Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera★ Gold
Book Page

Bahiyya Book One Complete Hausa Novel

Author: Oum Ameera★ Gold
Paragraphs: 1588
Starting position: 1
Reading position: 1 / 1588
Listen Mode
Login and upgrade to premium to unlock listening.
Reader Top
Ad slot ready: reader_top

                  💝 *BAHIYYA* 💝

   *ADABI WRITERS ASSOCIATION*

     

*Amina Ibrahim*

(Oum-Amir)

Follow me on wattpad:

@Oum-Ameer

  *FREE PAGE*

              *BABI NA ƊAYA*

Kaduna Road

Suleja Niger state.

BAHIYYA

A irin yanda jikina ke ƙyarma yana mazari tamkar ana kiɗamin goge a gidan 'ƴan bori shi zai tabbatar maka da irin tsananin tashin hankali da firgicin da ni ke ciki marar misaltuwa, ga wani irin zufa da yake fetsomin tun daga tsakkiyar kaina har zuwa tafin ƙafa ta kamar na haɗiyi kunama. Ban tabbatar da cewa fitsari na ke ba sai da wani jibgegen basamude ya kwashe ni da marin da sai da ya sani ganin wasu taurari, murya cike da ban tsoro yace.

“Don ubanki fitsari ma kika sakar min har ya gangaro zuwa ƙafata ko”

Wani irin ciri jikina ya ƙara ɗauka tamkar an jona ni a shocking, da sauri na shiga girgiza kai na cikin matsanancin kuka ina faɗin.

“Kayi haƙuri ban sani ba ne”

A irin dukan da suka yiwa Babanmu banyi tunani zai iya sake motsa ko da ɗan yatsan sa ba. Amma cike da jarumta irin ta tsayayyen uba ya ɗago da ƙyar yana faɗin.

“Dan Allah duk abinda zaku yi min kuyi amma ina roƙonku kada ku taɓamin mata ta da yara na, ku tafi dani kamar yadda kuka buƙata amma dan Allah kar ku cutar min da iyali n.....”

Daram! Muka ji saukar wata mummunar ƙara mai hirgita ruhin mai numfashi tamkar saukar aradu haka ta dirar mana a masarrafar sauraronmu, ashe harbin bindiga ne ya sauka akan ƙirjin Baba kai tsaye suka kashe shi har lahira.

Wani irin gigitaccen ihu na saki tare da zubewa akan gawar Baba somammiya.

Kalma Mama ta ɗauka tare da durƙushewa akan ƙafafunta tana faɗin.

“La'ilaha illallah - Muhammadur-rasulullah sallallahu alaihi wassalam! .Allahumma ajirni fi musibatina wa akhlufni hairan minha. Shi kenan Malam Jafar ka yi shahada ka tafi ka barni a duniya ni da Bahiyya da Nuhaira....”

Nuhaira da ta duƙunƙune kanta a jikin Mama ta runtse ido gam ko kaɗan bata sake motsawa ba sai kukan da take wanda yake bayyanar da tsantsar tsoro da tashin hankali. Ganin baba shimfiɗe a ƙasa matacce yasa lokaci guda taji tsoron ya fita daga zuciyar ta ta faɗa kan Baba tana kuka mai ban tausayi.

Daga haka suka tattara duk kuɗin da suka karɓa daga hannun Baba da Mama suka fita kai tsaye suka bar gidan.

“Babaaaa... Dan Allah ka tashi Baba, wayyo Babaaa....”

Da ƙarfin tsiya Nuhaira ta shiga jijjigani tana faɗin.

“Anty Bahiyya! Anty Bahiyya dan Allah ki tashi mafarki fa kike yi”

A zabure na miƙe zaune tare da saka dukkan ƙarfina na cakumeta na rungume gam,Ina faɗin.

“Nuhaira Baba...Baba an fita da gawar shi shi kenan ba zai dawo ba...”

Hankaɗo ƙyallen ɗakin namu Mama tayi tare da duba agogon da ke kan screen ɗin ƙaramar wayar hannun ta, kusan ƙarfe ɗaya saura na dare ya nuna mata,ƙara sa shigowa ɗakin tayi tare da dakamin tsawa tace.

“Wai Bahiyya ke ba zaki fawwalawa Allah al'amarin ki ba ne? Ubangiji shi yake jarabtar bayinsa yadda ya so, ya baka ko ya hana ka duk yana daga cikin ikon sa. Jafar bawan sa ne shi ya kawo shi duniyar kuma ya ɗauke abinsa, kukan ki, ihun ki, duk abinda zaki yi wallahi ba zai dawo da malam duniyar nan ba, gwara ma tun wuri ki sauya tafiyar ki”

Cikin gunjin kuka mai ban tausayi na shiga girgiza kaina still ina lafe a jikin Nuhaira ina faɗin.

"Wallahi Mama ba laifi na bane, babu wani dare da zai zo min in kwanta bacci ba tare da nayi mafarki da wannan baƙar ranar da aka kashe Baba ba, wadda har in koma ga mahalicci na ba zan manta da ita ba....”

Jikin Mama ne yayi sanyi. A hankali ta zo ta zauna kusa damu tare da kwantar da murya tace.

“Bahiyya! Ki yi haƙuri, na san da ciwo sosai, amma wanda ya mutu komai zaki yi ba zai dawo ba, na sha faɗa miki ki riƙi azkhar ya zame miki abokin hira, duk za ki shiga bacci ki yi alwala kiyi addu'a, ki tashi cikin dare kiyi sallah ki roƙa masa gafara a wurin Allah, shi kadai zaki yi masa ki tabbatar masa ya bar 'ƴa' ƴa masu yi masa addu'a, idan kuma kin wayi gari ki yi haƙuri ki saki ranki kiyi walwala kamar yadda 'ƴar uwarki ta ke yi, rayuwa ba za ta ci gaba a haka ba. Dole ki koyi rayuwa a duk irin yanda ta zo miki. Tabbas mun rasa jigo, mun rasa linzamin kamawa amma ya zamuyi? Wannan ita ce ƙaddarar mu kuma ya zama dole mu amshe ta hannu biyu muyi godiya. Sannan mu sake shirin yanda zamu rayu domin mu ci gaba da rayuwa cikin aminci,

saboda haka kiyi haƙuri Bahiyya ki rage wannan damuwar a ranki, shekara ɗaya har da watanni ya ci ace kin haƙura saboda kin fi kowa sanin wanda ya mutu ba zai dawo ba”

Miƙe wa nayi na fita waje jiki a saɓule nayo alwala na dawo na shimfiɗa sallaya na fara nafila, duk mama tana zaune tayi tagumi ita ma da irin abinda ta ke saƙawa a cikin ranta.

Ganin na duƙufa yasa ta miƙe ta wuce ɗakinta, Nuhaira ma gyarawa tayi ta kwanta abinta tare da lumshe ido tana nazarin rayuwar mu ta baya har ɓacci ɓarawo ya sace ta.

************

Washe gari mun fito ni da Nuhaira muka yi duk wani morning routine ɗin mu, bayan mun kambala naga kusan ƙarfe goma amma Mama bata fito ba yasa na shiga ɗakin ina faɗin.

“Mama wai lafiya har yanzu baki fito ba, ga kunun ki har ya soma yin sanyi”

ɗago kanta tayi tana daga kwance tace.

“Bahiyya ciwon da na faɗa muku ina ji a ƙirjina kwana biyu fa yau ya so ya matsamin”

Cikin damuwa nace

“Subhanallah! Sannu Mama, bari to in fita wurin mai chemist in samo miki magani, Nuhaira sai ta tafi kasuwar tunda naga kayan miyar duk sun ƙare kuma mutane sai shigowa nema su ke, ba zamu iya kaiwa ranar kasuwa ba kayan miyar ba”

“To wa zaiyi niƙar injin ɗin naji yara sun taru waje?”

“Daman ni ce da niƙa yau Nuhaira kuwa bada Kayan miya, amma sai suyi hak'uri su kai niƙan wani wuri har zuwa yamma mu gani..”

Lallaɓawa tayi ta miƙe zaune tace.

“A'a, tafi ki samomin maganin in sha, idan ciwon ya faɗamin sai in niƙe musu ke kuma ki je kiyi wa Malama kitsonda ta aiko tun jiya tana neman ki”

Miƙewa nayi ina faɗin.

“Af! Ni wallahi har na manta da zancen kitson malama, bari to in yi sauri in dawo”

Bayan ficewa ta Nuhaira ta shigo ɗakin da kuɗi a hannun ta tana faɗin.

“Sannu Mama ya jiki?”

Mama ta amsa.

“Jiki Alhamdulillah Nuhaira. Naira Nawa ne nan kika haɗa?”

Tana ƙara murza kuɗin tace.

“Dubu goma sha ɗaya ne da ɗari bakwai na ɗanyun kayan miya, dubu bakwai kuma na magi da kayan tarkace”

“To yi maza dan Allah Nuhaira kada ki tsaya ko ina, ki yi ki dawo kada mutane su tsaya suyi ta jira”

Hijabi ta zuba ta fita tana faɗin.

“In sha Allah kamar walkiya Mama zaki ga naje na dawo yanzu, kiyi min addu'a”

“To Allah ya tsare ya sa a dawo lafiya”

Cikin mintuna da basu gaza ashirin ba na dawo gidan. Kunun na ɗauko mata tasha na ɓalla mata magani na ƙwaya da na ruwa tasha sannan na shirya na ce mata na tafi gidan Malama Rabi.

Cikin ikon Allah ko a hankali taji ciwon ya washe, hakan ya bata damar tashi ta shiga niƙawa yara abubuwan da suka kawo. Mama er hustlen ce ko can baya lokacin da baban mu yana da rai, yana da shagon sa itama bata fasa nema ba. Yanzu ma da ya kasance baya nan dole ta ƙara ƙaimi wurin nema domin ta kula damu.

**************

Life Camp.

Abuja Nigeria

Hanifah

Kwance ta ke akan rantsatstsen makeken cushion ɗin palourn ta tana kallon wani Korean film cike da nishadi da kwanciyar hankali. A yadda ta natsu sosai ta zuba Fitilun ganinta akan tvn nan tana murmushi, ko ina na parlourn tsaf yake sai walwali yake tamkar yanzu aka halitta shi saboda tsabtar sa, ga sassanyar Acn da ya gauraya da sihirtaccen ƙamshin turaruka masu azabar ƙamshi da wanzar da kwanciyar hankali ga wanda ya ke ɗakin. Ga laptop da wayoyinta nan zube a gefen ta, yadda tayi ɗai-ɗai tana kallon tana nishadi shi zai tabbatar maka da cewa ba ta da wata sauran damuwa a duniya.

Jin motsin fitowar mijin nata yasa ta miƙe da sauri tana wani irin murmushi mai kama zuciya ta nufe shi tana faɗin.

“Har ka fito?”

Tsadadden agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya duba shima yana mai mayar mata da murmushin yace.

“Getting to 9:00am Hanifah, I'm already late and I have told you since yesterday that the meeting is 10:00am, but sai da kika san yanda kika yi kika sakani yin latti, Mahi is waiting for me, so ki bar breakfast ɗinki kawai na gode, ki sa a nema min lunch kafin na dawo”

Dariya tayi tace.

“Sure! But Ko da ma ace ka dawo baka same ni ba, the food will be ready, am gonna meet with Rasi'ah, akan zancen tafiyar nan tamu Cyprus....”

Side hug ya bata tare da kissing forehead ɗinta yayi gaba da sauri yana faɗin.

“Let's catch up on phone Hanifah, Mahi sai Kirana yake”

“OK bye”

Kallon shi take har ya ɓace wa ganinta, murmushi ta saki tare da komawa kan cushion ɗin taci gaba da kallon da ta ke a tv.

**************

Farooq

At around 1:30pm bayan sun dawo daga sallahr zuhr, suna cin lunch ɗin da Mahid yasa aka kawo daga gidan sa,ya kalli Farooq ya ce.

“I never thought the meeting would go smooth like this Wallahi, Saboda yanda naga mutanen nan zuwan farko sai a hankali”

Dariya Farooq ɗin yayi yace.

“That's the challenges of life. We must plan on how to deal with our business partners always, along the line ka shirya shirin amsar faɗuwa duk lokacin da abubuwa ba su zo maka kamar yadda kayi expecting ba. A fuska sam kamar ba zasu yi daɗin hulɗa ba amma daga baya dubi yadda muka ƙare da su”

Gyaɗa kai Mahid ya yi yace.

“Haka ne fa, bari in maka ta karin maganar malam bature yace wai 'do not judge a book by it's cover'. While Ya Madinah ta ke? Kwana biyu”

Wani irin sassanyar ajiyar zuciya ya saki yana murmushi yace.

“Madinah is doing Good Mahi, Ina missing ɗin tsohuwar nan kwana biyu wallahi, gashi aiki ya hana min zuwa ganin ta, ita kuma ƙiri-ƙiri taƙi Abuja wai ba zata zauna da ni ba”

With full confidence ya Kalli Farooq ɗin cikin idonsa yace.

“Farooq mi yasa zata zauna da kai? Zama ba zai yi tsakanin ta da Hanifah ba, dama ace kun haihu ne, ko don saboda yaran zata zauna ko kuma ta riƙa zuwa a kai a kai”

Taɓe baki yayi yace.

“Haihuwa? Ba saboda haihuwa ba dai kawai bata so zuwa ba ne...”

“Farooq! Madinah ko bata furta maka ba nasan a cikin ranta tana da burin ganin 'ƴa' ƴan ka a duniya. Aure shekara bakwai! At least ka saka hankali da lissafi a cikin wannan maganar, kai kaɗai ta raina ƙwallin ƙwal nasan abu mafi farin ciki yau ta gan ka da 'ƴa' ƴa....”

Hannu ya ɗaga mishi alamar baya son zancen yace.

“Mahi please! Mubar wannan maganar, Hanifah ta ishe ni rayuwa ita da Madinah, ni ka ɗai ne na rayu a duniya ta sai yanzu da na samu Hanifah, babu kalar farin cikin da bata bani, babu abinda muka nema muka rasa....”

Miƙewa Mahid yayi tare da dangwarar da spoon ɗin hannunsa akan plate ɗin abincin da kwata kwata basu yi masa cokali uku na kirki ba, cike da jin haushi yace.

“Farooq ka daina yi min zancen banza a nan, aure ba 'ya' ƴa miye ribar sa? Manzon Allah S. A. W ya faɗamana cewa muyi aure mu hayayyafa zai yi alfahari da hakan ranar gobe ƙiyama. Sannan ya sake faɗa mana a cikin wani hadith ɗin cewa, yayin da ɗan Adam ya mutu dukkan ayyukan sa zasu yanke, fa ce abubuwa guda uku zasu rakasa zuwa ƙabarinsa, bayan an binne sa dukkan su zasu dawo ɗaya ne kawai zai tsaya tare da shi a cikin ƙabarinsa,kasan mi ne ne shi? Aikin sa walau Hairan ko Sharran. Abubuwan da ya bari kuma a doron ƙasa waɗanɗa ba zasu yanke ba matukar ya gina su a lokacin da yake raye a ban ƙasa su ne:Sadaka mai gudana, na biyu waladun salih yaro na gari wanda zai riƙa yi masa addu'a a lokacin da baya raye, na uku ilimin da ya wanzar a ban ƙasa mutane na ci gaba da amfana da shi. Ka gayamin idan baka haihu ba ta ina zaka samu yaron da zai riƙa yi maka addu'a idan ka mutu? Tun wuri ina kiran ka da babbar murya ka aje wannan banzar aƙidar yahudancin da ka ɗaukar wa kanka tun lokaci bai ƙure maka ba ka haihu, 'ƴa' ƴa su ne farin ciki sanyin idanuwan iyayen su matuƙar sun taso akan turba madaidaiciya”

Daga haka ya kwashe kayan sa ya juya da nufin ficewa daga Office ɗin.

Cike da ɓacin rai Farooq ya ce..............

Ki biya 500 ki sha karatu sister

3132703269

First Bank

Amina Ibrahim

                💝 *BAHIYYA* 💝

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*AMINA IBRAHIM*

  *(OUM-AMIR)*

*FOLLOW ME ON WATTPAD:*

*@UMMU-AMEER*

*PAID BOOK 500*

*3132703269*

*FIRST BANK*

*AMINA IBRAHIM*

*08068974831*

*FREE PAGE*

*BABI NA BIYU*

“......... Mahi ji yanda kake magana dani tamkar ni ba shugaban ka bane, what's your problem about my marital life kana da matsala da hakan ne?”

Juyowa Mahid ya yi yace.

“Kai mai gidana ne saboda ina aikin a ƙarƙashin companynka and again don't forget I'm also a friend to you. So if you want zaka iya cewa na ajiye maka aikin ka saboda na faɗa maka gaskiya amma ba zaka iya datse iyakar abotar mu ba Farooq”

Daga haka ya juya ya fice daga ma'aikatar baki ɗaya ya nufi gida, yana ƙara jinjina al'amarin Farooq da matar sa Hanifah. Abu wasa wasa tun yana ɗauka amarci ne kawai suke morewa idan suka gama za su nemi su haihu amma sam a iya yanda ya fahimci Hanifah sam bata kawo zancen haihuwa ko kaɗan idan aka yi mata kuma ko da wasa bakin gaskiyar ta zata kafe cewa, 'ya' ƴa problem ne saboda haka ko babu su mutum zai iya rayuwa, kuma yayi farin ciki.

Mahid Baffa abokin Farooq ne tun a UK Allah ya haɗa su wurin karatu, sosai ta su ta zo ɗaya wurin halayya da mu'amalantar juna. Shi Mahid ɗan Kano ne yayin da Aiki yanzu ya kawo shi Abuja tare da Farooq ɗin.

*************

BAHIYYA

Sai kusan ƙarfe biyar na yamma na dawo ma gidan ina mai faɗuwa zaune a gindin bishiryar da suka shimfiɗa tabarma suna zaune na ce.

“Wash Allah! Wallahi duk na gaji jikina ji ni ke tamkar an naɗa min duka, aikin lalle da kitso wallahi akwai wahala...”

Nuhaira tana dariya ta ce.

"Amma kuma akwai kama naira ba. Ko da yake mutanen basa son biyan kuɗin ƙwarai sai dai kayi musu dan Allah dan zaman tare”

Girgiza kai Mama tayi tace.

" Ku dai har yanzu yara ne, ko naira goma ake samu ai yafi maganin zaman banza kuma yau da gobe in dai ana saka haƙuri sai naira gomar ta koma naira ɗari.”

Cike da zumuɗi Na ce.

“Ai Mama na manta ma in yi miki albishir, Malam ta ce zata riƙa zuwa dani cikin gari domin in riƙa yiwa mutanen ta kitso da lalle tunda Maryam ta yi aure. Tace kullum sai damunta su ke yi da kira wai ta kawo musu mai lalle da kitso...”

Shewa Nuhaira tayi tare da tafa hannu tace.

“Shikenan Aunty Bahiyya Allah ya kawo miki hanyar samun biyan kuɗin kitso da lalle mai tsoka domin su mutanen nan sun san darajar wahalar mutum, kamar yadda Maryam ɗin ta ke faɗa. Ki ji fa yanda cikin unguwar nan a ke ta zagin ta wai ta cika girman kai yanzu kowa ba ta iya yiwa lalle da kitso a yankin nan namu saboda tana zuwa manyan gidaje cikin Abuja tana kama kuɗi. Amma ji dan Allah irin sayayyar kayan kitchen ɗin da tayi....”

Katse ta Mama tayi da faɗin.

“Nuhaira wuce ki duba mana sanwa kinji”

“To lallai kam, daga fara magana kin a re kin yafe kamar ke nike faɗawa maganar. Ni mi kike dafa mana ne yau? yunwa ma ni keji”

Daga bakin Murhun Nuhaira ta bani amsa tace.

" 'ƴar sada mana, shinkafa da wake da mai da ya ji”

“To don Allah kiyi sauri I'm hungry Wallahi. Mama ya jikin naki?”

“Jiki da sauƙi Bahiyya, ni har na manta ma,saboda Ina shan maganin shi kenan na nemi ciwon na rasa”

“To masha Allah. Haka ni ke son ji Mama, Allah ya ƙara miki lafiya, ya kuma ji ƙan Baba”

“Ameen! Bahiyya nicce dai shi zuwa kitson da Malama Rabi ta ce ba dai zuwa akeyi a kwana ba ko?”

Hijabina na cire tare da ɗan gincirawa kaɗan na ce.

“A'a, ba kwana ba ne Mama wuni ɗaya ne, amma tace ma zata shigo da kanta tayi miki bayani, duk lokacin da buƙatar hakan ta taso sai mu tafi”

“To Allah yasa mu dace. Ni yanzu burina ki samu ki koma makarantarki ki iyar da ƙarasa aji shidan nan ki amshi takardun mu gani kamar yadda Malam yayi buri. Ita ma Nuhaira a maida ta Js3 ɗin ta samu itama ta kambala ko da secondary ɗin ce kuka kambala ai zai fi...”

Jin Mama ta ambaci sunan Baba ban san lokacin da zuciyata tsinke ba sai ji nayi hawaye suna kwaranya daga kwarmin idanuwana. Gefen in da zuciyata take harbawa na dafe ina faɗin.

“Mama kinji zuciyata yadda ta wani buga da ƙarfi? Wallahi ban san lokacin da zuciyata zata manta da baba ba, kullum kwanan duniya mutuwar Baba sabuwa take dawo min, duk burin da ya ci a kanmu ya tashi a banza....”

“Bai tashi a banza ba Bahiyya, a iya yadda kuka samu kula da tarbiyya daga wurin Jafaru hakan ya nuna cewa yayi nasara, kawai Addu'a ita ce yafi buƙata Bahiyya, muyi ta yi masa addu'a da nema masa gafara a wurin ubangiji”

Hawayena na share nace.

“Hakane Mama, Allah ya yi mana jagora ya gafarta masa. Gaskiya Mama ni dai yanzu na fiso ayi ƙoƙari a mayar da Nuhaira ɗin. Kin san bokon nan ba kamar na Zamfara da muka baro ba ne. Na tambayi malama kudin register WAEC kuɗi ne masu yawa. Shi ne nake ganin yafi ita ta fara komawa ni kuma daga baya idan an samu yadda ake so sai nayi register nayi exam ɗin kawai ba tare da na sake komawa Ss3 ɗin ba.”

Mama tace

“Kina ganin hakan zai fi?”

“Eh Mama. Haka za'a yi”

“Allah ya hore muna abin hidimar, ya bamu rai da lafiya”

“Amin Mama, bari in watsa ruwa kafin nan abincin ya ida kambala”

**************

FAROOQ

Tunda Mahid ya fita ya bar shi bai samu wani ƙwarin guiwar barin office ɗin ba har yamma. Duk iya ƙure tunani ya gama yi ko da zai samu wata mafita amma babu wani haske, Hanifar sa kawai ya ke tunanin, farin cikin ta shi ne nasa. Ta daɗe da nuna mai bata da wata buƙata da yara sannan shima kuma haka. But ya rasa gane mi Mahi yake nufi da shi akan dole sai ya kutsa kai a cikin rayuwar gidan sa.

Sai 7:00pm ya tattara kayan sa ya nufi gida jiki a saɓule.

Yana shiga parlourn Hanifah ya saki wani sassanyar ajiyar zuciya, saboda wani ƙamshin Rahama da ya ziyarci ƙofofin hancin sa. Ɗakin sa ya wuce direct yayi wanka shap-shap ya fito ya jera sallar Asr da ya barta bai yi ba sai yanzu ya haɗa da magrib yayi.

A hankali Hanifah ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shigo.

Kallo ɗaya da yayi mata sai da ya sanya shi mantawa da duk wata damuwar na wucin gadi. Hanifah ba dai iya wanka ba.

Wata ficiciyar riga ce a jikin ta wadda ba tada maraba da tsirara, ga shi ko rabin cinyar ta bata gama rufewa ba.

Gefe ɗaya ta tubke gashin kanta da yasha gyara sai ƙamshin mayukan gyaran kai yake.

Har ta iso inda yake bai ɗauke idanuwansa daga kanta ba. Tsabar burgeshi da tashi. Cike da Soyayya tayi mazauni akan cinyar sa tana faɗin.

“Welcome back Mr. Mai Gishiri”

Jin yayi shiru yasa ta haɗe fuskar ta da tasa cikin iya kanta tace.

“Hey Mr. Any problem?”

Jin yadda numfashin su ya gauraya shi ya ƙara kashe masa jiki, a kasalance yace.

“I need you Hanifah, please don't reject my offer...”

Cikin ƙwarewa ta haɗe bakin su wuri ɗaya ta shiga aika masa da zafafan kisses. Lokaci guda ta birkita sa ya juye ya koma mata tamkar mayuwancin Zakin da ya jima a cage bai samu abinci ba. A zafafe ya shiga kissing ɗin wuyanta with wet lips ɗinsa hannayensa na sending mata signals a bare body ɗinta.

A hankali ya gangaro ya sauka akan boobs ɗinta wanda ya saka ɗan yatsan sa ɗaya ya fige siririn hannun rigar ta ta, wani irin azababben nishi ya saki tare da kai musu cakuma yana lumshe ido. Tun daga kan wuyanta ya gangaro da harshen sa har kan nipple ɗinta. Yanda ta ke responding to each and every touch ɗinsa romantically Shi ya ke ƙara hauka tasa yana tabbatar masa da cewa yau ta amince da gaske ta amshi gayyata, wanda a iya tunanin sa zai iya cewa ya manta yaushe ne ta ba shi haɗin kai a wannan harkar, a duk lokacin da ya buƙace ta idan bata so ba haka zata zayyana masa fake reasons kuma dole ya haƙura ya ƙyale ta.

A irin aƙidar Hanifah sakarwa miji jiki kowa ne irin lokaci ya buƙata yana saka gundura da kuma lalacewar halittar jikin mace da wuri.

A yanda take narke masa tana zuba shagaɓa tana sakin sabbatu tare da mayar masa da martani hakan ya tabbatar masa da cewa tana karɓar saƙon sa yanda ya kama ta.

Duk wata ƙishirwar sa sai da ya tabbata ya kashe ta a wannan daren a jikin Hanifah. Bayan sun sararawa juna ya matse ta gam a jikin sa yana mai shafar jikin ta kamar wanda ya samu jaririyar mage a hankali yana sauke numfashi. Bayan kusan 30mnt sun shuɗe a hankali ya buɗa baki kamar mai koyon magana yace.

“Firstly, Thank you for not turning down my offer today, thank you for the love. Amm! Secondly we need to talk about important issue Hanifah”

Juyowa tayi tana facing ɗinsa ta ce.

“Me too Love I have a good news for you.......

*OUM-AMIR* *Oum Ameer*

                  💝 *BAHIYYA* 💝

      *ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*AMINA IBRAHIM*

      (OUM-AMIR)

     *WATTPAD:*

*@UMMU-AMEER*

  *PAID BOOK 500*

     *3132703269*

      *FIRST BANK*

   *AMINA IBRAHIM*

   *08068974831*

*FREE PAGE*

          *BABI NA UKU*

 

    Miƙewa yayi ya sun kuce ta suka nufi toilet yana faɗin.

“let us clean our self first muyi sallar Isha sannan mu zauna it will be better”

Ko a toilet ɗin sai da suka shafe kusan mintuna talatin sannan suka fito. Mamakin sa ya kasa ɓoyuwa akan yadda ta saki jiki da shi yau yana ta abinda ya ga dama da jikin ta.

Bayan sun gama sallar ɗakin ta ta wuce ta shirya shima ya shirya cikin simple wears ya fito dining area, already cooks sun riga sun gama preparing table for dinner.

Da kanta tayi serving na su different dishes suka zauna suka ci sannan su koma parlour suka zauna.

Kallon shi tayi tana murmushi cikin zumuɗi tace.

“Farooq burina ya cika, my dream has turn to reality today”

Kallon ta yayi cikin ido da mamaki shimfiɗe akan fuskar sa yace.

“Hanifah can you explain more?, ni ban gane zan cen ba”

With so much agitation tace.

“Burina na kafa  Ɗan-Ali Decor and event a United Arab Emirate. Daddy ya kirani ɗazu yace min everything is set and ready ni ka ɗai ake jira. So tafiyar mu zuwa Cyprus ni da Rasi has been canceled I will branch to Cairo first daga nan sai mu shirya mu tafi tare da Su Momma zuwa Dubai ɗin. But please also your presence will be utmost important....”

Hannun shi ya janye daga riƙon da tayi mishi cikin rashin jin daɗin bayanin ta yace.

“But Hanifah na ɗauka tun lokacin da kika zo da wannan buƙatar na faɗa miki bana da ra'ayi da ita kin watsar da zancen nan, ashe kina can ta ƙarƙashin ƙasa kina shirya abinda ranki ya ke so without me knowing...”

“Farooq wannan magana ce ta feature development, Idan ka zauna a yadda kake a haka zaka ƙare nobody will understand that you exist, but by creating and developing many works and interacting with different world shi zai sa tarihinka ya ba zu a duniya, by the time kayi gwagwarmaya har duniya ta sanka a lokacin ne kai kanka zaka tabbatar cewa you are existing in the right world. Farooq ina so duniya ta sanni kamar yadda ta san Ikrama Ɗan-Ali, both Nigeria and other countries....”

Cike da damuwa yace.

“Hanifah even now you are existing in the right place, remember you are my world and everything, kina da ni ina dake Hanifah. I own Al-madinah Textile and more industry, a nan, a Ghana, and Kenya. I own Al-madinah Architecture and Design company a nan and Kuma London. And also your father is a famous and Generous man that has own many Businesses and also an Ambassador in Egypt. Ke kanki kina da Ɗan-Ali Decor and event center. Dan Allah Hanifah of all this ni'imar Allah da yayi miki bayan shi mi kike nema kuma?”

“Farooq a ko da yaushe fa ina faɗa maka kama da wane ba wanen ba ne. Babana da abunda yake da shi daban da ni, mijina da abinda yake da shi daban da ni, so please don't complicate this issue dan Allah Farooq...”

“Billah Hanifah bana son kina nisa da ni ko kaɗan, ni ina daga cikin Maza masu ra'ayin kasancewa tare da matan su every time. Ko wannan center ɗin taki ta nan ya na ƙare da ita? Yau kina can gobe kina nan, jibi kina wancan ƙasar. Sai ki fi wata wani lokacin ba kya tare da ni Hanifah, a gaskiya ina cutuwa, to ina ga yanzu ki buɗa branch a wata ƙasar? Hanifah time yayi da ya kamata mu zauna mu fara shirya how we can start a family by planning to give birth...”

Zaro ido tayi cikin Mamaki tace.

