn ya sa ta yanke shawarar zuwa ganin Malam Sufin ɗin tare da Amina.
Washegari kuwa suka niƙi hanya sai Tafawaɓalewa don kai Amina wurin Mallam Sufi ko Allah zai sa a dace kamar kowa ita ma ta rayu cikin farin cikin.
*GRA, BAUCHI*
Cikin jerin gwanon gidajen da suka amsa sunan gida motar ta fito, bayan fitar ta free man ya rufe ƙatoton gare ɗin hakan ya sa ban samu damar kutsa kai cikin ba sai na bi motar don ganin ina za ta.
Unguwar Zango ta nufa kai tsaye, dai-dai wani gida wanda in ban manta ba gidan Idrisu ne!
Wane ne wannan kuma? Kafafuwansa ya ziro don fitowa, kamar wani basarake haka yake taku yayin da fuskar sa ke sanye da face mask Amma tsaro da yanayin jikinsa uwa uba kuma yanayin dressing ɗinsa zai tabbatar wa mai karatu da cikar izzarsa, da gani ka matashin ba zai wuce shekara 29-30 ba.
Takawa ya ci gaba da yi har isa daidai kofar gidan da ke sanye da kwaɗo. Tsaki ya ja tare da ƙara nazartar kwaɗon wadda alamun an jima da maƙala sa ta bayyana saboda yadda yake cijewa ga kuma tsatsar da ke jiki.
“Ya Allah!” ya furta yana dafe kansa tare da addu'ar Allah yasa dai ba tashi suka yi ba. Nan ya ga wani mutumin da sauri ya ƙarasa gunsa yana faɗin “Am sannu da rana Malam.” “Yauwa sannu ɗan saurayi”
“Baba don Allah tambaya nake” ɗan tsohon ya amsa da “Allah ya sa na sani.”
Gyara tsayuwar sa yayi sannan ya nuna masa gidan da ke kallonsu. “Baba don Allah masu gidan nan ko sun yi ƙaura ne?” Tsohon yace “E to ba zan ce kamai ba amma dai kwanaki na ji mai ɗaki na tana faɗin ko matar gidan ce aka sace ko meye, amaryar gidan kuma kamar dai sun sayar gidan ita da ƴar ta sunyi gaba.”
Zuciyar matashin ne ya tsananta Bugu sakamakon zancen da yake ji daga wurin tsoho. Tattara jarunta da ke shirin barin gangar jikinsa ya yi sannan yace “To Baba, shi Mai gidan fa?” “Ai yaro bari in gajarta maka zancen nan, shima Mai gidan babu wanda yasan ina yake.”
“Shikenan ba gode Baba, ga wannan” Ya faɗa yana miƙo masa kuɗin da ke jikinsa, nan tsoho ya fara godiya, ba tare da ta saurari godiyar ba ya masa sallama tare da nufar motarsa fuskarsa na nuna tsantsar tashin hankali da damuwa, a haka ta figi motar, bai tsaya ko ina ba dai gidansu. Ko da ya Yi parking sai ga Guards ɗin sa sun kewaye shi to see if he's alright saboda taka tsan-tsan da suke da aikin su. Uban gidansu ya musu warning kan shalelen ɗansa, saboda haka ko da ya ce ba zai fita da su ba zaman addu'ar Allah ya dawo da shi lafiya suke yi.
Wannan kenan!
*ABATCHA ESTATE*
*Yayan Lily*
Bayan sallar maghrib ya dawo, kai tsaye part ɗin su ya wuce, sai da yayi wanka tukun ya fito, lokacin kuma Mommah na zaune parlourn ta caɓa uban ado ga kuma yadda ta make fuska babu annuri. Tana ganin fitowar sa ta nufi inda yake. “Aliyu!” ya dakata jin ta ambaci sunansa sai kuma ya waiwayo yana smiling “Sannu da gida Mommah” Ba tare da ta amsa masa ba sai ma cakushe fuska da ta ƙara yi tace “Aliyu sau nawa zan faɗa maka cewa ka cire zancen auren wannan ƴar iskar a ranka? Me yasa ba ka jin magana ta? Remember Ni Mahaifiyarka ce K kumaum ina da ikon hana wannan auren. Wallahi tun muna shaida juna da arziƙi ka ce musu ka janye!”
Lumshe idanuwansa ya yi ya buɗe waɗanda lokaci guda kuma suka yi jawur, ya gaji da irin wannan hali na mahaifiyarsa, ƙoƙarin controlling temper ɗinsa yayi sannan ya kwantar da Murya “Mommah Please, ah beg you ki daina batun janye aure, Sanin kan ki ne fa Alhaji Baba da kansa ya yi wannan hukuncin kuma babu wanda ya isa ya ja da shi kin sani, so Please Mommah ki kwantar da hankalin ki kawai ki rungumi ƙaddara.”
A hasale tace “Na kwantar da hankali na fa kace Aliyu! Ka san kuwa me kake faɗi?”
Ganin ta hau da yawa yasa ya ja hannunta ya zaunar da ita kan ɗaya daga cikin kujerun da ke parlourn sannan ya ɗauki cup da ke kan Centre table ya tsiyaya mata ruwa yana miƙa mata. “Have this” ganin tana bukatar ruwa yasa ta amsa ta kafa kai, tas ta shanye sannan ta miƙa masa cup ɗin. Ajiyewa yayi shima sai ya zauna gefenta tare da riƙo hannunta, motherhood bond is different, tuni ta fashe da kuka tana faɗin.
“Ni yanzu shikenan so kake na kashe kaina kafin ka haƙura da auren?” ta faɗa sounding so serious. “Ba Haka ba nee Mommah, get one thing please, cewa sai an fasa aure kin san ba mai yiwuwa ba ne tunda Alhaji da.....”
Katse shi tayi tana ɗaga masa hannu “Ya isa haka Aliyu! Na gaji da jin fasawa ba zai yiwu ba, na gaji! sai cewa kake Alhaji Baba ne ya yanke hukunci ba zai yiwu ba nace shi Alhaji Baban Allah ne In ya yi hukunci dole a bi? Nace shi ya haifa min haifa min kai ne da zai ke nuna ikonsa a kanka, let him show his power only on his children muma ya bar mu muyi iko da namu!” ta idasa tana share ƙwallar da ke zubo mata.
Handkerchief ɗin sa ya ɗauko yana share mata hawayen “Is ok Mommah, ya isa kukan kada ki ja ma kanki ciwo, ina riƙon ki da Allah ku kwantar da hankalin ki kada ki yi abun da za ki zubar da ƙimarki cikin gidan nan.”
A ɗan zafafe tace “Aliyu ƙima? Maganar ƙima naji kana yi? To ai already ba Ni da ita a gidan nan, Im da a ce ina da ita ai da ba za a yanke hukunci a kan dab na ba tare da an bani damar amincewa ko akasin hakan ba. Wallahi Aliyu ko igiyoyin aure na za su tsinke wallahi ba zan bari a yi auren nan ba.”
Tana faɗin haka ta tashi fuu ta nufi Bedroom ɗinta yayin da ta bar Yaya Sadauki kamar statue. Miƙewa shima yayi jiki ba ƙwari ya fice. Direct Masjid ya tafi ko da aka isar kamar kullum ya biyo su Alhaji Baba suka taho tare da sauran Uncles ɗin shi har da waɗanda bai yi tsammanin gani ba. Ko da suka isa a an parlourn suka yada zango har Hajjaty ta fito suka gaisa sannan shima da ke zaune kan carpet ya gaida Uncles ɗin nashi.
Alhaji Baba ne ya unarve su da su tashi a ci abinci sai a lokacin Hajjaty ta lura da ba Zahrah a wajen. Ba ta ce komai ba ta je ta kira Zahrah. A tare suka ƙaraso Zahrah ta ja ma Hajjaty kujera, bayan ya zauna ta fara gaida Uncles ɗin ta suka amsa fuska sake, nan ya Yi serving kowa including her Heart's desire 😳.
*Na san kuna da tarin tambayoyi gare Ni my esteem readers, ku dai kawai mu je zuwa.* _React and share please._
[12/31/2024, 10:17 PM] Diamond Bhatool:
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 2️⃣0️⃣
﷽
Bayan sun gama dinner dukkan su suka dawo parlourn kamar yadda yake. Alhaji Baba bai ware kowa ba, kai tsaye ya fara magana kan dalilin tara su.
“Kamar yadda kuka sani irin wannan kira na gaggawa na ɗauke da ma'anoni mabanbanta, haka zalika yau ma dai na ƙara tara ku saboda wani muhimmin batu, ɓarakar da aka samu a kwanakin baya tsakanin Sadauki da kuma Mabruka ƴar wajen Sadiƙu, na san dukkan ku abun ha jijjiga ku musamman iyaye a ɓangare biyun, ko da ba su nuna wa juna ba tabbas zukatan su sun munana. Dalilin haka ya sa na yanke hukuncin ɗaura aure a tsakaninsu bayan tabbatar da cewa babu komai ɗin da ya faru kawai shiri ne na maƙiya, sai na ga mu toshe bakin maƙiya ta hanyar haɗa auren su zai fi. Ya kuke gani a matsayin ku na iyaye?”
Cike da biyayya kowannensu yayi na'am da hukuncin Alhaji Baba, Nan ya ƙara da faɗin. “Ma sha Allah, ina ƙara godewa Allah da ya bani ƴaƴa masu tarbiyya waɗanda ba su taɓa ja da hukuncin da na zartar, Ubangiji ya baku masu yi muku biyayya kwatankwacin yadda kuka min.” Nan suka amsa da “Amin!” Alhaji Baba ya ɗaura da “Saboda gabatowar azumi nan da wata ɗaya, na yanke ranar bikin cikin makonni biyu ma su zuwa, kowa sai ya fara shirye-shirye.”
Nan gaba ɗaya su Daddy, Appa, Abie da sauran suka fara addu'ar Allah ya sanya alkhairi. Daga nan kuma suka fara taɗin su na ƴaƴan da iyaye.
*Ina Zahrah?*
Tun da ta fahimci akwai abun da za a tattauna ta fara tashi daga dining ɗin sai ta fice daga apartment ɗin ta tsaya bakin ƙofar saboda ta samu damar ji. (Babu kyau gulma fa Zahrah?” A lokacin da ta ji Alhaji Baba ya ce an yanke ranar bikin Yayanta in 2weeks time ji ta yi kamar an ɗiga mata wani tafasasshen ruwa a zuciyarta. A zabure ta fice ta zagaya ta ƙofar baya, da ƙyar da taimakon Ubangiji ta isa Bedroom ɗinta.
Tana shiga ta faɗa kan Bed ɗin ta tare da fashewa da wani matsanancin kuka, ta rasa ina za ta jefa ranta ta ji sanyi a duniyar nan, ga shi babu kafaɗar wanda za ta kwanta ta zubda ƙwallarta. Nan zuciyarta ta fara tariyo mata moments ɗin da yayanta, why ta yi sauri falling in to his love? Ashe son sa take tsawon lokacin nan?
“No, ba na sonsa, kawai dai ɗan'uwa na ne!” ta faɗa a bayyane. Da sauri zuciyarta ta ƙaryata ta da faɗin “Idan har you're not in love with him why kike jin kishinsa?” Da sauri ta furta “Kishi? Kishinsa nake?, Noooooo!” ta faɗa tana buga pillown da ke hannunta “That's impossible!”
Zuciyarta ta ƙara ce mata “Is Possible Zahrah, ki dawo hankalin ki, idan ba kishi ba ne why kike jin zafin aurensa?” “Wayyooo Allah...” ta faɗa tana dafe kanta da hannayen ta biyu sakamakon yadda kan nata ke juyawa. Daga haka kuma ta yi luuuu ta koma ta baya kamar wacce aka zarewa rai.
Hot love kenan! Su Zahrah yau an yi ƙaramar hauka.
**************************************
Fitowa yayi daga motar kamar wadda aka zarewa laka, a haka ya shiga ciki, Thanks to Allah bai tarar da kowa ba kamar yadda yayi tsammani, a haka ya fara haye benen har ƙafarsa na harɗewa. Daidai Bedroom ɗin da ke nuna mallakinsa ne ya murɗa handle tare da shigewa. Ba tare da ya zare mask ɗin sa ba ya faɗa Bed ɗin.
Numfashin sa ne ke ƙoƙarin kokawa yana shirin barin gangar jikinsa, da ƙyar ya iya cire mask ɗin. Ai ba shiri mai ɗauko report ta ja baya ganin fuskarsa. Yaya Ishaq ne tabbas sai dai ba wancan Ishaq ɗin da mai karatu ya sani a baya ba ne, wannan Ishaq ɗin wayewa ta bayyana tsantsa a fuskarsa duk da yana cikin tashin hankali.
Wani irin numfashi yake ja tare da fesarwa yana kuma juyi kan katafaren Bed ɗin sa. “Why angel? Why? Ina kika tafi kika bar Ni? Angel angel! Ko'ina kike in dai a doron duniya kike sai na nemo ki, ke ɗin rayuwa ta ce, na so ko tun baki san kanki ba, ina sonki har yanzu kuma zan kasance mai cigaba da son ki har zuwa numfashi na na ƙarshe, to my last breath angel.!” ya idasa yana fashewa da kuka mai tsuma zuciya.
Wai dama haka so yake? Haka so yake dama? Idan haka so yake baya yi wa wasu mutanen adalci a rayuwa duba da yadda yake kai su ga rasa jin daɗi, da yawa sun rasa nutsuwarsu saboda so, wasu sukan rasa hankalin su su koma tamkar mahaukata, wasu sukan rasa dukiyarsu da muƙamin su saboda so, wasu kuma iyalinsu da abokai kan juya musu baya dalilin so, so so! Wasu kuma sukan rasa wani sashe daga jikinsu, wani so kan zama sanadiyyar makancewarsa, wani kuma sanadiyyar kurumcewarsa, wani sanadiyyar rasa ɗanɗanon bakinsa wani kuma kan rasa rayuwar sa gaba ɗaya. Tabbas so cuta ce ga duk wanda bai yi dace ba ko kuma ɗaya daga cikin abubuwan nan suka same shi silar sa.
Miƙewa Yaya Ishaq yayi da ƙyar saboda yadda yake ganin dishi-dishi, wayarsa ce ta nuna buƙatar agaji yayin da sautin ringing ɗin ya karaɗe ɗakin, waƙar Saleem Smart ne dai-dai wurin da yake cewa. Haka so yake dama, ya maida kai bawa.......
Sauraran waƙar ya ci gaba da yi har ƙiran ya yanke.
_Flash back_
Masu karatu za su ce tun da Yaya Ishaq ya tafi bai ƙara neman Zahrah ba tsawon waɗannan shekaru! Abun da ya faru shine, bayan tafiyarsa karatu bai taɓa mancewa da Zahrah ba tsawon wannan lokaci, kullum cikin tunani da kewarta yake ga shi ba shi da wani abu nata da zai ɗebe masa kewa sai pictures ɗin ta guda uku.
Bayan ya kammala karatu kuma Daddynsa tare da Mom ɗinsa suka yi residing a can saboda hare-haren da ake kaiwa mahaifin nasa, ya kuma kafa masa dokar babu shi babu Nigeria har sai In tare za su je, shi kuma ba shi da ranar zuwa.
A haka soyayyar Zahrah ta ci gaba da kama zuciyarsa har ta kai ga ta yi masa kamun da ba zai iya cire kansa ba, tun yana ɓoyewa har abun ya fara yawa har da su kwanciya jinya.
Wannan karon ma ganin in har ba su bar shi ya zo ya ga angel ɗin sa ba za a samu matsala saboda likitan da je kula da shi ya sanar da su lallai in ba a Masa abun da yake so ba zai iya rasa ransa.
Hakan ya sa babu shiri Daddynsa yayi booking Musu flight suka diro Nigeria duka kuma sauƙa gidansa da ke GRA, a ranar ya so ya tafi don ganin Angel ɗin sa amma suka ba shi haƙuri ya bari sai washe gari. Wannan shi ne taƙaitaccen bayanin abun da ya faru bayan tafiyar ya Ishaq.
_To the story...._
*SADAUKI'S POV*
Tunda Alhaji Baba ya gama magana ya sulale ya bar parlourn ba tare da sun kula ba, kai tsaye part ɗin su ya wuce don ya kwanta in b haka ba yada zuciyarsa ke wani irin mahaukacin bugu da sauri da sauri ba lallai gangar jikinsa ta iya ɗaukar sa ba, the amazing part of it is that Sam ba ya so ko kaɗan iyayensa su fahimci cewar kawai sadaukarwa ce yake son yi musamman Alhaji Babba, wanda duk cikin gidan babu mai ƙaunarsa kwatankwacin yadda yake kai har mahaifin da ya haife shi, idan har ya fahimci baya so to tabbas auren nan sunan sa an fasa.
Ko wankan da ya saba yau bai yi ba, kan Bed ɗin sa ya faɗa yana dafe saitin heart ɗin sa, ba zai ce ba ya son auren ba sai dai kuma yana jin wani iri, yana ji kamar akwai wata zuciyar da ta fi buƙatar aurensa fiye da Mabruka, yana jin anya ya yi wa wannan zuciya adalci?.
“Who's that person?” ya tambayi kansa. Tashin mafita ga kuma tunani da ya sa shi gaba kamar ya haukatar da shi yasa ya miƙe a daddafe ya shiga toilet tare da ɗauro alwala. Nan ya yi ta jera nafilfilu ba adadi yana kai kukansa ga mai sama tare da neman ya masa zaɓi mafi alkhairi.
*MAMI*
Da yake duk matan babu wanda ya san da dawowar Abba ko da ya shigo a main parlour ya sauƙa, lokacin kuma dukka matan na zaune a parlourn kowacce ta hakimce sai hura hanci take.
Small Mom dama can ita ta iya kula da miji da sauri ta miƙe tana masa sannu da dawowa, shi ma ya amsa, ganin dai Mami ko alamar furta A ba ta da shi yasa ya jijjiga kansa yana mata addu'ar shiriya.
“Baraka!” Abba ya ƙira sunanta Ɗagowa tayi ta kalle shi sannan ta mayar da kanta. “Kina gani na amma ko sannun da dawowa babu? Kina ganin hakan daidai ne?” “Haba Abban Faruq, ya za a yi ka titsiye Ni gaban wannan matar hakan daidai ne?”
“Ka ga Alhaji na, ka ƙyale ta kada ta ɓata maka ranarka while you look so happy I can see, mu je ka watsa ruwa ka ci abinci.”
“To ƴar'iska! A gaba na kike karuwancin naki ko? Hehehehe! Sai ki faɗa min wane dare ne jamage bai gani ba!”
Small Mom ba ta bi ta kanta ba ta ja hannun mijinta ta bar Mami sai harare harare take tana magana ita ɗaya kamar mahaukaciya.
Ba ta bar parlourn ba kuma sai da ta suka fito. Nan taji Abban na faɗawa Small Mom cewa an saka bikin Sadauki da Mabruka, sosai ta yi murna yayin da Mami ta miƙe tsaye a zafafe tace “Ba zai yiwu ba! Dole na tarwatsa auren nan don Sadauki ba shi da matar da ta wuce Kausar”
Kallon ba ki da hankali Abba ya cilla mata sannan yace “Dama can ke ba hankali gare ki ba Baraka, sai ki tarwatsa auren, nace bismillah ki tarwatsa auren in kin cika ƴar halak” rai ɓace kuma ya wuce zuwa turakarsa da ke jikin main parlourn.
Da harara Mami ta bi shi tana faɗin “Zan kuwa tabbatar maka Ni na cika Baraka Abban Faruq!” Cike da mamaki Small Mom ke kallonta sannan ta miƙe tsaye tana faɗin “To iyayen haddasa, a dai sano hassada ga mai rabi taki ce! Mtsss” daga haka ta bi bayan Abba. Ita kuwa Mami kamar mahaukaciya ta fice ta nufi part ɗin ta tana tunanin ta ya za ta yi ta tarwatsa wannan aure!
*Ammie*
Wani lukutin bala'i, Part ɗin Papa ma dai haka aka gwabza bala'i don Ammie rasa nutsuwarta ta yi bayan jin bayani daga bakin Papa, ita dai Mimie fatan alkairi tayi musu tana nuna tsantsar farin cikin ta, tun da Papa ya ga yadda ta yi reacting tare da ficewa a hasale ya sa Ayar tambaya kan ta.
Haka ta faru a sauran sassan gidan kuma ko ina shigen abun da ke faruwa, sauran matan da ba su ƙulli kowacce da sharri ba taya su murna tare da musu fatan alheri.
*Hajiya Babba*
A lokacin da Alhaji Babba ya shigo gidan fuska sake ya tadda su a main parlourn gidan ne saɓanin sauran sassan gidan, a nan hirarsu suke gaba-dayan su, yaran kuma na wasan su.
Shigowarsa yasa yaran suka nutsu, ƙananan cikin su suka rungume shi suna oyoyooo Alhaji. Da farin ciki ga amsa musu sannan ya yi wa kansa mazauni a parlourn, nan duk matansa suka masa sannu da dawowa.
Hajiya Babba ya kalla yace “Ina Mabruka ne?” Hajiya Amina da ta kasance uwar ɗakin ta tace “Tana ciki, Meerah, maza kira Auntynku ki ce mata Alhaji na kiranta.” Da gudu ta zuwa parlourn Hajiya Amina don kiranta.
Kallonsa suka yi ganin yadda fuskarsa ke nuna farin ciki Hajiya Karima ta ce “Babbansu yau dai alamun kana cikin farin ciki” ta ƙarasa cikin sigar zolaya. Murmushi yayi yana faɗin “Ba shakka, ina cikin farin ciki maras musaltuwa.....” katsewa yayi sakamakon shigowar Mabruka parlourn wacce ta tsugunna gabansa kan ta ƙasa. “Sannu da dawowa Alhaji, An yini lafiya?” Fuska sake ya amsa mata da “Lafiya ƙalau Mabruka, ya aikin?” “Alhamdulillah” ta ba shi amsa. Shiru parlourn ya ɗauka na wani lokacin kafin Alhaji Babba ya gyara zamansa tare da gyaran murya.
💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃 _Yanzu ma aka fara! Yanzu ma aka fara, kuna jin wata lukurar Masifa kuwa people? Gaskiya akwai ban tausayi sosai musamman ga love birds ɗin nan, fatan mu Allah ya sa abun ya zo da sauƙi._
*Masoya littafin A babban Gida musamman followers ɗin ~DBRC~ waɗanda ke ƙarfafa min guiwa da reacting wadda ke nuna zallar soyayyar su gare Ni da alƙalami na ina godiya, alkhairin Ubangiji ya kai gare ku a duk yadda kuke, tabbas ina ƙaunar ku ƙauna ta gaskiya kuma saboda Allah.* *Sannan waɗanda ke min comments daga wasu groups ɗin da kuma na musamman masu min ta PC Allah ya saka muku da alkhairi, kar ku manta ko yaushe ƙofar gyara a buɗe take Habibties, zaku iya samu na kai tsaye ta +2347061707238 ina godiya sosai* *Love You all.*
[1/11, 7:14 PM] Diamond Bhatool:
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 2️⃣1️⃣
_For those willing to be updated about this book should kindly follow my channel, a can kaɗai nake update yanzu._
﷽
“Hajiya Ruƙayya, Hajiya Karima da kuma Hajiya Amina.” “Sai kuma ke Mabruka na tara ku ne a nan ba don komai ba sai don na sanar da ku abun farin ciki da ya tunkaro mu.” Gaban Mabruka ne ya bada wani irin sauti mai karfin gaske wanda har fuskarta sai da ta bayyana hakan. Babu wanda yace komai hakan ya ba wa Alhaji Babba damar cigaba da jawabinsa.
“A matsayin ku na iyaye ga yarinya ina fatan za ku yi farin ciki da abun da zan faɗa, ke kuma Mabruka” ya nuna ta da hannunsa wanda har lokacin kanta ke duƙe. “Ina fatan za ki biyayya a kan wannan hukunci.” nan gabanta ya ƙara bugawa
“A yau Alhaji Baba ya yanke auren Mabruka da kuma Sadauki cikin makonni biyu masu zuwa in Sha Allah, sai ku fara shirye-shiryen bikin, zan tura muku kuɗi ta a account ɗin Ruƙayya, In da buƙatar ƙari sai ku min magana.
A hankali ta ɗago jajayen idanuwanta ta dubi Alhaji Babba ta furta “Allah ya Ƙara girma Alhaji.” daga haka kuma ta bar parlourn da gudu har tana shirin faɗuwa sakamakon karo da Humaira da suka yi. Da kallon mamaki Humaira ta bi ta wondering why is Aunty Mabruka acting so strange, Nan ita ma gaban ta ya ba da wani irin sauti, daga nan ta ƙaraso, a lokacin su Hajiya Babba duk sun tashi, iya su Meerah ne zaune. Fuska ɗaure Humaira ta kalli Meerah tace “Meerah me ya samu Mabruka?” Meerah ta amsa mata da “Albishir Aunty Humaira! Saura sati biyu bikin Aunty Mabruka da Yaya Sadauki.”
Gaban Humaira ne ya ba da wani irin sauti, bata tsaya idasa jin zancen Meerah ba ta wuce Bedroom ɗin Hajiya Babba da sauri yayin da numfashin ta ke kokawa don ya bar gangar jikinta. Da taimakon Allah ta idasa shiga, yanayin yadda ta tura kofar ne ma ya sa Hajiya Babba juyowa don ganin waye. Yanayin da ta ga Humaira ya ɗaga mata hankali amma sai ta dake tana bin ta da kallo har ta iso wurin da take. Kanta ta ɗaura kan cinyar Hajiya Babba tare da fashewa da wani irin azababben kuka.
Cike da kulawa Hajiya Babba ke shafa bayanta ba tare da ta ce mata komai ba, sai da ta yi kukan ta ta fara sauƙe ajiyar zuciya tukun Hajiya Babba ta ɗago ta yayin da fuskar su ke kallon ta juna. “Lafiya Humaira?” kamar jira dama take taji an tambaye ta sai ta ƙara fashewa da wani kukan, ba tare da ta yi shiru ba ta fara magana wacce ba a gane me take faɗi. “Kin ga calm down Humaira, faɗa min me ke damun ki Please!” Hajiya Babba ta faɗa cikin wata raunananniyar murya Ɗagowa Humaira ta yi tace “Hajiya nima wallahi ina ƙaunarsa, kuma wallahi In ba a aura min shi ba zuciya ta bugawa za ta yi na mutu.”.
Tashin hankali, a gigice Hajiya Babba ta ce “Ba za ki mutu ba Humaira, a kan waye kike magana? Ko waye dole ya aure ki tunda kina son sa, tell me who's that person da har kika mace kan sa”
“Hajiya Yaya Sadauki!...” Bata bari ta ƙarasa ba ta tura ta gefe tana bin ta da wani irin kallo. “Lallai Humaira ba ki da hankali ma, mijin ƴar'uwar taki kike so? Abun hauka ne aka ce miki?”
A raunane Humaira tace “Haba Hajiya, Ni na ɗaura wa zuciyar tawa son sa ne? Allah ne fa ya halicci zuciya ta da son sa, na girma da son sa sai yanzu kawai za a raba Ni da shi? Ba a min adalci ba kuwa” raunin da Muryar ta tayi yasa ta dakata ta juya za ta fice daga ɗakin tana kuka.
“Wait, come here Humaira!” Hajiya Babba ta dakatar da ita, ba musu ta koma bakin Bed ɗin ta Zauna.
“Humaira haƙuri za ki yi kawai, Alhaji Baba ne ya yanke wannan hukunci. Da a ce ma ita Mabrukan akwai wani tsayayye a wajen ta za a iya dakatar da auren amma babu.” “Hajiya Aunty Mabruka ba ta son Yaya Sadauki, she never get even a single feeling for him, in fact tsawon rayuwa ta da ita ban taɓa jin ko sau ɗaya ta yaba kowa ba sai Captain Hisham wanda tun ba yau ba suke tare, meyasa kuke son raba ta da farin cikin ta? Hajiya don Allah kar ki bari na rasa Yaya Sadauki, idan hakan ta faru I'm useless, ba Zan amfanu ba don ƙarshe ma dai I'll lost my life and....”
