💖💖RAYUWAR MU💖💖
_Written by ✍️ _
*Jagaban Jajirtattu*
_(Ta Batulu)_
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
*(J.W.A)*
_Wannan shine Whatsapp group ɗin da zaku samu cigaban wannan labarin. Ku taya ni shering Please👇._
https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT
(Tafiyar ƙaddara kamar tafiyar ajali take, duk inda ka kai gurin guje mata sai ta risƙe ka. Komai na duniya yana da lokaci kuma yana da iyaka, Rabbi ka yi daɗin salati ga shugaban kowa da komai, manzon tsira manzon Rahama Annabi Muhammad s a w.)
*Bismilahi rahamanun Rahim.*
*Page 1-2*
Wata matashiyar budurwa ce sanye da uniform ɗin makaranta blue black sai farin hijjabi wanda ya wuce guiwa tafe take ta na ran gaji.
Kana ganin uniform ɗin ka san na islamiyya ne ba za ta wuce 20 yrs ba duk da uniform ɗin sun koɗe amman babu datti ko kaɗan ajikin shi.
Ta na tafe ta na ya mutsa fuska da dukkanin alamu akwai gajiya a jikinta.
A bakin wani ƙaramin gida mai dakali guda biyu ta tsaya.
Ta yi kusan 9 minutes a zaune a kan ɗaya daga cikin dakalin kafin ta shiga gidan bakin ta ɗauke da sallama.
Wata mata ne zaune a kan kujera a ƙofar wani ɗaki daga gani ɗakinta ne ta amsa sallamar ta ce.
"Shukrah har an dawo?"
Wannan matashiyar da aka kira da shukrah ta ce.
"Eh na dawo Umma sannu da gida"
Shukrah ta ƙarema ummanta kallo a ƙalla za tai 40 years amman ya na yin rayuwa yasa ta zama kamar mai shekara 40 da wani abu.
Kana ganin gidan ka san a kwai ya nayin rayuwa ɗakuna uku ne a gidan sai ban ɗaki a ƙarshen gidan.
Kana shigowa a kwai ɗakin farko ɗakin babansu Shukrah.
Daga ɓarayin dama kuma ɗakin umman Shukrah sai ta ɓangaren hagu ɗakin amaryan Abba.
Sai kitchen kusa da ɗakin baban su Shukrah.
Umma ta na ta magana Shukrah ba ta ce komai ba.
Umma ta tashi ta riƙo Shukrah ta ce.
" Ki rage ma kanki wannan tinanin bai da amfani"
Shukrah ba ta ce komai ba ta shiga ɗakin su ciki da parlour ne
parlourn ya na da faɗi ba laifi Amman kujeru biyu ne kawai a parlourn mai zaman mutum biyu.
Sai mai zaman mutum uku masu ruwan toka duk ya ji jiki amman tsaff suke babu datti.
Sai carpet shima mai ruwan toka da ratsin baƙi shima duk ya koɗe amman babu datti a jikinshi.
Akan kujera Shukrah ta zauna ta jingina bayanta ta lumshe danun ta kamar tana bacci.
Ba ta jima ba ta ji hayaniya na tashi a waje ta shige cikin bedroom ta na tsaki.
Ta na shiga sai ga wasu mata san ƴan mata sun shigo da sallama mata ne su biyu sai namiji ɗaya.
Su kaiwa Umma sannu da gida Umma ta amsa tana cewa "Har kun dawo?"
Suka amsa da
"Eh Umma mun je bata nan sai da muka jira ta"
Umma ta kali ƙaramin yaron ta ce.
"Mudan na ga ka yi shiru hala sun gajiyar mun da kai?"
Mudan ya rausayar da kai ya ce.
"Ehh wallahi Umma Aunty Darraini sai jana take yi"
A cikin ƴan matan da suka shigo wacce tafi girma a cikin su.
Ta taso zata dake shi ta na cewa tinda sharri zai mata.
Umma ta tare ta na faɗin ba zata dukar mata autan ta ba ai gaskiya ya faɗa.
Mudan ya kalli Darraini ya yi mata gwalo Darraini ta yi ƙwafa ba ta ce komai ba.
Umma ta kalli ɗayar yarinyar da tinda suka shigo ba ta ce komai ba ta ce.
"Manaheer lafiya ki kai shiru ba ki ce komai ba?"
Wanda aka kira da Manaheer sai ta zumɓuro baki ta ce.
"Umma ni da nake jin yunwa Ina naga bakin surutu"
Umma ta kalli Auta ta ce.
"Autan maman shi ka naj in yunwa?"
Mudan ya ce.
*Eh mana ummana ji nake kamar banda hanji"
Yana faɗin hakan suka kwashe mai da dariya.
Darraini ta kalli Umma ta ce.
"Umma har yanzu Yaya bata dawo da ga islamiyar ba?"
Umma ta ce.
"Ta dawo tana ɗaki"
Suna jin hakan suma suka shiga ciki bakinsu ɗauke da sallama .
Basu ganta a parlour ba sai suka shiga cikin bedroom su na shiga suka ganta ta kwanta rigingine fuskanta na kallon rufin ɗaki,
Idonta biyu Manaheer ta na ta magana shiru da alama tayi nisa domin tunda suka shigo bata motsa ba.
Ganin hakan sai Darraini ta je ta taɓa ta ta na taɓa ta tayi ajiyar zuciya.
Duk suka mai da idanun su kanta Shukrah ta kalli ƙanin na ta guda biyu ta kau da kai.
Ganin ba tace musu komai ba sai suka sata a tsakiya suka kewaye ta.
Ganin hakan sai Shukrah ta tashi ta zauna ta na ƙare musu kallo ba tare da ta ce musu komai ba.
Suna da sanin cewa in zasu kwana a hakan Shukrah ba za ta ce musu komai ba.
Darraini ta ce.
"Aunty Shukrah mai ke damunki ko baki da lafiya lafiya ne?"
Ita kuma Manaheer ta yi shiru tasa musu ido
ta na jiran ta ji abin da Shukrah za ta ce duk da ta san abune mai wahala ta faɗa musu damuwarta.
Babu zato ta ji muryar Shukrah na faɗin yanzu haka zamu cigaba da rayuwa kullum jiya iyau babu wani cigaba a rayuwar mu?"
Dukansu sun gane mai take nufi suka kasa bata amsa ta kalli Manaheer ta ce.
"Tunda muka taso muke shan wahalar rayuwa har yanxu bamu san wani abu wai shi farin ciki ba.
Ku duba ku gani yanda Umma take wahala akan mu kullum burinta ya za ayi mu koma school amman hakan yaƙi samuwa"
Itace cin mu da shan mu itace sutturan mu itace maganin mu komai itace kuma kuna ganin babu wani sana'ar da ta ke yi kullum faɗi tashi ta keyi a kan mu"
Ta na gama faɗin hakan kuka yaci ƙarfinta.
Suka haɗe suna ta kuka sunyi 20 minutes suna kuka kawai ji su kayi an dafa su.
Suna ɗagowa suka ga Umma tsaye a kansu ta na ƙare musu kallo ta ce.
"Nayi ta magana a fito ai sallah na ji shiru sai na shigo in ga abinda ya hana ku jin kiran sallah ashe kuna nan kuna aikin da kuka sa bayi"
Umma taci gaba da cewa "Da a ce kuka na maganin damuwa da tini baku da sauran damuwa a duniya"
"Ku tashi kuje ku fuskanci ubangiji shiɗin maji roƙon bawa ne kuma duk duniya shi kaɗai zai iya yaye muku damuwarku,
Ta na gama faɗa musu hakan ta shiga ciki ta ɗau darduma ta fita ta basu guri.
Ita kanta ƙarfin hali tayi ta rike kanta domin tunda suka fara magana take tsaye a kansu tazo tai musu magana a kan suzo su naimo abinda za suci sai taji suna wannan zancen.
Ita kanta haƙuri take da mahaifinsu ta na da gata da komai amman ta zaɓi zama dashi ko dan ƴaƴanta.
Basu motsa ba daga in da suke har sai da Auta ya shigo ya ce
"Umma ta na kira"
Sannan suka tashi kowannensu jiki a san yaye suka fita parlour suka sameta a saman darduma ta na jan casbih.
Da ido kawai ta kallesu kowa ya yi waje yaɗau buta Shukrah ta shiga toilet ta fito Darraini ta shiga ta na fitowa.
Manaheer ta tashi zata shiga har ta kai ƙofar toilet ta ji an bangajeta sai da ta faɗi ƙasa aka rufe ƙofar toilet ɗin da ƙarfi Manaheer tayi saurin janye ƙafarta.
Darraini na ganin hakan tai sauri taje ta faɗawa umma domin ta san halin Manaheer ba ta yafiya idan ka ta ɓata.
Ta na zuwa taga Umma na sallah sai ta tsaya tana jiran ta idar da sallahn.
Ita kuma Shukrah taje ta ɗaga manaheer ta ce.
"Idan kika ƙyale wannan yarinyar keba jinin umman mu bane"
Ta na gama faɗa mata hakan ta tashi ta shiga ɗaki tana leƙen Umma domin ta ga abin da take yi.
Ta na leƙawa taga Umma sallah take Darraini na gefenta a zaune.
Shukrah tai hamdala ta koma tsakar gida ta sa kujera ta zauna tana kallon Manaheer da ta kasa magana kawai toilet ɗinsu take kallo idanunta sunyi jajir kamar wanda aka zuba ma yaji.
Ita dai shukrah ta na ta kallon Manaheer domin ta san idan ta kama na cikin bayin nan sai allah.
Manaheer duk ta fisu jiki kuma tafi su cika.
Ƙaran buɗe toilet ne ya dawo da shukrah cikin tunanin da ta fara.
Allah allah take ta fito daga toilet ta ga abin da zai faru.
Bata gama tinanin da take ba ta ji wani gigitaccen ƙara sai da gidan ya amsa ta na kallon Manaheer taga abin da tayi sai da ta zaro ido ta miƙe tsaye.
Mimah ne a kwance a ƙasa Manaheer na dukan ta. Shukrah ta ce.
"Yauwa sister baki daki bakin rashin kunyar ba"
Ai Manaheer najin hakan kamar an ƙara mata ƙarfi ta dinga jibgan Mimah.
Jin ihun ya yi yawa ne yasa Umma fitowa jiki na rawa Darraini da gyangyaɗi ya fara ka mata itama ta yi waje da gudu,
Ganin abin da ke faruwa suke kamar a film duk da sun san Manaheer bata da haƙuri amman basu taɓa tunanin za tai ma Mimah wannan dukan ba.
Ganin Umma ta fito yasa Shukrah ɗaga murya ta ce.
"Sister bugun ƙarshe ga Umma nan"
Ai ko Manaheer na jin hakan ta saɓi Mimah zata buga da ƙasa Umma ta yi mata tsawa ta ce.
" Mata kull kika aikata hakan sai ranki ya ɓaci"
Manaheer ta saki Mimah ta faɗi ƙasa kamar kayan wanki ta saki wani marayan kuka.
Umma ta kalli Shukrah ganin hakan sai Shukrah tai huf ta faɗa ɗaki.
Umma ta ce.
"Manaheer tazo ta huce ɗaki"
Ba tai alwalan ba.
Cewar Darraini Umma ta kaɗa kai ta ce.
"Yi alwalan mu wuce ɗaki"
Manaheer ta tsallake Mimah dake yashe a ƙasa tana ta gunjin kuka ta shige toilet ta bugo ƙofa saura kaɗan ta bige ƙafar Mimah
Umma ta kama Mimah ta miƙar da ita ta na kakkaɓe mata ka yanta da yasha ƙura.
Umma ta ce,
"Kiya haƙuri Mimah dan allah"
Mimah ba tace mata komai ba ta fisge jikinta ta shige ɗakin su,
Darraini ta yi dariya ta ɗaga murya ta ce.
"Amman fa Mimah sai kin gasa bakinki da ruwan ɗumi"
Umma ta kalli Darraini ganin kallon da Umma take mata yasa tai wuf ta faɗa ɗaki tana ƙunshe dariya.
Ta na shiga ta samu Shukrah a saman darduma ta idar da sallah ta na jan casbih.
Darraini ta kalli Shukrah ta kwashe da dariya sister a na ta lazimi kenan Shukrah ba ta ce ma Darraini komai ba taci gaba da jan casbihn ta.
Suna cikin haka Umma ta shigo ita da Manaheer Umma na gaba Manaheer na baya.
Ganin Umma ta shigo yasa Darraini ta yi shiru Manaheer ta ɗauki hijjab ɗin Umma taje gefen Shukrah ta tayar da sallah.
Darraini na ganin hakan ta tashi da sauri ta fita taje ta ɗau buta ta sake sabon alwala.
Ta shiga ɗaki ta samu Umma zaune akan kujera Darraini na ganin Umma ta zauna sai ta kau da fuska kar Umma tai mata magana
Umma tayi kamar bata ganta ba.
Darraini ta matsa kusa da Shukrah ta ce.
"Sister ɗan matsamun in yi sallah."
Shukrah ta ɗago ta watsama Darraini harara sannan ta tashi.
Ta koma kusa da Umma ta zauna a ƙasa.
Umma ta kalli manaheer da ta idar da sallah.
Manaheer ta zo ta zauna kusa da Shukrah.
Umma tayi shiru ba ta ce komai ba.
Auta ya shigo da sallama suka amsa suka amsa mishi ya shigo ya kwanta a jikin Manaheer .
Umma ta kalli Auta ta ce.
"Daga Ina kake domin na san ba daga masallaci kake ba?"
"Bayan an idar da sallah banga Bashir a massallaci ba shine na je gidansu na duba shine na ga baida lafiya cewar Auta"
Umma najin hakan ta maida dubanta gun Darraini.
Ta na lura da ta idar da sallahn amman taƙi sallamewa Umma ta yi murmushi.
" Baki idar da sallahr bane?" cewar Umma ta na kallon Darraini.
Darraini bata ce komai ba ta zo ta zauna kusa da Manaheer.
Umma ta kalli Shukrah ta ce.
"Zan fara ta kanki saboda duk kinfi su laifi.
"Yanzu a matsayin ki na babba ya dace abin da ki kayi?"
Dukan su suka duƙar da kai ƙasa.
Umma taci gaba da cewa " Nayi tunanin ke mai tsawatarwa ne a garesu bamai sawa suyi ba"
"Idan kinga su nayin abin da bai dace ba sai ki tsawatar musu a matsayin ki na babba"
"Amman abun takaici kece mai sawa suyi kuma kece mai basu umarni"
"Kin bani kunya kuma kin bani mamaki wallahi Shukrah a kan hakan zan saɓa miki ba zaki barni da abin surutu ba ku bakwa gudun abun magana a rayuwarku?"
"Yanzu a kan abinda kuka aikata kun san abin da zai je ya dawo kuma kun san a kaina komai yake ƙarewa"
Maiyasa idan za kuyi abu bakwa tsayawa ku yi tinani maiyasa bakwa tausayin halin da muka tsinci kan mu aciki" Umma ta na magana muryanta cike da rauni?,
Manaheer ne tai ƙarfin halin cewa " Kiya haƙuri Umma in sha Allah ba za mu ƙaraba"
"Dan allah kiya haƙuri" cewar Darraini.
Auta ma ya ce.
"Umma sun ce kiya haƙuri ba zasu sake ba"
"Dan allah ki yafe mana ɓata miki ran da mu kayi in sha Allah allah hakan ba zai sake faruwa ba" cewar Shukrah fuskan ta ɗauke da hawaye.
Umma ta nu na ma kowa kuskurenshi kuma sun yi mata alƙawarin ba zasu sakeba,
Darraini ta kalli Umma ta ce.
"Nifa cikina yana ciwo"
Shukrah ta watsama Darraini harara.
Kije saman gado ta gefen pillow ɗina za kiga ɗari biyar ki ɗauko kije ki siyo garin kwaki da sugar cewar Umma.
Darraini ta je ta ɗauko ta zo zata fita Auta ya tashi ya bita suka fita tare.
Shukrah ta tashi ta je ta ɗauko bucket ta zuba ruwa ta shiga toilet ta watsa ta fito.
Ta buɗe wardrobe ɗin kayan su wardrobe ne mai ƙofa huɗu ta buɗe na farko ta ɗauko doguwar riga na yadi tasa.
Ta fito parlour tazo ta zauna kusa da Umma Manaheer ma taje ta watsa ruwan ta sanja kaya.
Umma na zaune da casbih a hannunta Auta ya shigo bayan ya yi sallama.
Ya zauna kusa da Umma
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT
RAYUWAR MU
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Written by
Jagaban Jajirtattu 🥰
(Ta Batulu)
*Page 3~4
Darraini ta yi sallama ta shigo hannunta riƙe da baƙar leda ta a'je ta fita sai ga ta da kwano mai ɗan faɗi.
Ta juye wannan garin a ciki ta ɗauka ta fita.
Ba ta jima ba ta dawo hannunta ɗauke da spoons ta zuba sugar ta sa spoon ɗin aciki ta zauna.
Duk abin da take Umma na zaune ta na kallonta.
Auta ya sauko ya zauna a ƙasa Manaheer ta zauna kusa dashi.
Darraini ta zauna kusa da Auta su kai bismillah suka fara sha.
Shukrah na hakimce a gefe ta na kallon su ko alamar tashi babu a tare da ita.
Umma ta kalli Shukrah ta ce.
"Hala kin ƙoshi ?"
Shukrah ta turo baki ni ba naci.
Gaya mun abin da kika ci tin da kika dawo?
Cewar Umma.
Shukrah tayi shiru Umma ta ce.
"Ki tashi ko kuma yanzu ranki ya ɓacci."
Shukrah ta tashi ta na turo baki ta je kusa da Darraini ta zauna.
Ta ɗau spoon dama saura ɗaya ne.
Ta naci ta na ya mutsa fuska spoon ɗaya tayi ta mayar dashi ta a'je.
Manaheer tayi waje bayan ta ɗau buta ba ta jima ba ta dawo ta zauna kusa da Umma.
Darraini ma ta tashi taje ta zauna kusa da Manaheer
Shukrah ta tashi ta ɗau buta tayi waje Umma tayi ƙwafa ta dawo da kallon ta kan Auta.
Ta ce
"Auta meke damun Bashir na ji kace bai da lafiya?"
Kafin Auta ya ba Umma amsa sukaji hayaniya na tashi a tsakar gida.
Umma ta ce.
"Allah ya kyauta"
Manaheer zata fita Umma ta hana tace su jirata ta je ta ji.
Umma ta fita Auta yabi bayanta.
Amaryan Abba ne Aisha take masifa.
Ta na zagin Shukrah dake zaune a tsakar gidan.
Ta na ganin Umma ta fito ta ce.
"Yauwa ga babban munafukar nan ta fito"
Ta nufo Umma ta na cewa
"Maine yarinya na ta yi muku za kuyi mata taron dangi ku dake ta?
Umma ba tace komai ba ta yi shiru ta na kallon Aisha tana jiran taga mai take shirin aikatawa ta na zuwa gaban Umma taja ta tsaya ta gama zagin Umma tass.
Sannan ta shiga ɗaki ta na cewa kujira mai gidan ya dawo wallahi sai ya yi mana iyaka daku.
Umma ta sauke kai ƙasa ta na ajiyar zuciya.
Shukrah da tinda aka fara bata iya ɗago da kaiba.
Tazo ta kama Umma ta shiga da ita ɗaki ta zaunar da ita saman kujera ta zauna kusa da ita.
Ta kwantar da kanta a jikin Umma ta fashe da kuka ganin Shukrah na kuka yasa sauran suka matso kusa da Umma
Suka dafa Shukrah su ka ce.
"Kiya haƙuri sister dan allah domin idan ki kai kuka mu ma kukan za muyi babu mai rarrashin wani munji komai kuma mu ma muna jin abin da ki keji a ranki"
Umma tasa hannu ta na shafa kan Shukrah ta na cewa.
"Babu wani dauwamammen abu a duniya kuma duk abin da ku kaga ya yi farko to ya na da ƙarshe"
Auta ya zauna ajikin Umma ya na kuka.
Umma ta kalli Auta ta ce.
"Kaifa Jarumine ko ba ka san jarumi baya kuka ba?"
Auta ya ce.
"To ai Umma ka ɗan zanyi."
Su na jin haka dukan su suka mai dariya shima autan na ta ya su.
Umma ta ce.
"Suzo suje su dubo Bashir da jiki"
Auta ya nata murna ya na tsalle Manaheer ta sa hannu ta ran kwashe shi akai.
Auta ya ɓata fuska zai yi kuka Umma ta ce.
"Rabu da ita ka ji haushi ta ke ji ka fita kyau."
Suka shirya su uku banda Shukrah da take jin gine jikin Umma ita ko motsi ba ta yi ba.
Suma ganin hakan ba su ce mata komai ba domin sun san ba za ta je ba.
Su kai wa Umma sallama suka tafi "Kuce ina gaida shi da jiki" cewar Shukrah.
Bayan fitan su Umma ta kalli Shukrah ta ce.
"Ina ta tinanin sana'ar da zanyi na rasa mafita"
"Ko za muyi a waran sai dawa naga ana ciniki sosai" cewar Shukrah.
Umma ta ce.
"A'a ba na son tallah"
"Ba tallah za mu yi ba a cikin gida zamu din ga yi ana zuwa ana siya" cewar Shukrah.
Umma ta yi shiru ta ce.
"Zanyi tunani akai"
Shukrah ba ta ƙara cewa komai ba, ta zame ta kwanta.
* Asalin Labarin*
Mallam Abdallahi ɗan asalin garin saminaka ya na da mata biyu da ƴaƴa shida.
Hajjiya Adama uwar gida mai yara huɗu amarya na da biyu.
Ɗakin Hajjiya Adama Aliyu ne babba a gidan Naseer sannan Umar sai auta Fatima.
Ɗakin Hajjiya Aisha Isma'eel Amina Isma'eel da Fatima saanin juna ne tare a kai goyon su.
Hajjiya Adama suna kiranta Mama Hajjiya Aisha suna kiranta Inna.
Hajjiya Adama mace ce mai tsananin haƙuri ga kawaici itace auran saurayi da budurwa bata da wani damuwa.
Hajjiya Aisha a bazawara ya aure ta mace ce mai ta ƙama da izzah.
Ga rashin son zaman lafiya ga tsananin kishi suma yaran duk ta koya musu halinta.
Ta na kishi da ƴaƴan Mama musamman Aliyu saboda shine babba a gidan.
Mallam Abdallahi mutum mai rufin Asiri domin ya na noma sosai.
Kuma Alhamdulellahi ya na wadata iyalanshi shima ya na da tsananin haƙuri sosai.
Shima hakuri yake da Hajjiya Aisha domin koshi ba ta raga mai.
Gidan Mallam Abdallahi ya na ɗauke da ɗakuna uku akwai ɗakin zaure inda yake a'je ka yan noma.
Kana shigowa ɗakin mazan gidan ne a farko parlour ne babba mai ɗauke da ɗakuna uku sai banɗaki a cikin parlour na wanka.
Ɗakin farko na Aliyu ne shi ka ɗai sai na biyu Naseer shima shi ka ɗai sai ɗakin ƙarshe Umar da Isma'eel suke kwana.
Kowani ɗaki da ƙaton katifa aciki da sauran kayan buqata na maza amman ɗakin Aliyu duk yafi nasu kyau akwai shi da gayu gashi baya son ƙazanta.
Ɗakin Mallam a gaba da na mazan shima ciki da parlour ne da toilet.
Idan ka shiga ciki kuma ɗakin Inna ne itama ciki da parlour ne da toilet.
Sai ɗakin Mama shima dai kamar sauran ɗakunan yake.
Banɗakin tsakar gida guda ɗaya.
Mallam Abdallahi mutum ne mai tsananin son ibada kuma ya tsaya ma yaran shi suyi karatu tun daga na zamanin zuwa na muhammadiyya.
Yaran shi Shi kaff suna karatu idan ka cire Isma'eel shi duk baya so
tin Mallam Abdallahi yana faɗa yazo ya samai ido.
Idan yacna mai faɗa uwarshi cewa ta ke duka duka guda nawa yake ita kawai ya tsani ƴan ɗakinta ne shiyasa dan haka ya rabu mata da yaro yayi abinda yake so lokacin shine.
Aliyu tinda yayi candy ya ce ma mahaifinshi kasuwanci yake so ya fara shi kuma mahaifin nashi ya haɗa shi da abokin shi suna zuwa kasuwa tare suna sai da atamfofi da shadda da sauran kayan sawa.
Aliyu mutum ne mai zuciya gashi da son girma amman baya da raini yana girmama na gaba dashi yana son karatun addini.
Idan ya dawo gida da daddare bayan sallahr isha'i yana ɗaukan karatu gun mallam.
Yanzu haka Aliyu yana da shekara 25 babban burin mallam yaga Aliyu yayi Aure ya samu mace ta gari ƴar gidan mutunci ya aura.
Naseer 23 Umar 19 Fatima 16 shekarunsu ɗaya da Isma'eel sannan auta Amina 13
Ta Batulu ce 🥰✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oTRAYUWAR MU
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Babu Rayuwar da Babu ƙalubale acikin ta 👌
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu 🥰
( Ta Batulu)
*Page 5-6
Aliyu ya shigo gida bakin shi dauke da sallama Inna ta amsa mai sallamar ta na hararan shi.
Aliyu ya yi kamar bai ganta ba sannu da aiki cewar Aliyu Inna tayi kamar bacta jishi ba ganin haka bai ƙara cewa komai ba,
Ya leƙa ɗakin Mama ya ganta akan darduma tana jan charbi ya shigo ya zauna bakin shi ɗauke da sallama Fatima ta amsa.
Sannu da zuwa ya Aliyu ya ce.
"Yauwa Auta ya aiki"
Lafiya qalau ya kasuwa cewar Fatima Aliyu ya ce.
" Alhamdulellahi"
Daga nan ta je ta kawo ruwa mai sanyi
Aliyu ya ƙarba ya yi godiya.
Aliyu bai ƙara cewa komai ba ya jingina da kujeran da yake zaune.
Ɗakin Mama yasha saitin kujeru blue black da ratsin golden a tsakiya.
Sai fridge mai ɗan girma ɗakin yasha tayis fari ƙal ya na ta ɗaukar Ido.
Fatima akwai tsafta bata son ƙazanta ko kaɗan hakan ya samu ne da tarbiyan Mama.
Fatima ta leƙo ta ce. "Ya Aliyu in kawo maka abinci"
"A'a ba zanci yanzu ba"
Cewar Aliyu.
Mama ta kalleshi bayan ta gama jan charbin "Mai kaci da za ka ce ka ƙoshi?"
Aliyu ya yi shiru Mama tasa Fatima ta kawo abinci da ruwa.
Mama ta kalli Aliyu ta na cewa "Ban san yaushe bane zan daina maka faɗan cin abinci"
Aliyu ya sunkuyar da kai "Kiya haƙuri Mama cewar Aliyu"
Fatima ta shigo bakinta ɗauke da sallama hannunta riƙe da plate ta a'je gaban Aliyu shinkafa da miya da salat.
Fatima ta buɗe fridge ta ɗauko mai zoɓo mai sanyi a gora ta zo ta a'je.
Aliyu ya saukoh ƙasa ya yi bismillah ya fara cin abincin.
Yaci kusan rabi saboda Mama na zaune a kusa dashi saboda ta na yawan fadan rashin son cin abincin da ba ya yi.
Aliyu ya ce. "Fatima zoki ɗauke abincin nan"
Mama ta zuba ma Aliyu ido
Fatima ta ɗauke plate ɗin ta fita mama ta ce. "Dama Ina son magana da kai"
Aliyu ya kalli Mama da ta zuba mishi ido.
Fatima ta shigo ganin kamar suna magana ya sa ba ta zauna ba ta shige ciki.
Mama ta ce. "Aliyu koza ka je ka duba yarinyar Alhaji Ibrahim ne idan ta yi maka sai ku dai dai ta?"
"To Mama zanyi ƙoƙarin hakan in sha allah ko zuwa gobe idan allah ya kaimu"
Mama ta ce. "Masha allah ubangiji ya yi maka albarka
Allah ya zaɓa maka mafi alkhairi"
Aliyu ya a'je mata ledar da ya shigo dashi ya fita.
Yana fita Fatima ta yi tsalle ta fito dama jira take ya fita ta samu damar fitowa,
Fatima ta ce. "Mama wallahi yaya Aliyu ya yi sa'ar mata Amina bata da matsala gata da kunya allah yasa su dai dai ta"
Mama ta ce. "Nima yarinyar ta na burgeni wallahi gashi bata da hayaniya"
Fatima tana ta murna Mama tana mamakin yanda Fatima ke murna bayan basu san juna ba.
Fatima ta janyo ledar da Aliyu ya a'je ta bude kayan tea ne a ciki komai da komai.
Mama ta ce.
"Ta ɗauka ta je ta aje"
Bayan fitan Aliyu ɗakin mahaifinsu ya shiga ya same shi yana karatun Qur'ani.
Aliyu ya zauna a ƙasa kusa da mahaifinsu wanda suke kira da Baffa.
Bai daɗe da zama ba ya rufe Qur'anin ya kalleshi ya ce. "Ya akayi gadanga?"
Wasu lokutan haka yake kiran shi dashi.
Aliyu ya gaishe shi ya ce.
"Na dawo ne banji motsinka ba shine nace bara in duba ashe kana ciki"
Baffa yayi murmushi "Da fatan dai babu wani matsala?" cewar Baffa.
Aliyu ya yi murmushi ya ce.
"Ba komai"
Baffa ya yi murmushi irin nasu na manya ya ce.
"Gadanga Ina son ka riƙe abubuwa guda 4 wanda ko bayan babu raina za kai alfahari da hakan"
Aliyu ya yi shiru Baffa yaci gaba da magana "Ina son ka ji tsoran allah kaji tsoran zalunci ka guji addu'ar wanda aka zalunta kariƙe gaskiya a dukkan lamarin ka"
"Lallai idan kariƙe waɗannan abubuwan guda 4 zaka zauna lafiya"
Aliyu ya yi murmushi ya ce.
"Nagode Baffa allah ya ƙara lafiya da nisan kwana in sha allah zan kiyaye"
" Ubangiji ya yi maka albarka kai da ƴan uwanka allah ya ƙara rufa muku asiri duniya da lahira"
Aliyu ya duƙar da kanshi ya na amsawa da ameen.
Su na cikin haka aka shigo zuruf haɗe da sallama.
Ko basu waiga ba sun san mai wannan halin Inna ce ta shigo ta zauna kusa da Baffa ta ɗaure fuska.
Aliyu na ganin haka ya miƙe yana cewa Baffa a tashi lafiya ya fito bai tsaya jiran amsar Baffa ba.
Parlourn su ya shiga bakinshi ɗauke da sallama Ismael ne zaune a bakin kofar ɗakin su ya na ganin Aliyu ya ɗaure fuska ya kau da kai.
Aliyu ya yi kamar bai ganshi ba ya shiga ya buɗe ɗakin shi ya shiga yana kwafa yana mamakin yanda kwata kwata Ismael bai da kunya.
Ya yi murmushi yana tunanin irin punishment ɗin da zai ba shi idan ya kama shi.
Ya na shiga ya fito da bucket ya shiga cikin gida ya na shiga ya samu Amina a tsakar gida ya ce. "
Mata kije gurin Mama ta baki ruwan zafi ki kawo mun"
Ya miƙa mata bucket ɗin.
Amina tazo karɓa tana tura baki tana zuwa kusa dashi ya bige bakin nata.
Ai ko kamar jira take ta fashe da kuka.
Aliyu ya tsaya yana kallonta shi kallon mamaki yake mata.
Da ya ji zata cika mishi kunne ya ce.
"Wallahi idan baki rufe mun baki ba sai nayi miki mugun duka"
Wato rashin kunyar naki yanzu ya dawo kaina ni zan aikeki k ina tura mun baki koh?"
Amina tayi tsit domin ta san halin Aliyu baya son raini ta karbi bucket ɗin ta shiga ɗakin Mama tayi sallama ta faɗa.
Aliyu ya kaɗa kai yana mamakin yanda Inna take lalata tarbiyan ƴaƴan ta da kanta.
Kuma idan ka yi musu fada ta ce ka zalunce su.
Ya na tsaye ta fito ita da Fatima suka shiga kitchen ganin haka Aliyu ya ce.
"Fatima ta zo ta huce ta bashi guri"
Fatima ta zo ta wuce tana ƙunshe dariya.
Daman tana kallon su ta window har turo Amina amsar ruwa duk ta gani da abinda ya faru.
Aliyu ya kalli Amina dake tsaye tana kallan shi ya ce.
"In zo ne in zuba ruwan da kaina?"
Amina ba tace komai ba ta shiga ta ɗibo ruwan ta kawo mishi gaban shi ta aje.
Aliyu ya yi gaba ya ba ta guri ba tare da yace mata komai ba.
Ganin haka sai tabi bayan shi da bucket ɗin ta riga Aliyu shiga saboda ya tsaya amsa waya.
Ta samu Ismael zaune a in da yake tin ɗazun suna haɗa ido ta watsa mishi harara shi kuma ya hau mata dariya.
Suna cikin haka Aliyu ya shigo ya kalli Ismael ya ɗaure fuska
"Tashi ka wanke mun toilet yanzu" cewar Aliyu.
Ya kalli Amina ya ce.
" Shigo mun da ruwan ki share mun parlour nan"
Amina da Ismael suka kalli juna kafin kowa ya kama kanshi.
Domin sun san abu kaɗan za suyi ya basu punishment din da sai an kwana biyu suna jinshi,
Amina ta bi bayan Aliyu da ya shiga daki Ismael kuma ya dau bucket ya yi cikin gida.
Amina ta na shiga ta samu Aliyu zaune a saman katifa ya na danna waya ta aje ruwan a bakin ƙofa ta fita.
Tsintsiya ta ɗauka ta fara shara ta na yi ta na surutai ta na gamawa Ismael ya shigo da bucket cike da ruwa.
Ya shiga toilet dashi ya aje ya fito ɗakin su ya shiga ya ɗauko omo da abun wanke toilet 10 minutes ya gama ya fito ya mai da kayan ɗakin su.
Ya shiga ɗakin Aliyu da sallama ya samu Amina a tsaye Ismael ya ce.