“what? Oh no Farooq! To be honest with you nothing like wani Abu wai shi haihuwa a tare dani kaima ka daɗe da sanin wannan, so dan Allah ina roƙon ka daina ma wannan zancen, let's understand each other, you know that I love you right? We can live our life and be happy together with out a kids. Yara damuwa ne Farooq duk yadda ka ke ganin muna da freedom daga lokacin da muka fara haihuwa kafin ka tantance matsala ta fara kunno mana ko a tsakanin mu, sannan ba zamu sake samun wani freedom kamar yadda muke lokacin da bamu da Kids ɗin ba. Dan Allah mu rufe chapter yara daga nan mu biyu mun ishi kanmu farin ciki ba dole sai da yara ba, beside kana da Madinah ni kuma I have my parents with me. Sannan shi kuma zancen aiki na Farooq ina son ka fahimta cewa komai a rayuwar nan lokaci ya ke da, ba zamu samu cikar burinmu ba har sai munyi aiki tuƙuru. Tafiyar da nikeyi ba kullum ni ke yinta ba sai idan buƙatar hakan ta taso,kuma watarana zai zama tarihi. Ni ba zan zauna kamar kai ba ,abinda ya kamata ace kana yi da kanka sai dai kayi assigning somebody ya je yayi un-be half of you, Dan Allah ka yi haƙuri ka bani dama....”

Sai kuma ta fashe masa da kuka taci gaba da faɗin.

“Baby you know how much I love you in this world Ina matuƙar matuƙar ƙaunar ka da duk wani farin cikin ka, bana so kana fushi da ni ko kuma idan zanyi wani abin ka ƙi goyamin baya, idan kuma nayi maka wani laifi ne ka yi haƙuri ka yafe min please”

Ganin yadda  duk ta rikice tana risgar kuka haiƙan ba ƙaramin daga masa hankali yayi ba, Domin daga cikin abubuwan da Farooq ya tsana a duniya akwai kukan hanifah a ciki. Lokaci guda ya ruɗe bai san sanda ya janyo ta jikin sa ya rungume ba yana famar bata haƙuri.

Sai da tasha kuka mai isar ta sannan tayi shiru shi kuma bai gaji da aikin rarrashin ta ba. Jin tayi shiru yasa shi calmly fara mata magana da cewa.

“I'm Sorry Hanifah, my intention was never meant to hurt you, kawai dai Ina ganin rashin dacewar Hakan ne kuma bana so kina nisa dani. Maganar yara kuma kawai Mahi ne yaga dacewar hakan amma kiyi hakuri”

Cikin shagwaɓa tace.

“To kuma ni dai dan Allah ka amince min da ƙudurina akan wannan business ɗin wallahi idan kace zaka hanani zan iya mutuwa wallahi....”

Cikin damuwa yace.

“Ki daina ma zancen mutuwa Hanifah shikenan na amince”

Kanta ta ɗago da sauri with teary eyes ɗinta tana murmushin nasara tace.

“Thank you so much Love. Ban san irin kalmomin da zanyi amfani da su wurin gode maka ba...”

“No Hanifah just continue to love me sannan ki ci gaba da kasancewa da ni a koda yaushe till my last breath”

“Ko  bayan na mutu Farooq son ka ba zai daina gudana a cikin jini da jijiyoyin jiki na ba, Ina son ka sosai”

Murmushi ya saki mai sauti domin har cikin ransa kalamanta sun shiga zuciyar sa tare da yin register a brain ɗin sa.

“Ok! To yanzu yaushe zaki yi tafiyar? And yaushe zaki dawo?”

“Ba zan wuce 3 to 4 month ba a yadda na tsara, but idan na tafi ya danganta da yanayin abinda zai iya riƙe ni ko dai in dawo da wuri ko kuma in fi haka jimawa”

“OK wish you safe trip”

Daga haka ta janye jikin ta ta nufi ɗakinta tana faɗin

“I need to arrange some of my documents,I will joined you later in the bed ”

Bayansa ya jinginar a jikin cushion ɗin yana mai lumshe ido dramar sa da Hanifah na dawo masa beat by beat. Ya rasa ya zaiyi da Hanifah, always Abinda yake so ita ba shi ta ke so ba. Kullum ita a bauɗe take. Amma a haka yana farin ciki da ita da kuma tsananin ƙaunarta. Ya san cewa sarai Hanifah bata jin maganar sa amma ya rasa yadda zai yi da ita. Musamman abinda ya shafi marital life ɗin su, shi ya san da cewar yana da tsananin buƙata but duk yadda zai kashe ta da magiya da roƙo matuƙar bata so ba ko zai mutu ba zai samu ba.

Wayarsa ce ta hau ɓurari ko bai duba ba yasan wacece ta ki rasa domin tana da ringing ɗinta na musamman irin na mutane masu matsayi da daraja. Mutum ɗaya tilo da yake da shi a duniya masoyiyar kakarsa Madina.

Ɗaga kiran yayi yana mai yi mata sallama cikin ladabi da mutuntawa.

Bayan ta amsa daga can ɓangaren tace.

“Faruku ya naji sautin muryarka ya canja ko ba ka da lafiya ne?”

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace.

“Ina lafiya Madinah,kawai dai Hanifah ce, but we have sought everything out. She is gonna branch her business center in Dubai”

Ɗan jim tayi kaɗan tana juya maganar a cikin ranta, idan bata manta ba last year da yayi wani zuwa yayi mata complain akan Hanifah ta zo masa da magana makamanciyar wannan amma bai amince ba kuma ba zai taɓa amincewa ba. Amma yanzu lokaci ɗaya kuma yace mata har Hanifah ta shirya komai.

Jin shiru daga ɓangarenta  yasa shi cewa.

"Grand Ma are you hearing me.”

Gyaɗa kanta tayi kamar yana gabanta tace.

“Ina jinka Faruku Masha Allahu, that's nice to hear, Allah ya taimaka yasa a yi cikin nasara da aminci.”

Lumshe ido yayi yace.

“Amin. Yau tun safe baki sake ji daga gare ni ba ko? I'm sorry nayi meeting ne Bayan na fito kuma wani abu ya ɗauke mini hankali.”

"Eh, nakira Mahid akan wasu yaran maƙota na da nike so a basu gurbin aiki a nan wurin ku, shi ne yake sanar mini cewa kuna meeting ne, to Don Allah za su zo su uku ne sai ku bincike su ku basu gurbin da ya dace. Na gayawa Mahid su sauka gidan sa amma tunda ita Hanifar zata tafi gobe sai su zo nan gidan naka”

Yace

“OK, ba matsala in sha Allah, sai dai kawai su sauka wurin Mahi ɗin because zan tafi Lagos nima a gobe kuma zai iya ɗaukata sati kafin na dawo amma Yadda kika ce haka za'a yi ”

Tace

“OK no problem Sai ayi Hakan ai”

Yace

“Ok to Allah ya kawo su lafiya”

Tace

“Amin. Ka gaida Hanifah, idan ta je gidan kuma  ta gaida iyayenta.”

Yace

“Zata ji in sha Allah. Sai da safe”

Tace.

“Allah ya bamu alkaiiri”

Tashi yayi ya koma ɗakin sa ya kwanta abinsa, yadda Mahi bai nemesa a waya ba shima haka ya share sa domin ya fahimci sarai cewa fushi yayi.

Har ɓacci ɓarawo ya sace sa Hanifah ba ta zo gare shi ba.

*************

BAHIYYA

Bayan sati ɗaya da yin maganar mu da Mama akan batun karatun Nuhaira. Ina zaune Ina bayar da kayan miya, mama ta fito daga ɗaki tana faɗin

“Bahiyya ki duba min numbern Malam Maharazu kwana biyu ina ta neman sa layin ya kasa tafiya ko kuma dai ba numbern ce nake kira ba”

Bayan na sallami Yaron na sa hannu na karɓi wayar tare da sake gwada numbern amma kamar yadda ta faɗa layin a kashe yake. Kallon ta nayi nace

“Mama fa da gaske ne wayar a kashe ta ke”

Tace

“Subhanallah! Ko miye dalili? Gaskiya da wuya ka kira lambar malam Maharazu kaji ta a kashe, kuma nima nayi mamakin da yasa ya share har kusan sati biyu bai kira mu ba.”

Nace.

“Eh fa, tun kiran da yayi wancan ranar Nuhaira ta ɗauka bai sake kira ba. To amma Mama neman mi kike masa haka?”

Zaunawa tayi akan kujerar tsugunno tana faɗin.

“Nuhaira ni ke so idan ya samu lokaci ya zo ya kai min ita makarantar”

Nace

“To Allah yasa a same shi, idan ma ba'a same shi ba ga Malama Rabi nan sai ta yi mana jagora”

Daga haka ta koma ɗaki ni kuma naci gaba da bayar da kayan miyar ga wata yarinyar da ta shigo yanzu.

*OUM AMEER*

💝 *BAHIYYA* 💝

      *ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*AMINA IBRAHIM*

      (OUM-AMIR)

     *WATTPAD:*

*@UMMU-AMEER*

  *PAID BOOK 500*

     *3132703269*

      *FIRST BANK*

   *AMINA IBRAHIM*

   *08068974831*

*FREE PAGE*

            *BABI NA HUƊU*

Mohandessin.

Giza Governorate

Cairo, Egypt.

Hanifah

 

      Zaune suke a dining table suna breakfast. Hanifah, Mahaifiyar ta Hajiya Nuriyyat, Mahaifin ta Alhaji Ikirama Ɗan-Ali da kuma junior sister ɗinta Hamrah wadda ta dawo jiya daga school sanadiyyar matsa mata da Hanifah tayi akan lallai dole sai ta zo an hallara tare sun tafi Dubai. Cike da farin ciki da cikakkiyar walwala suke cin abinci suna fira jefi jefi. Hanifah ta kan ji ta free tamkar sakakkiyar tsuntsuwa a duk lokacin da take cikin familynta. Saboda family ne na wayayyi gogaggun 'ƴan boko wanda kowa ya ke rayuwar sa cike da cikakken 'ƴan ci babu wata takurawa duk abinda kake so ka zaɓa shi za ka yi, musamman ma ita Hanifah wadda ta kasance First born a garesu ta kasance rainon taɓara. Kusan tazarar shekara goma ne ke tsakanin ta da Hamrah shiyasa ta taso cikin gata da soyayya marar misaltuwa.

Tun lokacin shekarun gwagwarmayar sa ya kasance Pediatrician Doctor a ƙasar sa Nigeria, sai kuma Allah ya haɗa shi da ƙungiyar NGO's wanda a hankali ya zama sanadiyyar samun matsayi a United Kingdom ƙarƙashin ƙungiyar Saboda Ɗan-Ali ya kasance Jajirtacce mai ƙwazo wurin aiki shiyasa ya zama lamba ɗaya. Daga baya ya dawo da matarsa Nuriyyat suka ci gaba da zama wanda a nan a ka Haifi Hanifahr  da kuma Hamrah, haka yayi ta aiki kala kala daga nan UK zuwa gida Nigeria da kuma businesses da ya keyi na daban daban tsawon shekaru. Shekara 4 da suka gabata ya samu zama jekadan Nigeria a ƙasar Cairo Egypt, in da suka dawo nan da zama a yanzu.

   Hanifah tayi karatu har zuwa matakin Degree a nan UK a fannin Business, ta taso cikin gata da samun cikakken 'ƴan ci wanda ya bata damar yin duk abinda taga dama kuma ta yarda da cewa a duniyar nan babu abinda ya ke fin ƙarfin ta matuƙar zata nema sai ta samu saboda suna da kuɗi da freedom, Hanifah ta waye ta buɗe ido da rayuwa tayi karance karance iri iri, ta sha shiga ƙungiyoyin matasa mata da maza domin ta ƙara samun gogewa da kuma iya zaman duniya.

A hanyar ta ta zuwa Nigeria daga UK wurin wani gagarumin taron ƙarama juna sani a harakar business suka haɗu da Farooq suka ƙulla abota daga nan kuma ta juye zuwa Soyayya, Hanifah bata so auren ba a wannan lokacin ganin irin naci da tsananin sonda Farooq ya nuna mata yasa ta saukar da kai bori ya hau.

Ga shi kuma Allah ya haɗa jinin Daddy da Farooq sosai domin ganin irin ci gaban da Farooq ya samu a irin ƙananun shekarunsa abin alfahari ne kuma yayi amanna cewa Hanifah ta samu mijin da ya dace da matsayin ta haka ma a wurin Hajiya Nuriyyat.

Ba'a ɗauki dogon lokaci ba Madinah ta shirya da wakilanta aka shirya zancen aure ba ɓata lokaci akayi gagarumin bukin da ya amsa sunan shi buki, an sha daga sosai da Hanifah domin cewa tayi ita fau-fau ba zata zauna a Nigeria ba, Farooq yasha matuƙar wahala kafin ya samu ya shawo kanta akan tayi hak'uri ta zauna a Nigeria sai da aka haɗa da su Madinah wurin bata baki. Shine dalilin da yasa ya tafi Life Camp ya tantatsa mata gida naji da gani a Abuja sannan ya zuba mata masu aiki birjik da body guide kamar yadda ta buƙata. Wanda lokacin baya iyaka ya zo Abuja wurin harakar business ɗin sa idan ya gama ya koma Kaduna.

  A irin  karance-karance da kalle kallen da Hanifah tayi da kuma mu'amalantar mutane daban daban a fadin duniya yasa ta fahimci cewa rayuwar aure kawai cike take da takurawa da kuma wahala da ƙarewa da ɗaukar nauyin namiji kullum, ko kuma ayi ta samun domestic violence sanadiyyar rashin jituwa tsakanin ma'aurata musamman wasu ma'auratan akan 'ƴa' ƴa za'a yi ta samun saɓani. Shi yasa ita a aƙidar ta ba zata iya sakarwa namiji jiki ba ko da yaushe yayi ta duk abinda ya ga dama da ita. Sannan ganin yadda mata ke shan wahala tun wurin ɗaukar ciki yana farko har zuwa haihuwa da shayarwa abin ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya ke ba, ga wahala kuma ita babbar damuwar ta ma shine idan mace ta ɗauki ciki a hankali cikin zai fara buɗewa yana girma saboda abdominal muscles zasu riƙa stretching a hankali given room for a baby to grow well, Daga zaran Kuma ta haihu sai cikin ya canja shape ya buɗe, sannan ga tear da ake samu ko kuma a bada episiotomy lokacin labour daga nan vagina ɗin mace ta samu matsala, a wurin breastfeeding Kuma breast zasu lakuce su canza shape suyi sagging, Idan kuma CS shima dai duk uwa ɗaya suke domin sai kin samu scar, sannan kuma ka dawo renon yaro yayi ta kuka kana rarrashi duk a banza, yayi kashi yayi fitsari. Ita a ganin ta duk wannan wahala ce is better kawai kayi zamanka a haka. Ganin yadda Farooq ya ɗauke ta tare da nuna mata tsantsar kula da bata freedom yasa ta saki jikinta tana abin ranta yake so, duk abinda Hanifah tace shi kenan ya zauna ko da ya masa daɗi ko bai masa ba shi dai kawai ya na so ya faranta mata suyi rayuwar auren su cikin soyayya da kaunar juna.

Tsawon shekara bakwai da tayi a Nigeria bata fi zuwa huɗu ba Kaduna wurin Madinah, ita ma kuma Madinah ganin kalar matar da Farooq ɗin ya aura sai ta ja wa kanta layi da shiga al'amarin ta. Itama Madinah tunda aka kawo Hanifahr sau biyu ta taɓa zuwa Abuja gidan ta, a lokacin aurenta da kuma sanda ta buɗe Ɗan-Ali Decor and event center.

Daga haka sai dai ta waya idan sun samu sararin gaisawa.

Ci gaban labari.........

Zaune suke a palourn Daddyn da yamma suna tsara yadda tafiyar su zata kasance gobe. Hamrah ta kalli Hanifah tace.

“Fav Sis Yah Farooq ba zai zo bane?”

Zaro ido tayi tace.

“What! Inji wa, yana nan zuwa daga zaran mun isa in sha Allah”

Hamrah tace.

“Ah to, ai naga yah Farooq ɗin ne kamar anyi masa kafi a Nigeria duk sanda zamuyi waya na tambaye ki shi sai ki ce min yana office”

Hannunta Hanifah ta ɗauke daga kan system ɗin da take aiki a kai ta kalli Hamrah tace.

“But  I said he's coming, ba shi kenan ba”

Daga nan kuma ta kalli Daddy tace.

“Daddy please sai kayi magana da su na tura musu kalar furnitures ɗin da nike so ayi amfani da su”

Yace

“OK!”

Washe gari ƙarfe tara jirgin su ya ɗaga zuwa Dubai.

**************

Abuja

      Nigeria

Kusan watan Hanifah biyu da tafiya Farooq har yayi tafiye tafiye kusan sau huɗu zuwa Kenya da London. A duk lokacin da ya shigo gida ji yake can ƙasan ransa yana mugun jin kewar matarsa but bashi da abinda zai yi sai dai ya jira dawowar ta.

Yanzu ma kwance yake kawai a ɗakin ta yayi shiru yana ta karanta wasiƙar jaki.

Bayan ya kai kusan 1hour a kwance daga ƙarshe ya tashi kamar wanda aka tsikara ya je ya shirya ya nufi gidan Mahi.

Ganin shi tsaye a balcony ɗin gidan nasa yayi matuƙar bashi mamaki.

“Yaushe kama dawo ƙasar ban sani ba, har gaka tsaye a cikin gidana?”

Kallon sa yayi yace.

“Da safe, na kiraka baka ɗauka ba”

“Wallahi a lokacin tana hannun Amrah 'yar rigima. Juyawa yayi ya nufi Parlour yana faɗin....  Shigo ciki mana”

Parlour suka shiga yaje ya kira Husnah matarsa ta fito ta gaishe sa, Zarah da Amrat ma suka gaishe sa cikin ladabi ya amsa duk da maganar Amrat ba wani fita sosai ta ke yi ba because she's just 3years, Zarah Kuma itace babba wadda zatayi 6years.

Cikin shaƙiyanci Mahi yace.

“Husnah kawo wa gauron nan abinci dan Allah, nasan akwai yunwa tare da shi”

Harararsa Farooq yayi yace.

"You are not serious, Yanxu Haka na baro abincin da aka jera min a gida ko taɓawa banyi ba”

Mahi yace.

“Saboda mai gidan bata nan shiyasa komai ya fita a ranka ko?”

Maganar suke amma kallon Yaran da ke wasa jikin Mahi shi ya ɗauke masa hankali. Amrah ce da ƙaramin ƙanin ta Haidar wanda he's just 8 month now.

Zarah Kuma tana gefe da littafanta tana rubuta. Wannan yanda ake ta drama da Amrah da Haidar shine abinda ya burgesa, Amrah ta kafe akan Lallai sai Haidar ya sauka itama ta hau, shi kuma daga zaran an ɗaga shi sai ya fara kuka, ganin taƙi samun yadda ta ke so kawai sai ta fasa ihu ta faɗi ƙasa zata fara birgima.

Lokaci guda Farooq ya ɗaga ta sama ya ɗora ta akan thigh ɗinsa yana murmushi ya gyara mata tsorayen kalbanta da suka sha bit zuwa baya yace.

"Is ok.....”

Kuka kawai take tana nuna Mahi da Haidar tana faɗin.

" Abbah... Abbah ne, Haidar...”

“Shiihhh! It OK! Sai na yiwa Abbah duka”

Mahi kuwa sai dariya yake yana jefa Haiydar sama suna ƙyaƙyata dariya.

Husnah ce ta katse su da faɗin.

“Abbahn Zarah na gama shirya abincin”

“Owk, thank you, zo ki shiga da yaran nan ciki ya samu ya ci abincin.”

Zarah najin haka ta miƙe ta kwashe tarkacenta ta shige ciki. Husnah ta zo cikin nutsuwarta  ta karɓi Haiydar da ƙyar ta amshi Amrah daga jikin Farooq shi kuma sai murmushi yake yana lallaɓa ta har ta tafi.

Suna kan cin abincin ya ajiye spoon ɗin hannunsa ya kalli Mahid cikin damuwa yace.

“Mahi am missing Hanifah so much. Sai mu yi kusan kwana biyu bamuyi waya ba idan taga na matsa mata da kira sai ta ɗauka ta fara bani excuses ɗin cewa she's busy shi yasa bata samun cikakken lokacin magana dani ba.”

Ganin damuwa kwance ƙarara akan fuskar sa yasa a hankali Mahi ya shiga kwantar masa da hankali yace.

"Haba Farooq kamar ba ka san sha'anin kasuwa ba,kafi kowa sanin irin wahala da gwagwarmayar da ake shiga musamman idan zaka kafa branch in da ba ƙasar ka ba yafi komai wahala kafi kowa sanin haka. Is a matter of time kayi mata uzuri nasan itama ba don tana jin daɗin hakan ba da ta riga ta gama shikenan. Yanzu a ina aka tsaya da zancen”

Ajiyar zuciya ya sauke because sai yanxu yaji ɗan sauƙi sauƙin abinda ya taru ya danne masa zuciya. Yace.

“she spend almost 6weeks a Cairo Sai last two weeks suka Isa Dubai ɗin amma ta faɗamin Friday ne bukin zai gudana.”

Mahi yace.

“To ai shi kenan, kaga zuwa Friday komai ya ƙare za kuma iya dawowa tare”

Farooq yace

“Hmmm! Allah yasa”

Mahi yace

“Amin”

Miƙewa yayi tare da kallon Mahi yace.

“Thank you for the food. Ina so zan tafi Kaduna gobe da safe in sha Allah tun last month da naje har yanxu bata sake gani na ba”

“Owk! Allah ya tsare ka gaida min ita”

****************

Malali

Kaduna state

           Nigeria

Washe gari ƙarfe goma na safe a gidan Madinah tayi masa kamar yadda ya tsara.

Zaunawa yayi kusa da ita ya ɗora kansa akan gefen shoulder ɗinta for almost 15mnt relaxing him self from all the stress that he's going through. He used to feel safe and secure when ever he's with his amazing Grandma.

Sai da ya jima a haka Daga baya yayi taking deep breath sannan ya ɗago ya kalle ta yace.

“madinah zaki zo tare dani wurin taya Hanifah murna?”

Murmushi tayi tace.

“Satin nan ne gaba ɗaya busy nake gaskiya, kawai ka faɗa mata ina gaishe da ita ina mata fatan nasara”

“Owk!, zata ji in sha Allah. Ki tashi ki samamin wani abin yunwa ni keji”

“To ai kai ne baka sanar dani zuwan naka ba da yanzu ka isko komai a shirye, amma karka damu yanzun nan in sha Allah zaka samu abinda kaci”

Tashi tayi ta nufi kitchen shi kuma ya wuce ɗakin ta ya kwanta a kan gadonta.

Dakatar da masu aikinta tayi akan su bata wuri idan ta kambala sai su dawo su gaba da abinda suke.

**************

BAHIYYA

  Kamar yadda Malama Rabi ta alƙawartamin, kwatsam muna zaune da safe ina niƙa kamar kullum Nuhaira na kan sana'ar ta ta kayan miya ta shigo tace min. Ina Mama na ce mata tana ɗaki, ɗakin ta wuce ni ban ji mi suka tattauna akai ba kawai dai mama ta kira ni tace in zo maza in shirya mu tafi zanyi wa wata hajiya kitso da lalle ita da 'ƴa' ƴan ta. Nan da nan na shirya muka tafi.

Duk yadda naji ana ambatar kyau irin na garin babban birnin Abuja ban taɓa zaton kyaun shi da tsarin shi ya kai haka ba sai yau.

Gidan ma da muka shiga da Malama Rabi tunda uwata ta haife ni ban taɓa gani gida irin wannan ba. Ya haɗu iya haɗuwa ya tafi da Imani na.

A yadda naga tsarin cushion ɗin parlorn da abinda ke cikinsa a baki-baki na ɗan ɗosana ɗuwawu na zuciya ta sai bugu take tamkar ace kyat in zura da gudu.

Munfi kusan minti talatin sannan naga wata ƙofa ta buɗe wata kyakkyawar matashiyar mata ta fito wadda aƙalla zatayi arba'in zuwa arba'in da biyar tare da yara mata guda uku mabiyan juna, farare tas masu kyau da su anyi musu parking dogon gashin su da yasha gyara.

Da sauri na sauka ƙasa kamar yadda naga malama Rabi tayi nace.

"Ina kwana”

Zaunawa tayi tana mai sakin tattausan murmushi ta kalleni tace.

“Lafiya lau, kece mai Lallen kenan”

Ɗan ƙara yin ƙasa da kaina nayi nace.

“Eh nice”

Matar ta kalli Malama Rabi tace.

“To Malama sai ta fara musu Lallen ina zuwa yanzu, Ku koma can Main parlour kuyi a can”

Tashi mukayi kamar yadda tace muka koma wurin da tayi mana umurni, ware ido nayi da kyau na ƙarewa Parlourn kallo a raina nace masu kuɗi sunji daɗin su yanzu shi wannan Parlourn daban da wancan kuma a nan zamuyi zaman lalle.

“Bahiyya Ki haɗa Lallen ki fara kin san lokaci ba wahala yayi nisa”

Aikin lalle Indai na saka kaina nan da nan nike zane sa in tashi domin ni daman ina da zahin nama wurin yin abu.

Kafin kace mi har na gama tsantsare su da Lalle, kuma a yadda naga  yaran na farin ciki shi ya tabbatar min da cewa lallen ba ƙaramin  burgesu yayi ba. Ina gama musu nayi sallahr zuhr aka kawo abinci mai rai da lafiya naci nayi hani'an sannan na hau yarfa musu kitso, Ina cikin yi musu kitson ne wasu yara maza suka shigo guda biyu matasa haka ganin kamannin su da yaran da nike wa kitso shi ya tabbatar min da cewa yayyunsu ne.

Ɗayan wucewa yayi ya buɗe wata ƙaramar locker ya ɗauki takardu ya fice shi kuma ɗayan ya tsaya yana ta santin lallen wadda naji ya kira da Nimrah yana tsokanarta.

Bayan an kambala komai na wanke musu lallen matar ta fito tana ta godiya tace itama da bada ita ba amma dan Allah zuwa Friday ta kawo ni in zo in yi mata domin ta yaba da aiki na yafi burge ta fiye da na Maryam. Kasancewar yamma ta riga tayi dole zamu tafi gida.

Kuɗi ta ƙundula ta bani tare da kaya a wata ledar shopping, sannan ta bani wasu kuɗin daban ta ce min 5k ne kuɗin kayan lallen da na siyo cikin mamaki nace mata ai kuɗin bai kai haka ba tace to in tafi kawai komai ta bani bata biya ba domin yaran ta sunyi kyau sosai. nayi mata godiya sosai muka dawo gida. Bayan mun shigo gida nabawa malama Rabi kuɗi tace min a'a in riƙe duka nawa ne itama ta sallameta. Nuhaira uwar kaɗaɗi ita ta buɗe ledar bayan Malama ta tafi. Turmin atamfa ne da kayan cusmetics masu tsada na 'ƴan gayu. Kuɗin kuma da ta ban daban dubu ashirin ne cif. Mamaki ya kasa ɓoyuwa akan fuskokinmu musamman Mama, zunzurutun dubu ashirin da biyar kai tsaye kamar tsintuwa. Addu'a tayi ta min ni dai Nuhaira tana yi mana fatan alheri wanda hakan ba ƙaramin daɗi yake min ba.

*************

Jumeirah Lakes Towers (JLT)

Dubai, UAE.

  Ranar Friday itace wadda ta kasance ranar ƙaddamar da center Hanifah kamar yadda tayi buri.

    Wurin ya ƙayatu iya ƙayatuwa fiye da yadda bata zata ba, Daddy ya shirya mata taro wanda har a cikin ranta taji ta ƙayatu ainun sannan kuma ya fitar da ita kunyar baƙin ta. Babu abinda zata cewa daddy sai godiya................

*OUM-AMEER *

💝 *BAHIYYA* 💝

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*AMINA IBRAHIM*

(OUM-AMIR)

*WATTPAD:*

*@UMMU-AMEER*

*PAID BOOK 500*

*3132703269*

*FIRST BANK*

*AMINA IBRAHIM*

*08068974831*

*FREE PAGE*

*BABI NA BIYAR*

............... A makare ya iso wurin shiyasa bai samu haɗuwa da ita ba sai a filin taron. Tunda ta tunkaro shi ya kasa ɗauke idon sa a kanta domin ba ƙaramin kyau ta masa ba. Wata arniyar Maroon Red carpets gown ce mai jela a baya a jikinta wadda ta bi jikinta ko ina ta manne tamkar an bita da fenti, an yi mata tsaga daga guiwar ƙafarta ta ta dama a ta gaba zuwa ƙasa, wuyan rigar V shaped ne yayin da ɗayan hannun rigar yake dogo duk an bishi da tsagu sai kuma ɗayan aka yi shi guntu cure da chipom. Gashin kanta kuma yasha gyara wanda aka nannaɗe wuri ɗaya a bayan ƙeyar kanta. Ta sha kyau sosai mutane sai yabawa suke. Daga inda Mahi yake zaune yana hango ta ji yake ranshi yana mishi wani iri, wai wannan matar Farooq ce, wai nan ita musulma ce mai sallolli guda biyar, kuma ƙarin abin haushin ma wai ga iyayenta a wurin duk suna kallon ta kuma ko a jikin su, sai kuma ya juya ya kalli dressing ɗin mamar ita kanta da kuma ƙanwar ta Hamrah kawai sai naga yayi murmushi tare da girgiza kai a ranshi yace wata Wayewar dai in dai haka take Allah ya tsare mu da ita.

Murmushi suka sakarwa juna ita da Farooq ɗin ta , a hankali ya tare ta tare da bata wani hurt hugging a hankali cikin shauƙi ya ɗora soft lips ɗinsa akan bare neck ɗin Hanifah yayi kissing ɗinta sannan yayi taking deep breath ya shaƙi ƙamshinta Mai ɗadi sannan ya janye ya saita idanuwansa a nata a hankali ya furta mata.

“ I so much miss you Hanifah, without you my life is going to be miserable. You look very beautiful and adorable wife, I'm really proud of you, Ina yi miki fatan nasara da fatan albarka ga duk abinda kika sa ma gaba Indai na alkaiiri ne, Grand Ma Itama tace in faɗa miki haka”

Hawayen farin cikin da suka gangaro mata ne tayi saurin sharewa tare da jin daɗin Kalaman mijinta with so much happiness tace.

“Thank you Farooq, you are the best husband ever, I really appreciate, a yanzu na gama sakankancewa da cewa duk abinda ka ke min da zuciya ɗaya kake yinsa a matsayi na na matarka, ka bani matsayin da ba kowa ne irin namiji ne ya ke iya bawa matar sa ba, I'm proud of you for being my lovely and caring husband, ban san ta ya zan iya gode maka ba....”

Ɗan yatsan sa ya ɗora akan lips ɗin ta yace.

"Shhh! kullum ni kawai abinda ni ke so Hanifah muddin zaki ƙaunace ni ki So ni, ni hakan ma is ok for me. I love you”

Hugging ɗin shi tayi tana murmushi tace.

“I love you so much Farooq”

Kawai ji sukayi ɗakin ya ɗauki tafi raf-raf-raf. Ana ihu ana yi musu kirari. Bayan like 20mnt haka aka gama shirya komai, aka shiga gudanar da ƙayataccen bukin yadda ya kamata.