Da hannunta ta toshe bakin Humaira tana jijjiga kanta “A'a Humaira, U won't lost your life saboda namiji, ba za ki mutu ba Humaira, ki yi haƙuri kin ji, zan duba naga yaya abun zai kasance, go and sleep now.” ba tare da ta ce komai ba ta fice sai sauƙe ajiyar zuciya take. Nan ta bar Hajiya Babba cikin kogin damuwa musamman da abun ya kwaɓe mata amma to Allah we belong, sai ta ƙara roƙon sa da ya kawo agaji.
*MORNING* *Zahrah's POV*
A hankali ta fara motsa yatsun kafafuwanta wanda take jin kamar an ɗaure mata su, can kuma ta fara kiciniyar buɗe idanuwanta da suka yi mata wani irin nauyi, da ƙyar ta iya buɗe su tana mai bin parlourn da kallo sam jikinta babu Kwari ko kaɗan, a haka ta fara ƙoƙarin miƙewa tana tunanin what makes her so dull today. Nan ta fara tariyo daren jiya, da sauri ta koma shagab ta kwanta tana ƙara rintse idon ta. “Ya Allah!” Ƙoƙarin miƙewa ta ƙara yi har sau uku tana komawa saboda yada jikinta yayi laushi, da ƙyar ta miƙe ta nufi toilet tana mai bin jikin gini. Bayan ta yi alwala ta yi sallar ta wacce a zaune ma ta yi ta tana mai roƙon Ubangiji da ya kawo wa rayuwar ta ɗauki. Alhamdulillah sai ta ji zuciyar ta ta ɗan yi sanyi ba wai don ta daina jin yadda zuciyar ke zafi ba, sai dai ta ji ƙarfin guiwar coping ma wannan bada moment ɗin da ya zo mata a ba zata.
Bata fita parlourn ba sai da Hajjaty tazo duba ta nan ta tarar da ita jikinta zafi kau, hankalin Hajjaty ta tashi matuƙa da sauri ta fita ta kwaso drugs da kuma abinci ta dawo. Sosai ta ba wa Zahrah kulawar da ta ɗan ƙara ɗauke hankalin Zahrah daga tuna wannan abu. Yinin ranar dai kusan tare suka yi.
Can wajen yamma Yaya Sadauki ya shigo Part ɗin, ko da ya tambayi Laraba nan ta kora masa bayanin ai Zahrah ce ba ta da lafiya Hajjatyn take wurin ta. Nan take zuciyarsa ta bada wani irin sauti, da sasaarfa ya ƙarasa zuwa room ɗin Zahrah, handle ɗin ya murɗa ya yi wa kansa iso. Bayan sun gaisa da Hajjaty ya maida dubansa ga Zahrah, gaban sa ne ya faɗi saboda yadda ta rame kamar wacce ta shekara tana jinya. “Hajjaty why ba a Kai ta asibiti ba? Bari na kai ta asibiti yanzu, look how she's been wasted!” ya faɗa a ɗan kiɗime yana kai hannunsa zai ɗauki Zahrah wacce take bacci.
“A'a ai ka bar shi ma Sadauki an, ta riga ta ji sauƙi” Hajjaty ta dakatar da shi. Noo ba zai iya ba, ba zai bar amanar sa a haka ba, dole ya kula da ita. Kamar bai ji Hajjatyn ba ya sunkuci Zahrah yayi waje da ita sai cikin mota, daidai lokacin da motar Ammir ta wuce ta wurin. Bai ma kula da su ba ya tayar da motar sai wani private hospital na Indians da ke kusa da estate ɗin. Abunku da ƙwararrun likitoci tuni suka karɓi Zahrah hannu biyu aka fara duba ta.
Har wajen ƙarfe 8:00 na dare ba su bari ya shiga kallonta ba don kuwa gwaje-gwaje sun kai shida aka mata. Can bayan sun kammala physician ɗin ya ce da Yaya Sadauki su je zai yi magana da shi, he's eager to know what's wrong with Zahrah ai da sauri ya bi bayan doctor ɗin. Bayan sun gaisa ya fara masa jawabi.
“Maras lafiyar da ka kawo yanzu haka bacci take don tana da buƙatar hutu sosai, zuwa gobe za mu sallame ta.” ya faa cikin harshen Ingilishi. “To me yake damunta?” yaya Sadauki ya tambaya. “Honestly speaking Mr. Kuna gab da rasa ta matsawar ba za ku ba ta kulawar da ya dace ba, at this her age ta Yi ƙanƙanta da samun heart attack, to be sincere with you in ba a ba ta kulawa to condition ɗin will worsen, thank God ma an yi diagnosing early.”
Cike da mamaki da kuma damuwa Yaya Sadauki ke kallon Dr ɗin, har sai da ya gama jawabin yace “Ok Dr. Yanzu dai takamaiman shi me yake kawo Heart attack ɗin?” Dr ya gyara zaman glass ɗin sa ya fara magana, bayan ya gama masa bayani nan Yaya Sadauki ya fice fuskarsa ɗauke da damuwa. Wayarsa ce tayi ringing da ba zai ma ɗaga ba sai kuma ya duba, ganin Dude ɗin sa yasa ya ɗaga, bai ce komai ba sai kuma can yace “BHAAT SPECIALIST” Can ya Kuma cewa “Ok”.
Reception ya koma ya zauna har Yaya Khalil yazo. Da yake su tsarin asibitin babu patient relatives, ba a zuwa dubiya saboda suna rendering care yadda ya kamata ga patient. Da ƙyar dai aka bar su suka shiga da sharaɗin kada su yi motsin da zai tayar da patient ɗin. Fitowar su kowa fuskarsa ta sauya wanda hakan ta yiwu yana da alaƙa da yadda suka ganta, daga nan suka wuce tare. Da suka isa sai da suka samar da Hajjaty tukun hankalin ta ya ɗan kwanta, da cewa ma tayi sai dai a kai ta taga Zahrah, da suka mata bayanin tsarin asibitin yasa ta haƙura.
Daga nan kuma Yaya Sadauki ya wuce Part ɗin su don yana bukatar hutawa, wanka ya yi ya Saka wasu soft pyjamas blue colour, kamar kullum yayi shafa'i da witr sannan ya nufi Bed ɗinsa, bayam ya Yi addu'a ya ja Blanket yana mai lumshe idanunsa. Tunani yake me yayi causing wannan sickness na Zahrah, he later concluded it as dalilin rashin Mama ne. Hakan ya sa ya ƙuduri aniyar da safe zai ƙara tunkarar abokin aikinsa Inspector Wada Usman kan batun.
Ba ita ta farka ba sai wuraren 3:00am, a hankali ta fara bin ɗakin da take da kallo, hannun ta ta ɗaga sai taji igiya like a jiki, da sauri ta mayar da duban ta ga hannun, zaro ido tayi ganin cannula ce ga Kuma wani ƙatoton I.V fluid da aka maƙala mata. Sai a lokacin ta fahimci cewa a asibiti take, gabanta ne ya faɗi don bata san ya aka yi ta zo asibiti ba, shikenan asirin ta ya tonu?
Ƙarfe 6:30am na safe yayi parking motarsa a harabar makeken asibitin saboda saurin da yake yi ya dubo Lilynsa. Masu kula da asibitin suka tsayar da shi har sai da ya mayar da motarsa wurin da aka tanada domin parking. Yana gamawa ya fito da basket ɗin daga booth ya nufi cikin asibitin. Ko da ya isa reception Nan ya sanar da su wurin patient ɗin sa ya zo, da ƙyar suka bar shi ya shiga saboda irin yadda ya musu kwarjini.
Lokacin da ya shiga ya tarar da Zahrah kwance sai dai da alama ba bacci take ba amma idanuwanta a lumshe suke, alamar buɗe ƙofar yasa ta ɗan buɗe idonta don ganin waye. Cikin rashin Sa'a suka haɗa ido da Yaya Sadauki wanda ya sakar mata wani kyakkyawan murmushi da sai da ji zuciyarta ta buga.
Kujerara ya ja ya zauna yana bin ta da kallo ba tare da ya ce mata komai ba, ita ma sai ta mayar da idanuwanta ta kulle. Can dai yayi murmushi ya ce “Jira kike na fara miki magana ko Lily?” Bakin ta ta ɗan turo gaba tace “To ai Ni ce ba Ni da lafiya kai za ka gaida ni” Mamaki da al'ajabi suka cika shi jin zancenta sai ya danganta hakan da larurar ta. “Is alright good morning Lily, ya jikin ki?” Baki ture ta amsa da “Da sauƙi” Murmushi yayi ganin dai yau tabbas da rigima ta tashi “Ok speedy recovery dear, an jima za mu koma gida, kin shirya?”
*React please and help me share this update please.* *I'm alerting you with my precious 2025 story Ruɗin Zamani which I'll be starting May be tomorrow or day after tomorrow, sai dai paid book ne, amma In na samu reactions daga gare ku zan mayar da shi free, soyayyar ku kaɗai nake buƙata.*
[1/12, 11:52 AM] Diamond Bhatool: https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 2️⃣2️⃣
﷽
Yamutsa fuska tayi tace “Uhm” daga haka kowa yayi shiru, nashi ɓangaren yana tunanin why is Lilyn Yaya so quite nata ɓangaren tana ƙoƙarin koyawa zuciyarta cire soyayyar sa da ta shige shi ba zata.
Abincin ya fara fitarwa sannan ya ɗaura a bedside locker, bayan ya zuba mata papper soup ɗin da Hajjaty ta yi mata ya ce “O Yah Lily tashi, hope kin yi salla ma” Kai ta gyaɗa masa “Ok tashi ki ci abinci” da sauri ta miƙe saboda yunwar da take ji. Kaɗan taci daga nan ta sha fruits ɗin da ya ke miƙa mata. Sai da tayi nak tukun tayi ƙoƙarin komawa ta kwanta. “No Lily, Bari abincin ya gama shiga kada ki ce za ki kwanta kin ji?”
Ba a daɗe ba aka yi discharge nata, bayan ya gama settling komai da taimakon sa suka fice sai Abatcha estate. Daga nan kuma ya damƙa ta hannun Hajjaty saboda yana son a haɗa lefen bikin sa ta hannun Mommy Nasiba wacce take matsayin ya ga Mommah.
Ba shi ya dawo ba sai da yamma, ko da ya shigo bai tarar da kowa ba, direct bedroom ɗinta ya nufa and luckily yana nocking yaji ta bashi amsa da “Come in” A kwance ya tarar da ita, ganin shi ne sai ta turo baki gaba, sarai ya ganta amma sai ya sake kamar bai ga ba. Sai da ya zauna gefen Bed ɗin yace “In kina tura min bakin nan Lilyn Yaya zan yanke shi” Kamar bata ji ba ta ƙara tura bakin wanda hakan ya shagaltar da shi ga kallonta ba tare da kifta ido ba na tsawon minti guda da wasu sakanni. Kallon nasa da taga ya yi yawa yasa ta langwaɓe kai tana faɗin “Ni ka bar kallo na Yaya” Kansa ya kawar gefe ya haɗe fuskar nan sannan yace “Wa ya ce miki kallon ki nake, ina duba yanayin jikin ki ne ko akwai progress, ba wannan ba ba na son Wasa Lily, ki faɗa min gaskiya me yake damunku, wace damuwa kike da ita da take shirin jefa ki ga wani yanayi na daban?”
Shiru tayi tare da mayar da kallonta ƙasa, a ɗan kausashe yace “Kin ga Lily, bana son Shirun Nan, don't let me repeat myself” Fuska a shagwaɓe tace “Yaya babu komai fa” Hararar da ya banko mata yasa ta mayar da hankalinta. “Eh ah ah Yaya ba komai da gaske nake nima kawai zazzaɓi nake”
“Will You shut up?” ya dakatar da ita “Idan ba ki faɗa min ba wallahi sai na lahira ya fi ki jin daɗi, Ni sa'an ki ne?” Jiki na rawa tuni hawaye suka wanke mata fuska, ta ya ma za ta iya ce masa soyayyar sa ce take shirin hallaka ta?, That's impossible.
Ganin hawaye a fuskarta ga kuma yadda ta tsorata yasa yace “Is ok, daina kukan tunda ban dake ki ba, faɗa min me ke damun ki” “Mama ce har yanzu ba ta dawo ba, kuma ina so na kalle ta.” Nan ya fara lallashin ta yana ce mata Mama ta kusa dawowa in Sha Allah. Daga nan yace ta faɗi me take so zai siyo mata. Daga haka ya fice.
*Ina Mommah?*
Mommah dai har yanzu tana kan bakar ta na a fasa wannan aure wanda tuni har an fara shirye-shiryen sa. Ya ma za a yi a yi mata haka? Nan da nan ta tada hauka bisa zigin Aminanta, Daddy har tsoron shigowa gidan yake saboda bai san tsiyar da zai tarar ba. Abun nata har ya wuce nan ta kan shiga har sashrn Hajiya Babba ta mata tijara daga nan kuma ta nufi sashen Hajjaty nan ma ta sauƙe kwandon tsiyarta.
*A week later*
Cikin satin nan Zahrah ta koma makaranta sannan ta mayar da hankalinta ga karatun ta, ba wai don ta daina son Yaya Sadauki ba Amma a halin yanzu tana iya ɓoye feelings ɗin ta a game da shi yayin da kusancin su kuma ya Karu, kulawar da yake bata ta ninku.
A yau talata Zahrah, Nasreen, Zakiyya, Nainarh da kuma Rumaysa suka je amso ɗinkinsu daga wurin tailor. Sun ci Sa'a kuwa ɗinki ya kammala. Duk an ɗinka, ankon Dinner, Yini da kuma Family and friends day duk an gama. Nan ƴan matan suka biya tailor daga nan suka dawo gida.
Suna dawowa suka tarar an kawo lefen Aunty Mabruka. Bayan sun ajiye kayan su a Bedroom ɗin Zahrah suka dawo parlourn. Mommy Nasiba ce da kuma wasu yayyen Mommah suka kawo. Kaya ne na kuzo mu gani wanda duk idon da yayi tozali da su sai ya tabbatar Naira ta sha wahala. Su Mimie, Aunty Amarya da sauran matan gidan sai yaba kayan suke yayin da Mamie da Ammie ke jin zukatan su kamar su yi bunga musamman da suka ga kayan, kowaccen su cikin ranta tana faɗin da yanzu fa na ɗiyarta wannan dukiya da aka narka.
Basu bari an gama gani ba suka ɗunguma don kai report ga uwar ango, ai kuwa suka ɗaura ta kan layi, ba a jima ba sai ga ta ta shigo parlourn Hajjaty gadan-gadan, biye da ita kuma Ammie da Mamie ne. Tana isa ta ja burki ganin Yayyenta da ƙannenta a parlourn musamman da ta ga akwatunan da ke Baje a parlourn.
Kamar wacce aka hankaɗa ta nufi cikin parlourn sai ka ce mai taɓin hankali. Sai da ta isa tsakiyar ta nuno Mommy Nasiba da yatsa “Ashe har da ku ake cin amana ta Yaya? Ke ma har da ku?” ta fara nuna su ɗaya bayan ɗaya. “Na rantse da Allah ba a isa an mun cin kashin nan ba, har ku ba zan bar ku ba, kuma ku kwashi kayanku don wallahi auren nan ba za a yi shi ba ko zan bar gidan nan.”
Galala Mommy Nasiba ke kallon Ƙanwar Tata musamman in ta tuna dama ba ta da kirki can da amma bata yi tsammanin rashin ɗa'arta ta kai haka ba. “Haba Sughrah! Ashe ba ki da hankali ke?”
A gadarance Mommah ta rufe ido tace “E ba Ni da shi, akan haka wallahi ko da me za a ƙira Ni ba zan ja da baya ba, ku kuma ɗaya bayan ɗaya sai na yi maganinku.”
“Haba Sughrah! Meye kike haka kamar marar ilimi?” Hajjaty ta faɗa tana tsare Mommah da ido.
“Ki ƙira Ni da marar ilimin kai tsaye Hajjaty, ai dama can ba so na kike yi ba, har zan ce ba na son haɗin auren amma a ƙi saboda Ni ba Ni da ƴanci? Tukunna ma wai akwai wanda ya haifa min ɗan ne?” Ba shiri taji an ɗauke ta da mari, ba kowa bace sai Mommy Nasiba.
“Idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri! Hajjaty ai ba sa'ar yin ki bane In kin mana mun yi shiru ba zan zuba ido ki ɓata tarbiyyar gidan mu gaba na ba, shashasha kawai”
“Ni kika mara Yaya?” “Ƙwarai kuwa Sughrah ke na mara” “Ni kika mara ko yaya?” ta nuna kanta da yatsa har lokacin hannunta na kan kuncinta.
“Wallahi ba a isa ba, ko duniya za ta kifa sai an fasa auren nan, don me ma zan bar ɗa na ya auri matar da ta hana Ni shan iska a gidan aure na, ta toshe min duk wata kafa da zan sarara, wallahi ba zai auri Mabruka wacce ta gama yawon banza ba kam, never! Ɗa na Ni na haife shi saboda haka babu wanda ya isa yayi min iko da shi.”
“Ai ba ke kaɗai kika haife shi ba kuma ba ke kaɗai kike da iko da shi ba.” Muryar DADDY ta sauƙa a kunnenta. A zabure ta waiwayo sai kuma ta kama kunkumi tace “Ai duk laifin ka ne Daddynsu, na ce bana so dole sai kun nuna min isa akan cikin da na raina na kuma haife har ya zama mutum?, Wallahi ka ji na rantse Umar wallahi sai an fasa auren nan ko kuma ran kowa ya ɓaci don ba zan bari a yi min cin kashin nan ba.”
Mommy Nasiba ce wannan karon take shirin ƙara saukewa Mommah wani marin taji Daddy yace “Rabu da ita Hajiya Nasiba, ta gama haukarta babu abun da zai fasaya.”
A harzuƙe Momma tace “Ni Kake cewa mahaukaciya ko Umar? Wallahi za ka san ba ni da hankali, bari ku ga haukar, tattara kuɗin ɗa na zanyi na yi idan ya so ku da kuka nace sai ya yi auren kwa haɗa masa lefen.” nan ta kai hannun ta kan akwatunan tana faɗin “Habiba ku zo ku taya Ni mu kwashe”
Sai a lokacin su Ammie suka fito don da a maƙale suke.
“Wallahi Sughrah kika kuskura kika taɓa abu anan zan ɓata miki rai.”
Dariyar takaico tayi tana mai kallon Daddy da fuskarsa ke ɗaure “Wane ɓacin rai ne ban gani ba a wurin ka tunda Gashi yanzu ina gani kai da iyayenka masu gadarar tsiya kuna shirin nuna min iyaka kan ɗana.”
A harzuƙe wannan karen ma Mommy Nasiba ta Yo kanta sai dai Daddy ya dakatar da ita. Murya a kausashe yace “Sughrah ki koma ɓangaren ki” Tsoro ta ji kawai sai ta juya tana burga ta bar parlourn, muƙarrabanta suka bi bayanta.
Nan dai aka tattara kaya aka shiga da su ɗakin Alhaji Baba, Hajjaty sai haƙuri take ba wa su Mommy Nasiba, su ma suna bata haƙuri don ko ba komai yau ƴar'uwarsu ta sa sun ji kunya kuma ta ɓata wayonta.
Duk abun da yake faruwa Yaya Sadauki bai sani ba saboda yana can kan aikin neman Mama. Wuraren Isha ya dawo. Har aka yi sallah ya wuce da su Alhaji Baba babu wanda ya ba shi labarin abun da ya faru yau. Bayan ya yi Dinner ya nufi part ɗin su don ya huta.
A parlour ya ci karo da Daddy bayan sun gaisa yana shirin Hayewa sama ya dakatar da shi. Tsawon wasu mintuna suka kwashe suna magana ƙasa-ƙasa can dai yaya Sadauki ya wuce DADDY kuma ya ciro wayarsa ya kira Ya Junaid Wanda ke Abu Dhabi da zama tare da matarsa. Shi ma sun jima suna waya kafin nan ya yanke, nan ya wuce Bedroom ɗin Mommahn.
Bai tsaya ɓata lokaci ba ya kira sunanta sai tayi kamar ba ta san da wanzuwarsa ba, sarai kuma ya san ta ji ɗin tunda idonta biyu. Bulb ya kunna ai kuwa ta Zabura ta miƙe daga kan Bed ɗin “Mallam ya za ka kunna min haske ina bacci”
Murmushin takaici ya saki yace “Ba wani dogon zance ko rigima nazo ba, ba kuma shawara ko suggestion na bayar ba, umarni nake baki da...” Shewa tayi tace “Dama ta Nan ka fi kauri ai, sai iya ba da umarni kamar kai ka haifi mutum, Ni zan kwanta, idan ka gama ka kashe min bulb.”
Zata haye Bed yace “Na ba ki yau zuwa gobe ki tattara kayan ki na sawa ki bar min gida, ban yadda ki ɗauki komai ba bayan kayan sawar ki sai ki tafi tunda ba ki daraja kowa a gidan.”
Duk da cewa jikinta yayi sanyi amma da ta tuna karatun da ta sha sai tace “To sai me in na tafin, ta fi nono fari ai. Kuma wallahi ku tabbatar kun dakatar da bikin da kuke shirin yi ba izini na.”
Bai tsaya jin me zata ce ba ya wuce Bedroom ɗinsa Rai a ɓace.
Washegari kuwa da sassafe Daddy da zai fita ya shiga ya ƙara nanata mata cewa Kada ya dawo ya tarar da ita. Bata damu ba ta fara tattara kayanta sannan ta yi shirin ficewa, ATM card ɗin ta tayi wa neman duniyar nan amma bata gani ba, haka keys ɗin motarta babu alamun su nan jikin ta ya bata cewa Daddy ne ya ɗauke.
Wayarta ta ɗaga ta kira Number su Mamie cewa tana son ganinsu, ba jimawa kuwa ta suka zo, nan ta labarta musu halin da take ciki, sa yake su ƴan duniya ne suka ƙara ɗaura ta layin kada ta kuskura ta bari ayi auren nan tun da yanzu ya ce ta bar masa gida. Da wannan shawara suka wuce, Mommah kuma tayi amanna da ita. Ba tare da ta damu ba kuwa ta haɗa ta fice, ko ta kan auta Ra'ees bata bi ba ta fice, daidaita ta hau bata tsaya ko ina ba sai gidansu.
Nan ta biya mai a daidaita kudinsa da sauran cash ɗin da ya rage mata. A bakin gate ta tsaya tana ƙarewa gidan kallo, babu laifi gida ne mai kyau sai dai kana gani za ka fahimci cewa masu gidan tsoffin masu kuɗi ne. Ko a mafarki ba ta jin za ta iya zaman gidan amma a haka ta daure ta jefa ƙafarta ciki.
*Ina buƙatar reactions ɗinku sosai my esteem people, don girman Allah na ci albarkacin Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama a yi min share zuwa wasu groups ɗin. Thanks You so much, Diamond Bhatool taku ce🦋💞!*
[1/13, 9:42 AM] Diamond Bhatool:
https://vm.tiktok.com/ZMkaSGVu8/
*Please follow my Tiktok handle*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 2️⃣3️⃣
﷽
Mahaifin Mommah ya daɗe da rasuwa, mahaifiyarta ce kawai a gidan sai kuma yayyenta maza uku da matansu tare da yaransu da suke zaune gidan.
Tun daga hanyar da zata sada ka da mai flt ɗin ta ci karo da ruwa kwalale a ƙasa, ɗage rigarta tayi tana yamutsa fuska kamar ta taka kashi. A main parlourn ta tarar da mahaifiyarta Hajja wacce ke zaune tana kallon SunnahTV. Sallama tayi ciki-ciki Hajja ta amsa tana aika mata wani mummunan kallo na za ki sani don tuni su Mommy Nasiba suka sanar da ita abun da ya faru.
Da yake ma can ba zuwa take ba tunda taga mijinta mai hali ne dama kuma can akwai ji da kai su Hajiya Sughrah sai ta janye ƙafafunta, sai ta share shekara bata ziyarci mahaifiyarta ba, amma su Yaya Sadauki suna zuwa duk juma'a su gaida Hajja.
Gaida Hajja Mommah tayi, ba tare da Hajja ta ɗago ba ta amsa daga haka bata ce komai ba sai da aka gama karatun tukun ta kashe TV ta juyo ta fuskanci Mommah fuska ɗaure. “Ba dai zaman gidan kika zaɓa ba Sughrah? Madalla da ke! Ga can ɗaki sai ki zo ki gyara ki zauna tunda ba za ki taɓa yin hankali ba. Ai Umar ya kyauta ma da ya dawo dake, shashasha kawai.”
Kamar Mommah za ta saka kuka haka ta tashi ta nufi ɗakin da Hajja ta nuna mata, subhanallah! Sai da ta dafe ƙirji ganin yanayin ɗakin, ƙura ce cike da ɗakin ga kuma yana kamar an shekara goma ba a buɗe ba, abun da ya fi ɗaga mata hankali ko labule babu ga shi ko fanka babu a ɗakin. Kamar za ta yi kuka haka ta naɗe gyalenta ta ɗaure saman rigarta da kwalinta sannan ta fara shara, tsabar an dade ba a haɗu ba sai da idonta ya raina fata har shaƙewa numfashin ta yake. Da ƙyar ta gama ta nufi toilet ɗin ta fara share ƙurar da ke ciki. Ko da ta kunna ruwa tap ɗin ba ya zuwa, kamar za ta yi kuka ta fito ta tambayi Hajja. Amsar da Hajja ta bata ne ta sa gabanta bugawa.
“Ki tambayi su Rahina la'alla su ba ki, idan babu kuma sai ki fita waje ki ɗebo. Babu yadda ta iya haka ta nufi sashen babban yayansu Alhaji Kabir. Kallon arziƙi bata samu ba saboda dama sun tanadi wulaƙancin da za su mata musamman da ya kasance umarnin Hajja ne. Kamar wacce lakar ta ta saki ta ƙaraso. Ba tare da ta gaishe da Aunty Rahina ba tace “Ki ɗan san min ruwa zan wanke bayi” Hararar ta Aunty Rahina tayi tace “ki ɗauki plastic ɗaya daga haka kar ki dawo saboda wuta ta ɓaci ba lallai mu samu ruwan ba.”
Babu yadda ta iya ta buɗe randar ta fara zuba ruwan a plastic ɗin sai dai kafin ta gama tuni ta gaji saboda a gidan ta iyakaci ba da umarni ne. Ƙasa ɗaukar ruwan tayi ta juyo tana kallon Aunty Rahina. “Don Allah ki taimaka ki miƙa min wallahi na kasa”
Abun mamaki wai yau Sughrah ce ke haɗa ta da Allah? Kamar ba zata ɗauka ba sai kuma ta ɗauka mata ta kai mata. Mommah tace “Na gode” Daga haka ta wanke bayin sai yamutsa fuska take..
Bayan ta gama ta shimfida tabarma a sabon ɗakinta ta zauna, nan ta jera kaya sannan ta kira Ammie take sanar da ita ta iso, bayan ta gama mata karatu ta fara laluɓen Numbern Yaya Sadauki coz akwai abubuwan da za ta buƙata amma Numbern ba ya shiga. Duk abun da Mommah take yi a kan idon Hajjja ne, jijjiga kai kawai ta yi tana mata fatan shiriya.
*Yaya Sadauki*
Aka ce biki ya yi biki, zaune yake shi da Ya Khalil sai kuma wasu friends ɗin su da Ya Khalil ɗin ya gayyato waɗanda suka iso safiyar yau. Ban da tsokanarsa babu abun da suke shi kuma mutumin ya tsuke fuska kamar a filin daga. Kamar wanda aka tsikara ya ciro wayarsa, Mommah ce ta fara faɗo masa a rai amma sai ya sauya fuska yana yamutsa ta, Numbern Hajjaty ya lalaɓo ya dannawa Kira, cikin Sa'a kuwa wayar na hannunta. Suna gaisawa ya miƙe zai fice sai tsiya suke masa ba tare da sun san wane irin ware zai yi ba. Tambayar Hajjatyn yayi ko Zahrah na nan, tace “Gaskiya to bari dai na duba,sun dai ce za su karɓo ɗinkin su ita da su Nasreen” jim yayi kafin yace “Don Allah ki duba min ita Hajjaty.” Katse kiran Hajjaty tayi taje dubo Zahrah.