"Yaya na gama"
Aliyu ya yi kamar bai ji shi ba Ismael ya a kalli Amina ya harareta ita ma ta rama.
Aliyu ya ɗau kayan wankan shi da ruwan zafin ya fita yaje parlourn su ya surka daman suna da roban ruwa a cikin parlourn ya shige toilet.
Bai jima da shiga ba Fatima ta shigo da sallama ta shiga ɗakin yayan na su ta samu Amina da Ismael a tsaye ta ce. "Dan allah Ina ya Aliyu"
Babu wanda ya kullata a cikin su Fatima na ganin haka ta kwashe musu da dariya ta ce. "Yau la yi ya biyo ta kanku"
Ta na cikin dariyar ta ji motsin bude ƙofar toilet ai ko tayi tsitt kamar wanda ruwa ya cinye.
Aliyu ya shigo bayan ya yi sallama duk da yaga Fatima amman ya yi kamar bai ganta ba ya auce saman mirror ya dauƙo man shafawa ya aje ya nemi guri ya zauna,
Ya ɗauko wayar shi yana dannawa Fatima ta matsa kusa dashi ta ce.
"Ya Aliyu dan allah zan je gidan su Nusaiba na tambayi Mama bata ce mun komai ba"
Aliyu ko kallon inda take bai yi ba ballatana tasa ran zai bata amsa.
Amina ta hau murmushi tana yima Fatima gwalo Aliyu na kallonta shi koh Ismael tunda ya ga abinda aka yima Fatima ya aro na tsuwa ya yafa ma kanshi.
Aliyu ya kira Nasser a waya ya ce. "Idan zai dawo gida ya tsaya ya amso mai form guda 4 Na islamiyyar dake ƙasan layinsu"
Fatima na jin hakan ta fara tunanin zuci nasan wannan form din namu ne bana kowa ba.kuma nasan duk wa innan su ka ja mana.
Aliyu katse ma Fatima zancen zucin da ta ke ya ce.
"Ma Fatima ta fita ta bashi guri ba za taje ba kuma yana nan zuwa ya sameta"
Ai kafin ma ya gama rufe baki fitt ta fice a dakin daman neman hanyar guduwa ta kecyi.
Aliyu ya kalli Amina ya ce.
"Kema zamu haɗe dake sai na yi maganin ki"
Amina nacjin haka ta fara kuka ta na bashi haƙuri.
Aliyu ya daka mata tsawa ya ce.
"Ta fita ta bashi guri zai shigo gidan ya sameta" Amina da gudu ta bar ɗakin.
Aliyu ya kalli Ismael da ya yi fuskan tausayi ya ce.
"Kai kuma ka sameni anjima bayan sallahr la'asar"
Ismael ya yi waje yana sauke numfashi ya fita yana surutai wallahi unguwar ma zan bari gaba ɗaya ba gidan ba kuma sai kayi bacci zan dawo.
Aliyu ya gama shafa man ya samu kaya ma rasu nauyi ya sa ya koma ya kwanta ya rufe ido daga hakan bacci ya ɗauke shi.
Sai bayan la'asar ya tashi shima saboda kiran waya ne ya tayar dashi ya na duba time ya tashi a gurguje ya je ya yi alwala ya yi sallah koda ya idar bai tashi ba ya dauko Qur'ani ya fara karantawa cike da ƙwarewa ga muryan shi mai daɗin sauraro.
Aliyu matashine mai cike da haiba da kwarjini mahaifiyar shi ba fullatana ce ta asali domin danginta duk suna ruga Aliyu dogo ne mara kiba amman ba siriri bane yana da fadin ƙirji ga manyan idanu ga hanci har baka fuskan shi dai dai masha allah duk cikin su Aliyu yafi su haske.
Ya jima yana karatu kafin ya miƙe ya aje Qur'anin ya fita cikin gida ya shiga ya na shiga ya ji hayaniya a ɗakin Mama.
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oTRAYUWAR MU
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu 🥰
( Ta Batulu)
Haquri mai cimma rabo 🥰
Dukanin abinda haquri bai baka shiba rashinsa ma bazai taɓa baka,
Page 7-8
Shima ɗakin ya shiga bakin shi ɗauke da sallama yana shiga ya samu Nasser tare da umar da Fatima sun sa Mama a tsakiya su na ta fira.
Nasser ya na ganin Aliyu ya ce.
"Na shigo na samu ka na bacci ashe ka tashi"
Eh na ta shi daman gajiya ce kawai cewar Aliyu.
Umar ya ce.
"Barka da wannan lokacin ya haydar"
Aliyu ya yi murmushi ya rungume shi ya na cewa barka dai ƙanin yayan shi.
Daman wani lokacin haka suke kiran juna.
Aliyu ya kalli Nasser tun kafin ya yi magana Nasser ya ce.
"Umar jeka dau koh mun jakar da na shigo da shi.
Aliyu ya zauna kusa da Fatima da ta yi shiru tunda ya shigo.
Ya ce. " Ya akayi teemah?"
Haka ya ke kiranta wani lokacin.
Fatima ta yi murmushi bata ce komai ba.
Mama ta ce.
" Ba dole ta yi shiru ba zaki yazo gurin"
Ai shine dai dai dasu a gidan nan cewar Nasser
Shi dai Aliyu bai ce komai ba.
Umar ya shigo da sallama ya mika ma Aliyu jakan Nasser ya karɓa ya buɗe ya ciro baƙin leda ya mika wa Aliyu.
Umar ya ciro ruwa mai sanyi ya ɗauko kofi ya jawo table ɗin dake tsakiyar parlourn ya ɗaura ruwan akai ya aje a gaban Aliyu.
Nasser ya ce. "To sarkin iyayi"
Umar ya yi dariya ya zauna kusa da Aliyu Fatima ta tashi za ta shiga ciki.
"Dawo ki zauna" in ji Aliyu ba tare da ya kalleta ba.
Fatima ta dawo ta zauna
Aliyu ya fito da form din duka yaba Nasser ɗaya yaba Umar ɗaya itama Fatima ya ba ta ɗaya shima ya ɗau ɗaya.
Ya kalle su ya ce.
"Ku cike mun"
Ya kalli Nasser ya ce.
"Amina zaka cikewa"
"Kai kuma naka za ka cike" cewar Aliyu yana kallon Umar.
Tun kafin ya ce ma Fatima daman ta san na ta ne.
Aliyu ya kalli Fatima "Ke kuma fa daga baki abu har kin fara rubutu baki tsaya kin ji ko na waye ba"
Fatima ta yi dariya ta ce.
"Ai na san nawa ne shiyasa na fara cikewa"
Aliyu bai ce komai ba ya maida hankali akan form din gaban shi ya cike ma Ismael.
Ita dai Mama tana zaune ta na kallon su cike da sha'awar yanda suke kulawa da junan su ta na musu addu'ar su ɗore a hakan.
Bayan sun gama cikewa Aliyu ya kalli Fatima ya ce. "Tunda kun kusa gama makaranta zaku fara zuwa islamiyya ranar monday zan bawa Nasser kudi ya yanko muku uniform sai a bada ɗinki"
Umar ya ce.
"Yaya har dani?"
Aliyu ya kalli Umar ya ce.
" Ko ka girmi karatun ne?"
Nasser ya kwashe da dariya Umar ya ɓata fuska ya ce.
" A'a"
"To dukan ku zaku koma babu wanda na ware a cikin ku" cewar Aliyu.
Ya kalli Mama ya ce.
"Ba ki ce komai ba?"
Mama tayi murmushi "Mainene nawa a ciki bayan ka yi komai yanda ya dace ubangiji ya yi muku albarka" cewar Mama.
Dukan su suka amsa da ameen Aliyu ya ɗauki ruwan da Umar ya aje yasha ya ta shi ya yiwa.
Mama sallam ya fita ya na fita Umar ya je kusa da Mama ya ce.
"Da girma na za a kaini makaranta kamar wani yaro "
"Wato ita ka raina shi wanda ya yi maganar ka kasa faɗa a gabanshi" cewar Nasser.
Fatima tayi dariya ta ce. "Ƙyalle shi ya Nasser kamar a kunnen yaya"
"To munafuka sai kin dawo" cewar Umar.
Nasser ya kallesu dukan su ya ce. "Kun san wani abu?"
Suka ce a'a yaci gaba da cewa "Wallahi bro gata ya yi muku kai Umar ka gama makaranta kayi candy wannan shekaran mai ya rage maka?"
Umar ya hau washe baki "Saura jami'a"
Fatima ta ce. "Ai shi mafarkin shi kenan dama"
Nasser ya cigaba da cewa "Amman kasan ba kai tsaye bro zai barka ka tafi jami'a ba?"
Umar ya yi shiru sai Nasser ya cigaba da cewa "Ni dai shawaran da zan ba ka itace karka nu na mai baka son wannan makarantar daya saku idan kuma ka nu na mai baka so kasan abinda zai biyo baya"
Ya kalli Fatima ya ce. "Kema bakya so?"
Fatima ta ce.
"Banda zaɓi"
"Kin wuta ma kanki" cewar Nasser shima ya tashi ya yiwa Mama sallama ya fita.
Umar ya kalli Fatima ya ce.
"Wallahi Ismael nake tausayawa domin nasan baza su kwashe ta daɗin rai ba shida yaya"
Fatima tayi dariya ta bashi labarin abinda ya faru ɗazun.
Shima dariyan ya yi ya ce. "Anjima akwai kallo"
Dukan su har yanzu basu san halin yaya ba.
Umar ya ce.
"Na tina wani mari da ya taɓa mun sai da na suma"
Fatima tayi dariya Mama ita kanta sai da ta dara Fatima ta ce. "Nidai karka ƙullar mun da ciki bari in ɗauko assignment ɗina dan allah"
Fatima ta shiga ciki ta fito da jaka ta aje a gaban shi ta ce mishi ya koya mata ne.
Fatima ta na da wani ɗabi'a guda ɗaya ita ko abune bata iya ba bata cewa ayi mata sai dai ta ce a koya mata saboda gaba.
Umar ya sau koh ƙasa ya zauna itama ta zauna a kusa dashi ta bude littafin ta suka fara,
Fatima tana SS two ne going to three ita kuma Amina JSS one
Ismael kuma tare suka zana jarabawa da Umar duk da shi zana mishi a kayi Umar kuma yafi son ya zana da kanshi.
Nasser kuma degree yake ɗaurawa a cikin garin jos yana karantar fannin lafiya sannan ya iya gyaran wayoyi
Yana zama a shagon abokin shi idan ya dawo makaranta.
shi kuma Umar shagon ɗinki yasa Aliyu ya kai shi yana koyan ɗinkin keke.
Bayan sun gama assignment din Umar ya tashi ya ce.
" Mama bari in je shagon mu in dawo"
Mama ta ce.
"Yamma ya yi sallah ake shirin kira"
"Ba zama zanyi ba yanzu zan dawo" cewar Umar.
Mama ta ce.
"Adawo lafiya"
Fatima ta kwashe jakanta da da form din da suka bari a parlourn ta shiga dasu ciki ta zuba su a cikin jakan ta na makaranta ta shiga toilet ta yi alwala ta dau Qur'ani ta fito parlour ta zauna kusa da Mama a saman darduma irin darduman nanne mai girma da taushi.
Mama ta tashi ta shiga ciki Fatima kuma ta fara karatu cike da natsuwa Fatima bata da tsawo kamar ƴan uwanta sannan kuma ta na da jiki ga diri masha allah ta na da hanci sosai .
Daman duk ƴan dakin Mama su nada hanci kuma itama Mama bata da tsawo kamar dai Fatima amman dukan su suna kama da juna.
Bata jima da fara karatun ba aka kira sallah ta rufe Qur'anin ta tashi Mama ta fito daga bedroom ta hau darduman suka bi jam'i.
Bayan an idar Fatima ta kwaso littafan ta na addini tazo Mama ta na mata bita sun jima a haka kafin Fatima ta mayar da littafan tazo ta fara azkar.
Bayan ta idar ta ɗauko chasbi ta naja har aka kira sallahr Isha'i bayan sun idar da sallah su kayi nafila sannan Fatima ta tashi ta je kitchen.
Ta na zuwa ta samu Amina zata shiga ɗauko abincin Baffa Fatima na ganin haka ta bata guri ta huce itama ta shiga ta ɗauko abincin su ta koma ɗaki.
Tana shiga Umar na shigowa shida Nasser suka gaida Mama suka zauna Fatima ta koma kitchen ta kwaso plate da spoon ta aje.
Bayan ta aje ta shiga bedroom tana shiga Umar ya miƙe yana cewa "Daɗin abun dai muna da hannu"
Mama da take gefe ta yi murmushi Nasser kuma yace "To acici mala'ikun tauna"
Fatima dake fitowa ta yi dariya tace "Wallahi kuma sunan ya dace dashi"
Umar bai tanka musu ba ya buɗe kular abincin shinkafa ne jallop na manja da wake, ya zuba a plate ya koma ya zauna.
Fatima ta buɗe fridge ta ɗauko zoɓo da ruwa ta aje mishi Umar ya ce. "Kinyi taimako domin bana gane baƙin karatun shiyasa ban tsaya naiman ruwa ba"
Fatima ta kalli Nasser "In zuba maka abincin? "
Nasser ya ce. "A'a sai bro ya shigo"
Daman ta yi tunanin haka indai suna gida basu cika cin abinci ba tare ba.
Ta ɗiba ta koma kusa da Mama ta zauna ta faraci da bismillah bata ci da yawa ba ta tashi ta shiga ciki ta fito da roban yaji.
Umar na ganin haka ya ce.
" Daman tun ɗazun nake tunanin in da zan samu yaji"
Dukan su suka hau dariya saboda tunda ya fara cin abinci bai yi magana ba.
Fatima ta ɗiba ta aje mishi roban yajin a gaban shi.
Mama ta ce. " Fatima idan kin gama ki ɗaura mun lipton "
Fatima ta ce. "Ai muna dashi a cikin flask"
Idan kin gama ki zuba mun Aliyu ya shigo bayan ya yi sallama hannun shi riƙe da baƙin leda.
Yana zuwa ya mika ma Fatima.
Ya gaida Mama ya zauna kusa da Nasser suka gaisa Umar kam sai da ya gama cin abinci sannan ya ce.
"Sannu da zuwa"
Aliyu ya yi murmushi "An gaishe da acicin gidan mu" cewar Aliyu.
Umar ya ce. "Kuma banci da yawa ba domin nasan zaka dawo mana da tsaraba"
Fatima da ke shigowa ɗakin ta ce. "Kaji tsoran allah ya Umar duk irin abincin da kaci"
Umar ya kalleta ya ce. "Ina ruwanki dani"
Nasser ya ce. "Haba Fatima ya za ki tona mishi asiri"
Mama tayi dariya ta ce.
"Karku tasa mun yarinya a gaba"
Fatima ta zauna bayan ta shigo da babban plate ta juye abinda Aliyu ya shigo dashi nama ne mai yawa sai ƙamshi yake tashi.
Fatima "Ɗibarwa Inna ki kai mata" cewar Mama.
Fatima ta dau plate guda ɗaya acikin wanda ta kwaso domin suci abinci ta ɗibo naman aciki ta fito.
Ta shiga ɗakin Inna bakinta ɗauke da sallama Inna ta amsa sallamar ta ɗauke kai.
Fatima ta ce. "Barka da dare Inna gashi inji mama tsaraban ya Aliyu"
Inna ta ce. "Ajiye a nan kice angode"
Fatima ta fita daga ɗakin tana fita Amina ta sauko da sauri tazo ta bude plate ɗin ta ga nama ne aciki.
Inna ta ce. "Amman baci za kiyi ba koh?"
Amina tasa hannu ta faraci ta yi banza da Inna.
Amina ta na cikin cin namar Ismael ya shigo babu sallama bai ce musu komai ba ya zauna kusa da Amina yasa hannu acikin plate ɗin namar
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oTRAYUWAR MU
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Written by ✍️
SA'ADATU I FULANI
(Ta Batulu)
Page 9-10
Inna ta kalle su ta ce.
"Amman baku da zuciya"
Babu wanda ya kalle ta sai da suka gama cin namar Ismael ya kalli Amina ya ce.
"Zuba mun abinci"
Amina ta yi banza dashi ta tashi zata fita.
Inna ta kalli Amina ta ce.
"Ba kiji abinda ya fada bane ki ka tashi za ki fita"
Amina ta tura baki
"Bana son irin wannan halin naki ace keda ɗan uwanki baza ku haɗe kanku ba" cewar Inna.
Ismael ya kalli Inna ya ce.
"Wallahi wata rana sai na karya wannan yarinyar ace yarinya gaba ɗaya ta raina mutane"
"Wallahi bana jin daɗin yanda ku keyi kamar wasu kaji dan allah ku haɗe kanku" cewar Inna.
"Isma'eel kaine babba dan allah ka ja girmanka ke kuma Amina bana son rashin kunya shiɗin yayan kine ki daina mishi irin wannan halin"
Amina ta tura baki tashi ta je ta zubo mishi abincin ta aje a gaban shi ta shige bedroom.
Shima ɗakin irin na Mama ne komai da komai sai dai yana yin kayan ɗakin daban ɗakin duk ya yi ƙura kamar babu masu rayuwa aciki.
Inna akwai ƙazanta kuma ta koya ma ƴarta.
Domin tarbiyya ana koya ne daga uwa ba daga uba ba.
Tarbiyan uwa da ban na uba daban duk yanda kike yi a gidan mijinki itama ƴarki haka za tayi a gidan nata mijin ubangiji ka datar damu allah ka haɗamu da iyaye na gari.🙏
Inna ta kalli Isma'eel yana cin abinci ta ce. " Ya maganar makaranta nifa na gaji da ganinka a haka bokon baka mayar da hankali ba islamiyyar ma haka gashi kowa yana zuwa gurin sana'a amma banda kai"
Isma'eel ya ce.
"Nifa bana son wahala ne shiyasa kuma ni nagama makaranta sana'a kuma ina tunanin wanda zai dace dani Inna ki daina damun kanki a kaina"
Ya na gama fada mata haka ya yi waje Inna ta yi "Ƙwafa za ka dawo ka same ni"
Ɗakin Mama bayan sun gama cin abinci Mama ta kalli Aliyu ta ce.
"Karka manta da maganar mu ta ɗazun"
"Bazan manta ba in sha Allah" cewar Aliyu.
Suka taɓa fira da ƴan uwan shi yana jadadda musu maganar tafiyan su islamiyya babu fashi su zauna cikin shiri.
Ya yi musu sallama ya fita yana fita Naseer shima ya yi musu sallama ya fita
Aliyu ɗaki ya shiga ya ƙara shiryawa ya fita.
Mama ta ce wa Umar ya duba mata dakin Baffan su idan yana nan
Ya na fita ya ga Inna ta na tsaye a bayan windows din ɗakin su.
Ta na ganin Umar ya ganta ta fara borin kunya ta na ta zagin shi.
Umar bai ce mata komai ba ya wuce
Mama ta na jinsu.
Umar ya shigo da sallama ya ce.
"Fatima ta kai wa Baffa lipton"
"Ki kai mishi wanda kika zuba mun idan kin dawo kya zuba mun wani" cewar Mama.
Umar ya ce.
"Bari in zuba miki"
Ganin haka Fatima ta ɗauki na Baffa ta fita.
Fatima tayi sallama ɗakin Baffa baffa ya amsa ya bata izinin shigowa.
Ta na shiga Inna ta shigo babu ko sallama Fatima ta yi kamar bata ganta ba ta je gaban Baffa ta mishi barka da dare ta aje kofin ta tashi ta fita.
Inna ta kalli Baffa ta ce.
"Wannan zalunci ne ba adalci ba Allah ya na gani wallahi sai ya yi mun sakayya"
Harta gama maganar ta Baffa bai ce mata komai ba sai ma tashi da ya yi ya shiga ciki hannun shi ɗauke da kofin da Fatima ta kawo.
Inna ta yi kwafa ta ce.
"Wallahi zaka dawo ka same ni"
Fatima ta shiga ɗakin su bakinta ɗauke da sallama ta samu Umar suna fira da Mama ta zauna suka cigaba da firan da ita.
9:30pm
Baffa ya shigo ya zauna suka ɗan taɓa fira ya yi musu sai da safe.
Ya na fita shima Umar ya tashi ya yi musu sallama ya tafi ɗakin su.
Mama tayi alwala ta hau darduma Fatima tayi alwala ta kwanta.
Agurguje anyi auran Amina da Aliyu mallam ya basu gidan zama amma ba unguwa ɗaya suke ba.
Umar ya tafi jami'a Fatima anyi mata baiko da saurayin da Baffa ya zaɓa mata.
Duk da Aliyu baya gidan suna zuwa islamiyyar da ya saka su.
Amina rashin kunya ya ƙaru tunda mai tsawatar wan ya bar gidan.
Ismael Baffa ya kai shi garin zaria karatu bayan ansha fama da Inna.
Yanzu gidan daga Fatima Amina Nasser sannan Umar.
Fatima tayi candy Baffa ya ce. " Ta hakura idan ta je ɗakin mijinta taci gaba a can"
Yanzu Amina kaɗai ke zuwa school itama ba kullum ba.
Gidan Aliyu zama suke cike da farin ciki da jin daɗi.
Amina ta na girmama shi suna son junansu sosai gashi allah ya fara dafa mishi mai gidan shi ya bashi shago ya zuba mishi kaya
Ya ce.
"Kuɗin kayan shagon kawai zai bashi ya riƙe ribar shima ya kula da kanshi tunda yanzu ya aje iyali"
Bayan shekara uku anyi auren Nasser da budurwan shi maryam har ma ta na da ƙaramin ciki.
Nasser ya gama makaranta ya kama sana'ar wayoyi a shagon da Aliyu ya buɗe mishi.
Shima Baffa ya bashi gida kusa da Aliyu daman gidan ya siyan musu ne idan sun tashi aure su zauna ciki.
Fatima tayi Aure da mijinta Abubakar yana sai da motoci suna zaman lafiya da mijinta domin Fatima sak halin mahaifiyarta ne.
Abubakar yana sonta sosai kuma yana kulawa da ita yanda ya dace.
Umar yana cigaba da karatu Isma'eel kuma yana zaria yana zare ido😂.
Mama ta ɗauko ƴar ƙanwarta mai suna Rabi'a ta na taya ta zama.
Amina kuma a na ta tara samari a ƙofar gida tun Baffa na faɗa uwarta na kareta ya gaji ya sama ta ido.
A cewar inna gwanda ta zaɓa ta darje ta samo wanda yafi mijin Fatima kuɗi.
Gidan Aliyu suna rayuwa cike da farin ciki yarinyar su ɗaya mai sunan Mama suna cemata Shukrah yarinya mai kama da babanta sakk duk da itama uwan ba baya ba gurin kyau
Amman idan ka ga Shukrah kana ganinta ka san waye babanta
Shekarun Shukrah 3 a duniya Fatima tana son Shukrah sosai shima Baffa yana sonta domin itace jika na farko agurin shi kuma ta fito daga gurin ɗa mafi soyuwa a zuciyar shi.
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu 🥰
(Ta Batulu)
*Page 11-12
Bayan wani lokaci abubuwa da yawa sun faru dawowar Isma'eel gida auren Amina Umar ya kammala karatu ya samu aikin a banki.
Fatima ta haiwu na miji sunan shi Aliyu suna kiran shi Sajjad.
Matan Nasser ma ta haiwu mace sunan yarinyar Khadija.
Yaran Aliyu biyu bayan Shukrah sun ƙara samun Sa'adatu suna ce mata Darraini sai da aka haifi Darraini sannan aka haifi Khadija.
Tsufa ya kama Baffa sosai domin yanzu yaran suke riƙe da gidan.
Amina ta yi aure bayan ta gama ruwan ido ta zaɓo wani mai suna Sager suna zaune a cikin garin jos yana sana'ar sai da takalma.
Shima Naseer kudi sun fara zama.
Matar Aliyu da matan Nasser kan su a haɗe yake duk da ka san cewar ba gida ɗaya suke zaune ba amman suna zaman lafiya babu mai jin kan su.
Aliyu ya gina gidan shi mai kyau sun tare plat biyu sai nashi plat ɗin daban.
Kowani plat two bedroom ne kowanne da toilet aciki sai kitchen a parlourn gidan yasha tayis ga famfo harda gate.
Yanzu haka shagon Aliyu biyu ɗaya a garin su ɗayan kuma a jos.
Ya na ta tunanin ya ɗaura Isma'eel a shago ɗaya tunda duk cikin su kowa ya na da abinyi amman banda shi.
Saboda yaƙi karatu ko yanzu da ya dawo gida babu abinda yake yi face zaman majalissa.
Aliyu ya tara ƴan uwan shi ya faɗa musu abinda ke cikin zuciyar shi game da Isma'eel
Naseer ya ce.
"Ashawarce ka fara jaraba shi ka bashi jari ko treda ka buɗe mishi ka ga kamun kan shi kar kaje ka ɗaura shi a kan dukiyar ka a samu matsala"
Shima Umar ya goyi bayan Nasser Aliyu ya ce.
"Zanje gida anjima gurin Baffa za muyi magana"
Daga haka ya sallame su kowa ya kama gabanshi.
Da daddare Aliyu ya shirya tsaff zai je gida Amina ta ce.
"Dan allah zata bishi domin ta kwana biyu bata je ta gaida Baffa ba"
"Kiyi sauri inajiranki karki ɓata mun lokaci" cewar Aliyu.
Amina bata jima sosai ba ta fito hannunta riƙe da Darraini ɗayan kuma leda ne mai ɗan girma tana tafe Shukrah na binta a baya.
Aliyu ya ɗauki Shukrah ya fita yana cewa Amina ta same shi a waje.
Daman lokacin auren Amina ya sai mashin.
Amina ta na fitowa ya sa Shukrah a gaban mashin ya goya Amina hannunta ɗauke da Darraini suka tafi.
Bayan sun isa gida ya aje mashin ɗin ya riƙe Shukrah suka shiga cikin gida bakin su ɗauke da sallama.
Babu kowa sai Isma'eel a tsakar gidan shima yana ganin su ya fara zare ido ka na ganin shi kaga mara gaskiya.
Aliyu ya yi kamar bai ganshi ba Shukrah ta ƙwace hannunta ta shige ɗakin Baffa tana kiran sunan shi.
Amina ta nufi ɗakin Mama hannunta ɗauke da Darraini.
Aliyu ya kalli Isma'eel ya ce.
"Mai ka keyi a nan?"
Isma'eel ya yi ƙasa da kai "Babu komai" cewar shi.
Aliyu ya ce.
"Ka ji rani in fito ina neman ka tunda kai baka zumunci da kowa"
Aliyu bai jira cewar shi ba ya wuce ɗakin Baffa ya yi sallama ya shiga ya samu Shukrah ta haye jikin Baffa ta na ta surutu.
Aliyu ya na mamakin yanda Shukrah take sa kewa da Baffa duk da cewa bata yawan ganinshi.
Shukrah bata da yawan magana duk da kasan cewar Aliyu muskili ne amman Shukrah tafi shi ita ko magana kayi mata idan bai mata ba ko kallonka baza tayi ba.
Amman idan ka ji zancen ta tazo gurin Baffa ne idan ka ji dariyar ta mai yawa ta na tare da Baffa.
Aliyu ya kalli Baffa ya na zaune yana jan charbi duk ya tsufa domin wani lokacin ko fita ba ya yi Aliyu ya gaishe shi ya mishi ya jiki.
Baffa ya ce. "Jiki alhamdulellahi"
"Daman wata magana ne ke tafe dani" cewar Aliyu yana fuskantar Baffa.
"Inajinka" cewar Baffa ya na gyara zama.
Aliyu ya faɗa mishi shawaran da suka yanke da ƴan uwan shi.
Baffa ya yi farin ciki sosai ya yi murna daman abin yana damun Baffa zaman shi a haka babu sana'a tunda shi yaƙi yin karatun gaba ɗaya.
Sauƙin ta ɗaya ma daya kai shi zaria babu laifi ya yi karatu domin har sauka ya yi.
Baffa yasa musu albarka dukan su sannan ya ƙara da nasiha kamar yanda ya saba,
Baffa yana yawan gaya ma Aliyu yaji tsoran allah ya kula da hakkin iyalin shi karya zalunce su domin suɗin amana ne a gurin shi kuma za a tambaye shi yanda ya tafiyar da wannan amanar da aka bashi.
Aliyu ya yi ƙasa da kai ya ce.
" In sha allah zanki ya ye nagode Baffa allah yaƙara nisan kwana"
"Jeka gaisa da mutanan gidan kazo ku tafi gida kar dare ya yi muku a hanya" cewar Baffa.
Aliyu ya fita ɗakin jiki a san yaye saboda har yanzu ya kasa sabawa da wannan nasihar na Baffa gani yake kamar nasiha yake barin mishi.
Aliyu ɗakin Inna ya shiga bayan ya yi sallama aka amsa ya shiga ya zauna a ƙasa ya gaishe ta.
Ita fa har yanzu Inna bata sanja halin ta ba domin duk cikin yaran Baffa kishi take da Aliyu sosai.
Inna ta amsa tana washe baki ta ce.
" Ina rigimammiyar ƴarka?" Sunan Shukrah kenan a bakin Inna.
Saboda Inna Shukrah bata son zuwa gidan domin jinin su bai haɗu ba.
Bayan sun gama gaisawa ya tashi ya fita Inna ta bishi da harara.
Aliyu ya yi sallama ɗakin Mama ya sameta a zaune Amina tana shafa mata man zafi a ƙafafun ta.
Amina tana ganin ya shigo ta ce. "Bari inje in gaida Baffa"
Daga nan kya tawo da sarkin rigima cewar Mama.
Amina tayi murmushi ta fita.
Ɗakin Baffa ta shiga bayan ta yi sallama yanda Aliyu ya barsu shida Shukrah haka ta same su.
Amina ta duƙa har ƙasa ta gaida Baffa ta yi mishi sannu da jiki Baffa ya amsa da "Jiki ya warware"
Baffa ya kalli Amina ya ce.
"Dama ina neman ki"
Amina ta yi ƙasa da kai tana cewa "Allah yasa ba ƙarana Shukrah ta kawo gurinka ba"
Baffa ya yi dariya yana cewa "Amana nake son baki"
Amina tayi shiru tana sauraron Baffa.
Baffa ya yi ƙasa da kai murya cike da rauni ya ce.
"Amina dan Allah ko bayan raina kiyi mun alƙawarin za ki zauna da Aliyu duk yanda yake"
Amina ta yi tsit kamar wanda ruwa ya cinye Baffa yaci gaba da magana "Amina akwai tarin ƙalubale a gabanki"
"Kinga Aliyu duk cikin ƴaƴana yana da wata ɗabi'a wanda ba kowa ya san da ita ba amman ina da tabbacin kinsan da wannan ɗabi'ar tashi"
"Ki rage bacci domin akwai aiki mai tarin yawa a gabanki sannan ki kula da yaranki duk rintsi karki bari tarbiyan yaranki ya lalace duk tsanani yana tare da sauƙi"
Baffa ya shiga daga ciki ya fito hannun shi ɗauke da wani babban gora yazo ya zauna inda ya tashi.
Ya miƙa ma Amina ta karɓa hannu biyu jikinta yana rawa.
Baffa ya ce.
"Rubutu ne a ciki ina so kiba yaran ki su sha kema kisha shima Aliyu kiba shi yasha"
Amina ta yi godiya ta tashi ta je ta ɗau Shukrah da ta fara bacci a jikin shi ta yi mishi sai da safe har ta kai bakin ƙofa Baffa ya kirata.
Amina ta dawo ta zauna Baffa ya ce.
"Ki ƙara haƙuri a kan wanda ki ke dashi kuma kiya haƙuri da duk abinda za ki gani a cikin rayuwarki kuma ki ƙara riƙe sirrinki da kyau duk abinda zaki gani ki ya haƙuri komai zai wuce"
Amina ta kasa magana "Za ki iya tafiya" cewar Baffa.
Bayan fitan Amina Baffa ya yi murmushi tabbas ubangiji baya zalunci kuma baya barin azzalumi.
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu 🥰
(Ta Batulu)
*Page 13-14
Bayan Amina ta fito daga ɗakin Baffa ta ɓoye jarkan da ya bata a cikin hijjab ta nufi ɗakin Inna.
Ta shiga bakinta ɗauke da sallama ta samu Inna zaune a kujera suna fira da Isma'eel.
Amina ta zauna ta gaishe da Inna Ismael ya gaishe ta Amina ta ce.
"Ba zan amsa ba saboda tun da ka dawo ban ganka a gidana ba"
"In sha allah zan zo gobe idan allah ya kaimu" cewar Isma'eel
Amina ta ce.
"Allah ya kawo ka lafiya"
Inna ta kalli Shukrah dake ka faɗar Amina tana barci ta ce.
"Sarkin rigima ta yi bacci"
Amina ta ce. "Eh"
Idanun Inna yana kan hannun Amina tana son ganin abinda ke ɓoye a hannunta saboda ta san daga ɗakin Baffa ta shigo.
Amina ta yi kamar bata ganta ba hassalima da ta ga kallon ya na yawa ta tashi ta yiwa Inna sai da safe ta fita.
Ɗakin Mama Amina ta shiga ta samu Aliyu da Umar suna zaune suna fira.
Aliyu yana ganin Amina ya ce.
"Daman ke nake jira mu wuce"
" Aunty na ni ka ɗai barka da dare"
Amina ta yi dariya ta kalli Umar ta ce.
"Allah ya shirya mana kai"
Umar ya yi dariya.
Aliyu ya ce.
"Karki biye ma wannan sarkin surutun kinga dare ya yi ga Shukrah ma tayi barci zo mu wuce gida"
Mama ta fito daga bedroom hannunta riƙe da leda taba Amina.
Amina ta duƙa har ƙasa ta karɓa ta na godiya Aliyu ya karɓi Shukrah Umar ya ɗau Darraini dake barci suka fita.
Sun fita suka ga Inna a bakin window ta na tsaye.
Dukan su sun ganta amman suka nu na kamar basu ganta ba domin idan da sabo sun saba da halinta
hatta Amina ta san halin Inna.
Bayan sun fita Aliyu ya kalli Umar ya ce.
"Ka gayawa Isma'eel ya same ni a gida gobe idan Allah ya kaimu"
Aliyu ya karɓi Shukrah Amina ta karɓi Darraini a hannun Umar suka tafi.