Farooq bai san Mahi na wurin ba sai bayan da aka gama taron duk rabin mutane sun watse sannan ya gansa kawai yana masa murmushi. Ba ƙaramin mamaki ya bawa Farooq ba har bai san lokacin da yace.

“Mahi you are the most crazy friend in this world, when did you arrived here?”

Dariya Mahi yayi yace.

“While tunda Baban Soyayya ya kama Hanifah ya riƙe ta kamar zai cinye ta”

“Mahi I have every right because she's my wife, so don't judge me, kayi Abinda ya shafe ka”

Hannayensa ya ɗaga sama yana dariya yace.

“I rest my case”

Murmushi Farooq yayi yace.

"Better.” sai kuma ya sake kallon Mahi ɗin yace.

“ And thank you for coming, I really appreciate your presence.”

“Kafi haka a wurina Farooq, Ina Hanifah murna...”

Da sauri Farooq ya ɗaga masa Hannu tare da ciro wayar sa a pocket ɗin sa yace.

" Wait! Let me call her she's around here Sai ku gaisa zai fi”

Cikin mintunan da ba su gaza sha biyar ba ta iso wurin. Hannunta ta saƙala cikin wuyan hannun Farooq tana murmushi ta kalli Mahi tace.

" Mahi welcome”

Murmushi yayi yace.

“Congratulations Mrs Mai-gishiri, Allah ya sanya alheri yasa rai aka yiwa, ya kuma ƙaro dimɓin nasarori”

“Amin, thank you Mahi”

Daga haka ta juya ta ci gaba da sallamar baƙin ta. Su ma su Farooq ɗin daga nan suka wuce wurin nasu yi.

Washe gari ya zo gida ya same ta, bayan sun gama gaisawa da Momma ya wuce zuwa ɗakin da take, Hamrah na zaune akan couch ita kuma Hanifah tana tsaye tana saka kayan ta bayan ta gama mulke jikinta da mayuka. Da sauri Hamrah ta miƙe tana murmushi tace.

“Good morning Yah Farooq”

“How are you Hamrah and studies?”

Tace.

“I'm doing great Yah Farooq, Ina ta yaku murna da ƙarin wannan nasarar”

Yace.

“Thank you Hamrah. Allah ya albarkaci rayuwar ki...”

Hanifah ta karɓe zancen tana dariya tace.

“Ya kuma bata miji mai nagarta kamar Farooq ɗina”

Dariya Hamrah tayi tace.

“A'a fav. Sis wanda yafi shi ma zaki ce”

Dariya suka saka su duka ukun sannan Hanifah tace.

“Ina ga kin fara shan ƙwaya Hamrah, because ba zaki taɓa samun mijin da yafi shi ba... Oya get out please allowed couples to have some privacy”

Taɓe baki tayi tare da ɗaga shoulder tace.

“OK oo! Hamrah doesn't have problem with that, I can excused you love bird”

Daga haka ta fice ta barsu. Kamar jira yake Hamrah ta fita saboda ba ƙaramin jan hankalin sa Hanifah tayi ba, da sauri ya matsa in da take ya rungumeta ta baya gam-gam ya ɗora fuskar sa akan wuyanta tamkar ya haɗiyeta haka ya keji.

Tana murmushi tace

“Do you missed me?”

Yace.

“what! Wife are you teasing me? Common you too you know word can't express how much you I missed you”

Daga haka ya yi turning ɗinta tayi facing ɗinshi a hankali ya shiga kissing ɗin lips ɗinta romantically with his hand rubbing every part of her body passionately.

Ba laifi itama tasan cewa tayi missing fitinanne mijin nan nata saboda haka bata hana shi ba sai da taji ya fara ɓalla hook ɗin bra ɗinta da sauri ta janye tana kallon shi tace.

“Please don't...”

Cikin wani irin mawuyacin hali ya watsa mata rinannun idanuwansa da suka rikiɗe suka canja launi, murya a dishashe yace.

“Please Hanifah allowed me, idan kika hanani ban san ya zanyi ba.... Dan Allah Hanifah”

“Farooq I'm sorry, yanzu haka ina da muhimman mutanen da suke jirana a Office beside the whole staff are there waiting for me Idan na bar su hakan bai kyautu ba. Kayi haƙuri kawai har na dawo gida dan Allah tunda ba tsere maka zan yi ba.”

Jingina bayansa yayi a jikin wardrobe ɗin ɗakin with so much heart break yace.

“Buht I thought we are going back together Hanifah?”

“What! No gaskiya kaima kasan komawa na gida yanzu ba zai yi yu ba, I have to ensure that everything has fall apart kafin na koma gida”

Wani zafi yaji zuciyar sa nayi masa, ya tabbata idan bai yi da gaske ba Hanifah zata saka mishi ciwon zuciya. Cikin jin haushi yace.

“Hanifah ya ya kike so in yi da rayuwata ne? Shin shi wannan aikin na zuwa lahira ne? Of all the time that you have spend with out me ke ko kaɗan baki ji cewa a ranki ya kamata kiyi min adalci ba, Hanifah ke ba yarinya ba ce atleast ya kamata ki riƙa tunani irin na matan aure saboda you are not alone, you are married remember ni ba saurayin ki bane, ni mijin ki ne, hakan kike yi zunubi ne Hanifah Allah baya so....”

Hannayenta ta sanya a waist ɗinta tayi burning face tace.

“OK! Halin ku na maza yau kake so ka nuna min Farooq? What's the big deal here? Ban San nayi maka wani abun da har zaka ji haushi ka fara ihu haka ba. You are my husband but I know that I have my right too, you have no right to force me akan abinda banyi niyya ba ka gane?kuma magana ta ƙarshe I'm not going back with you Idan na gama settling business ɗina zan dawo”

Daga haka ta ɗauki purse ɗin ta ta wuce ta ƙyale shi, tana ji yana ta ihun kiran sunan ta amma ko sau ɗaya bata waiwayeshi ba.

**************

Abuja

Nigeria

Tunda ya dawo gida yake kwance bashi da lafiya, sai da Mahid yazo gidan yaga situation ɗinsa cikin gaggawa ya kira masa family doctor ɗinsa wato Dr. Nicholas. Zazzaɓi mai zafi ne ya kama sa, Dr. Nicho yayi mamakin ganin Mai-gishiri a wannan yanayin. Ba ɓata lokaci ya bashi taimakon gaggawa bayan ya samu bacci ya ɗauke sa ya shiga tambayar Mahi Ina Madam Hanifah ne, shine ya faɗa masa ai taje wurin familynta, shine ma ya saka Farooq ɗin Zazzaɓi. dariya ce ta kama dr. Nicho ta yaya za'a ce don matarshi ta tafi zai kamu da irin wannan zazzabi haka to idan haka ne ko duk zata tafi ya kamata ya riƙa binta suna tafiya tare. Bayan sun gama firah suka tafi tare ya karɓo masa magani ya dawo gidan yasa cook suka shirya abinci ya kai mai ɗaki amma har yanxu bai farka ba.

Ya daɗe har kusan yamma sannan ya farka yana buɗe ido yaga Madinah a gefen sa.

Cikin mamaki yace.

"Madinah! Yaushe kika zo?”

Matsowa tayi tare da share hawayen idanunta tace.

“Sannu Faruku, dan Allah kayi min alƙawarin ba zaka sake kwantawa ciwo ba, wallahi ba zan iya jurewa ba”

A hankali ya tashi zaune yana murmushin ƙarfin hali ya share mata hawayen ta yace.

“Ji wannan tsohuwar waye yace miki bani da lafiya da har zaki zo ki na min kuka a nan?...”

“Don't joke with me Faruku, I'm serious”

Hannunta ya sanya cikin nashi yace.

“Calm down please, you know that I'm a strong person, kawai guntun zazzaɓi ne kuma in sha Allah shikenan na warke daga yanzu ma”

“Allah yasa haka. Ga abinci kaci, mi kake so in zuba maka?”

Yace.

“Duk abinda kika bani Madinah zan ci, na gode”

Da kanta ta shiga bashi abincin a baki kamar sanda yake ƙarami, bayan ya gama ta zauna kusa da shi tana shafa suman kansa can cikin zuciyar ta kuma fal take da tausayinsa.

Shiru ne ya ratsa tsakanin su na dogon lokaci sai daga baya ya kira sunan ta yace.

“Grand Ma”

Tace.

“Na'am Faruku”

“A karo na barkatai kuma na ƙarshe ina roƙonki da ki faɗamin su waye mu?”

Gyara zamanta tayi da kyau tace.

“Yanzu kuwa zan faɗa maka abinda na daɗe ina ɓoyema. Asalin sunana Rebecca Samuel ne, mijina kuma Carlos Ishaya, Asalinmu mu en jahar Enugu ne, mu Christian ne gaba da baya lokacin da ƙaddarar kasuwanci ta kawo Carlos Kaduna sai muka dawo nan da zama a hankali sai muka karɓi addinin musulunci na canza suna zuwa Madinat Carlos kuma ya canza zuwa Modu garba, kuma mun sani cewa zunubi ne daga cikin dangin mu duk wanda ya canza addini to daga ranar ya fita daga cikin family har abada za'a ɗauka cewa mutuwa yayi, muna nan zaune lafiya har na haifi Azizat wato mahaifiyarka muka yita renonta cikin kulawa tayi karatu har ta gama Ss3 sai ga wani mutumin Nijar yazo neman aurenta har ni na ce ban amince ba amma Kakan ka yace sam tunda shi take so dole shi zamu bata dole ba dan na so ba aka yi mata aure da Lawali Mai-Gishiri. Bayan auren suka tafi can Birnin Yamai har Allah yasa ta samu cikin ka aka haife ka bayan kayi shekara biyu suka shirya suka zo nan sai da tayi wata biyu a gida tana shirin tafiya na nace da magiya akan dole sai ta barmin kai bata tsaya jayayya ba ta haɗa dukkan ka yanka ta ajiyemin sannan baban ka yazo ya ɗauke ta suka tafi, a wannan ranar muka samu mummunan labarin cewa sun yi haɗarin mota sun mutu haka aka kawo muna garwasu domin basu yi nisa da barin garin Kaduna ba accident ɗin ya faru muna nan kuma muna rainonka ni da Kakanka shima tsakanin sa da Azizat 3years ne. Mijina yayi fice sosai domin sannannen ɗan siyasa ne kuma ɗan kasuwa. Da Dukiyar da ya tara na ci gaba da yin business ina kula da kai a hankali na buɗe Almadinah Textile and more a nan Kaduna, daga nan kuma bayan ka gama secondary nasan kasan da wayonka na ɗauke ka mu ka koma UK kayi karatuttukanka Daga baya muka dawo gida Nigeria. Dangin Mahaifinka basu san in da muke ba kuma har yau babu ko tsuntsu da ya taɓa zuwa ya ce min yazo neman Lawali da Azizat. Kaji yadda rayuwar mu ta kasance Faruku.

Cike da Mamaki yace.

“To miye abin ɓoyo a nan Grand Ma? Ko wane bawa ai da irin ƙaddarar sa”

Sai kuma yayi hugging ɗinta yace.

“Da kin sani da baki wahalar da kanki wurin ɓoyen wannan maganar ba har zuwa tsawon lokacin nan, Allah ubangiji yaji ƙansu da Rahma mu kuma ya kyautata tamu idan ta zo.”

“Amin. Ni ɓoye maka ne kada kayi ta jin ba daɗi”

Yace.

“Nothing like that Madinah, Dan Allah ki daina wannan kukan da kike wallahi bana so, Allah shi ne mai yadda yaso da bayin sa, sannan ina alfahari da ke, ko ban samu wasu dangi ba ke kaɗai da Hanifah kun ishe ni farin ciki, you meant so much to me Madinah, I love you. Kawai dai Ina so in san ina ne tushen mu kuma yau naji shi kenan”

Tace

“Hakane, Allah yasa mu dace. Tashi ka lallaɓa kaje kayi Sallahr magrib wata ƙila ma ko asr da zuhr ba kayi ba. Ni na san kana da sakaci da Sallah Faruku bafa abune mai kyau ba”

A hankali ya sauka yana faɗin.

“in sha Allah Grand ma zan gyara”

**************

Washe gari da Mahi yazo duba shi suna zaune Parlourn sa bayan sun gama gaisawa kamar ba zai yi magana ba sai kuma yace.

“Mahi please ka bani shawara mi zanyi Hanifah ta fahimci irin rayuwar da nike so da ita? Can you imagine Hanifah telling me that she knows her right ni ban Isa komai da ita ba, bayan nasan ni mijinta ta ne”

Gyaran Murya Mahi yayi yace.

“Da farko ina baka haƙuri Farooq, kasan wasu matan basu san abinda ya kamata ba sai an lurar da su suke ganewa, kayi haƙuri Kayi ta lallaɓata kana nuna mata hanya in sha Allah watarana zata fahimce. Abu na biyu kuma shawarar da zan baka nasan ba lallai ne tayi daidai da ra'ayin ka ba, amma Ina mai baka shawara zama a haka ba zai sa ku samu ci gaba a rayuwar auren ku matuƙar ba haihuwa kuka yi ba, wato Farooq ina so kasan wani abu, ɗaukar cikin ɗanka da mace zata yi har ta haife shi yana ƙara muku bonding da kafa wata ƙauna ta musamman ko don 'ƴa' ƴan nan. Duk wannan borin da take yi maka daga zaran kun in sha Allah zaku samu fahimtar juna da ita, sannan kuma Farooq ko don tsohuwar nan ya kamata ka tausaya mata ta samu yaran da zatayi wasa da su kafin ta koma ga Mahaliccin ta, zata yi matuƙar farin ciki. Dan Allah kayi tunani Farooq I'm not forcing or commanding, ni kawai Mai bayar da shawara ne. Yara farin ciki ne, rahama ne Farooq.”

“Sannan abu na gaba Farooq, Wayewar Hanifah tayi yawa, wallahi idan baka yi wasa ba sai kun shiga wutar Jahannama domin kuwa ku musulmai ne, kasani a cikin Alƙur'ani mai girma Allah yace ku tsare kawunan ku da iyalanku daga shiga wuta. Farooq ji irin shigar fitsarar da matarka take yi ta gaisa da wannan namijin ta rungumi wannan namijin duk da sunan wayewa. Ka riƙa yiwa matarka nasiha kana gayama ta gaskiya domin ku tsira ranar gobe alƙiyama”

*OUM AMEER*

💝 *BAHIYYA*💝

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*BY*

*AMINA IBRAHIM*

*(OUM-AMIR)*

*BAHIYYA NOVEL ƊIN KUƊI NE KIBIYA 500 TA WANNAN ASUSUN 3132703269 FIRST BANK AMINA IBRAHIM SAI KI TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08068974831*

*FREE PAGE*

*BABI NA SHIDA*

Jingina bayan sa yayi a jikin cushion ɗin tare da lumshe idanunsa relaxing himself yana digesting shawarar da Mahi ya basa.

Shi kuwa Mahi ganin ya ƙi ce masa komai yasa ya miƙe tsaye yace.

“Ni zan tafi I'm leaving to Ghana in sha Allah, kai kuma sai ka shirya kayi scheduling time ɗinda zaka gana da mutanen nan da na faɗa maka sun iso tun shekaranjiya, sunce ba za su gana da kowa ba sai kai”

Daga haka ya juya ya fice daga gidan.

Farooq kuwa yafi hour a haka duk wanda ya gansa zaiyi tunanin cewa bacci yake nan ko ba baccin da yake kawai matsalolin gidan sa yake ta lissafi yana neman hanyar warware su.

Miƙewa yayi ya shiga ɗakin da Madinah ta ke, gefen window ya sameta tana tsaye tana kallon waje amma ganin quick action ɗinta tana goge Hawaye ya tabbatar masa da cewa kuka take, cikin mamaki yace.

“Wai Madinah minene? Why have you been crying since yesterday ? da na san cewa tilas taki ki amsamin tamboyoyin zai sa ki yi ta kuka da na haƙura kawai,ko dai akwai wani abin ne bayan wannan ? Please idan har kina da wata damuwa just tell me”

Matsawa yayi in da ta ke tsaye ya rungumeta cikin nuna kulawa yace.

“Madinah Farukun ki ne idan akwai wani abu dan Allah ki faɗamin, idan ina ganin ki kina kuka zuciya ta ba zata iya daurewa ba”

Murmushi tayi tace.

“Haba ba fa komai, kawai dai tunawa da nayi da Azizat da Modu ne yasa zuciya ta ta kasa daurewa”

Cikin tausayawa yace.

“Nasan ba zan taɓa fahimtar yadda kike ji ba domin ke kika rayu tare da su ke kika san zafin su da muhimmancin su a rayuwar ki, to amma ni kuma da na san ke kaɗai ce rayuwa ta dole zan damu idan kina cikin wata damuwa, kiyi haƙuri”

“Na gode Umar”

Sake tambayar ta yayi yace.

“But Grand Ma, is that only my Mom you gave birth to?”

Gyaɗa kai tayi alamar eh sannan tace.

“Bayan haihuwar Azizat nan ma wata Azal ɗin ce ta sake faɗamana ni da Modu, bayan wata shida da haihuwar ta na je wajen wani spiritualist shima daga garin mu Enugu ya fito na san shi tun daga gida, buƙata ta na faɗa shi akan ina son maganin tsayar da haihuwa kafin yarinya ta ta girma saboda bana so inyi ciki da goyo, ya tambayeni sunan Mijina da kuma sunan da na canja nima na faɗa mishi, daga nan ya tashi ya shiga wani bukka sai da ya ɗauki lokaci ya fito ya ce min an gama aiki,aikin na binnewa a cikin ƙasa saboda haka duk lokacin da na ke buƙatar haihuwa in zo daga zaran an to ne shikenan. Hmmm! Faruku ban sake komawa wurin mutumin nan ba sai da Azizat ta cika shekara biyar cif a duniya, ko da naje na riski labarin da har in koma ga Mahalicci na ba zan manta da shi ba, domin kuwa ko da naje mutumin ya mutu shekara biyu da suka wuce, wurin nashi ma gaba ɗaya an rushe shi anyi gini kamar bai zauna a wurin ba. Kuma asirin an riga an binne sai idan an tone zan iya sake haihuwa, to kaji yadda mahaifiyarka ta kasance a gare ni ita kaɗai, nayi kuka nayi kuka har na gode Allah na riga na aikata kuskuren da ba zai gyaru ba, a duk lokacin da naga abokanan hulɗa ta da yara fiye da uku huɗu sai na ji zuciya ta ta tsinke in yi ta kuka ina istigfari. Hakan yasa ni da kakan ka muka ɗauki son duniya muka ɗorawa Azizat bayan ta mutu kusan zaucewa na kusa yi, hakan yasa da soyayyar kaka da jika da kuma soyayyar mahaifiyarka duk muka haɗa muka baka har Modu ya mutu ya bar mu daga ni sai kai”

A labarin jiya da ta bashi bai ji abinda ya girgiza shi irin na yau ba, haƙiƙa ya tausayawa wannan tsohuwar matuƙa.

Shiru ne ya ratsa tsakanin su bayan some minutes ya ce.

"I'm so sorry Grand Ma”

Murmushi tayi tace.

“thank you. Ka je ka shirya ka zo ka kai ni gidan Victoria nayi mata alƙawarin watan watarana zan zo tare da kai idan damar hakan ta samu”

“Wace Victoria?”

“She's my old friend since from child hood we were from the same state”

"OK.”

Bayan ya gama duk abinda yake suka shirya around 12:00pm suka bar gidan.

Sun samu tarba mai kyau gidan da suka je, sai 4pm suka dawo.

Madinah tayi hakan ne domin ta rage masa damuwar da take damun sa, Mahi yayi mata duk bayanin da yake ciki to amma ba zata shiga al'amarin gidan sa ba, zata dai taya shi da addu'ar da ta saba yi masa kullum, kuma shi ma bai damu da ya sanar mata ba saboda duk lokacin da ya mata lodging wani complain tsakanin shi da Hanifah sai dai ta ba shi haƙuri tace yayi haƙuri Hanifah yarinya ce watarana zata daina.

A haka tayi ta ɗau ke masa hankali suna yawon kai ziyara na tsawon kwanaki daga baya kuma ya warware ya koma Office, amma Kullum kwanan duniya da matarsa yake kwana a rai da ita yake tashi.

***********

BAHIYYA

A 'ƴan watannin nan na samu kuɗi ba laifi domin Malama Rabi ta sama min customers da nike wa aikin lalle da kitso sun fi a ƙirga kuma kowa da kalar irin biyan da yake min na karamci. Hakan yasa muka haɗa kuɗi kusan dubu saba' in Mama ta baiwa Malama akan mu tafi tare a samu makaranta private dai dai da matsayin mu a sanya Nuhaira kafin zuwa wata shekara ni kuma a biya min kuɗin WAEC.

A ta dalilin rashin samun Baba Maharazu a waya shine sanadiyyar da Malama ta shiga gaba gaba aka yiwa Nuhaira komai har uniform har komai ya kama kuɗi dubu saba'in da huɗu termly kuma Dubu ashirin da biyu. Ss1 to Ss3.

Malama ta kasance maƙociyar mu ce tunda muka dawo nan garin Kaduna Road suka haɗu da Mama, da ita da mijinta duk malaman makaranta ne suna da yara huɗu, bariki ba kamar gida ba ne namiji zai bar matarsa ita ma ta fita ta nema domin su taru su rufawa juna asiri matuƙar zata iya, hakan yasa Malama bayan aikin koyarwa ta shiga hulɗa da mutane daban daban tana kai kayan mata cikin gari da kuma sauran State tana kuma da shago ƙofar gidanta. Ta iya kanta sosai shiyasa duk yadda kake tana iya zama da kai tana kuma da kirki irin nata.

Sanadiyyar komawar Nuhaira school yasa aiki ya taru ya min yawa ni da Mama in kuma na fita cikin gari ita kaɗai tayi ta wahala shiyasa na nema mata almajiri mai taimaka mata.

Yauma haka nayi ta bada kayan miya idan an kawo niƙa kuma in tashi in yi domin Mama ta ɗan fita unguwa, ƙarfe uku nayi na yamma na shirya na fita islamiyya nabarwa Sharifu almajiri sauran aikin kafin Nuhaira ta dawo daga school domin sai uku da rabi suke tasowa kafin ta iso gida kuma huɗu tayi shiyasa take zuwa islamiyya yanzu a makare.

Ko da muka shigo gida ana kiran sallar magrib ganin banga mama a waje ba na shiga ɗaki na tadda ta kwance a duƙunƙune da sauri muka isa gareta ni da Nuhaira muna rige rigen tambayarta mike damun ta,ko iya ɗaga kanta ba tayi hakan yasa hankalinmu ya tashi sosai na cakumota da ƙarfi nace.

“Mama mi ne ne? Mi ya same ki?”

Sai tin zuciyar ta ta shiga nuna min da hannu alamar nan ne yake mata zafi. Cikin ruɗewar kuka nace.

“InnaLillahi! Wannan ciwon zuciyar ya matsa miki Mama. Tashi ki daure mu tafi chemist, yau da ke zan tafi domin ya duba ki.... Nuhaira ɗauko mata hijabi da mukulli mu tafi”

Da sauri Nuhaira tayi yanda nace muka rufe gidan a hankali muka lallaɓa da ita wanda ko a chemist ɗin kasa zaunawa tayi sai da na zauna ta kwanta a jiki na. Tambaya ta mutumin yayi mike damunta.

Kai tsaye na share hawayena na ce.

“Ta daɗe tana complain cewa ƙirjinta yana ciwo, to duk lokacin da abin ya tasar mata sai inzo in sayi mata magani ko nan ko kuma wani wuri in bata tasha, to yau dai bama nan ko da muka dawo kuma mun cimmata a haka”

Nidai ganin nayi ya ɗauko wani abu ya ɗaura mata a hannun ta sannan ya saka wani a kunne bayan ya gama. Ya kalle ni yace min hawan jini ne da ita kuma ya hau sosai fiye da ƙima.

Cikin tsantsar mamaki ni da Nuhaira muka haɗa baki wurin kiran.

“Hawan Jini likita?”

Cikin kuka na sake cewa.

“Hawan jini ta yaya? Wane irin hawa jini dan Allah, muna zaune lafiya”

Mutumin yace.

“While, ba abin mamaki ba ne ai, musamman idan akwai wata damuwa tare da ita tana yawan tunani da rashin samun ishashshen bacci, amma...”

Sai ya juya ya hahhaɗo magunguna ya bani na kusan dubu goma sha ɗaya.

A nan ya buɗe ya bata maganin, sannan yace

“idan akwai abinda yake saka ta damuwa kuyi ƙoƙari ku ɗauke mata hankali a kai, ta riƙa samun bacci yadda ya kamata tana cin abinci mai kyau, in sha Allah zata ji sauƙi”

Daga haka na cewa Nuhaira taje gida ta ɗauko masa kuɗin shi, bayan ta dawo muka koma gida, kafin shiga bacci har mun samu taji sauƙi domin har ta tashi tayi Sallah taci abinci.

Washe gari bayan mun gama sallar Asuba muka je muka gaishe ta nayi sauri na haɗa mana break fast Nuhaira ta shirya ta fita makaranta ni kuma na kai mata abin karin nata ɗaki bayan ta ɗanci ba yawa na bata magani kamar yadda likita yace.

Bayan na kwashe kayan na dawo na zauna cikin tausasa murya na kalle ta nace.

“Mama miye yake damunki haka? Mi kike tunani da har ya sa miki hawan jini nan take? Dan Allah Mama ki gayamin”

Girgiza kanta tayi tace.

“Ni dai ban san ina da wata damuwa ba Bahiyya, gaskiya ban sani ba.....”

Cikin rashin gamsuwa da maganar ta nace.

“A'a Mama, dan Allah ki gayamin minene damuwar ki,irin wannan ciwon ba zai kama mutum ba muddin ba damuwa ce a ransa ba.”

“Ni kam bani da wata damuwa Bahiyya”

Juyin duniyar nan nayi amma Mama ta kafe tace min babu abinda yake damunta dole na hak'ura na ƙyale ta ina faɗin.

“To tunda kince ba abinda yake damunki, dan Allah ki kwantar da hankalinki idan ma akwai wani abinda ba zaki iya gayamin ba kiyi haƙuri ki cire sa a ranki, bana so mu koma wurin likitin bayan kwana biyu ya aunaki yace min ga wata damuwa, idan wani abu ya sameki Mama ban san ya zamuyi ba. Kece ƙwarin guiwar mu, kece kaɗai muke da, ke kika zama bangon jinginar mu idan wani abu ya sameki ban san in da zamu shiga ba. Mama ke ce fa kullum kike min faɗa akan in dai na damuwa, in zama mai tawakkali, yau kuma ace kece wai hawan jini ya kama, mi kika nema kika rasa? Idan ma mutuwar Baba ce ya kamata ace kin saba kamar yadda kike faɗamin Mama...”

Hawayen da suka gangaro min na share tare da Miƙewa tsaye na fita waje jin sallamar yaro ya shigo gidan namu.

Mama kuwa mirginawa tayi ta kwanta akan pillow wasu hawaye masu zafi na bin gefen kuncin ta. Haƙiƙa mutuwar Jafaru ta nakasa mata zuciya ta yadda ma bata yi tsammani ba. Idan tace tana samun wadataccen bacci tsawon shekarar nan tayi ƙarya, babu abinda take tunani sai mijinta da kuma rayuwar marayun 'ƴa' ƴan ta mata guda biyu, waɗannan mutanen da suka kashe mijinta sunyi mata illar da har ta kwanta damanta ba zata warke ba. Domin shine jigonta shiya kawo ta wannan ƙasar ta Nigeria ba tare da tasan wani mutum na daban ba bayan shi. Gashi har ya koma ga Allah ƙasar ta sa ta gagare shi komawa akan wani dalilin banza na son zuciya irin na mutanen yau. Har baro garin Gusau tayi ko zata samu sauƙi ta manta da rayuwar su ta baya amma abin ya ci tura. To kuma yanzu ga ƙarin wata matsalar ta kunno kai tunda likitan ya faɗa mata tana da hawan jini damuwar ta da fargabar ta suka ƙaru, damuwa ta ƙara baibaye ta fiye da ta baya.

Ita tsoron ta kullum idan ta mutu a wane halin rayuwar 'ya' ƴan ta za su kasance? Sannan idan suka isa aure wa zai aure su idan akaji cewar ba su da dangin uwa babu na uba suka ɗai ne su uku suke rayuwar su.

Bayan kwana biyu kamar yadda likitan yace, na shirya na cewa mama ta shirya mu koma wurin mai chemist kamar yadda yace, ƙin amincewa tayi ta kafe kai da fata tace min taji sauƙi ba sai mun koma ba. Ƙarshe ma faɗa ta rufe ni da shi wai duk laifi na ne, daman su mutanen nan matuƙar kana ziyartar su to kullum cikin kira maka matsala suke, da ace na siyo mata maganin ta tun ranar tasha da yanzu kowa na nan hankalin sa kwance, to ita babu in da za ta je ta warke.

Dole na na kama kaina na ja baki na nayi shiru na ƙyale ta, amma Ina kula da ita sosai duk wani motsin ta yana kan idona, sai dai daga baya na gano tabbas Mama bata samun bacci kamar yadda likita yace, akai akai idan na farka naje ɗakin ta zaune nike samun ta kan sallayah.

Tun daga wannan lokacin na bata shawara ta riƙa sai ta lokaci idan ma tashin zatayi na dare to ta ta shi amma ta rage ɗaukar dogon lokaci.

Haka mukaci gaba da rayuwa, Mama ta samu sauƙi sosai a gaban idanunmu kamar yadda take nuna mana idan abin ya tasar mata sai ta tafi can wani chemist ta sayi magani ta dawo gida ta ɓoye tana sha don kar mu gani hankalin mu ya tashi. Nuhaira taci gaba da karatun ta, nima ina yawon lalle na da yanzu na ƙara yawan customers.

*************

Hanifah

Ko bayan rabuwar su da Farooq sai da ta sake share wata biyu da sati biyu a Dubai sannan ta wuce Egypt ta sake yin sati biyun ta masu kyau sannan ta dawo.

Duk iya yanda Farooq ya ɗauki fushi da ita kasa daurewa yayi dole ya dawo kiranta a waya yana jin muryarta amma bai taɓa tambayar ta cewa ina take ba, mi take yi ko yaushe zata dawo. Iyaka suyi wayar su idan sun ƙare su kashe. Sau biyu tafiya tana kama shi zuwa Dubai bai taɓa attempting na cewa ya je wurinta ba. Ya ƙyale ta har lokacin da ta ga dama ta dawo don kan ta.

Ko da ta iso ma baya ƙasar yana Saudiyya tare da Madinat sun je aikin Umrah sai da tayi kwana huɗu da dawowa sannan ya dawo.

Tare da Madinah suka shigo gidan, tunda yayi rashin lafiyar nan ta zo bata koma Kaduna ba. Cikin murna tazo ta tare shi tana faɗin.

“Welcome”

Kamar wanda yake mafarki haka yayi hugging ɗin ta back yace.