Yana zaune ba tare da ya ce da su komai ba wayarsa ta yi ringing. “A'a ta ƙira fa! Wannan kuwa za ta bar mu da abokin?” Ya Salim ya faɗa yana ɗage masa gira. Ba tare da ya ɗaga kiran ba har ya katse ya dubi Ya Salim yayi murmushin takaici kana ya miƙe, kiran Hajjaty ya bi, bayan ta ɗaga tace masa “Ga Zahra'un”
Jin shiru ba a yi magana ba yasa Zahrah faɗin “Hi! Who's on the line?” Gyaran murya yayi, lokacin ta fahimci waye ne. “Ah Yaya Kai ne?” ba tare da ta jira amsarsa ba tace “Hajjaty tace za ka yi magana da Ni ”
“Eh Lilyn Yaya, idan ban takura ki ba please lazy creatures ɗin nan su taimaka miki ku yi mana girki Ni da baƙi na.” Amsa ta bashi da “To Yaya, In an gama zan sanar da Hajjaty cewa ta ƙira ka, Bye Ango..”
Maganarta ta ƙarshe ta so ta bugi zuciyarsa wai ango? Da gaske wai angon zai zama? Ya tambayi kansa. Murmushin takaici yayi yana mai ƙara tausayawa ƙanwarsa Mabruka, kamar wanda aka zare masa laka ya fara laluɓen Numbern da jiya ta ƙira shi tana masa magiyar ya ce ya fasa auren don Allah. Bai ɓata lokaci wurin shawara da zuciyarsa ba ya danna mata kira, ringing ɗin farko ta ɗaga kiran. Shiru yayi sai da ta yi sallama ya amsa mata. Shirun ne ya ƙara kasancewa tsakanin su kafin tace “Yaya Sadauki ina jin ka” Ƙuƙƙifta ido ya fara yi kamar wani maras gaskiya yace “Akwai abun da kuke buƙata na hidimar biki, kuyi listing sai ki tura min ko?” Amsa ta bashi da “To Yaya, na gode” daga haka ta cire wayar a kunnen ta tana mai fashewa da kuka.
A nasa ɓangaren katse kiran yayi yana mai ƙara kallon sararin samaniya na tsawon daƙiƙu kafin ya koma cikin ƙawayen nasu.
Can ɓangaren Zahrah tuni ta tattaro Aminanta suka nufi kitchen don cika umarni mai martaba sarkin da ke mulkar zuciyarta. Nan kuma suka hau aiki.
*GRA, Bauchin Yakubu*
“Yanzu shi ke nan Mom, na rasa Zahrah! Na rasa ta kenan har abada?” Ya Ishaq ya faɗa yana share ƙwalla. Kan sa Mom ta kwantar bisa cinyarta tana share masa hawayen da ke zuba, bangare guda zuciyarta na tsananta bugun yadda tilon ɗan ta ke wahaltuwa kan soyayya. Lallashin sa ta fara tana ƙara kwantar masa da hankali. “Is ok son, ya isa kukan haka, jarumi kamar ka bai kyautu a ce yana kuka ba idan matsala ta tunkare shi, ina so ka ƙara samun ƙarfin zuciya, In Sha Allah in dai Zahrah rabon ka ce za ka same ta duk daren daɗewa.”
Idanuwansa da suka gama yin ja ya buɗe a hankali kana yace “Mom In babu ita ba zan rayu ba! Ban san ta ina zan fara neman ta ba, ko da numfashi na ƙarshe zai kasance to ina so ya kasance na haɗu da Zahrah, na so angel da zuciya ta da kuma gangar jiki na, ta ya za a ce na rasa ta? Nooo ba zai yiwu ba Mom, Idan ban same ta mutuwa zan yi” sai kuma ya fashe da wani irin kuka mai ban tausayi.
Tapping bayansa Mom ke yi tana faɗin “Ya isa son, be brave man Mana, na maka alƙawarin zan taya ka neman ta only on one condition” Kamar ba shi bane mai kuka ba nan take yayi shiru tare da miƙewa zaune yana mai zubawa Mom ɗin ido. “Ina jin ki Mom, ai ko meye sharaɗin na yadda da shi” Kamar za ta yi dariya ganin yadda ya sauya lokaci ɗaya, hakan yasa ta ƙuduri taimakon sa wurin dawo masa da farin cikin da ya rasa tsawon wasu shekaru dalilinsu ita da mahaifinsa tana kuma tirr da hakan.
“Kana ji ko Son?” Kai ya gyada kamar wani ƙaramin yaro “In har kana so na taya ka neman Zahrah to dole za ka zama mai ƙarfin zuciya, wannan kukan da kake kamar wani baby boy duk za ka daina shi, be strong and pray, Allah zai ji ƙan ka ya tausaya maka sannan ya samar maka da mafita, ok?” Kai ya gyaɗa yana murmusawa amma kallo ɗaya mai karatu zai masa ya san cewa murmushin nan ne da ake kira Yaƙe. “Oya now, tashi ka ci wani abun, zama da tunda ba na jarumin ɗa na bane!” babu yadda ya iya haka ya miƙe gudun kada ta samfo har yanzu fa damuwar ba raguwa tayi ba.
*ABATCHA ESTATE*
Aunty Mabruka ce tare da wasu ƙawayen ta guda biyu sun sa ta tsakiya sai rarrashinta suke akan ta cire damuwar komai ta fuskanci zahirin. Ma'eesha ta ƙara dafa kafaɗarta tana faɗin “Haƙuri za ki yi Barrister Mabruka, kowa da yadda ƙaddararsa take zuwa masa, karɓanta hannu bibbiyu sai kiga Ubangiji ya dube ki ya musanya miki da mafi alkhairin ta. So calm down.”
Kanta kawai ta jijjiga tana mai goge ƙwallar da ta zubo mata. “Ba za ku taɓa gane raɗaɗin da nake ji a zuciya ta ba, ba wai ban karɓi ƙaddara ta bane ko wani abun makamancin haka, ina so ku fahimci matsaya ta ne, ina da wanda nake so, amma saboda wani dalili an katange Ni da shi.”
Galala su Raudha suka yi suna kallon ta, ko yaushe rai ta fara kula samarin bare har ta ce akwai wanda take so, dey play.
“To ke Mabruka ina ce dai ko samarin dama ba ki kulawa, ƙarewarta ɗan'uwa na dake mutuwar ƙaunarki ma haka fir kika ƙi saboda wani ra'ayin ki, yanzu ga shi Allah ya baki namiji son kowa ƙin wanda ya rasa amma kina neman butulce masa.” Raudha ta faɗa tana hararar Mabruka.
“Rabu da ita Raudha, wai ma uban waye take cewa tana so ɗin, ina ce duk cikin masu son nata ma iya Captain Hisham ne ya samu arziƙin kallo, shi kuwa har yau ba ta amsa soyayyar sa ba, and see her wai akwai wanda take so, na rantse da Allah Mabruka in kika yi sake mijin nan ya kuɓuce miki ba za ki samu ya shi ba.”
Caraf Raudha tace “Wallahi ko Ni aka haɗa da guy ɗin nan da gudu zan yadda, wallahi maza irin su wuya suke Mabruka, kin sani ko cikin ƴan matan familyn ku ba za a rasa waɗanda ke son shi ba, in za ki kama abun ki ki riƙe Tom, In ba Haka ba za ki ji ana labari.”
Ba ta ce komai ba saboda ta san duk abun da suka faɗa gaskiya ne, ya za a yi su fahimci cewa mahaifiyarsa ba ta son ta bare kuma auren? Meye makomar auren bayan duk su biyun ba su son juna? Ga shi kuma ƴar'uwarta uwa ɗaya uba ɗaya ta mace a son mijin? Da a ce tana da wata dama da ba shakka za ta yi wa ƴar'uwarta wannan ƙoƙarin ko don yadda ta kasance mai iya ɓoye damuwarta. Da haka dai suka ci nasarar shawo kanta har ta saki ana hira, zuwan wasu gang ɗin friends ɗinta yasa ta sake kamar ba komai, fatan ta Allah ya sa zaɓin ya zama alkhairi.
*Zahrah's POV*
Ba su daɗe ba suka kammala haɗa girkin ko don suna da yawa ne oho, sai da ta tabbatar ta jera komai cikin basket kafin ta sanar da Hajjaty. Daga nan suka koma Bedroom ɗin Zahrah suka ci gaba da gwada ɗinkin da suka karɓo, su saka wannan su cire su saka wancan gashi duk ba wanka suka yi ba.
Rumaysa da ke gefe tana kallon su tace “ku ci gaba da saka kayan ba wanka idan kula gumama su da tsami kwa yi bayani ai” ta idasa tana hararar su Nainarh tace “Kut! Rumaysa mu ne za mu gumama kayan da wari? Me kike nufi?” “Abun da kika fahimta” ta bata amsa a taƙaice.
Zahrah tace “kin dai san ba mu kai matakin gumama kaya da wari ba don mun shiga kitchen tun da duk cikin mu kin fi kowa kitse, look at you, wata tiƙeƙiya da ke” ta idasa tana aikawa Rumaysar gwalo.
A hasale Rumaysa ta miƙe ta yo kan Zahrah, ai ba shiri Zahrah ta daka tsalle ta haye Bed, Nasreen sai dariyar mugunta take “Tab! Yau Zahrah sai ɗan buzun ki”
“Na rantse da Allah kika taɓa Ni sai na faɗawa Hajjaty, kawai daga faɗan gaskiya! Naga kema kin gasa mana maganar mun ƙyale ki.” Zahrah ta faɗa tana sauƙe ajiyar zuciya, daidai nan Hajjaty ta shigo da wayarta tana faɗin “Ungo Yayan ku zai yi magana da ke” Amsa tayi ta kara a kunnenta tana faɗin “Assalamu Alaikum”
*React please, sannan a taimaki baiwar Allah a taya ta sharing.*
[1/13, 8:15 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 2️⃣4️⃣
﷽
Amsawa yayi yana faɗin “Out of those girls wata ta rako ki ki kawo min abincin garden ɗina” Daga haka ya katse kiran, miƙawa Hajjaty wayar ta yi ta diro daga saman Bed ɗin, “My people, a Zo a min rakiya Please”
Kallon ta suke alamar they no gerrit, ganin hakan yasa ta kau da kanta gefe tace “I'll be taking the food to him” Nainarh tace “To who? Ba da Ni ba wallahi, naje ya kakkauɗe Ni da slap, rufa min asiri” Dariya dukkansu suka yi kowa sai zamewa yake shi ba ya zuwa. Daga ƙarshe dai zuciya tayi tace “Kar Allah yasa ku je, kuma wallahi In naje sai na ce duk ƙin raka Ni kuka yi” a fusace ta ja hijab ɗin ta ta bar musu ɗakin wannan na faɗin “Wallahi ba zan je ba, ai sai na bari mun haɗu da shi ko?” Nasreen ce tayi ƙarfin halin bin bayanta suka wuce su kuma suka yi ƙirmisisi suka baje sai mita suke.
Suna Isa gate ɗin garden ɗin Nasreen ta ja ta tsaya, juyowar da Zahrah ta yi ta ga babu Nasreen, a ɗan fusace ta dawo baya tace “Malama ya za ki tsaya?” Ƙasa-ƙasa take maganar gudun kada ya jiyo tace “Kin ga Zahrah ki rufa min asiri ki je ki kai masa, kin ga duk cikinsu Ni kaɗai na rako ki” ta idasa cikin sigar ban tausayi. Zahrah ba ta ce komai ba ta ƙarasa ciki, daidai wani ɗan building flat ta gefe wanda bai fiye girma ba ta tsaya, door bell ta Danna, few seconds sai ga Yaya Sadauki ya fito, murmushi Zahrah tayi tace “Yaya ga shi” sannan ta miƙa masa. “Thank You, You can go....” ko rufe baki bai yi ba two of his friends da suka biyo bayansa don ganin amarya coz su a tunaninsu amaryar ce. Bangaje shi ɗaya yayi ɗayan kuma ya ja Yaya Sadaukin baya saying “Ya! Mallam ban wuri na ga amaryar” Wata muguwar harara ya Banka masa sannan ya aika guntuwar wa Zahrah, tuni ta yi disappearing a wurin.
Ganin ta tafi yasa ya dawo kan su rai ɓace yace “Why Are You people behaving unnaturally? Eh?” Dariya suka saka suna kallonsa ganin yadda ya wani haɗe girar sama da ƙasa. Ɗaya daga cikinsu ne ya kalli ɗan'uwansa yace “Prince ka ga yadda Man yake wani huci don Allah kamar wani mayunwancin zaki, Allah ya ba ka haƙuri, ka san ba lallai muna nan za a kai ta ba shiyasa.” Wanda aka kira da Prince murmushi kawai yayi yace “Rabu da shi kawai, wallahi don dai an riga an kusa ɗaurawa da ba abun da zai hana nima na hau layin manema Detective”
Dukan wasa Detective Hamad ya Kai wa Prince yana faɗin “Ba ka da kirki Prince, to da sanin Allah, shiyasa bai yi wa jaki ƙaho ba, Ni dai Man I'm sorry!” ya faɗa yana haɗe hannu biyu, ɗaga idon da yayi yaga babu Ya Sadauki ba alamun sa, tuni ya yi ciki saboda yadda ya ji su Prince na yaba Lilyn sa.
Ko da suka shigo ciki haka ƙememe yace ba zai ba su abincin ba, da ƙyar Yaya Khalil ya tausasa shi har yayi hakuri ya basu, suna gama ci aka hau hira wanda shi ba wani magana yake ba, iyaka yayi murmushi ne ko kuma ya kaɗa kai.
*A GURGUJE*
Ranar Laraba aka yi family and friends day, abun so ma sha Allah, Aunty Mabruka an Sha kyau kamar ka sace ka gudu. An ci an sha kuma an zubar da Naira, wanda bai je wannan biki ba ya yi missing gaskiya. Can na hango su Maman Tajuddeen riƙe da Taj ɗin ta sai muzurai take alamun dai ita ma kishi take da Aunty Mabruka, ga su nan dai jama'a cikin shiga ta alfarma kamar ba a san da talauci ba.
Team Zahrah ma dai cire kishi aka yi gefe aka gwangwaje, komai dai ya yi kyau kamar yadda aka tsara. Ana daf da kammala shagalin kwatsam sai ga wata mata fuskarta rufe da baƙin ƙyalle, ta cikin mutane ta kutsa har ta kai ta wurin da aka tanada domin amarya. Ta kuwa ci Sa'a that time Babu kowa a wurin, bridesmaids duk sun ja gefe nasu uzururrukan.
“Ke!” ta ƙira sunan amaryar a hankali, kamar daga sama Aunty Mabruka taji ana kiran sunanta, tana juyawa taci karo da matar da ba za ta iya tantance wace ce ba, wata ƴar ƙaramar wuƙa ta zaro wacce ke zuba sheƙi ta nuna mata sai kuma ta mayar da ita. “Kin ga wannan wuƙar, ina miji rantsuwa da wanda ya yi ki, In kika bari aka ɗaura auren ki da wannan mutumin, ba shakka kin kawo kan ki ne ga halaka, za ki fuskanci uƙubobi iri-iri, ke da kan ki za ki yi da-na-sanin bari a yi auren a lokacin da ba zan bar ki ba sai dai gawarki, In kin ƙi ji kuma, ba kya ƙi gani ba.” Daga haka matar ta fara shigewa kafin kace me? Babu alamar ta babu alamar ta taɓa wanzuwa a wurin. Hankalin Aunty Mabruka ne ya tashi kamar za ta yi hauka, tuni idanuwanta suka fara zubar da ƙwalla, Thank God lokacin an kammala shagalin, ai kuwa ta samu ta faki idanuwan jama'a ta fice daga hall ɗin don samar wa kanta mafita.
Ba tsaya ba ta fara takawa da sauri da sauri kasancewar babu nisa daga hall ɗin zuwa apartment ɗin su tana tafe tana waiwayawa kamar munafuka, bata ji horn ɗin da yake mata ba har ya kusa buge ta Allah ya bashi ikon taka brake, a fusace ya fito don ganin waye sai dai abun da ya gani Yasa ya ɗan zaro idanuwansa waje. Da sauri ya Sadauki ya isa gareta tare da ɗaga ta tsaye don lokacin ta riga ta saddaƙar shikenan ta mutu.
“From where are you Mabruka?, Ina za ki je da gudu haka?” Bata ce masa uffan ba sai ma lafewa da tayi a jikinsa tana sakin wani irin kuka mai raunana zuciyar mai sauraron sa, bai yi ƙoƙarin janye ta daga jikinsa ba kuma bai hana ta kukan ba tsawon mintuna biyar kafin tayi shiru tana sauƙe ajiyar zuciya. Hannunta ya ja bai tsaya ko ina ba sai front seat, ya bude mata ta shiga shima ya zagaya ya shiga, bai tada motar ba sai da ya dube ta tsawon wasu sakanni yana nazartar ta, can kuma ya kau da kansa gefe yace “Daga ina kike?” Cikin rawar murya tace “Daga can nake..ehm hall ɗin da ake event ɗin.” Kansa gefe yace “An gama ne?” “A'a” ta bashi amsa tana jijjiga kanta “Then why are you out, baki son bikin ne?” Shiru tayi ba ta ce masa komai ba. “Ki bani amsa” Kai ta jijjiga masa alamar a'a
A ɗan hasale yace “Ba a min magana da ka” Da sauri tace “I'm sorry” Shiru yayi ba kuma shi da alamar tayar da motar ga shi maghrib ta kusa “Then why are you out?” Kuka ta fashe masa da shi tana jijjiga kai, bai san lokacin da ya janyo ta jikinsa yana tapping bayanta ba har ta Yi shiru tana sauƙe ajiyar zuciya akai akai. Gently in his melodious voice yace “Tell me, Ko Mommah ta je wurin ne?” “A'a” ta bashi amsa “Ok tell me why are so frightened kika fito ba ki jira an mayar da ke ba, sai kace ba amarya ba.”
Kokawar da take da zuciyarta akan ta sanar da shi ko akasin haka ta kawo karshe. Zuciyar ta ta bata goyon baya ɗari bisa ɗari kan ta faɗa masa, atleast he'll know something to do, probably he might confront the issue and resolve it, ko kuma a fasa auren gaba-daya.” Nan ta buɗe baki ta sanar da shi abunda ya faru. Ɓacin ransa ya ɓoye don ya ma samfo waye ya aikata hakan, ba kowa bace face Mommah, kuma ko za ta mutu auren nan babu fashi.
Lallashin ta yayi cikin kalmomi marasa yawa, and he encouraged her to be brave, nothing bad will happen in Sha Allah. Daga haka ya ja motar, daidai bakin flat ɗin su yayi parking, sai da ya tabbatar ya gana shigar ta ya sauke wani gauron numfashi sannan ya ja motar.
Can wurin event lokaci ɗaya aka nemi amarya aka rasa, duk neman duniyar nan an yi ba ta wurin, hakan yasa aka ƙira gida aka sanar nan ake ce musu ai ta koma ba ta jin daɗi ne. Nan aka fara jigilar mayar da kowa gida.
*Mommah*
Cikin kwana ɗayan da ta yi a gidansu ta galabaita, ta saba kwana kan makeken gado ta juya yadda taso wai yau ita ce kan gayar tabarma, a can gidan mijinta ta kan manta da wata halitta ta sauro amma daren nan haka sauro suka hana ta rintsawa, da ta juya nan sai wannan ya mall mata. Da safe fuskar nan Tata ta kumbura suntum saboda rashin samun bacci, ko ina na jikinta ban da ciwo babu abun da yake yi, maimakon ta risina sai ma ƙara zafi da tayi, alwashin ta sha ma kanta tabbas aka yi auren nan sai ta hana su zaman auren nan.
Babbar magana, su Mommah an saba da samun ruwa ko yaushe sai da ta shiga wanka ta tarar ashe babu ruwa ko ɗiso, haka ta fito ranta ɓace, Hajja ta tarar a parlourn amma ko kallo ba ta samu ba, gaida ta tayi ta amsa kamar dai jiya daga haka ta ɗauke kanta. Cikin ta ne ya ba da sautin ƙulululuu, nan ta tuna rabin ta da abinci tun jiya da safe. Kamar za ta yi kuka ta ƙira sunan Hajja. “Hajja” kallo ɗaya Hajja ta mata ta ɗauke kanta “Ina abinci na?” Wani kallo da Hajja ta aika mata sai da ƴaƴan hanjin cikinta suka motsa “Dama nauyin ciyar da ke a wuya na yake Sughrah?, Ba dai ke kin isa da kan ki ba? Sai ki yi zaman gidan idan daɗi ne da shi aka ce miki, ga fili ga mai doki.” Daga haka Hajja ta miƙe ta bar parlourn ranta na ƙuna.
Baki sake Mommah ke kallon ta, “ko meye na ɗaukan zafin rai?” Ta tambayi kanta. Daga haka ta kyaɓe baki ta wuce zuwa ɓangaren Yaya Kabir, bayan sun gaisa da Aunty Rahina sai ta rasa mai zata ce mata, ga shi yunwa take ji ga kuma izza ta hana ta faɗin abun da ya kawo ta, sarai ita ma Aunty Rahina ta fahimta amma sai ta kafse ta ci gaba da wankin kayan yaran da take yi. “Don Allah nace ba” Mommah ta faɗa ranta na ƙuna tare da kawar da kanta gefe. “Idan akwai abinci ki bani” “Babu” shi ne kaɗai amsar da ta samu daga gareta. Daga haka Aunty Rahina ta ci gaba da wankin ta. Ran Mommah ina ya yi dubu to yau ya ɓaci, haka ta fice a hasale, ta shiga ƙofar Yaya Sa'ad, gwanda Aunty Rahina ta amsa mata, Aunty Maryama ko kallonta bata yi ba har ya gaji da tsayuwa ta fito don kanta.
Part ɗin ƙaninta Sadiq ta shiga, amaryarsa tace ita ma gaskiya ba isanta zai yi ba bare ta ba wani. Rai ɓace Mommah ta dawo Bedroom ɗin da aka bata, wayar ta ta ciro tana doka wa Sadauki kira amma har yau numbern ba ta shiga, hankalinta ne ya tashi amma sai ta tuna ba iya shi ta haifa ba, hakan ya sa ta ƙira ɗan'uwansa sai dai shi ma bai yi picking ba.
Ta ma rasa ta ina za ta fara ga yunwar da ta sako ta gaba, can ta yanke shawarar sayar da wayarta idan ya so ta siyo abubuwan buƙata da kuɗin kafin ta samu su yi magana da Junaid. Da wannan shawara Mommah ta fice, cikin samarin unguwar ta samu wani Ɗahiru ta bashi wayar ya sayar mata, bayan ya dawo ya bashi 3k sannan ta je ta yi siyayyar abun da za ta buƙata, indomie, macaroni, da sauran abubuwan amfani. Yara ne suka shigo mata da su har ɗakin da aka bata, ƴar katifar ta irin ta ƴan boarding school ɗin nan ta ajiye, sannan ta ƙara fitowa ta samu wasu yara suka siyo mata petrol ta tayar da generator tukun ta samu ruwan amfani.
*My readers! How did you see Mommah's life now? Shin ta cancanci hakan? Anya kuwa an kyauta mata?* *Ina team Zahrah ne? Kun haƙura da Yaya Sadauki kenan? Mu je zuwa*
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 2️⃣4️⃣
﷽
Amsawa yayi yana faɗin “Out of those girls wata ta rako ki ki kawo min abincin garden ɗina” Daga haka ya katse kiran, miƙawa Hajjaty wayar ta yi ta diro daga saman Bed ɗin, “My people, a Zo a min rakiya Please”
Kallon ta suke alamar they no gerrit, ganin hakan yasa ta kau da kanta gefe tace “I'll be taking the food to him” Nainarh tace “To who? Ba da Ni ba wallahi, naje ya kakkauɗe Ni da slap, rufa min asiri” Dariya dukkansu suka yi kowa sai zamewa yake shi ba ya zuwa. Daga ƙarshe dai zuciya tayi tace “Kar Allah yasa ku je, kuma wallahi In naje sai na ce duk ƙin raka Ni kuka yi” a fusace ta ja hijab ɗin ta ta bar musu ɗakin wannan na faɗin “Wallahi ba zan je ba, ai sai na bari mun haɗu da shi ko?” Nasreen ce tayi ƙarfin halin bin bayanta suka wuce su kuma suka yi ƙirmisisi suka baje sai mita suke.
Suna Isa gate ɗin garden ɗin Nasreen ta ja ta tsaya, juyowar da Zahrah ta yi ta ga babu Nasreen, a ɗan fusace ta dawo baya tace “Malama ya za ki tsaya?” Ƙasa-ƙasa take maganar gudun kada ya jiyo tace “Kin ga Zahrah ki rufa min asiri ki je ki kai masa, kin ga duk cikinsu Ni kaɗai na rako ki” ta idasa cikin sigar ban tausayi. Zahrah ba ta ce komai ba ta ƙarasa ciki, daidai wani ɗan building flat ta gefe wanda bai fiye girma ba ta tsaya, door bell ta Danna, few seconds sai ga Yaya Sadauki ya fito, murmushi Zahrah tayi tace “Yaya ga shi” sannan ta miƙa masa. “Thank You, You can go....” ko rufe baki bai yi ba two of his friends da suka biyo bayansa don ganin amarya coz su a tunaninsu amaryar ce. Bangaje shi ɗaya yayi ɗayan kuma ya ja Yaya Sadaukin baya saying “Ya! Mallam ban wuri na ga amaryar” Wata muguwar harara ya Banka masa sannan ya aika guntuwar wa Zahrah, tuni ta yi disappearing a wurin.
Ganin ta tafi yasa ya dawo kan su rai ɓace yace “Why Are You people behaving unnaturally? Eh?” Dariya suka saka suna kallonsa ganin yadda ya wani haɗe girar sama da ƙasa. Ɗaya daga cikinsu ne ya kalli ɗan'uwansa yace “Prince ka ga yadda Man yake wani huci don Allah kamar wani mayunwancin zaki, Allah ya ba ka haƙuri, ka san ba lallai muna nan za a kai ta ba shiyasa.” Wanda aka kira da Prince murmushi kawai yayi yace “Rabu da shi kawai, wallahi don dai an riga an kusa ɗaurawa da ba abun da zai hana nima na hau layin manema Detective”
Dukan wasa Detective Hamad ya Kai wa Prince yana faɗin “Ba ka da kirki Prince, to da sanin Allah, shiyasa bai yi wa jaki ƙaho ba, Ni dai Man I'm sorry!” ya faɗa yana haɗe hannu biyu, ɗaga idon da yayi yaga babu Ya Sadauki ba alamun sa, tuni ya yi ciki saboda yadda ya ji su Prince na yaba Lilyn sa.
Ko da suka shigo ciki haka ƙememe yace ba zai ba su abincin ba, da ƙyar Yaya Khalil ya tausasa shi har yayi hakuri ya basu, suna gama ci aka hau hira wanda shi ba wani magana yake ba, iyaka yayi murmushi ne ko kuma ya kaɗa kai.
*A GURGUJE*
Ranar Laraba aka yi family and friends day, abun so ma sha Allah, Aunty Mabruka an Sha kyau kamar ka sace ka gudu. An ci an sha kuma an zubar da Naira, wanda bai je wannan biki ba ya yi missing gaskiya. Can na hango su Maman Tajuddeen riƙe da Taj ɗin ta sai muzurai take alamun dai ita ma kishi take da Aunty Mabruka, ga su nan dai jama'a cikin shiga ta alfarma kamar ba a san da talauci ba.