Sun isa gida Amina ta kwantar da Shukrah a ɗaya bedroom ɗin da suke kwana ita da ƙanwarta ta yi wanka tasa kayan bacci ta tsaya tana ma Shukrah addu'a.
Aliyu kuma ya wuce da Darraini bedroom ɗin su ya kwantar da ita ya shiga toilet ya yi wanka yasa kayan bacci ya yi addu'a ya kwanta.
Amina ta shiga ɗakin bayan tayi sallama Aliyu har ya yi bacci Amina ta zuba mishi ido tana kallon shi.
Ta na nazarin maganar Baffa tabbas akwai abinda yake shirin faruwa da rayuwar su.
Ita da kanta ta san Aliyu yana da yawan ɗaukar maganar mutane koda kuwa ba gaskiya suka fada mishi ba sannan akwai shi da yarda da abinda yaran shi suka faɗa mishi koda ƙarya ne sai ya hau kai ya zauna ya yi ta faɗa kamar zai ari baki.
Amina ta daɗe a zaune tana tunanin maganar Baffa tabbas ta san akwai dalilin da yasa Baffa ya faɗa mata wannan maganar.
A ƙarshe dai ta yanke shawaran zata tsananta addu'a koma mainene yazo musu da sauƙi.
Darraini ta farka daga bacci ta na kuka Amina ta ɗauke ta shiga da ita toilet ta yi fitsari tasa mata pampas ta haɗa mata tea ta bata bayan ta gama sha ta kai ta bedroom ɗin su ta sama ta kaya ma rasu nauyi ta kwantar da ita kusa da Shukrah.
Har ta fita ta dawo ta ɗau Shukrah ta shiga da ita toilet tayi fitsari ta sanja mata kaya ta kwantar da ita ta ƙara musu addu'o'i ta jamu su kofar ta fita.
Kitchen ta shiga ta haɗo lipton ta zauna a parlour tana sha ta na tunani parlourn ya na ɗauke da saitin kujeru pink da fari ga ƙaton carpet a tsakiya shima pink da fari.
Lokacin da zasu tare Aliyu ya sanja mata kayan ɗaki komai na parlourn pink da fari ne kayan kallo fridge ɗin su babba show glass masha allah komai ya ji a parlourn.
Gaba ɗaya jikin Amina ya yi sanyi gashi Baffa ya ce ta ƙara riƙe sirrinta.
Babu wanda zata iya shawara dashi bata da ƙanwa ko ɗaya mahaifiyarta ta rasu bayan haihuwar Shukrah bada jimawa ba.
Sunan Darraini sunan mahaifiyar ta ne suke kiranta da suna Darraini Saadatul Darraini.
Amina ta kai wajen ɗaya da wani abu a zaune, kafin ta shiga bedroom ta yi alwala ta shimfiɗa darduma ta fara sallah.
Bayan ta idar ta ɗauki Qur'ani ba ta tashi a gurin ba sai da aka kira assalatu.
Amina ta shiga kitchen ta na shiga suka kawo nepa ta jona kettle ta ɗau plas ɗin ruwan zafi ta fita.
Bedroom ɗin su ta shiga ta aje plas ɗin ta shiga toilet ta ɗauko bucket ta juye ruwan plas ɗin ta shiga wanka bata jima sosai ba ta fito ta zauna a gaban mirror ta na shafa lotion.
Simple make-up ta yi ta sa doguwar riga ta fesa turare tayi ɗaurin ɗankwali ta yi kyau sosai.
Ta je gaban gado ta na cewa.
"Abban Shukrah lokacin sallah ya yi"
Aliyu da ya jima da farkawa tun kafin ta shiga wanka ya ƙura mata ido ya kasa cewa komai Amina ta tashi zata fita.
Aliyu ya ce.
"Zo kiji wata magana"
Amina ta yi hanyar barin ɗakin tana cewa
"Zaka rasa jam'i"
Ta fita ɗakin ta leƙa bedroom ɗin su Shukrah suna ta barci ta ja musu ƙofar ta fita kitchen ta koma ta samu ruwan da ta jona ya na tausa.
Ta koma ɗaki ta samu Aliyu har ya yi alwala zai fita massalaci ta ce.
"A dawo lafiya"
Ta ɗau flas ɗin ta koma kitchen ta juye ruwan ta ƙara jona wani ruwan ta fita ta koma bedroom daman bata ɗauke darduman da ta yi sallah a kai ba tana shiga a ka tayar da sallah.
Daga masallacin zuwa gidan su babu nisa gida uku ya raba.
Amina ta idar da sallah ta yi addu'o'i ta yi azkar bayan ta idar ta fita ta koma kitchen ta na zuwa ta samu ruwan ya tausa.
Ta kashe jikin socket ɗin ta fita ta koma ɗaki ta shiga toilet ta ɗauko bucket ta shiga kitchen ta juye duka ruwan zafin a ciki ta ƙara jona wani ruwan ta ɗau bucket ɗin ta fita.
Bedroom ɗin yaran ta shiga ta tayar da Shukrah ta shiga da ita toilet ta wanke mata baki ta yi mata wanka tasa ta ta yi alwala bayan ta yi ta ɗaura mata ɗaya daga cikin towel ɗin dake ra taye a toilet.
Amina ta fito Shukrah na biye da ita a baya Shukrah ta zauna saman ƙaramin kujeran dake gaban mirror Amina ta buɗe man shafawa ta miƙa wa shukrah.
Ta ɗauki Darraini ta shiga da ita toilet ta cire mata pampas ta yi mata wanka ta wanke mata baki ta ɗauko ta suka fito.
Amina ta na fitowa ta samu Shukrah tasa uniform ɗin school ta na sallah da hijjab ɗinta har ƙasa.
Ta aje Darraini ta fita ta koma kitchen ta samu ruwan ya tausa ya kashe kanshi ta koma toilet ta ɗauko bucket ta juye ruwan zafin ta fita dashi.
Bedroom ɗin yaran ta leƙa ta samu Shukrah na shafama Darraini cream daman ta saba shirya ƙanwar na ta ganin Shukrah ta rage mata aiki
Amina ta yi hanyar bedroom ɗin su hannuta ɗauke da ruwan zafi.
Ta samu Aliyu zaune a saman darduma yana karatu.
Amina ta shiga bayan ta yi sallama toilet ta shiga ta ƙara wankewa saboda lokacin da za ta yi wanka ta wanke shi ta ɗauko bucket ɗin da ruwan zafin yake ciki ta shiga dashi toilet ta aje ta janyo ƙofar ta fito.
Ta samu Aliyu zaune ya na kallon ƙofar toilet.
Amina ta je kusa dashi ta duƙa ta gaishe shi Aliyu yasa hannu ya jawota jikin shi ya ce.
"Sannu da ƙoƙari matar aljanna"
Amina ta ɓata fuska ta ce.
" Baka amsa gaisuwata ba"
"Na yi kewarki da yawa" cewar Aliyu.
Amina za ta yi magana ta ji sallamar Shukrah a bakin ƙofa Aliyu ya amsa sallamar.
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu 🥰
(Ta Batulu )
*Page 15-16
Amina ta tashi a jikin Aliyu sannan ya basu izinin shigowa.
Shukrah ta shigo Darraini na binta a baya da uniform ɗin school Aliyu ya kalli Amina ya ce.
"Madam kin manta yau monday baki bamu breakfast ba"
Amina ta ce.
" Ruwan wankan ya na jiranka a toilet"
Shukrah ta duƙa har ƙasa ta gaishe da Aliyu sannan ta gaida Amina
Darraini itama tayi kamar yanda ta ga Shukrah ta yi.
Amina ta ce.
" Shukrah zo muje kitchen"
Darraini ta zauna ta jira mu
Aliyu ya ce.
"A'a karki
ƙona mun yarinya"
Amina ta yi dariya ta riƙo Shukrah suka fita
Aliyu ya aje Darraini a saman gado ya shiga toilet.
Amina taba Shukrah kayan miya ta gyara mata.
Ita kuma ta haɗa tea a ƙaramin cup ta fita bedroom ta shiga ta ɗauki Darraini da ta fara bacci ta fara bata tea saboda ita bata da juriyan yunwa.
Bayan ta gama bata tea ta kwantar da ita ta fita ta koma kitchen ta samu Shukrah har ta niƙa mata kayan miyan a greater.
Amina ta kunna gas saboda sun kashe wuta ta kwaso kayan ƙamshi ta zuba a tukunya tasa sugar tasa ruwa ta ɗaura a wuta.
Shukrah ta fita daga kitchen ta yi sallama ta shiga ɗakin Amina.
Amina ta cigaba da aikin ta bayan ta sauke ruwan shayin ta ɗauko wani flas ɗin ta juye wannan ruwan zafin a ciki.
Ta ɗaura tukunya a wuta ta zuba mai ta soya kayan miya ta yi sanwa tasa spices ta rufe tukunyar.
Sannan ta koma parlour ta fara gyarawa ka san cewar babu datti sosai yasa ba a ɗau dogon lokaci ba ta gama gyarawa ta sa turare ta koma kitchen ta samu ruwan ya tausa.
Ta kwaso indomie ta zuba ta rufe tukunyar ta kwaso albasa tana yanka bayan ta gama yan kawa ta zuba a ciki ta rufe ta yi ƙasa da wutan ta fita.
Bedroom ɗin yaran ta shiga ta gyara tasa turare ta kwaso musu jakan makaranta ta ɗauko darduman da suke shimfiɗawa idan zasu ci abinci ta rufe ɗakin ta fito.
Parlour tazo ta aje kayan hannunta ta kira Shukrah tazo ta fara kwaso cups a kitchen.
Ita kuma ta shimfiɗa darduman ta shiga ɗaki ta samu Aliyu zaune Darraini tacna jikin shi yana mata wasa Amina ta ce.
"Abban Shukrah komai ya yi ready"
Aliyu ya ɗauko Darraini ya fito Amina kuma ta ɗau flas ɗin data aje ta fita.
Amina kitchen ta shiga ta aje flas ɗin ta sauke girkin ta ɗauko plas ɗin Darraini na school ta zuba mata indomie sauran ta juye a plate guda biyu.
Shukrah ta shigo kitchen Amina ta bata kayan tea ta je ta aje a saman darduma.
Amina ta fita da plates ɗin data zuba indomie.
Ta samu Aliyu zaune a saman darduman da suke cin abinci ya na haɗawa Shukrah tea
Amina ta aje plate ɗin ta ɗau cup ta na haɗa wa Aliyu nashi.
Shukrah abinci bai dame ta ba domin ko school bata zuwa da abinci sai dai drinks da biscuits.
Bayan sun gama breakfast Aliyu ya tafi kai yara school Amina ta ƙara gyara gurin ta yi wanke wanke.
Ta shiga toilet ɗin yara ta wanke ta fita ta koma bedroom.
Ta zauna zaman make-up ta yi kyau sosai ta samu kaya riga da wando tasa Amina akwai diri ga idanu dara dara masha allah.
Bayan ta gama ta ƙara gyara bedroom ɗin har toilet sai da ta ƙara gyarawa ta ɗau rigan da Aliyu ya cire ta haɗa da na ta tayi waje.
Bedroom ɗin su Shukrah ta shiga tasa musu turare ta shiga toilet ta ɗauko bucket ta kwaso kayan da suka cire ta haɗa da na hannunta ta fito dasu.
Ta za gaya ta baya inda igiyar shanya yake ta aje wankin ta fita ta koma toilet ɗin su Shukrah ta ɗauko sabulun wanki da omo ta fito.
Ta zo ta fara wankin bata daɗe ba ta gama saboda kayan babu datti a jiki ta shanya ta wanke buckets ɗin da tai wanki ta koma ciki.
Ta aje su a inda ta ɗauko su ta ɗau wayarta ta koma parlour ta zauna.
Ta na chart ta ji sallamar Aliyu kallo ɗaƴa ta yi mishi ta ɗauke idon ta bayan ta amsa sallamar.
Aliyu da sauri ya shigo ya zauna kusa da ita ya ce.
" Haba madam irin wannan kwalliyar haka ko kin manta yau monday ina da ayyuka da yawa?"
Amina ta juya ido ta ce.
"Allah ya kiyaye hanya ranka ya ɗaɗe mijin Amina"
Aliyu ya ce.
"Ai yau babu inda zani madam"
Amina tayi dariya bata ce komai ba.
Aliyu ya ce.
"Daman shekarun Darraini 4 ta na buƙatar ƙani ko ƙanwa"
"Ai na gama haihuwa yanzu domin Darraini ita ce auta na" cewar Amina
Aliyu ya ce.
" Za kiga auta"
Suna cikin haka su ka ji sallamar almajirin su mai suna Sani.
Amina ta sa hijjab ɗin dake kusa da ita Aliyu ya bashi izinin shigowa.
Sani ya shigo ya tsaya daga bakin ƙofa ya duƙa ya gaishe da Aliyu sannan ya gaida Amina ya tashi ya fita.
Amina ta tashi ta shiga kitchen domin ta ɗauko ma Sani abinci tana tashi Aliyu ya bi bayan ta.
Ta shiga kitchen ta ɗauko kulan da take zuba mishi abinci haɗa tea a cup ɗin shi tazo fitowa taci karo da Aliyu tsaye a bakin ƙofa yana kallon ta.
Amina ta ɓata fuska ta ce.
" Abban Shukrah zan wuce"
Aliyu bai ce komai ba ya bata hanya tazo wuce wa ya riƙo ta ya na cewa
"Haba madam laifin mai nayi ake share ni?"
Amina ta ɓata fuska Aliyu ya ce.
"Na tina abinda ya faru ya karɓi kayan hannunta ya fita dashi.
Ya samu Sani yana shara ya bashi abincin ya ce.
"Idan ka gama aikin kaje ka dawo"
Bai jira amsar Sani ba ya koma ciki.
Yana shiga parlour yaga Amina zaune a saman kujera ya zauna kusa da ita yana cewa tazo suje ya nuna mata wani abu
Amina tayi shiru taƙi magana
Aliyu bai ƙara cewa komai ba ya ɗauke ta yana dariya ya nufi bedroom ɗin su.
Bari mu leƙa gidan Baffa mu dawo
Ta Batulu ce 🥰 ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu 🥰
(Ta Batulu)
Page 17-18
Isma'eel zaune a ƙofar ɗakin Inna suna fira da ita Rabi'a ta na wanke wanke a ƙofar ɗakin Mama.
Amina ta shigo idonta jajir fuska ta kumbura babu sallama bata ce musu komai ba ta shiga ɗakin Inna.
Isma'eel ya ce.
"Zanga lokacin da yarinyar nan za tayi hankali wallahi ana girma ana ƙara hankali amman ita ƙara hau kacewa ta keyi"
"Dan allah ka rufa mun baki ban san dogon zance baka ga yanda ta shigo a furgice ba" cewar Inna ta na hararan shi.
Isma'eel ya ce.
"Allah yasa ba wani haukan tayi wa mijin ba ya zane ta"
Inna ta yi banza dashi ta shiga ɗakin ta samu Amina kwance a saman kujera tana kuka Inna ta riƙo Amina ta ce.
"Dan allah ki natsu ki faɗa mun abinda yake faruwa"
Amina ta yi banza da Inna ta ci gaba da kukan ta.
Inna ta yi ta yi ta faɗa mata abinda yake faruwa amman Amina ko kallonta ba ta yi ba ballatana tasa ran zata gaya mata abinda ke faruwa.
Inna ta tashi ta yi waje ta nufi ɗakin Baffa ta shiga ko sallama babu ta bankaɗe labulen ta faɗa.
Baffa yana zaune a saman darduma yana jan carbih Inna ta shigo ta fara bashi labarin abinda ke faruwa har tayi ta gama Baffa bai ɗaga kai ya kalleta ba.
Inna tasa kuka ta na cewa "Saboda ita ba yarinyar so bane shiyasa kacyi banza dani"
"Wallahi kacji tsoron allah ka daina nuna bam bamci a kan iyalan ka" cewar Inna
Har tacyi ta gama bai kalleta ba tasa kai ta fita.
Bayan ta fita Baffa ya yaje ya tsaya a bakin ƙofa ya hango Rabi'a ta na kwashe wanke wanke Isma'eel yana zaune a inda yake tun ɗazun bai motsa ba.
Baffa ya kira Rabi'a ya ce.
"Jeki kira mun Mamanki sannan kice ma Amina tazo"
Baffa ya kira Isma'eel sannan ya koma ciki.
Isma'eel ya tashi yabi bayan Baffa.
Baffa ya miƙa ma Isma'eel ƙaramar wayar da Aliyu ya siya mai ya ce.
"Kira mun Aliyu ko Nasser ka bani wayar"
Isma'eel ya kira Aliyu ta na ta ringing bai ɗauka ba ya kira Nasser ringing ɗaya ya ɗauka Baffa ya karɓi wayar bai tsaya amsa gaisuwar da Nasser yake ba ya ce.
"Kazo gida ka sameni yanzu"
Nasser ya ce.
"Gani nan zuwa"
Isma'eel ya amshi wayar ya kashe Mama ta yi sallama ta shigo.
Baffa ya samu guri ya zauna Mama ta zauna kusa dashi
Baffa ya kalli Isma'eel ya ce. "Ka gayawa tsohuwarka ita nake jira"
Isma'eel ya fita yana murmushi ɗakin Inna ya shiga ya same su zaune ta sa Amina a gaba tana kallo ita kuma Amina ta na ta kuka.
Isma'eel ya kalli Inna ya ce. "Baffa ya na jiranku keda wannan mara kunyar"
Ya na faɗin haka ya yi waje da gudu.
Inna ta ce.
"Daka sani ka tsaya kaga abinda zanyi maka ƙaramun mara kunya kawai"
Inna ta na ta lalaɓa Amina akan ta tashi suje kiran da Baffa yake musu.
Daman tun ɗazun take lalaɓa ta amman taki motsawa Nasser ya yi sallama ya shigo ya tsaya daga bakin ƙofa.
Inna ta amsa sallamar ya gaishe da Inna bayan ta amsa.
Ya kalli Amina ya ce.
"Waye sa'an wasan ki a gidan nan da za ki shanya mutane zaman jiranki?"
Amina ta duƙar da kai ƙasa.
Inna tayi karaf ta ce
"Bacci ne ya ɗauke ta yanzu ta farka"
Nasser bai kara magana ba ya fita Amina ta tura baki ta bi bayan shi Inna tabi ta a baya.
Amina ta yi sallama ta shiga ɗakin ta gaishe da Baffa ta gaida Mama ta samu guri ta zauna Baffa ya kalli Amina ya ce.
"Maike faruwa kika zo kina kuka kuma an tambayeki kinƙi magana"
Amina ta duƙar da kai ta na hawaye ta ce.
"Daman cewa ya yi inzo gida sai ya nemeni"
Baffa ya kalli Nasser ya ce. "Kira shi muji gaskiyar zance"
Nasser ya miƙawa Amina wayarshi ya ce.
"Samun number shi"
Amina taƙi karɓan wayar Baffa ya daka mata tsawa ya ce.
"Idan ki kai wasa yanzunan zansa ya zaneki"
Jin haka hannu na rawa ta amshi wayar ta sa number Nasser ya karɓa ya buɗe kiran gaba ɗaya sannan ya kira ringing ɗaya a ka ɗauka da sallama.
Suka gaisa da Nasser tun kafin Naseer ya yi magana ya riga shi
"Amina ta zo gida" cewar Sager
Nasser ya yi banza dashi Sager bai damu ba ya cigaba da magana.
"Amina bata da mutunci ga rashin kunya rainuwa idan na yi mata abu sannan duk kyautatawar da zanyi mata babu godiya a tsakanin mu sannan ta raina mahaifiyata ban isa in sa ta ko in hanata ba"
"Duk abinda nayi mata ban iya ba ga hangen rayuwar wasu hatta mahaifiyata gaya mata magana ta ke yi"
Dan allah kaya haƙuri a barta a gida ta kwana biyu ko za ta sanja hali amman gaskiyar magana wallahi na ga ji da ita.
Cewar Sager da baiyi tunanin Baffa na gurin ba shi a lissafin shi Nasser ne kawai ya kira shi ya ji dalilin turo ƙanwarshi da ya yi gida.
Nasser zaicyi magana Baffa ya karɓi wayar ya ce.
"Idan babu damuwa ina san ganinka zuwa anjima"
Cike da kunya Sager ya amsa cewar in sha allah zanyi ƙoƙarin zuwa
Bayan sun gama magana ya kalli Inna da ke tsaye a bakin ƙofa ya ce
"Za ki iya shigowa muyi magana?"
Inna ta shigo Baffa ya kalli Nasser da Amina tun kafin ya yi magana suka fita saboda sun fahimci zancen Baffa.
Bayan fitan su Baffa ya kalli Inna ya ce.
"Hanakalin ki ya kwanta kin ɓata mun tarbiyan yarinya da fatan za kiyi farin ciki da hakan?"
"Daga faɗar magana za ka hau ka zauna babu bincike ita yarinyar mana a tambayeta aji ta bakin ta" cewar Inna
Baffa ya kalli Inna ya ce.
"Duk abinda ya faɗa ba ki ji bane?"
"Wallahi kinji na rantse duk abinda ya faɗa ta aikata shi saboda a cikin ƴaƴana na san halin kowa na san abinda in a kace sun aikata zan yarda amman saboda ƙin gaskiya irin naki kince sharri a kai mata" cewar Baffa
Inna ta fara hawaye Baffa ya ce.
"Adana hawayenki domin lokacin zuban su baiyi ba"
Fitan mun a ɗaki zan zo in sameki Inna ta fita ta na kuka.
Mama ta kalli Baffa za ta yi magana ya da katar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu ganin haka Mama ta yi shiru ta na kallon shi.
Baffa ya ce.
"Kisa Rabi'a ta kawo mun lipton idan kin fita"
Mama najin haka ta miƙe ta na cewa
"Dan allah kayi haƙuri kar kasa wannan damuwar a zuciyarka tunda kaga ba isashen lafiya ka ke dashi ba"
Mama ta fita ta nufi ɗakinta Rabi'a ta na guga Mama ta ce.
"Haɗa ma Baffan ku lipton ki kai mishi"
Bata jira amsar Rabi'a ba ta shige bedroom saboda kanta dake ciwo.
Rabi'a ta kashe socket ta fita kitchen ta shiga ta haɗa kamar yanda ta san ya na so ta shiga ɗakin ba yan ta yi sallama ta samu Baffa zaune a inda Mama ta barshi.
Rabi'a ta duƙa tayi mishi sannu da jiki ta miƙa mishi lipton ɗin Baffa ya karɓa ya na sa mata albarka.
Rabi'a ta na girmama Baffa saboda yanda ya ɗauke ta kamar ƴar cikin shi duk haɗuwarsu sai ya sa mata albarka ko gaishe shi ta je yi da safe zai ta mata addu'o'i allah ya bata miji na gari wanda zai kula mishi da ita sosai take shan addu'o'i a gurin Baffa.
Rabi'a ta koma ɗaki ta cigaba da aikin ta.
Bari mu koma gidan Aliyu
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu 🥰
(Ta Batulu)
*Page 19-20
Aliyu ya fito daga kitchen ya na dariya hannunshi ɗauke da plate ɗin abinci Amina ta na bayan shi ta na dariya.
A saman two seater suka zauna, Aliyu ya kalli Amina ya ce.
"Ɗauƙo mun wayana a ɗaki"
Amina ta ɗauko wayar ta kawo mishi ya amsa ya zaunar da ita suka fara cin abinci.
Bayan sun gama cin abinci ya ɗau wayar shi ya ga tarin miss calls Baffa Nasser Mama.
Ya rasa wanda zai fara kira a ciki gaba ɗaya hankalin shi ya tashi.
Ya ce.
"Amina bani makullin mashin"
Bayan fitan Aliyu Amina kitchen ta shiga saboda ta girka abincin rana.
Ta na cikin aiki Sani ya shigo da sallama daman basu da kayan miya ta bashi kuɗi ya siyo mata.
Ita kuma ta ɗaura farar shinkafa ta na yi tana chart a waya.
Aliyu ya shiga gida ɗakin Baffa ya nufa bakin shi ɗauke da sallama ya samu Baffa ya na sallah.
Ganin haka ya ji hankalinshi ya kwanta ya fita ya shiga ɗakin ya shiga ɗakin Inna ya gaishe ta ya koma ɗakin Mama ya samu Rabi'a na goge goge a ɗakin.
Aliyu ya kalli Rabi'a ya ce. "Ina Mama?"
Kafin ta ba shi amsa Mama ta fito daga bedroom hannunta riƙe da charbi ta samu guri kusa da Rabi'a ta zauna.
Aliyu ya duƙa ya gaishe ta Mama ta kalli Aliyu ta ce.
"Baffan ku yana neman ka tun dazun amman bai samu wayarka ba"
Aliyu ya ce.
"Daga wajen shi nake yanzu na same shi yana sallah"
Mama ta ce.
"Ina yaran suke?"
Aliyu ya yi sauri ya kalli clock ya ga lokacin ta shin su ya yi.
Aliyu ya ce.
"Suna makaranta kuma gashi lokacin tashin su ya yi"
Mama ta ce.
" Rabi'a ta zo ga kuɗin abin hawa ta je ta ɗauko su ta kawo su nan idan zaka wuce sai ya ka tafi da su"
Rabi'a ta ɗauko hijjab Aliyu ya bata kuɗin abin hawa ta tafi.
Aliyu ya kalli Mama ya ce. "Bari in koma in gani ko ya idar da sallahr"
Aliyu ya shiga ɗakin Baffa bayan ya yi sallama ya samu Baffa yana zaune ya na karatun Qur'ani ya samu guri ya zauna kusa da shi.
Bai jima da zama ba Baffa ya aje Qur'anin bayan ya yi addu'o'i.
Bayan Aliyu sun gaisa da Baffa suka ɗan taɓa fira sannan Baffa ya gaya mishi abin da ya sa ya kira wayar shi.
Game da zuwan Amina gida sannan ya faɗa mishi yanda suka yi da mijin ta.
Aliyu ya yi shiru yana sauraron Baffa bayan Baffa ya gama bashi labarin abinda ya faru.
Aliyu ya fara da bama Baffa haƙuri yana kwantar mishi da hankali domin ya fahimci har yanzu ran shi a ɓace yake sosai.
Aliyu ya daɗe a ɗakin Baffa kafin ya yi sallama da shi a kan cewa zai dawo zuwa anjima idan mijin Amina yazo.
Aliyu ɗakin Mama ya shiga ya samu Shukrah kwance a saman kujera Darraini ta na kwance jikin Mama.
Mama ta kalli Aliyu ta ce. "Sunƙi cin abinci dukan su ɗauke su ku tafi gida su samu su ci abinci"
Aliyu ya yi sallama da Mama ya ɗauki Darraini ya fita Shukrah ta bi shi a baya.
Ya ɗaura Shukrah a baya Darraini na gaba suka tafi.
Sun kusa isa gida Shukrah ta ga fruit ta ce.
"Abba dan allah ka siya mana fruits"
Aliyu ya tsaya ya siya suka wuce gida.
Amina ta na jin ƙaran mashin ta fito tayi kwalliyar doguwar riga ta yi kyau ta samu Aliyu suna shigowa da yara da gudu Darraini ta je ta rungumeta ta na kuka.
Aliyu ya kalli Darraini ya kalli Shukrah sannan ya kalli Amina ya ma kasa magana.
Amina ta karɓi ledar hannunshi ta na mishi sannu da zuwa.
Aliyu ya ɗauki Darraini suka shiga ciki daga.
Suna shiga Aliyu ya yi alwala ya tafi massallaci Amina kuma ta juye ruwan zafi ta yi musu wanka.
Ta sa musu kaya ma rasu nauyi ta bar Shukrah na sallah ta fito Darraini na binta a baya tana rigima Amina ta zaunar da ita a saman kujera ta shiga kitchen ta shiga ta wanke fruit ɗin da suka shigo dashi ta zuba a fridge daman sunada freezer a kitchen.
Amina ta kwaso plates da spoon ta zo ta aje inda suke cin abinci ta jera komai ta ɗauko ruwa mai sanyi da zoɓo ta aje.
Ta koma kitchen ta ƙara gyara gurin ta fito ta samu Aliyu zaune Darraini na jikin shi.
Ta kira Shukrah da ke ɗaki suka zauna dukan su ta zuba musu shinkafa da miya da salad.
Darraini da Shukrah plate ɗaya ita da Aliyu plate ɗaya.
Suna ciki cin abinci Darraini ta mayar da hannunta plate ɗin su Aliyu daman haka take bata son cin abinci da Shukrah.
Bayan sun gama cin abinci Shukrah ta kwashe kayan ta kai kitchen Amina ta gyara gurin da suka ci abinci.
Ta shiga kitchen ta wanke kayan da suka ci abinci ta mayar da komai gurin shi ta fito.
Ɗakin yaran ta shiga ta kwaso uniform ɗin su ta fito parlour ta samu Aliyu zaune da yaran ya na musu karatu.
Ta fita ta wanke kayan ta shanya ta dawo ta zauna suka cigaba da karatun tare.
Sai da aka kira sallahr la'asar sannan suka tashi Aliyu massallaci ya tafi.
Amina da shukrah suka yi sallah bayan sun idar sai ga sallamar matar Nasser Maryam.
Amina ta karɓi Khadija ƴar shekara 2 ta na cewa Maryam.
"Yanzu nake tunanin ki ashe kina hanya?"
Maryam ta yi dariya ta ce "Haka kullum ki ke cewa"
Amina ta kawo ruwa ta aje mata Shukrah ta gaishe da Maryam ta shige bedroom ɗin su.
Darraini ta na jikin Amina bayan sun gaisa Amina ta kawo mata abinci da zoɓo.
Bayan Maryam ta gama cin abinci ta kalli Amina ta ce.
"Nifa magana na zo muyi da ke "
Amina ta mayar da hankalinta gaba ɗaya ta na sauraron Maryam.
Maryam ta ce.
"Kasuwanci nake son farawa shi ne na ce bari in tambaye ki ko kina da ra'ayi zaman haka babu daɗi"
✍️ Ta Batulu 🥰 Jagaban jajirtattu 🥰
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT*💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖*
_Written by ✍️_
*Jagaban Jajirtattu*
_(Ta Batulu)_
Page 21-22
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
★
Amina ta kalli Maryam ta ce "Wani irin kasuwanci ne?"
Maryam ta ce. "Dogayen riguna, takalma, da sauransu"
Amina tayi shiru ta na kallonta suna cikin hakan sai ga sallamar Aliyu.
Suka gaisa da Maryam ya ɗauki Khadija Darraini dake kusa da Amina ta sa kuka.
Aliyu ya kama hannunta suka shige bedroom.
Amina ta kalli Maryam ta ce. "Na daɗe ina son fara sana'a sai dai matsalar banda kuɗi kuma ban san inda zan samu ba"
Maryam ta matsa kusa da Amina ta ce "Nima banda kuɗi amman duk da banda kuɗi ba zan ƙi samo ma kaina mafita ba"
Maryam taci gaba da cewa "Kawai ki matsama Aliyu ya baki jari shi ne kawai mafitarki domin nima Nasser nake so ya bani"
Amina ta kalli Maryam ta ce. "Ni kuma bana hangen hakan mafita ne kin ga dai dai gwargwado suna ƙoƙari damu
Kar muzo mu lalata zaman auren mu"
Maryam tayi shiru ta na kallon Amina daman sai da ta yi tunanin hakan
Aliyu ya fito daga bedroom Darraini tana biye da shi.
Ya tsaya ya kalli Amina ya ce.
"Bari in je gida in dawo Khadija na ciki tayi bacci."
Amina ta ce.
"Abban Shukrah bari in baka saƙo ka kaima Baffa dan ALLAH!" Amina ta shige kitchen Aliyu kuma ya yi waje yana cewa ta same shi a waje Darraini ma tabi shi a baya.
Amina ta fito da ƙaton leda a hannu ta yi waje ta na tsokanar Maryam.
Ta miƙa ma Aliyu ledar ta na ce mai da saƙon Mama a ciki kace ina gaida ta.
Aliyu ya ɗauki Darraini ya na tambayar Amina inda Shukrah take Amina ta ce,.
"Tana ɗaki ƙila tayi bacci ne."
Aliyu ya tafi bayan Amina ta yi mishi addu'o'i Darraini ta na ta ɗaga mata hannu.
Amina ciki ta koma Maryam tayi dariya ta na ce mata "Sannu da ƙoƙari gaskiya kina aiki"
Amina tayi murmushi bata ce komai ba Maryam ta ce.
"Zan baki lokaci ki yi tunani duk hukuncin da kika yanke ki sanar dani"
Daga nan suka sanja fira.
Aliyu ya tsaya a hanya ya sai fruits ya saima Darraini biscuits sannan ya tafi.
Ya na shiga Nasser shima ya na shigowa suka rungume juna suka nufi ɗakin Mama hannun Nasser ɗauke da Darraini.
Mama taxna zaune a kujera Rabi'a tana zaune a ƙasa ta baza littafai ta na karatu.
Nasser da Aliyu suka ƙara gaida Mama sannan suka zauna a saman carpet ɗin dake shinfiɗe a tsakar ɗakin.
Darraini ta kwanta a jikin Nasser.
Aliyu ya ɗauko ledar da Amina ta bashi ya haɗa da fruits ɗin da ya siyo ya miƙawa Mama ya ce.
"Ga saƙon Amina dake da Baffa"
Mama tayi murmushi ta karɓa tana ta sa albarka.
Mama ta kira Rabi'a ta bata ledar tace "Ki duba zaki ga sakon Baffa a ciki"
Rabi'a ta karɓa ta aje ta fita.
Aliyu da Nasser suna fira da Mama Rabi'a ta shigo da plate mai fadi ta juye fruits ɗin aciki ta fita.
Mama ta kalli Aliyu ta ce
"Kun dubo Baffan naku?"
Aliyu ya ce "A ahh ba muje ba yanzu dai zamu tafi"
Mama ta tsaida su ta tashi ta ɗauko ledar da taba Rabi'a ta buɗe ta ciro wasu robobi masu murfi guda biyu ta ba Aliyu ɗaya ta ce ya kaima Baffa.
Aliyu ya karɓa Nasser ya shinfide Darraini a saman two seater suka wuce da Aliyu .
Ɗakin Baffa suka shiga bakinsu ɗauke da sallama suka same shi ya na kwance a saman kujera ya na jan casbih.