“Am i dreaming?”

Dariya tayi tace.

“No! Not at all. Is your Hanifah”

Ƙara riƙe ta yayi gam a jikin shi yana faɗin.

“Welcome back home my love”

“Thank you”

Ganin Madinah yasa tayi saurin janye jikin ta taje gareta with soft smile on her face ta bata side hug tace.

“Welcome Grand Ma”

Cikin Kalaman hikima Madinah tace.

“Thank you Hanifah. Da fatan an dawo lafiya”

Hanifah tace

“Lafiya lau Grand Ma”

Madinah tace

“Ya kasuwa? Ya familyn ki? Da fatan komai lafiya?”

Hanifah tace

“Everything is fine, my family are doing good”

“That's nice to hear.”

Madinah tace tare da kama hanyar zuwa masaukinta,luggage ɗin ta da suke hannun shi da kanshi ya wuce har ɗakin ya kai mata, daman tun a mota da suka sauka ya hana kowa ɗaukar kayan yace aikin shi ne saboda haka shi zai kwashe kayan.

Yana fitowa ya zarce ɗakin shi ya je yayi wanka ya shirya itama Hanifah da sauri taje ta sake yin wanka ta shirya cikin riga da wando da suka amshi fatar ta sukayi raɗau, sai wata hular net da ta saka ta naɗe kanta da ita tayi matuƙar kyau. Daman kuma kafin ta shiga ciki sai da ta saka Nafisat cook ɗinta cewa ta shiryawa Farooq table kafin su fito.

Ta riga shi fitowa hakan yasa ta wuce ɗakin shi direct ta sa meshi ya gama shiryawa yana tsaye jikin window yana kallon waje, hannayensa soke a cikin trouser pocket ɗin shi.

A hankali taje ta rungume shi ta baya tare da ɗora kanta a bayan shi tayi lamo, dukkan su babu wanda yacewa kowa komai tsawon lokaci suna a haka. Sai daga baya ta ja numfashi a hankali sannan cikin pleading tone tace.

“I'm sorry. I'm very sorry for what I did. I know that I hurt you, but what ever it is you are....”

Da sauri ya birkito ta ya rufe bakin ta da nasa yayi kissing ɗinta passionately sannan ya janye ya kalle ta cikin shauƙi yace.

“karki damu ni komai ya riga da ya wuce a wurina Hanifah”

Murmushi tayi tace.

“Thank you. Muje kaci abinci Nafisat ta gama shirya table”

Ba musu ya bi ta suka je suka zauna zaman cin abinci, yana cikin ci ya ji an kira sallahr magrib a masallacin gidan sa, da sauri ya miƙe yace.

“Hanifah an kira sallah, ya kamata ace na bar cin abincin nan har in dawo daga isha”

Kallon shi tayi tace.

“To kabari ka ƙarasa mana tunda ka fara”

Hanyar waje ya nufa yana faɗin.

“No, Idan na dawo after isha prayer sai ki sa a sama min wani abin”

Daga haka ya wuce ya barta. Zaman sa tare da Madinat wannan karon ya sa shi ya ɗan canza sosai, domin a lokutan baya Sallah a jam'i bata wani dame shi ba musamman idan yana gida. Amma yanzu ya dage sosai har asubahi yana fita.

Sai bayan ya dawo ya wuce ɗakin Madinah direct ya cimma bata nan, ba kayan ta, Wayar ta ya kira kai tsaye tace mishi gata a Kaduna. Abin yayi matuƙar bashi mamaki kamar wadda ake kora, ya rasa ya ta ɗauki Hanifah a rayuwar ta ko dai surukar ta ce iyaka kenan.

Ko da ya shigo bata nan, dining ɗin ya wuce ya ci abinci sannan ya shige ciki. Kwantawa yayi yay lamo yana tunani. Shi yanzu ya gama yankewa ba zai sake matsawa Hanifah ba akan buƙatarsa ba domin ɓacin rai ne kawai zai yi ta addabar sa, shiyasa yanzu ya yankewa kansa yin azumi domin ya riƙa samun sauƙi.

Yana nan yaji an murɗa handle ɗin ƙofar a hankali, ko bai duba ba yasan wacece ta shigo.

Kwantawa tayi akan ƙirjinshi ta saƙala hannayenta cikin wuyan shi. A hankali taji sautin Muryar sa yana faɗin

“Hanifah time yayi da ya kamata ace munyi settling mun samu yara, duk wannan maganar taki a baya ba tunani ba ne”

Cikin fargaba da tashin hankali tace.

“What! Haba Farooq yanzu duk tsawon lokacin nan da muka ɗauka ba ma tare da abinda zaka tare ni kenan? Bayan kasan cewa abinda ba zai yi yu ba ne....”

“Zai yi yu mana Hanifah,I'm fertile you are fertile too, to minene ba zai yi yu ba a nan?”

“Farooq No!”

“Hanifah abinda nike so kenan”

Miƙewa tayi without thinking twice kawai ta bar mishi ɗakin, abinda ba zai taɓa ma yiyu wa ba kenan. To Farooq Wai ko dai ya fara shaye shaye ne? Kawai kuma sai tayi tsaki domin babu abinda ya faɗo mata a rai sai Grand Ma Madinah da Mahid, ta sani sarai duk sune manyan munafukai da suke so su sanya mata ido a rayuwar gidanta. Ba ta taɓa jin ta tsani Madinah ba a rayuwar ta ba sai yau.

Ƙarshe kwanciyar ta tayi abinta tayi baccin ta ta ƙyale shi bata sake komawa kan shi ba, domin ta gama yankewa a ranta komai zai faru ba zata amince da wannan shirmen nasa ba, iyakaci dai ya gama fushi da ya huce zai dawo, ballantana ma tasan Farooq ba ya iya fushi da ita.

Washe gari ko da ta fito har ya fice daga gidan ko break fast Bai yi ba, nan ya bar mata kayanta yayi tafiyar sa.

Wanda hakan ba ƙaramin shayar da ita mamaki yayi ba.

Waya ta ɗauka tayi ta kashin wayar sa amma yaƙi ɗagawa, Ƙarshe sai ga text ya turo mata kamar haka.

“Ki amsamin buƙata ta kawai Hanifah”

Ajiye wayar tayi tare da zaunawa tayi break fast ɗin ta sannan ta shirya ta fita.

*OUM AMEER*

💝 *BAHIYYA*💝

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

               *BY*

*AMINA IBRAHIM*

  *(OUM-AMEER)*

*BAHIYYA NOVEL ƊIN KUƊI NE KIBIYA 500 TA WANNAN ASUSUN 3132703269 FIRST BANK AMINA IBRAHIM SAI KI TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08068974831*

*FREE PAGE*

          *BABI NA BAKWAI*

  BAHIYYA

   Yau ma da wani irin matsanancin faɗuwar gaba na farka sakamakon mummunan mafarkin da nayi a daren jiya,wanda har yafi wanda na saba yi a kullum muni. A sukuku na fito ɗaki bayan na gama sallah tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki, ɗakin mama na shiga na gaidata sannan na fito waje na zauna na buga tagumi ina karanta wasiƙar jaki. Ganin wankin hula na nema ya kai ni dare ga tarin ayyukana a gaba na yasa ni yunƙurawa da nufin miƙewa sai kwatsam Malama tayo Sallama ta shigo.

Cike da mamaki na amsa mata sallamar ta domin duk da cewa ban duba agogo ba nasan cewa iyaka ƙarfe shida ne yanzu na safe.

Da sauri tace min.

“Bahiyya ina mamanku? Yi maza ki shirya mu tafi Maman Khadijat ta kira ni yanzu tace dan Allah ki zo tafiya biki ta kama ta garin su ki zo kiyi mata lalle zuwa ƙarfe biyu zata wuce.”

Nima miƙewa nayi cikin sauri nace.

“Mama tana ciki bari naje to na shirya”

Bayan sun gaisa da Mama tayi mata bayani na shiga ɗaki na ɗanawa Nuhaira duka a cinya saboda takaicin baccin da take kwantawa bayan asuba, duk da cewa tasan tana zuwa school amma akan mugun bacci kullum sai ta sake kwanciya bayan sallar Asuba.

Firgigit ta miƙe cike da mita tace.

“Haba Aunty Bahiyya!”

Cikin jin haushi nace.

"Dan Allah ta shi kije ki nema abinda zaku karya ni fita zanyi, kada kiyi latti”

Miƙewa tayi tare da yin gunguni ta zo ta wuce nima naje na yiwa Mama Sallama muka tafi.

Ina jin daɗin zuwa gidan Maman Khadijat masu kuɗi ne na gaske amma babu ruwanta, ta iya sakin jiki da kowa, bata da wulaƙanci, hakama 'yar ta Khadijat da ta ke ji da ita, Allah ya haɗa jinin mu da ita sosai, bata ma wani jin Hausa sosai ni kuma ba wani dogon turanci nike ji ba, haka zamu zauna in tsantsara mata kalar kitson da suka nuna min in yi mata lalle tayi ta santi, tana ce min Aunty Bahiyya Thank you.

Hakama yayanta Ahmad da zaran ya ganni muna haɗa ido zai sakar min murmushi yace. Aunty Bahiyya hi! Mamar take gayamin cewa kullum idan suna fira ta sai yayi ta ce mata ina da kyau sosai ina burgeshi. Shiyasa ni ke jin daɗin zuwa gidan domin ba su da matsala.

*************

HANIFAH

Duk iya ƙoƙarin ta tayi akan cewa taga ta shawo kan Farooq amma abu ya faskara, zata iya cewa tunda take da shi wani abu makamancin haka bai taɓa shiga tsakanin su ba, duk yadda zasu samu ƙololuwar misunderstanding bai taɓa ɗagawa daga wurin ba sai ya tabbata ya shawo kanta komai ya wuce. Baya fushi da ita kai zata iya cewa ma basu taɓa samun makamancinyar wannan matsalar ba, domin zata iya bugun gaba ta tsaya ko a gaban waye tayi alfahari da mijinta tace yafi na kowa kaf a faɗin duniya.

Amma yau Farooq ne yake gudun ta, ko da zata farka ta wayi gari ya wuce abinshi ko da zata dawo daga office kuma bai dawo wa gidan ba sai cikin dare ya ke shigowa koda zai shigo tayi bacci.

Ranar da ta ritsa shi kuma sai ya wayance mata yace aiki ne yayi masa yawa a Office shiyasa.

Har office ta je ta sameshi yace mata taje gida idan ya gama zai dawo haka ta koma amma ƙarshe ma da ta bincika wai yayi tafiya zuwa Kenya.

Ganin ta kasa gane masa yasa ta shirya da wuri ta wuce gidan Rasi'at her best friend.

Tana shiga gidan ta cimma Rasi'at rungume da Khadijat Bahiyya na yi mata kitso.

Murmushi Rasi'at tayi tana mai kallon ƙawarta ta tace.

“Welcome Hanifah”

Ƙugu Hanifah ta riƙe cikin mamaki tace.

“Wai Rasi har yanzu ba zaki sararawa kanki ba ki daina ɗora Khadijat a jikin ki, yarinya shekara bakwai amma kullum kin maidata kamar 'ƴar shekara ɗaya.”

Khadijat waving ɗin hannunta tayi da lalle tana murmushi domin bata ma fahimci wane zancen Hanifah ke yi ba tace.

“Hi' Aunty Hanifah! See my beautiful Henna Aunty Bahiyya done it for me”

Duba lallen tayi tana murmushi tace.

“Wow! You look beautiful Baby, how are you?”

Khadijat tace.

“I'm fine, welcome...... ”

Sai kuma ta kalli Bahiyya tace.

“Aunty Bahiyya can't you greet Aunty Hanifah? But you are the one that told me to be greeting our visitors”

Sai yanzu Bahiyya ta ɗago cike da kunya ta kalli Hanifah tace.

“Ina wuni”

Kallon ta Hanifah tayi up and down sannan tace lafiya ta sakai ta wuce Babban farlourn Rasi'at.

Cikin hanzari Rasi'at ta sauke Khadijat daga jikin ta tacewa Bahiyya su ci gaba tana zuwa.

Tana shiga ta iske Hanifah ta dafe goshinta alamar damuwa ta bayyana akan fuskar ta tace.

“Friend is there any problem?”

Hanifah mace ce mai zurfin ciki da wuya abu ya dameta ta nemi wani ta faɗa mishi ko mahaifiyarta bata iya faɗawa abinda yake damunta in dai ba ta kama dole ɗin sai ta sanar mata ba.

Gyara zama tayi cikin damuwa ta fallasawa Rasi'at sirrin ta gaba ɗaya komai bata ɓoye mata ba har abinda ya faru a Dubai tsakanin ta da Farooq sai da faɗa mata.

Shiru ne ya ratsa tsakanin su na ɗan lokaci sannan Rasi'at ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Hanifah tace.

“You are at fault for everything Hanifah,kuma kin bani mamaki matuƙa. Miye a cikin haihuwa da zaki ce ba zaki iya ba? 'ƴa' ƴa sune farin ciki Hanifah, knock senses in to your brain, ba'a haihuwa aka haifeki?.....”

“Look Rasi, please I just need a way out, ni ba wani dogon zance nike so ba”

Cike da ɓacin rai Rasi'at tace.

“You are not serious Hanifah! Wallahi you better shine eyes, tunda har mijinki ba haka yake ba ta ƙarfin tsiya kika canja shi to ina tabbatar miki kwaɓarki tana gab da yin ruwa. Ni ban ma taɓa jin miji irin Farooq ba, abu sai kace a film ko a novel, duk abinda kika ga dama shi kike yi kuma wai ranshi bai taɓa ɓaci ba, ji abinda kika ce kin Mishi a Dubai kuma ya dawo kiran ki sannan kika dawo gida yace miki ba komai komai ya wuce, wallahi in baban Amed ne a ranar sai na gane nayi kuskure. Miye a cikin haihuwa? na haifi Amed gashi shekara Goma na haifi Khadijat she's seven years now, kinga wani abu ya fita a jiki na?....”

With full confidence Hanifah tace.

“Wallahi kin ragu Rasi, ke kanki kin san ba zaki taɓa haɗa kanki da wacce ba ta taɓa haihuwa ba irina”

Rasi tace.

“Eh bazan haɗa ba domin nasan cewa Allah ya bani girman da yafi naki, ke bari in faɗa miki wani ɗan ƙaramin sirrin samun yara da baki sani ba; a duk lokacin da kuka samu wani saɓani da namiji ya ƙona miki rai, da zaran kin zo ga yaran ki kin kalle su kunyi fira sai kiji duk wata damuwar ki ta wanke to idan baki da su fa? Sai dai damuwar nan ya kashe ki a banza kuma wata matar zai sake aura. Hanifah ki zama mai tunani da hangen nesa kar ki zama mai son kai, ki duba duk irin ƙaunar da mijinki ya nuna miki amma ke ace Common ƙaramin abu ba zaki iya yimai ba ya neme ki alfarma, Haba ki yi tunani in dai ke mai hankali ce...”

Hura hanci Hanifah tayi tare da runtse ido ta buɗe ta kalli Rasi'at tace.

“Is that all you have for me? A matsayin ki na aminiyata na kawo miki damuwata ina neman mafita abinda zaki faɗa min kenan?”

Matsowa Rasi'at tayi tare da janyo hannun Hanifah ta riƙe ta saukar da murya ƙasa tace.

“Hanifah, in dai ni kin yarda cewa best friend ɗin ki ce, to ina roƙon ki da ki amsa buƙatar mijin ki, ki haihu tare da shi matuƙar kina son sa, dan Allah Hanifah, wallahi babu abinda zai rage ki da shi face ma ƙara kusanta ki da mijinki ƙaunar da yake miki ta ƙara ninkuwa ninkin ba ninkin. Maza da dama basu yarda cewa matayensu na son su sai idan sun haihu da su to a lokacin zasu yarda cewa mace ta na son su and she is ready to die together with him. Let me give you an example with my self Hanifah ;ko da mukayi aure da Abdul-fatah bai yarda cewa ina son shi na shirya zama da shi ba sai da na haifi Amed, a lokacin na fara ma sanin miye soyayyar namiji kuma har yau muna respecting juna, I'm a business woman like you, but nothing can deprived me daga kula da mijina. Hanifah ki riƙa kulawa da mijinki, Farooq ba ƙaramin yaro bane kuma ba ƙaramin mutum bane, karki yarda ki bar wata ƙofar da zai fara yarda da cewa bai samu matar da ta dace da shi ba. Ki duba irin kyau da zubin da Allah yayi miki ki kuma duba siffar mijin ki shima, zaku samu 'ya' ƴa masu kyau da nagarta. Hanifah from the bottom of my heart that's the only advice I have for you Ko Nasibat ce sister na iya abinda zan faɗa mata kenan, idan kin ɗauka yayi miki amfani idan baki ɗauka ba watarana zaki ce na faɗa miki haka”

Ajiyar zuciya Hanifah ta sauke tare da gyaɗa kai tace.

“Thank you Rasi. I will think about it”

Miƙewa Rasi'at tayi tace.

“Thank you for understanding. Let me bring you something, kinzo na cika ki da surutu ba tare da na kawo miki abun taɓawa ba”

Dawowa tayi hannun ta ɗauke da tray with handmade juice da Kuma tsire tana dariya tace.

“Kin zo a daidai friend saboda na yi tsiren tukunyar da kike so”

“Wow! Thank you”

Bayan ta ajiye mata tace.

"Let me check on Bahiyya, Kar taga kamar na ƙyale ta....”

Ajiye Juice ɗin hannunta Hanifah tayi tace.

“Wait Rasi! Ina Wai kika samo wannan ita kuma? I wanted to ask you na manta ne, duk shagun nan da ke akwai na masu saloon komai kuma ana yi na masu kuɗi shine zaki ƙare da wannan tana taɓa miki jikin ki har kuna dariya da ita”

Zaunawa Rasi'at tayi tana murmushi tace.

“Eyyah! She's Bahiyya by name, wallahi Malama Rabi ce ta kawo min ita, yarinyar tana da kirki bata cika hayaniya ba, kuma ta iya sosai, Abdulfatah bai cika son zuwa saloon ba shi yasa na raba kaina. Hanifah yarinyar abin a tausaya ce, Mahaifin ta ya rasu daga ita sai Mahaifiyarta da ƙanwar ta ne a nan Nigeria duk sauran dangin su suna Nijar, kuma ba zasu iya Komawa ba...”

Cikin mamaki Hanifah tace.

“And who told you all this, is she the one? Kin san buzayen nan sun iya ƙarya, so karki wani saki jiki da ita wallahi zata iya aure miki miji, daga wannan kirkin nata zaki ji zance ya canza”

Dariya sosai Rasi'at tayi sannan tace.

“No! Ba ita ce ta faɗa min ba malama ce kuma ko shi ni na tambayeta bayan Bahiyyar bata nan nace miyasa bata yin school. Allah na tuba mi Abdulfatah zai yi da Bahiyya”

Daga haka Hanifah ta miƙe ta ɗauki jakar ta tace.

“Ni dai kar ki ce ban gaya miki ba watarana, kice mi Abdulfatah zai yi da ita, ko ni da na san na fiki kyau Rasi wannan yarinyar ta Cuna min balle ke. Ni Kinga tafiyata”

Dariya sosai Rasi tayi sannan tace.

"To ba matsala ni yoruba ita Buzaye sai mu shiga asirtar juna in ga ni da ita waye zai yi nasara”

Hanifah tace.

" Maganin dai kar ayi kar a fara, ki kore ta kawai”

Ko a parlorn sai da Hanifah ta sake ca ke ta da kallon ƙurullah, ganin yadda suke ta karatu ita da Khadijat da Ahmed suna dariya yasa ta taɓe baki ta wuce abin ta.

Rasi kuwa tsiren ta kawo wa Bahiyya tace.

“Bahiyya na gaya miki daman tafiya zan yi kuma sai gashi nayi baƙuwa, lokaci kuma yanzu ya ƙure ba zaki iya yi min ba. Sai dai idan na dawo kamar zan iya kai 1week saboda auren ƙanwata ne zanje idan nadawo zan aika Malama ta kiramin ke”

Cikin girmamawa Bahiyya tace.

“Allah ya kai lafiya, ya sanya alheri ya bada zaman lafiya”

Ƙarfe biyu na rana ta saka driver ya kai Bahiyya gida bayan ta cika ta da sha tara na arziki.

***************

BAHIYYA

Duk irin ɗaukin da na shigo da shi gida akan irin abin arzikin da maman Khadijat tayi mini lokaci guda ya suranye samakon wani irin mummunan yanayin da na riski Mama a ciki. A bakin bishiyar tsakar gidan mu na iske ta kwance shame shame a jikin Nuhaira Ko motsi bata yi. Wani irin jifa nayi da duk wani abinda yake hannuna nayo kanta tare da zunduma ihu nace.

“InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Nuhaira miye ya samu Mama? Miye ya same ta dan Allah??”

Itama cikin Kuka tace.

“Nima Aunty Bahiyya ban sani ba, Ina makaranta Sharifu yazo ya kirani wai Mama tana cikin yin Niƙa a injin shi kuma yana wanke wanke kawai suka ga ta yanke jiki ta faɗi, ko da nazo har Maman Walida ta shigo tana tare da ita, ni kuma na ruga wurin mai chemist na ce ya zo dan Allah ga halin da Mama take ciki shine bayan ya zo yace kawai muyi gaggawar kai ta asibiti, to naje Malama da mijinta duk basa nan, shi ne na zauna jiranki....”

Cikin masifa na ce.

“Amma sai yau Nuhaira na yarda cewa baki da hankali, shine zaki zauna ki barta ta mutu? bayan kinji abinda likitan yace cewa ayi gaggawar kai ta asibiti, uban mi kika tsaya jira baki san in da kuɗi yake ba, wawiyar banza”

Da gudu na faɗa ɗaki na ɗauko kuɗin da ban san ma adadin nawa ba ne na fito.

Da gudu na fita waje na hau mashin naje na ɗauko mota nadawo.

In banda kuka itama Nuhairar ba abinda take sai famar bani haƙuri take tana cewa ta ruɗe ne shi yasa.

Wata private hospital muka kaita in da aka taɓa admitting ɗin ɗiyar Malama wato Umaimah. Da sauri suka karɓe mu aka shiga da ita emergency. Tare da tsare mu da tambayoyin mi ye yake damunta.

Kusan kwanan mu biyu muna reto tare da Malama har da mijinta ƙarshe suka tura mu federal medical center bayan sun caje mu kuɗi sunfi dubu hamsin.

Ni dai biye kawai nike daga Malama sai mijinta Uncle Idris suka ɗai ke kai da kawo.

Ƙarin ruwa ne ake ta yi mata da allurai, tun muna waccan asibitin ta farfaɗo amma dai tana nan zurum kawai tana bin mu da ido malama kuma ta kasa yi min bayanin komai.

Ranar da muka cika kwana huɗu a ranar akace muna result ya fito na gwaje gwajen da duk aka yi mata wanda ko a nan an caje mu kusan dubu saba'in, har kuɗin da muke da yayi ƙasa nan ta ke.

Malama ta jima a ɗakin ganin likitan sannan daga bisa ni ta zo ta kirani muka shiga tare. Shekara ta sha takwas yanzu, duk da irin ƙananun shekaru na, Ina iya fahimtar abu akan fuskonki mutane na daɗi ko aka sin haka. Kafin ma likitan ya fara mini magana naji gaba ɗaya zuciya ta ta gama tsinkewa domin ji nike a jiki na wani mummunan abu ya faru da Mama.

“Bahiyya ko?”

Likitan ne ya faɗi hakan lokacin da ya dallomin Fitilun ganin sa babu ko ƙyaftawa.

Gyaɗa kaina kawai na iya yi ina wani muzurai tamkar an tsoma kaza a ruwan zafi.

“Da ace akwai wani na gaba da ke da dashi zamu tattauna wannan zancen, but unfortunately you are the only person na kusanta da zan iya yiwa bayani, Allah yasa zaki fahimce ni”

Lumshe jiƙaƙkun idanuwa na nayi waɗan da suka shabke da ruwan hawaye na sake buɗe su akan shi nace.

“Ina jinka likita. Miye matsalar, na roƙe ku da girman Allah ku faɗa min gaskiya kada ku ɓoyemin komai, nayi muku alƙawari zamowa jajirtacciya”

“To Alhamdulillah! Bahiyya haƙiƙa kowa ne irin mutum a duniya yana da irin tashi ƙaddarar ke musulma ce saboda haka nasan addinin ku ya koyar da ku yarda da ƙaddara...”

Ta wutsiyar ido na sake ƙare mishi kallo a karo na biyu, a raina nace yanzu kai duk haibar nan taka da iya bada magana kahiri ne kenan? To kuma ji yadda yaji Hausa kamar jakin Kano.....

“Bahiyya are you listening?”

Da sauri na gyaɗa kai na alamar eh sannan yaci gaba da cewa.

“Mahaifiyar ki tana ɗauke da ciwon hawan jini wanda ya fara cin jikin ta ne a hankali har ya girmama yayi tsanani ba tare da kunyi wani huɓɓasa wurin kawo ta asibiti da wuri ba sai da komai ya lalace”

Cikin matsanancin kuka nace.

“Likita muna yawan zuwa da ita chemist, da farko ni nike zuwa ina siyo mata magani a duk lokacin da tace tana jin ciwon ƙirji, daga baya da abin ya matsa mata sai muka kaita chemist likita ya duba ta ya bata magani, tun daga lokacin gaskiya ta warke”

Murmushi yayi cikin nutsuwa ya kalleni yace.

“Bahiyya baku san bambancin asibiti da chemist ba ne shiyasa, baku kaɗai ba mutane da yawa basu san bambancin tsakanin asibiti da chemist ba. A Nan asibiti muna da kalolin likitota sun fi a ƙirga, misali ;ni yanzu likita ne na zuciya, duk wani abinda ya shafi heart is my field, akwai likitan yara wanda shi harakar ciwon yara ne kawai ya sani, akwai likitan kunne, akwai likitan ƙashi, akwai likitan ido, akwai likitan tiyata shi aikin tiyata kawai ya sani, akwai likitan matsalolin mata duk abunda ya shafi ciki da haihuwa da reproductive system complication Shi ya sani, kowa da irin aikin sa da irin abinda ya karanta ya ƙware a kai, idan kika zo asibiti akace miki dukkan waɗannan conditions ɗin da na ambata da ma wanda ban ambata ba akace miki mutum ɗaya duk yake managing ɗin su renin hankali ya shigo ciki ko bai shigo ba?”

Cikin gamsuwa da bayanin sa na gyaɗa kaina alamar Eh haka ne.

Yace.

“To mai chemist Kamar haka ya ke Bahiyya duk kalar ciwon da za'a je mai da shi kai tsaye zai karɓa ya bada magani ko maganin yayi daidai da ciwon ko bai yi daidai ba shi dai kawai ya bayar, in ya bayar da abinda ba'a nan ya kamata a bada shi ba kinga shi kenan ya sanya rayuwar mutum a matsala, ba zai taɓa kallon condition yace ayi asibiti ba sai ya gwada yin karambani to sai kiga idan ba'a dace ba kuma an ƙara shiga wata wahala. Saboda haka ku riƙa kiyaye wa ku riƙa zuwa asibiti duk lokacin da kuka ji matsala, bance kada kuje gun mai chemist ba, amma sai idan an rubuta muku magani daga asibiti kuka ga can yafi sauƙi sai ku je ku siya idan yana da shi shine zaman lafiyar ku....”

Hannu ya miƙa ya janyo folder ɗinta ya buɗe ya bani duk gwaje gwaje da hotunan da aka yi mata yace.

“Wannan shine sakamakon gwajin da aka yiwa mahaifiyarki, sakamakon hawan jinin da take da shi yayi yawa har ya kai ga taɓa jijiyoyinda ke harɓa jini zuwa ga zuciyarta sunyi blocking wanda ake kira (Coronary artery diseases) wannan ya samu asaline sakamakon rashin samun cikakkiyar kulawar likita da kuma rashin bin ƙa'ido jin shan magani. Idan mutum yana da High BP abinda ke kawo irin wannan ciwon nan take ya haɗa da; yawan damuwa ta ƙololuwa, rashin samun wadataccen bacci, rashin motsa jiki da sauran su...”

“InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Allahumma ajirni fi musibatina wa akhlufni khairan minha”

Abinda na ke ta nanatawa kenan yayin da idanuwa suka ci gaba da tsiyayar da Hawaye marar misaltuwa.

“Bahiyya! ba kuka zaki yi ba a yanzu mafita zaku nema, a gwaje gwajenda muka gabatar ya nuna sai anyi mata wani aiki da ake kira Coronary artery bypass grafting (CABG). Wanda idan anyi shi shine zai taimaka jijiyon su buɗe jini yaci gaba da gudana yanda ake buƙata”

Cikin damuwa Malama Rabi tace.

"Yanzu likita aikin zai iya kaiwa naira nawa??

" While CABG procedure ta kasu kusan gida huɗu, sannan ko wane da kalar irin kuɗin da ake yin sa wanda ni dai a sanin da nayi mishi gaskiya a nan gida Nigeria ana yin sa, 4-8 million, akwai na 5-10 million, akwai na 6-12 million a sanin da nayi mishi amma ban sani ba ko yafi haka a yanzu, sai mun bincika munji....”

Kafin ma ya iyar da rufe bakin sa ban san lokacin da na yanke jiki na faɗi somammiya ba.

*************

Hanifah

Tunda taji shawarar Rasi sai ta ɗan ji maganar ta shige ta kaɗan, shiyasa tunda ta dawo ta kasa zaune ta kasa tsaye tana neman mafita. Kwana tayi zaune cikin internet tana ta searching tana samun bayanai da wankin ƙwakwalwa akan tana so ta haihu da mijinta ba tare da wahala ba amma bata san ya zatayi ba nan tayi ta samun bayanai kala kala har ta zo kan Surrogacy, sai da ta karanta bayanai da kyau wanda ya sanyata taji har cikin ranta cewa ta gamsu da wannan hanyar. Gari na wayewa ta wuce wurin Family doctor ɗin su wato doctor Nicholas.........

*OUM AMEER*

💝 *BAHIYYA*💝

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

               *BY*

*AMINA IBRAHIM*

  *(OUM-AMIR)*

*BAHIYYA NOVEL ƊIN KUƊI NE KIBIYA 500 TA WANNAN ASUSUN 3132703269 FIRST BANK AMINA IBRAHIM SAI KI TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08068974831*

*FREE PAGE*

          *BABI NA TAKWAS*

Nicholas Clinic and

            Maternity Hospital.

                  Kubwa, Abuja

 

  Zaune ta ke office ɗin Dr. Nicholas, Bayan sun gama gaisawa ta yaɗa masa manufarta ba tare da wani tunani ba.

Tunda ta fara magana Nicholas ke murmushi yana ta hasaso abubuwa na wauta irin na Mrs mai gishiri.

Bayan ta gama ya kallleta yace.