Team Zahrah ma dai cire kishi aka yi gefe aka gwangwaje, komai dai ya yi kyau kamar yadda aka tsara. Ana daf da kammala shagalin kwatsam sai ga wata mata fuskarta rufe da baƙin ƙyalle, ta cikin mutane ta kutsa har ta kai ta wurin da aka tanada domin amarya. Ta kuwa ci Sa'a that time Babu kowa a wurin, bridesmaids duk sun ja gefe nasu uzururrukan.
“Ke!” ta ƙira sunan amaryar a hankali, kamar daga sama Aunty Mabruka taji ana kiran sunanta, tana juyawa taci karo da matar da ba za ta iya tantance wace ce ba, wata ƴar ƙaramar wuƙa ta zaro wacce ke zuba sheƙi ta nuna mata sai kuma ta mayar da ita. “Kin ga wannan wuƙar, ina miji rantsuwa da wanda ya yi ki, In kika bari aka ɗaura auren ki da wannan mutumin, ba shakka kin kawo kan ki ne ga halaka, za ki fuskanci uƙubobi iri-iri, ke da kan ki za ki yi da-na-sanin bari a yi auren a lokacin da ba zan bar ki ba sai dai gawarki, In kin ƙi ji kuma, ba kya ƙi gani ba.” Daga haka matar ta fara shigewa kafin kace me? Babu alamar ta babu alamar ta taɓa wanzuwa a wurin. Hankalin Aunty Mabruka ne ya tashi kamar za ta yi hauka, tuni idanuwanta suka fara zubar da ƙwalla, Thank God lokacin an kammala shagalin, ai kuwa ta samu ta faki idanuwan jama'a ta fice daga hall ɗin don samar wa kanta mafita.
Ba tsaya ba ta fara takawa da sauri da sauri kasancewar babu nisa daga hall ɗin zuwa apartment ɗin su tana tafe tana waiwayawa kamar munafuka, bata ji horn ɗin da yake mata ba har ya kusa buge ta Allah ya bashi ikon taka brake, a fusace ya fito don ganin waye sai dai abun da ya gani Yasa ya ɗan zaro idanuwansa waje. Da sauri ya Sadauki ya isa gareta tare da ɗaga ta tsaye don lokacin ta riga ta saddaƙar shikenan ta mutu.
“From where are you Mabruka?, Ina za ki je da gudu haka?” Bata ce masa uffan ba sai ma lafewa da tayi a jikinsa tana sakin wani irin kuka mai raunana zuciyar mai sauraron sa, bai yi ƙoƙarin janye ta daga jikinsa ba kuma bai hana ta kukan ba tsawon mintuna biyar kafin tayi shiru tana sauƙe ajiyar zuciya. Hannunta ya ja bai tsaya ko ina ba sai front seat, ya bude mata ta shiga shima ya zagaya ya shiga, bai tada motar ba sai da ya dube ta tsawon wasu sakanni yana nazartar ta, can kuma ya kau da kansa gefe yace “Daga ina kike?” Cikin rawar murya tace “Daga can nake..ehm hall ɗin da ake event ɗin.” Kansa gefe yace “An gama ne?” “A'a” ta bashi amsa tana jijjiga kanta “Then why are you out, baki son bikin ne?” Shiru tayi ba ta ce masa komai ba. “Ki bani amsa” Kai ta jijjiga masa alamar a'a
A ɗan hasale yace “Ba a min magana da ka” Da sauri tace “I'm sorry” Shiru yayi ba kuma shi da alamar tayar da motar ga shi maghrib ta kusa “Then why are you out?” Kuka ta fashe masa da shi tana jijjiga kai, bai san lokacin da ya janyo ta jikinsa yana tapping bayanta ba har ta Yi shiru tana sauƙe ajiyar zuciya akai akai. Gently in his melodious voice yace “Tell me, Ko Mommah ta je wurin ne?” “A'a” ta bashi amsa “Ok tell me why are so frightened kika fito ba ki jira an mayar da ke ba, sai kace ba amarya ba.”
Kokawar da take da zuciyarta akan ta sanar da shi ko akasin haka ta kawo karshe. Zuciyar ta ta bata goyon baya ɗari bisa ɗari kan ta faɗa masa, atleast he'll know something to do, probably he might confront the issue and resolve it, ko kuma a fasa auren gaba-daya.” Nan ta buɗe baki ta sanar da shi abunda ya faru. Ɓacin ransa ya ɓoye don ya ma samfo waye ya aikata hakan, ba kowa bace face Mommah, kuma ko za ta mutu auren nan babu fashi.
Lallashin ta yayi cikin kalmomi marasa yawa, and he encouraged her to be brave, nothing bad will happen in Sha Allah. Daga haka ya ja motar, daidai bakin flat ɗin su yayi parking, sai da ya tabbatar ya gana shigar ta ya sauke wani gauron numfashi sannan ya ja motar.
Can wurin event lokaci ɗaya aka nemi amarya aka rasa, duk neman duniyar nan an yi ba ta wurin, hakan yasa aka ƙira gida aka sanar nan ake ce musu ai ta koma ba ta jin daɗi ne. Nan aka fara jigilar mayar da kowa gida.
*Mommah*
Cikin kwana ɗayan da ta yi a gidansu ta galabaita, ta saba kwana kan makeken gado ta juya yadda taso wai yau ita ce kan gayar tabarma, a can gidan mijinta ta kan manta da wata halitta ta sauro amma daren nan haka sauro suka hana ta rintsawa, da ta juya nan sai wannan ya mall mata. Da safe fuskar nan Tata ta kumbura suntum saboda rashin samun bacci, ko ina na jikinta ban da ciwo babu abun da yake yi, maimakon ta risina sai ma ƙara zafi da tayi, alwashin ta sha ma kanta tabbas aka yi auren nan sai ta hana su zaman auren nan.
Babbar magana, su Mommah an saba da samun ruwa ko yaushe sai da ta shiga wanka ta tarar ashe babu ruwa ko ɗiso, haka ta fito ranta ɓace, Hajja ta tarar a parlourn amma ko kallo ba ta samu ba, gaida ta tayi ta amsa kamar dai jiya daga haka ta ɗauke kanta. Cikin ta ne ya ba da sautin ƙulululuu, nan ta tuna rabin ta da abinci tun jiya da safe. Kamar za ta yi kuka ta ƙira sunan Hajja. “Hajja” kallo ɗaya Hajja ta mata ta ɗauke kanta “Ina abinci na?” Wani kallo da Hajja ta aika mata sai da ƴaƴan hanjin cikinta suka motsa “Dama nauyin ciyar da ke a wuya na yake Sughrah?, Ba dai ke kin isa da kan ki ba? Sai ki yi zaman gidan idan daɗi ne da shi aka ce miki, ga fili ga mai doki.” Daga haka Hajja ta miƙe ta bar parlourn ranta na ƙuna.
Baki sake Mommah ke kallon ta, “ko meye na ɗaukan zafin rai?” Ta tambayi kanta. Daga haka ta kyaɓe baki ta wuce zuwa ɓangaren Yaya Kabir, bayan sun gaisa da Aunty Rahina sai ta rasa mai zata ce mata, ga shi yunwa take ji ga kuma izza ta hana ta faɗin abun da ya kawo ta, sarai ita ma Aunty Rahina ta fahimta amma sai ta kafse ta ci gaba da wankin kayan yaran da take yi. “Don Allah nace ba” Mommah ta faɗa ranta na ƙuna tare da kawar da kanta gefe. “Idan akwai abinci ki bani” “Babu” shi ne kaɗai amsar da ta samu daga gareta. Daga haka Aunty Rahina ta ci gaba da wankin ta. Ran Mommah ina ya yi dubu to yau ya ɓaci, haka ta fice a hasale, ta shiga ƙofar Yaya Sa'ad, gwanda Aunty Rahina ta amsa mata, Aunty Maryama ko kallonta bata yi ba har ya gaji da tsayuwa ta fito don kanta.
Part ɗin ƙaninta Sadiq ta shiga, amaryarsa tace ita ma gaskiya ba isanta zai yi ba bare ta ba wani. Rai ɓace Mommah ta dawo Bedroom ɗin da aka bata, wayar ta ta ciro tana doka wa Sadauki kira amma har yau numbern ba ta shiga, hankalinta ne ya tashi amma sai ta tuna ba iya shi ta haifa ba, hakan ya sa ta ƙira ɗan'uwansa sai dai shi ma bai yi picking ba.
Ta ma rasa ta ina za ta fara ga yunwar da ta sako ta gaba, can ta yanke shawarar sayar da wayarta idan ya so ta siyo abubuwan buƙata da kuɗin kafin ta samu su yi magana da Junaid. Da wannan shawara Mommah ta fice, cikin samarin unguwar ta samu wani Ɗahiru ta bashi wayar ya sayar mata, bayan ya dawo ya bashi 3k sannan ta je ta yi siyayyar abun da za ta buƙata, indomie, macaroni, da sauran abubuwan amfani. Yara ne suka shigo mata da su har ɗakin da aka bata, ƴar katifar ta irin ta ƴan boarding school ɗin nan ta ajiye, sannan ta ƙara fitowa ta samu wasu yara suka siyo mata petrol ta tayar da generator tukun ta samu ruwan amfani.
*My readers! How did you see Mommah's life now? Shin ta cancanci hakan? Anya kuwa an kyauta mata?* *Ina team Zahrah ne? Kun haƙura da Yaya Sadauki kenan? Muje zuwa*
[1/14, 9:06 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 2️⃣5️⃣
﷽
*BAUCHIN YAKUBU, ƘARAMAR HUKUMAR TAFAWAƁALEWA*
Malam Sufi ne zaune da mai ɗakinsa Baba Laure wacce ke dama masa ruwan shayi, tana gamawa ta miƙa masa. Kurɓa ɗaya yayi ya juyo gare ta. “Uwar yara yau ina so na kammala da aikin Goggo Balki, ki taimakawa maras lafiyar ku zo a kammala.” miƙewa Baba Laure tayi ta nufi cikin gidan, ɗakin da aka sauƙi Inna da maras lafiyarta sai kuma Asma'u da Balkisu ta shiga.
Fuska sake tace “Goggo Malam yace ko Amina za ta zo a ƙarasa aikin nata” “Ah ai dole, taimaka mata ku je tare, ko Asma'u da Balkisu ku taya ta in ba za ta iya ba.”
“Dama kuwa taraddadin yadda za mu tafin nake, Takwarar Goggo ku taya Ni mu tayar da ita.” Da haka suka taya Baba Laure suka ɗaga Baba Amina suka nufi Ɗakin da Malam ke aiki, ko da suka kai ta fitowa suka yi Mallam yace Inna ta Zo Ayi gabanta.
Tabbas Alqur'ani waraka ne, a yau dai Malam ya samu damar warware sihirin da ke jikin baiwar Allahr ta hanyar ladabta shaiɗanin da aka wakilta don juya mata tunani. Nan ta baje kuma sai bacci.
Ba ita ta tashi ba sai wuraren la'asar, a hankali ta fara buɗe idanuwanta da suka yi nauyi cikin ranta tana ayyana wane irin nauyayyan bacci haka ta yi? Bismillah t furta tare da ƙoƙarin tashi ta zauna wanda yayi daidai da shigowar Baba Laure. Cike da farin ciki ta ce “Ah! Baiwar Allah kin tashi? Goggo, Goggo!” Kiran da take ƙwala musu yasa Inna fitowa da gudu ta shigo ɗakin kamar ba ƴar tsohuwar nan ba. Saboda rashin ƙarfin jiki har ta kusa gama tashi ta koma yaraf ta kwanta. Rintse idanuwanta tayi tana ambaton sunan Allah.
Da sauri Inna ta Zauna kusa da ita ta taimaka mata ta miƙe zaune. Idanuwanta da ta kasa buɗewa ta ƙara ƙoƙarin buɗe wa, alhandulillah kuma sun buɗu, ɗakin ta bi da kallo ba tare da ta furta komai ba, can ƙwaƙwalwarta ta fara tariyo mata last moment da ta yi aiki. A zabure ta furta “Zahrah!” “Ma sha Allah” Inna ta furta tana faɗin “Baiwar Allah tashi ki watsa ruwan zafi ko kya ji daɗin jikin ki.” Sai a lokacin ta Kai dubanta ga Inna wacce ke washe mata baki. Ganin ba ta santa ba yasa ta fara kokonto kan me ya same ta “Wace ce wannan?” ta tambayi kanta
Ganin shirun ya yi yawa yasa Inna ƙwala ƙiran Asma'u da Balkisu. Suna zuwa Inna ta basu umarnin su taimaka mata ta je ta watsa ruwa wanda tuni Baba Laure ta haɗa shi a bayi. Ƙoƙarin gocewa matar take tana faɗin “Ina kika je ne Zahrah?” Cikin sigar lallashi Inna tace “Yi haƙuri baiwar Allah ki watsa ruwa kin ga jikin ki ba ƙarfi, In kin sa abu a cikin ki kin yi salla sai a yi magana ko?” Cikin ruɗanin zuciya matar ta gyaɗa kai. Nan su Asma'u suka kai ta har bayin kafin su fito, nan suka baro ta tayi wankan suna jiranta a ɗan nesa kaɗan da bayin. Tsantsar farin cikin da fuskarsu ta nuna zai tabbatar da irin yanayin da suke ciki.
Ta jima sosai a bayin saboda yanayin tariya da ƙwaƙwalwarta ta faɗa, can dai ta watsa ruwan ta fito, da sauri su Asma'u suka zo suka taimaka mata zuwa ɗakin da aka ba su tun farko. Kayan Baba Laure da yake ba ta cika ƙiba ba aka ba ta ta saka. Nan aka baje mata tsiren da Inna ta sa a siyo takanas don ita. Duk da bakinta babu daɗi a haka ta daure ta saka tsiren ciki, da ƙyar ta iya cin yanka biyar ta sha ruwa sannan ta jinginar da kanta jikin gini. Damuwarta ɗaya ina ƴarta take? Me take a nan kuma su waye waɗannan?”
Cikin ƙarfin hali ganin ba ta ra'ayin magana Inna tace “Baiwar Allah kin tashi lafiya” sai lokacin ta mayar da kallonta ga Inna. “Alhamdulillah, yau kusan kimanin shekaru biyu zuwa uku kenan kina kwance sai yau Allah yayi kika dawo daidai, na godewa Allahn da ke warkar da marasa lafiya, ya kuma azurta su da lafiya a karo na gaba.
“Ina yarinya ta Zahrah?” Murmushi irin na manya Inna tayi tace “Ke kaɗai muka tsinta Ni da ƴan jikoki na, amma Alhandulillah ki huta zuwa jimawa Mallam zai zo sai mu ji daga bakinsa.
*ABATCHA ESTATE*
A yau juma'a Ya Junaid ya diro ƙasarsa ta haihuwa don shaida auren ɗan'uwansa shi da iyalinsa. Abokinsa Jamal shi ya ɗauko su, kai tsaye Abatcha estate aka wuce da su. Saboda rashin gyara gidansa sakamakon a bagatatan ya zo yasa ya sauƙa Part ɗin su, surprisingly Mommah was nowhere to be found. Daga parlour suka yada trolleys nasu, matar shi Aunty Na'eema ta baje a ɗaya daga cikin kujerun da ke ɗakin shi kuma ya zaga kowanne room Amma ba kowa, fitowa waje yayi niyyar yi suka ci karo da Nainarh wacce ta shigo ɗaukar hand bag nata da zata yi amfani da shi yau.
Da gudu tayi hugging nasa tana faɗin “Oyoyo big Bro, yaushe ka zo? Kai ɗaya ne? Ina baby Arya” lokaci guda ta jera masa tambayoyi tare da sakin sa tana jiran jin amsoshinta. Fuska sake ya ja kuncinta yace “My rigima Sis, waɗannan tambayoyin naki ai sai su sa na ɗimauce, wanne kike so na fara da shi?” Fuska shagwaɓe tace “Duk nake so ka amsa min, shine kazo babu sanarwa ko?” Murmushi yayi yace “I'm sorry, ai ban san da zancen bikin ba sai jiya da dare, I've to book flight for us mu zo a yi da mu”
Ta buɗe baki za ta ce wani abu yaja kuncinta “Allow me to rest, Ina Mommah? I've been calling her number but not reachable.” Shiru tayi ba ta ce komai ba saboda ba ta so a ji mutuwar sarki a bakin ta sai ta ce “Ai Mommah ba ta nan, ta yi tafiya tun shekaranjiya, but we're expecting her return today or tomorrow” “Good! Ki shiga ki kai kayan In-law ɗinki ciki sai ki sa masu aiki su gyara mata one of the bedrooms. Ok?” Cike da zumuɗi tace “Har da Aunty Na'eema aka Zo?” ba ta jira amsarsa ba ta shige da gudu tana hugging in-law ɗin ta tana mata sannu da zuwa. Sai lokacin kallon ta ya kai ga Baby Aryan, her soul, da sauri ta ɗaga shi tana cilla shi sama tana mai wasa, shi kuwa sai ƙyaƙyatawa yake. Aunty Na'eema ce tace “Kin ga Nainarh shiga da Ni ciki, ina so na gasa jiki na” “Sorry Aunty na” Nainarh ta faɗa “Mu je ciki” nan ta kai ta Bedroom ɗin ta sannan ta wuce kitchen ta sa Saratu ta shiga da kayan sannan ta gyara musu ɗakin. Komawa ɗakin tayi ta ɗauko handbag ɗin sannan ta fice ganin Aunty Na'eema ba ta fito ba.
Ko da ta koma Zahrah ce ta fara kallon ta, ganin kyakkyawan baby yasa ta furta “Ma sha Allah, Sis Nainarh Ina kika samo wannan baby Mai kama da ke?” Sai lokacin sauran ma hankalin su ya kai ga Baby Aryan da ke hannun Nainarh. “Yaron Big Bro na ne, yanzu suka zo daga Egygt, meet my son Aryan” Zahrah tace “Wow! Nice name” kuncinsa ta taɓa nan yaro ya miƙo mata hannu. Dariya dukkansu suka yi, nan yaro ya dawo hannun Zahrah.
Ko da Aunty Na'eema ta fito bata tarar da Nainarh ba murmushi tayi ta nufi part ɗin Hajjaty don ta san ba za ta wuce nan ba. Cike da girmamawa suka gaisa da Hajjaty, nan take sanar da ita ba su san da batun bikin ba. Hajjaty tace mata ai abun ya zo babu zato ne, amma Alhandulillah tunda sun zo. Daga nan ta tambayi Hajjatyn ko ina Nainarh, Bedroom ɗin Zahrah ta nuna mata, ko da ta je don ta amshi Aryan su shiga sauran sassan gidan ne yaro Yace a'a, ga uwarsa amma ya maƙale wa Zahrah, haka Aunty Na'eema ta fice ita da Nainarh don ta raka ta. A hanya take tambayarta ko wace ce wacce Aryan ke hannunta?, Nan Nainarh ta fere mata zancen tas.
Aunty Na'eema ƴa ce ga Mommy Nasiba, mace ce wayayya shiyasa tun auren su ba a taɓa jin ta da wani ko wata ba. Shiyasa kuma kowa ke mutunta ta don In ta zo kamar a jefa ta ciki haka ake. Part ɗin Hajiya Babba ta yada zango wurin amarya, shirye-shiryen duk sai ya dawo hannunta.
Da yamma aka gabatar da rantsattiya kuma hamshaƙiyar walima wacce ta tashi kan duk wanda ya halarta musamman ɗan waje da ahalin. Kowa ya koma da kayan kwatance, daga nan aka watse. Aunty Na'eema dai na ɓangaren amarya.
*Yaya Ishaq's POV*
Kamar yadda ya mayar da abun tamkar ibada, yau juma'a sai da yaje can gidansu Zahrah, amma jiya i yau babu wani sauyi. Rai babu daɗi haka ya dawo gida yana kewar abar ƙaunarsa.
*TAFAWAƁALEWA L.G.A*
Bayan shigowar Mallam mai ɗakinsa ta sanar da shi cewa maras lafiyar ta warke. Sai da suka ci abincin dare ya aika kiransu gabaɗayansu don jin bayani daga gare shi. Bayan sun zo Mallam Sufi yayi gyaran murya yace “Assalamu Alaikum Warahmatullahi wabarakatuhu, bayan gaisuwa irin ta addinin musulunci ina so na miƙa godiya ta ga Ubangiji, tabbas godiya ta tabbata ga Allah mai rayawa da kashewa, mai juya al'amuran duniya, Ubangijin da ya halicci cuta ya kuna tanadar da maganinta. Tsira da aminci su tabbata ga Manzon tsira, shugabanmu kuma jagoran mu, cikamakin annabawa Sallahu alaihi Wasallama tare da iyalinsa, sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsa i zuwa ranar ƙarshe.”
“Ina mai farin cikin samun lafiyar wannan baiwar Allah, Goggo Balki Ubangiji ya biya ki, tabbas samun mutane irin ku masu zuciyar tausayawa abu ne mai wahala. Ba tare da ɓata lokaci ba muna son jin taƙaitaccen tarihinki baiwar Allah don mu samu mayar da ke ga ahalinki.”
Gabanta ne ya bada sautin dimm, amma sai tace “Suna na Madina, ina da ɗiya ɗaya ƙwal a duniyar nan, Zahrah. Muna zaune ne a garin Bauchi.”
“Ma sha Allah” malam ya faɗa “Madina sannu, za ki iya tuna unguwar da kike ai?” kai ta gyaɗa masa, yayi murmushi. “Ma sha Allah, kamar yadda kika ga wannan, wato Goggo Balki” ya nuna Inna da yatsa “Ita ce ta tsince ki kwance a hanyar ta na dawowa daga gaida wata aminiyarta ta yarinta tare da jikokin ta a wani kango, har sun wuce ta sa jikokin ta gaba su koma baya su ga kamar mutum ta gani, ai kuwa ta tarar da ke kwance alamar ba ki san yadda kike ba ma. Da yake mutuniyar kirki ce kuma zuciyarta akwai hasken imani haka ta sa jikokin ta suka nemo mai adaidata sahu ita kuma ta tsaya tare da ke, nan ta kai ki gidanta tana baki magungunan gargajiya sai dai babu wani cigaba. Ba ki taɓa yin magana ba tsawon lokacin sai dai a tayar a kwantar, abinci kuwa iya kunu kike iya sha, duk wannan ɗawainiyar ita da ƴan mata biyun nan suka yi, watannin baya Goggo ta min magana game da ke, da yake nima ina da sabgogi sai na manta. Yau sati guda kenan da kawo ki nan ana ta fama kan matsalar sai yau ɗin Allah ya kawo ƙarshen ta, Alhandulillah”
Shiru yayi jin Madina na kuka Inna Kuma sai lallashin ta take kan ta godewa Allah ba kuka ya kamata tayi ba. Sai da kukan y tsagaita Malam ya ci gaba da magana. “Haƙiƙanin gaskiya na ji daɗi sosai, ba kuka za ki yi ba Madina, godiya za ki yi wa Ubangiji da ya sa kina da sauran rayuwa a matsayin mai hankali. Domin kuwa da ace ba a nema miki magani ba babu shakka a haka za ki dauwama, sai dai buwayar Allah gagara misali ce.”
“Abokiyar zamanki ita ta aikata miki hakan, shine aka haɗa ki da wani shaiɗani wanda ya juyar da tunanin ki ya mayar da ke maras amfani. Amma tunda kin dawo dai-dai ina roƙon wata alfarma a gare ki, ko da kin koma can gidanki ki bar ta da halinta kada ki ce za ki ɗau mataki.”
Cikin Muryar kuka da al'ajabi Mama tace “Ai ko ba ka nemi alfarmar nan ba Mallam ba zan yi magana ba, Nima Zan koma ne ga ahali na saboda......” Nan ta kwashe tas tarihin rayuwarta ta sanar da su. Inna kam har da kukanta tana share hanci sai Allah wadai take da Kawu da Baba Amarya. Nan Mallam ya ɗaura da nasiha wa Mamah kan guduwa da tayi ta bar ahalinta ba tare da ta ƙara waiwayarsu ba. Inna ma tayi Tata kafin a tsayar da sai Mamah ta murmure tukun su je a mayar da ita, don Inna cewa tayi tare da ita za su tafi in lokacin yayi. Daga haka suka koma cikin gida.
*Don Allah a yi sharing, kuma a yi reacting* *I love you people*
[1/16, 5:16 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 2️⃣6️⃣
﷽
*Friday* *ABATCHA ESTATE MOSQUE*
A yau juma'a, dubban mutane suka shaida auren ALIYU UMAR ABATCHA da kuma amaryarsa MABRUKA ABUBAKAR ABATCHA akan sadaki dubu 500 Alhaji Babba shi ne ya biya kuɗin a matsayinsa na waliyyin ango yayin da Papa ya amsa matsayinsa na waliyyin amarya. Allah ya ba da zaman lafiya.
Fuskar kowanne ɗaya daga cikin alhalin ɗauke da hasken farin ciki musamman Alhaji Baba da kuma ƴaƴansa. Ta can gefe ango ne zaune kansa ƙasa coz ya ma kasa tashi saboda yadda jikinsa yayi mugun sanyi. Prince Bello ne da Yaya Khalil suka yo kansa fuskarsu sake. Ganin kamar bai san da zuwansu ba yasa Yaya Khalil ya ɗan zungure shi, a ɗan rikice ya ɗago, ganin yadda suka ɗan tsoratar da shi yasa ya banka musu harara.
“Ango ka sha ƙamshi” Prince ya faɗa yana miƙa masa hannu. A zahiri ba za ka taɓa fahimtar wane yanayi Yaya Sadauki yake ciki ba kasancewar fuskarsa ba ta bayyana hakan ba, but deep down wani irin tsoro ne ya shige shi lokaci ɗaya daidai lokacin da auren ya gama ɗauruwa. Murmushin da ya yafa a fuskarsa yasa Yaya Khalil jin sanyi cikin ransa. “Ya! Man, mu je waje, friends namu na waje sai neman ka suke” babu yadda ya iya ya miƙe, a tare suka taho suna ta yi masa shaƙiyyanci shi bai ma san suna yi ba coz hankalinsa ba ya wurin. Sosai aka shiga gaisawa suna masa fatan alheri da addu'ar zaman lafiya tukun aka fara wucewa for reception da za a yi a makeken hall na estate ɗin.
*Amarya*
Gabanta ne ke tsananta Bugu tun da gari ya fara wayewa, haka ta fara safiyar ta jikinta sukuku babu wani ƙarfi. Zaune suke ita da friends ɗin ta Raudha da ma'eesha sai kuma Aunty Na'eema da ta kasa ta tsare amaryar tana counseling nata musamman da ta sanar da ita komai, ta tausaya mata ƙwarai kuma ta ƙuduri kafin su koma Egygt za ta taimaka mata har su daidaita da mijinta. Ita ta shirya amaryar cikin wani expensive lace da ya Sha ɗinki, kana doso ɗakin ƙamshin amarya zai tabbatar maka da wanzuwarta. Sosai tayi kyau abun ta sai dai kuma deep down her heart is beating faster, tsoro da fargaba sun cike zuciyarta. Aunty Na'eema da kuma su Ma'eesha suka sa ta gaba da surutu hakan yasa ta ware.
Sallamar mahaifinta da ta jiyo tare da wasu mazan yasa gabanta bugawa, wannan fargaba ta zama jiki na kowacce amarya. Humaira ce ta shigo fuska ɗaure tace “Aunty Mabruka su Alhaji na jiran ki a parlour” “Ban gane ba” ta tambaya Kamar ba za ta amsa mata ba amma tunawa da mai faruwa ta faru yasa ta ce “Ki fita ki ji mana” daga haka ta wuce nata Bedroom ɗin ta saki kukan baƙin cikin rasa nagartaccen miji irin Yaya Sadauki.