Baffa ya amsa sallamar ya basu izinin shigowa Aliyu a gaba Nasser a bayan shi.
Baffa ya tashi ya zauna suka ƙara gaida shi sannan Aliyu ya bashi saƙon Amina Baffa ya amsa yana murmushi ya ce.
"Nasan wannan aikin sai Amina"
Baffa ya dinga sa mata albarka yana ƙara jadadda ma Aliyu ko bayan ranshi bai yarda ya rabu da Amina ba.
Suna zaune suna fira aka kira sallahr magrib Baffa ya ce. "Kuje kuyi alwala yau tare za muje massallaci".
Tun da Baffa ya ƙara tsufa kuma ga yana yin jikin nashi yau ciwo gobe lafiya ya daina fita zuwa massallaci yin sallah ko sallahr juma'a Aliyu ke zuwa ya ɗauke shi a mashin.
Bayan sunyi alwala suka saka Baffa a tsakiya suka tafi massallaci yin sallah.
Bayan an idar Baffa ya ce,
"Su zauna suyi karatu zuwa lokacin da za ayi sallahr isha'i sai su dawo gida"
Sai da aka yi sallahr isha'i Baffa ya fito shi da su Aliyu suna fitowa Nasser ya ɗauko wayarshi ya kira Maryam.
Ring ɗaya ta ɗauka bakinta ɗauke da sallama Nasser ya ce.
"Ta jira shi a gidan brother zai biyo ya ɗauke ta su wuce gida"
bayan ya gama maganar ya yanke wayarshi ya mayar aljihu.
Su ka saka Baffa a tsakiya suka nufi gida suna tafe suna fira.
Su na zuwa ƙofar gida suka ga Isma'eel da mijin Amina su na zaune suna fira.
A haka su Aliyu suka iske su Baffa ya shiga ciki ya na cewa Aliyu ya shigo da Sager ciki.
Nasser da Isma'eel suka ta kewa Baffa baya Aliyu da Sager suna bayan su.
Bayan sun shiga gidan ɗakin Baffa suka nufa dukan su Baffa ya zauna a saman carpet ya kalli Ismael ya ce. "Ka ƙira mun Amina"
Aliyu ya zauna kusa da Baffa Nasser ya zauna kusa da Aliyu Sager ya na kusa da Nasser Amina ta shigo bakin ta ɗauke da sallama.
Bayan sun amsa ta samu guri ta zauna Baffa ya kalli Amina ya ce. "Ina so ki gaya mun gaskiyar abinda ya haɗaki da mijinki"
Amina ta yi shiru ta na hawaye Baffa ya mayar da kallon shi kan Sager ya na cewa.
"Tunda da ita ta kasa faɗa mana abinda ya faru ko zaka gaya mana abinda ya haɗaku da ita?."
Sager ya sunkuyar da kanshi ƙasa Baffa ya ce. "Kar kaji nauyin kowa a nan gurin ka faɗa mana domin yiwa tufka hanci"
Sager ya buɗe baki zaiyi magana Inna ta faɗo ɗakin kamar an jefota daga sama.
Baffa ya kau da kanshi ya mayar da hankalin shi kan Sager ya ce "Ina jinka.....
*Ta Batulu ce🥰✍️*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu 🥰)
Page 23-24
*
Sager ya ce.
"Amina babu irin maganar da bata faɗa mun sannan idan na bata kuɗin cefane ta jefe ni da shi hatta mahaifiyata zaginta ta ke yi"
"Ga yawan fita unguwa ba tare da na sani ba idan na yi mata magana ta ce babu ruwana da rayuwarta"
Biki ko a ina ake yi ta na gurin ko an gayyaceta ko ba a gayyace ta ba sai ta je"
Yaƙara mai maita abinda ya faɗa a waya.
Sager ya ce.
"Sannan kuma"
Inna tayi saurin ka tseshi ta ce. "Ya isa haka sai wani faɗan maganganu ma rasu kan gado ka keyi kamar wanda aka sawa battery"
Baffa ya ɗago ya kalli Inna akai sa'a suka haɗa idanu ta ƙara kallon fuskan shi da kyau ta ga yadda idanun shi suka rine fuskan shi har zufa ta keyi saboda ɓacin rai.
Baffa ya mayar da kallon shi kan Sager ya ce.
"Na ji dukkanin abinda ka faɗa kuma abinda ka aikata kayi mun dai dai sannan kuma zan tambayeka shin har yanzu kana jin za ka iya cigaba da zama da ita?"
Sager ya yi ƙasa da kanshi ya na mai jin kunyar Baffa ya na jin nauyin ya faɗa mishi abinda ke cikin zuciyar shi.
Baffa ya kalli Sager ya ce.
"Ta shi ka tafi gida duk hukuncin da ka yanke kazo ka sanar dani"
Sager ya miƙe ya yi sallama ya tafi Nasser ya kalli Amina ta na ta kuka ya ce.
"Wallahi ko ki rufe mana baki ko yanzu kici duka"
Baffa ya kalli Inna ya ce.
"Kinga tarbiyanki koh?"
Baffa ya ci gaba da cewa "Wannan ranar ita nake ta guje miki amman ki ka nuna ban isa ba har kike ganin na waresu a cikin ƴaƴa na"
Baffa ya kalli Amina ya ce.
"Wallahi idan Sager ya haƙura da auren ki ba zan yi mishi dole sai ya mai da ke ba"
Baffa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba ya haɗa su dukansu ya yi musu tass sannan kuma ya ce.
"Su tashi subar mishi ɗakin shi baya son ya ƙara ganin su"
Inna ta kama Amina da ke ta faman ku ka suka fita Isma'eel ma ya tashi zai bisu Baffa ya ce.
"Dawo ka zauna ina da magana da kai"
Aliyu da Nasser su na ta bawa Baffa haƙuri Nasser ya ɗauko ruwa a cikin ƙaramin fridge ɗin dake parlour ya buɗe ya miƙawa Baffa.
Baffa ya karɓa ya sha sannan ya jingina da kujera ya na mayar da numfashi.
10 minutes Baffa ya ta shi zaune ya kallesu dukan su ya ƙara yi musu nasiha mai ratsa zuciya.
Sannan ya basu umarni tafiya suka miƙe dukan su Baffa ya ce.
"Isma'eel ya zauna ya na da magana dashi"
Bayan fitan su Aliyu ɗakin Baffa ya ƙara yima Isma'eel nasiha mai ratsa jiki har sai da ya zubar da hawaye"
Baffa ya ƙara da cewa
"Ka riƙe ƴan uwan ka hannu biyu ko bayan raina ban yafe ba idan ka a butulce musu"
Baffa ya ce.
"Ya tashi ya tafi" Isma'eel ya miƙe yana ƙara bawa Baffa haƙuri sannan ya fita.
Ya na fita yaga Mama za ta shigo hannunta ɗauke da plate an rufe saman shi.
Isma'eel ya yi mata barka da dare sannan ya wuce ɗakin su.
Mama ta shiga ɗakin bayan ta yi sallama ta samu Baffa a zaune a inda su Aliyu suka barshi ya na ta haɗa zufa.
Ta zauna kusa dashi ta na mishi fifita Baffa ya ce. "Tunda na ga plate ɗin chan na san abin daɗi ya samu"
Mama cikin dubara ta mantar da Baffa damuwar shi ta na ta bashi labarai.
Aliyu da Nasser ɗakin Mama suka shiga suka samu Umar a zaune ya na cin abinci.
Umar ya na ganin su ya fara dariya ya na cewa
"Ai tinda naga sarkin rigima na san kuna gidan shiyasa na zauna zaman jiranku"
Nasser ya ce.
"Ta ya ya kasan dukan mu muna gidan?"
Umar yayi murmushi ya ce
" Ajiki na naji cewar kuna gidan"
Mama da shigowarta ke nan ɗakin ta katse shi ta na cewa "Idan ku ka tsaya biye ma sarkin surutun nan kwa kai dare ba tare da kun sani ba"
Umar ya tura baki Nasser ya na ta mishi dariya Umar ya kalli Mama ya ce.
"Banga Rabi'a ba"
Mama ta ce.
"Ta yi barci tun ɗazun"
Nasser ya ɗau Darraini dake bacci tin fitar su Aliyu da Nasser su kayi wa Mama sallama suka tafi ita kuma ta nufi ɗakin Baffa hannunta ɗauke da kofin lipton.
Aliyu ya goya Nasser Darraini tana ka faɗar Nasser suka nufi gidan Aliyu.
Suka tsaya su kai siyayya suka ƙarika gida bayan Aliyu ya shigar da mashin ciki.
Nasser ya ce.
"Shi ba zai shiga ciki ba idan ya shiga ya turo mishi Maryam su wuce"
Aliyu ya karɓi Darraini su kayi sallama sannan ya wuce.
Bai jima da shiga ba Maryam ta fito bayan ta goye da Khadijah hannunta riƙe da leda suka wuce gida.
Aliyu bayan shigan shi parlour sai da ya lumshe ido Amina dake zaune ita da Maryam ta miƙe ta karɓi Darraini tana mishi sannu da zuwa.
Aliyu ya kalli Amina taci kwalliya tana ta ƙamshi parlour yasha turaren huta.
Aliyu ya ce.
"Kamar wata Amarya irin wannan kwalliyar ai sai ki ruɗani"
Amina tayi murmushi Shukrah da gudu ta rungume Aliyu ta na murmushi.
Maryam ta na ta kallon su kamar ta samu tv Aliyu ya shigo ya zauna sannan ya kalli Maryam ya ce.
"Kinga na manta Nasser ya na jiranki a waje'
Maryam ta yi murmushi ta ɗauki Khadija dake bacci a gefen ta.
Amina ta ce.
"Ta jirata dan allah" Amina kitchen ta shiga ta samu flask ta zuba abinci mai yawa ta ɗauko wani jug ta zuba drink wanda ta yi blanding ta sa a leda ta fito taba Maryam ta ce.
"Dare ya yi idan ki ka ce za ki ɗaura girki za a wahala da yunwa"
Maryam ta yi murmushi ta amsa ta yi musu sai da safe ta fita Amina har bakin ƙofa ta raka ta sannan ta dawo ta shiga kitchen ta kwaso plates da flask ɗin abinci ta aje.
Shukrah ta shinfiɗa darduman cin abinci ta kwashe kayan abincin ɗaya bayan ɗaya ta ɗaura a kai.
Amina ta buɗe fridge ta ɗauko fruits ɗin da ta gyara ita da Maryam ta aje.
Ta raba fruit ɗin biyu ne ta yi blanding ta gyara ɗayan ta sa a fridge.
Ta Batulu ce✍️ 🥰
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
💖💖💖💖💖
💖💖💖💖
💖💖💖
💖💖
💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu🥰
(Ta Batulu)
Page 25-26
Bayan sun gama cin abincin basu sha fruits ɗin ba Amina ta mayar fridge ta ƙara gyara gurin Shukrah ta kwashe kayan da su ka yi amfani da shi ta kai kitchen.
Aliyu ya shi ga bedroom ya na ce ma Amina ta juye mishi ruwan wanka.
Shukrah ta fito da ga kitchen Amina ta ce ta je ɗakin su gata nan zuwa da ruwan wankan su.
Darraini ta na kwance a two seater ta na bacci lokacin da Amina ta karɓeta a hannun Aliyu a nan ta kwantar da ita.
Amina ta kulle kofar parlour ta shiga kitchen ba ta jima ba ta fito hannunta ɗauke da bucket da ruwan zafi a ciki bedroom ɗin su ta nufa bayan tayi sallama ta shiga.
Ta samu Aliyu kwance a saman gado ta wuce toilet ta aje bucket ɗin ta shiga ta ɗauko wani bucket wanda yafi na hannunta girma ta juye ruwan zafin a ciki ta shiga ta surka mishi ruwan sannan ta fito.
Ta na fitowa su kaci karo da Aliyu tayi murmushi ta ce.
"Ruwan wanka ya na jiran ka a toilet"
Aliyu bai ce komai ba ya zuba mata ido ya na ta kallon ta.
Amina ta raɓa shi za ta wuce ya yi saurin riƙeta ya na cewa "Naga kullum ƙara kyau ki keyi meye sirrin?"
Amina ta yi murmushi ta ce.
"Abban Shukrah ne sirrin"
Aliyu ya ƙara matsowa kusa da ita ya yi mata raɗa a kunne Amina ta ƙwace da gudu ta bar ɗakin.
Aliyu ya yi dariya ya na cewa "Zama ki dawo ne ki same ni"
Toilet ɗin ya shiga ya na shiga Amina ta shigo daman bata ta fi ba ta jira ne ya shiga toilet ɗin gurin wardrobe ta je ta fito mishi da kayan sawa ta fita.
Darraini ta ɗauka a parlour ta shiga da ita ɗakin su ta samu Shukrah ta na karatu Amina ta kwantar da ita sannan ta ce. "Shukrah ta cire kayan jikinta"
Amina toilet ta shiga ta ɗauko bucket ta je kitchen ta juye ruwan zafin dake cikin flask ta fito ta koma ɗakin yaran.
Shukrah ta fara ma wanka sannan ta ce ta wanke baki Amina ta fito ta ɗau Darraini dake bacci ta shiga da ita toilet ta yi mata wanka ta zo tasa mata kayan bacci.
Shukrah ta ce.
"Umma baki bani nawa kayan ba"
Amina ta aje Darraini ta ɗauko ma Shukrah kayan sawa ta fita.
Kitchen ta shiga ta haɗo ma Darraini abinci bata sa da yawa ba saboda ta san zata tashi shan tea.
Ta shiga ta samu Shukrah ta kau da kayan da suka cire har ta kwanta.
Amina ta ɗau Darraini dake ta faman raba ido ta zaunar da ita sannan ta fara bata abinci sai da ta tabbatar ta ƙoshi sannan ta bata ruwa tasha.
Ta kaita toilet ta wanke mata baki ta sa ta ta yi fitsari sannan ta kwantar da ita tayi musu addu'a ta rage hasken ɗakin ta ja ƙofar ta fita.
Kitchen ta shiga ta haɗo iipton ta fito ta nufi bedroom ɗin su ta samu Aliyu zaune yana karatu Amina ta zauna kusa dashi ta na shan lipton.
Bayan ta gama sha toilet ta shiga ta wanke baki ta ɗauro alwala ta fito ta can za kaya ta sa turare tayi addu'a ta kwanta.
Har lokacin Aliyu ya na zaune yana karatu bata jima da kwanciya ba Aliyu ya aje Qur'anin ya shiga toilet bayan ya fito ya yi addu'o'i ya rage hasken ɗakin sannan ya kwanta a bayan Amina.
Asuba ta gari
Da safe Amina ta gama dukkanin abinda take yi na ayyukan gida su ka yi breakfast ta shirya yara Aliyu ya kai su school daga nan ya biya gida.
Ya gaishe da su Baffa ya fito Isma'eel na wanki a tsakar gida Aliyu ya ce.
"Idan ka gama wankin ka same ni a gida yanzu"
Aliyu bai jira amsar shi ba ya yi gaba.
Ya dawo gida ya samu Amina zaune a parlour tana kallo ga plate ɗin fruit ta na sha.
Aliyu ya yi sallama ya shigo ya zauna kusa da ita Amina tayi mai sannu da zuwa ta tashi ta kawo ruwa ta miƙa mai.
Aliyu ya karɓa ya aje a saman table ɗin dake tsakiyar parlourn Amina ta ce.
"Na yi tunanin ka wuce kasuwa"
Aliyu ya ce.
"Akwai wanda na ke jira na ce ya same ni a gida"
Amina ta ce.
"Abban Shukrah dama ina son magana da kai idan babu damuwa"
Aliyu ya yi murmushi ya ce.
" Inajinki matar kirki"
Sunan da yake kiranta ne idan ya na cikin farin ciki.
Amina tayi murmushi ta ce.
"Shawara nake so ka bani dan Allah"
Aliyu ya ɗauki fruit ɗin da Amina ta aje a saman table ya fara sha yana lumshe ido.
Ganin hakan sai Amina ta ce.
"Sana'a nake son farawa Abban Shukrah amman na rasa wani irin sana'a zanyi kuma kaga sana'ar yabna da amfani sosai"
Aliyu ya kalli Amina ya ce.
"Akwai abinda na ra geki dashi a cikin gidan nan?"
Amina ta ce.
"A'a
Aliyu ya ce.
"Akwai abinda ba na yi a cikin gidan nan wanda nasan hakkina ne inyi shi?"
Amina ta ce.
"A'a komai kanna yi dai dai gwargwado"
Aliyu ya ce.
"Mai kika nema kika rasa da kike sha'awar fara sana'a?"
Amina tayi shiru tana kallon shi Aliyu ya ce.
"Baki bani amsar tambaya ta ba"
Amina ta ce.
" Inason fara sana'a ne ba dan ka rageni da komai ba"
Aliyu ya yi shiru ya na kallonta ganin hakan Amina bata ƙara cewa komai ba ta zuba ma tv ido.
Aliyu ya yi gyaran murya Amina ta kalle shi ya yi mata murmushi ya ce.
"Matar kirki a ƙara mun fruit ɗin na shanye wannan bai ishe ni ba"
Amina ta tashi ta je zata ɗau plate ɗin dake gaban shi Aliyu ya janyo ta.
Ta faɗa jikin shi Amina ta kawar da fuskan ta shi kuma ya ƙara juyowa da ita.
Amina ta ɓata fuska ta fara hawaye Aliyu ya kama dariya ya na cewa "Daman na daɗe ina binciken wanda ya koya wa Darraini rigima ashe a gurinki ta koya" Amina ganin ya na mata dariya ta sa mishi ku ka
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
💖💖💖💖💖
💖💖💖💖
💖💖💖
💖💖
💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu 🥰
(Ta Batulu)
Page 27-28
Sai da ya gama dariyar shi sannan ya fara share mata hawaye yana cewa
"Haba mana matar kirki ya kike mun asaran hawaye"
Aliyu sai da ya ga ta bar ku kan da take yi sannan ya kalleta ya ce.
"Wani irin sana'a ki ke son farawa.?"
Amina ta gyara zaman ta a jikin Aliyu ta ce.
"Ni dai kawai ka bani shawara domin na riga da na baka wuƙa da nama"
Aliyu ya ce.
"Lokacin kina gida ba kina yin turaren sai dawa ba.?"
Amina ta ce.
"Eh mana kuma ana samun ciniki sosai."
Aliyu ya ce.
"To ni a nawa shawaran ki cigaba da sana'arki tunda kina da customer."
Amina ta yi tsalle ta na murna Aliyu ya yi ƙara ya na cewa
"Za ki karya ni."
Amina ta tashi ta na mishi gwallo Aliyu ya bita suka fara zagaye parlourn su na jifan junan su da pillows ɗin kujeru.
Duk sun hargitsa parlourn sai da su ka gaji sannan Aliyu ya kwanta a saman carpet Amina ta kwanta ajikin shi suna mai da numfashi.
10 minutes Amina ta tashi ta ɗauko ruwan da ta kawo ma Aliyu ta buɗe ta zuba a kofin data ɗauko haɗe da ruwan tasha.
Ta zuba ma Aliyu ta bashi yaƙi karɓa ya tashi ya zauna ya ɓude baki ta zuba mishi ruwan a haka ta bashi ruwan har sai da ya kau da kai sannan ta aje kofin.
Su na cikin haka su ka ji sallama a bakin ƙofa Aliyu ya leƙa ya ga Isma'eel a tsaye.
Ya dawo ya ce,
"Amina sa hijjab zan shigo da baƙona."
Sannan ya fita ya samu Isma'eel a tsakar gida.
Suka jero zuwa cikin parlour hannun Isma'eel da baƙin leda Amina ta gyara pillows ɗin kujerun tun kafin su shigo ko da suka shigo bata parlourn.
Ya samu guri ya zauna Aliyu ma ya zauna Isma'eel ya gaishe da Aliyu suka ɗan taɓa fira kamar na 20 minutes yawanci firan Aliyu nasiha yake mishi akan abokan banza da yake tare dasu.
Suna cikin firan Amina ta fito daga kitchen hannuta ɗauke da plate wanda ta dafa macaroni yaji kifi ta aje ta ɗauko ruwa da zoɓo ta aje sannan ta zauna suka gaisa.
Bayan sun gama gaisawa ta tashi ta koma kitchen tabna cewa Isma'eel ga abinci nan kar ya bari ya yi sanyi.
Aliyu ya ta shi ya yi hanyar kitchen yana cewa Ismayel yaci abinci kafin yazo su yi magana.
Aliyu ya na shiga kitchen ɗin ya samu Amina ta na soya kayan miya.
Bayan kayan miya ya soyu ta tsayar da sanwa ta kwaso spices ta zuba ta rufe
tukunyar juyowar da za ta yi ta ji an rungumeta Amina ta buɗe baki za ta yi ihu Aliyu ya yi saurin rufe mata baki da hannun shi.
Amina tace.
"Haba dan Allah wallahi har ka bani tsoro"
Aliyu ya ce.
"Tunda na baki tsoro bani abina."
Amina ta yi dariya ta ɗauko albasa ta na yan kawa Aliyu ya riƙota ta baya ya na cewa
"Nifa ina da magana dake."
Amina ta ce.
"Kunnuwan Amina suna sauraron Jaruminta"
Aliyu ya karɓi wuƙar hannunta ya aje ƴa rungumeta gaba ɗaya ya na cewa.
"A kullum ina ƙara gode ma ubangijin da ya mallaka mun Amina a matsayin matata uwar ƴaƴa na"
Amina ta ce.
"Ba kai kaɗai ba Abban Shukrah ni kaina kullum ina ƙara jaddada godiya ta ga ubangiji da ya bani mijin marainiyya."
Amina ta fara hawaye Aliyu duk ya bi ya ruɗe yabna tambayarta abinda ya faru.
Amina ta ce.
"Dan Allah Abban Shukrah ko da nan gaba ka ƙara aure karka wulaƙanta ni"
Aliyu ya share mata hawayen fuskan ta ya na cewa.
"Ta ya ya zan hulaƙanta uwar ƴaƴa na kuma muradin zuciyata"
Aliyu ya cigaba da cewa "Ta ya ya zan wulaƙanta mai sani farin ciki a kowani lokaci ta ya ya Aliyu zai rayu ba tare da Amina ba?"
Amina ta yi murmushi Aliyu ya ce.
" Ƙarin aure baya daga cikin tsarin rayuwata amman idan hakan na cikin ƙaddarata ba zan iya guje mata ba."
Aliyu ya cigaba da cewa
"Ina son Amina ta sani cewa Aliyu ba zai taɓa wulaƙanta ta ba Aliyu ba zai taɓa rabuwa da Amina ba duk irin matsayin da ya taka a rayuwar shi "
Fuskan Amina ya cika da farin ciki suka ƙura ma juna ido kiran wayar Aliyu ya dawo dasu hayyacinsu Aliyu ya yi murmushi bai ce komai ba ya fita Amina taci gaba da girkin ta.
Aliyu ya samu Isma'eel zaune a parlour ya gama cin abinci ya na kallo.
Aliyu ya yi sallama ya zauna yana cewa Isma'eel "Har ka gama cin abincin?" Ismael ya ce. " Eh."
Aliyu ya kira sunan Isma'eel fuskan shi a ɗaure ganin haka Isma'eel ya ƙara maida dukkanin natsuwar shi ya na jiran ya ji abinda zai faɗa.
Aliyu ya faɗa mishi dalilin kiran da ya yi mishi sannan ya ƙara da ce mishi zai bashi aran jari ya juya idan ya samu na shi sai ya dawo mishi da kuɗin shi.
Aliyu ya ce.
"Ya je ya binciko shagon da yake son zama ya zo ya faɗa mishi."
Isma'eel yama kasa magana sai hawaye kawai ya ke yi ya na tunanin irin zuciyar Aliyu duk irin rashin kunyar da suke mishi da abubuwan da suke aikata mishi a ɓoye amman ƙoƙari yake ya ga rayuwar su ta yi kyau.
Aliyu ya kalli Isma'eel ya ce.
" Kuɗin ƴan uwa na ne kuma duk abinda zai faru tsakanin mu sunanku na ƴan uwa na ba zai taɓa san jawa ba."
Ismael ya fashe da kuka ya riƙe ƙafafun Aliyu ya na cewa "Dan allah ka yafe mun dukkanin abinda nayi maka da wanda ka sani da wanda ma ba ka sani ba"
Aliyu ya miƙe ya kamo Isma'eel ya zaunar dashi a kusa dashi ya ɗauko ruwa ya bashi yasha.
Sannan Aliyu ya kalle shi ya ce.
"Ta ya ya kake tunanin zan iya ƙullatar ƴan uwa na?"
Aliyu bai jira amsar shi ba yaci gaba da cewa.
"Yanda zan yi ma Nasser abu haka zanyi ma ka domin ni ɗaya nake kallon kai dasu ban taɓa ban banta ku a cikin zuciyata ba."
Aliyu ya kalli Ismael ya ce.
"Zan baka lokaci ka je ka yi shawara duk abinda ka yanke kazo ka gaya mun."
Isma'eel ya ce.
" Shi baya da wanda zaiyi shawara dashi da ya wuce shi dan haka ya amince ba sai ya kama shago a wani guri ba yafi son shagon dake jikin gidan su."
Daman a gidan su Aliyu idan mai karatu bai manta ba akwai ɗakin da Baffa ke ajiye amfanin gonar shi a zaure.
To ɗakin ƙofa biyu yake dashi akwai ƙofa ta waje akwai ta ciki to yanzu Baffa baya ajiye komai a ciki.
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
💖💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖
💖💖💖💖
💖💖💖
💖💖
💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu 🥰 see
(Ta Batulu)
Page 29-30
Sun a'je magana Aliyu zaije gida ya samu Baffa su yi magana Isma'eel ya na ta godiya har sai da Aliyu ya nuna ɓacin ranshi sannan ya yi shiru.
Amina ta shigo parlour ta ɗau plate ɗin da Isma'eel ya gama cin abinci za ta fita Isma'eel ya tsaida ita ya miƙa mata ledar da ya shigo da shi a hannun shi ya ce.
"Gashi Inna ta ce a kawo ma yara"
Amina ta karɓa ta na godiya tace dan Allah ya gaida mutanan gidan kuma ya ƙara miƙa mata godiya gurin Inna Amina ta koma kitchen Isma'eel ya yi sallama da Aliyu ya fita.
Aliyu bedroom ya shiga ya ƙara shiryawa ya fito ya samu Amina ta na kwashe abinci a kitchen Aliyu ya za gaya ta bayan ta ya rufe mata idanu.
Amina ta ce.
"Ka na duba time Abban Shukrah ka kusa makara"
Aliyu ya cire hannun shi a fuskan Amina ya ce.
"Idan na makara ai ke ki ka makarar dani da kulawarki a gida"
Amina ta ɗauƙo basket ɗin da take haɗa ma Aliyu abinci idan Sani zai kai mishi kasuwa ta zuba duk abinda ya dace ta sa.
Ta rufe ta fuskan ce shi ta ce.
"Dole ne Amina ta kula da mijinta a kowani irin hali ta ke ciki"
Aliyu ya amshi basket ɗin da take miƙa mishi sannan ya ce.
"Mijin Amina zai tafi kasuwa ko Amina zata mai rakiya da addu'o'i kamar yanda a kasa ba.?"
Amina ta amshi basket ɗin hannun shi ta fito parlour Aliyu ya na take mata ba ya fridge ta buɗe ta ɗauko zoɓo a wani irin jug mai kama da gora ta saka a cikin basket ɗin ta rufe fridge ta ɗauko key a saman kujera ta matsa gefe ta na nuna ma Aliyu hanya fuskanta ɗauke da murmushi.
Aliyu ya riƙe hannunta suka jera a tare suna tafe ya na gaya mata yanda zai yi kewarta na tsawan lokacin da zai kasance a kasuwa.
Amina ta na ta kwantar mishi da hankali har sukaje inda ya aje mashin ɗin shi sannan ya hau Amina ta miƙa mishi basket ɗin ta na jero mishi addu'o'i masu ratsa zuciya.
Ta buɗe mishi ƙofa ya fita sannan ta koma ciki ta cigaba da aikin ta.
Bayan Amina ta gama aiki ta gyara kitchen tayi wanke wanke ta rufe kitchen ɗin ta ƙara gyara parlour tasa turaren huta.
Ta nufi bedroom shima ta ƙara gyarawa ta kwashe kayan da Aliyu ya zuba a saman gado.
Amina ba ta zauna ba sai da ta ƙara gyara ko ina a cikin gidan sannan ta tayi wanka ta sa kaya les riga da zani ta duba time taga biyu saura hijjab ta sa ta yi sallah.
Bayan ta idar da sallah ta zauna tayi make-up Amina akwai son gayu da kwalliya kuma a kai sa'a ta iya kwalliyar ta ɗaura ɗan kwalli ta ɗauko turare ta na sawa taji a na buga ƙofa.
Amina ta ɗauƙo ƙaton mayafi ta rufe jikinta sannan ta fita Sani ta gani a bakin ƙofa ta buɗe mishi ya shigo ta ce dan allah Sani bari in ɗauko maka kuɗin napep ka ɗauko mun yara a makaranta.
Amina ta shiga ciki ta ɗauko ɗari biyar ta ba shi ya karɓa ya fita.
Amina har ta fara tafiya za ta shiga parlour ta ji ana buga ƙofa cike da mamakin ko Sani ne ya yi mantuwa ta buɗe ƙofar.
Maryam ce a tsaye a bakin ƙofar hannunta ɗauke da Khadija Amina ta yi murmushi ta ce sannu da zuwa bismillah mu shi ga daga ciki Amina ta bar kofar a buɗe saboda Sani.
Suka shiga parlour suka gaisa daga nan Amina ta aje mata ruwa suka cigaba da fira Maryam ta na tambayarta yanda su ka yi da Aliyu.
Amina ta ce.
"Bari kici abinci ki huta ma yi maganar"
Cike da sa rai Maryam ta ce.
"Amina ta bata buta za ta yi alwala"
Amina ta ɗau Khadija suka nufi ɗakin yara su na shiga Maryam ta shiga toilet Amina ta shimfiɗa mata darduma ta fito.
Kitchen ta shiga ta zuba ma Sani abinci ta rufe ta ɗau plate ta zuba wani abincin shima ta rufe ta fito parlour ta zauna Khadija na jikinta.
Amina ta ɗau waya ta kira Aliyu ta na tambayar yanda ya isa kasuwa.
Aliyu ya ce.
"Bai jima da shiga kasuwar ba daman yanzu zai kirata ya gaya mata ya sauka lafiya"
Ganin fitowar Maryam ya sa Amina ta yi mishi sallama ta a'je wayar.
Maryam ta zauna ta na cewa
"Amina ki na bani mamaki wallahi"
Amina ta yi shiru ta na sauraronta
Maryam ta ce.
"Baki san na Miji ba a mishi haka ba?"
Amina ta ce.
"Ni fa har yanxu ban san akan abinda kike magana ba"
Maryam ta ce.
"Gaba ɗaya kin saki jiki da namiji kin tattara dukkan kulawarki a kanshi baki san namiji ba abin yarda bane?"
Amina ta ce.
"Eh to kinsan Maza su na suka ta ra kuma ba duka bane aka taru aka zama ɗaya ba sannan kuma zan tambayeki."
Amina ta ce.
"Dan allah mainene laifin Matar da ta ke kulawa da Mijinta?"
Maryam ta yi murmushi ta ce.
"Bata da laifi amman kulawa da yardan da kika ba Aliyu ta yi yawa bakya tsoran abinda zai iya faruwa nan gaba?"
Amina ranta ya baci amman bata nu na ba ta ce
"Aliyu shine duniya ta kuma kinga bani da kowa idan bashi ba"
Amina ta kalli Maryam ta ce.
"Duk wata Mace zaki sameta da ƙokarin farantawa Mijinta inbdai ta cika Matar ƙwarai,
Duk wata Mace tana da burin Mijinta ya kalleta ita kaɗai,
Duk wata Mace burinta ta kula da Mijinta ba tare da yaji sha'awar Matan dake yawo a waje ba"
Maryam ta yi dariya ta ce.
"Na fahimci kin yi nisa yanzu domin duk abinda zan gaya miki ba zaki taɓa fahimta ba "
Amina ta ce.
"Kinsan maiyasa nake kulawa da Mijina sosai?"
Maryam ta ce.
A'a amman inna son sani koni ma zan ƙaru da wani abun"
Amina ta ce.
"Kulawa na ƙara ƙarfin alaƙa duk rauninta sannan kuma rashin kulawa na rage ƙarfin alaƙa duk ƙarfinta"
Maryam ta ce.
"Uhmmmm karki manta da wani abu guda ɗaya"
Amina ta ce,
"Innajinki"
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
💖💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖
💖💖💖💖
💖💖💖
💖💖
💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu 🥰
(Ta Batulu)
Page 31~32
Maryam ta ce.
"Yanzu ku ɗin fa ba yara ba ne"
Amina ta ce.
"Har yau har gobe ni yarinya ne a gurin mijina"
Amina taci ga ba da cewa
"Mata su na bani mamaki wallahi dan kinyi haiwuwa biyu sai kice girma ya kama ki? To akwai masu haiwuwa biyar ba su yarda da cewa sun tsufa ba"
"Wata macen za ki ganta haiwuwa shida amman wallahi idan kika ga yanda ta ke sai kin ce ba ita ke da wannan ƴaƴan ba"
"Shifa namiji da kika ganshi yana son kulawa sannan tsafta gyara idan na ce gyara kin san abin da nake magana akai?"
Maryam ta zuba ma Amina ido ta ce.
"Ina mamakin yanda idonki ya rufe akan Aliyu baki san halin maza bane wallahi ba gyara ko kulawa ba in dai suka tashi tsula tsiyar su mantawa suke da sun taɓa saninka"
Amina ta fahimci duk abin da za ta gaya mata ba za ta fahimta ba dan haka sai ta ce.
"Bari inzo"
Ta shige kitchen ta ɗauko abincin da ta haɗa a plate ta fito da shi ta aje ta ɗauko drink ta aje ta ce.
"Na cika ki da surutu tun ɗazun"
Maryam ta ce.
"Aa babu komai domin a wannan ɗan zaman har na ƙaru dake"
Amina za ta yi magana ta ji sallamar yara Darraini ta shigo da gudu tabna kuka Shukrah na bayanta da school bags a hannunta.