“While! you made a very sound decision, but Mrs. Mai gishiri i want to explain what surrogacy actually means. So that you may be able to decide what will be best for you and your family. Surrogacy mostly is for the couples who are infertile dealing with inferlity complications waɗanda suka kasa achieving pregnancy due to may be ga macen ne take yawan samun recurrent miscarriage, cancer or pelvic surgery, premature ovarian failure da sauransu, ko kuma may be ga mijin ne ya ke da problem na low sperm count or poor sperm quality, Ko kuma erectile dysfunction. Waɗannan suna daga cikin dalilai da suke sa ayi Surrogacy. But you Mrs. Mai gishiri and your husband doesn't have any problems,so to me, my suggestion for you shine kiyi haƙuri ki haihu da kanki, since you are not facing any challenges, you can do it......”

Da sauri ta girgiza kanta tace.

“Doctor Nicho, I have already made my mind, so I just need your help and please don't let my husband know about this until I decide to tell him my self. Yanzu ya ka ke ganin za'a yi, miye way out, zai yiyu ko ba zai yiyu ba ?”

With full confidence yace.

“Zai yi yu mana, sai dai akwai kuɗi sosai...”

Hanifah tace.

“No don't worry money is not a problem”

Yace mata ba damuwa, nan ya shiga yi mata bayani tiryan tiryan yadda procedure ɗin ta ke da duk process ɗin da za'a bi wurin ganin anyi achieving abunda ake so, but akwai high risk complications especially abortion, multiple gestation more than one, two, or even triplets.

Cikin gamsuwa da bayanin sa tace.

“I understand, to yanzu idan har buƙatar hakan ta kasance, a ina zan iya samun wadda zatamin in biya ta? You know it cewa kunfi hulɗa da mutane daban daban, I think you can get someone to do that for me right?”

Gyaɗa kan shi yayi yace.

“Since cewar akwai kuɗi, I will find some one for you”

“And which country do you think is the best to perform the procedure successfully, or can we go to UK?”

Yace.

“Yes, UK suma sun ƙware sosai wurin wannan aikin, may God help you”

Miƙewa tayi cikin farin ciki tace.

“Thank you so much doctor Nicholas for the help, Idan har buƙatar hakan ta taso zan nemo ka, sai muji ya za'a yi”

“You are must welcome Mrs. Mai Gishiri, till I hear from you”

Daga haka ta fito hospital ɗin driver ya tuƙa ta zuwa gida.

****************

BAHIYYA

Tunda likitan ya shaidamin zunzurutun uban kuɗin da ake da buƙata domin ayi wa mama aiki ban sake sanin ina kaina yake ba, sai da na farka na ganni kan gadon asibiti.

Da ƙarfin tsiya na juya na hantsilo ina mai ƙara rushewa da kuka nace.

“Miye na wani ɗora ni akan gado, ni ba wannan gadon ne buƙata ta ba, Mama ta ni ke buƙata malama, dan Allah ki gayamin ina zan samo wannan kuɗin kaf a faɗin duniya? Ko kurkukun gidan mu aka siyar ba zai biya ko kwatar kuɗin da aka nema ba. InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Yah Allah kai ne Mahaliccin mu, kai ne kafi mu sanin daidai a cikin rayuwar nan tamu, yah Allah ka kawo mana mafitar wannan masifar da ta kunno mana kai”

Rungume ni Maman Walida tayi cikin tausayawa tace.

“Bahiyya kin riga kin gama magana tunda ki ka ce Allah, in sha Allah shine manyasha'u shi zai yi muku mafita”

Murya malama na tsinkaya tana faɗin.

“Bahiyya kiyi haƙuri in sha Allahu zata samu lafiya”

Juyowa nayi da rinannun idanuwa da suka gama canza launi tsabar azabar kuka nace.

"Malama ta yaya? Gaban ki fa likita ya ambata mana zunzurutun kuɗi da bansan adadin su ba, bamu da kowa sai Allah, nasan haka zata mutu ta barmu mu biyu, kaico..”

“Tashi kije kiyi Sallah zuhr ki zo mu tattauna mafita, wannan kukan bashi da wani amfani a yanzu”

Ina dirowa daga kan gadon na wuce ɗakin da Mama ta ke kwance na tsaya bakin ƙofa ina ƙare musu kallo daga ita har Nuhaira wanda su basu san cewa ina wurin ba. Wani abu mai ɗaci naji ya zo ya tare mini maƙogwaro na, girgiza kai kawai nike ina ƙara jin wani sabon tausayi da ƙaunar mutum biyu ɗin nan suna ƙara yiwa zuciya ta ƙawanya. Idan muka rasa Mama ina zamu shiga kuma a duniyar nan?

Jin wani sabon kuka na neman ƙara ƙwacemin yasa nayi saurin janye jikina na wuce wurin ɗoro alwala.

************

Farooq

Duk gudun Hanifah da ya ke ba wai yana yinsa ne cikin daɗin rai ba, sai dai kawai yana so ta amince da buƙatarsa su samu ɗa tare kamar yadda Mahi ya bashi shawara, shi a plan ɗin sa Idan har ta amince ta haihu wata ƙila zasu iya samun fahimtar juna yadda yake so, idan ta haihu it may be ta fara sanin muhimmancinsa da kuma bashi damar da zai ji cewa yes shi ɗin mijinta ne. Domin abinda tayi masa ranar da ta dawo Nigeria tayi matuƙar bashi Mamaki, taya za'a ce duk tsawon lokacinda suka ɗauka basa tare saboda kawai ya yi mata zancen haihuwa zata hau dokin zuciya har ta iya barinsa tayi tafiyar ta ɗakin ta, to shi dutse ne da baya da zuciya a cikin ƙirjinsa ko ya ya?

Shiyasa kawai ya bata iska wata ƙila nisantar ta zaisa taji ko kaɗan ne a cikin ranta cewa tayi masa ba dai dai ba. Allah ne shaidar sa da irin tsananin son da yake yiwa HANIFAH, ya na so su rayu cikin soyayya da kulawar juna, yayi mata duk abinda take so haka shima tayi masa duk abinda yake so

amma ita sam bata gane hakan a wurinta ba abu mai yiyuwa ba ne, saboda haka he must take action Ko da zai sa ta shiga hankalin ta.

Idan yana tuna irin stories ɗinda Madinat ke basa dangane da rayuwar ta da mijinta Modu sai yaji ina ma ace Hanifah zata amince suyi irin wannan rayuwar tare da juna.

Ya jima tsaye a balcony ɗin gidan nasa kafin daga bisa ni yaja ɗan guntun tsaki ya shige cikin gidan, turus sukayi suna masu kallon juna tamkar yau ne ranar haɗuwar su ta farko.

Murmushin yaƙe yayi mata wanda iya ka cinsa kan leɓensa sannan yace.

“Hi..”

Da gudu taje ta rungume sa tare da sakin wani rikitaccen kuka tana faɗin.

“Why? Why are you doing all this to me? Farooq Ko ka daina so na ne ka faɗa min inji?”

Jin yanda take kuka yasa zuciyar sa jin wani irin ba daɗi.

Hannayensa ya sanya ya zagaye bayan ta a hankali yace.

“Idan na daina sonki wa zan so a duniyar nan? You are my heart beat Hanifah, da sonki kaɗai zuciya ta take bugawa. So ni ke mu haihu Hanifah, idan har kina so na kasance cikin farin ciki to tabbas ki amince ki haihu dani”

Janyewa tayi ta koma jikin faɗeɗiyar windown palourn tana mai zurawa waje ido tace.

“Sai naji kamar zan iya Farooq sai kuma zuciya ta tayi ta nuna min ba haka ba, ɗan Allah Farooq kayi haƙuri.....”

“No Hanifah, ni a yanzu shine kaɗai ni ke so daga gare ki”

Cikin ƙara ji tace.

“Toh let's adopt a child mana, zamu iya, yes we can get as many children as we want Saboda muna da dukiyar da zata iya bamu ko adadin 'ya' ƴa nawa muke so...”

Runtse idanunsa yayi tare da girgiza kansa sannan ya buɗe yace.

"No Hanifah! That's not part of my plan, ba zan iya adopting child ba as far as ubangiji na ya bani lafiyar samun yara bani da wata naƙasa....”

Rintse idanunta tayi tare da yarfar da hannuwanta alamar zancen ya fara harzuƙa ta tace

“OK... OK! We can get a child through Surrogacy, Hakan yayi maka?”

A matuƙar mamakance ya kalleta yace.

“What!..”

Da sauri ta zo ta zauna in da yake zaune tare da cukuikuye hannunsa ta karyar da wuya in a pleading tone tace.

"Dan Allah mana Farooq ka amince. Ƙwanmu dai ka ke so ka gani a duniya ko? To we can achieve it through Surrogacy, Sperm ɗinka za'a haɗa da Egg ɗina a dasa cikin mahaifar wata macen in 9 months data haife mana shi kenan sai ta kama gabanta...”

“No Hanifah...”

Wani Sabon kukan ta sake fashe masa da shi, tana faɗin.

“Dan Allah mana Farooq! Dan Allah ka amince, matuƙar kana sona kana kuma son farin ciki na to ka amince.”

A duniya cikin abubuwan da Farooq ya tsana a rayuwar sa akwai kukan Hanifah ciki, baya son kukanta ko kaɗan baya so.

Ba tare da wani tunani ba yace.

“Shi kenan na amince. But yanzu a ina kike ganin zamu samun macen da zata amince tayi mana wannan sacrifice ɗin.”

Cikin murmushin nasara tace.

“No kar ka damu, just leave everything in my hand, Ni zan samo macen da kaina, babu zancen sacrifice a nan tunda biya zamuyi, kawai dai everything have to be in secret between us daga zaran 9 months yayi ta haife sai ta kama gabanta”

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace.

“OK. Allah yasa a dace”

“Amin sweet heart, let me ask Nafisat to prepared table for us, today is a special day to us. Thank you”

Murmushi yayi mata yace.

“Thank you too Hanifah, I love you”

Matsowa tayi gab da shi ta yi brushing lips ɗinta da na shi sannan ta kalle shi tace.

“Na miss I dey miss you Love”

Miƙewa yayi cikin jindaɗi ya miƙa mata hannu yace.

“Shall we?”

Itama hannun ta miƙa masa suka nufi sashen sa, da taimakon ta yayi wanka yau tana tare da shi har ya gama shiryawa suka zo dining yaci abinci, sannan suka wuce nata ɗakin itama ta shirya. Soyayya suka sha abinsu tamkar wani abu na ɓacin rai bai shiga tsakanin su ba, Farooq ya zage ya nuna mata irin yadda yayi mugun missing ɗinta,That's her sweet test wanda yake mugun driving ɗinsa crazy, ga taushin fatarta da take shan gyara kullum da kuma haɗaɗɗen ƙamshinta mai canza duniyar sa zuwa wata duniya mai wuyar fassarawa.

A daren ranar through out tare suke maƙale da juna ta zamto masa wata kalar Hanifah ta daban tamkar yau ya fara sanin ta.

Da gari ya waye tana gama shiryawa suka yi break fast shaf-shaf ta ɗauko Jakarta ta na dariya ta kalle shi tace.

“Mission started, so I need your absolute support”

Murmushi yayi yace.

“My support is always there with you Hanifah, bye bye”

Daga haka ta fice.

Tun a hanya ta kira Doctor Nicho tace mishi she's on her way coming ya samu matar, yace mata ya samu, cikin farin ciki tayi mishi godiya kafin ta ƙara sa.

Tana zuwa kuwa ya tarbeta, bayan sun gaisa yace.

“She's Agnes by name, er asalin jihar Oyo ce, ta amince ne bayan na gabatar mata da manufarki.....”

“OK.. Bani Account na ta in fara bata kafin alƙalami”

Ba musu ya janyo wayar sa ya buɗe details ɗinda already ta riga turo mai ya bata account number ɗin take yanke ta tura mata 5million.

Ba'a fi minti biyar ba sai ga kiranta ya shigo wayar Doctor Nicho, Hanifah tayi zaton godiya zatayi kawai ta ji ta fara bragging cewa mi ta ɗauke ta ne talaka ko me, kamar ita da girman ta tana neman irin wannan sacrifice ɗin amma ta tura 5million wannan ai abin kunya ne, ya faɗa mata kuɗin aikin ta tunda har lafiyar ta ƙalau haihuwa ce bata so to zata bayar da 100 million idan yayi mata to idan kuma bai yi ba shikenan.

Da sauri Hanifah tace.

“Tell her that I will pay the money, kawai ta zo a fara shirye shirye.”

Bayan ya gaya mata abinda Hanifah tace, sai tace. Ita yanzu haka ma bata ƙasar, su jira idan ta dawo zata neme su but ta tura kuɗi kawai idan zata tura. Kai tsaye ta sake ca ke mata 45 plus wancan ya zama 50,tayi mata godiya tace sai taji daga gare ta.

Godiya ta sake yiwa doctor Nicho tace yanxu shi take jira taji daga gare sa su a shirye suke.

*************

BAHIYYA

A Yanzu kallo ɗaya zaka yimin ka fahimci cewa bana cikin hayyacina sakamakon gigicewa da ɗimautar da na shiga wurin neman kuɗin da za'a yiwa Mama aiki. Yanzu haka a kan magani take wanda a ƙalla anci kuɗi sunfi dubu dari uku. Malama Allah ne zai saka mata da mafifin alheri ita da mijinta domin kuwa sun dage wurin neman mana taimako wanda sun haɗa kuɗi yakai dubu ɗari bakwai, shima likitan namu doctor Samuel wanda ake kira doctor Sam ya taka rawar gani sosai wurin ganin cewa ya haɗa mu da ƙungiyoyi masu taimakawa marasa lafiya marasa ƙarfi, wanda a yanzu an haɗa mana kuɗi sunkai million ɗaya da rabi.

Nayi yawon nayi yawon har takalmin ƙafata sai da ya tsinke, yawo nake lungu lungu kwararo kwararo ina neman taimako amma ban iya haɗa ko dubu ɗari ba duk tsawon kwanakin nan, nayi ta gwada numbern Baba Maharazu amma shiru bata shiga tamkar malam yaci shirwa.

Har Gusau na shirya na tafi in da muka baro ko Allah zai sa a dace in samu Baba Maharazu da kuma mutanen unguwar mu ko zan samu wani taimako amma abin ba sauƙi saboda mutane rayuwar kowa ta kansa yake, haka dai suka yita yi muna addu'ar samun mafita ƙarshe sai maƙoncin mu ɗaya ne ya bani dubu ashirin yace dubu goma in yi na mota dubu goma kuma muƙara mu sayi magani.

Duniyar tayi min zafi, gabas da yamma kudu da arewa na duba na waiga na hanga amma babu wani sauƙi sai a wurin Rabbis-samawati.

Yau ma haka ne na gamo bilin bito na ban samu uwar komai ba sai tsabagen yunwar da ta addabi ciki na sai ƙugi yake, duk kuɗin mu sun ƙare komai yanzu sai a hankali ga asibitin kullum cikin bani bani.

Ɗakin na turo na shigo, a rakuɓe na hango Nuhaira gefe da alama bacci ɓarawo ne ya biyo ya saceta, domin ita na faɗa mata kada ta ɗaga ko ina, ko wane lokaci dole ta kasance tana kusa da Mama.

“BAHIYYA!”

Da gudu naje gare ta jin ta kira sunana, na fashe da kuka nace.

“Sannu Mama, in sha Allah zaki samu Lafiya ba jimawa..”

Girgiza kai tayi tare da sakin wani murmushin da yafi kuka ciwo tace.

“Bahiyya, abinda nike so in faɗa miki, ko da ta Allah ta kasance a gare ni, ki kula da ƙanwarki ku kuma tsare mutuncin ku duk wuya duk tsanani, sannan ku gwada tafiya tushen ku....”

Gefen yagalallen hijabi na na saka na share sabbin hawayen da suka gangaro min nace.

“Dan Allah Mama ki daina zancen mutuwar nan, wallahi a duk lokacin da kika ambaci mutuwa ki na mugun ɗaga min hankali. Shekara ɗayar nan da mukayi babu Baba ki duba yadda Rayuwa tayi mana juyin masa, Ina ga ace kema babu ke, duk kika tafi ki ka barmu Mama baki yi mana adalci ba, wallahi baki yi muna adalci ba, Ina kike so muje....”

A hankali Mama tace.

“Kayya Bahiyya! Ta Allah ai itace haƙƙun...”

Hannun ta na riƙe na kalleta nace.

“Na sani Mama, amma in sha Allah ba zaki mutu ba, sai mun samu kuɗin aikin nan an yi miki kin tashi da yardar Allah”

"Allah yasa haka Bahiyya, na gode, Allah yayi muku albarka”

“Amin Mama, dan Allah ki daina godiyar nan Mama”

Wani irin ƙarfi ne naji ya shige ni, duk wata yunwar da nikeji naji ta bar ciki na, miƙewa nayi ba tare da na san ina na nufa ba na fito daga cikin asibitin nayo kan titi. Lokaci guda tunani ya harɓa a ƙwakwalwa ta na cewa in tafi gidan Maman Khadijat mana, ai sati ɗaya ne tace zata yi nasan yanzu ta isa dawowa ko ban samu duka ba na ɗan rage wani abu ai zai fi.

Kai tsaye na yiwa gidan Maman Khadijat tsinke, a bakin gate ɗin unguwar su aka tare ni domin ban taɓa zuwa nikaɗai ba sai tare da malama da roƙo da magiya da komai na samu aka yi nasarar yin waya gidanta jin an ambaci sunana suka barni na tafi.

Ina shiga maman Khadijat ta tsuramin na mujiyarta ko ƙyaftawa babu. Bayan ta gama kallona murya a karye tace.

“Bahiyya what happened to you? Kin ganki kuwa?”

Ban tsaya nauyin baki ba na feɗe mata tun daga biri har wutsiya ban rage mata komai ba, a ƙarshe na fashe mata da kuka ina magiya nace.

“Ki yiwa Allah maman Khadijat ki taimakeni kamar yadda Allah ya taimakeki ki taimaka mana da ko nawa ne Allah ya hore miki.”

Guntun hawayen da ya sauko mata ta share tare da tasowa daga inda take zaune ta ɗago ni tsaye tace.

“share Hawayen ki Bahiyya, in sha Allah daga yau matsalar ku ta ƙare har abada, ni zan biya miki duka kuɗin in sha Allah, fatar mu ubangiji Allah ya bata lafiya yasa ayi aikin cikin nasara”

Bansan lokacin da na kai mata wata iriyar cakuma ba, na riƙe ta gam ina ta sabbatu wanda ni kaina ban san mi nike cewa ba.

Daga ƙarshe ta janye jikinta tace.

“Zauna ina zuwa yanxu”

Mai aikinta ta saka ta kawo min lafiyayyen abinci tace in cinye tana zuwa in bari ta shiga ta shirya ta fito mu tafi. Ni kam jin matsala ta tazo ƙarshe na zage na cinye abincin ras na kora da ruwan lemu.........

*OUM AMEER*

💝 *BAHIYYA*💝

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*BY*

*AMINA IBRAHIM*

*(OUM-AMIR)*

*BAHIYYA NOVEL ƊIN KUƊI NE KIBIYA 500 TA WANNAN ASUSUN 3132703269 FIRST BANK AMINA IBRAHIM SAI KI TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08068974831*

*FREE PAGE*

*BABI NA TARA*

BAHIYYA

..................... Tunda Maman Khadijat ta fito ni ke kallon ta. Kallo ne mai cike da abubuwa masu yawa waɗanda suka tsaya min a rai na masu wuyar fassarawa, ban san ma wacen irin kalar ƙauna zance ina yiwa wannan baiwar Allah ba, domin ta yi min abinda har in koma ga Mahalicci na bazan daina gode mata ba. Jin nike bayan Uwar da ta haife ni da Nuhaira babu kuma wani makusanci na kusa da zuciya ta wanda yafi ta. Allahu ya sani daman can ina ƙaunar ta sai gashi kuma yau ta yi min abin alherin da baki ma ba zai iya magantuwa ba wurin gode mata, sai dai in yi ta yi mata addu'ar gamawa da duniya lafiya don bani da wani abinda zan bata wanda yafi wannan.

“Bahiyya let's go mana, Wai mi kike tunani haka?”

Cewar maman Khadijat ganin na shagala da kallon ta duk inda ta wulga tamkar naga farin wata ɗan goma sha bakwai.

Miƙewa nayi ina mai share guntun hawaye na nace.

“Ba komai maman Khadijaht na gode sosai”

Murmushi kawai tayi ta girgiza kai tare da yin hanyar waje nima na rufa mata baya.

Motar ta muka shiga mai sanyin daɗi, dani da ita duk baya muka shiga yayin da driver ya shiga gidan gaba.

Yana cikin warming ɗin motar sai ga wata rantsatstsiyar motar ta kunno kai cikin gidan a raina ina mamarin ganin wanene wannan da zai fito a cikinta.

Da sauri naji maman Khadijat tace.

“Wait.. Wait Ishaq”

Daga haka ya kashe motar ita kuma ta sauka tana cewa.

“Bahiyya fito ku gaisa da baban Amed shine ya dawo”

Kallo ɗaya na yi masa na gasgata zancen ta domin ba ƙaramin kama suke yi da Ahmad ɗin ba, mutumin ya haɗu ba ƙarya.

Har wurin motar naje bayan ya fito na duƙa har ƙasa na shiga gaishe sa.

Cikin ɗaure fuska ya tanka min tamkar wadda akace ta yi masa wani laifin. A raina nace shi kuma kalar tasa fuskar kenan.

Komawa na yi daga nesa da su na juya fuska ta su kuma suka ci gaba da magana ƙasa ƙasa. Bayan kusan mintuna goma na ji muryar maman Khadijat tana faɗin.

“Bahiyya shigo ki jirani ina fitowa yanzu”

Ba tare da wani tunani ba na bi bayan su na shige farlourn da muke zama zaman yin kitso ina jiranta ita kuma suka shige ciki.

Ruwa taje ta kawo masa da lemu as usual tace.

“Ka fara shan ruwa tukun Baban Amed, sai muyi maganar.....”

Wayar shi ya ajiye a gefensa in da yake zaune ya kalle ta yace.

“Sweetheart ba wani ruwan da zan sha, ko na sha ruwa ba wata maganar kawai ba zaki biya wannan kuɗin ba fa gaskiya”

Cike da mamaki ta kalle shi tace.

“But baban Amed why? This poor girl need help badly, why won't I help her since Ina da yanda zanyi?”

Girgiza kansa yayi yace

“Rasi, to tell you the truth the money is too much....”

Cikin nuna ɓacin rai tace.

“But it's my money not yours, I have every right over my wealth...”

Cikin mamaki yace

“Oh! Is that So? You are telling me that is your money not mine...”

Sai yanzu ta fahimci katoɓarar da ta aika ta, cikin sigar rarrashi ta zauna a ƙasa tare da dafa ƙafar sa tace.

“Abdulfatah, na sani cewa ni da abinda duk na mallaka mallakin ka ne, I beg you in the name of God, ka barni in taimakawa mutanen nan dan Allah...”

Ajiyar zuciya ya sauke ya kalle ta yace.

“Rasi'atu, ban hana ki taimaka mata ba, but kuɗin ne sunyi yawa Rasi, 10 million fa, Haba! Da Allah bai sa naga text ɗin na yi saurin garzayowa na zo gidan ba da shikenan sai kije ki narka wannan uwar dukiyar ga wasu mutane waɗanda ma ni ban san su ba..”

“Baban Amed idan kai baka san su ba ai ni na san su, kuma manzon Allah (S. A. W) ya faɗamana a cikin hadith ɗinsa mai girma cewa duk wanda ya korewa ɗan uwansa wani baƙin cikin duniya Allah zai kore masa nasa baƙin cikin ranar gobe alƙiyama. So miye a cikin ten million Baban Amed, ni kaina nafi ƙarfin ta balle kai..”

“Sadaƙallahul Azim! Malama Rasi, ki fahimta, ni fa bance kada ki taimake ta ba, cewa kawai nayi kuɗin yayi yawa and I'm serious about it, zaki iya bata tunda ga 100k har 500k idan kuma ya fi haka to ban amince ba.”

Cikin karyewar zuciya tace.

“Abdulfatah kasan mi manzon Allah (S. A.W) yace ? ;cewa yayi ko wace irin al'umma tana da kalar ta ta fitinar, amma ni fitinar al'umma ta, itace dukiya. Idan ba fitinar dukiya ba miye a ciki don na biya musu kuɗi? Kafi ƙarfinsu na fi ƙarfinsu, Don mun bayar da 10 million miye a ciki Baban Amed??”

Miƙewa yayi yace.

“Mun gama magana Rasi, ban amince ba idan har ni kin yarda mijin ki ne shugaban ki ne”

Wani irin kuka ne ya kubce mata mai ban takaici da baƙin ciki, wai maza miye suka dauki kan su ne? Shi da yake yin duk abinda ya ga dama da kuɗin sa ta taɓa yi masa shamaki a kai ne?

Har ya kai ƙofa da sauri ta waiga tace.

“Baban Amed Kaji tsoron Allah, wannan yarinyar suna da buƙatar taimako, ba wani abin saɓa shari'a ne zan yi ba, ceton rai ne zanyi, Allah ya ga zuciya na da niyyana. Matuƙar muna da rai to jarabawa ba zai taɓa ƙare mana ba kar kayi mamakin hukuncin ubangiji kaima ya zama na ya jarabce ka ta wani hanyar da kake neman wani taimako wanda kai kuma kuɗi basu iya yi maka magani to sai ka yi yaya kenan..?” ko kuma ace Ɗanka Amed ko 'ƴarka Khadijat suna neman wani taimak....”

Cikin ƙaraji yace.

“Stop it! Stop it Rasi'at, kada ki tsaya ki nemawa kan ki zunubi akan wani dalilin ki na banza da wofi har yasa ki kai ga ɓatamin raina in yi abinda bai kamata ba. Na ce ban amince ba, ban amince ba! That's final. And pack all your things we are leaving this country tomorrow morning as early as possible”

Daga haka ya juya ya wuce abin sa ba tare da ya sake bata damar furta ko da kalma ɗaya ba.

Kuka ta ke sosai tamkar ranta zai fita. Wannan abun sam bai yi mata daɗi ba,Abdulfatah bai kyau ta mata ba, to ta ya ya ma zata iya fuskantar yarinyar nan da wannan mummunar magana? Tace mata mijinta ya hana ta ko ya ya?

Bayan ta gama darzar kukan ta mai isar ta ta gama duk wani saƙe saƙen ta taga cewa babu wata mafita dole ta miƙe jiki a saɓule ta fito zuciyarta na wani irin tuƙuƙi tamkar an ɗora ta akan tuƙubar tsire.

Tana shiga farlourn ta suka yi ido biyu da Hanifah. Take taji wani sabon kuka ya ƙwace mata, da gudu taje ta yi hugging ɗinta murya a raunane tace.

“Hanifah why is men like this? Su Idan suna son abu babu mai hanasu sai amma idan kai ne ka ke son abu kai da abun ka su nuna maka fin ƙarfi”

Cikin rashin Fahimta Hanifah tace.

“Me I don't understand you, can you made your self clear please?”

Zaunawa tayi ta gaya mata komai da ya wakana tsakanin ta da Bahiyya da kuma irin rashin mutuncin da Baban Amed ya gurza mata. Ƙarshe tace.

“Kin ma san wani abun takaici Hanifah? I'm 6weeks pregnant, cikin ɗoki yace min dole zai zaɓi wata ƙasar mai daɗi muje muyi renon cikin a can har na haife sai mu dawo na ce masa ban amince ba ya bari dai idan cikin ya kai term sai mu tafi,shine yace ya amince amma idan muka tafi sai babyn ya kai 2years zamu dawo nace na amince nima, a haka muka tsaya amma wai shine don yayimin baƙin ciki wai yanzu yake faɗamin in shirya gobe zamu bar ƙasar.”

Cikin Mamaki Hanifah tace.

“Ke ma dai Rasi kina bani mamaki wallahi yadda kike iya tolerating nonsense ɗin namiji, kuɗin sa ne? In da ace kuɗin sa ne don ya hana ba matsala ba ne...”

Wani murmushin takaici Rasi ta saki wanda yafi kuka ciwo tana girgiza kai tace.

“Hmm! Up to now you don't know men Hanifah, but bet me, one day one time sai namiji ya gurza miki watarana I promise you this, a lokacin zaki gane cewa maza maza ne kuma ba zaki iya yin komai ba a wannan lokacin, shiyasa nike gayamiki kiyi amfani da damar ki tun kina da lokacin ki”

Dariya ce ta suɓucewa Hanifah tace.

“Rasi, for get about it because wannan ranar ma ba zai taɓa zuwa ba”

“Hanifah bazan kira ki da yarinya ba, 8years in marriage kin wuce a ce baki san minene aure ba. while I don't blame you Saboda ba rayuwar auren tsantsa kike practicing ba daga ke har mijin ki baku san ma daɗin auren ba. But idan kika shirya rayuwar auren ta gaske watarana zaki ce na faɗa miki haka”

Taɓe baki Hanifah tayi tace.

“Rasi! yanzu dai duk abinda kike so nima shi nike so, tunda har Abdulfatah ya katangeki daga taimakon wannan yarinyar, me I will do that Ko don na kare miki mutuncin ki daga idon ta”

Cikin tsantsar farin ciki Maman Khadijat tace.

“Thank you, thank you Hanifah, wallahi ban san taya ya zan iya gode miki ba, thank you so much”

“Mention not Rasi, kinfi haka a wurina, tunda kin ƙi ki kore ta ya na iya, dole in so abinda kike so”

Rungume ta tayi tace.

"Naji dai, thank you matar Farooq.... Oya! Tashi muje bana so a tsaya wani jinkiri kuma kada wani abu yazo ya biyo baya”

***************

BAHIYYA

Tun ina zaune har sai da na kai ga gincirawa ba tare da na kawo komai a raina ba na zauna zaman jiranta, tunda har mijinta ne dole na san zata tsaya sai ta gama da shi sannan tayi ta tawa. To kuma ina nan zaune sai naga Ƙawarta ta shigo, hakan yasa na ƙara gyara zama domin na san dole itama sai ta bata time ɗin ta kafin ni.

Ganin har lokacin sallar Asr yayi yasa na miƙe naje na ɗoro alwala na zo na gabatar da sallah. Ina zaune Ina addu'a suka shigo tare da ƙawar ta ta.

Gaishe su na ƙara yi tare da baza kunne ina jira in ji tace na tashi mu tafi,sai dai ganin sun samu wuri sun zauna yasa ni jin wani abu ya ɗan ɗarsu a zuciyata.

“Bahiyya!”

Ɗagowa nayi na kalli Maman Khadijat nace

“Na'am”

“Tun ɗazu ina ciki da Baban Amed banki na yaƙi ya fitar da wannan kuɗin mai yawa, nayi ta gwadawa yaƙi bayar da haɗin kai shi yasa kika ga na jima ban fito ba, amma Alhamdulillah! Ga Ƙawata nan Hanifah in sha Allahu zaku tafi tare ita ce zata biya kuɗin babu wata matsala”

Rusunawa nayi inata gode musu wanda har sai dai Maman Khadijat taji tausayi na ya ƙara sarƙafe mata zuciya. A hankali tace.