Hijabi ta saka tana mai barin iya idanuwanta waje har ta isa parlourn. Tsugunnawa tayi ta sunkuyar da kanta ƙasa. Alhaji Uthman ne ya fara buɗe zaman da addu'a sannan ya ɗaura da nasiha ga amaryar tuni kukan da take haɗiyewa ya kufce mata, sosai yayi mata nasiha daga ƙarshe ya damƙa mata sadakinta a hannunta. Alhaji Baba ya ɗaura da faɗin “Ki yi shiru haka nan, duk wani abu da ya kamata a faɗa Papanku ya faɗa, a matsayi na na mahaifin ki kuma babu abun da zance illa iyaka ki kasance mace mai haƙuri a gidan aurenki tunda dama ibada ce ta kai ki, kul naji ko na gani kin yi rashin ɗa'a ga mijinki, ki bi shi sau da ƙafa shi ne kaɗai abun da zan roƙa a wurin ki. Kin gane?” Kai ta gyaɗa ta ci gaba da kukanta.
Bayan su Alhaji Babba sun fita Aunty Na'eema tazo ta ɗaga ta suka shiga ciki, wanka ta sa ta gaba tayi bayan ruwan ƙamshin da ta haɗa mata a toilet. Bayan ta fito ma wasu turaruka ta ƙara bata ta shafe jikinta da su sannan ta ɗaura wani mai mai Masifar kamshi. Atamfa ta fitar mata ta saka su Raudha sai yaba kyau suke suna santi, ita dai amarya zuciyarta ce ke wani irin bugu kamar zata fasa ƙirjinta ta fito. Bayan ta saka aka ɗaura mata alkyabba a kai sai ta fito kamar wata gimbiya, kai tsaye ɗakin Hajiya Babba suka nufa, nan iyaye mata ma suka mata nasiha, Hajiya Babba dai addu'a kawai take mata cikin ranta kan Allah ya basu zaman lafiya. Daga nan suka wuce Part ɗin Hajjaty bisa umarnin Alhaji Baba, daga nan kuma za a wuce da ita ɗakin mijinta.
A can Part ɗin Hajjaty ma ta sha nasiha sosai, Aunty Madina dai da ido ta bi ƙanwar Tata ƙasan ranta tana mata addu'ar Allah ya daidaita tsakaninta da mijinta su yi rayuwa mai inganci, daga nan kuma Papa ya sa ta a Mota bai tsaya da ita ko'ina ba sai gidan mijinta wanda Daddynsa ya masa kyautarsa. Ma sha Allah, nan ya kara jan kunnenta kafin ya fito. Yana tafiya sai ga su Aunty Na'eema, Raudha, Ma'eesha, Aunty Madina sun iso.
Aure dai ya riga ya ɗauru, masu farin ciki suna yi, ƴan baƙin ciki ma ana nan ana ƙulla ya za a yi a warware aure, sai dai ta Allah ba tasu ba, abunda Ubangiji ya tsara babu mai iya ja da shi.
*ZAHRAH*
Sosai wannan biki ya mata daɗi ko ba komai ta ƙara sanin wasu ahalinta kuma alaƙa mai kyau ta ƙullu tsakaninsu, Musamman Aunty Madina, tun da aka ce mai sunan Mama ce ta ji tana ƙaunarta ita da yaronta Aamir, Yaya Haidar ma sosai ya nuna kulawarsa gareta har yake cewa in sun gama WAEC& NECO za ta zo musu hutu don tuni sabo ya shiga tsakanin ta da su, Aunty Salma matarsa ma Babu kaifi tana da kirki ga kyakkyawar babynsu mai shekaru huɗu Nihal, yarinyar ba dai shiga rai ba shiyasa Zahrah ta tattare su ita da Aamir da baby Aryan. Tun su Nasreen na mita har suka gaji. Sosai yaran suka ɗebe mata kewa.
*Mommah*
Duk da cewa she can say now she's stable Amma ta rasa yaya za ta yi ta dakatar da auren nan, ganin dai ba riba za ta ci ba tunda an ɗaura yasa ta ajiye makaman yaƙin ta gefe tunda dama can zuga ce ta rufe mata ido har zuciyarta ta makance ta yanke wa kanta wannan mummunan hukunci, yanzu ya za ta yi? Tana buƙatar gidan mijinta a yanzu amma ba ta da kwarin gwiwar tunkararsa.
Ya Junaid ma da yaje Hajja ta feɗe masa komai, sosai yaji zafin hali irin na mahaifiyarsa tasa, nan Hajja ta ja kunnensa kan kada ya kuskura yace zai kashe mata kuɗi, ya bar ta sai ta yi hankali. Bai so hakan ba amma babu yadda ya iya sai ya nema mata waya ƴar keypad yace kafin a gama bikin zai san yadda zai yi da ita.
Da yamma kawai sai ga Ammie da Mamie sun kai mata ziyara, a maimakon da ta gano kuskurenta ta yanke alakar ta sa su sai ma ƙara ɗinkewa da suka yi, yanayin da suka ganta yasa suka fahimci akwai saura fa, hakan yasa suka koma bayan zigin da suka mata amma kafin su fita Hajja sai da ta tare su ta buga musu warning na su fita daga rayuwar ƴarta. Abun ku da ƴan duniya sai Ammie tace “Ki raba mu da ita tunda ke kika haɗa mu da ita, ka ji tsohuwa da iya shege” daga haka suka cika bujensu da iska.
*9:00pm*
Yaran Zahrah da Zakiyya suka kai wurin Hajjaty saboda su samu su shirya, da ƙyar Ya Aufa yace zai kai su da sharaɗin suka wuce time ɗin da ya sa ba zai kai su ba, nan suka wuce suka fara shiri a gaggauce.
Waɗanda ke gidan amarya tuni aka fara haramar tafiya Dinner, kowa sai kece ado yake kamar ba shi ba. Takanas make-up artist ɗin tazo ta sheƙawa amarya kwalliya, idan ba sanin cewa Aunty Mabruka ba ce ba lallai ka iya gane ta ba, ta yi kyau sosai abunta kamar ka jefa a aljihu ka gudu da ita.
Horn ɗin da suka ji ya tabbatar musu da cewa ango ne ya zo ɗaukar amaryarsa. Yaya Khalil ne ya rako shi har parlourn kana ya maka sallama, hakan yasa su Raudha fitowa suka ba su waje, shi kaɗai ya shiga ciki, “Tabarakallahu Rabbul khalikin” ya samu iya gurtawa can ƙasan maƙoshi yana yaba yadda tayi kyau. Tsinin idanuwansa da ke yawo kanta yasa ta ƙara sunkuyar da kanta, hakan yasa ya ɗan kauda fuska ya nufe ta tare da mika mata hannunsa “Amarya, Are we good to go?” Ba ta amsa masa ba sai ta miƙa masa nata hannun a kan nasa. Gaban su ne ya buga a tare.
Ganin za su ɓata musu lokaci yasa Yaya Khalil yin gyaran murya, da sauri ya ɗago ta tsaye har suna iya jin numfashin junansu. “Mu je” ya faɗa a hankali. Suna fitowa su Raudha suka rangaɗa guɗa, murmushin da iyakacin sa kan fuska ta saki har suka bar parlourn, nan masu hoto suka fara kashe musu aiki. Net ɗin da aka makala mata a ka ta take ta ƙasa sai tayi tagal-tagal kamar za ta faɗi, caraf ya riƙe ta sai ta ɗan kwanto jikinsa. Habaaaa ai pictures da videos ɗin da aka yi ba a magana a lokacin. “Ki kula da hanya” kai ta gyaɗa masa, nan suka wuce, shi ya buɗe mata motar ta fara shiga sannan ya rufe mata, ya zagayo ya shiga ɗaya side ɗin. Nan Prince Bello ya ja motar zuwa event center ɗin.
Lokacin da motarsu ta tsaya shi ya fara fitowa ya buɗe mata, bayan ta fito ya riƙe hannunta suka shige hall ɗin, daidai isowar su Zahrah da squad ɗin ta. Ma sha Allah, the growing ƴanmata kenan! Sun sha kyau abun su duk da cewa ba kwalliyar da suka yi, ɗinkin ya amshi jikinsu kamar dai an gwada su aka yi. Tare da Ya Aufa suka shige yana gaba suna bayansa. Cikin mintuna uku aka fara shagali.
Nan aka ƙira amarya da ango stage, kamar dai kowanne masoya haka suka fito suka ɗan taka, zo ku ga yadda ake watsa kuɗi kamar na tsugunna na kwashe amma babu dama, bayan sun koma aka ba wa ƙawayen amarya dama da su fito su ma, Raudha, Ma'eesha sai Aunty Na'eema suka fito, sosai su ma aka watsa musu kuɗi, me zan ga, daf da za su koma Yaya Junaid ma yazo ya gwangwaje amaryarsa da dollars, Ni ko nace har yanzu dama ana watsa dollars?.
Dangin miji aka fara kira, shiru kowa yaƙi fita sai ga su Jidda, Hibba an fito, kafin kace me sai ga su Zahrah an fito fili. Aka sa musu sauti su gwangwaje ai kuwa nan aka san an zo Dinner, bayin Allah rawa suke kamar an aiko su, nan fa hankalin jama'a ya dawo kan su, ashe tun fitowarsu Prince Bello ya ƙyalla idonsa kan Zahrah, hohoho abun da ake kira da love at first sight shi ya faru, yadda take rawa ana mata liƙi yasa yaji wani iri, da sauri ya fita, within a minute Sai ga shi ya dawo, dollars ya shiga liƙawa Zahrah wacce bata ma san yana yi ba.
Babu zato babu tsammani taji an ja hannunta da ƙarfi, ɗagowar da za ta yi idon ta ya sauƙa akan Yaya Sadauki. Gwalo idanuwa tayi ta ma kasa magana saboda yadda taga fuskarsa a ɗaure. Bai tsaya ko ina da ita ba sai da suka bar hall ɗin, a jikin wata bishiya ya tsaya yana aika mata wani mugun kallo, kanta ƙasa taji yace “Are You out of your senses Lily? Za ki shiga fili kina rawa ana miki liƙi saboda ba ki da kunya?” Mamakinsa ne ya kama ta, ko ina ruwan sa da rawar ta? Murya shagwaɓe tace “Haba Yaya, bikin ka fa ake yi kuma sai kar nayi farin ciki? Naga...” “Shut up!” ya dakatar da ita “Don ana biki na baki ga maza ne cike a hall ɗin ba?” Caraf Zahrah tace “To ai ƴan uwana ne”
A hasale ya ja hannunta jin furucin da tayi, ransa ɓace ya danna ta cikin motarsa da aka kawo su cikin. Tuƙi yake kamar mahaukaci har ya kai Estate ɗin su, a bakin Part ɗin Hajjaty yayi parking sannan ya daidaita kansa tare da juyowa ya kalle ta. Hawaye ne sharkab a idanuwanta, duk takaicin sa ya cika ta. Ko ina ruwan sa da ita da zai katse mata da nishaɗinta? Ta tambayi kanta. Ganin hawayen nata ba karamin karyar masa da zuciya yayi ba amma sai ya dake yace “Na duka ki ne kike min kuka?”
Sanin halin kayanta yasa ta ce “A'a” “Oyah wipe your tears or else...” ya faɗa yana miƙa mata handkerchief nasa, lumshe idanuwanta tayi a lokacin da ta ɗaura shi kan fuskarta. The scent is actually unique. “Lily?” ta ɗago ta kalle shi. “Why kike son ɓata min Rai? Eh?” Cikin shagwaɓaɓɓiyar muryarta tace “To ni me nayi yaya?” “Me kika yi ma kike tambaya? U don't even know abi?” Turo baki tayi without saying anything.
*React and share fisabilillah* *Masu taya Ni sharing Ubangiji ya biya ku da gidan Aljannarsa.*
[1/16, 5:17 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 2️⃣7️⃣
﷽
“Kul kike shiga irin wannan, kin shiga fili kamar ke kika fi kowa iya rawa? Wallahi In aka ƙara biki naga kin dage kina rawa irin wannan sai na saɓa miki” ya faɗa in a terrible voice “kin ji ni ko?” “E” ta bashi amsa “Oya! Out of my car” da sauri kuwa ta buɗe ta fice tare da banko ƙofar ta falfala a guje. Murmushi yayi yace “She'll never change, my headache” sai kuma yaja motar da mugun gudu ya koma hall ɗin, Thank God lokacin ne ake shirin fara ciye-ciye. Kau da kansa gefe yayi daga kallon da ƴan mata ke bin sa da shi ya koma mazauninsa. A hankali ya ɗan ranƙwafo daidai kunnenta yace “I'm sorry amarya, na fita saboda wani muhimmin uzuri” murmushi kawai Aunty Mabruka tayi, zuwa yanzu zuciyarta tayi sanyi, yadda yake nuna kulawarsa gare ta ya ƙara masa ƙima a idanuwanta. She never dream of such life with Yaya Sadauki.
*Flash back*
Lokacin da ya fizgo hannun Zahrah daga stage yayi waje ashe Detective Hamad na kallonsa, sannan Yaya Khalil da ke liƙawa Nainarh kuɗi shi ma ya gan shi, wanda aka yi wa buƙulun shima akan idonsa hakan ta faru, yayi mamaki sosai ganin Abokinsa ne. Cikin ransa yake tambayar “Ko me yasa yayi hakan?” Dawowa yayi ya zauna ba tare da ya cewa sauran komai ba. Ƙwaƙwalwarsa ce ta tariyo masa in bai manta ba wannan ita ce yarinyar da ta kawo musu abinci ashe ba ita ce amaryar ba. Hamdala yayi wa Ubangiji da ya nuna masa wannan fuska, je really loves her, “they called it love at first sight” ya faɗa yana murmushi. Fuska ta ɗaure yana tambayar kansa meye tsakanin ta da Abokinsa da zai zame ta daga stage ita kaɗai bayan ga wasu sisters ɗin nasa? “There is a question mark here” ya faɗa can ƙasan maƙoshi. “I love her!” he repeated it uncountably.
Bayan an tashi daga Dinner hankalinsu Nasreen ya tashi ganin sun rasa Zahrah bayan kuma tare da ita suka hau stage. Kai tsaye wurin Yaya Khalil suka je suka sanar da shi. Murmushi kawai yayi don shima zuwa yanzu ya fara fahimtar cewa abokinsa is in love with that creature unknowingly. “Ka Yi shiru Ya Khalil!” Nainarh ta maimaita “Kada ku damu ku samu ku koma gida, tun ɗazu aka mayar ta gida bata jin daɗi” Ba tare da sun yadda da abinda ya faɗa musu ba suka wuce Yaya Aufa ya mayar da su shima kan hanya yana tambayar su ina Parrot (Sunan da ya bata coz sosai shima suna mutunci da shi). Da suka faɗa masa addu'a kawai ya mata yace In sun je su gaida masa ita.
Su Yaya Khalil da Detective Hamad, Prince Bello su suka raka ango, Prince na driving Amarya da ango su kuma su Yaya Khalil suka tsaya suka saya kaji da youghurt. Daga nan kuma suka take motar and thank God suna Isa Suma suka isa.
Ƙememe Yaya Sadauki yace ai ba a isa a raka su ba, daga nan ya isa ya gode haka. Dariya suka yi suna tafa hannu, Yaya Khalil ya dakatar da shi, a kunnensa ya raɗa masa “Ka bi min ƙanwata a hankali ka ji ko?” Wani kallo ya cilla masa yana faɗin “Dallah ku bar min gida, gaurayen banza, In kun ji haushi kuma gobe a ɗaura naku.” daga haka ya shige ciki ya ajiye Ladar da suka bashi.
Dawowa yayi ya rufe ƙofa kafin ya koma. Lokacin da ya shiga bai tarar da ita ba, ƙarar ruwan da yaji yasa ya fahimci cewa tana toilet, ajiyar zuciya ya sauƙe sannan ya tafi ɗaya Bedroom ɗin yayi wanka sannan ya saka wasu milk pyjamas masu tsananin taushi. Bayan ya feshe jikinsa da turare ya fito ya nufi Bedroom ɗin da take, lokacin har ta haye Bed ta ja Blanket.
Sallamar da yayi yasa ta mike tana zare ido. Ba tare da ya kalle ta ba ya zube kan lallausan carpet ɗin dake ɗakin. Ledar ya fara buɗewa tuni ƙamshi ya cika hancinta, yunwar da ta tara a lokacin ta tashi tace ba ta san zama ba. Fara ci yayi bayan ya saka a plate, can taga bai kula ta ba da alamar ba zai ce ta zo ta ci ba kawai sai ta saƙƙo kanta ƙasa ta zauna ita ma ta saka ba tare da ta ce da shi komai ba, ita ta fara tashi ta nufi toilet, bayan ta yi brush ta dawo ta haye Bed sai lokacin Yaya Sadauki ya gama cin nasa. Korawa yayi da youghurt ɗin da ta bari daga nan shima ya mike.
Ƙasa-ƙasa yace “Ki yi alwala ina zuwa” Sauran kazar ya fice da ita zuwa kitchen kana ya wuce ɗaya Bedroom ɗin da ya mallaka wa kansa. Brush yayi daga nan ya ɗauro alwala. Lokacin da ya koma ita ma alwalar tayi ta saka ƙaroton hijabi, babbar praying mat ta shimfiɗa musu. Yana zuwa suka tada sahu kamar yadda ma'aiki ya koyar don nuna godiyar su ga Allah. Raka'a biyu suka yi sannan ya dafa goshinta ya karanta addu'ar da Manzon Allah ya yi umarnin kowanne ango ya karanta ta ga matarsa a daren su na farko.
Daga nan kuma yayi mata tambayoyi kamar yadda addini ya shar'anta, ta bashi amsoshin yadda ya kamata hakan yasa ya ƙara godewa Allah da kyautar macen da ya bashi, fatansa Allah yasa zamansu ya kasance alkhairi. Daga nan kuma yace ta tashi ta kwanta, sai da ta kwanta daga nan kuma shima ya naɗe praying mat ɗin bayan yayi shafa'i da witr nasa kamar kullum tukun ya nufi Bed ɗin ya kwanta.
(To amarya da ango, safiya mai albarka) nan na ja musu ƙofar da suka manta ba su rufe ba.
*Mommah*
Yau kwanan baƙin ciki tayi musamman idan ta tuna shikenan an daura auren ɗanta da wannan shegiyar yarinyar. Da ƙyar bacci ya ɗauke ta ga shi kuma kuɗaɗen da ke hannunta sun ƙare, kayan abinci da ta siyo ma yanzu saura kaɗan, tunani take da ina za ta samu kuɗi ga shi Daddy har yau bai je biko ba bare ta sa ran zai bar ta ta koma. Daga ƙarshe dai haka bacci ɓarawo ya sace ta.
*Prince Bello*
Ko da suka koma daren nan hana su bacci yayi, ko mutum ya fara bacci sai ya tayar da shi yana faɗin “I'm In love” sai kuma yayi murmushi. Samun sauƙinsu da bacci ɓarawo ya sace shi tukun suka samu suka rintsa.
*Devil Klans*
A daren yau sai da suka gabatar da meeting na musamman don taimakawa uwargijiyarsu ta cimma burinta. Akuyoyi da tauruna goma aka ba ta ta sha jininsu a lokacin saboda ƙarfin ikon ta ya ƙaru, daga ƙarshe dai suka rufe taron kowa ya ɓace ɓat kamar ba a halicci mutane a wurin ba.
*ZAHRAH'S POV*
Lokacin da su Nasreen suka dawo already ta yi bacci, tayar da ita suka yi suna mitar me yasa bata faɗa musu ba ta da lafiya ba. Tunani ta yi can tace musu su yi haƙuri. Dandalin hira suka tayar su ma. Nasreen tace “Zahrah kika tafi aka sha da rabin ki, ina baki labari Yaya Khalil.....” Nainarh ce ta katse ta tana rufe mata baki Zahrah ta harari Nainarh tace “Dalla Malama meye Hakan? Nasreen ina jin ki” Bakinta ta janye tana dariya tace “Wato Zahrah ashe Nainarh tun ba yau ba raina mana hankalin take, ashe ita da Yaya Khalil love suke sha ba mu sani ba”
Zaro ido Zahrah tayi tace “Lallai Nainarh! Kin shammace mu ashe” Zakiyya tace “Wai kina nufin kice min ba ki san Nainarh ba, Ni tun ba yau ba na fara jiyo ƙamshi-ƙamshin hakan, shiyasa koyaushe za ki ga tana rubuta letter K a littattafanta Ashe Yaya Khalil take nufi, O Ni Fadimatu!” Dariya Zahrah da Nasreen suka yi, Zahrah tace “Oh Ni Zahrah'u ashe dai su Nainarh an tafasa!”
Harararta Nainarh tayi tana kai mata dukan wasa tace “To ina ruwan ku da Ni ne, naga kema Zahrahn kina yi?”
“Niiii Zahrah?” rufa min asiri ban kai ba tukunna” Harararta tayi a karo na biyu sannan ta kalli su Rumaysa. “Wai ku har yanzu ba ku san Zahrah ma tana yi ba?” Cike da zumuɗi Rumaysa tace “Ba mu mu sha” Dariya Nainarh tayi sannan tace “Ban tabbatar ba, I'm joking Amma na San cewa dukkanku akwai waɗanda ke burge ku cikin familyn nan, In za ku fito ku fito kawai, don ni dai da na gama secondary school Zan auri Yaya Khalil ɗina”
Dukan wasa suka kai mata Zakiyya tace “Uhmm Ni fa ba zan yi auren gida ba, duk da cewa Yaya Taj na mugun burge Ni amma ba na jin zan iya aurensa ko da ace ya furta kalmar so gare ni” Kama baki Nasreen tayi tace “Baki dai falling ma soyayyarsa ba, tuni kuka ba da kai, ku dai duk ina ganin ku, kowa zan ga ina zai je” “Lallai Zakiyya ɗan'uwan nawa ne kika cewa ba za ki aura ba?” Rumaysa ta faɗa “Ni kuwa kinga Ya Auwab yana matuƙar burge Ni wallahi, da zai ce yana so na da gudu zan yadda, mu yi auren mu da mun yi candy”
Baki buɗe Nasreen ke kallon su tace “Allah ya shirya min ku ƙanne na, amma kun ba Ni kunya, Ni dai har Yanzu ban fara tunanin wani aure ba, la'alla sai zuwa nan gaba. Ke kuma Zahrah yauwah” Gyara zama suka yi don jin me Nasreen ɗin za ta ce “Wannan guy ɗin da yayi miki liƙi daga ina rai?” Rau-rau da ido Zahrah tayi tace “Wanne kenan?” Dariya dukkansu suka yi, Rumaysa tace “Ƴar rainin sense wannan abokin Yaya Sadauki ɗan Sarkin Adamawa.”
Zaro idonta tayi tace “Na shiga uku, rufa min asiri Rumaysa wallahi ban san wani ɗan sarki ba, ku yadda da Ni ƙarya take.” ta faɗa tana bin kowannensu da kallo. “Is ok, na yadda da Zahrah, Please to sleep don ni na gaji” Da haka aka rufe zancen kowa ya kwanta.
Washegari around eleven pm sai ga ango da abokansa sun fito gaisuwa, Prince Bello dai ƙyalla ido yake yaga ta ina tauraruwar tasa za ta ɓullo. Part ɗin Hajjaty suka fara zuwa, lokacin da suka shigo kuma Zahrah ta biyo Zakiyya da gudu kan ta ba ta lip balm ai ta riga ta yin wanka. Ba su yi tsammani ba kawai suka ji muryar Yaya Khalil yana faɗin “Hey girls” A zabure suka juyo duka su biyun daidai lokacin da Prince yayi tozali da abar begensa.
Cike da kunya suka gaishe su, da sauri Zakiyya ta koma bayan ta faki idonsu, Zahrah na shirin wucewa taji Yaya Sadauki ya ce “Zahrah Please ki sanar da Hajjaty zuwan nu” Kai ta gyaɗa tare da wucewa Bedroom ɗin Hajjaty. Shi kuwa Prince sai maimaita sunan yake a ransa. Murmushi yayi yace “She must be Zahrah, kyanta, komai nata daban yake da na sauran, i love you” Tunanin sa ya katse ne da fitowar Hajjaty Zahrah na biye da ita. Kitchen ta nufa ta kawo musu drinks da snacks daga nan ta koma Bedroom nata tana cika tana batsewa wai Rumaysa ta jawo musu Yaya Sadauki ya gan su suna gudu.
Dariya suka yi don ba su ga abun ɓata ran ba, Nainarh ta ajiye wata killer smile kan fuskarta tace “Saura kaɗan” A tare suka ce “A yi me?” waskewa tayi tace “Nithing ooo, kun san dai this week za a Fara registration na jamb ko?” “E eh haka fa, wallahi har na manta” Zahrah tace “Nima dai na manta, ya kamata mu ci serious mu fara karatu don mu samu na tafiya jami'a, au ashe ku kunce daga nan shikenan, to Allah ya kiyaye” Kallon banza suka bi ta da shi. Nainarh tace “Sai aka ce miki kuma mun gama, ai za mu yi a gidan mazajen mu ko?” “Allah???” ta ba ta amsa tana sakin dariya daga haka ta janyo school bag nata ta fara fidda littattafai, duk mai son cin serious sai ya min magana don na sa shi a layi, su ooo kuma zan ce Yaya ya siyo muku littafin soyayya ya yi?” ta idasa tana ɗage musu gira.
Shigowar Aunty Na'eema yasa Zahrah tasowa da sauri ta ɗauki babu Aryan sai washe mata baki yake. Da harara Aunty Na'eema ta bi Nainarh “Shi ne kika bar Ni Ni ɗaya a can ko?” Dariya Nainarh tayi tace “Naga Yaya Junaid yana nan”
*React and share please*
[1/16, 5:19 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 2️⃣8️⃣
﷽
Tun da suka fito yake damun Yaya Sadauki akan Zahrah amma ko ƙala bai ce masa ba, kamar maye haka yake ta masa magana. “Allah AU Abatcha I'm in love with her, and aurenta zan yi, don Allah ka haɗa Ni da ita” Banza ya ƙara masa amma an ce akan abun da kake so ba ka fushi. Da ya gaji sai ya dawo gun Yaya Khalil, “Aboki ko ina da wani hali ne da yasa ba za ku bani ita ba, wallahi i do love her with all my heart!” “Ai ga ka ga ta, babu wanda yayi maka Shamaki da ita” Amsar da Yaya Khalil ya bayar yasa Yaya Sadauki juyowa ya aika masa da wani irin kallo.
Bayan sun gama da Estate ɗin suka nufi gidan Mommy Nasiba da gida Hajja, sosai Hajja tayi farin ciki da ganin jikan nata sai zuba masa addu'a take yi. Kamar daga sama Mommah ta jiyo muryarsa, su da sauri ta fito don tabbatarwa. Ganin shi ne da gaske cikin manyan kaya da suka mugun yi masa kyau ga wani fresh da yayi yasa ta sauƙe ajiyar zuciya. Ƙarasowa tayi suka gaida ta cike da girmamawa sai ta tsinci kanta da kasa yi masa magana kamar yadda ta kudurta da ta gan shi. Jan ta ƙasa ta juya za ta koma Yaya Khalil yace “Mommah” ba tare da ta juyo ba tsaya, ko da ya isa sai ya ce “Don Allah Mommah magana nake so mu yi” kasa yi masa musu tayi sai ta nuna masa ɗakinta, gaba tayi ya bi bayanta.
Bayan sun shiga ya sunkuyar da kansa ƙasa sannan ya tsugunna gabanta yace “Mommah don Allah ki yi haƙuri ki dawo, sai jiya naji ashe kin baro gida, ki yi wa Allah da Manzonsa ki taimaka ki dawo ko dan saboda su Ra'ees, yaron har ya rame saboda rashin ki, don Allah Mommah ki dawo” ta yi niyyar ta hau shi da Masifa ne amma sai ta kasa, hawaye na zubo mata tace “Ai ba Ni na taho da kai na ba, Daddynsu ne ya ce na dawo, la'alla an gama zaman tunda har yau bai zo ba, In na Kira shi ba ya ɗagawa.”
Kamar zai yi kuka shima yace “Ki yi haƙuri Mommah, In Sha Allah zan yi wa Alhaji Baba magana za ki dawo, za mu wuce ga wannan.” ya ajiye mata bunch na 1k da ba ta san bawa bane sannan ya wuce. Kuɗin ta ɗaga tana hawaye tace “Shi ma ya bar Ni, sai abokinsa ne ma ya damu da Ni!”