Shukrah ta gaishe su Maryam ta amsa ta na tambayar abinda ya faru.
Shukrah ta ce.
"Kuka take saboda na ce ba za a siya mata sweet ba"
Amina ta lallashi Darraini ta ce.
"Muje inyi miki wanka in ba ki wani abu mai daɗi "
Darraini ta na ta murna Amina ta ce.
"Shukrah ɗauki abincin Sani ki kai mishi idan kin dawo ki same ni a ɗaki"
Amina ta kalli Maryam ta ce.
"Dan Allah bari in zo"
Amina ta kwashi school bags ɗin su ta nufi kitchen ta ɗauko plas ɗin ruwan zafi ta nufi bedroom ɗin yara Darraini na binta a baya.
Amina ta yi wa Darraini wanka ta ɗauko ta suka fito daga toilet ta samu Shukrah zaune a saman gado Amina ta wuce ta aje Darraini ta fara shiryata Shukrah kuma ta wuce toilet.
Bayan ta gama shirya Darraini ta buɗe wardrobe ta ɗauko ma Shukrah kayan sawa ta kama hannun Darraini suka fita,
" Na barki ki na zaune ke kaɗai" cewar Amina ta na fuskantar Maryam.
Amina ba ta jira amsar ta ba ta shiga kitchen ta haɗo tea ta ɗauko bread ta fito ta samu Darraini zaune kusa da Maryam Amina ta ce.
" Sauko ƙasa ki zauna karki ɓata mun kujera"
Darraini ta sauko ta zauna Amina ta miƙa mata cup ɗin da bread.
Shukrah ta shigo bayan ta yi sallama itama tayi wanka ta sanja kaya Amina ta ce.
"Kinyi sallah?"
"Eh na yi" cewar Shukrah.
Amina ta ce.
"Idan ki na jin yunwa kishiga kitchen ki ɗibo abinci "
Shukrah ba tace komai ba ta nufi kitchen.
Amina ta kalli Maryam ta ce.
"Ina sauraronki a ina muka tsaya?"
Maryam ta ce.
"Yanzu dai duk mu a'je wannan surutan mu yi maganar da zata fishe mu"
"Maganar sana'ar ya ku ka yi dashi?
Amina ta faɗa mata duk yanda su kayi da Aliyu.
Maryam ta riƙe baki ta ce.
"Kinga abinda nake gaya miki koh?"
"Yanzu duk wannan kulawar da kike bashi amman ya ka sa miki abinda kike so"
"Wato ba zai iya baki jarin da za ki ƙula kanki ba sai dai ya baki jarin turare danqari "
Amina ta ce.
"Jarin turaren ma bai ce zai bani ba ni kawai shawara na ce mishi ya ba ni "
"Ai saboda ya san shi zai bada jarin shiyasa ya zaɓan ma kanshi mai sauƙi wanda ba zai ja kuɗi da yawa ba" cewar Maryam.
Amina ta ce.
"Ni ba na da kuɗi kuma banda hanyar kuɗi"
Maryma ta ce.
"Ke kike da hanyoyin samun kuɗaɗe ma ba kuɗi ba"
Ita fa Amina lamarin Maryam ya fara ba ta tsoro amman bata nu na ba ta ce.
"Yanzu ya kike ganin za a yi?"
Maryam ta yi dariya ta ce.
"Yanzu kika zo in da nake son ki zo"
"Nasan ba zai rasa zuwa da kuɗi daga kasuwa ba ko mai yawa ko ɗan kaɗan"
Amina ta ce.
"Wannan ai sata ne kike so ki koya mun"
"Ai ba ki tsaya kinji ƙarshen maganar ba"cewar Maryam
Ita dai Shukrah ta na zaune ta na cin abinci amman hankalinta gaba ɗaya ya na sauraron Maryam.
Maryam ta ce.
"Idan ya dawo ki din ga ƙirƙiran wani abun ki ce babu acikin gidan koda akwai to ki ɗauka ki ɓoye "
"Sannan idan ya dawo da kuɗi ko babu yawa ki din ga cire wani abu ta yanda ba zai gane ba kidinga rage kuɗin cefane shima"
"Wallahi in dai kika ɗauki wannan shawaran nawa kafin nan da ƙarshen wata mun samu abinda muke nema"
Amina ta ce.
"Ko kuma nan da ƙarshen wata ya tura ni gida da takaddar saki?"
"Gaki dai a haka ina miki kallon wayayyiya ashe ba haka bane" cewar Maryam.
Amina ta ce.
"Maganar gaskiya ba zan iya ko ɗaya daga cikin abubuwan da kika lissafa ba sannan ma su yi ina musu fatan shiriya "
Maryam ta ce.
"Da zaki saurare ni na wasu ƴan mintuna dana fahimtar da ke ta yanda za ki gane"
Amina ta ce.
"Ina ga da mun bar wannan maganar zaifi domun duk abinda zaki gaya mun ba zan taɓa fahimtar kiba"
Maryam ta ce.
"Kin fi so ki ƙare rayuwarki a haka?"
"Eh zanvyi farin ciki da alfaharin hakan idan rayuwata ta ƙare ina bautar ubangiji domin zaman aure bauta ne ba wai gidan baje koli ba" cewar Amina
Maryam ta ce.
"Na san wata rana da kanki za ki zo naiman shawara gurina"
Amina ta ce.
"Uhmmmm ba zance komai ba domin nasan komai na Allah ne idan ya rubuto hakan a cikin ƙaddarata babu makawa sai na zo"
Daga nan suka sanja fira Maryam ba ta bar gidan Amina ba sai gurin biyar na yamma sannan ta tafi.
Ita Amina ta na mamakin yanda Nasser ke barin Maryam tabna yawan fita unguwa.
Wani lokacin idan ta cewa Aliyu za ta je unguwa ya dinga faɗa ke nan shi baya son yawo ta cika fita unguwa!
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu 🥰
(Ta Batulu)
Wannan page ɗin na kune Jajirtattun Marubuta group ubangiji ya ƙara haɗe kan mu.
Page 33~34
*
Bayan shekaru 15 abubuwa da yawa sun faru Amina ta haifi Manaheer Maryam ta na da ciki haiwuwa yau ko gobe Nasser shima alhamdulellahi buɗi ya samu domin har gida ya gina suka tare tsakanin Khadijah ta ba Manaheer shekara 2.
Isma'eel ya maida hankali a kan shagon da aka buɗe mishi alhamdulellahi ya na samun ciniki sosai ya yi aure ya na zaune a gidan da Aliyu ya fara zama sunan matar shi Safiyya.
Umar ya auri Rabi'a ya na zaune a gidan shi na kanshi alhamdulellahi shima ya samu rufin asiri sosai.
Fatima itama ta na da ƙaramin ciki Amina aurenta ya mutu ta na zaune a gida Baffa ya rasu shekaru biyu da suka wuce yanzu yaran suke riƙe da gidan.
Bawa baya gujema ƙaddarar sa.
A wannan lokacin ƙaddarar Amina da Aliyu ya fara sauyawa duk da cewa yanzu Allah ya ƙara buɗa mishi amman wasu hidindimun gidan duk ya daina yi.
Yanzu haka Aliyu ya na kasuwanci sosai domin har tafiye-tafiye yake yi domin yanzu haka ya sai gida a jos kuma yana da burin tarewa a chan.
Mama tsufa ya kama ta sosai yaran sunyi-sunyi ta dawo gidansu da zama amman taƙi amincewa ta ce babu in da za ta je.
Aliyu ya na zaune ya ji hayaniya ta yi yawa ya tashi ya nufi hanyar bedroom ɗin yara Amina ta na tsakiya su na fira.
Ganin shigowar shi yasa Amina ta miƙe Aliyu ya kalleta ba tare da ya ce komai ba ya fita Amina ta yi hamdala da bai ce komai ba.
"Umma ina jin yunwa" cewar Darraini.
Amina ta fita ba tare da ta ce komai ba Shukrah ta bi bayan ta Manaheer ta kwanta Darraini ta kwanta kusa da ita.
Bayan fitan Amina kitchen ta shiga ta na shiga Shukrah ta shigo Amina ta duba ta ga abin da ya yi saura farar shinkafa ta ɗaura taba Shukrah salat ta gyara mata.
Bayan sun gama girkin Amina ta zuba ma kowa ta zuba ma Aliyu a plate ta same shi a parlour ta yi sallama ta shiga.
Ta aje mishi plate ɗin ta ɗauko mishi ruwa ta a'je ta fita shima ruwan ɗurawa su keyi a gora mutumin da ya daina wadata iyalan shi ta ya ya zai siyo drinks ya a'je.
Bayan sun gama cin abincin sukai wanka Amina ta kwaso kayan makarantarsu ta duba taga babu omo ta aiki Shukrah gurin Abbansu.
Shukrah ta yi sallama ta gaida Aliyu dake zaune yana kallon tv.
Shukrah ta duƙa ta ce.
"Abba bama da omon wanki ya ƙare"
Aliyu ya yi kamar baiji abinda ta ce ba
Sai da ya ɗauki dogon lokaci sannan ya ce.
"Waya turo ki?"
Shukrah ta ce.
"Babu kowa daman zan wanke uniform ne"
Daga haka Aliyu bai ƙara cewa komai ba ya mayar da hankalin shi kan tv ganin haka Shukrah ta tashi ta koma bedroom ɗin su.
Amina ta kalli Shukrah ba tare da tace mata komai ba domin bata buƙatar sai ta ji abinda ya faru.
Amina ta fita daga ɗakin yaran ta shiga bedroom ɗin ta.
Bata jima da shiga ba Aliyu ya shigo hannunshi ɗauke da leda ya kalli Amina ya ce.
"Daga yau karki ƙara turo mun yara su tambayeni wani abu"
Amina ta kalle shi fuska cike da hawaye ta ce.
"Dan Allah Abban Shukrah ka dawo yanda kake gaba ɗaya ka sauya mana"
"Kai ne jigon rayuwar mu ni da ƴaƴana kaine komai namu idan ba kai mana ba wa zai mana?"cewar Amina ta na kuka.
Aliyu ya ce.
"Ni babu wani sauyawar da nayi kun kasa fahimtar yanzu haƙuri ake da rayuwa"
Amina ta ce.
"Wani irin hakuri da rayuwa kana tauye hakkin da ubangiji ya ɗaura maka"
Aliyu ya taso a zafafe yana cewa
"Karki kuskura ki gaya mun maganar banza kuɗi dai nawa ne kuma na ce ba zanyi ba duk abinda za ki yi ki je ki yi"
Amina ta yi murmushi ta ce.
"Babu abinda zan iya amman Allah zai yi ma kowa sakayyar abinda ya aikata "
Ta na faɗa mishi haka ta shige toilet ta barshi yana ta faman faɗa.
Bata fito ba sai da ta tabbatar da ya bar ɗakin sannan ta fito daman ta shiga ta yi alwala ne.
Darduma ta shimfiɗa ta fara kaima ubangiji kukan ta.
Shukrah ta shigo ɗakin ta samu Amina tana sallah ta duba ledar da ta ga Abban su ya shigo dashi.
Omo ne a ciki da sabulun wanka da man shafawa Shukrah ta ɗau omon ta fita.
Bayan Amina ta idar da sallah ta shiga bedroom ɗin yaran ta ga babu kowa ta ƙara gyara ɗakin ta rufo.
Parlour ta shiga ta samu plate ɗin da ta a'je ma Aliyu ya na nan yanda ta a'je ko taɓa ba a yi ba.
Amina ta ɗauka ta aje a kitchen ta fito parlour ta ƙara gyarawa ta fita bayan ɗaki in da su ke wanki ta samu Shukrah na wankin uniform ɗin su Darraini na taya ta Manaheer na zaune a gefen ta.
Amina ta karɓi wankin ta ce.
"Ku shiga ciki bari in ƙariƙa"
Shukrah ta shige suka bita a baya a parlour suka zauna Manaheer ta kunna musu tv.
A haka rayuwar Amina ta yi ta tafiya har zuwa lokacin da mahaifiyar Aliyu ta rasu kafin ta rasu ta jaddada mishi cewar ko bayan ranta ya rabu da Amina bata yafe ba sannan kuma ta yi wa Amina nasiha mai ratsa zuciya.
Bayan mutuwar mahaifiyar Aliyu daga nan komai ya ƙara lalacewa.
Aliyu ya sauya rayuwar shi gaba ɗaya.
Ubangiji ka bamu ikon yarda da ƙaddara mai kyau ko akasinta 🤲
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu 🥰
(Ta Batulu)
Page 35~36
Bada jimawa ba Aliyu ya sai da gidan da suke zaune ya yi sallama da ƴan uwan shi ya koma jos da zama gaba ɗaya komawar shi ba da jimawa ba ya yi aure da Aisha.
Shigowar Aisha rayuwar Aliyu komai ya ƙara lalacewa shakara ɗaya da aurensu da Aliyu ta haifi Zainab suna kiranta da Mimah.
Bayan wasu shekaru Abba ya samu karayar arziki ya sai da gidan da suke zaune a ciki ya naimi wanda bai kai shi ba ya siya.
Duk da hakan ba wai baya da rufin asiri bane amman karayar arzikin daya samu shiyasa ya ƙara janye jikin shi daga cikin hidimar gidan.
A yanzu haka shekarun Mimah 15 bata da mutunci ga rashin kunya babu wanda take ragama wa babu mai tsawatar mata idan ta yi ba dai dai ba sannan duk tafi yaran Aliyu jiki da tsawo.
Tunda Aliyu ya dawo jos bai ƙara zuwa saminaka ba lokacin da Amina ta haifi Muddansir ƴan uwan shi da na Amina sun zo mata suna.
A nan suka fahimci irin rayuwar da take fuskanta Fatima ƙanwar Aliyu ta ji babu daɗi sannan ta ƙara bawa Amina shawarwari gami da bata haƙurin duk abinda za ta gani ta daure ta riƙe ƴaƴanta.
Fatima ta samu yayinta da maganar Amina suma sunyi mamaki sosai domin basu yarda ba sai da suka zo garin tun a yanayin gidan da suka iske suna rayuwa a ciki suka fahimci akwai matsala.
Ƴan uwan Aliyu sun zauna dashi sunyi sunyi ya faɗa musu halin da yake ciki amman yaƙi harta Isma'eel yanzu kansu a haɗe yake
Umar shiya bada shawaran su fara siya ma yayan nasu gida daga baya sai su haɗa mishi jari su bashi a tunanin su baya samu ne gaba ɗaya a kasuwar.
Basu san cewa lamarin harda zalunci ba ƴan uwan Aliyu basu bar garin jos ba sai da suka haɗawa Amina jari mai tsoka suka siya mata waya.
Kafin su tafi sai da suka roke Amina akan duk halin da ake ciki ta dinga sanar musu a waya.
Bayan ta yaye mudan karatun Shukrah ya tsaya Darraini da Manaheer ne kawai suke zuwa makaranta ita kuma Shukrah Amina ta sata a islamiyar ƙasan layinsu.
A lokacin Inna ta so taja Amina a jiki amman ganin babu fuska sai ta koma kan Aisha suka haɗe kansu.
Kuma har zuwa lokacin Amina ba ta samu mijin aure ba yawon ta kawai ta keyi Inna tasa mata ido yanzu haka shekarun Auta 6
Cigaban Labari
Da daddare Abban Shukrah ya dawo gida Amina ta kai mishi ruwa toilet ta kawo abinci ta aje mishi ta fita.
Abban Shukrah koda ya fito bai samu umman Shukrah a ɗakin ba yana cikin shiryawa ta shigo ta taya shi shiryawa ta gabatar mishi da abinci.
Yana cin abinci suna fira da Amina duk da cewa sama sama take amsawa amman shi ko a jikin shi.
Mama ta yi sallama ta samu guri ta zauna.
"Lafiya ki ka shigo mun ki ka zauna baki ce komai ba?" Inji Aliyu
Mama.
"Ɗazun bana gida Amina ta kama Mimah ita da yaranta su ka yi mata dukan tsiya ga ta chan zazzaɓi ya rufeta"
Jiki na rawa Abban Shukrah ya tashi ya yi waje daman Aliyu akwai son ƴaƴa amman ba bu kulawar da ya dace.
Ya na zuwa ya samu Mimah kwance ta rufe jikinta ta na ta rawar sanyi ga jikinta zafi.
Mimah na ganin Abbanta ta fashe da kuka Aliyu ya zauna yana tambayar ina ke mata ciwo amman saboda raki taƙi magana kuka kawai ta keyi.
Aliyu ya fita ya kira Aisha ya ce.
"Zo ki shiryata mu je hospital"
Mama ta fito tana matse hawayen ƙarya ta shiga ɗakin ta riƙo Mimah tana cewa
"Tashi ki zauna Abban naku ya fita"
Daman ba wani ciwo bane zazzaɓi ne kawai Mimah ta tashi ta zauna Mama ta sa hijjab ta ce.
"Tashi mu je tun kafin ya gano shirin mu"
Abban Shukrah a fusace ya koma ɗakin shi ya samu Umma zaune a in da ya barta ya kalleta ya ce.
"Wallahi ba zan ɗauki asara ni kaɗai ba zaku sha mamakin abinda zanyi idan na dawo"
Umma ta na zaune ko kallon in da yake ba tayi ba.
Abba ya gama fadar shi ya yi waje ya na fita Umma ta tashi ta kulle mishi kofar ta fito.
Umma ta yi sallama ta shiga ɗakin ta Shukrah na zaune ta na ma ƙaninta karatu Umma ta samu guri ta zauna bayan sun gama karatun suka ɗauko na addini Umma ta ƙara musu.
Daga nan suka zauna suna fira Umma ta tara su dukansu ta ce.
"Ina son ku bani shawaran sana'ar da zanyi domin na gaji da zama haka babu sana'a"
Darraini ta ce.
"Ni dai muyi awarar sai dawa domin naga ana samun ciniki"
Shukrah ta ce.
"Musai koda ƙaramin fridge ne mudinga zoɓo da kunun aya"
Manaheer.
"Umma ni dai a shawarce mudinga yin snacks domin yafi duk abinda suka lissafo"
Umma ta yi shiru tana nazarin maganganu yaranta domin sune abokan shawaranta suma itace abokiyar shawaransu.
Basu da ƙawaye ko ɗaya a cikin rayuwar su iyaka a haɗu a makaranta a rabu a makaranta.
Umma ta jasu a jiki ta yanda basa ɓoye mata damuwar su.
Umma ta ce.
"Kowa yaje ya kwanta zuwa safe zamu yanke shawaran abinda ya dace"
Su kayi alwala suka kwanta amman banda Shukrah ta na zaune kusa da Umma suna fira sama sama.
Abba ya shigo ɗakin Umma Shukrah ta miƙe zata shiga ciki Abba ya kalleta ya ce.
"Koma ki zauna munafuka kawai da gidan ubanwa za kije?"
Shukrah ta sunku yar da kai ƙasa Abba ya kalli Umma ya ce.
"Duk abinda ke faruwa a gidan nan ke kike kunnawa domin yanzu nabga bakya son zaman lafiya"
Amina Amina Amina sau nawa na kira sunanki?"
Umma ta ce.
"Sau uku"
Abba ya ce.
"Gargaɗi dake da ƴaƴanki domin kune fitinannu a gidan nan yanzu kun kama yarinya kunyi mata taron dangi kamar kune ku ka haifeta"
"To da ga rana mai kamar ta yau kar hannunku yaƙara kaiwa jikin yarinya na saboda ita ɗin ba baiwarku ba ce"
Umma ta kalli Shukrah ta ce.
"Ba mu guri zanyi magana da Abbanku"
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Wannan page ɗin naka ne gaba ɗayan shi
Yaya na abin alfahari na mai share mun kuka na kaiɗin bango ne acikin rayuwata kaiɗin jigo ne acikin rayuwar Ta Batulu 🥰
Ya Salis M Reza.
Banda kamarka har gobe da jibi kaine abin kwaikwayo na
Ubangiji ya yi maka sakayya da mafificiyar alkhairi nagode. 🙏
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Page 37~38
*
Shukrah ta shiga ciki Umma ta dawo da kallonta gurin Abba yana tsaye fuska a ɗaure kamar bai taɓa dariya ba.
Umma.
"Ni kam na ce Abban Shukrah yaran nan dasu na zo gidanka?"
Abba.
"Bangane abin da ki ke nufi ba fahimtar dani yanda zan gane"
Umma.
"Uhmmmm babu komai amman ina jiye maka ranar nadama domin nasan komun daren daɗewa sai wannan ranar ta risƙeka"
Abba.
"Amina ki fito fili ki gaya mun abinda ki ke son faɗa wato mugun baki zakiy mun koh? To Allah ya fiki"
Abba ya fita yana
"Cewa zamu haɗu dake da ƴaƴanki zaku gane baku da wayyau"
Umma ta yi alwala ta kwanta.
Abinda ya faru bayan sun je kai Mimah chemist shi da Mama su na tafe ta na gaya mishi ƙarya da gaskiya shi kuma sai faɗa yake.
Abin da Mama bata sani ba Abba ya na faɗa ne saboda an sashi fitan kuɗi bawai saboda dukan da a ka yi mata ba.
Suka ƙarika chemis aka duba ta zazzaɓi ne kawai amman saboda ƙarya Mama cewa ta yi.
"Har amai sai da ta yi sau biyu kuma ta kasa cin abinci"
Mai chemist ya yi mata allura ya haɗa magunguna har da ruwan gishiri ya basu.
Abba ya biya kuɗin suka kamo hanya suna tafe Abba na cika yana batsewa Mama ta na ta ƙunshe dariya.
Su na shiga gidan ɗakin Umma ya nufa kai tsaye shine su kai wannan tattaunawar da su ka yi.
Da safe Shukrah ta gyara ɗaki Manaheer ta gyara tsakar gidan Darraini ta wanke toilet Manaheer da auta suka ɗibo ruwa tunda har ruwan ba kullum yake siya ba.
Suka gaishe da Mama su kaje gaida Abbansu a nan ya yi musu tass ya ƙara da cewa.
"Sadakar su zai bayar dukan su tunda sun zama ƴan iska"
Manaheer ta turo baki
Abba ya kalli Manaheer ya ce.
"Daman na daɗe da sanin baki da mutunci to wallahi ki fita idona in rufe idan wani ke hure miki kunne ma zan yi maganinku"
Sai da ya gama zaginsu tass ya ce.
"Ku tashi ku bani guri marasu mutunci kawai"
Suka miƙe har sun fita Manaheer ta dawo ta zauna ta ce.
"Abba kuɗin karyawa"
Abba ya yi shiru yama rasa mai zaice mata chan kuma sai ya ce.
"Manaheer yaushe na zama abokin wasanki?"
Manaheer ta gyara zama ta ce.
"Abba zamu je makaranta ne kar muyi latti"
Kafin Abba ya ce komai Mama ta shigo ta zauna Manaheer ta yi kamar bata ganta ba.
Abba ya kalli Manaheer da ba ta da niyyar tashi ya ce.
"Je ki duba saman pillow akwai ɗari biyar ki ɗauka kizo ki bani guri"
Manaheer ta shiga ciki ta ga ba bu ɗari biyar sai dubu ɗaya ta dudduba ta ga ba bu wani kuɗi bayan wannan ta yi murmushi ta ce.
"Rabonka ya na tare dakai a duk in da ka ke"
Ta ɗauki dubu ɗayan ta fito ta ce ma Abba.
"Angode Allah yasaka da alkhairi ubangiji ya mayar da dubunshi"
Abba ya hau washe baki ya na amsawa cike da jin daɗi Manaheer ta yi waje ta na dariya.
Ta samu Darraini ta shirya Auta ma ya shirya ta miƙa wa Umma kuɗin ta ce.
"Kuɗin karyawa in ji Abban mu"
Amina ta bi kuɗin da kallo cike da mamaki da al'ajabi ta san dai baya wuce ɗari biyar ɗari uku.
Manaheer ganin Umma na mata kallon tuhuma ta ce.
"Haba Umma kamar baki yarda dani ba"
Umma.
"Ba yarda da ke bane banyi ba nayi mamakin hakan ne"
Manaheer.
"Umma kina yawan gaya mana babu abinda addu'a baya sauyawa"
Umma.
"Hakane ubangiji yasa komai yazo ƙarshe"
Ameen.
Umma ta bada ɗari biyar suka siyo kamu ta dama musu bayan sun karya kowa ta ɗau jaka suka tafi makaranta.
Gidan ya rage daga Shukrah sai Umma Shukrah ta ɗau wayar Umma ta ce.
"Bari in gaisa da Aunty Teemah"
Umma ta yi dariya ta ce.
"Kunfi kusa ke da ita amman ina ji ranar ta na miki kashedin ki daina kiranta da wannan sunan"
Shukrah ta yi murmushi ta ce.
"Ai sunan yafi daɗi ne"
Umma.
"Bari inje gurin Abbanku idan kun gama magana karki cinye mun charge naga sun kawo huta yanzu kisa mun charge"
Umma ta fita ba tare da tajira amsar Shukrah ba.
Umma ta yi sallama ta shiga ɗakin Abba yana zaune yana shan tea kakkaura ya ji madara ga soyayyan kwai a gefenshi.
Koda Abba ya ga shigowarta ko a jikin sa hasalima tsokanar ta ya fara.
Umma ta yi murmushi ta zauna sai da ta bari ya gama breakfast ɗin hankalin shi ya dawo jikin shi sannan ta fuskance shi.
Umma.
"Fatima ta na son Shukrah ta je mata hutun makaranta"
Abba.
"Ya ɗaure fuska nifa kinsan bana son suna yin nisa dani saboda yaran yanzu ka haifesu ne baka haifi halin su ba"
"A hakan ma suna gabana sai a hankali ballatana basa gabana"
Umma.
"Daman cemata na yi ba yara na bane yaranka ne ta kira ka ta gaya maka"
Abba.
"Banganeba wai ke dan Allah mai yasa bakya son zaman lafiya ne a rayuwarki?"
Umma.
"Uhmmmm yanzu idan na ce mata za ta zo ka ce mun da iznin wane yanzu kuma nace yara naka ne ba nawa ba shima ya zama laifi?"
Abba.
"Wallahi Amina ki dinga jin tsoran Allah"
Umma.
"Ta yi dariya Abban Shukrah kenan in tuna maka da wani abu daka manta?"
"Ka tuna lokacin baya da ka ke ce mun koda ka ƙara aure bazan zama abin hulaƙan tawarka ba"
"Koda ka ƙara aure matsayina ba zai taba san jawa ba ka tu na da hakan?"
Abba.
"Kinsan menene Amina?
Har yau kin kasa fahimta ta shi ya sa muke yawan samun matsala dake"
"A lokacin baya ko ban furta ba kina fahimtar abinda nake nufi saɓanin yanzu da gaba ɗaya kin sauya"
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Jinjinar ban girma da addu'ar neman da cewa.
Ya Salis M Reza
Ubangiji ya ƙarawa rayuwa albarka 🙏
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Page 39 ~40
Amina ta yi shiru ta na mamakin abin da yake faɗa wai ita ce ma ta sauya.
Wayar Abba ta hau ringing shi ya katse abinda yake shirin faɗa ya ɗau wayar ya fita Umma ta gyara ɗakin ta sa turaren wuta.
Abba ya jima bai shigo ba Mama ta shigo ɗakin ganin Umma na zaune ko sallama ba ta yi ba ta nemi guri ta zauna ta na buɗe hanci ga hancin nata masha Allah ba a faɗi ɗayan ba.
Abba ya shigo ya na washe baki Umma ta kalle shi ta ce.
"Da alama an biya maka kujaran makkah?"
Abba.
"Uhmmmm ke dai bari kawai Nasser ne ya kirani wai sun haɗa kuɗi za su sai mun gida"
Umma.
"Alhamdulellahi ubangiji ya sanya alkhairi"
Abba.
"Sun kira ne su tambayeni a ina nake son gidan wai ko zan dawo gida ko kuma a nan"
Umma.
"To sai ka zauna ka yi nazari ka faɗa musu a inda kake so"
Abba.
"Ni ba gwanda su haɗa mun kuɗina su bani in ƙara a kasuwa ba"
Mama tayi karaf.
"Nima dai haka na gani ai kama taye su baka kuɗin bawai su ce za su siya maka gida ba"
Umma ta miƙe ta ce.
"Abban Shukrah bari inje ina son zan aiki Shukrah yanzu zan dawo"
Umma ta fita Abba ya kalli Mama ya ce.
"Yau banga Mimah ba ko lafiya"
Mama.
"Ta na bacci ne ba ta tashi ba kasan jiya bata samu ta yi bacci ba"
Abba ya yi kamar baiji abinda ta faɗa ba
Mama.
"Alhaji ina da magana da kai"
Abba.
"Kiyi sauri inajinki domin zan fita ne"
Mama.
"Daman ina son baka shawara ne game da su Shukrah"
Mama.
"Gaskiya ya dace kasa musu ido sosai domin ni yanzu idan na yi wata magana sai a ce dan bani na haifesu ba shiyasa ma ba zan ce komai ba"
Abba ya kalleta hankalin shi a tashe ya ce.
"Wani abun ki ka ga sunyi wanda bai dace ba?"
Mama.
"A'a kawai dai shawara na baka domin na ɗaukesu kamar yanda na ɗauki Mimah"
Ta na gama fadan haka ta tashi tayi waje tabar shi cike da zulumi.
Umma ta shigo ta same shi a wannan yanayin cike da damuwa take tambayar shi abinda ya faru.
Abba ya kalleta cike da tuhuma amman ya kasa ce mata komai yabar abin acikin zuciyarsa.
Abba ya ƙara shiryawa ya kalli Umma ya ce.
"Zan tafi kasuwa"
Umma.
"To baka bada kuɗin cefane ba kuma babu abinda za a dafa"
Abba ya ce.
"Banda kuɗi gaskiyar magana sai dai kuya haƙuri"
Umma.
"Duk lokacin da na tambayeka abinda za a dafa haka kake ce mun kullum baka dashi haba dan Allah harda karamun yaro kake azabatarwa da yunwa"
Abba.
"In da Aisha ta fiki hankali kenan domin in dai ta tambayeni na ce mata banda shi sai ta kwana biyu bata ƙara tambayeta ba"
Umma.
"Ai daman dole ta fini hankali a gurinka"
Abba.
"Ni dai na faɗa miki banda kuɗi idan za kuyi haƙuri kuyi haƙuri idan ba za kuyi ba shikenan kinga tafiyata idan kin fita kijamun ƙofar ki tafi da makullin"
Yasa kai ya na ta baza ƙamshi Umma ganin zaman ba zai fisheta ba ta miƙe ta kullo ƙofar ta tafi ɗakinta.
Ta samu Shukrah har ta yi bacci Umma ta zauna ta na tunanin mafita ko sana'ar da ta ce za suyi bata da ko sisi ko ƴan uwanta basu san halin da take ciki ba.
Ta na zaune ta ji sallamar Maryam matar Nasser ta na tafe da tsowon cikinta a gaba wannan shine ciki na uku wancan ta yi ɓarin sa Umma ta yi mamakin ganinta kasan cewar bata taɓa zuwa ba tunda suka dawo jos da zama sai dai waya jefi jefi amman sai ta share.
Ta miƙe ta na mata barka da zuwa Maryam ta na cike da mamakin yanda ta ga Amina ta samu guri ta zauna suka gaisa ta kawo mata ruwa.
Aka fara firan yaushe gamo sun jima su na fira kafin Umma ta shiga bedroom ta taso Shukrah ta gaya mata zuwan Maryam sannan ta bata raguwar ɗari biyar ɗin da ya rage wanda ta ɓoye ne domin su samu abun da za su ci da rana.
Umma ta ce.
"Kije da ɗari biyar ɗin nan ki samo mata wani abun tunda kinga ba girki za mu yi ba kuma Abbanku bai san da zuwanta ba"
Shukrah ta karɓi kuɗin ta sa hijjab Umma ta koma parlour Shukrah ta biyo bayan ta suka gaisa da Maryam ta fita.
Bayan fitan Shukrah Maryam ta ce.
"Ya na ganta a gida ta na zaune babu makaranta ne?"
Umma.
"Bata jin daɗin jikinta ne shiyasa kika ganta a gida"
Daga nan suka cigaba da fira a nan Maryam take gaya wa Umma ita da Nasser suka zo ya na kasuwa gurin Abban Shukrah.
Umma na jin hakan ta yi hamdala domin ta yi tunanin ko bai san da zuwanta ba ashe ma ba ita kaɗai ba ce.
Shukrah ta yi sallama hannayenta ɗauke da ledoji manya ga almajiri na bin bayanta ɗauke da wasu kayan.
Umma ta karɓi na hannun almajirin Shukrah ta ajiye na hannunta Umma ta kalleta fuskan ta ɗauke da mamaki.
Shukrah.
"Ina fita na haɗu da yaron shagon Abba zai kawo kayan cefane ya na ganina ya roƙeni da in ƙariko dashi gida yana sauri Abba ya na jiran shi a kasuwa"
Umma ta shanye mamakin da ta ke yi ta fara duba kayan.
Shinkafa ne sai kayan miya mangyada harda su kaza a ciki guda biyu da salad.
Shukrah ta miƙa wa Umma dubu biyar ta ce.
"Gashi ya ce a sai abinda ya dace"
Umma ta shanye mamakin da take ta ba Shukrah kuɗin gawayi ita kuma ta fara gyara kayan miya su na fira da Maryam kafin Shukrah ta dawo siyo gawayin harta gama gyaran kayan miyan.
Ba bu jimawa sosai suka gama dafa abincin gidan sai tashin ƙamshi yake Mama ta na daga cikin ɗaki ƙamshi duk ya cika mata hanci.
Bayan sun gama girkin Umma ta haɗa zoɓo irin wanda ta saba haɗawa ta aiki Shukrah siyo ƙanƙara ita kuma ta ƙara gyara ɗakin Abba ta sa turare ta fito.
Umma ta shiga wanka bayan ta fito ta samu Maryam ta na sallah Shukrah ta na gyara gurin da su kai aikin abinci bayan ta gama gyarawa ta shiga wanka.
Ƴan makaranta sukai sallama suka shigo Auta ya na tafe ya na kuka.
Umma ta ce Manaheer ta ɗau abincin Mama ta kai mata sannan ta kalli Auta ta na tambayar Darraini abinda ya sa shi kuka.