“Bahiyya ba buƙatar duk wannan please, fatanmu dai shine Allah ya bata lafiya....” Sai kuma tayi murmushi tace.

“Bahiyya kin san ɗan Adam da kuɗi, tunda kuɗin nan yaƙi fita a banki na naji Zazzaɓi yazo ya kamani lokaci guda, bana jin daɗi jikina a yanzu ba zan iya fita ba, saboda haka kice ina gaida maman ku kinji ko, Allah yasa ayi cikin nasara. Tashi kuje”

Duk da cewa ban san abinda ke faruwa ba, wani irin abu naji mai sanyi ya mamaye zuciyata da gudu naje na ƙanƙame maman Khadijat ina ta rusa kuka tare da sakin sabbatunda ni kai na ban san mi nake cewa ba.

Daga haka muka tashi muka tafi a motar wadda ta kira da Hanifah.

Har muka isa asibitin ni da ita babu wanda yayi magana kowa da irin abinda ya ke saƙawa a cikin ransa.

Bayan mun isa bakin asibitin na miƙa hannu da nufin buɗe motar tace min.

“Dakata, akwai maganar da nike so muyi da ke..............”

*OUM AMEER*

💝 *BAHIYYA*💝

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*BY*

*AMINA IBRAHIM*

*(OUM-AMIR)*

*BAHIYYA NOVEL ƊIN KUƊI NE KIBIYA 500 TA WANNAN ASUSUN 3132703269 FIRST BANK AMINA IBRAHIM SAI KI TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08068974831*

*FREE PAGE*

*BABI NA GOMA*

........... Kafeta nayi da Fitilun ganina tamkar zan karanto wani abu daga allon fuskar ta.

“Daina kallo na haka da waɗannan idanuwan naki”

Jin ta furta haka a gare ni yasa nayi saurin saukar da idanuwana ƙasa da sauri kamar yadda ta umurceni, a can ƙasan raina kuma sai naji wani iri domin kalmar tayi min kama da ta muzantawa duk da cewa ban san abinda yake ranta ba.

Mun jima shiru kafin ta iya buɗe bakinta tamkar wadda aka tilasta akan dole sai ta yi min magana tace.

“Zan biya kuɗin aikin Mahaifiyarki kamar yadda Rasi tayi miki alƙawari, but sai dai ina da wata 'ƴar ƙaramar buƙata zuwa gare ki, idan kin amince fine, zan biya ko da sun kai million ɗari ne ba tare da ɓata lokaci ba...”

Ban tsaya nauyin baki ba kaina na ƙasa tunda ba taso na kalle ta nace.

“Zanyi koma mine ne kika buƙata muddin zaki biya kuɗin aikin mahaifiyata, ita kaɗai ta ragemin a duniya sai ƙanwata”

Gyaɗa kai tayi tace.

“While, ba wani abu bane mai wahala, kawai dai zaki tayani renon ciki ne zuwa wata tara daga zaran ya fito duniya sai kiyi tafiyar ki kawai aikin ki ya ƙare...”

Cikin azama na tare numfashin ta nace

“Na amince! in don ɗan waɗannan aikin ne tabbatas na amince”

Murmushi tayi wanda har sai da na jiyo sautin sa sannan tace.

“Ki dai ƙara tunani, kije kuma ki yi shawara na baki daga nan zuwa jibi....”

Hawayen da suka zamomin abokan rayuwata ne suka fara zarya akan kuncina, girgiza kai na na fara yi ina magiya nace.

“Dan Allah Hajiya ki taimaka min, in dai akan mahaifiyata ne babu wani tunanin da zan tsaya yi, duk da yanzu cewa an ɗora ta akan magani likita ya gayamin cewa rayuwar ta tana cikin haɗari aikin nan da wuri shine maslaha, bana son in rasa mahaifiyata dan Allah ki bada kuɗin ko aikin da yafi wannan ne ni na amince miki zanyi matuƙar zaki biya mata kuɗin aikin nan, kuma zan yi ta gode miki har in koma ga Allah ba zan manta da alherin ki gare ni ba”

Ajiyar zuciya ta sauke a hakankali tace.

“Shi kenan. Gobe da safe zan zo, amma Kuma aikin namu ba a nan ƙasar zamu zauna ba ƙasar waje ne zamu tafi”

Daga haka naji ƙofofin motar sun ce ƙitt! Alamar cewa sun buɗe daga nan na buɗe tare da ƙara yi mata godiya na sauka cikin tsantsar farin ciki na shige cikin asibitin.

Ina shiga na cimma Malama ta kawo abinci kamar kullum,Daman bayan ta taso daga makaranta idan mai aikin ta tagama girki sai ta shirya ta wuto asibitin tare da abincin.

Spoon ne riƙe a hannun Nuhaira tana bawa mama da ke jingine jikin pillow abinci a hankali tana mai ƙureta da kallo. Jin sallama ta yasa duk suka juyo, Nuhaira da malama suna rige rigen tambaya ta ina na shige duk yinin yau, domin ban faɗamusu in da zanje ba.

Da sauri naje na karɓi spoon daga hannun Nuhaira nace.

“Bani spoon ɗin Nuhaira, duk yinin yau ban hidimta mata da komai ba, bani ko wannan ladar na samu.”

A hankali na shiga bata abincin tana mai kafeni da ido wanda nasan ko bata furta ba itama tambaya ta take daga ina nake.

Kauda kanta da tayi shi ya bani tabbacin cewa abincin ya ishe ta daman ba wani abun kirki ta ke ci ba. Ruwa na bata sannan na tambaye ta ko akwai abinda ta ke buƙata, girgiza kanta tayi alamar ba komai sannan na miƙe na tattara kayan na dawo.

Gajen haƙuri ne yasa malama sake jefomin tambayar daga ina na ke.

Zaunawa nayi ina mai sakin sassanyar murmushi na kalli malama nace.

“Malama kin san daga ina na ke kuwa?”

Tsuromin na mujiyarta tayi tare da girgiza kanta alamar a'a.

Nace.

“Gidan Maman khadijat naje”

Cike da mamaki tace.

“Gidan Maman Khadijat Bahiyya! Kina nufin gidan Hajiya Rasi'a?”

Gyaɗa kaina nayi nace.

“Eh malama. Wallahi ko da na bar asibitin nan ɗazu bansan ina na nufa ba, sai daga baya tunanin zuwa gidanta ya ɗarsu a zuciyata....”

Nan na shaida musu duk yadda nayi da maman Khadijat da kuma wadda muka zo tare da nufin gobe zata zo ta biya kuɗin aikin baki ɗaya.

Kabbara Nuhaira ta ɗauka tare da zuwa ta ƙanƙameni ta saki wani kukan farin ciki tana mai faɗin

“Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Haƙiƙa dukkan wani tsanani yana tare da sauƙi Aunty Bahiyya da yardar ubangiji, waɗan nan mutane Allah ubangiji ya saka musu da mafificin alkairi. Amin.”

A hankali Mama ta runtse idon ta hawaye na sauka daga gefen kuncin ta, bakinta sai motsawa yake tana ta jera kabbara da yabo da nuna godiya a wurin Allah.

Malama itama rungume ni tayi cikin farin ciki tace.

“Haƙiƙa kin cika jajirtaciyya 'ƴa mai nagarta Bahiyya, kin saka kaifin hankali da basira wanda ni kaina tunanin hakan bai zo min ba, Hajiya Rasi'a mace ce mai taimako sosai, gaba ɗaya Allah ya mantar da ni da tunanin zuwa wurin abokan hulɗarki. Mungode mata sosai in sha Allah zan je har gida na yi mata godiya...”

Dariya ce ta suɓuce min bayan tunawa da Yarjejeniyar mu ni da Hajiya Hanifah na kalli malama nace.

“To amma kun san wani abu? Ita wannan hajiya Hanifah ɗin sai da mukayi wani sharaɗi a tsakanin mu, cewa wai zan taya ta renon cikinta idan ta haihu sai in dawo gida, nace mata ba matsala, wai harda cewa naje nayi shawara, ban san lokacin da na saka mata kuka ba, nace ba wata shawara ni na amince kawai tazo ta biya mana kuɗin.”

Cikin mamaki Malama tace

“ renon ciki kamar yaya? Ke da ba mijin ta ba taya zaki taya ta renon ciki? Kuma na san dai tana da masu aiki birjik duk basu ishe ta ba sai ke?”

A wauta irin tawa ban kawo komai a raina ba nace.

"Malama kin san halin masu kuɗin nan shegen son jikin tsiya ne da su, kuma mijin dole ya fita wurin sabgoginsa na yau da kullum, to wata ƙila ko ruwa tafi so a bata a baki, ni kuma ba ruwa ba ko wanka tace in yi mata wallahi tsab zan iya ina ruwana..”

Dariya Nuhaira ta fashe da ita tace.

"Kai Aunty Bahiyya wanka fa?”

Nima dariyar nayi nace.

" Wallahi Nuhaira da gaske na ke, ko wanka ta ce in riƙa yi mata zan yi matuƙar buƙata ta zata biya, biyan buƙata ai yafi dogon buri. Su masu kuɗin nan kawai idan tsabar jin daɗi yayi musu yawa haukacewa ma su ke, har a rasa mima za'a yi da kuɗi”

Murmushi Malama tayi tace.

“Abu ɗaya muke fata, Allah ya sa ayi aikin nan cikin nasara ya tashi kafaɗunta ”

Duk muka amsa da amin.

***************

HANIFAH

Bayan fitowa ta daga motar wani farin ciki ne ya lulluɓeta domin ba ƙaramar sa'a ta taka ba. Ainahin dalilin zuwanta gidan Rasi'a shine; bayan fitowar ta daga asibitin Nicholas direct office ɗin Farooq ta wuce cike da farin ciki ta sa mesa ta shaida masa yadda suka yi. Nan fa suka hau daru yace shi sam bai yarda ace Christian ce zata ɗaukar masa cikin ɗansa ba, ai addinin mu ya faɗamana cewa tun a ciki yaro yake fara koyon abubuwa kafin ya fito duniya, kuma ya kan ɗauko halayya da ɗabi'u saboda haka ba zai yi farin ciki ba ace wai ɗansa zai fito daga tsatson da addinin su bai zo ɗaya ba. Matuƙar tana so ya amince to ba zai yarda ayi dashen ɗansu a mahaifar Agnes ba, sai dai a fasa. Wuta sukayi sosai da shi. Ƙarshe cikin fushi ta baro Office ɗin direct ta nufi gidan Aminiyarta Rasi'a don ta koka mata matsalar ta sannan ta nemi shawarar ta akan ina ya kama ta a samo wadda za'a yi wannan aikin da ita. Kwatsam cikin sa'a sai gashi tayi katari da wannan damɓarwar tsakanin Rasi da Mijin ta. Cikin ƙwarewa da iya kanta ta jefi tsuntsu biyu da dutse Ɗaya.

Tasan idan ta faɗawa Rasi manufarta akan Bahiyya a yanda taga tana ƙaunar yarinyar nan ba zata amince ba, amma cikin ruwan sanyi gashi buƙatar ta zata biya. Addu'a take a cikin ranta Allah ya tabbatar da tafiyar su a gobe ɗin shi kenan itakam hankalin ta kwance.

Bayan ta gama nazare - nazarenta ta umurci drivernta akan ya nufi hanyar gida.

Tana shiga cikin sa'a kuwa taci karo da farooq ɗin ya dawo, masallaci ya wuce bai dawo ba sai bayan sallar Isha.

Har ɗaki ta samesa bayan ya fito daga wanka tayi murmushi ta ce.

“Welcome!”

Shima murmushin ya mayar mata yace.

“Thank you Hanifah. Ina kika je ne? Na je har office ɗin ki bakya nan?”

Murmushi tayi tace.

“Ina da wani sauran hutu ne bayan nasan cewa ban cika maka muradin ka ba. Na je neman matar kamar yadda ka buƙata...”

Runtse idanunsa yayi tare da girgiza kai yace.

“Hanifah! Hanifah! You are there stressing your self. Ni fa abun ma ya fara fita daga kaina...”

Cikin shagawaɓewa tace.

“But I have already found the woman, musulma Mai addini kamar yadda ka buƙata. Dan Allah Farooq ka karɓi abun nan da zuciya ɗaya please”

Kafaɗar sa ya ɗaga tare da ware hannayensa alamar shi kenan.

Hugging ɗinsa tayi tare da narke masa tana sakar masa sabbatu, shi kuma daman can in dai Hanifah zata biye sa to yafi ƙaunar wannan rayuwar soyayyar fiye da komai a duniya . Duk son sa da abinci haka suka lalace a wurin suna ta abu ɗaya.

***************

BAHIYYAH

Firah muka sha sosai muna ta tsara yadda zamuyi da likita kamar yadda ya faɗa mana cewa da zaran an samu kuɗin zai shige mana gaba a shirya yi mata aikin. Mama ma jefi jefi ta kan ɗan sako bakinta kaɗan. Gaba ɗaya da ka kalle mu kasan cewa cikin kashi saba'in kashi talatin na daga cikin damuwar mu ya tafi da ikon Allah.

Sai da aka gama sallar Isha mijin malama yazo ya gaida Mama, malama ta faɗa mishi abinda ake ciki ya nuna farin cikin sa yayi mana addu'a sannan suka fita zuwa gida.

A bakin get ɗin asibitin na tsaya nace.

“Malama dama akwai maganar da nike so in sanar miki.”

Tsayawa tayi shi Kuma uncle Idris yayi gaba wurin mashin ɗinsa ya tsaya jiran mu.

Kallon ta nayi tare da marairece murya na riƙe hannun ta nace.

"Malama akwai abinda na ɓoye ban faɗa muku ba. Matar tace ba a ƙasar nan zatayi renon cikin ba kuma dole in amince in tafi tare da ita, to na san idan na faɗa kai tsaye hankalin Mama na iya tashi ni kuma bana son abinda zai ɗaga mata hankali a halin yanzu”

Jinjina kai Malama tayi alamar abin babba ne tace.

"Dole kuma sai tare da ke Bahiyya? Anya zan yarda da wannan matar kuwa?”

Cikin magiya nace.

“Malama dan Allah kada ki ce a'a please, wallahi nayi imani ba zata cutar dani ba, gobe fa da kanta tace zata zo nan, kuma na faɗa miki babbar Aminiyar maman Khadijat ce idan har ba ta kirki ba ce maman Khadijat ba zata haɗani da ita ba. Malama wannan hanyar ita kaɗaice hanyar da zan iya ceto rayuwar mahaifiya, ba zan iya bari wannan damar ta wuce ni ba, domin idan Mama ta mutu wallahi ni kaina rayuwata tazo Ƙarshe, kawai abinda nike so da ke shi ne ki tayani da addu'a kuma ki kula min da Mama ta da Ƙanwata, shekara kamar kwana ce take cikin Ikon Allah zaki ga shekara ta zagayo, in sha Allah kuma zaku same ni mai kiyaye wa”

Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace.

“Bahiyya duk don saboda mahaifiyar ki kika yarda da ɗaukar wannan kasadar, dole zan kirashi da kasada domin ba ki san ina zaki ba kuma baki san mi zaki tarar ba, amma koma minene ina miki fatan tsarin ubangiji a duk inda kike, tunda har saboda mahaifiyarki kika ɗauki wannan nauyin in sha Allah ubangiji zai saka miki da abinda baki yi tsammani ba domin uwa ta sha gaban komai da albarkar ta zaki yi nasara a rayuwar gwagwarmayar ki in sha Allah. Zan kira Hajiya Rasi'a zuwa gobe in sha Allah domin in ƙara tabbatarwa daga gareta”

Rungume ta nayi ina hawaye nace.

"Na gode sosai Malama, kema in sha Allahu ke da mijin ki, tsaya mana da kuka yi sai ubangiji ya saka muku ta inda baku zata ba, domin da ace ubangiji bai haɗamu da ku ba ban san wace irin rayuwa zamu faɗa ba.”

" Ba komai Bahiyya ki koma ciki, dare yayi sai da safe in sha Allah, go be ma ba zan fita school ba, nan zan zo in sha Allah sai muga yadda za'a yi”

Daga haka mukayi sallama suka wuce ni kuma na koma ciki...........

*OUM AMEER*

💝 *BAHIYYA*💝

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

               *BY*

*AMINA IBRAHIM*

  *(OUM-AMIR)*

*MI KI KE JIRA NE ER UWA DA HAR YANZU BAKI YI PAYMENT BOOK ƊIN BAHIYYA BA??? ZANEN ƘADDARAR SU NE ZAI SOMA DAGA LOKACINDA AKA DASA SPERM ƊIN FAROOQ DA ƘWAN HANIFAH A MAHAIFAR BAHIYYA WANDA AKE KIRA SURROGACY A KIMIYANCE.WAI MIYE DALILIN SURROGACY ƊIN NE? DALILIN RASHIN LAFIYA NE?? A'A!! DUNIYA CE KAWAI TAYIWA HANIFAH DAƊI TAKE GANIN ITA SAM BA ZATA IYA HAIHUWA BA DOMIN DAUKAR CIKI DA HAIHUWA DA RENO SUNA CANJA HALLITAR MACE. SHI KUMA FAROOQ HAIHUWA YA KE SO, TO FA!! SHINE TA YANKE WANNAN SHAWARAR SABODA TA NEMAWA MIJIN TA FARIN CIKI, YAYINDA BAHIYYAH TA FAƊA KOMAR HANIFAH IDO RUFE TANA NEMAN KUƊIN DA ZA'A YIWA MAHAIFIYARTA AIKI, TO WANE ALFANU HANIFAH ZATA CIMMAWA? SHIN HAƘAR TA KUWA ZATA CIMMA RUWA KO KUMA TAYI SHUKA NE A IDON MAKWARWA????? KU BIYO NI IN SHA ALLAH TAFIYAR BABU DANA SANI*

*BAHIYYA NOVEL ƊIN KUƊI NE KIBIYA 500 TA WANNAN ASUSUN 3132703269 FIRST BANK AMINA IBRAHIM SAI KI TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08068974831*

*FREE PAGE*

     *BABI NA GOMA SHA ƊAYA*

         

    BAHIYYA

   Kwana nayi ina abu ɗaya wato tunani da zullumi, gaba ɗaya jin nike can ƙasan zuciyata na karaya domin tunda nike ban taɓa nisa da iyayena ba ko sau ɗaya sai yau da na amince da ƙudurin wannan matar, ba wai ina nadamar hakan ba ne a'a, nisantar ahlina da zanyi shine ya tsaya min a rai. Taya zan iya rayuwa babu Mama a tare dani har na tsawon shekara ɗaya? Wace irin rayuwa zan tarar a can? Wai ƙasar waje kamar yadda naji ta faɗa, Hmm!.

Abubuwan da suka yi ta cizon ƙahon zuciyata kenan gashi ina Allah Allah gari ya waye ni dai in ga an biya kuɗin aikin nan an yi mata a lokacin ne  hankalinmu zai kwanta.

Kiran sallahr Farin ko a masarrafar sauraro na ya sauka, da sauri na miƙe na ɗoro alwala na zo bayan na kambala raka'atanul Fajr na zauna na yi ta addu'ar samun nasarar aikin Mama da kuma zaɓin mafi alkairi a cikin rayuwar da zanyi ta shekara ɗaya.

Da wuri na je gida na shiryo mana abin karyawa na ɗauko wa Nuhaira tufafi kamar yadda ta buƙata.

Ƙarfe tara a Office ɗin doctor Sam tayi min, cikin farin ciki na shiga shaida ma cewar na samo kuɗin aikin Mama, shima congratulations ya shiga furta min tare da faɗin in bari ya kira asibitin yaji yaya za'a yi.

Muna nam sai ga malama ta zo abinda take shaidamin shine tayi ta neman layin maman Khadijat baya shiga ga shi har 10:00am tayi amma Hajiya Hanifah shiru.

Bayan mun gama tattaunawa da likitan ɗakin da mama take kwance muka koma muka ci gaba da tattaunawar a can.

Firar mu ke amma gaba ɗaya yanzu hankali na ya dugunzuma ya koma kan Hajiya Hanifah, ƙirjina sai dukan uku-uku yake ganin ta kai har zuwa wannan lokacin bata zo ba, kar dai ace fasawa tayi? Wayyo Allah na....

Ban tantance cewa kuka nake ba sai da naji Malama na faɗin.

"Subhanallah! Bahiyya lafiya kuwa?”

“Matar nan fa har yanzu bata zo ba Malama, kada ta canja niyyarta gashi har sha biyu tayi.”

“Kwantar da hankalinki haba, in sha Allah tana tafe”

Daga haka ban sake cewa komai ba na yi shiru cikin raina ina faɗin Allah yasa haka.

Ba mufi minti ashirin da gama maganar ba sai gashi an aiko ɗan aike cewa ana nema na a Office ɗin doctor Sam.

Ko da naje zaune take a office ɗin suna magana da ita da turanci da alama maganar aikin Maman ce suke yi.

Na jima a tsaye kafin nan suka gama ta juyo ta kalle ni kai tsaye tace.

"Aikin ki ya kambala, na cika nawa alƙawarin saura naki”

Murmushin nasara na saki ina faɗin.

“Nagode na gode Allah ya saka da alkairi....” daga haka na fita da gudu  naje na kira Malama da Nuhaira suka zo.

Kallon halittar ta Nuhaira ta tsaya yi tana mai ƙara tsinkewa da lamarin ta domin ba ƙaramar mace ta gani ba, tasha wasu riga da wando, rigar bakin guiwa ne sai wando plazo tayi ɗan ƙaramin rolling ɗin nan na manyan matan nan, ko mai hassadar ka idan ka kalli Hanifah sai ka sara mata, fatar luwai-luwai ga faranta mai ɗaukar hankali ga wanka komai na ta manyan mata.  sai zubo mata addu'o'i take tamkar wata zararrariya bayan ta gama ne Malama ta kalle ta Itama tace.

“Mungode sosai Hajiya, Allah ya saka miki da mafificin alkairi...”

Sai yanzu tayi murmushi tace.

“Ba komai ai dani da Rasi duk ɗaya ne. Allah yasa a dace.”

Daga haka ta miƙe ta fice ni kuma na bi bayanta har bakin motar ta. Ba tare da ta kalle ni ba tace.

"Na gama nawa, idan kin shirya ki zo wurin wannan doctor ɗin naku zai sadaki da ni, bana so ki bar ni na tsaya jira da yawa”

“Ɗan risinawa nayi duk da cewa bata kallo na nace”

" In sha Allahu ba zan jima ba daga zaran an kambala zaki ji ni”

****************

NATIONAL HOSPITAL ABUJA,

CENTRAL BUSINESS

DISTRICT, ABUJA.

Wannan ita ce asibitin da aka shirya za'a yiwa Mama aiki nan da kwana huɗu mai zuwa.

Bayan an yi booking likitan yace sai nan da sati shida za'a aikin, but ganin condition ɗinta ya zama emergency doctor Sam ya shige mana gaba aka yi postponding ɗinsa zuwa kwana huɗu.

Kukan farin ciki na fashe da shi a lokacinda malama ta ke sanar min an gama biyan kuɗin aiki har da kuɗin magani, sannan akwai 500k daga maman Khadijat  inji ita Hanifah ɗin. Sannan kuma tace bayan shi ko da ace an gama aikin idan akwai wata matsala za'a neman ta kai tsaye ta hanyar doctor sam, sannan kuma tace idan anyi nasarar aiki an bata sallama akwai million biyu da za'a bawa Mama daban ta ci gaba da kula da kanta da Nuhaira kafin na dawo, tunda likitan ya gaya mata cewa ni ce babbar 'ƴarta duk wani rabin nauyin ya rataya ne a wuyana yasa ta ƙara mana da wannan kuɗin na daban. Nan Malama ta ji ta saki jiki da ita tayi amanna da kirkin ta tare da yi mata addu'a.

Bayan an gama shirya komai kwana biyu tsakani muka tattaro kayanmu da Mama muka dawo nan asibitin. Ɗaki ne aka bamu mai zaman kansa wai shi amenity, komai akwai cikin ɗakin tamkar kana gida zaune.

Bayan Malama ta koma gida na zo na zauna kusa da Mama na kalle ta da murmushi a fuskata na saƙala hannuna cikin nata nace.

“Mama na! Ina sonki, Ina matuƙar sonki ina alfahari da ke Mama. Haƙiƙa duk mai haƙuri yana tare da Allah, ubangiji ya dubi maraicin mu ne yaga bamu da wata mafita shi ne ya turomana agaji ta hannun wannan baiwar tasa mai cike da albarka. Alhamdulillah! Allah shi ne abin godiya, Allah ya ji ƙan Baba da Rahma. Haƙiƙa kin kula dani kin bani tarbiyya da ke da Baba iya gwargwadon iyawarku na yi miki alƙawarin zan kare mutunci na a duk in da na shiga a faɗin duniya komai wuya komai tsanani.”

Murmushi ta sakar min itama tana mai gyaɗa kanta a hankali ta buɗe bakinta murya can ƙasan maƙoshi tace.

“Allah yayi muku albarka Bahiyya, yadda kuka ji ƙaina kuka tausayamin ina roƙon ubangiji ya baku rayuwa mai albarka ya baku mazaje na gari ko bayan bani a duniya”

Kallon ta na sake yi tare da jin nauyin kalmar ta ta ƙarshe a ƙirjina tamkar an ɗoramin falalen dutse nace.

“Mama kullum na tambaye ki sai kice zaki faɗamin Mama, dan Allah ki faɗamin mi yasa muka kasance mu huɗu kawai a duniyar mu? Ga shi mun rasa Baba duniyar mu ta sake canzawa zuwa mu uku kacal, shin mi yasa Mama ba zamu iya komawa ƙasar mu ba?”

Girgiza kanta tayi tare da haɗiye wani yawu mai ɗa ci a maƙogwaronta tace.

"Bahiyya ba ina ɓoye muku bane don wani abu, babu kalma ɗaya mai ɗaɗin saurare a cikin wannan mugun labari, domin idan har na sanar dake zaki yi ta damuwa ne a banza, zaki tsani dangin Mahaifin ki tsana ta har abada, sannan kuma zaki yarda cewa tsakanin 'ƴan uwa na jini babu amana. Ki bar wannan maganar Bahiyya”

Shiru tayi tare da juyamin baya alamar bata son ma zancen ganin haka yasa nima na kama baki na nayi shiru tare da tattara kaya na fita na kira Nuhaira nace ta dawo in da take.

***************

Tunda aka shiga da Mama na je na ɗoro alwala na fara jera nafila ina ta kai kuka na a wurin mai duka akan ya taimake mu yasa ayi lafiya a ƙare lafiya,yayinda Nuhaira da Malama suke girke a bakin ɗakin suna zaman jira.

Wannan likitan doctor Sam ba musulmi ba ne amma yayi mana abinda tsawon rayuwar mu ba zamu manta da shi ba, komai ake yana nan tare damu yana taimaka mana.

Ƙarfe biyu na rana aka fito da Mama daga ɗakin tiyata zuwa ɗakin hutu. Muna nam jugum jugum muna ta kallo aka yi mata duk abinda ya kamata ayi mata na bayan fitowa tiyata.

Mu kuma muna nan muna ta aikin kula da ita duk da cewa bata cikin hankalin ta yanzu.

Ku san Ƙarfe biyar na yamma ta farfaɗo wanda ni kai na da nake kusa da ita bana jin mi take cewa, muna cikin murnar kawai muka ga ta fara fisge numfashi ƙirjin ta na sama da ƙasa, jikin duk ya ɗau mazari, a gigice na nufi waje wurin nemo likita, yayin da Nuhaira ta shiga rera kuka mai ban tausayi........

*Oum Ameer*

💝 *BAHIYYA*💝

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

               *BY*

*AMINA IBRAHIM*

  *(OUM-AMIR)*

*BAHIYYA NOVEL ƊIN KUƊI NE KIBIYA 500 TA WANNAN ASUSUN 3132703269 FIRST BANK AMINA IBRAHIM SAI KI TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08068974831*

*FREE PAGE*

          *BABI NA GOMA SHA BIYU*

......... A Irin yadda muka ga jikin Mama ya rikice bamuyi tunanin likita zai kai ga shigowa ba ruhinta bai bar gangar jikin ta ba. amma cikin ikon Allah sai gashi a hankali bayan likitan sun shigo sunyi iya yinsu ta dawo normal.

Kulawa mai kyau Mama ta samu tun daga doctors har zuwa nurses da mu kanmu, Alhamdulillah! Aiki ya yi nasara domin Mama ta samu lafiya sosai tamkar ba ita ce a mawuyacin hali a kwanakin baya ba. Saida muka kwashe sati biyar masu kyau sannan aka bamu sallama da kuma lokacin follow - up a kai a kai domin gujewa matsala bayan an ɗora ta akan tsarin maganin da ya dace. Kuma doctor Sam ya tabbatar mana cewa daga yanzu har abada ya dawo likitan ta duk lokacin da taji wani sauyin yanayi a jikin ta zata iya zuwa gare shi.

Gida mai daɗi. Tunda muka koma nayi sallar zuhr bacci ya ɗauke ni sai bayan asr sosai na farka da wani irin tsoro, domin mafarkin dai kamar ko yaushe babu daɗi, wanda har ya zame min jinin jiki wanda a yanxu sai dai inyi addu'ar da manzon Allah (S. A. W) ya koyar da mu, in ci gaba da abubuwan gaba na.

Bayan kwana biyu.

      Zaune muke mu uku muna cin abinci a faranti ɗaya, ni, mama, Nuhaira. Mama ta kalle ni tace

“Bahiyya Malam Maharazu shiru, rashin samun sa a waya ya dame ni”

Cikin alhini nace.

“Wallahi kuwa mama. Abin da mamaki, ki duba duk tsawon lokacin da kika ɗauka a kwance har aka miki aikin nan ace har yau babu labarinsa abun akwai alamar tambaya, ni jiki na yana faɗamin ba lafiya ba”

Nuhaira ce tace.

“Wai Mama da ke da Baba kunce Baba Maharazu ɗan uwanmu, to mi yasa shi yake iya zuwa Nijar ɗin mu ace bamu iyawa?”

Girgiza kai mama tayi tace.