*Couple of weeks later*
Sosai Yaya Sadauki da Aunty Mabruka suke zaune lafiya, tana ba shi girmansa yadda ya kamata shima kuma yana ganin kimarta, sosai duk su biyun suka yi fresh kamar ba su ba. A safiyar yau yake so ya gana da mutumin da yace ya san yadda Mama take, itama kuma yau take son komawa bakin aikinta, da wuri suka shirya, bayan sun yi breakfast ta fito ɗauke da briefcase nasa a hannunta cikin shigar ta ta lauyoyi. Ganin har ya shiga Mota yasa tayi sauri ta ajiye briefcase ɗin nasa a back seat ta koma ta ɗauko laptop Bata da basket ɗin da ta haɗa masa abinci ko zai ji yunwa tunda yace ba lallai ya dawo da wuri ba. Entrance door ɗin ta rufe sannan ta shiga motar, bayan gateman ya buɗe suka wuce.
Ita ya fara sauƙewa kafin ya tafi ta tuna masa da briefcase nasa da abincin a back seat tukun ta fice tana waving Masa hand. Ko da ta shiga ciki ta haɗu da su Barrister Raudha da Ma'eesha sosai aka buɗe banin hira daga ƙarshe suka buge da zolayarta ko har an samu rabo, murmushi kawai tayi tace “Tukunna dai” Raudha tace “Allah wannan freshness ya Yi yawa, gaskiya ba ke ɗaya ba.” shashantar da zancen tayi ta mai da hankalinta kan aikin da ke gabanta.
*Zahrah*
Sosai suka mayar da hankalinsu kan karatu, Islamiyya already sun yi sauƙarsu, Zahrah har an ɗauke ta koyarwa a can, kullum Yaya ya kan shigo, idan ta fita ya shigo zai bar sakon zuwansa a hannun Hajjaty. Hidimar da yake mata bai daina ba har yanzu, In ya ga abu zai siya huɗu yace a basu. Ba don ta daina son shi ba haka ta danne zuciyarta ta hakura da shi, ta kuma yi alkawarin ko da wasa ba za ta ƙara barin so ya yaudare ta ba, In fact ba ma za tai sake ba, babu ruwan ta da kowa, karatun ta shine a gabanta.
*Yaya Sadauki*
Duk da cewa yana kewar Mommahnsa amma ya yi alkawarin ma Daddy cewa ba zai je gurin ta ba, hak Hajja ma ta sa shi ya ɗau alƙawarin nan. Ko da ya isa kan abinda ya kai shi ya sauƙa. Ko five minutes da zuwansa ba'a yi ba sai ga mutumin ya zo, bayan izinin shiga da ya samu ya shiga ya zauna. Ganin babban mutum ne yasa Yaya Sadauki gaida shi cike da girmamawa. Bayan ya amsa yace “Baba kai ne aka ce ka san yadda wannan baiwar Allahn take?” Murmushi tsohon yayi yace “Ƙwarai kuwa, Madina dai mai masa a kasuwa da naje garin iyaye na can Toro kwana biyu da suka wuce na ganta, har muka gaisa, na tambaye ta yarinyar ta da suke zuwa kasuwar tare tace ai tana tare da iyayenta.”
Ajiyar zuciya Yaya Sadauki ya sauƙe yana faɗin “To Baba yanzu ma za mu biya maka kuɗin jirgi ka koma, za ku je can ɗin da Detective Musa Wanda yake riƙe da case ɗin, ina dai ka san takamaimai inda take?” “Ƙwarai kuwa” ya ba shi amsa “Ai da jikokin Cikin umma ta na gan su.”
“Ma sha Allah” Yaya Sadauki ya furta yana murmusawa, zuciyarsa ne tayi wasai kamar an wanke ta. Daɗi ne ya kama shi yasa yace wa baban “Baba ka jira Ni a wannan ɗakin farkon, zan samar maka da jirgin da za ka wuce ko?” “To to yaro babu damuwa” Daga haka ya fice. Flight ɗin da zai tashi yau zuwa Bauchi Allah ya so sai 3pm, nan yayi booking Masa sai da ya tabbatar ya gama settling tukun ya fito. A wurin da ya faɗa masa ya same shi. Nan yace ya zo su tafi, restaurant ya Kai shi, bayan ya ci abinci ya tsaya bank ya cire kudi tukun ya nufi Airport da shi. Kuɗin ya damƙa masa Baba Manu yace ai da ya bar shi, da ƙyar ya karɓa saboda rashin nuna jin daɗin da Yaya Sadauki yayi. Bayan ya karɓa ya masa sallama, sannan yace da zarar sun sauƙa ya kira Detective Musa. Da haka suka rabu.
Kai tsaye gaida Hajjaty ya wuce saboda yau bai shiga mata ba. Bayan sun gaisa ya koma gida. Sai around 12:30pm ya ƙira Aunty Mabruka yace mata in ta gama ta kira shi saboda ya riga ya koma gida. A lokacin tace masa ai ta gama da aikin yau, saboda su Raudha sun taimaka mata ta yi clearing na baya. Bayan sun dawo ta ɗaura musu lunch, tana gamawa ta sheƙa wankanta sai baza kamshi take.
Bayan sun ci abincin take tambayarsa yaushe zai kai ta ta gaida Mommah? Fuska ya haɗe yace “Ba yanzu ba” A ɗan shagwaɓe tace “Haba Yaya na, In Kai ka yi alƙawarin rashin zuwa ai Ni sai ka bar Ni, ba ka tsoron fushin Allah?, Mahaifiya ba abar wasa bace, na ji in ka kaini sai ka tsaya a waje ko ka tafi, In ma ba za ka mayar da Ni ba zan shiga taxi.” da irin kalaman nan ta lallame shi har ya yarda yace zai barta taje sai weekend.
*Yaya Ishaq*
A halin yanzu ya fara dangana da Zahrah, ya ɗauki soyayyarta a matsayin jarrabawa daga Ubangijinsa, hakan yasa yace da Mom ɗin sa su koma can Abuja babu amfanin zamansu a Bauchin, sosai tayi farin ciki ganin ya fara dawowa daidai, cikin ranta kuma tana masa addu'ar idan Zahrah rabonsa ce Allah ya bashi, idan kuma babu aure tsakaninsu Allah ya haɗa shi da mace ta gari. Nan ta taimaka masa ya haɗa trolleynsa don ita dama a Bauchin nan kamar kan ƙaya take haka take jin kanta.
Da Yamma Yaye Sadauki ya fita don yin siyayya kamar yadda ya saba a kowanne azumi yakan siya kayayyakin abinci ya bi family da su sannan kuma waje ma bai bar su ba. Ko da ya shiga kasuwar Kayan abinci wurin Alhaji Sammani ya wuce, dama can a wurinsa yake siya, duk da cewa farashin kayan ya hau kusan ninki uku zuwa huɗu bai fasa siya ba, yawan yadda yake siya hakan ya siya sannan yace a kai can Estate ɗin su gidan kakanninsa, shi kuma ya wuce, har zai wuce gida ya tsaya a wata plaza, ba tare da ya san me zai siya ba ya shiga, kamar an ce ya ɗaga kai yaga wani abokinsa da suka daɗe basu gamu ba a wani shago, shiga yayi da sallama bayan sun gaisa Yaya Sadauki ya tambaye shi ko me yake sayarwa? Yace “Ai ga can ainihin shagon upstairs na wayoyi da laptops ɗin nan”
Fuska sake Yaya Sadauki yace “Amma jarin naka ya kai nawa?” “5million ne” Shiru yayi kamar mai nazari can yace “Ɗan bani account details naka” yana ba shi Ya masa transfer na 5million yace ka ƙara jari, Allah yasa albarka cikin kasuwancin ka, wallahi na ji daɗin ganinka mai sunan Daddy” Alert ɗin da ya gani yasa ya zaro ido waje, tsabar mamaki ko addu'ar da ya masa bai bi ta kai ba yace “5millions? Kai amma na gode sosai Ɗa na (kamar yadda yake kiransa da shi a da) Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, wallahi ba zan taɓa mantawa da alkhairin ka gare Ni ba, Ubangiji ya ƙara tsawon rai ya kare ka daga sharrin mutum da aljan”
Murmushi Yaya Sadauki yayi yace “Ya Isa Daddy na, ai ka wuce haka a wuri na, mu je naga shagon ko da abun siya” sama suka hau nan kawai Yaya Sadauki yaji ya siyawa sisters nasa waya da laptop ɗin ai ko ba komai za su yi karatu da shi. Kuɗin da ya ji sun ƙara shigowa na system 4 da phoned 4 da ya siya yasa Umar faɗin “Haba Ɗa na, ai nima yayansu ne, zan mayar maka da kuɗin ka in Sha Allah” “No need” ya ba shi amsa a taƙaice. Fdgd haka suka yi Musabaha, Yaya Sadauki ya wuce gida.
Bayan ya yi sallar maghrib ya kwaso phones da systems ɗin, sai a lokacin Aunty Mabruka ta gan su, bayan ta tambaye shi without thinking if anything yace “Na su Zahrah ne” gabanta ne ya ɗan faɗi don zuwa yanzu ba ƙaramin so take wa mijin nata ba, karo na farko da ta ji kishinsa a ranta da ta tuna scene ɗin da ya faru a bikinsu. Ganin kamar ta shiga wata duniyar yasa ya huta mata iskar bakinsa a idonta, a ɗan zabure tace “Bye, sai ka dawo, ” daga haka ta juya da sauri ta nufi Bedroom nata tana sakin kuka.
Jim ya bi ta da kallo har ta shiga, bai ji daɗin yadda ta tafin ba duk da ya gano kamar kishinsa take amma ai ƙannensa ne, kuma ta sani sarai tun kafin su yi aure shi yake kula da al'amuran Zahrah, why daga faɗin sunanta za ta sauya fuska. Kafaɗarsa ya ɗage irin I don't care ɗin nan ya nufi motarsa da ke fake.
Yana shirin tayarwa wayarsa ta fara ringing, ganin Detective Musa yasa yayi connecting da Bluetooth tare da picking, gaisawa suka yi, Yaya Sadauki yayi shiru yana sauraran sa. “Sir kana ji?” Da “Eh” ya amsa sannan yayi shiru. “Yauwah sir yanzu Baba Salahu ya ƙira Ni game da Issue na matar nan, ya ce wai ka ce mu je tare da shi ya nuna min gidan da take sannan....” Dakatar da shi yayi sanin halin Sarkin zance “Eh Ni ne” “Ok sir, sai na kira ka” ya faɗa cike da girmamawa.
Daga haka ya katse kiran tare da jan motar, bai tsaya ko ina ba sai ɓangaren Hajjaty.
*React and share please*
[1/18, 2:25 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 2️⃣9️⃣
Bayan sun gaisa da Hajjaty nan yake tambayar Zahrah, bai rufe baki ba ta fito daga Bedroom nata don ɗaukar snacks da drink ta sa a bakinta saboda karatun da tayi ya sa duk glucose nata ya ƙone.
Turus tayi ganin Yaya Sadauki a parlourn, da sauri ta ƙarasa wurin da yake tana washe baki. “Oyoyo Yaya Ango, an yini lafiya?” Ba tare da ya kalle ta ba yace “Lafiya lau Lily na, ya karatun, ana maida hankali dai ko?” Fuskarta ɗauke da murmushi tace “Alhamdulillah Yaya ana yi sosai.” Ɗagowa yayi ya dube ta sannan yace “Ma sha Allah, ban da biye samari dai.” Ƙasa tayi da kanta ba tare da ta ce komai ba, Hajjaty kuma tayi karaf tace “Tooo! Ji min wani zance, In ba ta kula su ba ta ya za ta samu mijin?”
Kunya ce ta kama Zahrah jin zancen Hajjaty, ba ta san lokacin da ta ruga da gudu ta koma Bedroom nata ba. Kallonsa ya mayar kan Hajjaty yace “A'a Hajjaty, Lily na ta yi yarinya da kula samari yanzu, In lokacin ta yayi ma already na mata miji” Baki sake Hajjaty ke kallon sa kana tayi dariya irin tasu ta manya tace “Lallai ne Ishyaku.”
Shima dariyar yayi yace “Yanzu ga shi kin sa ta ji kunya ta tafi, kuma ban faɗa mata saƙo na ba” “In na fahimce ka so kake yanzu naje na kira maka ita?” “Ni ban ce ba Hajjaty, zan je na faɗa mata da kaina ma” Harararsa Hajjaty tayi tace “Ɗan baɗo kawai, ya Mabruka?” “Lafiya” kawai yace daga haka ya nufi Bedroom ɗin Zahrah.
Littafan da ya gani gabanta yasa ya murmusa sannan yace. “Put on your Hijab and follow me Lily” Kamar yadda ya faɗa tana saka Hijab ta bi bayansa. Ɗan gefe ta tsaya ganin ya buɗe motarsa. “Come closer” ya faɗa a hankali. Pointing mata jerarrun laptops ɗin yayi yace “Choose one” PINKY....ai kuwa tana hango pink ta nuna masa, Phones ɗin da yake iri ɗaya ne sai ya miƙa mata su yace, pick yours sauran ki ba ma sisters naki”
Kasa magana tayi tsabar farin ciki sai jujjuyo Phones ɗin take, wai iPhone dai da take gani yau ita Yaya ya mallakawa. Ganin ta tsaya yasa ya ɗan kalle ta yace “Lily?” Sai a lokacin ta dawo daga duniyar tunanin, fuskarta na nuna zallar farin ciki tace “Thank You so much Yaya na, Allah ya ƙara maka buɗi yasa ka fi haka, mun gode” Without minding at her appreciation yace “Mu je na taimaka miki ki shiga da su” daga haka yayi gaba tana biye da shi, ta ma rasa ina za ta sa kanta saboda tsantsar farin ciki.
Bayan ya kai mata har Bedroom nata ya miƙa mata wasu kuɗaɗe yace “Ban samu siya muku Sim cards ba, gobe In kun dawo daga school sai driver ya Kai ku ku siyo, banda waya da samari Lilyn Yaya, karatu na siya muku ku yi da su.” Cike da ladabi tace “In sha Allah Yaya, mun gode sosai, mu kwana lafiya” Daga haka ya wuce abunsa.
Kai tsaye gida ya koma, sosai Aunty Mabruka ta tada masa rigima don ya siya ma su Zahrah waya da system, shi mamaki ma ta bashi, sai kace bai ƙannenta ba, share batun ta yayi ganin tana so ta kawo masa wargi da ta gaji da kanta ta sauƙo.
Yana Zaune yana aiki a system nasa wayarsa tayi ringing. Ganin Detective Musa yasa yayi picking a hanzace. “Hello Sir, ga Ni ga Baba a gidan da matar take, kafin ka iso za ka iya hawa Whatsapp kuyi magana da ita.” Bai tsaya ƙarasa jin zancen ba ya datse kiran ya hau Whatsapp. Video call ya Danna direct, lokacin da suka zama connected Detective Musa ya miƙawa Mama da ke zaune kusa da inna, da yake akwai adequate light a gidan a kan fuskarta idanuwansa suka sauƙa, ko ba a faɗa masa ba ya tabbatar ita ɗin ce, ba tare da ya ce uffan ba ya katse kiran, ɓangaren Mamah ma kusan abun da ya faru kenan, tana kallonsa fuskar ɗan'uwanta ta zanu a zuciyarta har sai da gabanta ya faɗi.
Ko da yayi ending call ɗin bai tsaya ɓata lokaci ba yayi booking flightpip duk da cewa yau za a tashi da azumi gobe ne. Ganin yadda yake zakwaɗi yasa Aunty Mabruka faɗin “Kwana nawa za ka yi ne Yaya?” “Ai sai kun ganni kawai.” Kamar za ta yi kuka tace “Ya batun zuwa gaida Mommah?.” “Kar ki wani damu da wannan, In ba na Nan ma Khalil Yana nan, zai iya kai ki. Daga haka ba ta ƙara cewa komai ba ganin dai alamun har yanzu fushi yake da ita.
*Washegari*
Bayan sun shirya a part ɗin Hajjaty suka haɗu bayan sun gaisa Zahrah ta dube su cike da zumuɗi tace “Guess what?” a tare suka ce “What?” Murmushi Zahrah tayi tace “Tukuicin me zan samu?” Nainarh tace “Na baki Yaya na” Sauran ma duk irin amsar da suka bayar. Ɗauko musu system ɗin ta fara yi, kowaccen su ta zaɓa cike da zumuɗi “A ina kika samo waɗannan kuma?” murmushi tayi tace “Ku ba kwa cin ribar zance, to Yaya ne jiya ya siya mana bayan kun tafi, bari ku ga”
Kwalayen wayoyin ta fitar ɗaya bayan ɗaya, ihun murna suka saki suna faɗin “Wayyo mun more wallahi, kai Zahrah Allah ya bar ki da Yayan mu”. Ganin za su makara yasa ta fara fita saying “In Kun gama kwa zo mu tafi ai” da sauri suka ajiye suka bi bayanta.
Suna ficewa Yaya Sadauki ya shigo, da yake kayan da ya siya duk sun iso hakan yasa ya ɗebo masu aikin rabon, kowanne Part aka ba su nasu sai addu'a suke zabga masa, sauran kuma kai tsaye yace a wuce da su masallatai a rabawa mabuƙata kafin ya dawo. Bayan sun gaisa da Hajjaty ya mata sallamar cewa zai tafi Bauchi, addu'a sosai ta masa haka Alhaji Baba ma, bayan sun gaisa da Daddy ma ya faɗa masa, shi ma dai addu'ar ya masa daga nan Yaya Khalil yazo ya miƙa shi airport.
Haka kawai Aunty Mabruka take jin gabanta na faɗuwa, da ta ga hakan ya yawaita sai ta kira Ya Khalil tace yazo ya Kaita za ta gaida Mommah. Bayan ya Kaita har ciki ya raka ta lokacin iya Hajja ce a parlourn tana kallon maimaicin wani tafseeer a AfrikaTV3. Cike da girmamawa suka gaisa, Yaya Khalil ya gabatar da Aunty Mabruka matsayin matar Yaya Sadauki, nan Hajja ta ƙara sakewa da ita suna hira. Daga nan Yaya Khalil yayi musu sallama yace In ta gama ta kira shi.
A hanyar waje suka ci karo da Mommah, da ya gaida ta ta amsa kamar koyaushe tana kawar da kanta gefe. Da ta shigo kai tsaye ɗakinta ta wuce ba tare da ta dubi mutanen da ke parlourn ba bare su samu ran za ta kula su. Murmushin takaici Hajja tayi sannan ta miƙe tace “Ina zuwa” ganin gun Mommah Hajjan za ta je yasa ta ce “Ehm Hajja, ki koma ki zauna, zan je ai ba sai ta fito ba” Ba tare da Hajja ta Musa ta ba ta dawo ta zauna tana ƙara yaba kyan hali irin na Aunty Mabruka.
Da sallama ta shiga ɗakin, ƙasa-ƙasa Mommah ta amsa saboda wajibcin hakan bayan ta yi tozali da halittar da take zargin ta jaza mata shiga halin da take ciki. A kan tabarma Aunty Mabruka ta Zauna tana wasa da ƴan yatsunta. “Ina yini Mommah” “Lafiya” ta amsa murya a kausashe. Tsawon mintuna arba'in babu wanda yayi magana a cikinsu, hakan yasa Aunty Mabruka ta ƙira Yaya Khalil tace mishi ta gama.
Cike da tsoro duk da cewa ta ga alamar buƙatar taimako da Mommah take ga shi ta fige tace “Ehm Mommah ki bani account Numbern ki don Allah” Ai da sauri jin zancen kuɗi Mommah ta juyo ta dubi Aunty Mabruka. Fitar da tayi neman bashi taje amma bata samu ba, jikinta ne yayi sanyi tana shirin magana Aunty Mabruka tace “Mommah don Allah ba don na raina ki ba ne kawai ina so na kyautata miki ne, Please....” Abun da ta gama yi tana roƙon a ba ta bashi aka ƙi ga shi yanzu abun da ta raina yana roƙon ta da ta amince ta amshi kyautarsa. Cikin wata raunananniyar murya kamar ba Mommah ba tace “Ai yanzu ba Ni da wata account already Daddynsu ya yi deactivating nasa” Cike da tausayawa Aunty Mabruka ta fitar da nata ATM card ɗin ta miƙa wa Mommah. A hankali tace “Pin ɗin 1990, ki riƙe shi a wurin ki don Allah, duk lokacin da kike da uzurin amfani ki cira a ciki, kada ki ce a'a Mommah” Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa Mommah, Aunty Mabruka ta share mata tana faɗin “Please Mommah ki daina kuka, na tabbsta In Yaya ya Gani ba zai yi farin ciki ba.”
“Dole nayi hawaye Mabruka, na yi wasa da dama ta, meyasa bani da tunani? Yau abun da naje nema bashi aka hana ni sai ga shi na samu daga wurin mutanen da nafi ƙyamata a rayuwata ba tare da sun min laifin komai ba, na yi hasara a rayuwata Ni Sughrah” Kuka ne ya ci karfin ta, Aunty Mabruka ji tayi kamar Hajiyar ta ke kukan hakan yasa ta matsa kusa da ita, ba ta san time ɗin da tayi hugging nata ba. “Ya isa haka Mommah, don Allah ki yi shiru kada ki yi saɓo, ki ɗauka hakan a rubuce take zai faru, don Allah ki yi haƙuri, na san kina fushi da yaya amma ki yafe masa, kullum cikin zancenki yake sai dai yana tsoron tunkararki ne.”
Hawayen ta ta share tana faɗin “Na gode Mabruka, Allah ya miki albarka ke da mijinki, ya sa albarka cikin rayuwar auren ku, sai na zo muku” “Amin Mommah, sai kin zo”
Bayan fitarsu Mommah ta ƙara ɗaga ATM card ɗin da Aunty Mabruka ta bar mata, wasu irin zafafan hawaye na baƙin ciki da nadama ta share kana ta fito zuwa wurin Hajja. Bayan ta ba wa Hajja labarin komai murmushi kawai irin na manya tayi tace “Ke ce kika kasa fahimta Sughrah, tun ba yau ba nake nuna miki hanya, ba a ƙyamatar Mutum saboda zuciya na ƙinsa, Rukayya tun ba yau ba na san cewa mutuniyar ƙwarai ce duba da irin yadda kike mata son ranki ba ta taɓa yi min wani kallo na rashin ɗa'a ba bare kuma zagi. Yanzu ya rage naki ki san me Yakamata kiyi.”
Cikin wata irin murya da ke nuna zallar nadama tace “Ki yi haƙuri Hajja, kada ki ƙara bari na da hali na, ki yi wa Ubangiji ki yafe min, na bi ki na bi mijina, na bi Allah.” Sai da Hajja taso yin dariya amma ta make tace “Kin ga Habibah da Saudatu da kuke wa kallon masu son ki? Wallahi da za su samu dama su za su fara ruguza rayuwarki. Yanzu zan baki wani aiki, daga nan za ki tabbatar da me nake faɗa miki.”
“Abun da nake so da ke shine, ki kai musu ziyara har ita Ruƙayya ɗin, ki nuna musu buƙatar ki ta taimako, idan suka nuna a'a ki ce su ba ki bashi to....ina tabbatar miki kan kuɗi halin kowacce su zai bayyana gare ki, sai ki yi taka tsantsan da rayuwarki.”
Da wannan shawara suka rufe wannan babin, nan Hajja ta sake mata fuska karo na farko tun zuwan ta, sosai suka yi hira kamar ba su ba.
*Aunty Mabruka*
Bayan ta koma haka tayi ta al'ajabin yadda rayuwa ta mayar da Mommah, tabbas duniya ba abar tinƙaho bace ba kuma wurin zama ba, idan yau kai ne to gobe ba komai bane, sosai jikinta yayi sanyi.
*React and share fisabilillah!!!🙏🙏🙏😍😍😍, Much love my fans.*
[1/21, 10:03 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 3️⃣0️⃣
﷽
*ZAHRAH'S POV*
Bayan sun dawo daga school basu 'bata lokaci ba saboda zumu'din wayar da suke, duk da cewa tana jin wani iri a jikinta kamar wani ba'kon al'amari na tunkararta amma ta dake, suna dawowa babu wadda yayi lunch wanka kawai suka yi suka fita don tsabar mazari, gani suke kamar in ba su je yanzu ba abubuwan za su 'kare ne.
Cikin shigar Abaya da suka yi rolling veil akai suka fito, Zahrah wacce ke ri'ke da handbag nata da sauri ta juya ciki, ku'din ta kwaso daga nan kuma driver ya ja motar. Sosai suka hidimtawa sabbin wayoyinsu bayan sun sayi Sim cards sun yi register, daga nan kai tsaye suka koma gida suna 'dan banzan mazari.
Ganin har dawowarta ba ta ga 'kiran Yaya Sadauki ba yasa ta 'dauko wayarta ta lalumo numbernsa tayi dialling, five times tana 'kira amma shiru ba ya tafiya, ta ala'kanta hakan ne da ko baya bu'katar distraction but her mind did'nt believe with that statement, gabanta ne ke bugawa da sauri-sauri. "He should have let us know ya isa lafiya Allah yasa all is ok" ta fada cikin ranta. Girkin da ta tashi za ta yi ma fasa shi tayi saboda yadda gabanta ke fa'duwa.
A can 'bangaren su Hajjaty ma sun 'kira wayarsa amma dai amsar 'daya ce, not reachable, Yaya Khalil ya 'kira ya 'kara shima abun ya fara 'daure kansa, ba tare da ya sanar da kowa ba coz shima bai san specifically abun da Yaya Sadaukin zai yi a Bauchi ba tunda iya saninsu dai ba su da wasu ahalin a can sai dai in aiki ne ya kai shi.
*Ya Ishaq's POV*
Alhamdulillah, there's a little bit progress regarding his condition kuma yana coping yadda ya kamata sai dai deep down his heart is suffering, how he wish ko da sau 'daya ne ya kamata a ce ya 'kara kallonta, even once, amma tun da 'kaddara tai masa yankan 'kauna da ita ya amshi hakan tare da fatan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi saboda ko ka'dan a halin yanzu ba ya so ya 'kara sanya iyayensa a damuwa duk.da cewa they were behind the issue, da ba dan selfishness nasu ba da ba tabbacin zai rasa Zahrah, ga shi yanzu ya rasa ta rashi na har Abada in dai ba suna da rabon ganawa ba.
Haka yinin ranar ya shu'de ba tare da kowa yaji daga Yaya Sadauki ba, sosai hankalinsu ya tashi musamman Hajjaty da Alhaji Baba wana su ka'dai suka san ya bar Abuja, to babban abun da ya gama 'daure kanunsu bai wuce rashin samun wayarsa ba, hakan ba ta ta'ba faruwa ba, bai ta'ba aikata wani abu kwatankwacin hakan ba domin duk tafiyar da zai yi in ya kai masau'ki yakan 'kira ya sanar da su. Sai a lokacin suka fara tunanin me ma yaje yi a Bauchi? Rashin mai ba su amsa yasa suka fauwalawa ubangiji al'amarin don ganin ya zai 'kare tare da addu'ar Allah ya sa jikan nasu yana cikin aminci.
Ko da Zahrah ta fahimci halin da ake ciki sosai ta shiga wata matsananciyar damuwa har kanta ya fara ciwo, fatanta da addu'arta Allah yasa a wani mugun abu bane ya faru da shi duba da yadda gabanta ke tsananta fa'duwa tunda ta shi daga bacci. A haka ta sa su Hajjaty a gaba tana kwantar musu da hankali that Yaya Sadauki na lafiya may be yanayin aiki yasa bai 'kira ba, su masa uzuri ko yaya ne zuwa safiya in sha Allah zai 'kira, Allah sarki tsofi, da haka hankalinsu ya 'dan kwanta ka'dan.