Darraini ta ce.
"Tunda mu kaje makaranta cikin shi ke ciwo shine yake ta faman kuka.
Umma ta riƙo shi.
"Bari kuka jarumin Maman shi bari Shukrah ta fito wanka ta siyo maka magani a chemist"
Umma shiga ɗaki hannunta riƙe da na Auta su na shiga Maryam ta fara tsokanar shi Auta ya duƙa ya gaisheta.
Manaheer Darraini suka shigo bayan sunyi sallama suka gaisa da Maryam suna tamabayar ta Khadija.
Maryam.
"Ta na gida ta na ta rigima wai sai ta biyoni ta ganku na ce ta bari idan su kai hutun makaranta sai tazo shine ta bani saƙo in kawo muku"
Darraini.
"Anty Maryam amman ba yau za ki koma ba?"
Umma.
"Daga dawowarku za ku tsareta da surutu"
Maryam.
"Nayi kewarsu ne tun ɗazun domin sune abokan firan ita wancan miskilar bansan yanda ake fira da ita ba"
Dukansu ta basu dariya harda Auta mai kukan ciwo sai gashi ya na dariya Shukrah ta yi murmushi shigowarta kenan ta ji abinda ake tattaunawa.
Bayan sunyi alwala sun yi sallah suka ci abinci su kai wanka Umma ta aiki Darraini chemis ta siyo wa Auta magani.
Bayan fitan Darraini bada jimawa ba Abba ya shigo shida Nasser Umma ta aiki Shukrah ta kai mishi makullin ɗakin.
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Page 41~42
Shukrah ta kai makullin ta dawo ta kwashi kayan abinci ta kai Abba ya na ta washe baki.
Nasser ya kalli Shukrah ya ce.
"Yarinyar tawa ta girma"
Shukrah ta yi murmushi Abba ya ce.
"Ga ta nan sai miskilanci tsiya"
Shukrah ta fita ta na murmushi Nasser ya kalli Abba ya ce.
"Idan ina kallon Shukrah kai nake tunawa kasan ance magaji mafiyi"
Abba ya yi dariya suka fara cin abinci suna ci Nasser ya na santi.
Shukrah ta samu Aunty Maryam Darraini Manaheer suna ta fira Umma ta na ba Auta magani.
Shukrah ta shige bedroom ta na shiga Manaheer ta bi bayan ta ganin haka Darraini ma tabi bayan su.
Anty Maryam ta kalli Umma ta ce.
"Kinga abin da Shukrah ta yi ta kwashe mun abokan fira"
Umma ta yi dariya ta ce.
"Kunfi kusa ba mai shiga tsakanin ku ballatana ku ba shi kunya"
Aunty Maryam ta yi dariya ta ce wa Umma.
"Ni ban san abinda ya faru bayan kun dawo nan da zama ba"
"Kuma nasan kona tambaya ba za ki gaya mun ba"
"Amman ina son ki gaya mun ko kaɗan daga cikin halin da kike ciki domin in san ta inda zan taimaka miki"
Umma.
"Babu abinda ya faru bayan rabuwa kawai dai ya samu karayan arziki kamar yanda ki ka gani kuma alhamdulellahi bamu naimi komai mun rasa ba"
Anty Maryam.
"Ni daman nasan ba za ki taɓa sauyawa ba"
Aunty Maryam.
"Haba Amina mai yasa baki ɗaukeni a matsayin ƴar uwa ba"
Umma.
"Da ace ina cikin matsala tabbas zan gaya miki domin samun shawararki"
Aunty Maryam.
"Amina ki ɗaukeni a matsayin abokiyar shawara wanda zaki iya gaya mata dukkanin abinda ya dameki"
Umma.
"Na jima da ɗaukanki a matsayin ƴar uwata ki yarda da ni babu abinda zan ɓoye miki"
Aunty Maryam ta yi shiru ba dan ta yarda ba.
Aunty Maryam ta ce.
"Wace sana'a ki ke yi yanzu haka?"
Umma.
"Ina ta tunani har yanxu ban yanke shawara ba"
Aunty Maryam.
"Mai zai hana ba za ki sai fridge ba idan yaso sai a haɗa da wani abun"
Umma.
"Nima nayi tinanin hakan"
Daga nan suka sanja fira Shukrah da Manaheer Darraini suka fito Umma ta kalle su.
"Ina za ku je da ku ka fito a tare?"
Manaheer.
"Za muje gaida uncle Nasser ne"
Umma za ta yi magana Aunty Maryam ta hana ta ce.
"Ku je abinku"
Bayan fitan su Aunty Maryam ta kalli Umma ta ce.
"Nifa ban yarda da abinda kika faɗa mun ba dan Allah ki gaya mun gaskiyar abin da ke faruwa"
Hawaye ya zubo a idanun Umma ta ce.
"Dan Allah karki karya mun zuciyata domin faɗa miki abin da ke damuna daidai ya ke da tsinke igiyar aure na da Aliyu"
Cike da mamakin furucin da ya fito daga bakinta Aunty Maryam ta dafa ka faɗar Umma ta ce.
"Ba zan matsa miki sai kin gaya mun abin da ke damunki ba amman dan Allah ki cire damuwar komai a cikin zuciyarka"
Anty Maryam ta yi ta rarrashin Umma da kalamai masu daɗi.
Shukrah ta shigo ta ce.
"Umma uncle zai shigo ku gaisa"
Bayan fitan Shukrah Umma ta shimfiɗa darduma.
Nasser ya yi sallama ya shigo suka gaisa da Umma suka taɓa fira kafin ya kalli Aunty Maryam ya ce.
"Madam za mu yi dare a hanya na ga kin miƙe ƙafa ne"
Umma ta yi dariya ta ce.
"Ba ta gama hutawa ba ne"
Nasser ya yi sallama da Umma ya aje mata kuɗi masu kauri ya fita ya na cewa Aunty Maryam ta fito su wuce.
Bayan fitan shi Aunty Maryam ta kalli Umma ta ce.
"Za muyi magana zan kiraki ko zuwa anjima"
Su kai sallama ta kawo kuɗi ta ce.
"Gashi a sai ma Auta biscuit"
Ba ta tsaya jiran amsar ta ba ta aje kuɗin ta yi waje domin ta san ba za ta karɓa ba.
Umma ta bi bayan ta Mama ta fito tsakar gida ta na yamutsa fuska ta ce.
"Ashe baƙi mu kayi a gidan"
Anty Maryam ta yi murmushi suka gaisa ta na tambayar su gajiyar hanya.
Bayan sun gama gaisawa Aunty Maryam ta kalli Shukrah ta ce.
"Sa hijjab muje mota in baki saƙonku"
Shukrah ta sa hijjab ta fita waje ta samu Abbansu tsaye da uncle Nasser ta matsa gaban motan in da ta hango Aunty Maryam.
Aunty Maryam ta buɗe ƙofar baya ta ce ga kayan nan ta kwashe.
Manyan ledoji ne guda huɗu ta kwashi biyu ta shiga dashi gida harta wuce idon Abba ya na kanta.
Ta dawo ta ɗauki sauran ledar ta matsa ta na ma Aunty Maryam godiya ta ce.
"Dan Allah ta gaishe mata da Khadija"
Shukrah ta ƙara so gaban uncle Nasser suka ƙara sallama za ta shiga gida ya kirata ya ce.
"Ban tsaya siyo muku tsaraba ba ga wannan ke da ƴan uwanki"
Shukrah ta duƙa har ƙasa ta na godiya Abba ya na ta washe baki ya ga kuɗi.
Shukrah ta shiga gida ta samu ƴan uwanta zaune a parlour ta aje ledar ta miƙa wa Umma kuɗin da uncle Nasser ya basu.
Umma ta yi godiya ta amsa ta aje Manaheer ta ɗau kuɗin ta na ƙirgawa Umma ta yi kamar bata ganta ba.
Abba ya shigo ya na washe baki Umma ta yi mishi barka da zuwa ya amsa ya na zaunawa a kusa da Shukrah.
Ya kalli Umma ya ce.
"Baƙi sun tafi sai fatan Allah ya sau kesu lafiya"
Ameen cewar Umma
Abba.
"Ni dai ban samu ko sisi ba gashi na ga kamar Nasser ya bama Shukrah kuɗi"
Umma ta kalli Manaheer ba tare da ta yi magana ba.
Manaheer ta turo baki ta miƙa mishi kuɗin hannunta bayan ta zare wasu daga ciki.
Abba ya karɓa yana washe baki ya ƙirga dubu ashirin cif.
Ya ɗau dubu biyar ya basu ya ce gashi nan su raba.
Manaheer ta miƙe ta shige bedroom Abba ya ce.
"Kyaji da baƙin halinki"
Umma ta karɓi kuɗin ta yi godiya.
Abba.
"Uhmmmm an samu raguwar kuɗin cefane?"
Umma za ta yi magana Shukrah ta riga ta.
"Aa ba a samu ba nima sai da kuɗina ya shiga ciki"
Abba ya yi murmushi ya ce.
"Allah ya yi miki albarka ubangiji ya baki miji na gari"
Ameen cewar Shukrah ta na shiga bedroom.
Abba.
"Uhmmmm ke baki samu ko sisi ba?"
Umma.
"A'a"
Abba.
"Allah sarki ai na ga Maryam a nan ta sauka na yi tinanin ko ta baki wani abu"
Umma cike da takaici take kallon Abba.
Ganin irin kallon da take mishi ya ce.
"Wannan ledar menene a ciki?"
Umma ta kalli Darraini da ke zaune ta ce.
"Kwashe ledojin nan ki kai ɗakin Abbanku"
Abba ya miƙe yana cewa.
"Allah ya baki haƙuri tambaya kawai na yi"
Har ya kusa fita ya dawo ya ce wa Umma.
"Zan koma kasuwa kisa yara su gyara mun ɗaki"
Bayan fitan Abba Shukrah ta fito Manaheer na bayanta suka zauna.
Darraini ta sauko ƙasa tana duba ledojin ta ga ko wanne da suna a jiki ta fitar ma da kowa nashi ta miƙa mai.
Duka ledojin kayan sawa ne a ciki sababbi da takalma a ledar Umma harda kayan Auta nashi duka sababbi ne da takalma ƙafa uku.
Umma ta zuba ma kayan ido kafin ta umarci kowa ya ɗauka ya aje a gurin kayan shi.
Umma ta ƙirga kuɗin da Nasser ya bata dubu talatin ta ɗauko wanda Maryam ta bata dubu ashirin.
Manaheer ta matso kusa da Umma ta ce.
"Umma na yi miki laifi amman kafin in gaya miki zan fara neman afuwarki"
Umma ta zuba mata ido ta na jiran ta ji abinda za ta ce.
"Manaheer Umma dan Annabi karki hukuntani"
Shukrah Darraini Umma suka zuba mata ido suna jiran ta faɗa musu abin da ta yi.
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Page 43~44
Shukrah ta yi murmushi domin har ta gano laifin da ta yi.
Manaheer ta ciro kuɗi ta miƙa wa Umma Shukrah ta karɓi kuɗin ta ƙirga dubu goma cif.
Shukrah ta kalli Manaheer ta ce.
"Kuɗin da uncle Nasser ya bayar kika rage?"
Manaheer ta duƙar da kai Darraini ta ce.
"Wallahi kin yi mun daidai kinga duka kuɗin da ya bamu dubu talatin kenan"
"Abba ya ƙwace dubu ashirin kin zare mana dubu goma"
Shukrah.
"Duka idan aka haɗa kuɗin ya ta shi dubu sittin"
Darraini.
"Amman ta ya ya ki ka fahimci Abba zai ƙwace kuɗin?"
Manaheer ta kasa cewa komai ta na jiran hukuncin Umma.
Shukrah ta kalli Umma Darraini ma haka Umma idonta na kan Manaheer tunda ta fito da kuɗin ita ma ta fahimci abin da ta aikata.
Umma ba ta ce komai ba ta mayar da hankalinta kan Auta ya na kwance a jikinta.
Shukrah ta shiga bedroom ta fito da kula mai ɗan girma ta aje gaban Umma ta ce.
"Ga raguwar miyan girki"
Umma ta kalli Darraini.
Darraini ta yi dariya ta ce.
"Ni ban ɓoye komai ba"
Sai da ta ba su dariya dukkansu har Auta dake kwance sai da ya yi dariya.
Umma ta kalli Manaheer ta ce.
"Gaskiyar magana banji daɗin abin da ki ka yi ba maiyasa ki ka aikata hakan?"
Manaheer.
"Umma ki ya haƙuri nasan ban kyauta ba amman dan Allah karki mayar ma Abba kuɗin nan"
Darraini.
"Uncle Nasser mu ya bawa kuɗi amman kina gani dai acikin dubu ashirin dubu biyar kawai ya bamu"
Shukrah.
"Kuma wallahi uncle ya bashi kuɗi amman ki duba kiga abin da ya bamu"
Manaheer.
"Umma dan Allah ki fahimce mu"
Umma.
"Tabbas kun yi kuskure kuma na yi muku uzri amman kar ku sake aikatawa"
Shukrah Umma ta kira sunanta duk suka waigo suka kalleta.
Umma.
"Kin bamu abinci ba miya ashe kin kwashe miyan kin ɓoye sannu da aiki"
Dukan su Umma ta basu dariya Manaheer ta ce.
"Umma wace sana'a zamu fara tunda kinga mun samu kuɗi?"
Shukrah.
"Kuɗin bai kai na siyan fridge ba mu fara sai da awara muga abinda Allah zai yi"
Umma.
"Gaskiya bana son sai da awara saboda zama gaban wuta za kuyi baƙi"
Manaheer.
"Umma neman halak da wuya.
Umma.
"Ku bani lokaci zan yi shawara in ga abin da ya dace"
Bayan sati ɗaya
Umma ta fara sana'ar sai da turare kuma alhamdulellahi ta na samun ciniki sosai.
Darraini ta gama secondary school ta na zuwa islamiyya tare da Shukrah.
Mama ta kama sana'a ganin Umma na yi daman akwaita da ga sa.
Mimah kuma ta zama ƴar yawon celling birthday party da sauransu wani lokacin ita ke taimakawa uwar da abinda za suci.
Komawar Aunty Maryam da kwana biyu ta haiwu na miji yanzu haka Umma ta na shirye shiryen zuwa suna ita da yaranta.
Abba ne ya dawo gida akan mashin ɗin shi ya shigo zaure ya ga mace da namiji rungume da juna.
Mimah ba ta yi tunanin dawowar Abba a lokacin ba hankalinta ya ta shi ganin asirinta zai tonu ta saki saurayin ta yi waje da gudu saurayin ya take mata baya.
Da gudu Abba ya bisu amman sun ɓace ma ganin shi ya yi kwafa ya ce.
"Wallahi za ki dawo ki sameni koma wace ce acikin ku yau dubu ya cika"
Ya shiga gida ya na kiran matan shi kusan a tare suka fito suna kallon shi.
Abba hankali a tashe ya ce.
"Ina yara suke?"
Mama gabanta ya faɗi ta ce.
"Mimah ta na ɗaki ta na karatu"
Abba ya kalli Umma tun kafin ya tambayeta.
"Darraini da Shukrah su na ɗaki"
Tun kafin ta ƙarika ya taso a hassale ya ce.
"Manaheer ta na ina?"
Umma hankali kwance ta ce mishi.
"Na aiketa gidan hajiya Zulai ta kai mata turare"
Abba ya kasa magana zufa kawai yake yi daman girkin Mama ne Umma ta koma ɗaki.
Abba ya kalli Mama ya ce.
"Ɗauko mun darduma yau a tsakar gidan zanyi sallah"
Mama hankali tashe ta ɗauko darduman ta shimfiɗa ta aje mishi buta ta yi cikin ɗaki da sauri.
Ta na shiga ta ɗauko wayarta Mimah ta kira bata tsaya jiran abin da zata ce ba ta riga ta.
"Duk inda ki ke kiyi ma za ki dawo gida ta faɗa mata abin da ya faru"
Mimah ta ruɗe uwar ta kwantar mata da hankali ta ce.
"Yanzu kina Ina?"
Mimah.
"Gani a ƙofar gida zan shigo"
Mama.
"Karki kuskura ki shigo bari in janye hankalin shi ki kasance a shirye"
Mama ta yanke wayar ta fita Abba har ya kusa idar da alwala ta kalleshi ta ce.
"Alhaji ka yi mantuwa baka shiga toilet ba"
Abba ya kalleta hankalinshi a tashe ya ce.
"Bana son matsawa ko nan da chan so nake in ga mara kunyar da zata shigo mun gida"
Da dubara Mama ta janye hankalin shi ya na shiga toilet Umma ta na fitowa daga ɗaki.
Mama ko kallon Umma ba ta yi ba ta je zaure ta riƙo hannun Mimah suka shige ɗaki suna shiga Abba na fitowa daga toilet.
Umma ta yi murmushi Abba ya watsa mata harara.
Ya yi alwala ya tayar da sallah Umma ta zauna kusa dashi bayan ya idar da sallah ya shiga ɗakin shi ya ɗauko ƙaton dorina ya aje.
Ya kalli Umma ya ce.
"Lafiya kin zo kin tasa ni a gaba da kallo kamar mai ɗaukar photo?"
Umma.
"Daman maganar tafiya zanyi maka?"
Umma ta na rufe baki ya fara faɗa kamar ta cinna mishi huta.
Su na cikin haka Manaheer ta yi sallama ta shigo hannunta riƙe da na Auta Abba ya yi tsalle ya ɗau dorinar shi ya fara dukan ta dashi.
Umma hankali tashe ta nufi Abba Shukrah Darraini su kayo waje da gudu Abba ya ture Umma saura kaɗan ta faɗi Shukrah ta riƙo ta.
Manaheer na tsaye Abba na dukanta ko motsawa ta ƙiyi daga inda ta ke.
Mama ta fita daga ɗaki ta na bawa Abba haƙuri Abba ya yi banza da ita Darraini ta na kuka ta na cewa Manaheer ta gudu.
Manaheer jinta da ganinta ne suka ɗauke ta yanke jiki ta faɗi Abba duk ya farfasa mata jiki.
Abba ya ce.
"Gwara ace kin mutu da ki jawo mun abin kunya"
Umma ta fashe da kuka ta ce.
"Darraini Shukrah ku zo ku kama ta mu kaita ɗaki"
Suka kamata suka shiga da ita Mama ta na ta bawa Abba haƙuri.
"Ɗan yau ne ka haifesa baka haifi halinsa ba" cewar Mama.
A ɗakin Umma sun yayyafawa Manaheer ruwa amman bata farfaɗo ba hankali tashe Umma ta ce.
"Shukrah ɗauko mayafi mu kai ta hospital karta mutu"
Darraini ta fita ta samo mai napep suka kulle ɗakin suka nufi hospital.
Har su kaje hospital Umma na kuka su na zuwa a ka yi emergency da ita.
Shukrah ta na ta safa da marwa ta ma kasa zama Darraini da Auta suna jikin Umma suna kuka.
Idan ka gansu a lokacin sai ka tausaya musu
An ɗauki dogon lokaci kafin Doctor ya fito ya tambayi Shukrah sune suka kawo Manaheer ta ce. "Eh"
Doctor.
"Kira mun mahaifinku"
Shukrah.
"Baya gari"
Doctor.
"Kira mun wanda kuka zo tare"
Umma ta taso ta bi bayan doctor Shukrah ta bi ta a baya.
Doctor ya cire glass ɗin idon shi ya ce.
"Waye ya yi mata irin wannan dukar?"
Shukrah.
"Ba duka bane accident su ka yi a mashin"
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Page 45~46
Doctor.
"Wannan bai yi kama da hatsari ba."
Shukrah.
"Mu dai abin da muka sani kenan."
Daga haka ta ja ba kinta bata ƙara cewa komai ba.
Doctor.
"A binciken da mu kayi munga alamun faɗuwa saboda haka zuwa anjima za muyi mata hoton kai domin tabbatar mana da lafiyarta."
Umma ta yi ajiyar zuciya doctor ya miƙawa Shukrah takarda ya ce.
"Kije ki kawo mun yanzu ina jira zanyi amfani dashi ne."
Shukrah ta karɓa ta fita Umma ta bi bayan ta Darraini ta taso da sauri ta na tambayar Shukrah abin da ya gaya musu.
Ba tare da ta ce komai ba ta karɓi kuɗi gurin Umma ta tafi siyo abin da ya rubuta.
Umma ta kalli Darraini ta ce.
"Za kuje gida keda Auta da Shukrah idan Allah ya kaimu da safe kwa dawo."
Darraini.
" Umma dan Allah Aunty Shukrah su tafi su barni a nan."
Umma.
"Yaushe na fara magana kina bani amsa.?"
Darraini ta yi shiru saboda ta fahimci ranta a ɓace ya ke.
Umma ta kamo Auta da har yanzu kuka ya ke yi ta rarrashe shi.
Auta.
"Umma mai ya sa Abba ya daki Aunty Manaheer.?"
Umma ta yi shiru domin ba ta da amsar da za ta bashi.
Ganin Umma ta yi shiru ba ta ce komai ba Auta bai ƙara magana ba.
Shukrah ta zo ta wuce ta shiga officer ɗin doctor 10 minutes suka fito tare ya na gaba Shukrah na binshi a baya Shukrah ta tsaya a gurin Umma.
Doctor emergency ya koma ya samata drip da allurai ya kira nurse ya ce. "A canza mata room."
Bayan an canza mata room dukkansu suka shiga suka samu ta na kwance fuska ya haye kamanin ta duk ya sauya.
Umma ta kalle su.
"Shukrah ku tafi gida dukan ku da safe idan Allah ya kaimu kwa dawo."
Shukrah ta matsa gaban gadon cike da tausayawa ta na kallon yanda fuskan Manaheer ya sanja.
Hawaye ya zubo a idanun Shukrah Umma ta kau da kai Darraini ta rungumeta ta na rarrashin ta ita ma Darraini hawaye ne a fuskanta.
Umma.
"Ku zo ku wuce gida dare ya nayi bana son tafiyar dare."
Shukrah ta kama hannun Auta suka fita Umma ta ba Darraini kuɗi su sai wani abun kar su kwanta da yunwa Darraini ta amsa ta bi bayan Shukrah.
Napep suka hau ya kai su har ƙofar gida Abba suka samu a tsaye a zaune a saman dakali ya na ganinsu ya taso da sauri ya na tambayar daga ina suke.
Auta ya dinga jan hannun Darraini har sai da ta bishi suka wuce suka bar Shukrah ta na bashi amsa.
Bayan shigan su ɗaki suka rama salolin dake kansu Shukrah ta kallesu ta ce.
"Nasan ku na jin yunwa gashi dare ya yi ko zamu dafa taliya ne.?"
Darraini.
"Ba na jin yunwa."
Auta shima ya ce.
"Nima ba na jin yunwa."
Shukrah ta dinga lalaɓasu amman suka dage basa jin yunwa.
Shukrah ta kwaso kayan da ta san zasu iya buƙata daman da ruwan zafi a flask ta ɗauka ta kalli Darraini ta ce.
"Zan koma hospital domin nasan dole zasu buƙaci wannan kayan."
"Ba zama zanyi ba ina kai musu zan dawo ki kulle ƙofar idan na dawo zan ƙwanƙwasa."
Shukrah bata jira cewar su ba ta yi waje Darraini ta kulle ƙofar ta ɗauko Qur'ani ta na karantawa.
Shukrah ta isa hospital goma saura ta tura kofar ɗakin ta shiga Umma na zaune a gurin da suka barta da alamu tun fitarsu ba ta tashi ba.
Shukrah ta na ta sallama shiru Umma bata amsa ba.
Shukrah ta dafa mahaifiyarta Umma ta yi ajiyar zuciya ta kalli Shukrah.
"Maiya dawo dake cikin daren nan.?"
Shukrah.
"Kaya na kawo"
Umma ta karɓi kayan ta ce "Ki tafi gida kar dare ya ƙarayi."
Shukrah.
"Umma a yanzu bama da wanda muke kalla mu ji daɗi idan bake ba."
"A yanzu bama da gatan da wuce ka san cewa a tare dake."
"Umma idan wani abu ya sameki nida ƴan uwana ba zamu iya jurewa ba."
"Umma dan Allah ki rayu damu ba tare da wani lalura ba."
Umma ta yi shiru ta na sauraron ƴarta mafi soyuwa a gareta.
Shukrah.
"Tun fitar mu kike zaune a nan ko motsawa ba kiyi ba."
"Umma dan Allah karki bari damuwa ta sa miki wani laluran."
Shukrah ta fashe da kuka Umma ta na hawaye ta na shafa kan Shukrah ta ma kasa magana.
Tun fara maganar Shukrah Manaheer ta farka kuma ta saurari dukkanin abin da Shukrah ta faɗa hankalinsu ya yi nisa shiyasa ba su lura da ita ba.
Shukrah ta kalli in da Manaheer ke kwance ta ga hawaye nabin fuskan ta hankali tashe ta ƙarika gaban gadon.
Manaheer jin motsin Shukrah a kusa da ita yasa ta fashe da kuka Umma ta matsa ta na rarrashin su domin dukansu kuka su keyi kuma ta rasa wanda zata fara rarrashi.
Shukrah ta yi shiru tana kallon ƴar uwanta cike da tausayawa ta ke tambayar Manaheer.
"Ba bu in da ke miki ciwo.?"
Manaheer ta kaɗa kai Shukrah bata ƙara magana ba ta fita Umma ta zauna gefen gadon ta na cigaba da rarrashin Manaheer.
Shukrah bata jima da fita ba ta shigo hannunta ɗauke da manyan ledoji guda biyu.
Umma ta bi Shukrah da ido Shukrah ta haɗawa Manaheer tea Umma ta na zaune ta ma kasa motsi a gurin.
Shukrah ta taimakawa Manaheer ta wanke baki ta zaunar da ita gefen gadon ta fara bata tea.
Umma.
"Shukrah a ina kika samu kuɗin da kika siyo wannan kayan.?"
Shukrah.
"Ina fita daga ɗakin nan zanje shago na haɗu da wani ya na ta bina har shagon siyayyar sai da ya rakani."
"Shine ya biya kuɗin siyayyar harda abinda ban ɗauka ba."
Umma ta ɓata rai Shukrah ta aje cup ɗin ta duƙa a gaban mahaifiyarta ta ce.
"Umma dan Allah karki ɓata ranki wallahi nima ba a san raina ba."
"Bi na yake tayi yana mun magiya shiyasa na karɓa amman nayi miki alƙawarin ba zan ƙara ba."
Umma.
"Shike nan yanzu ki tafi gida dare ya yi."
Umma ta ɗau cup ɗin ta cigaba da bawa Manaheer tea.
Shukrah ta shafa kan Manaheer ta yi musu sallama ta fita.
Shukrah ta na sauka ta samu Abba zaune a in da ya zauna ɗazun Abba ya na ganin Shukrah ya fara masifa.
"Wallahi ba zan ɗauki wannan iskanci ba saboda ba a ɗaukeni a bakin komai ba shine zaki sa ƙafa kibar gida ba tare da sanina ba.?"
Ta inda yake shiga bata nan yake fita ba Shukrah ganin maƙota sun fara leƙowa suna bashi haƙuri yasa ta zame jikinta ba tare da ya lura ba ta shige gida.
Ta na shiga ta samu Darraini ta buɗe kofa ta faɗa ɗakin ta mayar ta kulle.
Darraini.
"Bayan fitanki Abba ya shigo ya na tambayar in da ki ka je shina na faɗa mishi."
"Ina gaya mishi ya fara faɗa ya fita ƙofar gida ni kuma ganin hakan sai na buɗe kofar ban rufe ba."
Shukrah.
"Ai kinyi taimako wallahi domin Abba jama'a ya ta ra mun kamar wace ta yi sata."
Darraini ta yi murmushi ta ce.
"Aunty Shukrah Manaheer ta tashi.?"
Shukrah.
"Eh ta tashi har tasha tea."
Darraini.
"Alhamdulellahi."
Suna cikin haka suka ji shigowar Abba ya na faɗa ai da gudu suka shige bedroom suka kashe fitila.
Abba ya zama boss😂😂😂
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Wannan page ɗin na sadaukar dashi ga Oum Ihsan
Muna godiya da yanda kike kulawa damu ubangiji ya ƙara miki lafiya da nisan kwana dama sauran manyan namu Allah yaƙara kula mana daku ubangiji ya yi muku sakayya da gidan aljanna 🙏
Page 47~48
Washe gari duk ayyukan da ya dace su yi sai da suka yi sukai wanka suka shirya sun fito suna rufe ƙofa Mama ta zo ta ce.
"Babanku bai gaya muku za ku yi girki ba.?"
Darraini.
"Eh bai faɗa mana ba kuma na ga ba girkin Umma bane."
Mama.
"Rashin kunya za ki yi mun saboda na faɗa muku saƙon ubanku.?"
Shukrah ta gama kulle kofar ta yi gaba ta na cewa Darraini
"Idan kin gama tsayuwar ni na yi gaba."
Darraini ta raɓa gefen Mama zata wuce Mama ta riƙeta gam ta ce.
"Wallahi baku isa ba sai kun yi abin da mahaifinku ya ce."
Shukrah har ta kai zaure ta ji abin da Mama ta ce ta dawo ta fasa fitar ta zuba wa Mama idanu ta na mata wani irin kallo ga idanun masha Allah.
Mama ta saki Darraini ta na zare ido Shukrah ta sa Darraini a gaba suka tafi.
Bayan fitan su Mama ta fashe da kuka Abba ya fito daga ɗaki cikin shirin fita.
Mama ta na ganin shi ta ƙara fashewa da kuka Abba hankali a tashe ya matsa ya riƙeta yana tambayar abin da ke faruwa.
Mama.
"Cema Darraini na yi dan Allah ta tsaya ta yi girki ina son zan je duba Manaheer da ga nan in wuce gida kasan na gaya maka Umman mu bata da lafiya.?"
"Shike nan daga faɗan haka su ka fara zagina wai ni ce nasa ka daki Manaheer."
Mama ta ci gaba da kuka tana yi tana kallon Abba gashi hawayen yaƙi zuwa Abba ya kalleta ya ce.
"Ina Mimah ba sai ta yi miki girkin ba."
"Mimah ba ta nan sun je registration ɗin makaranta."
Abba ya bata haƙuri ya ce.
"Ta kwantar da hankalinta zai ɗau mataki."
Mama ta ce.
"Ni dai bance ka duke su ba amman dan Allah ka nu na musu muhimmanci na a gurinsu nima fa uwarsu ce amman sun tsaneni."
Ta ƙara fashewa da kuka Mama.
"Na rasa abin da na yi ma ƴaƴanka suka tsaneni gashi ni kuma Allah ya jarabceni da ƙaunarsu."
Abba ya dinga bata haƙuri har ta yi shiru ya kalleta ya ce.
"Shirya muje hospital ɗin nima chan zan je."
Mama ta ɓata fuska ta shige ɗaki ta yi kusan 30 minutes kafin ta fito Abba ya goyata suka nufi hospital.
A bakin hospital ɗin Abba ya tsaya ya ce.
"Bari in sai musu fruits."
Mama.
"Alhaji ba sai ka siya ba kasan duk wanda yazo duba mara lafiya baya zuwa haka kawai."
"Gwanda ka basu kuɗin su ƙara."
Abba ya ja mashin ya fasa siya bayan ya aje mashin suka shiga ciki da ƙyar suka gane room ɗin.
Suka shiga da sallama Manaheer na kwance suna fira amman ganin shigowar Abba yasa ta rufe idonta.
Umma na gefen gadon a zaune Shukrah ta na zaune saman kujera ta na danna wayar Umma.
Darraini ta na yanka fruits Auta na gefenta Umma ta amsa sallamar tana musu barka da zuwa.
Abba ya matsa gaban gadon ya na tambayar mai jiki.
Umma.
"Jiki da sauƙi."
Mama ta gaisheta ta yi mata ya mai jiki Umma ta amsa ta kau da kanta.
Abba.
"Yanzu fisabiliahi kin kyauta Kenan.?"
"Daga ɗan wannan abun kin kwaso yarinya kin kawo ta hospital kuma kin san ba kuɗi na ke dashi ba."
Abba ya na rufe baki doctor ya yi sallama ya ce. "Su zo ga mai hoton nan yazo."
Shukrah ta taɓa Manaheer ta ce.
"Sister za muje gurin hoto yanzu zamu dawo."
Manaheer ta tashi taƙi kallon in da Abba ya ke tabi bayan Shukrah suka tafi Darraini ma tabi bayan su.
Abba ya kalli Umma ya ce.
"Amina laifin me na yi miki da za ki cusa ma yarana tsanata.?"
Umma ko kallon shi ba ta yi ba zai fara faɗa Umma ta ce.
"Karka nu na musu halinka dan Allah ka ga nan hospital muke abin magana baya wuya"
Mama ta ce.
"Amman gaskiya Amina kin yi kuskure."
Umma ta katse ta.
"Kar in ƙara magana kina samun baki da fatan kin gane.?"
Mama ta tashi ta kalli Abba ta ce bani kuɗin mota in wuce daga abin arziki na ga zai zama na tsiya.
Daga haka Umma bata ƙara cewa komai ba ta ɗau fruits ɗin ta cigaba da yankawa.
Abba da zai tafi ya ajiye musu dubu biyar ya ce
"A sai magani raguwar kwayi cefane."
Umma ko kallo bai isheta ba har ya gama surutun shi ya fita Mama na binshi a baya.
Suna tafe Mama na ƙara zu gashi
"A gaskiya Alhaji sai kayi da gaske."
"Kaga wani kallon tsana da yaran nan ke binka dashi kamar ba mahaifinsu ba.?"
Har ya kaita in da zai kaita bai ƙara cewa komai ba.
Bayan ya ajiyeta kasuwa ya wuce bai jima da zama ba Naseer ya kira shi a waya bayan sun gaisa yake tambayar.
"Yaushe Umma za su taso Aunty Maryam ta ce ya tambaye shi."
Abba.
"Gaskiya ba zata samu zuwa ba."
Nasser.
"Saboda mene.?"
Abba.
"Manaheer ne bata da lafiya yanzu haka suna hospital an basu gado."
Nasser.
"Subhanallahi shine baka sanar ma kowa ba.?"
Abba.
"Bana son tayar muku da hankali ne amman jikin nata da sauƙi."