“Aminin babanku ne haƙƙun, tun suna yara suke abota har kasuwanci ya kawo su nan tare suka fara zuwa Nigeria, kuma tare suka kasance har mutuwa ta ɗauki babanku. Abokan taka ce ta haɗa su ba jini ba, saboda haka ba inda ƙaddarar Mahaifin ku ta shafe shi. Tun kafin ya auro ni yake xuwa nan, bayan mun aure ya dawo dani lokaci zuwa lokaci munkaje gida mu dawo, a lokacinda na haifi Ishaq yayanku kenan, Malamam yaga cewa ga ɗawainiya ta ƙaru ya kamata ace ya mallaki gidan kansa ya daina haya wanda ni kaina naga dacewar hakan domin ga sayen abinci ga kuɗin haya ga lalurar yaro ta ƙaru,daga haka sai muka yanke shawara cewa idan na tafi kai musu jariri, zai sayar da gonar guda biyu da ƙannen sa ke nomawa sannan a bashi nashi gadon Mahaifin su da ya bari. Tunda muka je kowa yake murnar zuwan mu kamar ko yaushe amma tunda yayi wa su Amadu zancen gona da kuɗin sa shikenan zance ya canza. Tun yana can ya so a siyar suka dage da lallai ya kamata ya koma wurin kasuwar sa su kuma idan suka sayar daga baya sai su haɗa komai su je da kansu su kai masa, tunda dai abin dole yana da jan lokaci, ni tunda naji sun fara mishi wannan hanya hanyar nace mishi ban yarda da su ba, amma abin ka da ɗan uwa yace min ai ba matsala, nayi sallama da iyayena da mahaifiyarsa kamar ko yaushe muka shirya muka dawo gida. Bayan dawowar mu saida akayi rabin shekara babu su Amadu babu dalilin su, tun babanku baya magana har ya fara tuntuɓa ta da zancen kai tsaye nace mishi ai saida nicce kada ka yarda dasu tun farko kace ba haka ba, ƙarshe muna nan Abu wasa wasa har aka shekare, daga nan ya yanke shawarar sake komawa yaji ina zance ya kwana, to tunda Malam ya sa ranar tafiyar nan ya kwanta wani irin mummunan ciwo wanda idan mutum ya kallesa ba zai sa ran zai ƙara kwana ba, mukayi ta yawon asibiti duk a banza, watarana sai nace mishi Malam ko dai zaka je Nijar ɗin ne daga can ka nemo magani ko Allah zai sa a dace. Sai ya girgiza kansa yace min shi yanzu ya bar zancen Nijar ɗin nan sai dai wani lokaci kuma, in faɗa muku cikin ikon Allah tunda yace ya janye tafiyar sa muka nemi ciwo muka rasa, abu kamar wasa. Muna nan kuma aka ɗauki lokaci ya sake saka ranar tafiya sai ga ciwo ya dawo kamar ba zai yi rai ba, to daga nan sai muka fara tsora ta, da kaina nace malam ka janye tafiyar nan har wani lokaci yace min ai ya bar zancen kuma shi ya ma cire rai da wannan tafiya, shima tun daga nan ciwo ya warke, haka haka tun bamu gasgata ba har muka yarda cewa akwai wani abu a ƙasa...”

Cikin tsananin firgice wa da ruɗewa nace.

“Mama karki ce min don Baba ya nemi haƙƙinsa ne Su Baba Amadu suka aikata mishi haka, kina nufin asiri suka mai kenan??”

Kuka take mai tsuma rai cikin raunatattar murya.

“Bahiyya wannan abun ba Babanku kaɗai suka yiwa ba, har da ni, domin shine silar da yasa har yau ban sake komawa tushe na ba, kuma ko yanzu ban isa nace zan tafi ba ni kaina, kuma abin da ya bamu tsoro, firgici da ban al'ajabi muka kasa warware shi har Mahaifinku ya bar duniya shine 'ƴan uwana da na Mahaifinku har yau babu wanda ya sake neman ina muke yau shekara ashirin da shida kenan rabon mu da gida, a wurin Malam maharazu kawai muke samun labarin su, a ta hannunsa ne Malam ya samu labarin rasuwar mahaifiyarsa, Nima a wurin shi na samu labarin rasuwar iyayena, da sauran Labaran dangi na daɗi ko akasinsa....”

Jikina sai ɓari yake ina wani irin kuka mai ban tausayi, cikin ruɗewa nace.

“Yanzu Mama akan abun duniya, suka rabaku da dangin ku?? Saboda abun duniya Mama! InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Kai duniya ina zaki damu,'ƴan uwanka uwa ɗaya uba ɗaya sune zasu aikata maka wannan mummunan aika aikar saboda wani ban zan abun duniya wanda dole watarana sai an barsa”

In banda kuka babu abinda Mama da Nuhaira suke, lallai tabbatas zancen Mama haka yake banga wani abun burgewa ba a cikin wannan labarin wanda har na koma ga Allah ba zan manta sa ba. Dafa kafaɗarta nayi nace a hankali nace.

“Lallai Mama da ciwo sosai a cikin rayuwar ki, wannan labarin da ban al'ajabi ya ke, Don bare yayi maka abu ba zai zama da ciwo sosai ba kamar ɗan uwanka, yanzu ta dalilin laifin babanmu shi ne ya shafe ki kema kika rasa dangin ki ba gaira ba dalili, kiyi haƙuri Mama, Wallahi Allah baya zalunci kuma baya yafe haƙƙin wani akan wani, kuma addu'ar wanda aka zalunta bata da wani shamaki tsakanin ta da ubangijin mu, na san cewa kun daɗe kuna addu'a akan wannan zaluncin da suka muku kuma muma daga yau zamu ɗora, matuƙar bamu da haƙƙin su suka yi mana wannan aika aikar to muna addu'a Allah ya bi mana haƙƙinmu a inda ba su da wani tsimi ba su da dabara”

Nuhaira ce tace.

“To Mama shi Yah Ishaq ɗin kenan ya samu zuwa Nijar ɗin kafin ya rasu??”

Gyaɗa kanta tayi tace.

“Eh! Tun zuwan da muka yi yana zanen goyo, bamu samu komawa ba har ya rasu”

Ajiyar zuciya na sauke ina ƙara jinjina girman wannan al'amari a raina na sake kallon Mama nace.

“Mama mutanen nan sun aikata kuskure, kuskure babba domin raba iyaye da ɗansu baban zunubi ne, saboda tsabar rashin imani Mama suka raba ki da duk dangin ki babu tausayar suyi tunani cewa ke fa mace ce, zuciyar ki ba zata iya jurewa ba”

Daga haka sautin kukan ta ya ƙaru sosai da ƙyar muka samu ni da Nuhaira muka rarrashe ta ta samu bawa zuciyar ta magana.

Daga haka kowa ya miƙe ya tafi wurin nasa yayin da zuciyoyinmu suka cika da rauni da damuwa.

Da dare cikin gabatar da sallar Isha, Ikram ta shigo tana mai ƙwala kiran sunana, Nuhaira ce ta tare ta tana tambayarta ya a kayi, Ina ji tace wai Maman su ce take Kirana cewa da Malama. Bayan na idar naje na sanar wa Mama na tafi.

Ina shi ga muka gaisa da Ita na samu wuri na zauna tare da rungume autar Fahaira nace.

"Gani Malama”

Tattaro nutsuwar ta tayi ta Kalleni da kyau tace.

" Bahiyya kyaun alƙawari cikawa, kuma da ilminki yadda kuka yarjejeniya da Hajiyah Hanifah ya kamata ki cika, ta kira doctor Sam ya kirani tace tana buƙatar zuwa UK ganin likita domin jikin ta ya matsa mata kuma tare take so ku wuce kamar yadda kuka alƙawaltama juna”

Gyaɗa kai nayi cikin gamsuwa da maganar ta nace.

"Haka ne malama, kyaun alƙawari cikawa. Daman can ba mantawa nayi ba, taya zan manta Malama? Matar da ta dalilin ta ne muka tsinci kanmu da sake darawa a rayuwa, ko kaɗan bana dana sani, wasu ma da ake ɗauka aikatau tun daga garin su zuwa wata uwa duniya na tsawon shekaru suyi ta wahala dare da rana ballanta kai da aikin bai taka kara ya karya ba kuma shekara ɗaya kacal. Kawai dai Mama ta nike tunani har yanzu ban iya faɗamata ba, kullum cikin zullumi nike.....”

Cike da ƙwarin guiwa tace.

“No kar ki damu in sha Allah zan yi mata bayani kuma zata fahimta da yardar Allah, ke dai abinda nike so da ke shine ki tsaya matsayin ki da Allah ya ajiye ki, ki ki ye yi kanki ki kuma  zama mai wadatar zuci da godiya da duk abinda aka miki, ki riƙe ibada Bahiyya, mutanen nan sai a hankali, wasu wallahi ko ibada bata dame su ba, saboda haka kada kije ki samu canjin wuri ki ce zaki canja ɗabi'arki”

Gyaɗa kai na nayi na ce.

"in sha Allah zaki same ni mai kiyaye. Roƙona shine kuci gaba da kulamin da Mama da Nuhaira, sannan wannan kuɗin ku yanke shawara a tsakanin ku wace kasuwa za'a yi da su, ni bani da ja da hakan, Allah ya yi mana jagora”

Daga haka na miƙe tare da yi mata sai da safe na shige gida.

Bayan kwana biyu da maganar mu da malama, sai ga mama da kanta ta kirani ɗaki tace min.

“Bahiyya naji komai daga bakin Malama, ba abinda zance sai dai ince Allah ya kiyaye ki a duk in da kike, amma ba don abun yayi min daɗi a rai ba, to amma wani lokacin muna kan so abu ya zama ba alheri ba ne garemu, wani lokacin kuma sai muƙi abu ya zama shine mafi alheri a gare mu. Tace min gobe ne zaku tafi”

Cikin faɗuwar gaba na ce.

“Gobe kuma Mama??”

“Eh, tace matar tace ba tada lafiya kuma likitan na ta a can yake”

Cike da Murmushi Nuhaira ta kalle ni tace.

“Aunty Bahiyya kin ji daɗin ki ke kam, kina baƙin cikin baki je Nijar ba gashi yau Allah yayi zaki je garin da yaci uban Nijar ɗin, wani hanin ga Allah bai wa”

Ɗan guntun murmushi na saki tare da girgiza kai na nace.

“Nuhaira ba zan biye miki ba, domin ke har yanzu tunani bai gama shigar ki, in ba shi taya zaki haɗa tafiyar zumunci ta jini da wannan tafiyar da babu haɗin iya babu na Baba...”

Tare numfashi na tayi tace.

“Ni dai ba ruwa na, UK tafi Nijar, kuma dan Allah ki yo min tsaraba Aunty Bahiyya ki sawomin kayan kanti irin riga da wandon nan da naga matar nan ta saka ranar, wallahi ni dai ta burgeni ainun”

Ni dai jinta kawai nike domin can ƙasan zuciyata wani abu ni ke ji yana yimin ba daidai ba.

Washe gari ko har ƙofar gida wata haɗaɗɗar mota tazo tayi parking wanda kallo ɗaya zaka yi mata ka tabbatar cewa ba daga ƙaramin gida ta fito ba. Tsayuwar Motar da zatayi sanadin canja alƙiblar tafiya ta a idon 'ƴan unguwar mu zuwa sayar da jikina domin karuwanci na biyawa Mama na kuɗin aikin lalurar ta bayan sun san bamu da wannan kuɗin bamu da dalilin su.

Kuka na ke sosai tare da riƙiƙƙe Mama tamkar raina zai fita, yayin da Malama da sauran' ƴan uwa da masu da zuciya ɗaya da masu yi don munafurci suka tsaya suna ta bamu baki, suna neman jin tushen maganar ina zanje. Wanda har suka ƙaraci gulmar su suka gama babu wanda yace musu ga inda zani.

Har na shiga motar sai kuma na fito da gudu na zo jikin mama na ƙara fashewa da kuka ina faɗin.

“Mama dan Allah dan girman Allah Mama ki tsare shan maganin ki a kan lokaci akan kuma ƙa'ida, duk sanda kika ji matsala Nuhaira ta rakaki asibiti mama, kuma ki yimin alƙawarin cewa ba zaki sake shiga wata damuwa ba har abada, ko da ace bamu da kowa mu uku Mama mun wadaci kanmu, a haka muna farin ciki sosai, ki kula da Nuhaira Mama.....”

Daga nan kuma na juyo ga Nuhaira na rungume ta nace.

“Ke ƙanwata marar jin magana da baccin safen da bana so dan Allah ki kula da kanki sosai, ki kula da Mama kinji ko, nayi miki alƙawarin zan saya miki duk abinda kika ce kina so, kamar gobe ne zaku ga na dawo, in sha Allahu”

Daga haka na wuce direct na shige motar ina ta ɗaga musu hannu tamkar wata ƙaramar yarinya har suka ɓacewa gani na.

Bayan mun fito kan Titi malama ta hau ƙara yi min nasiha saboda tare muke ita zata rakani zuwa gidan Hanifah domin su ƙara tabbatarwa cewa a hannu nagari nike.

Nan na roƙe ta cewa dan Allah mu fara bi ta gidan Maman Khadijat in ƙara yi mata godiya kafin na tafi, sai gashi ko munyi nasarar zuwa gidan amma bata nan kamar yadda masu gadi suka shaida mana. Daga nan drivern ya fito ya juya akalar mota zuwa gidan Hanifah.

Tun daga farkon unguwar na fara kalle Kalle domin wannan ba kamar sauran unguwanni ba ce, duk yadda nike ganin unguwar su Maman Khadijat da mugun kyau wannan unguwar ta cuna mata, tamkar ba'a Najeriya ka ke ba, Gate ne gasu nan kala kala, idan mun wuce wannan mu kai ga wannan, ga kaki nan kala da kala duk a matsayin masu gadi.

Ban ƙara tsinkewa da al'amarin ba sai da muka shiga cikin tamfatsetsen gidan kacokam na ƙara tabbatarwa kai na da cewa Lallai yau ni Bahiyya zan shiga wata duniya ta daban.

Kallon malama nayi kamar yadda itama naga take kallo na tare da yimin alama cewa mu fita.

Jiki na take ya hau karkarwa tamkar ana kiɗamin mazari ta dalilin tozali da nayi da wasu shirga shirgan samudawa waɗanda babu alamun wasa a tare da su sun ƙaƙƙame tamkar wasu sandararrun gunku na................

   

                             *OUM AMEER*

💝 *BAHIYYA*💝

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

               *BY*

*AMINA IBRAHIM*

  *(OUM-AMIR)*

*BAHIYYA NOVEL ƊIN KUƊI NE KIBIYA 500 TA WANNAN ASUSUN 3132703269 FIRST BANK AMINA IBRAHIM SAI KI TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08068974831*

*FREE PAGE*

     *BABI NA GOMA SHA UKU*

........... Wani ƙayataccen falour ne na alfarma akayi mana masauki muka zauna, ni dai ko a nan a darare ni ke zaune, Malama ce ma naga ta saki jiki sai aikin kalle kalle take.

Jiga jigan hotuna ne kala da kala ita dai Matar gidan kallo daya nayi mata a wani hoton na gane ta, sai dai hotunan maza ne biyu na gani ba zance ga mai gidan ba.

Bayan malama ta gama ƙare musu kallo ta kalle ni cikin mamaki tace.

“Bahiyyah kin san nan ko gidan waye?”

Girgiza kai na kawai nayi alamar ban sani ba.

Gyaɗa kai tayi tana mai ƙara jinjina girman al'amarin tace.

“Daman farkon tozali na da ita raina ya bani cewa kamar ita sai dai girma da matsayi irin wanda take da shi shine ya hana zuciya ta amincewa da cewa ita ce, to ashe ita ɗin ce. Babbar 'ƴar kasuwa ce, ita ce mammallakiyar Ɗan-Ali Decor and Event wanda ake ji da shi a faɗin ƙasar nan wanda bata jima da sake buɗe reshenta a United Arab Emirate ba,Mahaifinta shahararre ne kuma sananne yanzu haka Ambassador ne a ƙasar Cairo , mijinta kuma Umar Farooq mai gishiri shima shahararre ne kuma sannan ne a faɗin waje da kewaye Bahiyya,shi jika ne ɗaya tilo ga Madinat shahararriyar mai kamfanin Almadinah textile and more da ke da rassa daban daban a faɗin ƙasar nan da kewaye....”

Ajiyar Zuciya ta sauke sannan ta kalle ni jiki sanyaye tace.

“Ban san wace kalar ƙaddarar ce ta haɗaku ba Bahiyya,Don wannan haɗuwar taku da ƙaddara zan kira ta, na san ba don tana neman komai daga gare ki ba sai dai don tayi niyyar ta taimaka miki kawai because you have nothing to pay her in return, banga abinda zaki bata ba a duniyar nan domin tafi ƙarfin ki ta ko ina, in ma masu aiki ta ke nema nasan dole sai masu kwalin karatu mai zurfi don ko a gidan hajiya Rasi'at da bata kai ta ba suma haka tsarin su ya ke. Allah ne kaɗai masanin abinda yake zuciyarta akan neman ki da tayi ɗin nan har na tsawon shekara ɗaya, abinda zan faɗa miki na ƙarshe shi ne Bahiyyah ki tsare mutuncin ki komai wuya komai tsanani, ki yi musu biyayya daidai yadda zaki iya.”

Gyaɗa kaina nayi tare da jinjina girman lamarin a kaina nace.

"In sha Allah Malama zan kiyaye”

Zaman mu a nan munfi 2hours, bayan an cika mu da kayan ciye ciye abinci kala da kala muka ci muka ƙoshi sannan daga baya sai ga wata matashiyar mata da hausarta bata fita sosai ta zo tace mu tashi mu biyo ta. Haka muka yita bin ta mu shiga nan mu wuce nan ko ina gwanin burgewa tamkar duniyar da ba'a mutuwa a cikin ta, sai daga ƙarshe muka isa wani parlour na alfarma mai wani sanyi da ƙamshin rahama mai kwantar da zuciya.

Ko a nan ma sai da muka shafe kusan mintuna talatin sannan sai gata ta iso cikin takun ta na ƙasaita da girma na manyan mata ta samu wuri cikin ɗaya daga cikinsu cikin lumtsatstsun kujerunta ta hakimce.

Tuni ni da Malama muka shiga miƙa gaisuwa ni kuma a zuciyata ina ta mamakin yadda malama ta wani baje a ƙasa tana faman kwasar gaisuwa yayinda ni na san cewa itace ya kamata ace ta gaidata domin ko bata haife ta ba saura kiris.

Murmushi tayi sannan ta kalli Malama tace.

“Na gode”

Murmushin itama Malama tayi tace.

“Ba komai Hajiya, Daman cewa nayi bari na rakota domin in ƙara tabbatar da cewa a hannu na gari zata faɗo, Allah ubangiji ya baki lafiya ya kuma zaunar da ku lafiya”

Murmushi Hanifah ta sake yi hannun ta riƙe da wayar ta tana latsawa ba tare da ta kalle ta ba tace.

“Kar ki damu In sha Allah babu wata damuwa”

“To nayi murna da jin haka, ni zan koma sai Allah ya sake haɗamu da alheri”

Daga haka Malama ta miƙe nima na yunƙura da nufin miƙewa tayi saurin dakatar da ni tace in zauna ba sai na rakata ba, amma fir na ƙi saurarenta Sai da na biyo ta har mota, kaya ne ake ta tula mata niƙi niƙi Wai gashi nan in ji Hajiya, Malama kuma daga gefe sai faman ƙara jaddada min take cewa in bi matar nan sau da ƙafa bata da wata matsala, a raina har abin ya soma bani Mamaki ni dai toh kawai nike kira mata har ta shige mota ta wuce. Hawayen da suka silalo min na goge tare da yin sauri na bi bayan matar nan da ta ɗazu domin ba lallai ne na sake maida kaina wurin ba.

Wani irin tsoro ne ya dirar min a zuciya ta wanda ban san dalilin hakan ba, ko don yanzu ya rage parlourn daga ni sai ita ne Oho! Tunda na zauna bata sake kallon in da nike ba tamkar Allah bai yi ruwana a wurin ba haka tayi min wanda sam banji daɗin hakan ba, ko ba komai atleast ya kamata tace min wani abu don ta nuna tasan cewa ina wurin kai ko kallona tayi ni hakan ya wadatar, amma tayi da ni kashi duk ɗaya wanda maman Khadijat baya daga cikin halayyar ta, shiyasa ni ke sonta.

Ba abin da nike sai tubka da warwara ni kaɗai a cikin zuciya ta, daga ƙarshe na ɓige da tunanin Mama da Nuhaira wanda ba san lokacin da Hawaye suka shiga kwaranya daga cikin idanuwa na ba. Bayan na gama hawayena na tsayar da su don kaina, sai na sake ɗago kaina da nufin sake kallon wannan ishashshiyar matar sai dai wurin wayam ba kowa ban san lokacin da ma ta tashi tayi tafiyar ta ba, wasu sabbin hawaye ne suka sake zubomin raina ya hau wani ƙuna kamar in tashi in tafiya ta gida. Ina nan na zuba ma sarautar Allah ido sai ga wannan matar ta ɗazu ta sake dawowa ta kalle ni da sakin fuska tace.

"Oya ta shi ki biyo ni”

Ba musu na tashi na bita tamkar wasu akala da raƙumi har muka kai wata killatattar ƙofa haka duk a cikin rufi ɗaya. Shiga tayi nima nabi bayan ta.

Parlour ne mai kyau wanda ke ɗauke da set ɗin cushion ash and black, komai na parlourn haka kalar take komai an jerashi a tsari. Baki na saki kawai ina bin ko ina da kallo kamar wata wawiya.....

“Nan shi ne in da zaki zauna...”

Daga haka kuma ta jani muka shiga bedroom wanda ko toilet ɗin kaɗai abin kallo ne, muka dawo ta sake nuna min wai inda kitchen yake duk a cikin wannan ɗan madaidaicin part ɗin, komai yayi kyau ba ƙarya. Bayan ta gama nuna min ta jani toilet ta shiga koyamin yadda zan yi amfani da komai na toilet ɗin bayan mun gama  muka koma kitchen nan ma ta nuna min, muka dawo Parlour ta nuna yadda a kunna TV da AC da sauran su. Daga haka tace min zata je ta dawo.

Kan kujera na zauna tare da ƙurawa TV ido ina kallo, a raina ina mamaki wai yau nice a nan wai a gaban wannan tangamemen TV ace wai ƙarƙashin iko na yake. Allah mai yadda ya so kenan.

Nan na ƙaraci zamana daga ƙarshe da na duba agogon da ke manne a bangon parlourn nan na gane cewa har lokacin sallar Asr yayi gashi ko zuhr ban yi ba. Da sauri na wuce toilet ɗin daman can na saba amfani da irin su a irin gidajen su Maman Khadijat, so sai ban sha wata wahala ba

nayi alwala na zo na tayar da Sallah na gabatar da salloli na. Bayan na gama na sake komawa parlourn naci gaba da kallo har magrib tayi.

Bayan na idar da sallahr magrib ne sai matar dai ta ɗazu ta sake dawowa hannayenta ɗauke da warmers ɗin abinci sai wata matar a bayan ta sanye da kalar wani uniform a jikin ta ta ajiye kayan hannun ta ta fice.

Murmushi na sakar mata kamar yadda itama naga tayi min, tace min sannu. Nima sannun na mayar mata tare da kafe ta da ido ina jira in ji mi kuma zata faɗa mun.

“Wannan abincin Dinner ɗin ki ne, wannan kuma kayan amfani ne yanzu zan nuna miki yadda zaki yi amfani ko wane abu a nan”

Ni dai babu abinda nike sai binta da kallo, kaya ne tundaga na sanyawa har zuwa kayan gyaran jiki su mayukka da na gyara gashi da takalmi da sauran su. Komai sai ta tayi min bayanin shi ɗaya bayan ɗaya daga ƙarshe tace min duk abinda ban gane ba na riƙa tambayar ta don kada a samu matsala,ni ko a raina na tambayi kai na nace matsala? Wace irin matsala to? Ganin bani da amsar ta yasa na sake mayar da hankali na ga kallon ta yayin da taci gaba da yi min bayani. Komai da aka kawo min mai kyau ne, kayan dai ne nagan su wasu iri domin ni ba kayan da sukayi daidai da tsari na bane, gaba ɗaya kayan daga riga da wando sai riga da skirt, sai kuma Abayas sun kai shida, to suka ɗai ne nikejin a raina cewa zan iya sanyawa amma su kam waɗancan haram shan giya a gidan Malam, mamaki na babu atamfa ko kala ɗaya a ciki.

Da dare ma haka na kwanta a kan gadon tare da janyo bargo na rufe jikina saboda sanyin ACn da yake ratsani.

Sati ɗaya na kwashe a gidan ba tare da na sake sanya Hajiya Hanifah a ido na ba, wannan matar da a yanzu na saba da ita Nafisat itace kaɗai ni ke gani, ta dage sosai wurin koyar da ni abubuwa waɗanda tuni nayi nisa sosai a iya wasu abubuwan wasu kuma sai dai a hankali, ni kaina idan na kalli madubi na kan yarda da cewa jiki na ya canza sosai ba kamar yadda na zo ba, tsabar hutu da cin kayan daɗi iri iri,ko gashin kai na ban san cewa ina da dogon gashi sosai mai santsi ba sai yanzu da ya ke shan gyara a wurin Aunty Nafisat domin haka tace in riƙa kiranta.

A kwana na takwas ne ina zaune, bayan na gama sallar azahar ina tunanin su Mama a raina sai ga Aunty Nafisat ta shigo tacemin in shiryo mu tafi madam tana nemana. Lokaci guda annurin fuskata ya ɓace tare da jin wani irin faɗuwar gaba take na hau karanto addu'o'i. Daman nayi wanka already, wata Abaya ce maroon colour na ɗauko na saka tare da ɗaura ɗan kwalin na sake zura hijabi na a kai na cimma Aunty Nafisat Parlour muka tafi.

Wani parlourn ne na daban mai faɗi gaske ta nuna min yayin da ta juya daga bakin ƙofar ta koma abinta. Sai da na tsaya na gama sai ta kaina sannan na shiga ɗauke da sallama a baki na.

Ganin ta yau tare da wani wanda da alama mijinta ne yasa na tsaya tun daga nesa na tsuguna a ƙasa gaba na sai tsananta faɗuwa yake tamkar wadda za'a yanka naman jikin ta.

Na jima tsugune a wurin yayin da sukayi tamkar basu ganni ba suna ta maganar su a ƙasa ƙasa. Sai daga baya ta kalle shi tace.

“Farooq she's our surrogate...”

Sai kuma ta kalle ni tace.

"Hey! Look here. Kallo nan, tashi tsaye ya ganki”

Miƙewa nayi tsaye tare da kallon in da yake zaune kamar yadda ta umurce ni, sai dai daga ƙasƙantaccen kallon da naga ya fara bi na da shi ne yasa naji jikina yayi sanyi, kallo ne wanda har in koma ga Allah ba zan manta da shi ba duk da cewa ban san manufarsa ba. Wanda har cikin raina na ji na muzanta na kuma kunyata.

Cike da izgili ya zare ido ya kalli Hanifah yace.

“What! Oh no! It can't be possible Hanifah.Look at her Fa, wannan tsuntsuwar mi zata iya? daga ganin wannan ma abinci bai wadaci jikin ta ba, saboda haka she can't carry my baby gaskiya....”

Da sauri Hanifah tace..............

      

                         *OUM AMEER*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JDbgcC7yQyC5NhQw9Q1jFl💝 *BAHIYYA*💝

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

               *BY*

*AMINA IBRAHIM*

  *(OUM-AMIR)*

*BAHIYYA NOVEL ƊIN KUƊI NE KIBIYA 500 TA WANNAN ASUSUN 3132703269 FIRST BANK AMINA IBRAHIM SAI KI TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08068974831*

*FREE PAGE*

     *BABI NA GOMA SHA HUƊU*

.......... “She can do it Farooq, I have already started preparing her, da shawarar doctor Nicholas ni ke amfani, he planned all the necessary nutrients for her so that she and our baby will be in good condition. Beside we are gonna stay together with her, So is our duty to take good care of her”

Girgiza kan shi yayi tare da kallon Hanifah yace.

"Hanifah! Hanifah har yanzu kina ganin cewa akan daidai kike?”

With full confidence tace.

“I'm 100% sure love, in sha Allah everything will go smoothly beyond your expectations”

Taɓe baki yayi tare da sake kallo na a karo na biyu, tun daga ƙasa na har sama sannan yace.

“While tunda har kince hakan yayi miki is ok. You can ask her to leave”

“Ki tafi”

Abinda na ji kenan ta faɗa, hakan yasa na juya na fice zuciya ta na wani tuƙuƙin baƙin ciki. Wai shin mi masu kuɗi suka ɗauki kan su ne a duniyar nan? ba fa saya ta suka yi ba ballantana suce yadda suka ga dama za su yi dani, ji wani kallon wulaƙancin da ya ke min tamkar an tilasta shi dole sai ya kalle ni banza a banza kawai, idan kuna taƙamar kuɗi ai Allah ba ruwan shi da wannan da zukata yake aiki ba jiki ba ko wani abin mutum mtsww! Wai harda Kirana Tsuntsuwa tsabar raina halittar Allah ko miye marabar matarsa da ni Oho! Don itama naga ba wani jikin a zo a gani ne da ita ba. ita kuma wannan matar bana tunanin ma cewa ta san suna na domin ko da wasa ban taɓa jin ta kira ni ba tsabar wulakanci, ni sai a yau nayi baƙin cikin rashin jin yaren nasara da bana ji kuma bana iya mayarwa, ɗan abinda nikeji da wanda nike iya mayarwa ɗin banji sunyi ko ɗaya ba ballantana in ce na fahimta domin da ina ji nasan tabbas zan fahimci ina suka dosa miye suke magana a kai. Kuma ai ban tilasta ta ba itace ta zaɓeni idan ban musu ba su mayar dani gidan Mama na mana. Tsaki na ja sai kuma a raina nace, ko ma dai miye ni dai buƙatata ta biya tunda har Mama ta samu lafiya ai shi kenan. Maimakon in ganni na ɓilla ƙofa ta kawai gani na nayi a wani wurin na daban, cikin ruɗewa na fara zare ido na rasa ina zan nufa, ga shegun mutanen har masu aiki wai turanci suke yi tsabar kinibibi da sanabe, domin duk wacce naga zasu yi magana da Aunty Nafisat da turanci suke yi so ba ni da halin in tambayi wani. Ina nan tsaye kamar an dasa Icce sai Aunty Nafisat na gani tana faɗin

“Bahiyya ina zaki je ne? Kin sani sai faman neman ki ni ke”

Dariya nayi kamar wata sakarya nace.

“Wallahi Aunty Nafisat manta hanyar nayi, kawai sai na tsinci kaina a nan”

“Eyyah sorry. To yanxu biyoni muje”

Babban kitchen ne ta jani wanda tunda ni ke ban taɓa ganin kitchen irin shi ba,komai an shirya shi bisa tsari gwanin burgewa. waigowa tayi ta kalle ni tace.

“Mi kike so ki ci yanzu?”

Cikin Mamaki na ce.

“Ai ban jima da cin abinci ba ko kin manta”

Girgiza kai tayi tace.

“Ban manta ba, Hajiya ce tace ki riƙa cin abinci time to time ba dole sai kina jin yunwa ba”

Cikin rashin fahimtar zancen nata nace.

“Bana jin yunwa, amma ki bani madarar nan mai daɗi irin ta ranar sannan ki haɗamin da naman kaza dafaffe”

"OK to muje in rakaki kada ki ƙara manta hanyar, Yanxu zan kawo miki”

************

HANIFAH

Bayan fitar Bahiyya zaunawa tayi kan cinyar sa tasa hannu tana yamutsa sumar kansa da ta sha gyara sosai tana murmushi tace.