*AUNTY MABRUKA*
Sosai kanta ya fara sarawa saboda damuwar da ta ma'kalawa kanta na rashin samun wayar mijin nata. Bayan ta yi sallar Maghrib ta samu ta 'dan kwanta kan praying mat 'din cikin ranta tana nema masa kariyar ubangiji a kowanne hali yake. Kamar an zabure ta ta mi'ke ta fito parlour ta kwanta tsawon wasu da'ki'ku kafin daga bisani kamar mai shafin iskoki ta kunna TV, da yake jiya shi yayi kallon 'karshe a NTA, hakan yasa tana kunnawa ta yo baya ba tare da sanin takamaimai dalilin jin son ganin tashar ba kasancewarta mace maras son hayaniya da wargi, sam ba ta damu da kutsa kanta rayuwar kowa ba hakan yasa ba ta tashi da son kallon labarai ba.
Kwacakom hankalinta na ga TVn har sadda suka tafi talle, bayan wasu mintoci kuma suka dawo, kamar an ce ta gyara kwanciyarta kuwa ta 'dan zunku'da, maimacin labaran rana aka fara, tana gani zuciyarta na tsananta bugu kamar za ta faso 'kirjinta ta fice, ba ta ankara ba haka ta ga abun da yayi sanadiyyar tashin hankalinta, idan har ba ta manta ba to babu shakka Bauchi mijim nata ya tafi. A matu'kar firgice ta tashi tsaye tana dafe saitin zuciyarta, kafin ka ce me wani irin jiri ya kwashe ta, nan ta fa'di 'kasa sumammiya.
*YAYA KHALIL*
Tashin hankali, wai ba a sa masa date, tunda ya shiga facebook nasa ya fara cin karo da wasu irin post wanda kusan dukkansu are relevant to each other, a lokaci 'daya zuciyarsa ta 'kara tsananin bugu haka kuma 'kwa'kwalwarsa ta tsaya cak da aiki, ba abunda yake fahimta tsawon wani lokaci, abun kamar tsafi 'kwa'kwalwarsa ta dawo aiki. A matu'kar razane yace "What!" Sai kuma ya mi'ke tsaye yana 'kara zuba idanuwansa ga screen 'din wayarsa don 'karyata abun da idanuwansa suka hango masa. Bai kai ga cimma matsaya ba sai ga 'kira daga Alhaji Babba.
A matu'kar ru'de ya 'daga yana fatansa dai Allah yasa Alhaji Babba zai 'karya masa abunda ya gani ne. "Assalamu Alaikum, an yini lafiya Alhajinmu?" Sallamar kawai ya amsa masa, tun daga yanayin muryarsa Yaya Khalil ya rasa gaba'daya hope 'dinsa. Ba tare da ya bi takan gaisuwar da Yaya khalil ya masa ba yace. "Kai Khalil, ina 'dan uwanka ne?" kamar zai yi kuka yace "Alhaji ai Sadauki ya tafi Bauchi 'dazun nan ma jirginsu ya tashi, sai dai kuma...." ba tare da ya bar Yaya Khalil ya kai ga aya ba ya fara doka salati. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'una..innalillahi wa'inna ilaihi raji'una.." haka Alhaji ke ta doka salati ba tare da ya katse kiran ba, a matu'kar firgice Yaya Khalil ya katse kiran don zuwa yanzu ya yadda da abubuwan da ya gani. Tsabar yadda zuciyarsa ta gama raunana ta kuma bushe 'kayau hawayen ma kasa zubo masa suka yi, tunani ya fara me ya kamata yayi yanzu? Tunawa da 'yar'uwarsa yayi hakan yasa ya figi motarsa sai gidan Yaya Sadaukin.
Sallama yake kwa'dawa but shiru, hakan yasa ya shige da sauri yana addu'ar Allah dai yasa news bai kai gareta ba, bulb ya kunna sai dai abun da idonsa ya gani yasa zuciyarsa bugawa tare da 'kara raunana. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai yake furtawa, a hanzarce ya nufi Aunty Mabruka da ke kwance 'kasa a halin rayuwa ko mutuwa. Ya ma rasa mai ya kamata yayi sai da ya hangi glass cup 'din da ke kan centre table yayi hanzarin 'daukowa ya shafa mata a fuska, wani irin gauron numfashi ta sau'ke tare da fa'din "Shikenan..." ba ta kai ga 'karasawa ba jikinta ya 'kara saki.
A matu'kar tsorace ya 'kara 'daga hannunta, ganin ya sake yasa ya 'daga ta da sauri ya nufi mota da ita, ko da maigadi ya g haka tuni ya wangale get yana fatan Allaj yasa lafiya...musamman da ya san Yaya Khalil mutum mai barkwanci amma yau ko kallonsa bai ba, uwa uba kuma Hajiyar da yaga an fito da ita a hannu.
Da matsanancin gudu ya figi motar, bai tsaya ko'ina ba sai asibitin estate nasu, a matu'kar 'dimauce ya fito da ita a hannunsa, nan ya ma rasa ina ne mashiga sai dube-dube yake. Dr. Mubarak da ya fito don wucewa gida ya ga Yaya khalil ri'ke da maras lafiya yasa ya kwa'da masa 'kira, a matu'kar 'dimauce ya waiwayo, da sauri Dr. Yayi wa nurses magana, kan kace me sai gasu sun turo stretcher har zuwa wurin da yake. Babu 'bata lokaci suka shige ciki da ita don bata taimakon gaggawa. Yaya khalil bai tsaya ba ya kira Numbern Humaira yace tayi maza ta taho asibiti za ta kula da mai jinya, idan ba ta same shi ba tayi wa Dr. Muba magana zai kaita. Da haka ya katse kiran yana bin wayarsa da kallo, sai a lokacin ya ga missed calls ba adadi, Daddy, Papa, da sauran uncles nasa duk sun 'kira ba adadi, sauran cousins nasa da su Aunty Madina duk sun 'kira bai ma sani ba, haka friends nasu ma 'kira babu adadi.
Ta riga ta tabbata, hakan yasa ya nufi cikin estate 'din don ganin halin da suke ciki. Abun mamaki har lokacin su Hajjaty da alama labari bai kai musu ba sai dai suna cikin matsanancin tashin hankali. Ajiyar zuciya ya sau'ke daga nan ya juya ba tare da ya ida shiga ba, karo suka ci da Ya Qasim wanda fuskarsa tayi ja alamar dai kuka yayi ga kuma tashin hankali 'karara a fuskarsa. Rungume shi Yaya Qasim yayi tare da sakin wani irin kuka wanda duk wani mai sauraro ko mai gani yaji ko ya gani dole zuciyarsa ta raunana more especially da ya kasance namiji ne ke kukan, namijin ma irin Yaya Qasim da ya kasance mutum mai juriya da tawakkali.
Har lokacin Yaya khalil bai samu damar zubar da 'kwalla ba ko da kuwa 'digo 'daya ce, bai hana Yaya Qasim 'din kukan ba saboda shima kansa zuciyarsa ta gama raunana har hawayensa sun 'kafe, tsawon mintuna goma suka kwashe suna rungume da juna tukun Yata Qasim ya saki Yaya Khalil yana aika masa wani irin kallo da ke nuna bu'katar 'karin bayani. "Da gaske shikenan mun rasa shi?, kace min ba haka bane Khalil!" Ya fa'da a matu'kar raunane. Rasa wace irin amsa zai bashi yayi hakan yasa ya ke'be shi zai wuce. A matu'kar zafafe Yaya Qasim ya cakumo Yaya Khalil 'din.
"Ya za ka wuce ba ka bani amsa ba, ka fa'da min meye gaskiyar batun!" Ya fa'da cikin zafin rai "I can't afford to lose suck brother Khalil, ka ce abun da na gani ba haka bane!" Ya fada cikin raunin murya. Ganin yana shirin tara jama'a shi kuma ba ya so a ji mutuwar sarki a bakinsa yasa ya bu'de baki murya 'kasa-'kasa yace "It's all true Akhy, Yaya mun rasa 'dan'uwanmu da gaske....." Ba tare da ya 'karasa ba ya zame jikinsa zai koma mota sai dai me? Ganin su Hajjaty da wasu daga family members 'din yasa ya 'dan tsaya yana kallonsu.
Muryar Hajjaty ce ta doki kunnensa "Ban gane me kuke magana a kai ba Halilu,waye aka rasa kuma meyasa Qasim ke kuka? Me ya faru ku bani amsa!" Ta fa'da cikin sigar tsorata don ba shakka da za a gwada bugun zuciyarta a lokacin to tabbas ya tsananta.
Ajiyar zuciya Yaya Khalil ya sau'ke ganin convoy na motocin iyayensu sun shigo. Juyawa yayi ba tare da ya motsa daga yadda yake ba yayin da su kuma gabansu ya yanke da juyawarsa ba tare da ya amsa tambayar Hajjaty ba. A tsanake suka fito fuskarsu kame kamar ba abunda ke damunsu, sai dai fuskar Papa da Alhaji Babba ba ta iya 'boye yanayin da suke ciki. Haka suka tunkaro part 'din Hajjatyn a jere, abun da ya 'daurewa Hajjaty kai shine babu wanda yayi magana, ganin hakan yasa Alhaji Baba da ya kasa furta komai bayan bugun zuciyarsa da yake saurara ya ce "Mu shiga ciki"
Babu musu suka bi bayansa kowa ya koma, a matu'kar tsorace kowa yake ta yadda za ka fahimci hakan parlourn ya koma kamar wani graveyard ko sautin numfarfashinsu ba a ji yayin da kowa idanuwansa ke 'kasa.
Cike da dakiya Daddy ya yi sallama, bayan sun amsa ya fara jawabi. "Kamar yadda muka sani duk abunda ya faru da bawa mu'kaddari ne daga mahaliccinsa, ita 'kaddara kan zowa kowa ta fuskoki mabanbanta, kada mu mance duk abunda ya faru da bawa to a rubuce yake cikin zanen rayuwarsa, babu yadda kuma bawa zai yi ya tsallake abunda ubangiji ya gindaya a kansa."
Shiru yayi yayin da zuciyarsa ke wani irin bugu, cike da danne emotions nasa ya bu'de baki zi ci gaba, ku kiyasta cewa ku ne a wannan mataki kuke jiran jin me Daddy zai fa'da, kamar haka su ma mutanen da ke zaune a parlourn suka shiga hali irin na ru'du musamman wa'danda ba su san me yake faruwa ba.
"Ubaniji shi ke da ikon busa mana numfashi haka kuma yana da damar ya tsayar da shi a lokacin da yaso saboda cikar wa'adin numfashin da ya rubuta za mu yi tsawon rayuwarmu! Ubangiji kan 'dauki ran wani daga cikin mutane ba don ba ya son sa ba, kamar yadda ya 'dauke ran habibinsa kuma shugabanmu Annabi muhammad, zai iya 'daukar kowa duk kuwa yadda mutane ke tsananin sonsa, ko da kuwa duk duniya za su sadaukar da numfashin su saboda wannan rai 'daya, ubangiji ba zai dakatar da 'kudurinsa ba."
Shiru ya kuma yi, i zuwa wannan lokaci hankalin duk wani mazaunin parlourn ya kai ga 'kololuwar tashi yayin da masu raunin cikinsu suke share hawaye saboda zukatansu ba za su iya 'daukar wannan al'amari ba.
*React and share please*
[1/22, 4:40 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 3️⃣1️⃣
﷽
Shi kansa Daddy a wannan ga'bar jarumtarsa ta kusa gushewa, muryarsa na rawa ya ci gaba da magana.
"Na san kun 'kosa ku ji meyasa nake wannan dogon sharhi, ina so ku dubi maganganu na ku musu kyakkyawar fahimta, ku yi imani da 'kaddara mai kyau ko akasin haka, ku amshe ta hannu biyu kada ku yiwa ubangiji butulci."
Hajjaty da zuwa yanzu jikinta ke karkarwa ga yadda zuciyarta ta yanke tace "Muna sauraronka Umar, ka fa'da mana me yake faruwa."
Murmushin da na kasa fahimtar na meye Daddy yayi, shi ka'dai yasan yadda zuciyarsa ke yi. Daurewa yayi yace. "Tabbas mun yi babban rashi cikin wannan family, mun tafka rashi wanda in mun kar'ba da hannu biyu hala ubangiji ya kawo mana kwatankwanci." "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'una" gaba'daya parlourn ya 'dau salallami, wa'danda ba sa kuka ma tuni sun fara saboda yadda sa'kon rashi ya bugi zuciyarsutun kafin su ji wanene ma ya Rasu.
Shima Daddy sai da ya faki idanuwansu ya share 'kwallar da ta zubo masa. "Ubangijin da ya ba mu Sadauki yau ya 'dauki abunsa sakamakon ha'darin jirgin sama da ya afku, a halin yanzu babu abunda yake bu'kata daga gare mu matsayin masoyansa face addu'a, babu shakka kowanne mai rai mamaci ne." Yana gama rufe bakinsa Hajjaty ta sulale 'kasa sumammiya, Alhaji Baba kam hawaye ne kawai ke sintiri daga idanuwansa. Shikenan! Shikenan ya rasa jikansa mafi soyuwa gare shi? Zahrah kuwa tun lokacin da kalaman Daddy na 'karshe suka doki kunnenta ta daina fahimtar komai, nan duniyar tafara juya mata, kafin kace me ita ma ta sulale 'kasa sumammiya.
Wa'danda suka zubda 'kwalla su godewa Allah atleast sun rage wani kashi na tarin damuwarsu, har wannan lokaci ko 'digon 'kwalla ba ta zubo daga idanuwansa ba, ra'da'din da yake ji ba zai misaltu ba saboda duk duniya babu wanda ya sha'ku da shi sama da shi, tun ba su da hankali suke tare har zuwa wannan lokaci amma mutuwa ta yi musu yankan 'kauna, a rikice ya nufi Hajjaty da idonsa ya fara kaiwa gare ta kafin ya juyo 'daya 'bangaren da Zahrah da kuma Nainarh ke yashe 'kasa, Ransu na shirin barin gangar jikinsu.
Alhaji Babba da kuma Papa wannan mutuwa ta kaf 'daya ta bugi zukatansu haka nan Abba da saura kawunnan mamacin, ba 'karamar dauriya Daddy yayi ba saboda ya kwantar musu da hankali don ba lallai a samu wanda ya kai shi jin ra'da'din rasa nagartaccen 'dan nasa ba. Ganin yadda wasu suka fara fita hayyacinsu yasa ya 'daga waya ya 'kira aka turo ambulance don tafiya da Hajjaty, Nainarh da kuma Zahrah wa'danda suke sume, bayan an wuce da su asibiti ne kowannensu ya koma 'bangarensa don gobe da sassafe suke sa ran wucewa takamaimai wurin da za a samu pieces na jirgin la'alla ko za a samu gawarsa, in ba a samu ba kuma sai a yi masa salatul ga'ib.
Tabbas wannan rana ta shiga tarihin wannan ahali musamman da suka tafka babban rashi wanda kai tsaye za mu iya 'kiransa da 'kaddararsu, shikenan fa ya tafi, babu wanda zai kuma kallonsa a wannan gida na duniya, Allah sarki rayuwa. Amma duk da haka ana sa masa ran dacewa ne saboda shaidar da ya samu. Mutuwarsa in sha Allah hutu ce, ba ya shiga ha'k'kin kowa, ba ya zaluntar kowa kuma tsakaninsa da mahallincinsa ma ana kyautata zaton kyakkyawar mu'amala ce, ya gama aikin alkhairi, da azumi a bakinsa wannan abu ya afka masa.
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ubangiji ya ji'kan Yaya Sadauki yasa aljanna ce makomarsa. Tabbas kowanne mai rai sai ya 'dan'dana mutuwa, ina wa'danda suka shagala da duniya? Kuna ganin irin wannan mutuwa bagtatan kuwa?, ga dai Yaya Sadaukin nan da safiyar Allah kakanninsa sun gana da shi, haka kuma Zahrah da take da rabo, ya yi wa matarsa sallama lafiya lau yanzu ga shi ana labarin mutuwarsa, ya zama tarihi kuma.
Ya kamata mu 'kara kyautata ala'karmu da mahalicci haka nan kuma da mutane, muna tuna mutuwa, muke sanya ta a agenda namu, mu sa a ranmu in mun wayi gari lafiya ba lallai mu yammace da ran mu ba, haka nan in mun kai yammaci mu sa a ranmu ba lallai mu kasance raye ba safiya ta gaba. Wannan zai 'kara sa mu 'kara kusantuwa ga mahaliccinmu. Allah yasa mu dace, wa'danda suka riga mu gidan gaskiya tun daga kan al'ummar farko zuwa yanzu muna ro'kom ubangiji ya musu rahama, idan tamu mutuwar ta zo ubangiji ya sa mu cika da imani.
Kafin 9:00pm tuni mutuwar ta zaga kowanne sa'ko na ahalin kama daga na cikin gida da wa'danda ke nesa da gidan, mutuwar da ta ratsa zukatan mutane da dama yayin da ta zama sulhu ga wasu, ta kuma zama abun farin ciki a zukatan wasu sai dai su ma kada su manta ba tabbata za su yi a doron duniyar ba.
Sosai ABATCHA ESTATE ya zama tamkar ma'kabarta, kowanne sashe shiru yake kowa na 'kara jimamin mutuwar yana hawaye irin na yankan 'kauna, ba iya ahalin gidan ba hatta ma'aikatan gidan sun matu'kar razana da mutuwar Yaya Sadauki, sun yi kuka tamkar wa'danda suka rasa wane sashe na jikinsu, kai dole ma su yi kukan don kuwa ba lallai Marigayi ya mu'amalance ka ba ka ji 'kaunarsa cikin ranka ba, yana da salon mutuntawa da iya mu'amala. Saboda yanayin Alhaji Baba yasa Daddy ya zauna a tare da shi, Yaya Khalil da kuma Hajiya Babba suka wuce asibitin don zama kusa da marasa lafiyan, sai a lokacin ne Humairah ta koma, a nan kuma Hajiya Babba ta san da cewa Mabrukan ma ashe tana nan.
Duk wanda ya farfa'do cikinsu da zarar ya tuna da event 'din da ya faru sai ya koma, haka dai wannan dare ya kasance ga wa'dannan mutane uku, sai dai kuma wa'danda ke jinyar sosai zukatansu suka fi raunana, gwanda Hajiya Babba ta zubarda hawaye, Yaya Khalil kam ba a magana illa iyaka dai idanuwansa sun sauya daga wa'dannan fararen zuwa jajaye kamar gauta ga kuma yadda suke masa zafi kamar ana hura wuta a ciki, zafin da suke masa kuma in za a kwatanta shi da wadda zuciyarsa ke yi ba a magana, jijiyoyin kansa sun fito ru'du-ru'du. A hakan idan Hajiya ta gama kukanta sai kuma ta hau masa nasiha. Addu'a kuwa daren ranar ya sha ta daga masoyansa.
Wannan dare dai ya yawaita tsayi tamkar an dakatar da tafiyar lokaci haka suke gani ko dan saboda kashi 98% nasu ba su rintsa bane, sahur na azumin washegari ya gagara har alfijr ya keto. Bayan sallar asuba kai tsaye iyaye mazan banda Daddy da ke tare da Alhaji Baba suka fice daga gidan don nemo gawarsa shima a masa sutura a mi'ka shi gidansa na gaskiya. Allah ya masa rahama.
Washegari da safe su Aunty Madina suka diro, su Yaya Haidar da Yaya Junaid tare da ahalinsu su ma suna hanyarsu ta zuwa tunda sa'kon ya kai gare su, sai dai ba su wani 'daga hankali akai ba saboda ba su yadda da zancen mutuwar tasa ba.
Yaya Junaid da kansa ya 'kira Hajja a waya ya sanar mata. Sosai Hajja ta yi tawakkali sai dai damuwarta 'daya bata san ya za ta tunkari Momma da zancen ba, haka dai ta 'kira gaba'daya 'yan uwan Mommah ta sanar da su, kafin kace me duk sun hallara ana ta koke-koke, Mommah da ta fito don ganin su waye ke kukan ganin ahalinta yasa gabanta fa'duwa tana addu'ar Allah yasa ba Hajja ba ce ta rasu suke wannan kuka. 'karasawa tayi kusa da su tana rage girmn idanuwanta "Bayin Allah kun sa mu gaba da kuka, don Allah me ya faru"
Ganin Hajja ta fito itama tana hawayen yasa ta 'dan sau'ke ajiyar zuciya sai dai kuma hawayen Hajja sun sanya mata ru'dani da bugawar zuciya mai tsanani da ba za ta iya jurewa ba, 'karasawa tayi ta rungume Mommah . Sosai 'yan'uwanta suka tausayawa yanayin da ta shiga sai dai har lokacin Mommah ba ta san me yake faruwa ba. "Ki shirya Shughrah za mu fita ne." Hajja ta fa'da tana sakin Mommah tare da share 'kwallarta. "Ina za mu je ne haka Hajja? Sai kuka kuke kun 'ki fa'dama min dalili, don Allah ku fa'da min kada zuciyata ta tarwatse" Momma ta fa'da tana 'dan kawar da kanta gefe. "Ki ai shirya kawai Sughrah, idan mun je za ki ji me yake faruwa, sai dai kuma kafin nan ina ro'konki da ki yi ha'kuri da abunda za ki ji, kada ki yi tunanin ubangijin da ya salla'da hakan bai son ki ne, kin ji ni?" kai Mommah ta gya'da zuciyarta na 'kara karyewa. "Maza je ki yi wanka ki karya, ku kuma kukan ya isa, addu'a ce kawai mafita a yanzu."
*HOSPITAL*
Babu laifi Hajjaty da ta farka safiyar yau ta fauwala ubangiji komai ta kuma 'daura da yiwa shalelen marigayin jikanta addu'a, hakan ne ma yasa Dr. Muba da ke famar 'dawainiyar jinyarsu yayi discharging Hajjatyn, atleast in ta koma can ra'da'din will be relieved, Yaya Khalil ne yazo ya mayar da ita can aka ci gaba da zaman jiran tsammani tare da addu'oi.
*MOMMAH*
Drivern Mommy Nasiba ne ya 'dauko su Mommah, su Aunty Rahina da mazajensu suka taho da motar Yaya Kabiru, gaban Mommah bai daina yankewa ba lokaci bayan lokaci kuma takan le'ka fuskokinsu taga suna share 'kwalla. Mamaki ne ya cika ta ganinsu a Abatcha Estate yayinda tsoro da fargaba suka yi wa zuciyarta 'kawanya, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai take maimaitawa har motarsu ta daidaita parking, bayan sun fito suka shiga part 'din Hajjaty.
A lokacin an dawo da Hajjaty, parlourn nan kuwa cike yake da jama'a everywhere and every angle, abunda ya 'daure kan Mommah shine yadda kusan duk mutanen cikin ke share 'kwalla. "Tabbas mutuwa aka yi" ta fa'dawa kanta "Amma waye?" Babu mai ba ta amsa yasa tayi wa Hajjaty Ya ha'kuri ba tare da ta san 'Dan da ya wahala da miyagun halayenta ne ya bar mata duniyar da ta shana ba.
Tana rufe baki sauran jama'ar parlourn suka hau yi mata ta'aziyya saboda kowa ya san Mommah. Da kallon mamaki take binsu can dai ganin duk wanda ya le'ko sai ya mata ta'aziyya yasa ha'kurinta 'karewa ta tambaya. A wannan karon Hajjaty ce ta ba ta amsa da fa'din "Wanda kika cutar 'din dai Sughrah yau Allah ya kar'bi kayansa, sai ki huta ki kwa'da duniyar ki lashe ta." Tana mai share 'kwallar da ke sintiri daga idanuwanta. "Ban gane ba Hajjaty ki min bayani" Mommah ta fa'da cike da tsoro. Ba tare da jin wani abu ba Hajjaty ta ba ta amsa kamar yadda ta bu'kata "Sadauki dai, Sadauki shi ne yayi ha'darin jirgin sama jiya da safe, Allah ya...." kasa 'karasawa Hajjaty tayi tana mai share 'kwallarta da in har ta ci gaba da maganar kuka zai iya kufce mata.
A matu'kar firgice Mommah ta mi'ke tana sakin wani malalacin murmushi "Lallai Hajjaty, Sadauki ba zai mutu yanzu ba, bari ki ga yanzu yanzu zan kira wayarsa kuma zai 'daga" ganin ba ta cikin hayyacinta yasa kowaya fara jijjiga kai yana tausaya mata, Hajjaty ne ta nuna wa Mommah 'kofa tace "Sughrah ki je 'bangarenki, wasu ba'kin za su shigo" ba tare da fahimtar me Hajjatyn tace ba ta nufi 'kofa, su Mommy Nasiba suka bi bayanta to aid her with psychotherapy.
Abunda kuke tunani ya wuci hakan,tun fitarsu Mommah ba ta 'kara cewa uffan ba, ana tunanin mutuwar ba za ta ta'ba ta ba sai gashi ita lokaci 'daya hankalinta ya riga ya gushe, da ido kawai take amsar gaisuwar sai dai su Hajja su amsa da baki. Allah sarki Mommah, 'dan da take gadara da nata ne, 'dan da take fifita son zuciyarta a kansa yau Allah ya kar'be shi.
*Zahrah & Aunty Mabruka*
Hajiya Babba wacce itama hankalinta yake tashe ita ke jinyarsu, Allahn da yayi taimako Aunty Mabruka ma around 12pm ta farka kamar mahaukaciya, amma bayan nasiha da tunatarwar da Hajiya Babba ta mata ta 'dan risina, hakan yasa Dr ita ma yace ta koma gida za ta fi jin sau'kin ra'da'din mutuwar.
Zahrah ce dai ko sau 'daya ba ta farka ba tun jiya da sa'kon ya doki kunnuwanta, haka Hajiya Babba za ta tofa addu'o'i a cup ta shafa mata amma shiru. Tsawon wannan lokaci dai ba a samu wani update daga mutanen Bauchi ba. Can wuraren Asr ta farfa'do, Alhamdulillah itama a hankalinta ta tashi sai dai kuma banda hawaye ba abunda ke zarya kan fuskarta, 'kunci da damuwasun dabaibaye zuciyarta, ya ma za a yi a ce Yaya Sadauki is nomore alive a yi tunanin ita za ta rayu? That's impossible. Duk irin yadda Hajiya Babba ke ba ta baki tana mata nasiha babu abunda ya sauya coz Zahrah is not fully concious, physically dai ga ta amma mentally she's not there, tunaninta ya tafi can ga begensa tare da fatan wani ya tayar da ita daga nauyayyan baccin da ya 'dauke ta ko za ta samu ta farka daga wannan mummunan mafarki, a haka dai har aka mayar da ita gida ba ta magana sai dai kallo, kowa ya ganta ya san ta ta'bu da wannan rashi, sosai kowa ya tausaya mata.
*React and share fisabilillah* *𝓓𝓲𝓪𝓶𝓸𝓷𝓭 𝓑𝓱𝓪𝓽𝓸𝓸𝓵'𝓼 𝓹𝓮𝓷*
[1/23, 9:11 AM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 3️⃣2️⃣
﷽
Zahrah ba ta jima da dawowa ba su Nasreen suka dawo part 'din Hajjaty don kasancewa da ita, ba wai su mutuwar ba ta shafe su bane sai dai babu shakka sun an cewa Zahrah feels the pain more than them. Suna zaune su Aunty Na'eemah ma suka iso, tabbas na gaskata son da ake yi wa Yaya Sadauki, in-law 'dinsa ce amma how she looks will define the actuall pain she's in, Allah ya ma Yaya Sadauki Rahama.
Duk da tsananin 'kunci da suke ciki bai sa an dakatar da duk wani aikin alkhairi da ake yi a gidan ba, hasali ma shirin 'karawa ake yi, daf da maghrib aka kammal girkin da ake yi kai tsaye aka fara ficewa da maka-makan kuloli daga estate 'din zuwa masallatai mabanbanta kafin a kwashi abun sha a wuce da su. Ko da aka sha ruwa ma babu wani mahalukida ya bi ta kan abinci bayan ruwa da dabino da suka saka a bakinsu.