Su kai sallama 10 minutes yaga alert ɗin dubu hamsin daga Naseer.
Bada jimawa ba Umar ya kira shi a waya suka gaisa ya tambayi mai jiki.
Umar.
"In sha Allah idan na samu lokaci zan shigo."
Abba.
"Ai jikin nata da sauƙi kuma kaga gobe suna zamu haɗu idan na shigo."
Su kai sallama ya na aje wayar ya ji shigowar message yana dubawa yaga Umar yasa mishi dubu saba'in.
Abba ya washe baki ya fara lissafa abinda zai yi da kuɗin daman ya karɓi kuɗin gidan da za su siya mai ya zuba shi a cikin account.
Isma'eel ya kira wayar Abba suka gaisa kamar yanda su kayi da sauran shi kuma dubu arba'in ya sa mishi.
Umar aikin bank yake yi Nasser shagon sai da wayoyi manya har guda biyu dashi da Umar har mota suka siya Isma'eel kuma shagunan shi yanzu sun zama biyu.
Da daddare bayan sallahr isha'i Abba ya sai kayan abinci har da kayan tea ya tafi dashi gida.
Kayan abincin ma a ɗakin shi ya aje Mama ta na jin dawowar shi ta shigo ta zauna akan idonta ya wuce da kayan abincin.
Bayan Abba ya wuta ya tafi ɗakin Umma Shukrah Darraini suna zaune suna fira Auta ya na sa musu baki Abba na shigowa ɗakin su ka yi shiru Auta harda ɓoye kanshi ajikin Shukrah.
Abba ya ji zafin haka musamman yanda ya ga Auta ya na yi kamar wanda ya ga dodo amman bai nu na ba domin yafi ganin laifin Umma ita ce ta sa su suke wannan abun.
Shukrah Darraini suka haɗa baki suka gaishe shi ya amsa yana hararan su.
Abba.
"Ita Umman na ku bata gaji da zaman hospital ɗin bane.?"
Shukrah.
"Ba a basu sallama ba."
Abba har ya fita ya dawo ya ce.
"Kun ci abinci.?"
Shukrah.
"A'a ba muci komai."
Abba ya jefa musu dubu biyu ya yi waje abinshi.
Cike da mamaki suke kallon kuɗin Darraini ta ɗauko ta miƙawa Shukrah.
Shukrah ta ce.
"Ƙila ya bada ne mu kaiwa Umma."
Darraini.
"Ba na tunanin hakan gaskiya."
"Saboda bai ce komai ba da ya aje kuɗin kuma kin san Abba da kuɗi."
Daga nan suka sanja fira.
Bayan fitan Abba ɗakin shi ya koma ya samu Mama ta na jiran shi ya zauna suna ta fira a nan Mama take gaya mishi bata da lafiya ta na son ya kai ta hospital ko ya bata kuɗi ta je Abba dubu goma ya ba ta ya ce.
"Ta je hospital ɗin gobe idan Allah ya kaimu."
Mama ta kasa rufe baki saboda murna ta na ta mamakin yanda ya ɗau kuɗi haka ya bata.
Washe gari da wuri suka shirya saboda za su je unguwa da ga hospital sun fito Mama ta fito da mayafi a kai ta na waƙe waƙe babu wanda ya kalleta su ka yi waje.
Mama ɗakin Abba ta shiga yana zaune yana breakfast ta zauna suka yi tare a nan take gaya mishi fitar su Darraini.
Abba ranshi ya ɓaci ya fara faɗa Mama ta ce.
"Ni a nawa tunanin idan kabje hospital ka ta ka musu birki domin wannan ba ɗabi'ar arziki bane."
Kumafa kafin su fita sai da suka go gaishe shi amman shi a hakan suncyi mishi ba dai dai ba Allah ka ƙarawa iyayen mu lafiya ubangiji ka bamu ikon yi musu biyayya 🙏
Bayan ta gama zuga shi ta koma ɗaki Mimah na kwance tana bacci ta tashe ta.
Mama.
"Zanje hospital kuma jiya Abbanku ya gaya mun zai ai girkin rana."
"Kuma ina tunanin ba zan dawo da wuri ba dan haka idan ya aiko da cefane ki ɗaura"
Mimah ta tura baki.
"Amman kin san ban iya girki ba.?"
Mama.
"Ki koya."
Mimah ta fara ƙananun maganganu Mama ta yi waje abinta.
Mama tana fita Mimah ta tashi
"Wallahi babu girkin da zanyi sai dai kijira ƴan iskan chan su dawo sune su kafi kama da masu shiga kitchen amman bani ba."
Abba ya tura ɗakin da Manaheer take ya shiga da sallama Umma ta na zaune a saman darduma sauran duk sun haye gadon mai jinyar ma ta na zaune suna fira.
Ganin shigowar Abba su kai shiru Auta dake zaune a saman darduma ya ɓoye kanshi ajikin Umma.
Abba ko gaisuwar da Manaheer ke mishi bai amsa ba ya fara faɗa kamar ba a cikin hospital yake ba ta inda yake shiga bata nan yake fita ba.
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Page 49~50
Umma ta yi shiru ta na sauraron shi sai da ya gaji dan kan sa ya yi shiru ya samu guri ya zauna.
Doctor ya shigo ya ƙara duba jikin Manaheer ya yi mata tambayoyi ta bashi amsa.
Doctor.
"Zuwa anjima za mu rubuta muku sallama."
Umma.
"Alhamdulillah mungode likita Allah ya saka da alkhairi."
Doctor.
"Ba komai fatan mu shine Allah ya bata lafiya."
Daga haka doctor ya fita Shukrah ta kalli Umma ta ce.
"Bari muje mu dawo na san zuwa lokacin da zamu dawo an kawo takaddar sallamar daga nan sai mu tafi gaba ɗaya."
Umma.
"Dan Allah karku zauna."
Shukrah.
"In sha Allah."
Suka fita Auta ya bi bayan su Manaheer ta haye gadon ta kwanta Umma ta ɗau wayarta.
Abba ya ce.
"Na ga jikin na ta da sauƙi sosai."
Umma.
"Uhmmmm."
Abba ya ce.
"Yanzu ya dace yaran nan su dinga fita ba tare da iznina ba.?"
Umma.
"Uhmmmm."
Abba.
"Gaba ɗaya tarbiyan su ya lalace kuma Allah shine shaidata ina ƙoƙari daidai gwargwado."
Umma ta yi shiru ganin taƙi kulashi ya tashi ya aje mata dubu biyar ya ce.
"Gayi nan kun rage wani abun."
Umma.
"Allah ya saka da alkhairi."
Ta karɓa ta aje Abba ya fita Umma ta kalli Manaheer ta ce.
"A gaskiya ba najin daɗin yanda kuke wa mahaifinku dan Allah ku daina bana so domin laifin a kaina yake ɗaurawa."
Manaheer ta tura baki ta ce.
"Umma dan Allah karki sa damuwa a ranki."
Umma ta kaɗa kai ba ta ƙara cewa komai ba domin ta san tunda ta ce haka to baza ta yi abin da take so ba.
Wayar Umma ta yi ringing ta ɗaga Fatima ce take kiran ta suka gaisa take tambayar mai jiki Umma ta amsa da ta ji sauƙi za a sallame su yau.
Fatima ta ce.
"Nasan ba za ki samu zuwa suna ba.?"
Umma.
"Eh to naso zuwa amman ciwon Manaheer shi zai hanani zuwa."
Fatima.
"Karki damu Aunty Ai ciwo ya kore komai Allah ya bata lafiya."
Umma ta ce.
" Ameen." ta na miƙawa Manaheer wayar suka gaisa ta tambaye ta jiki daga nan ta mikawa Umma wayar su ka yi sallama ta aje wayar.
Fatima bayan sun gama magana ta turawa Umma dubu hamsin.
Umma bata lura da kuɗin ba sai da Shukrah ta dawo ta karɓi wayar sannan ta ga alert ɗin kuɗi ta nu na wa Umma.
Umma ta ce.
"Aikin Auntyn ku domin ɗazun munyi waya da ita."
Doctor ya kawo takaddar sallama suka haɗa kayan su gaba ɗaya suka samu napep ya kawo su gida.
Mimah zaune a tsakar gida kai ba ɗankwali ta na zaune a tabarma ita da wani saurayi suna fira da littafi a gabanta wai da sunan yana mata karatu.
Umma ta yi sallama ta shiga ɗakin ta Shukrah Darraini Auta suna biye da ita Umma ta shiga bedroom ta ce.
"Zan ɗan kwanta dan Allah banda hayaniyya."
Umma bata jira amsa ba ta shige bedroom tana shiga Manaheer ta yi murmushi ta kalle su ta ce.
"Bari in je gurin Mimah in dawo."
Manaheer ta yi waje Darraini ta bita kai tsaye Manaheer gurin su Mimah ta nufa ta kalli saurayin ta ce.
"Mallam ta shi kabar gidan nan."
Mimah ta ce.
"Saboda a kanki yake da za ki ce ya tashi ya tafi."
Manaheer.
"Jira mana ai zan dawo kanki bara in gama da wannan ɗan iskan mai shigowa gidan matan aure."
Mimah ta fara masifa Manaheer ta kalli saurayin ta ce.
"Idan ka isa ka zauna in shiga in fito."
Manaheer ta shiga kitchen saurayin ya kalli Mimah ya ce.
"A ina ku ka samo wannan mai ƙiran ƴar daba.?"
Kafin Mimah ta bashi amsa ya hango Manaheer ɗauke da taɓarya saurayin ya tsaya ya na jiran ya ga dagaske zata buga mishi.
Manaheer tana zuwa ta ɗaga tabaryan hannunta ai saurayin na ganin dagaske take ya zura da gudu ko takalmin shi bai ɗauka ba.
Manaheer ta juyo kan Mimah ta na juyo wa ta ga ba Mimah a gurin.
Lokacin da Mimah ta hango Manaheer ta tawo ɗauke da taɓarya Mimah tayi readyn gudu amman ganin Musa na zaune bai motsa ba yasa ita ma ta fasa guduwa tana ganin Musa ya gudu ita ma ta yi ɗaki da gudu ta rufo.
Domin ta san halin Manaheer tsab zata buga musu wannan tabaryan.
Manaheer ta kalli ƙofar ɗakin Mama taga an rufe.
Manaheer ta ce.
"Wallahi da kun tsaya sai na buga muku ashe ma ƙananun ƴan iska ne."
Shukrah dake tsaye a bayan Darraini ta yi tafi da hannunta ta ce.
"An gaishe da jarumar gidan mu."
Darraini da ke ta faman dariya ta ce.
"Aunty Shukrah yaushe ki ka fito.?"
Shukrah.
"Ina ganin fitowar ki na san akwai abin da ku ke ƙullawa."
Manaheer ta aje taɓaryan ta shiga ɗaki bedroom ita ma ta shige ta yi kwanciyarta kusa da Umma.
Shukrah Darraini suka fara gyara ɗakin bayan sun gama suka ɗaura girki daman suna da raguwar kayan abinci wanda Umma ta ke siya ta aje Shukrah ta aiki Darraini ta siyo abin da ba shi.
Suka dafa shinkafa da miya suka yanka salad Shukrah ta haɗa zoɓo irin wanda Umma ke haɗawa ta bawa Darraini kuɗi ta siyo ƙanƙara ta zuba.
Bayan sun gama aikin su kayi wanka lokacin aka kira sallahr la'asar su ka tashi Umma.
Bayan sun idar da sallah Umma ta tashi Auta Shukrah za ta tashi Manaheer Umma ta ce.
"Ƙyaleta kawai domin tunda mukaje hospital ina lura da ita bata yin bacci."
Umma ta yi wanka Shukrah ta yi ma Auta wanka suka shirya tsaf.
Darraini ta gabatarwa da Umma abinci Umma ta ji daɗi sosai tana ta sa musu albarka a plate ɗaya suka zuba suna ci Auta ya na santi.
Suna cikin cin abincin Abba ya yi sallama ya shigo Umma ta amsa yaran su kai mishi sannu da zuwa.
Abba ya zauna ya ce.
"Har an gama abincin.?"
Umma ta ce.
"Abinci tun ɗazun aka gama."
Abba ya washe baki ya ce.
"Bari in zo."
Abba ɗakin Mama ya tura ya ji a rufe ta ciki ya ƙwanƙwasa ya ce.
"Mimah lafiya ki ka shige ɗaki ke kaɗai.?"
Mimah najin muryan Abba ta buɗe ƙofar jiki na rawa.
Abba.
"Sannu da ƙoƙari yau kinyi aikin gidan nan kin gaji da yawa."
Mimah ta ya mutsa fuska ta ce
"Abba ni banyi aikin komai ba."
Abba.
"Bangane ba kiyi aiki ba fahimtar dani yanda zan gane."
Mimah ta yi rau rau da idanu ta ce.
"Manaheer ne ta biyoni da taɓarya wai zata karyani."
Abba hankali tashe ya ce
"Manaheer ɗin da bata da lafiya.?"
Mimah ta fashe da kuka ta fara rantse rantse Abba ya tafi ɗakin Umma ya tsaya ya na kallon su ya ce.
"Ina Manaheer ta ke.?"
Umma.
"Tana ciki tana bacci."
Abba ya ce.
"Ba dole ta yi bacci ba ta san abin da ta yi."
Umma ta kalli Shukrah ta ce.
"A kwashe kayan da aka ɓata a kai kitchen."
Darraini ta kwashe kayan Shukrah ta gyara gurin tsakar gida suka je suka shimfiɗa tabarma suka zauna.
Abba ya kalli Umma ya gaya mata abin da Mimah ta faɗa mishi.
Umma ta yi murmushi ta ce.
"Manaheer ta na ɗaki ta na bacci."
"Ko da na tambayi Darraini yaushe ta kwanta ce mun ta yi ina shiga bada jimawa ba ita ma ta bi bayana."
Abba ya yi shiru ya ma rasa abin da zai ce da yaga tsayuwar ba zata fisheshi ba sai ya fita.
Gurin Mimah ya koma ya ce.
"Yanzu dai fito ki ɗaura na dare kinga har yanzu Mamanki ba ta dawo ba"
Mimah ta ce.
"To."
Abba ya koma ɗakin Umma ya na shiga Auta ya fita ya je gurin su Shukrah.
Abba ya kalli Umma ya ce.
"Da raguwar abincin a samun."
Umma ta miƙe ba tare da ta ce komai ta shiga bedroom ba ta jima da shiga ba ta fito hannunta ɗauke da plate da spoon ta aje mishi ta ƙara komawa ta ɗauko jug mai ɗauke da zoɓo ta aje mishi ta zauna.
Ta Batulu ce ✍️
💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Page 49~50
Umma ta yi shiru ta na sauraron shi sai da ya gaji dan kan sa ya yi shiru ya samu guri ya zauna.
Doctor ya shigo ya ƙara duba jikin Manaheer ya yi mata tambayoyi ta bashi amsa.
Doctor.
"Zuwa anjima za mu rubuta muku sallama."
Umma.
"Alhamdulillah mungode likita Allah yasaka da alkhairi."
Doctor.
"Ba komai fatan mu shine Allah ya bata lafiya."
Daga haka doctor ya fita Shukrah ta kalli Umma ta ce.
"Bari muje mu dawo na san zuwa lokacin da zamu dawo an kawo takaddar sallamar daga nan sai mu tafi gaba ɗaya."
Umma.
"Dan Allah karku zauna."
Shukrah.
"In sha Allah."
Suka fita Auta ya bi bayan su Manaheer ta haye gadon ta kwanta Umma ta ɗau wayarta.
Abba ya ce.
"Naga jikin nata da sauƙi sosai."
Umma.
"Uhmmmm."
Abba ya ce.
"Yanzu ya dace yaran nan su dinga fita ba tare da iznina ba.?"
Umma.
"Uhmmmm."
Abba.
"Gaba ɗaya tarbiyan su ya lalace kuma Allah shine shaidata ina ƙoƙari daidai gwargwado."
Umma ta yi shiru ganin taƙi kulashi ya tashi ya aje mata dubu biyar ya ce.
"Gayi nan kun rage wani abun."
Umma.
"Allah ya saka da alkhairi."
Ta karɓa ta aje Abba ya fita Umma ta kalli Manaheer ta ce.
"A gaskiya ba najin daɗin yanda kuke wa mahaifinku dan Allah ku daina bana so domin laifin a kaina yake ɗaurawa."
Manaheer ta tura baki ta ce.
"Umma dan Allah karki sa damuwa a ranki."
Umma ta kaɗa kai ba ta ƙara cewa komai ba domin ta san tunda ta ce haka to baza ta yi abin da take so ba.
Wayar Umma ta yi ringing ta ɗaga Fatima ce take kiran ta suka gaisa take tambayar mai jiki Umma ta amsa da taji sauƙi za a sallame su yau.
Fatima ta ce.
"Nasan ba za ki samu zuwa suna ba.?"
Umma.
"Eh to naso zuwa amman ciwon Manaheer shi zai hanani zuwa."
Fatima.
"Karki damu Aunty Ai ciwo ya kore komai Allah ya bata lafiya."
Umma ta ce.
" Ameen." tana miƙawa Manaheer wayar suka gaisa ta tambaye ta jiki daga nan ta mikawa Umma wayar su ka yi sallama ta aje wayar.
Fatima bayan sun gama magana ta turawa Umma dubu hamsin.
Umma bata lura da kuɗin ba sai da Shukrah ta dawo ta karɓi wayar sannan taga alert ɗin kuɗi ta nu na wa Umma.
Umma ta ce.
"Aikin Auntyn ku domin ɗazun munyi waya da ita."
Doctor ya kawo takaddar sallama suka haɗa kayan su gaba ɗaya suka samu napep ya kawo su gida.
Mimah zaune a tsakar gida kai ba ɗankwali ta na zaune a tabarma ita da wani saurayi suna fira da littafi a gabanta wai da sunan yana mata karatu.
Umma ta yi sallama ta shiga ɗakin ta Shukrah Darraini Auta suna biye da ita Umma ta shiga bedroom ta ce.
"Zan ɗan kwanta dan Allah banda hayaniyya."
Umma bata jira amsa ba ta shige bedroom tana shiga Manaheer ta yi murmushi ta kalle su ta ce.
"Bari in je gurin Mimah in dawo."
Manaheer ta yi waje Darraini ta bita kai tsaye Manaheer gurin su Mimah ta nufa ta kalli saurayin ta ce.
"Mallam ta shi kabar gidan nan."
Mimah ta ce.
"Saboda a kanki yake da za ki ce ya tashi ya tafi."
Manaheer.
"Jira mana ai zan dawo kanki bara in gama da wannan ɗan iskan mai shigowa gidan matan aure."
Mimah ta fara masifa Manaheer ta kalli saurayin ta ce.
"Idan ka isa ka zauna in shiga in fito."
Manaheer ta shiga kitchen saurayin ya kalli Mimah ya ce.
"A ina ku ka samo wannan mai ƙiran ƴan daba.?"
Kafin Mimah ta bashi amsa ya hango Manaheer ɗauke da taɓarya saurayin ya tsaya ya na jiran ya ga dagaske zata buga mishi.
Manaheer tana zuwa ta ɗaga tabaryan hannunta ai saurayin na ganin dagaske take ya zura da gudu ko takalmin shi bai ɗauka ba.
Manaheer ta juyo kan Mimah ta na juyo wa ta ga ba Mimah a gurin.
Lokacin da Mimah ta hango Manaheer ta tawo ɗauke da taɓarya Mimah tayi readyn gudu amman ganin Musa na zaune bai motsa ba yasa ita ma ta fasa guduwa tana ganin Musa ya gudu ita ma ta yi ɗaki da gudu ta rufo.
Domin ta san halin Manaheer tsab zata buga musu wannan tabaryan.
Manaheer ta kalli ƙofar ɗakin Mama taga an rufe.
Manaheer ta ce.
"Wallahi da kun tsaya sai na buga muku ashe ma ƙananun ƴan iska ne."
Shukrah dake tsaye a bayan Darraini ta yi tafi da hannunta ta ce.
"An gaishe da jarumar gidan mu."
Darraini da ke ta faman dariya ta ce.
"Aunty Shukrah yaushe ki ka fito.?"
Shukrah.
"Ina ganin fitowar ki na san akwai abin da ku ke ƙullawa."
Manaheer ta aje taɓaryan ta shiga ɗaki bedroom ita ma ta shige ta yi kwanciyarta kusa da Umma.
Shukrah Darraini suka fara gyara ɗakin bayan sun gama suka ɗaura girki daman suna da raguwar kayan abinci wanda Umma ta ke siya ta aje Shukrah ta aiki Darraini ta siyo abin da ba shi.
Suka dafa shinkafa da miya suka yanka salad Shukrah ta haɗa zoɓo irin wanda Umma ke haɗawa ta bawa Darraini kuɗi ta siyo ƙanƙara ta zuba.
Bayan sun gama aikin su kayi wanka lokacin aka kira sallahr la'asar su ka tashi Umma.
Bayan sun idar da sallah Umma ta tashi Auta Shukrah za ta tashi Manaheer Umma ta ce.
"Ƙyaleta kawai domin tunda mukaje hospital ina lura da ita bata yin bacci."
Umma ta yi wanka Shukrah ta yi ma Auta wanka suka shirya tsaf.
Darraini ta gabatarwa da Umma abinci Umma taji daɗi sosai tana ta sa musu albarka a plate ɗaya suka zuba suna ci Auta ya na santi.
Suna cikin cin abincin Abba ya yi sallama ya shigo Umma ta amsa yaran su kai mishi sannu da zuwa.
Abba ya zauna ya ce.
"Har an gama abincin.?"
Umma ta ce.
"Abinci tun ɗazun aka gama."
Abba ya washe baki ya ce.
"Bari in zo."
Abba ɗakin Mama ya tura yaji a rufe ta ciki ya ƙwanƙwasa ya ce.
"Mimah lafiya ki ka shige ɗaki ke kaɗai.?"
Mimah najin muryan Abba ta buɗe ƙofar jiki na rawa.
Abba.
"Sannu da ƙoƙari yau kinyi aikin gidan nan kin gaji da yawa."
Mimah ta ya mutsa fuska ta ce
"Abba ni banyi aikin komai ba."
Abba.
"Bangane ba kiyi aiki ba fahimtar dani yanda zan gane."
Mimah ta yi rau rau da idanu ta ce.
"Manaheer ne ta biyoni da taɓarya wai zata karyani."
Abba hankali tashe ya ce
"Manaheer ɗin da bata da lafiya.?"
Mimah ta fashe da kuka ta fara rantse rantse Abba ya tafi ɗakin Umma ya tsaya ya na kallon su ya ce.
"Ina Manaheer ta ke.?"
Umma.
"Tana ciki tana bacci."
Abba ya ce.
"Ba dole ta yi bacci ba ta san abin da ta yi."
Umma ta kalli Shukrah ta ce.
"A kwashe kayan da aka ɓata a kai kitchen."
Darraini ta kwashe kayan Shukrah ta gyara gurin tsakar gida suka je suka shimfiɗa tabarma suka zauna.
Abba ya kalli Umma ya gaya mata abin da Mimah ta faɗa mishi.
Umma ta yi murmushi ta ce.
"Manaheer ta na ɗaki ta na bacci."
"Ko da na tambayi Darraini yaushe ta kwanta ce mun ta yi ina shiga bada jimawa ba ita ma ta bi bayana."
Abba ya yi shiru ya ma rasa abin da zai ce da yaga tsayuwar ba zata fisheshi ba sai ya fita.
Gurin Mimah ya koma ya ce.
"Yanzu dai fito ki ɗaura na dare kinga har yanzu Mamanki ba ta dawo ba"
Mimah ta ce.
"To."
Abba ya koma ɗakin Umma ya na shiga Auta ya fita ya je gurin su Shukrah.
Abba ya kalli Umma ya ce.
"Da raguwar abincin a samun."
Umma ta miƙe ba tare da ta ce komai ta shiga bedroom ba ta jima da shiga ba ta fito hannunta ɗauke da plate da spoon ta aje mishi ta ƙara komawa ta ɗauko jug mai ɗauke da zoɓo ta aje mishi ta zauna.
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Allahumma Sali Ala Sayyadina Muhammad Wassalim 🥰
Page 51~52
Abba ya yi bismillah ya fara cin abincin ya naci ya na santi.
Sai da cinye abincin tas ya ɗau zoɓon ya na sha Umma ta kwashe kayan ta fita dasu ta na fita Shukrah ta zo ta karɓa ta aje a gurin wanke-wanke.
Ta ce ma Darraini.
"Ɗibo mun ruwan ɗauraya in wanke kayan nan."
Darraini.
"Aunty Shukrah bari in yi kawai na ga yau kin sha aiki."
Shukrah ta ce.
"A'a sai dai muyi tare."
Suka fara wanke-wanken.
Bayan komawar Umma ɗaki Abba na zaune da jug a gaban shi ya na shan zoɓo Umma ta zauna Abba ya kalle ta ya ce.
"Daman ina son zan faɗa miki wata magana amman ban san yanda za ki ɗauke ta ba."
Umma.
"Karka damu zan fahimta in sha Allah."
Abba.
"Na yiwa Manaheer miji."
Umma fuska cike da mamaki ta ce.
"Shukrah ko Darraini.?"
Abba.
"Manaheer nake nufi."
Umma.
"Uhmmmm Allah ya sanya alkhairi."
Abba ya sauko ya zauna kusa da Umma ya ce.
"Amina kina hukuntani da wannan shirun naki."
"Nafi son ki dinga buɗe baki kina mun magana."
Umma.
"Zan gyara in sha Allah."
Abba.
"Ina Manaheer ɗin take.?"
Umma.
"Ta na ciki ta na bacci."
Abba ya ce na manta ban gaya miki ba.
"Kar a ƙara aiken ta ko nan da ƙofar gida."
Umma ta kasa shanye ɓacin ranta ta dubi Abba ta ce.
"Saboda mene ba za a aike ta ba kamar wanda ta yi cikin shege."
Abba.
"Saboda ba na son su haɗu da wancan ɗan iskan saurayin da na kama su tare."
Umma.
"Kuma kana da tabbacin Manaheer ne a zauren.?"
Abba.
"To idan ba ita ba wace ce mai rawar kai acikin yarana.?"
Umma ta kalli Abba fuska cike da hawaye ta ce.
"Dan Allah karka yanke hukunci ba tare da ka yi bincike ba."
Abba.
"Babu wani binciken da zanyi bayan gaskiya a bayyane take."
Suna cikin haka Manaheer ta fito bayan ta ji duk abin da Abba ya faɗa Umma ta share hawayen fuskan.
Manaheer ta yi kamar ba ta gani ba ta gaishe da Abba ya amsa yana tambayarta.
"Waye saurayin da na ganki a zaure ranar.?"
Umma ta shige bedroom Abba ya mai da hankalin shi kan Manaheer.
"Ni banda saurayi."
Abba.
"Koma kina da shi koma baki dashi na yanke hukunci kar in ƙara jin labarin kin fita ko nan da zaure ne."
Manaheer ta kaɗa kai ta na murmushi Abba ya ƙara da cewa.
"Na yi miki miji zai zo gobe idan Allah ya kaimu."
Manaheer ta ce.
"Ba damuwa Abba in sha Allah zan ka sance mai yi maka biyayya."
"Kuma dan Allah kaya haquri ɓacin ran da na saka."
Abba ya kalli Manaheer fuska ɗauke da mamaki shi dai ya san wace ce ita kuma ya ga ta yi saurin amsawa babu damuwa a fuskanta.
Abba ya washe baki ya ce.
"Ubangiji ya yi miki albarka dan Allah karki ɗauki zugan mahaifiyar ki dan na ga alamar ba ta son wannan lamarin."
Manaheer.
"In sha Allah ba zan ɗauka ba na gode Allah yaƙara girma."
Abba ya fita yana murmushi Manaheer ta yi dariya ta ce.
"Hmmmmm."
Umma tsaye a bayan ta bata lura ba Shukrah ta shigo ta samu guri ta zauna Umma ta kalli Manaheer ta ce.
"Mai ki ke ƙullawa.?"
Manaheer.
"Ba bu abin da nake ƙullawa."
Umma ta bar zancen ba dan ta yarda ba Darraini ta shigo Auta na bin bayanta Umma ta zaunar da su ta faɗa musu hukuncin da Abba ya yanke.
Hankalin Shukrah ya ta shi ta kalli Manaheer ta ce.
"Saboda baki da hankali shi ne za ki amince."
Manaheer.
"To ya kuke son in yi dan Allah kuna ganin dai abin da ya faru dani."
Darraini.
"Amman duk da hakan bai dace ki yankewa kanki wannan hukuncin ba."
Kafin Manaheer ta ba da amsa su ka ji an ce.
"To manya manyan munafukai zugata ku keyi ta bijire ma umarni na.?"
Kafin Abba ya rufe baki duk sun shige bedroom Auta da ya rasa hanyar da zai bi ya shige bedroom ya fashe da kuka yana maƙalewa a jikin Umma.
Abba ya kalli Umma ya ce.
"Wallahi kin ji kunya."
"Kalli yanda kika sa ƴaƴan cikina ke gudu na kamar sun ga dodo."
"Abba ya kalli Auta ya ce.
"Shi kuma wannan saboda munafurci kuka yake yi kamar wanda ake yagar naman jikin shi"
"Kuma duk saboda na zo gurin.?"
Manaheer ce kaɗai bata gudu ba ta na tsaye tana ƙunshe dariya.
Sai da ya gama fadan shi sannan ya kalli Umma ya ce.
"Yau zan tafi Jos a can zan kwana saboda raɗin suna kishirya Auta mu tafi tare da shi tunda ku ba za ku samu zuwa ba."
Ai Auta na jin haka ya tsayar da kukan da yake ya kalli Abba ya sulale ya faɗin a gurin ba numfashi.
Auta ya sume saboda tsoran Abba tun lokacin da ya ga irin dukan da ya yi wa Manaheer shike nan yake jin tsoran shi.
Bama Auta kaɗai ba hatta Shukrah Darraini tsoran shi su ke ji Manaheer ce kaɗai jan wuya.
Da gudu Manaheer ta ɗibo ruwa ta miƙawa Umma Shukrah Darraini suka fito jin abin da yake faruwa.
Abba ya na tsaye ya na kallon ikon Allah Umma ta kasa riƙe ruwan Shukrah ta karɓa ta shafa mishi a fuska.
Tana shafa mishi ya ja ajiyar zuciya Auta ya buɗe ido yana kwance a jikin Umma ya na ajiyar zuciya Abba ya kaɗa kai ya yi waje.
Bayan fitan Abba suka zauna neman mafita Manaheer sai dariya ta ke ita wallahi Auta dariya ya bata.
Tun Darraini na kau da kai har tazo ta fara taya ta Umma ita kanta sai yanzu abin da Auta ya yi ya bata dariya.
Bayan sallahr magrib Abba ya shigo ɗakin Umma Auta ya na ganinshi ya shige bedroom.
Abba ya yi kamar bai ganshi ba ya kalli Umma fuska a ɗaure ya ce.
"Zan wuce."
Umma ta shiga ciki ta fito da leda ta bashi ta ce.
"Leda biyu ne aciki akwai saƙon Fatima da Rabi'a."
Abba ya ce.
"Banganeba.?"
Umma ta ce.
"Fatima ko Rabi'a duk wanda ka samu acikin su."
Abba ya karɓa ya ajiye mata dubu biyar ya ce.
"Kuɗin cefane akwai kayan abinci a ɗakina."
Abba har ya fita ya dawo ya ce.
"Ban yarda ki bawa wani makullin ɗakina ba."
Umma ta ce.
"To."
Shukrah Darraini Manaheer suka fito suna mishi Addu'a Abba saboda Jin daɗin addu'o'in da su ka yi mishi ɗari biyar biyar ya ba su.
Har zai fita Manaheer ta ce
"Abba saura na Auta."
Abba ko kallonta bai yi ba kuma har lokacin Mama ba ta dawo ba Mimah kuma a na ta girki ba a gama ba.
Abba ya bawa Mimah dubu uku ta ajiyewa mahaifiyarta Mimah ta kalli Abba ta ce.
"Abba saura ni."
Abba ya ce.
"Ki ɗau dubu ɗaya ki bata dubu biyu."
Mimah ta ce.
"To Abba ka siyo mun tsaraba."
Abba ya yi gaba abin shi bayan fitan shi Mimah ta sauke tukunyar dake kan wuta daman ba komai aciki sai ruwa da ke ta faman tausa hijjab ta sa ta yi gaba ko ƙofar bata kulle ba.
Sai da suka zo kwanciyar bacci Umma ta kalli Manaheer ta ce.
"Ba zan gaji da tambayarki dalilin da yasa ki ka amince da zaɓin mahaifinki ba."
"Ina jin kamar akwai abin da kike shirin aikatawa shiyasa kika amince da wannan zaɓin."
Manaheer.
"Maganar gaskiya bana son zaɓin da Abba ya yi mun."
"Ba ni da mafitar da ya wuce amincewa da umarni shi."
"Duk da cewar ya yanke mun hukunci ba tare da ya yi bincike ba."
"Umma idan ban amince da zaɓin shi ba komai a kanki zai sauke."
Umma.
"Shike nan zanyi addu'a ubangiji ya zaɓa miki mafi alkhairi."
Asuba ta gari.
Abba yana sauka ya samu Nasser da Umar su na zaman jiranshi Umar ya rungume shi ya na tambayar shi gajiyar hanya.
Nasser ya ce.
"Ai ka bari mu ƙarika gida."
Umar ya buɗe wa Abba gidan baya shima ya shiga ya zauna Nasser ya kalli Umar ya ce.
"Waye drivernka.?"
Umar ya yi dariya ya ce haka nan za ka tuƙa Yaya na.
Nasser.
"Daman ai na san haka za ka ce wato idan ka na son abu shine za ka kirani da wannan sunan."
Abba ya yi dariya Nasser ya shiga motar bayan sun fara tafiya ya kalli Abba ya ce.
"A gidana za ka sauka."
Abba ya ce.
"A'a gidanmu na gado za ka wuce dani."
Umar ya ce.
"Dan Allah kayi haquri mu wuce gidan shi nima a can zan kwana."
Abba ya ce.
"Shi dai bai yarda ba kawai su kaishi gidan su."
Da ƙyar Nasser ya shawo kanshi ya amince zai bisu.