“Ba lallai suna samun abinci mai gina jiki yadda ya kamata ba, but mu a nan zamu iya bata, Nafisat is taking good care of her, sannan Kuma wani gefen halittar jikin ta ne haka, kada ka damu. Gobe in sha Allah we will go to the hospital together for possible investigation, Idan an gama screening ɗinta Sai mu wuce kawai, you will become a father soon as you wish”

Kallonta yayi yace.

“Hanifah ya zamuyi da su Daddy ya zamuyi da Madinah?”

Murmushi tayi tace.

“Wannan duk mai sauƙi ne, We are going to surprised them, daman can 2years back Momma ta taɓa tambaya na cewa har yanzu bata samu jika ba, nace mata sai time yayi, to since then bata sake tambayana ba kuma, so we will plan to hide it for them, it will serve as a secret, after she put to bed Sai mu kira su mu faɗa musu cewa na haihu, ita kuma sai ta tafiyar ta, har Grand Ma Itama.”

Gyaɗa kan shi yayi tare da ɗaga ta daga kan thigh ɗinsa ya miƙe tsaye yace.

"It's ok. I have meeting tomorrow morning, so zan je zan tattauna da Mahi...”

Wani faɗuwar gaba taji wanda bata san dalili ba saboda kawai taji ya kira sunan Mahi.

Da sauri tace.

" Wait.. Wait..!”

Tsayawa yayi yace.

"What?”

Kai tsaye tace.

“Please let it be secret, don't tell him anything pls”

Ɗan jim yayi kaɗan sai kuma ya Gyaɗa kai yace.

“Ok”

Tana ganin ficewar sa ta koma daɓas kan kujera ta zauna tare da sauke wani nannauyan ajiyan zuciya tana girgiza kai a ranta tana faɗin. I hate you Mahi! I so much hate you with passion, you are the cause of all my stress, we have plan and build our life simple and understandable with so much love and care, duk abinda na faɗawa mijina yarda yake bai taɓa fushi dani ba, but daga lokacin da ya fara zama da kai sai ka shiga canja sa a hankali ya fara dawowa mijin bahaushiya, ya fara yi min magana cikin ihu da nuna shine a gaba ni bani wani right, I promise you Mahi Sai na ɗaukeshi baki ɗaya daga ƙasar nan ka daina ganinsa.

Sai kuma ta ja guntun tsaki tana ƙara tuna yadda yanzu Farooq ya canja baki ɗaya, komai na sa ya dawo na ganin laifi, gashi yanzu two-four bai da wani zance sai na haihuwa. Taya zata iya yafewa Mahi Madinat, a yanzu ta gama yarda a duniya bata da wasu maƙiyanda suka wuce mutum biyu ɗin nan.

*************

BAHIYYA

Zaune nake na baje ina kwasar wainar ƙwai da shayi mai bala'in kauri ga dankalin turawa daban ga farfesun kayan ciki sai tashin ƙamshi yake,a gaskiya ina jin daɗin rayuwar da nike ciki a yanzu, amma da zaran na tuna da kalar masu gidan sai in ji komai ya fita kaina kuma.

Sallama Aunty Nafisat tayi ta shigo ciki tare da sakar min murmushi tace.

“Sannu Bahiyya, idan kika gama ki shirya zaku fita da Hajiya...”

Cikin damuwa nace.

"Ina zamu je kuma”

Aunty Nafisat tace

“I don't know”

Nace

" To tare da ke zamu tafi”

Girgiza kanta tayi tace.

“A'a, ki yi ki shirya she's waiting for you, don't waste her time”

Cikin zaƙuwa nace.

“Aunty Nafisat dan Allah ko zaki koyamin turanci nima in riƙa ji ina mayarwa kamar ku?”

Dariya tayi tace.

" Kai Bahiyya, kina nufin baki iya turanci ba? A ina kika makaranta?”

Taɓe baki nayi nace.

“A garin mu na da Zamfara, government ce nayi kuma kin san karatun can sai a hankali ba kamar na nan ba ne, sannan gashi na shiga Ss3 ba daɗewa muka dawo nan,nan ɗin kuma ban ci gaba ba”

“OK! Idan mun samu time zan riƙa koyar da ke ta baki da kuma rubutu”

Cikin jindadi maganar ta nayi mata godiya sannan ta juya ta tafi. Ina jin daɗin Aunty Nafisat a gidan nan, ban san matsayin ta ba amma tana da kirki sosai.

Miƙewa nayi domin abincin gaba ɗaya ji nayi ya fitar min a kai, amma kuma sai da naci naman tukun sannan na tashi, domin ni a gaskiya ina son nama ba wasa.

Wanka nayi shaf-shaf na fito na mulke jikina da mayuka na sababbi sannan naje gun kayana na buɗe na saka sabbin undies cikin waɗanda aka kawo min na zaɓo wata Abaya onion color na saka sannan na zuba black hijab ɗina a kai na sanya black shoe na fito.

Da Aunty Nafisat naci karo ta yi min murmushi ta juya na bita har bakin mota,ta buɗe na shiga sannan ta koma, wanda a raina na rasa gane wannan kulawar ko ta miye domin abin har mamaki yake bani. Ko a motar nafi minti talatin da ni da direba muna zaune sannan ta ga dama ta fito.

Tana shigowa na kalle ta kaɗan cikin tsoro tsoro nace.

"Ina kwana”

Ba tare da ta ko kalli in da nake ba tace.

" Lafiya”

Daga haka ta fitar da wayar ta ta fara latsawa cikin harshen turanci na ji tayi wa direban magana shi kuma na ji yace OK Ma.

Tsaki naja cikin raina nace shegu kawai idan na koyi turancin ai sai inga tsiyar ƙarya duk in da ta kwana.

Duk da ba'a faɗamin ba na gane cewa asibiti ce. Asibiti? Mi kuma zamuyi a asibiti? Tambayar da na yiwa kaina kenan wanda nasan cewa bani da amsar ta sai dai in zuba na mujiyata in yi kallo.

Bayan munyi tafiya naga mun shiga wani babban wuri mai girma gashi ya sha kyau kamar ba asibiti ba. Wani office muka shiga wanda naga wani likita zaune ya tsuke cikin suit baƙa mai blue ɗin necktie.

Da sauri ya miƙe suka fara gaisuwa su biyu bayan sun gama ya zauna tare da kallona yana murmushi yacemin.

“Welcome, please have a seat”

Murmushi nayi masa kamar yadda ya yi min na zauna akan kujerar da naga ya na nunamin.

Ba wata doguwar magana sukayi ba sai naga ya miƙe yace in biyo sa, ba musu na tashi na bi shi, zuciya ta sai bugawa take akan tsoro.

Jinina aka fara ɗiba, sannan aka kaini wani ɗaki ana ta min wasu abubuwa na gwaji kamar mai wata rashin lafiya, tambayoyi ne suke cizon raina bani da kuma wanda zan tambaya, domin duk basa jin Hausa. Mun jima sosai a asibitin sannan daga bisani na fito ni ka ɗai likitan ya rakoni har bakin mota, sai da na shiga na zauna sannan yace min.

“Sai Anjima Beautiful”

Ji nayi kamar na kafa masa mari ɗan iskan, wai daman yana jin Hausa amma yayi kamar baya ji, tsaki naja tare da juya fuskata nayi masa banza.

Daga haka ya rufe motar direban yaja muka tafi.

Bayan mun koma gida abun still yana raina, Ina ganin Aunty Nafisat nace.

"Aunty Nafisat mi yasa ta kaini asibiti hala?”

Cikin mamaki tace.

" Miya faru ?”

Nan na gaya mata duk abinda aka min na gwaje-gwaje da kuma Jinina da aka ɗiba.

Tace min ba komai nasan harakar masu kudin nan sunfi son komai suyi shi akan ƙa'ida.

Daga haka na wuce ciki na yi wanka nayi sallah sannan na ci abinci na zauna aikin kallo, domin shi kaɗai ne aikina a yanzu, daga ci sai kwanciya sai kallo sai Sallah.

Washe gari ma haka akayi, Ina zaune tace in shirya zamu fita, biye nike ni dai aka kaini wurin yin passport na shirye shiryen tafiyarmu, tafiyar da ban san dalilin ta ba, ko da yake renon cikin zan tayata dole su yi min gwaji kada ace ina ɗauke da wata cutar da zan iya shafa mata ita da ɗanta.

Bayan mun gama wani babban shopping mall muka tafi, a can na tarar da Aunty Nafisat mamaki duk ya gama kamani. Dariya tayi tacemin muje in zaɓi duk abinda nike so a nan. Ƙarshe dai ita ce ta shiga zaɓar min domin ni ban san komai ba, ganin ban taɓa saka wancan kayan ba yasa ta ƙara jibgamin Abayas masu uban yawa, da kayan shafe shafe muka koma gida.

A yanzu kam na saba sosai da Aunty Nafisat domin ina zagewa muyi ta fira, yawancin firar kuma duk akan turancin ne akan na dage dole sai ta koyamin ni kuma ko da bala'i na ƙuduri sai na iya.

Muna cikin firar mu naji an kira ta a waya ta ɗauka cikin ladabi tana magana daga Ƙarshe ta yanke bayan sun gama.

Kallona tayi tace.

“Bahiyya muje na ta yaki ki shirya kayan ki gobe zaku tafi”

Murya a sanyaye nace.

"Gobe kuma? To da ke zamu tafi ko Aunty Nafisat?”

Girgiza kanta tayi tace.

“A'a.”

Daga haka ta wuce na bi bayanta zuwa ɗaki na.

Trolley biyu tayimin babba da ƙarama sai wata jakar handbag da muka siyo ranar wadda sai dai na riƙe don passion domin ban san mi zan saka a ciki ba.

Muna nan tare da ita har lokacin tafiyar ta gida yayi na rakota har bakin motar ta har da guntun hawaye na duk da nasan cewa gobe da ƙila kafin mu tafi da wuri zata zo amma ina jin kewar ta sosai a ciki raina.

Da dare bayan na kwanta, bacci kasa ɗaukata yayi, tunanin Mama ne kawai a raina da kuma Nuhaira, sai yanzu naji takaici domin ba riƙe numbern Mama ba da kuma ta Malama sannan banyi azancin rubutawa na riƙe ba, sai yanzu na gane cewa nayi shirme babba, taya zan yi shekara ba tare da jin muryar Mama ba? Ga matar nan er renin hankali, ban gama damar ta balle na tambaye ta. Yanzu dai idan muka tafi sai inga wa kuma zata samu wanda zai riƙa yi mata magana da ni tunda bata so tana magana dani, wanda ban san dalilin hakan ba.

Washe gari ma da na farka, sukuku na tashi tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki.

Ina cikin shiryawa sai ga Aunty Nafisat ta shigo da murna naje na rungume ta.

Nan muka yi ta fira ta sai kuma ta tashi taje kitchen na bi bayan ta, ta gama shirya komai taje na jira ta, taje ta shirya musu table sannan ta dawo ni a nan ma nayi breakfast ɗin nawa. Sannan naje na shirya aka fitar da kayana zuwa mota.

Ƙiri Ƙiri suka hanani saka hijab Wai Sai dai in yi rolling da gyalen Abayar dole na tunda bani da wata mafita nayi.

Bansan cewa da ɗan renin hankalin mijinta zamu tafi ba sai da muka haɗu a filin jirgin. Ina ganin sa na ɗauke kai na kamar ban gansa, har ita matar yau bata samu gaisuwa domin gani nike kamar tilasta mata nike wurin ansa gaisuwar yawa saboda haka yau sai na hutar da ita.

Banza nayi da su na mayar da hankali na wurin bawa ido na abinci domin ganin abinda ban taɓa gani ba a rayuwata sai yau.

Yadda na nuna ban damu da su ba suma haka sukayi min sai da naga sun miƙe nima da sauri na bi bayan su, wani mutum sai faman kallo na yake sai da yagan ni kusa da mijin Hanifahr sannan yayi murmushi ya mishi magana da cewa.

"Congratulations! Two beautiful wives at young age, nice family....”

Take Hanifah taji jinin ta ya shiga tafasa ta kalle shi rai a ɓace tace.

" Please would you mind your business? I'm his wife alone, banga abinda ya shafe ka da rayuwar mu ba, minafiki kawai”

Daga haka mutumin ya wuce gaba abinshi zuciyar sa fal da mamakin Hanifah.

Mijin shi kuma yana tsaye kawai baice uffan ba. Ita kuma sai ta dawo bayan Mijin nata a maimakon da can da take gaban sa shi kuma yana bayan ta ni kuma a bayansa sai ya zamana ya shiga tsakiyar mu. Yanzu kuma sai ta dawo ita ce a tsakiya ni kuma a bayan ta.

Tana yi tana jan tsaki har muka shiga jirgin muka zauna wanda har yanzu fatar baki na da nasu bai haɗu ba, tafiya tamkar ta jaraba.............

*OUM AMEER*

💝 *BAHIYYA*💝

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

               *BY*

*AMINA IBRAHIM*

  *(OUM-AMIR)*

*BAHIYYA NOVEL ƊIN KUƊI NE KIBIYA 500 TA WANNAN ASUSUN 3132703269 FIRST BANK AMINA IBRAHIM SAI KI TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08068974831*

*LAST FREE PAGE*

      *LAST FREE PAGE*

          *LAST FREE PAGE*

*A nan muka kawo ƙarshen free pages in Sha wadda take so sai tayi payment ga account a sama taci gaba da karatu hankali kwance*

*FREE PAGE*

     *BABI NA GOMA SHA BIYAR*

BAHIYYA

  Mijinta ne ya fara wucewa ya zauna sannan ta zauna sai ni a ƙarshe, sai wani haɗe rai take tamkar an tilasta mata dole tafiya DANI, wanda a yanzu abun har mamaki ya ke ba ni. Sosai na shiga morewa bawa idona abinci, domin wata duniya ce ta daban na tsinci kaina a yau, Ina cikin kalle-kalle na a hankali bayan komai ya gama dai-dai ta jirgin ya fara tafiya a slow lokaci guda nayi tsit! nayi tamkar wadda ruwa suka cinye na fara zare ido, domin yanayin jin tafiyar jirgin yasa gabaɗai sai na ji ni ba dai-dai ba, kafin kace mi tuni jikina ya ɗauki mazari, akan tsabagen tsoro da firgici, Ina jin an yi wata fisga wani abu ya kaɗa can cikin hanta ta tamkar numfashi ne zai ɗauke ga wani jiri da ya ɗibeni, wata irin razananniyar ƙara na saki tare ƙanƙame hannun Hajiya Hanifah na runtse ido gam, Ina faɗin.

“Wayyo Allah Mama na! Na shiga uku, wallahi mutuwa zanyi, wayyo! Ni wallahi ku sauke ni tsoro nike ji, zamu faɗa ƙasa wallahi.....”

Wata irin muguwar tsawa Hanifah ta daka min tare da faɗin.

“Hey! What sort of nonsense is this? Ki na da hankali kuwa?”

Still idanuwana a rufe kuma hannun ta riƙe gam a nawa nayi saurin girgiza kai nace.

"Wallahi tsoro ni ke ji...”

Ganin yadda kowa ya zuro ido yana kallon mu shi ya sanya Hanifah jin wata irin matsananciyar kunya,take tayi ƙasa da kanta saitin kunnena murya a ƙasa ƙasa tace.

“Sai na miki mugun wulaƙanci idan kika sake ko tarin ki na ƙara ji, banza village girl kawai. Cikamin Hannuna!”

Da sauri na sake mata hannun ta kamar yadda ta ce, na riƙe gefen handle ɗin kujerar jirgin da ƙarfin tsiya, Ina ta karanto duk addu'ar da ta zo baki na,a raina ina istigfari ina ta kuma neman gafarar iyayena domin ban zaci numfashi na zai ci gaba da wanzuwa ba a ruhun jiki na.

Daga haka a hankali tsoron da ya mamaye dukkan ilahirin jikina ne ya fara tafiya a hankali yana bari na.

Farooq kuwa tsabar baƙin ciki da takaici tunda ya kallo ni sau ɗaya ya ɗauke kansa. A jikin seat ɗin ya jingina tare da kwantar da kansa ya lumshe ido yana ji wani ƙarin haushina ya na cika masa zuciya.

A cure nike wuri ɗaya na kasa yin wani ƙwaƙwƙwaran motsi, sai da yaje sauke a hankali tsoron ɗazu ya fara dawomin, rufe baki na nayi a wannan karon tare da runtse idanuwana ina ta addu'a cikin raina.

Ganin an fara miƙewa nima na miƙe na basu wuri suka fara yin gaba sannan na bi bayan su.

Mutumin ɗazu ne ya ƙara biyoni ya kalle ni da murmushi a fuskar sa yace.

“Hey pretty, Is this your first time being in plane?”

Gyaɗa kaina kawai nayi duk da cewa ban gama fahimtar mi yake faɗi ba.

Ɗan sake murmusawa yayi yace.

“Eyyah! Sorry....”

Sai kuma ya miƙomin hannunsa yana faɗin.

“I'm Shuraim Tafidah by name”

Ganin na maƙale hannun na ya sashi sakin dariya yace.

"OK! I understand, please can we be friends... Yeah, friends only...”

Tsinkayo muryar Hanifah nayi cike da masifa tana faɗin.

" Malama zaki zo mu tafi ne ko kuma mubarki a nan tare da shi?”

Zare ido nayi tare da yin gaba da sauri na bar shi a baya. Biyo bayan mu yayi yana murmushi yace.

" Haba Aunty! Kin ce ba mijin ku ɗaya ba kuma yanzu kin hana ta saurare ni hakan ba dai-dai ba ne....”

Sai kuma ya juya ga Farooq yace.

“Yayah please zan iya samun numbern ta? numbernta kawai”

Ina ga tunda ƙaddarar tafiyar nan ta haɗamu ban san ya waigo ko sau ɗaya ya kalleni ba sai yanzu. Kallo na yayi sama da ƙasa kallon da ke sakani ina jin matuƙar haushin sa domin sai inga tamkar kashi ya ɗauke ni marar amfani bayan su ne suka ɗauko ni don ƙashin kansu.

Sai da ya gama kallona sannan yace.

“I don't have any business with her, ruwanta tayi abinda take so”

Wani kallon tsana na bishi da shi a raina nace wato shi gani mai zaman kanta na fito yawon Bariki kenan ko? Lallai mutumin nan ban san ƙiyayyar tasa da ni ta kai haka ba sai yau.

Hanifah kuma dariya ce ta so suɓuce mata, yanzu ace classy guy kamar wannan ya tsaya wai zai karɓi numbern wannan village girl ɗin. Bai san ta ba ne shiyasa da zaran yasan wacece ba zai taɓa marmarin haɗa class ɗin shi da ita ba.

Daga ƙarshe sukayi gaba abin su suka barni nima ba shiri na bi bayan su raina cike da tsanar halayyar da suka nuna min ni ba baiwar su ba domin ba saya ta sukayi ba. Wannan tafiya wannan tafiya ta zame min ƙarfen ƙafa nikam Bahiyya. Allah ka nuna ranar da zan yasar da ƙwallon mangoro in huta da ƙuda.

Shuraim ma cikin rashin fahimtar wannan hargitsatstsiyar tafiya tasu kawai ya juya ya kama gaban sa. A ransa yace in dai da rabon ya sa meta in sha Allah watarana za su sake haɗuwa.

*************

Finchley Road, Hampstead.

London, United Kingdom.

Tun a mota nike ta kalle kallen gine-ginen benaye masu tsawo da kuma bala'in kyau, ga garin yayi duhu sai Fitilu kake gani masu azabar kyau da ɗaukar hankali. Ba ƙaramin burgeni garin yayi ba.

A hankali naga munyi parking a dai-dai wani bene mai masifar kyau ko a ta fuska.

Suna fita nima nabi su baya, bayan mun shiga gidan wani parlour ne babba na gammu a ciki wanda yaji kayan alatu iri da iri.

A nan na samu wani cushion mai laushi na ɗosana ɗuwawu na yayin da su kuma suka shiga ciki.

Kalle kalle kawai nike ina ta mamaki a raina cewa banga kowa a gidan ba kawai sa kai sukayi suka shigo, ko gidan waye wannan oho?

Sun ɓata kusan minti yafi talatin sannan daga ƙarshe ta shigo kamar ba zata min magana ba sai kuma tace min in biyo ta.

Ba musu na tashi na bi bayanta, wata hanya ce muka bi daga cikin parlourn sai gashi ta sadamu da wani katafaren ɗaki mai ɗauke da komai na more rayuwa.

“Nan shi ne ɗakin ki daga yau har ranar da contract ɗin mu zai ƙare.”

Daga haka ta fice ni kuma na taɓe baki, domin a yadda ta ɗauke ni nima haka na ɗauke ta, duk yadda suke ɗaukata yarinya dole ina da hankali da tunani dai-dai irin wanda Allah ya bani, a hakan nasan kyautatawa kuma nasan musgunawa. duk da cewa wata zuciyar na faɗin a irin taimakon da tayimin ta cancanci girmamawa da mutuntuwa sosai daga wuri na. To amma halin da take nuna min ne bana so.

Kan gadon na faɗa rub da ciki. Ina ta tunanin wannan sabuwar rayuwar da na tsinci kaina a cikin ta, ko wace kalar rayuwar zamu gurza a nan? Allah ma sani.

Nocking naji anyi, hakan yasa ni miƙewa da sauri naje na buɗe, wani mutum na gani fari ɗauke da tiren abinci a hannun sa. Jin yayi min wani kalar yaren da ban gama tantance cewa turanci ba ne ko yaya yasa na juya abina na koma ciki. Baya na ya biyo tare da ajemin tiren ya na sake yi min magana. Kamar in tartse shi da mari haka naji, banzaye kawai marasa aikin yi. Wata zuciyar ta ce min ko laifin mi sukayi min Oho!

Yana fita na sauko na bubbuɗe abincin, daman can yunwa na ciciyata. Hmmm! Kawai Kallon kalar abinci nike a raina ina faɗin uban waye zai ci muku wannan abun.

Naman kajin na zage na cinye duk da ba magin albarka a ciki, na shanye madarar da na fiso na ɗora da shan fruit da akayi slizing ɗin su a wani haɗaɗɗen bowl. Nan naji cikina ya ɗauka sannan na tashi na shige toilet na yi wanka na fito na buɗe kayana da aka shigo min da shi na ɗauki wasu riga da wando masu taushi ga faɗi na saka sannan na sanya hijabi na tayar da sallah.

Bayan na gama salloli na na daɗe ina Addu'a daga bisani na tashi na kwanta akan gadon, ganin bacci ya kasa ɗaukata yasa na tashi na janye labulen kantamemin windown na tsaya a kai, Ina ta kallon sabuwar duniyar da tsinci kaina a ciki. Daga kallon sararin samaniya ne kaɗai zaka gane cewa duhun dare ne, amma daga ka mayar da kallon ka ƙasa zaka ga hasken Fitilu mabanbanta masu walwali da ɗauke hankali suna ta aikin bada haske, ga motoci suna wucewa gwanin burgewa.

*************

FAROOQ

Bayan ya kambala duk wani muradinsa na daren yau, zaunawa yayi ya janyo system ɗin sa yana duba aikin da Mahi ya tura masa tun daren jiya.

Yana cikin aiki ne ta turo ƙofar ta shigo, sanye take cikin wasu night wears masu bala'in santsi da walwali pink color, kallon ta yayi tare da sakin murmushi yace.

“You look beautiful dear”

Haye jikin sa tayi tana murmushi itama tace.

“Really?”

Lumshe idanuwansa yayi yace.

“Yeah!. So can we get down to business? I'm always ready and available for that...”

Dariya tayi tace.

"Nifa wani zubin sai inga kwata kwata baka da kunya at all”

Zaro ido yayi da mamaki kwance a fuskar sa yace.

“Oh! A haka kika ɗauki abin Hanifah? Don't forget that you are my wife,I mean my Halal, to miye abin rashin kunya a ciki bayan sunnah ce mai ƙarfi, ni dai matuƙar za'a bani to zan karɓa in yi godiya ba da wasa ba....”

Miƙewa tayi ta koma kan gadonsa ta kwanta tana faɗin.

"That's not what brought me here, Wallahi a matuƙar gajiye ni ke, kawai ina so in faɗamaka mungama arrangement da Doctor Nicho gobe zamuje hospital ɗin.....”

Wayarsa ce tayi ƙara da sauri ya ɗaga tare da sakin murmushi duk da cewa baya gabanta. Sallama ya fara mata sannan ya gaishe ta daga can ɓangaren tace.

“Faruku ya kuka isa? Da fatan kuna lafiya”

Yace.

“We are fine Madinah, ya gida ya kike”

Tace.

“Komai Alhamdulillah. Allah ya taimaka ya bada sa'ar abinda aka je nema, ka gaisar da matar taka”

Cikin daɗin addu'ar ta yace.

“Amin Madinah, thank you so much, Hanifah zata ji in sha Allah”

Suna gama wayar Hanifah ta kalle shi tace.

“Farooq what did you tell madinat??”

Cikin mamaki yace.

“What did I tell her? Kawai na gaya mata cewa we are going for a business trip for one year, and you know it cewa Madinah is an understandable and supporting woman, fatan alheri kawai tayi mana.”

"While that's good to hear...”

Daga haka ta miƙe tana zabga hamma tace.

“I'm feeling sleepy, good night love, gobe zamu tattauna ko a mota ne”

Da sauri ya kalleta kafin ta iyarda ficewa yace.

“Why! Why Hanifah? Miyasa kullum kike son ɓatamin ne, ko tausayi na bakya yi, Hanifah sex is life....”

Da sauri ta saka hannunta ta toshe kunnen ta tare da yin waje da sauri tana dariya.

Kallon ta kawai yake har ta ɓacewa ganin sa. Ya ma rasa wane kalar tunanin zaiyi akan Hanifah, she's always always busy, Bayan Kuma yasan auren su shine kan gaban komai, amma idan zai kwana ya na faɗa mata ba zata amince ba,gani take kawai wannan kawai ra'ayin sa ne.

**************

BAHIYYA

Ganin duhun dare da wayewar gari da kuma tafiyar lokaci a agogon bangon da ke manne a ɗakin kaɗai ke nuna min shigowar dare da wayewar gari. Wani abu ne ajiye a side bed drawer Kamar alarm yake bugawa daga zaran lokacin sallah yayi sai ya fara kiran sallah.

Nafi kwana goma ban sanya kowa a ido na ba, tun ranar da muka zo ban sake ganin ko ɗaya daga cikin su ba. Abinci ne kawai wannan kukun ke kawo min ko wane lokaci wanda tun bana iya ci har yanzu dole na koyawa kaina don dole gudun yunwa amma kam shan madara da cin nama bana wasa da shi.

Fatar jiki na sai ƙara sheƙi ta ke tana ƙara luwui luwui tsabar hutu da shan sanyin AC mai daɗi. Can ƙasan zuciyata kuma kewar Mama ce ta addabeni, idan abin yayi min yawa har kuka nake. Ga kaɗaici duk yabi ya ishe ni, tashoshin da ke cikin wannan TV ɗin duk ba masu daɗi bane kamar na gida Nigeria. Shiyasa ban damu da kunna TVn ba.

.......... Ina tsaye jikin window kamar kullum ina kalle kalle na ta murɗa handle door ɗin ta shigo.

Kallonta kawai nayi tare da kau da kaina nace mata ina kwana sama sama naci gaba da kallon wajen da nike ba tare da sanin taji ko bata ji ba. Kallona tayi sama da ƙasa tamkar mai nazartar wani abu sannan tace.

“Zamuyi magana ne”

Juyowa nayi na kalle ta da kyau nace.

“Ina jinki”

Taɓe baki tayi sannan ta fara magana kamar haka.

“Yanda kika ɗauke ni ba shine mai muhimmancin ba, alaƙar da ta haɗamu itace abinda nasa a gaba. Daman can munyi yarjejeniya da ke zaki tayani renon ciki na wata tara kika amince da hakan nima na amince da biyawa mahaifiyarki kuɗin surgery ɗinta. So daman a nan ƙasar za'a yi kuma mun riga mun kambala shirye shiryen ranar Monday zamu je ayi aikin, so sai ki kasance cikin shiri”

Cikin rashin sanin in da zancen ta ya dosa nace.

"Aiki? Aiki kamar ya kenan?, ban fahimce ki ba, wane kalar aiki kike nufi?”

Kallona tayi da kyau tace.

“Za'a miki dashen Sperm ɗin mijina da Egg ɗina a mahaifarki, yayi girma a jikin ki ya rayu idan wata tara ya cika ki haife mana.....”

Wata irin gigicewa ce da ruɗewa suka ziyarci ƙwaƙwalwata lokaci ɗaya na zabura tamkar mai sabon taɓin hankali nace.

“InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Kiji tsoron Allah, kada ki danganta ni da alfasha,miye wannan kike magana akai??”

Wani kallon banza ta watsamin a wulaƙance tace.

“Ina ga kin hauka ce ne, mahaukaciya kawai, ko mata sun ƙare a duniya mi Farooq zai yi da ke, miye a jikin ki da rayuwarki baki ɗaya da Farooq zai kwanta da ke, wata ƙazama irin ki, ko zina yake mi zaiyi da ke a whole village girl like you. Common ki rufamin baki dan Allah ki saurari bayani na. Ƙwan halitta ta da Ƙwan halittar sa za'a ɗauka a saka a mahaifarki yayi girma ya rayu idan wata tara ya cika sai ki haife ki ƙara gaba shi kenan aikin.”

Cikin tsananin tashin hankali da ruɗewa na shiga girgiza kai tamkar wata zararriya ina faɗin.

“A'a ba zai yi yu ba, hakan ba zai faru ba, nifa budurwa ce. Ciki! Ciki fa kike magana Hajiya, inyi ya da shi to? Bani da aure zan yi ciki, Haba ki duba maganar nan kisa ma'aunin hankali a ciki. Gaskiya ba zai yi yu ba, ba zan iya ba...”

Taɓe baki tayi tare da ɗaga kafaɗa irin i don't care ɗin nan tace.

“While, since you say so, nasan Ina mahaifiyarki take a halin yanzu, tana asibiti ciwo ya taso mata, idan kina ganin kamar tunda na riga da na biya kuɗin aikin shikenan kinci bulus fine, kai tsaye zan kira likitan in faɗa masa ayi mata allurar mutuwa, kinga shikenan na yarda nayi asarar kuɗi na dana kashe ke kuma kin rasa mahaifiyarki.............”

*Tofa readers! Wannan shi ake kira ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Cakwakiya ce cike, danƙare a cikin wannan littafin, shin ya BAHIYYA zatayi???? Miye makomar HANIFAH a wannan TAFIYAR???? , kada fa ruwa ya ƙarewa ɗan Kada bai gama wanka ba. Farooqqq dai ya tsani BAHIYYA, ko ya abin zai kasance a tsakanin su. Ku biya kuɗin ku kuci gaba da karatu cikin nishaɗi*

                        “OUM AMEER”

End of current loaded text.