Sai da aka yi isha'i su Alhaji Baba suka dawo, hankalin kowa a tashe yake, a lokacin wa'danda suka 'karyata mutuwar suka yi surrender, tabbas ta tabbata. A part 'din Alhaji Baba aka aje gawar da nufi zuwa safiya a kai shi makwancinsa. Bayan sun huta ne su Hajja suka zo suka yi musu ta'aziyya, kan Mommah 'kasa ba ta bari sun ha'da ido da su ba, gani take kamar idon kowa a kanta yake ga abubuwan da ta aikata baya. Aunty Madina mai dauriyar itace ta sanar da Daddy yanayin da aka yini a ciki bayan tafiyarsa, sosai yayi fa'da kamar zai yi kuka. "Me yasa ba za ku amshi 'kaddararku ba? Shin kun fi mahaliccinsa 'kaunarsa ne? Ya kamata zuwa yanzu mu fauwalawa ubangiji komai, mu sani babu wani cikin mu da zai 'kara ko da second 'daya ne idan wa'adinsa ya cika, a yanzu addu'arku kawai Aliyu yake bu'kata ba wai kuka ba, 'kuncin da kuka yafawa zukatanku da wa kuke? Da ubangijin da ya 'dauke shi?" Shiru suka yi babu wanda yace 'kala. "Rashin cin abincin da kuke kuna tunanin in yana raye zai ji 'dadi ne? Kuna tunanin hakan zai dawo muku da shi ne? Kowa ya 'dan'dani mutuwar nan cikin ransa, amma 'kuncin da kuke jefa kanku ba dawowa da shi zai yi ba, ku yi ha'kuri don Allah, ku yi wa Aliyu Addu'a shine ka'dai maslaha." Daga haka ya mi'ke ya fice daga parlourn don ba ya bu'katar rauninsa ya bayyana garesu. Daga nan kuma su Hajja suka wuce da Mommah idan ya so sassafe sa dawo washegari.
Saboda Nasihar Daddy ne yasa aka 'dan ta'ba abincin, Zahrah dai ba ta ci ba saboda ba ta ma san ina take ba har lokacin. Haka wannan dare ahalin nan suka riske shi idanuwa bu'de sai dai kusancinsu da mahallicinsu da ya 'karu, sosai suke sanya marigayin cikin addu'o'insu.
Tun daren aka sanar da jana'izar Yaya Sadauki da za a yi a masallacin estate 'din, hakan ya sa da sassafe aka fara shirin yi masa sutura. Daddy da kansa yayi ma gawar 'dan nasa wanka wacce ta koma tamkar ba shi ba, babu alamar cewa fatar mutum ce wannan saboda yadda ta 'kone bare a zo gandin gane kamanninsa, babu alamar wata halitta kamar hanci a fuskarsa saboda yadda ta kwazazza'be.
Bayan an masa wanka aka shirya shi tamkar yadda ake wa kowacce gawa, sannan aka bar shi a nan 'bangaren saboda ba kowa ake so ya ga gawar ba, in so samu ne ma sai za a fita da shi masallaci za a kai shi in da masu masa addu'a su yi.
Da misalin 'karfe tara na safe aka fito da gawarsa zuwa parlourn Hajjaty saboda mutane sun riga sun taru za a masa salla. Ko da aka ce Hajjaty ta masa addu'a cike da 'karfin hali ta matso kusa da gawar tasa da ke 'kamshin turare ba tare da ta bu'de fuskar ba ta ha'da hannayenta tana masa addu'a, bayan ta kammala Alhaji Baba ya dubi Mommah yace ita ma in za ta kalle shi to, da sauri ta 'karaso gaban gawar ta tsugunna hawaye na zuba daga idanuwanta ta ha'de nata hannayen ta fara jera masa addu'o'i. Ko da ta gama aka 'daga gawar da niyyar ficewa da ita don a sallace ta kwatsam Zahrah da ke 'dakinta ta fito da gudu ta zube 'kasa tare da ri'ke 'kafar Papa da ke ri'ke da makarar tana fa'din "Ku yi wa Allah ku yi wa manzon tsira ku ajiye min Yaya na, wallahi bai mutu ba, da ransa kada ku bisne shi. Papa ka duba ka ga Yaya ya ce min zai zo min da dadda'dan labari amma kuce ya rasu? Wallahi Yaya na bai mutu ba, Yaya ka duba Lilynka ce fa" ta fa'da tana sakin wani irin murmushi "Ka tashi daga makarar nan ba wurin zamanka bane, Yaya ka bar wannan wasan da Lily..."
Fahimtar ba ta cikin hayyacinta yasa su Aunty Na'eemah da su Mimie suka ri'ke ta su kuma su Daddy suka fice da gawar, da 'kyar suka tisa ta gaba ta yadda ta koma bedroom nata wasu irin zafafan hawaye na zuba a idanuwanta. Nan aka wuce da Yaya Sadauki aka masa sallah sannan aka raka shi makwancinsa.
Tsawon wannan kwanaki biyu na rasuwar Yaya Sadauki, akwai mata da kuma 'ya'yan da ban ga giftawarsu ba cikin ahalin bare a yi tunanin za a yi zaman jimami a tare da su. Bayan kwana uku kuma Alhaji Baba yace kowa ya kama nasa wurin, a ci gaba da yi wa Yaya Sadauki addu'ar Allah yasa ya dace. Babu wanda ya tsallake wannan umarni na Alhaji Baba duk aka watse, Aunty Madina da mijinta da kuma sirkanta suka koma, Yaya Junaid ma ya koma haka Yaya Haidar.
'Bangaren Hajjaty ya rage daga ita sai Alhaji Baba sai kuma Zahrah wacce har yau ba ta farfa'do ba, magana ma ba ta 'kara yi ba tun lokacin da aka fice da gawar Yaya Sadauki. Nainarh wacce yanzu suke kwana tare da Zahrah ta yi iyakar iyawarta wurin ta sa Zahrah ta mance da Yaya amma abun ya fasaya, hakan yasa Hajiya Babba tace daga ita har Nainarh su tattaro su dawo part 'dinta idan ya so Ra'ees ya zauna tare da Hajjatyn.Da haka Zahrah tattara ta koma can 'din ba don ta so hakan ba.
Haka dai rayuwar taci gaba da tafiya, rashin wani ba zai sa a rasa wani ba, kowa da dalilin da ya sa ubangiji ya busa masa rai. Sati da guda da wannan rashi su Zahrah suka fara shirye-shiryen rubuta JAMB nasu, saboda haka suka koma makaranta kamar dai da amma Zahrah har yanzu ta kasa komawa daidai, gaba 'daya ta rame kamar ba Zahrah ba kuma har yau 'din ta kasa amincewa da cewa Yayanta ya rasu, gani take kamar wata rana zai dawo gare ta.
A matu'kar wahale ta dawo daga school saboda yadda azumi ya fara bata wahala coz sai a yau 'din ne ta fara. A part 'din Hajjaty ta yada zango saboda tana bu'katar hutu, can kuma in ta koma ba za su barta ta rintsa ba don ita ka'dai tasan yadda take ji a jikinta. Wayarta da ba ta iya rabuwa da ita a halin yanzu ta jefa gefe kana ta baje kan bed nata.
Ko da lokacin shan ruwa yayi Zahrah ta koma wurin 'yan'uwanta, bayan an sha ruwa suka gabatar da sallarsu ta maghrib daga nan kuma suka mi'ke don zuwa sannu da shan ruwa ga sauran jama'ar ahalin kamar yadda suka tsara, sai da suka ziyarci kowanne part na gidan, idan akwai squad member nasu sai su ha'du su 'kara gaba, bayan sun zaga ko'ina na gidan suka nufi part 'din Hajjaty. Tun daga door step gaban Zahrah ya buga har sai da ta 'dan dakata. Nainarh ta kalleta tace "Ya dai Zahrah" kanta ta kawar gefe ba tare da ta ce komai ba ta fara 'ko'karin shigewa, hakan yasa ita ma Nainarh ta bi bayanta suka shige.
Wasu ba'ki ne guda hu'du a zaune a parlourn tare da Hajjaty sai dai ba ka oya gane su wane ne saboda yanayin hasken 'dakin...dim light ne shiyasa. Cike da girmamawa suka 'karasa suna gaida ba'kin sai dai kamar yadda suka shigo ashe cikin ba'kin akwai wacce ba ta gaida Hajjaty ba, still dai ba kuma ta amsa gaisuwar su Zahrah ba a wannan karon. Ra'ees ne da 'dan banzan rigimarsa ya taho da gudu ya kunna light sannan ya yo gurin Hajjaty.
ko da aka kunna hasken abun da Zahrah ta fara cin karo da shi ya matu'kar sa bugun zuciyarta 'kara tsananta bugu, kamar a mafarki! Saboda ta farfa'do daga sumar tsayen da tayi ta murza idanuwanta da hannunta don 'kara confirming abun da idonta ya gani, gaskiya ba daidai ya nuna mata ba wannan karon ma hakan yasa Zahrah ta fara marin fuskarta tana fa'din "Farka farka Zahrah" Tana 'kara bu'de idanuwanta dai same abu haka take gani.
_Hajjaty_ tun da haske ya gama gauraye parlourn ta kai dubanta ga ba'kin, idan har mai karatu ya san ru'du, to Hajjaty ta shiga wani irin hali na ru'du, waye take gani haka gabanta? "Nooo that could not be her, ba ita bace" tayi reassuring kanta.
Ihun da Zahrah ta buga tana nufar 'daya daga cikin ba'kin tana ihu tana fa'din "Mamah na!" Sai kuma ta 'kara hugging nata tightly kamar za a 'kwace ta daga gareta. Wannan ihu da Zahrah tayi shi ya dawo da Hajjaty daga duniyar tunani, tabbas ba gizo Madina take mata ba,'diyarta ce yau ta dawo gareta, nan hawaye suka fara wanke fuskar Hajjaty, Zahrah ce ta raba jikinta da na Mamah ba tare da hawayen fuskarta sun daina zuba ba. "Mamah yau kam kin dawo..." bata ida fa'din abunda za ta ce ba taga Hajjaty rungume da Mamar dukkansu sai kuka suke. Babu wanda yayi 'ko'karin raba su haka aka bar su suna kukansu, they deserve to cry, kusan shekaru ashirin yanzu rabonsu da juna, dole kuwa su koka.
Nasreen, Nainah, Rumaysa, Zakiyya da yanzu sun fahimci cewa Mamah ce ta dawo yasa suma suka fara zubar da 'kwallar farin ciki tare da dawowa suka rungume Zahrah a tare. Inna, Asma'u da kuma Balkisu wa'danda su suka rako Mama su ma mamaki ya gama cika su musamman yadda suka ga Mama da Hajjaty na kukan farin ciki, hakan ya 'kara tabbatar musu da cewa ba 'karamar soyayya da sha'kuwa bace tsakaninsu.
Bayan an share mintuna goma da wasu sakannin ana kuka suka raba jikinsu koma na duban kowa. Hajjaty tana hawaye tace "Madina yau ke kika dawo? Farin cikin da na rasa tsawon shekarun nan yau ya dawo! Alhamdulillah" sai kuma ta sau'ka ta zube 'kasa tayi sujjada, itama Mamah sai ta bi bayan Hajjaty tayi sujjadar, sosai sauran mutanen suka bi su da murmushi da kuma tausayawa. Hajjaty da ta tashi ta dubi Hajjaty tace "Maza 'diyata tashi ki shiga ki yi wanka kafin a sanarwa Alhaji Baba da zuwanki ko?" "Ke Zahrah kai ta bedroom 'dina,ba'kin kuma ki kai su naki kafin Laraba ta gyara musu wurin kwanansu" Kallon ba'kin tayi tace "Ku samu ku watsa ruwa sai ku ci abinci, Allah yasa dai ba da azumin kuka zo ba"
Murmushi Inna tayi tana kallo Hajjaty tana kuma yaba kirki da sau'kin kan Hajjaty tace "A'a ai da yake tafiyar mai tsayi ce shiyasa bamu 'dau azumin ba" "Masha Allah, ku bi Zahrah ta 'karasa daku ko?" Hajjaty ta fa'da tana 'kwala kiran Laraba, ko da ta zo ta fa'da mata dalilin kiran sai ta wuce dining don taga me ya rage tunda ba a yi girki da su ba, an sha ruwa kuma in ta ce laraba tayi ita ma ta san ta gaji.
*MOMMAH*
Sosai wasu 'dabi'unta suka sauya sakamakon yadda rashin 'danta ya ta'ba ta, wannan hali na izza da kuma nuna isa duk babu shi, babu wannan rashin girmama manyan...haka dai duk ta koma ga ubangijinta, Sallah take tana addu'a babu dare ba rana ko Allah zai sa Daddy ya mayar da ita gidanta don nadama kam ta riga ta yi ta. A yau kuma ta kuduri aniyar tabbatar da maganar Hajjanta game da 'kawayenta wa'danda suka juya mata baya lokaci guda, kayan takaicin shine duk cikinsu babu waccetaga wulgwarta a rasuwar Yaya Sadauki, ta kuma 'kullace su za ta ji dalilinsu na 'kin ko da yi mata ta'aziyya ne.
Wannan kenan!
*React and Share please* *For those who share, jazakumullahu khairan, Allah bar ni da ku masu 'kamshin humra.*
[1/23, 3:05 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡* *TAKUN ƘARSHE* *©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_ _Arewabooks: @diamondbhatool3_ Please follow
*PAGE* 3️⃣3️⃣
﷽
Tabbas cikin wannan family babu wanda suke having good time fiye da Ammie, amma wai ace har a mata rasuwa ba za ta iya kira ko a waya ta mata ta'aziyya ba? Meye amfanin abotar. A matu'kar raunane ta wuce part 'dinta na da tana share 'kwalla tare da fatan Allah yasa wata rana tana da rabon sake rayuwa ciki. A haka har ta iso part 'din Ammie. Da sallama ta shiga ciki amma bakinta kusan biyar tukun Ammie ta amsa, sarai ta gane muryar Mommah amma ta share, sai da ta shafe kusan mintuna biyar tukun ta aiko Afifa ta shigo da ita.
A dadda'kile suka gaisa don kuwa nunawa tayi kamar ba ta san Mommah ba, tarin mamaki da al'ajabi suka cika Mommah duk takaicin kanta ya kama ta. A da idan ta zo wurinta takan ka'da yaran 'dakunan su tukun ta fuskanci Mommah, amma a yau sai ta ha'de girar sama da 'kasa ta 'daura 'kafarta 'daya kan 'daya. Gauron numfashi Mommah ta sau'ke kana ta fara magana.
"Hajiya Saudatu wurinki nazo" Fuska yatsine Ammie tace "Ina sauraronki ai, kika zo me?" Murmushin takaici Mommah tayi tace "Hajiya Saudatu dama na zo neman wani taimako ne a wurinki, don Allah ina so ki ara min ku'di ne zan biya ki da zarar Junaid ya zo" Wani malalacin kallo Ammie ta jefa mata tace "Ku'di har nawa Sughrah?" Mommah ta maimaita Sughrah cikin ranta, wai Hajiya Saudatu yau ita take ambaton sunanta gatsare babu wani girmamawa kamar ba ta fi ta ba? Kawar da tunanin tayi tace
"Million 'daya nace miki, in Allah ya yarda zan biya ki" wata irin shewa Ammie ta saka tana dariya har da dafe ciki, sai da tayi mai isarta ta dakata tana ha'de fuska. "Ke yanzu in na ara miki million 'dayar a ina zaki samu ki biya?" "Na riga ma fa'da miki Hajiya Saudatu, Junaid zai zo bikin abokinsa nan da wata biyu, da zarar ya dawo zan baki ku'dinki" "Hahahaha! Lallai kuwa! Wai zai zo biki, don yana 'kasar waje sai aka ce miki ni mahaukaciya ce zan 'dau ku'di na na baki, tab!"
Kallonta kawai Mommah tayi tace "Haba Hajiya Saudatu, cikin gidan nan in baki bani ba waye to zai bani? Ki duba abotar da ke tsakanin mu ki kuma dubi tsananin bu'kata ta da ku'din ki bani, wanda ya taimaki wani shima Allah zai taimake shi" "Toooo lallai Sughrah kin zo da bidi'a, har da wani wa'azi? To ki je masallaci ki hau mimbari sai ki yi musu, ke bari in fa'da miki mutum to mutum, ba zan bayar da bashin ba kuma ki tashi ki bani waje don kuwa babu wata ala'ka da ta rage tsakani na da ke, kada ki kuskura ki 'kara zuwa min gida, kin je kin kashe aurenki saboda son zuciya yanzu kuma za ki zo ki taya ni na kashe nawa? Wallahi ba ki isa ba, maza tashi ki bani waje, out!" Ta 'karasa a zafafe tana nuna wa Mommah 'kofa.
Jiki babu 'kwari Mommah ta mi'ke ta fara takawa Ammie na bin bayanta, sai da ta kai bakin 'kofa tace "Kin ci amanar abota Hajiya Saudatu, na gode, sai kuma gani na gaba" Harararta Ammie tayi tace "Eh maza dai fice ki bani wuri, dama can saboda tunanin za ki ha'da auren marigayin attajirin 'danki da Rumana ne, amma da na fahimci take-taken ki yasa na ja baya, can dama ni ba son ki nake ba, ku'din ki da na iyalanki nake so, yanzu tunda babu ko 'daya sai na kama gaba na, dalla can malama fice min a gida zan rufe." Ta idasa tana dakawa Mommah tsawa.
Murmushi Mommah tayi hawaye na zubo mata ta juya za ta wuce suka ci karo da Papa wanda da alama ya jima tsaye za ma a iya cewa ya ji kusan koma da suka yi, gaida Shi Mommah tayi for the first time, hakan yasa yaji banbara'kwai sai ya mayar mata da gaisuwar a maimakon ya amsa, daga Haka Mommah ta ra'bi gini ta fice abunta ta bar Papa da al'ajabin halin matar tasa yana tunanin dama can haka 'dabi'unta suke ne ko kuma dai a sama ta yafawa kanta. Da haka shima ya shiga ciki yana jinjina kansa.
Ko da Mommah ta bar sashen Ammie sashen Mamie ta nufa, a can dai ba a wula'kanta ta can ba amma an kashe mata warning na kar ta kuskura ko a hanya ta nuna ta san Mamie 'din daga 'karshe ta ba ta dubu biyar tace ga iya abunda za ta iya ara mata, tsabar takaici ko ku'din ba ta 'dauka ba ta nufi part 'din Hajiya Babba. Sosai ta samu kyakkyawar tarba daga Hajiya Babba ba tare da nuna mata wata 'kyama ba duk irin tsiyar kuwa da ta shuka mata a baya, bayan sun gaisa Mommah take tambayar Ina Aunty Mabruka. Nan Hajiya Babba ta gyara zama tace "Ai Mabruka tun rasuwar mijinta shikenan ta'ki lafiya, kullum cikin razana take, da dare kuwa ta rin'ka gane-ganen abubuwa suna kawo mata farmaki, gaba 'daya dai ta koma kamar mahaukaciya tsawon satin nan."
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'una, ubangiji ya ba ta lafiya, ko zan iya shiga na duba jikinta?" Hajiya Babba ta ba ta amsa da "Eh mana, muje na kai ki" Bayan ta gaida Aunty Mabruka wacce ba kowa take ganewa ba ta dan'ka mata Atm card nata da ba ta ta'ba amfani da shi ba ta sa mata albarka tukun ta dawo parlourn. A nan ta tarar da Hajiya Babban, nan ta fa'da mata dalilin zuwanta. Fuskarta babu yabo babu fallasa tace "Babu komai Hajiya Sughrah, ki ba da account details 'din ba kuma sai kin biya ni ba, kyauta zan baki."
Baki sake Mommah ke kallon Hajiya Babba tare da jin wata irn kunyarta ta sau'ka mata lokaci guda, hawaye ne suka fara zarya daga idanun Mommah. "Ya haka kuma Hajiya Sughrah?, meye na kukan kuma eh? Don Allah ki yi shiru kada yara su shigo suga kina kuka, zuciya 'daya na baki ku'din nan ba da wata manufa ba, ki 'dauke ni kamar 'yar uwarki Nasiba, don Allah ki bar kuka."
Ba tare da ta daina kukan ba ta dubi Mommah tace "Dole zan yi kuka Hajiya Babba, kuka yanzu na fara shi tunda ba ni da hankali, na 'dau yadda ta ta duniya na dam'ka musu ashe ba 'kaunata suke ba, sun sa na bar gidan aure na ashe duk shiri suka min, ke da nake wa kallon abar 'ki yau ke kika yi min abunda wanda nake wa kallon masoya suka kasa, na yi asara ni Sughrah...." Yatsarta Hajiya Babba ta 'daura kan bakin Mommah tukun tayi shiru. "Ya isa haka Sughrah, kuka ba naki bane yanzu, ki godewa Allah da ya sa kika gane kuskurenki da wuri, yanzu sai ki san matakin 'dauka. Ki tattaro kuma ki dawo 'dakinki, dama saboda auren Sadauki ne kika tafi, yanzu sai ki dawo tunda babu shi, ki gyara abubuwan da kika 'bata."
Murmushin da yafi kuka ciwo Mommah ta saki kana tace "Ba wannan bane Hajiya Babba, Daddynsu ya 'ki amincewa na dawo in na kira wayarsa ba ya 'dagawa, in na same shi a office nashi ba ya ko kallo na, Yaya zan yi ni Sughrah" Hajiya Babba tace "Kwantar da hankalinki in sha Allah za ki dawo 'dakin ki kwanan nan, ki dage da addu'a sannan kuma ki yi magana da Hajja, nima zan yi wa Alhaji Babba magana, da izinin Allah za ki dawo 'dakinki." Hawaye na zubowa Mommah tace "Na gode sosai Hajiya Babba, don Allah ki yafe min duk rashin albarkar da na miki tsawon wasu shekaru masu yawa..
"Ya isa haka, komai ya wuce Allah ya yafe mana baki 'dayanmu" da "Amin" Mommah ta amsa. Daga haka ta fara shirin tafiya bayan Hajiya Babba ta mata al'kawarin gobe Ya Khalil zai je har gidan Hajja ya kai ta a bu'de mata sabon account sai a saka mata ku'din daga nan kuma tayi wa Hajiya Babba sallama ta fice zuciyarta wasai tana kuma 'kara yabon halin dattaku irin na Hajiya Babba.
Tana fita sai taji ya kamata tayi wa Hajjaty Sannu da shan ruwa duk da ba ta zo da komai ba, bayan sun gaisa da Hajjatyn fuska sake Hajjatyn ke bata labarin ai yau 'diyarta Madina ma ta dawo, yanzu za ta fito daga wanka ta jira su gaisa don Allah. A matu'kar 'kagare Mommah ta zauna don itama ta ji tana son ganin Madina don rabonta da ita tun marigayin 'danta yana yaro, Allah sarki ashe tana raye.
Few minutes da zaman Mommah sai ga Mamah ta fito daga bedroom 'din Hajjaty. A matu'kar zabure Mamah tace "Hajiya Sughrah!" Ita ma Mommah tace "Maman Zahrah! Ke ce Madina kuma? Ya akai ban gane ki ba a wancan lokacin?" Mamah tayi murmushi tace "Ke ma a nan kike aure kenan? Ki sanni can damah?"
Murmushi Mommah tayi tana fa'din "'Kwarai a nan nake aure kin manta matar 'dan'uwanki Umar? Maman Junaid da Aliyu?" Da kallon Mamaki Mamah ke bin Mommah sai a lokacin 'kwa'kwalawarta ta tuna da hakan "Dama ke ce?, a lokacin da na fara ganinki a gidan Maman Badi'a na yi tunanin na sanki, amma iyakar tunani na na kasa tuna a ina, ashe dai matar 'dan'uwa na ne, Allah sarki duniya." Murmushi Mommah tayi tace "Nima da naga fuskarki a lokacin na fa'dawa 'yar'uwata cewa kamar na san ki, tace ai sai dai mai kama da ke saboda lokacin ne karo na farko da na fara zuwa Bauchi." "Ikon Allah, ashe dai da rabon za a 'kara gamo" sai kuma suka rungume Juna tunisuka manta da Hajjaty.
Saia lokacin itama ta farfa'dodaga sumar zaune da tayi tace "Sughrah? kin ta'ba ha'duwa da Madina ne bayan rasa ta da aka yi?" Zama Mommah tayi tace "'Kwarai kuwa Hajjaty, kin san 'yar'uwata Kubra dake Bauchi, a can naga Madina, nima iyakar 'ko'kari na na ganin na gano fuskar na kasa, ashe haka ita ma a nata 'bangaren, Allah sarki" Hajjaty tace "Ikon Allah, Allaj mun gode maka."
Sallama Mommah ta musu ta wuce, sai bayan tafiyarta Mamah ke tambayar Hajjaty Mommahn ta bar gidan ne? Nan tace mata ai dogon labari ne, in ta gama hutawa za ta bata labarin komai da ya faru a gidan. Da haka Mamah tayi shiru da batun bawan Allahn da aka ce ya rasu zuwa gobe ta yi tambayar. Daga nan Hajjaty ta kai ta wurin Alhaji Baba, sosai aka 'kara bu'de wani shabon shafi na kukan farin ciki daga nan kowa ya nemi makwancinsa.
*WASHEGARI*
Sai da aka idar da sallar maghrib Alhaji Baba yakawo musu zancen dawowar Mamah, a lokacin dukkansu suka 'dunguma wai za su je su ganta sai kace wasu yariya, murmushi irin na manya Alhaji Baba yayi yace "Kul! Ban ji ba ban yadda ba, kwa bari gari ya waye dai ko?" Kansu 'kasa suna murmushi suka ce to shikenan. Da misalin 'karfe 7:00am sai ga Daddy ya zo, idan baku mance ba Daddy na matu'kar 'kaunar 'yar'uwar tasa sai dai zuwansa har su Hajjaty babu wanda ya tashi, hakan yasa ya wuce office nasa ba tare da sun ha'dun ba, sosai yake jin da'di da bayyanarta, kuma ta bayyana a lokacin da ake bu'katarta ne, suna cikin jimamin rashin Yaya Sadauki kuma sai ga ta, Allah ya 'dauke ya kawo kenan.
Haka sauran 'yan'uwan nata duk suka fice wuraren ayyukansu ba tare da sun sa ta a idanuwansu ba. Ba su kuwa suka tashi ba sai wuraren 10am coz babu laifi sun sha gajiyar hanya, abuja to bauchi a cikin mota ai dole a jijjiga. Bayan an gaisa da juna, Zahrah ta ja Asma'u da Balkisu cikin sauran 'yan'uwanta su ma suka ja gefe suna hira, tun ba sa magana har suka saki baki suka fara.
Su Mamah ma hirarsu suke yi da Inna da kuma Hajjaty, Yaya Khalil ne ya shigo gaisuwar safe, yana 'karasowayaci karo da Mamah, shaye da mamaki yake kallonta, can dai yace "Ina yini Mommy Madina" "Lafiya lau" ta amsa masa fuska sake. Hajjaty ce ta 'dan ha'de rai tace "Ban gane ba Halilu, yau saboda ka ga uwarka shine ka manta da zamana har sai da ka gaishe ta? A hakan ma mu da alama ba za ka gaishe mu ba" kunya ce ta kama Yaya Khalil yace "Haba Hajjaty kya tsaya dai in gama da sabon hannu, ke kam ai....."
Hannun da ta mi'ko kamar za ta kwa'de shi ne yasa yaja baya yana dariya, gaba'dayansu suka saki dariyar suma, gaishe da Hajjaty da Inna yayi kana ya wuce corridorn da zai sada shi da 'bangaren tsoho mai ran 'karfe. Bayan sun gaisa da Alhaji Baba haka ya sako shi gaba wai sai ya fito sun yi hira da 'yarsa don ga can Hajjaty ta ma'kale ta kamar ita ka'dai ta haife ta, sosai Alhaji ya dara jin shiriritar Yaya Khalil, daga nan suka fito tare, Yaya Khalil yayi wa Mamah Sallama daga nan ya wuce office shima.
*React and Share Lillah, for those who share, Alkhairin ubangiji ya kai ku.*