Gidan Nasser masha Allah har da mai gadi gida cike da flowers masu ban sha'awa part 2 ɗaya na shi ɗaya na matar gidan.
Abba ya yi sallah Nasser ya kawo mishi abinci suka haɗu su naci suna tinawa da iyayen su.
Bayan sun gama cin abinci Abba ya gaya musu abin da ya faru da kuma hukuncin da ya yanke amman bai gaya musu dukan da ya yi mata ba ne yasa aka kwantar da ita a hospital .
Nasser ya yi murmushi ya ce.
"Kuma ka na da tabbacin Manaheer ce a zauren.?"
Abba ya ce.
" Lokacin da abin ya faru ita ce kawai ba ta gida."
Umar.
"Kuma na ji ka ce ka shiga toilet bayan ka yi shimfiɗa.?"
Abba ya ce.
"Eh na manta ma ban shiga toilet ba saboda ruɗewa Aisha ce ta tuna mun."
Umar da Nasser su ka yi murmushi su na kallon Abba.
Abba.
"Kuma a wannan lokacin Manaheer ta shigo gidan ita da Auta."
Nasser ya ce.
"Alhamdulillah ya zo da sauƙi."
Umar.
"Amman ka tambayi Auta in da su kaje?"
Abba fuska cike da damuwa ya ce.
"Yaron da ba ya son gani na acikin rayuwar shi."
Nasser Umar suka kalli Abba fuska cike da mamakin furucin shi.
A nan Abba ya ba su labarin abin da Auta ya yi daga cewa zai zo dashi nan.
Nasser ya ce.
"Lallai akwai babbar matsala a gidanka."
Abba.
"Ba bu wani matsalar da ya wuce Amina domin na san wallahi ita ke zuga su."
"Ko fira na samu su na yi suna ganina suke shiru ko kuma su zame ɗaya bayan ɗaya subar gurin."
Umar.
"Bana tunanin Aunty Amina za ta zuga su gaskiyar magana akwai dai abin da ba dai dai ba."
Nasser.
"Yanzu dai maganar haɗa manaheer aure da yaron shagonka dan Allah ka janye."
"Sannan kuma ina son idan ka koma gida ka yi bincike."
Nasser ya ciga da cewa.
"Ɗayan matsalar kuma zanji dashi."
Suna cikin haka Isma'eel ya yi sallama ya shigo.
Isma'eel ya kalli Umar ya ce.
"Yau na ga yanda ake raba zumunci."
Umar ya yi dariya ya ce.
"Ba laifina ba ne ka tambayi babban yaya ka ji."
Isma'eel bai ce komai ba ya samu guri ya zauna ya gaishe da Abba ya na tambayar shi gajiyar hanya.
Daga nan suka sanja fira Nasser ya ɗau wayar shi ya kira Aunty Maryam ya ce.
"Ta kawo mishi baby boy ɗakin shi."
Aunty Maryam ta shigo bayan ta yi sallama hannunta ɗauke da baby ta miƙawa Abba ta na gaishe shi.
Abba ya amsa Aunty Maryam ta tambayeshi mai jiki daga nan ta miƙe za ta tafi Abba ya kalli Umar ya ce.
"Ka shigo mun da jakar kayana.?"
Umar.
"Eh gashi a kusa dani."
Abba ya tsaida Aunty Maryam ya ce.
"Ga saƙonki inji Amina.
Umar ya ɗauko jakar kayan Abba ya karɓa ya zage ya ciro ledar da Umma ta bashi ya miƙawa Aunty Maryam ta amsa ta na godiya bayan ta fita Nasser ya kalli Abba ya ce.
"Ka yiwa yaronka huɗuba."
Abba ya yi murmushi cike da ƙauna ya ce.
"Mai ya sa.?"
Nasser ya yi shiru Abba ya na ganin haka bai ƙara magana ba ya yi mishi huɗu ba ya miƙawa Umar ya mayar da shi ciki.
Bayan fitan Umar Abba ya kalle su ya na murmushi ya ce.
"Sunan yaron Abdullahi."
Sunyi farin ciki da jin sunan dama babban burin Nasser kenan.
Bayan sun gama firan yaushe gamo suka kwanta Umar da Isma'eel ɗaki ɗaya Abba da Nasser ɗaki ɗaya daman part ɗinshi 3 bedroom ne kowanne da toilet aciki.
Asuba ta gari.
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Allahumma Sali Ala Sayyadina Muhammad Wassalim 🥰
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Page 53~54
Da safe Abba Nasser Umar Isma'eel kaya iri ɗaya suka yi anko Umar ya ɗinka musu shadda babbar riga.
Sunan yaro Abdullahi Nasser ya sa aka yanka ƙaton rago a kayi walimar suna da shi Isma'eel ya ɗau nauyin drinks gaba ɗaya.
Abba ya biya kuɗin hall da abin da za a ci a gurin masha Allah taro ya yi kyau Aunty Maryam ta samu kyauta da yawa daga ƴan uwa da abokan arziki can na hango Inna da Amina a kujarar baya.
Anci ansha an zubar da kuɗi sai zuwa yamma taro ya watse Aunty Maryam da Aunty Rabi'a matar Umar da Aunty Fatima ƙanwar Abba ankon kaya su ka yi Aunty Maryam ta ɗinka musu dukkansu har da Umma.
Da yamma bayan taro ya watse Aunty Maryam ta buɗe saƙon Umma acikin ledar akwai ƙarami an rubutu sunan Aunty Fatima da na Aunty Rabi'a.
Aunty Maryam ta ciro ta miƙa musu ta buɗe nata ledar duk yafi nasu girma turare ne acikin kwalabe masu ƙamshi Aunty Maryam ta yi murna sosai daman na show glass ɗin ta ya ƙare.
Khadija ta yi sallama ta shigo Aunty Maryam ta ce.
"Ba ki kwanta ba.?"
Khadija ta kwantar da kanta a jikin Aunty Rabi'a ta ce.
"Dan Allah Ammy ki sa baki Daddy ya barni in je gurin Umma."
Aunty Maryam.
"Babu ruwana a wannan maganar."
Khadija ta ɓata fuska ta fara hawaye Aunty Maryam ta ce.
"Ta shi ki fita ki bani guri."
Aunty Fatima ta ce.
"Je ki shirya kayanki zanyi magana da Yaya."
Khadija ta yi tsalle ta fita da gudu Aunty Rabi'a ta ce.
"Khadija ta na son zuwa gidan Umma."
Aunty Maryam.
"Uhmmmm."
Nasser
Abba yana zaune suna fira da ƴan uwanshi Fatima ta yi sallama ta shigo Umar ya na tsokanarta.
Fatima ta zauna suka ɗan taɓa fira daga nan ta sako buƙatar ta Nasser ya ce.
"Babu komai idan Yaya zai koma sai ta shirya ta bishi."
Fatima ta zauna suna ta fira Abba ya ce.
"Umar ɗauki matarka kuje gida dare ya yi."
Isma'eel ma sai da ya kora shi mijin Aunty Fatima ya kirata a waya ta tashi ta fita.
Bata jima ba ta dawo ta yi musu sallama ta tafi ɗakin Khadija ta shiga ta ce mata.
"Kishirya da wuri karki sa shi zaman jiranki."
Khadija ta yi tsalle ta rungume Aunty Fatima ta na dariya daga nan Anty Fatima ta yi wa Aunty Maryam sallama ta tafi.
Nasser
Ɗakin ya rage daga Abba sai Nasser sun jima suna tattaunawa game da matsalar gidan Abba kafin su kwanta bacci.
Gidan Abba
Mama bata dawo gida ba sai ana kiran sallahr isha'i ta samu ɗakinta a buɗe Mimah bata nan Mama ta ɗauko waya ta kira ta.
Mimah ta ɗaga waya tun kafin ta yi magana Mama ta ce.
"Kina in.?"
Mimah.
"Uhmmmm banyi nisa ba kin dawo ne.?"
Mama.
"Ban sani ba."
Mama ta yanke wayar ta shiga ɗaki Mimah ba ta shigo gida ba sai sha ɗaya saura.
Koda ta dawo Mama ba ta ce mata komai ba Mimah ba ta bawa mahaifiyarta kuɗin da Abba ya bata ba.
Mama ta kalli Mimah ta ce.
"Gashi ina jin yunwa kuma na san babu abin da ki ka dafa."
Mimah.
"Kisha tea kawai ki kwanta dare ya yi."
Mama.
"Ai ban da kuɗi."
Mimah ta ciro dubu ɗaya a kuɗin da Abba ya ba ta Mama ganin kuɗi ta washe baki ba bu tambayar in da ta samu kuɗin ta ce.
"Je ki siyo mun kayan tea bari in kunna gawayi."
Mimah ta fita ba ta jima da fita ba sai gashi ta dawo ta miƙawa Mama ta yi kwanciyarta.
Mama.
"Karki kwanta da yunwa."
Mimah.
"Na ci abinci a in da naje."
Daga haka ba ta ƙara cewa komai ba Mama bayan ta sha tea sai ta ɗibo rushi ta kwance jakar da ta dawo dashi anguwa ta ɗauko wani abu ta kwance ta zuba acikin wutar ta yi waje.
Ƙofar ɗakin Umma ta nufa sai da ta leƙa ta ga babu kowa a parlourn ta aje a bakin ƙofar ɗakin.
Abin da Mama ba ta sani ba ɗakin Umma ba a rufe yake ba dukansu suna cikin bedroom suna fira Manaheer ta tashi da sauri.
Umma ta kalleta ta ce.
"Ke kuma lafiyarki ƙalau.?"
Manaheer.
"Toilet zanje."
Ta fita ba tare da ta tsaya jin abin da Umma ta ke cewa ba ta na fita parlour ta ga hayaƙi na shigowa kaɗan kaɗan.
Manaheer da sanɗa ta buɗe ƙofar Mama ta gani tsaye ta na kiran sunan Umma.
Mama ta yi mamakin ganin Manaheer amman da yake ƴar duniya ce sai ta waske.
Manaheer ta ce.
"Wallahi babba ya kama girmanshi tun muna mu biyu ban kira jama'a su zo su ta ya ni gani ba."
Mama na jin haka ta ɗau kaskon ta yi gaba Manaheer ta ɗaga murya yanda za ta jiyo ta.
"In sha Allah mutum sai ya ga aniyar shi ba dai mugun nufi ba Allah zai gwada wa mutum abin da ba ya son gani."
Da sauri Mama ta shige ɗaki Manaheer ta juyo za ta koma ɗaki su ka haɗa ido da Shukrah Manaheer ta ɗaure fuska ta raɓa ta shige.
Shukrah ta yi murmushi domin duk abin da ya faru ta gani Manaheer ta ɗaure fuska ne kar Shukrah ta tambayeta abin da ya faru.
Haka suka kwanta ba tare da Mama ta ba su abincin dare ba kuma dama can Umma ba ta sa ran samun abinci daga gurin Mama ba.
Da safe suna cikin yin breakfast Mama ta zo gurin Umma a kan a bata makullin ɗakin Abba.
Umma ta yi shiru ta na tunani domin ta rasa abin da za ta ce mata gashi dai Abba ya bar sallahun kar a ba kowa keys.
Kafin Umma ta gama yanke shawara ta ji Manaheer na cewa.
"Abba ya ce ko waye ya zo karɓan makulli kar a bashi."
Mama ta kalli Manaheer ta ce
"Ba dake nake ba dan haka kar in sake magana ki samun baki."
Manaheer ta yi ƙwafa ta kau da kai Umma ta harare ta.
Umma ta fuskanci Mama ta ce.
" Abban Shukrah da zai tafi ya ba da umarnin kar wanda ya buɗe mishi ɗaki."
Mama ta fara masifa Umma ganin haka ta kalli Shukrah ta ce.
"Ku kwashi abin karywan ku shiga bedroom."
Mama ta na ta tijjara Umma ta ba banza ajiyarta Mimah ta tawo gurin ta kalli Umma cike da rashin kunya ta nu na Umma da yatsa ta ce.
"Mallama ki bamu key zamu ɗauki abin karyawa."
Mama ta washe baki ta ce.
"Haiwuwa mai rana Allah na gode maka."
Manaheer da fitowarta kenan daga bedroom ta ji abin da Mimah ke cewa ba bu wanda ya lura da fitowarta su dai jin ƙaran mari su kayi.
Umma da Mama a tare su ka kalli inda ƙaran marin ya fito Manaheer ce a tsaye ta murɗe hannun Mimah.
Tunda Umma ta ce su shiga bedroom Manaheer ta ke tsaye a bakin ƙofa ta na leƙen abin da ke faruwa.
Mari huɗu ta yi wa Mimah sannan ta murɗe hannun da ya nu na Umma.
Mimah na ta ku ka ta na zagin Manaheer amman ita ko ajikin ta.
Mama ta yi ta yi ta ƙwace hannun Mimah a gurin Manaheer amman ta ka sa
Umma
Manaheer ba na son tashin hankali sakar mata hannunta."
Manaheer ta saki hannun Mimah ta kama kunnenta.
"Wallahi ko kallon banza na ƙara ganin kin yiwa Umma sai na zane miki jikin ki."
Mama ta kama hannun da a ka murɗe ta na dubawa hannun ya yi jawur har ya ɗan kumbura.
Mama ta na ta zage-zage Manaheer da ta kusa shiga ɗaki ta juyo ta yi wa Mama kallon gargaɗi kafin ta shige ɗaki.
Ga mari ga tsinka jaka
Mama ta kama hannun ƴarta mai lafiya su ka shiga ɗaki.
Umma ta ɗau waya ta kira Abba wayar taƙi shiga Mimah sai kuka ta ke yi Mama ta daka mata tsawa ta ce.
"Dallah rufe mun baki sakarya kawai kin ishe ni da ihu ni ko a labari ban taɓa ganin sakarya mara wayyau irinki ba."
"Kwanaki haka ta yi miki gashi yanzu ma ta ƙara har da cewa sai ta za ne ki saboda kin zama shasha mara wayyau."
Mimah dai ba ta ce komai ba ta na fama da hannu Mama ta sa hijab ta kalli Mimah.
"Sa hijjab ɗinki mu tafi gurin magani dan banga ta zama ba".
Mama ta janyo ƙofar ta kulle ta riƙo Mimah iyayen raki su ka fita.
Umma ta yi ajiyar zuciya ta na mamakin wannan lamarin ganin tunani zai ci ƙarfinta ya sa ta tashi ta shiga bedroom Manaheer na kwance ta yi bacci sauran suna karatu.
Manaheer ɗin ma idon ta biyu ta yi haka ne dan kar Umma ta yi mata faɗa.
Umma ta kalli Auta.
"Yau mai ka ke son a dafa Autar Umma da Abba.?"
Auta ya yi murmushi cike da jin daɗin sunan da aka kira shi dashi ya ce.
"Umma dan Allah masa."
Dukkansu sunji daɗin zaɓin Auta daman an kwana biyu ba a ci masa ba.
Umma ta ba Shukrah kuɗi ta ce.
"A siyo duk abin da ya da ce."
Shukrah ta karɓi kuɗin Umma ta ce.
"Kaina ke ɗan sara mun bari in kwanta kafin ku dawo."
Shukrah ta bawa Darraini kuɗin cefane Auta ya ce.
"Dan Allah Aunty Darraini zan biki."
Bayan fitan su Shukrah ta wanke shinkafa ta jiƙa Manaheer ce ta fito daga bedroom ta na murmushi.
Shukrah ta yi kamar bata ganta ba Manaheer ta haɗa wanke wanke ta wanke ta gyara gurin ta zo ta zauna kusa da Shukrah.
Shukrah ta ɗauke kai Manaheer ta kwanto jikin ta.
"Wai dan Allah laifin mai na yi a ke shareni.?"
Shukrah ta kau da kai
Manaheer.
"Shike nan kunfi son in yi shiru a na cin zarafin mahaifiyar mu.?"
Shukrah ba ta ce komai ba Manaheer ta ci gaba da cewa.
"Wallahi ko yanzu Mimah ta ƙara aikata abin da ta yi yau sai na karya ɗan yatsar."
"Ai ko yau na ƙyalleta ne saboda Umma amman bayan haka wallahi da ta gane shayi ruwa ne."
Shukrah.
"Wato ma kin san abin da ki ka aikata koh.?"
Manaheer.
"Dan Allah mai yasa idan zan yi abu kike bin ba ya na ki na mun laɓe ko dai kema course ki ke ɗauka.?"
Shukrah ta kai mata duka ta kauce ta na dariya.
"Wallahi Manaheer ba za ki taɓa sauyawa ba ace mutum kamar ana kaɗa mishi ganga."
Manaheer.
"Ni dai ki ba ni amsar tambayar da na yi miki."
Shukrah.
"Sai na ji duka sannan zan ba ki amsar tambayarki."
Shukrah.
"Wallahi ina tausaya wa wanda Abba ya ce ya zo ku daidaita domin na san halin ka ya na sarai."
Manaheer.
"Uhmmmm kin ma tuna mun yau ina da babban baƙo."
Shukrah.
"Ubangiji ya nu na mun ranar da za ki shiryu."
"Ameen.
Darraini ta dawo Shukrah ta wanke kayan miya Auta ya kai ni ƙar shinkafa gidan a ku sa da gidan su ya ke.
Manaheer ta niƙa kayan miya a greater Darraini ta kunna huta.
Miyar su ka fara ɗaurawa a wuta kafin Auta ya dawo Manaheer na yanka alayyahu su na fira Shukrah na ɓare magi Darraini na daka gyada.
Bayan sun gama Shukrah ta ware kayan miya da ban ta aje Darraini ta yanka albasa ta zuba a cikin wannan kayan miyar da Shukrah ta aje.
Auta ya yi sallama ya shigo Darraini ta sauke robar da ke kanshi Shukrah ta raba ƙullin wainar biyu ta aje ɗayan a gefe ɗayan kuma ta sa sugar su ka fara suyar mai sugar gidan sai ƙamshi ya ke tashi.
Dukkansu su ka haɗu su ke suyar Auta na ta ya su.
Manaheer ta ɗauƙo rabin ƙullin wainar ta zuba acikin kayan miya da albasa ta zuba spices da kayan ɗanɗano ƙullin yaji albasa da kayan miya sai da ta tabbatar komai ya yi mata yanda take buƙata sannan ta rufe ta aje ta shiga kitchen ta ɗauko roba mai murfi ta aje.
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Page 55~56
Bayan sun gama suyar mai sugar suka ɗauko wannan ƙullin mai haɗi suka soya shi.
Darraini ta haɗa kunun aya Manaheer ta gyara gurin Shukrah Darraini suka wanke kayan da su ka yi amfani da shi.
Sallahr azahar aka kira suka yi alwala Auta ya shiga bedroom Umma ta na zaune a saman bed ta yi ta gumi Auta ya dafa ka faɗarta Umma ta kalle shi.
"Yaushe ka shigo.?"
Auta
"Yanzu na shigo ina ta magana kin yi shiru."
Umma
"Har kun dawo daga kasuwar.?"
Auta ya yi dariya ya ce.
"Har mun gama girki za ki ce."
Umma ba ta cewa Auta komai ba ta tashi ta fito parlour ta samu yaran duka suna sallah Umma ta kalli agogo ta ga biyu saura.
Umma ta ɗau buta ta yi waje Darraini ta idar da sallah ta kira Auta.
Auta ya fito daga bedroom Darraini ta ce.
"Zo ka yi sallah mu ci abinci."
Auta ya turo baki ya ce.
"Ni dai a fara bani abincin idan naci sai in yi sallahr daga baya."
Manaheer
"Wallahi in dai kaga an baka abinci a gidan nan to ka tabbata sallah ka yi."
Auta ya fara hawaye su ka yi banza da shi Umma ta shigo ta na tambayar abin da ya sa shi kuka.
Auta ya yi shiru ya na zare ido Manaheer ta faɗa mata komai.
Umma ta kalli Auta ta ce.
"Autar Maman shi zo mu yi sallah idan mun idar sai in zuba maka abincin."
Auta ya maƙe kafaɗa ya na share hawaye ganin haka Umma ta rabu dashi ta yi sallahrta Shukrah ta zuba musu abinci a babban plate Manaheer ta ɗauko kunun aya da cups suka haɗu su na cin abincin Auta na gefe ya na hawaye.
Bayan sun gama cin abinci Umma ta na ta santi su na mata dariya Shukrah ta kaima Umma ruwan wanka toilet.
Suka gyara gurin daga nan aka dasa sabon fira.
Auta ganin sun share shi ya fara kuka Manaheer.
"Wallahi idan ba ka rufe mun baki ba sai na zane ka."
Darraini
"Auta ka na son Allah ya ƙona ka.?"
Auta ya yi shiru ya ƙi magana Shukrah ta ɗauko dorina ta ɗaure fuska ta ce.
"Wuce ka ba ni guri."
Sum sum Auta ya hau darduma ya yi sallah ko da ya idar bai tashi a gurin ba Umma da fitowarta kenan daga toilet ta ce.
"Tunda ya yi sallah sai ku bashi abinci."
Auta ya ce.
"Na ƙoshi."
Manaheer
"Ya ƙara auki."
Umma ta shige bedroom Manaheer ta shiga wanka Auta dai ya na zaune a saman darduma ya yi tagumi.
Dukkansu sai da su ka yi wanka su ka shirya sannan Shukrah ta ce.
"Darraini ta yi wa Auta wanka."
Auta ya ɓata fuska ya ce.
"Ni fa ba yaro ba ne yanzu."
Manaheer ta yi dariya ta ce.
"Sannu babban saurayi ɗan shekara 8."
Umma dake zaune a kujera ta ce.
"8 ɗin ma bai gama haɗawa ba."
Da ƙyar ya yarda Manaheer ta yi mishi wanka yasa kaya ya zauna kusa da Umma.
Umma ta kalle shi a matsayin ta na uwa ta san haka kawai Auta ba zaiƙi yin sallah ba kuma sannan yaƙi cin abinci.
Umma ta dinga ma Auta karatu ta na nu na mishi irin azabar da akeyi wa mutumin da baya sallah.
Auta ya fashe da kuka ya ce.
"Umma haka kawai na ji ba na son yin sallahr."
Umma ta rarrashe shi ya yi bacci ba tare da ya ci abinci ba.
Umma ta kalli yaranta suma ita suke kallo daman mahaifin Umma babban mallami ne na addinin musulunci.
Manaheer ta ce.
"Umma yanzu fa Auta ba yaro ba ne."
Shukrah.
"Ai ba haka kawai za ki ga Auta ya yi zuciya da abinci ba."
Umma ta kalli Shukrah cike da jin daɗi ta ce.
"Mutumin da baya jure yunwa kuma duk tsawon lokacin nan Auta bai taɓa zuciya da abinci ba."
Sun daɗe suna tattaunawa game da Auta kafin a kira la'asar har lokacin Auta ya na bacci bayan sun idar da sallah Umma ta aiki Darraini ta siyo mata zam-zam a ƙasan layin su.
Umma ta yi shimfiɗa a ƙofar ɗakinta su na zaune dukkan su Mama ta shigo ba sallama su na haɗa ido da Umma ta yi mata dariya Umma ta kau da kai Manaheer ta ga sanda Mama ke yiwa Umma dariya.
Mimah na bayan mahaifiyarta Mama ta buɗe ƙofar ta shige Manaheer haka kawai ta ji ba ta yarda da Mama ba.
Babu jimawa Darraini ta dawo Umma ta ce.
"Ɗauko mun cup da ruwa ɗan kaɗan."
Darraini ta kawo cup da ruwa Umma ta karɓa ta buɗe zam-zam ta zuba fiye da rabi a cikin cup ɗin sannan ta yi addu'o'i ta tofa aciki ta ɗauki kusan 10 minutes ta na addu'o'i.
Umma ta aje cup ɗin ta shiga ɗaki hannunta ɗauke da raguwar zam-zam ɗin ta buɗe ta sa ka shi a drawer kayanta.
Auta da ke bacci ya fara kuka Umma ta fito parlour da sauri ta kira Shukrah ta ce mata.
"Ɗauko mun cup ɗin nan da sauri."
Shukrah ta fita da sauri ganin yanda ta fito ya sa Manaheer ta bi bayanta lokacin da ta ɗauki cup ɗin Darraini ma haka.
Umma ta karɓi cup ɗin da sauri ta zauna ta kama kan Auta ta ɗaura ajikin ta.
Umma ta zuba wannan ruwan Addu'ar ta shafama Auta a kanshi.
Auta ya yi shiru ya daina kukan amman idon a rufe Manaheer ta fita ta ɗau buta kamar za ta shiga toilet ta tsaya jikin window ɗakin Mama.
Mama ta na dariya ta na magana a waya Mama.
"Ai mai runguntsimi ya faɗa mun komai ƙawata."
Mama ta yi shiru ta na sauraron abin da ake faɗa a cikin wayar kafin ta ce.
"Ina fitowa bakin hanya na aikata yanzu saura na zubawa a cikin abinci ya rage."
Mama
"Ni abin da ke ɓata mun rai yanda ko na yi aiki ba ya kama su."
Mama bayan ta gama sauraron ƙawarta su ka yi sallama ta kalli Mimah da ke kwance ta na danna waya ta ce.
"Ki kwantar da hankalinki tunda Alhaji ba ya ɗaukan mataki a kansu ni zanyi magananin su ɗaya bayan ɗaya."
Mimah.
"Ni fa Mama ban yarda da aikin bokaye ba."
Mama ta fara masifa.
"Ubanwa ya gaya miki gurin boka na je."
Mimah.
"Duk da ba kije dani ba amman wallahi na san gurin boka kika je."
Mama.
"Mimah wallahi idan ba ki rufe mun baki ba sai ranki ya ɓaci."
Mimah ta turo baki Mama ta ce.
"Ko da na ajeki a gidan talatu gurin mallami na je ya yi mun Addu'a sannan ya bani maganin tsari."
Mimah ta kalli Mama a ɗage ta ce.
"Uhmmmm shine harda na zubawa a cikin abinci."
Mama ganin Mimah za ta ɓallo mata ruwa sai ta yi banza da ita.
Bayan fitan Mama gidan ƙawarta talatu ta je suka tafi gurin wanzami ya duba hannun ya bata magani.
Bayan sun dawo Mama ta cewa Mimah.
"Na yi mantuwa bari in je in dawo daga nan Mama ta nufi gurin boka ta zayyana mishi abin da ke faruwa.
Boka mai runguntsimi ya yi dariya ya ce.
"Na faɗa miki da wahala asiri ya kama su amman kinƙi yarda."
Mama.
"Ni yanzu babbar matsalata wannan shegiyar yarinyar da ta hanani sakewa ni da ƴata kuma ko aikin da ka bani ita ce ta gani bayan ka ce mun kar in yarda kowa ya gani."
Mai runguntsimi.
"Aiki ɗaya zanyi miki shima ba akan kowa sai ɗan ƙaramin yaron nan."
Mama ta washe baki ta ce.
"Na baka huƙa da nama."
Daga nan ya bata wani laya ta binne inda ba mutane sannan ya bata ƙullin magana guda biyu ɗaya ta zuba musu acikin abinci ɗaya kuma ta shafa a hannunta ta taɓa kan Auta dashi.
Mai runguntsimi ya jaddada mata in dai ta kuskure guda ɗaya to sauran ma ba zaiyi ba.
Daga nan ta dawo gidan talatu su ka zauna zaman fira.
Manaheer bayan ta gama sauraron Mama ta yi sauri ta shiga toilet jin kamar za a fito daga ɗakin.
Umma ta buɗe bakin Auta Shukrah ta zuba mishi ruwan Addu'ar nan duk da cewa ruwan baya shiga sosai amman haka suka ɗura mishi sai da suka bashi rabi sannan su ka aje cup ɗin.
Manaheer ta shigo da sallama ta zauna kusa da Auta cike da tausayawa.
Yaro ne ya yi sallama su ka amsa ya ce.
"Wai Manaheer ta zo inji wani a zaure."
Umma sai da gabanta ya faɗi amman haka ta ɗaure ta ce ma yaron.
" Ga ta nan zuwa."
Yaron ya fita da gudu tun kafin Umma ta yi magana Manaheer ta ɗau hijjab ta yi waje Umma ta na shirin magana ta ji Auta ya na tari.
Umma ta ɗago shi Auta ya buɗe ido Shukrah ta ɗauko raguwan Addu'ar nan ta mikawa Auta.
Auta ya yi bismillah ya sha Umma ta karɓi cup ɗin.
Darraini ta kalli Auta da ke ta faman haɗa zufa ta ce.
"A zubo maka abincin.?"
Auta ya ce.
"A'a na ƙoshi."
Shukrah ta shiga bedroom Auta ya kwantar da kanshi a jikin Umma Shukrah ta fito hannunta ɗauke da cup ta haɗa tea.
Umma ta karɓa ta na bawa Auta bayan Auta ya gama shan tea ya kalli Umma ya ce.
"Umma kaina kamar a na mun hayaniya a ciki."
Umma ta kama kan ta yi addu'o'i daga nan Auta ya tashi Shukrah ta taimaka mishi ya yi alwala ya yi sallah itama Shukrah alwala ta yi ta ɗau Qur'an Darraini ma haka.
Manaheer da sallama ta shiga zauren ta na ƙare mishi kallo babu laifi yana da nashi kyan dai dai gwargwado sai da ta gama kallon shi tsaff sannan ta gaishe shi ya amsa ya na washe baki.
Manaheer ta ɗaure fuska matashi mai suna Auwal ya na ta surutu amman ta ƙi kulashi sai can da ta gaji da tsayuwa ta ce.
"Sai anjima."
Ba ta jira cewar shi ba ta shige gida Umma ta kalle ta ba ta ce komai ba Manaheer ta shige bedroom ta ɗauko jakan Umma wanda take aje magungunar gargajiya Manaheer ta kwashi guda biyu ta fita.
Umma na zaune Manaheer ta zo ta wuce ɗakin Mama ta nufa daman lokacin da ta ke zaure ta ga wucewar Mimah.
Manaheer ta shiga ɗakin a hankali Mama an saki baki da hanci a na bacci ta lalaɓa ta ɗau jakar Umma ta fita.
Manaheer toilet ta shiga ta kwaso kayan da ke cikin jakar ta ga magani ƙulli biyu a baƙin leda ta kwaso ta sanja da wanda ta kwaso a ɗakin Umma.
Ta lalaɓa ta mayar da jakan ta aje ta fita buta ta ɗauka ta shiga toilet ta zazzage maganin ta kora da ruwa.
Sai da ta tabbatar da maganin ya bi ruwa sannan ta fita ledojin kuma ta zuba a toilet.
Manaheer ɗaki ta shiga ta ɗau wayar Umma ta yi wa Abba plsh da ga nan ta zauna kusa da Umma.
Kiran sallahr magrib ya ta da su a gurin bayan sun idar su ka yi azkar Umma ba ta wasa da ibada haka ma yaranta.
Umma har Auta sai da ta koya mishi azkar saboda halin rayuwa.
Bayan sun yi sallahr isha'i Umma ta ƙara musu karatu daga nan su ka ci abinci banda Umma da ke ta lazumi bayan ta idar ta kalli Manaheer ta ce.
"Zu bo mun abincin amman ba mai sugar ba."
Manaheer ta yi dariya ta ce.
"An gama firs lady a gidan Abbanmu."
Umma sai da ta yi dariya Darraini ma haka Shukrah ta harareta Manaheer ta yi mata gwallo.
Manaheer ta zuba wa Umma ta ɗauko robar yaji ta aje Umma ta na ci ta na yaba musu Manaheer ta sa hannu ta ɗau guda ɗaya ta ce.
"Bari in ɗanɗana in ji ko ta yi daɗi."
Mama ta yi sallama hannunta ɗauke da flsak ɗin abinci
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Ma rasu lafiya na gida kona Hospital ubangiji ka basu lafiya ciwo ba daɗi 😓.
Page 57~58
Umma ta amsa sallamar ta shigo ta na washe baki ta ce.
"Umman Shukrah barka da dare."
Umma.
"Yauwa sannu da aiki."
Umma ta karɓi flask ɗin Mama ta tsaya ta na jan Umma da fira Manaheer ganin haka ta kalli Auta ta ce.
"Dan Allah ɗauko mun cup a kitchen."
Auta ya ɓata rai Shukrah ta ce.
"Ki duba cikin bedroom ki ɗauka."
Manaheer.
"Na fa duba ne banganiba dan Allah Auta ka ɗauko mun."
Auta ya tashi ya zo zai fita Mama ta yi murmushi ta ɗaura hannunta a saman kanshi ta ce.
"Zanga lokacin da za ka girma."
Auta ya fita Umma ta ce.
"Shi Auta ko da ya girma Auta ne."
Mama.
"Daga lokacin da ki kai mishi ƙanwa ya tashi a matsayin Auta."
Umma.
"Uhmmmm."
Daga haka Mama ta fita Shukrah ta yi ajiyar zuciya Umma ta kalleta.
"Lafiya ki ke?."
Shukrah.
"Lafiya ƙalau."
Wayar Umma ta yi ringing daman ta na hannun Manaheer Umma ta karɓa Abba ne ya ke kira.
Umma ta ɗaga su ka gaisa daga nan ta ba yaran bayan sun gama gaisawa su ka miƙawa Umma wayar.
Umma ta karɓa bayan ta gama sauraron shi ya yi musu sai da safe ya kashe wayar.
Darraini ta buɗe plask ɗin da Mama ta kawo shinkafa ne jallop na manja ta mayar ta rufe ta yi alwala ta sa Auta shima ya yi alwala ta shige ta barsu suna fira.
Shukrah sai da ta tabbatar da Umma ta yi bacci ta kalli Manaheer kallo mai cike da tuhuma domin ta san aiken da ta yiwa Auta ba haka kawai ba kuma ta ga lokacin da Mama ta dafa kanshi.
Manaheer.
"Ni kam naga ta kaina."
Darraini da ba ta san abin da ke faruwa ba ta kalleta Manaheer ta fuske kamar ba ita ta yi maganar ba.
Shukrah ta tashi tayi alwala ta shige bedroom Darraini ma haka Manaheer ta tashi ta kulle ƙofa ta shige bedroom ta kwanta.
Ƙarfe ukun dare Umma da Manaheer su ka tashi su kayi alwala su ka hau darduma bayan sun idar da sallah su ka ɗauki Qur'an bayan sun gama karatun Manaheer ta ɗau charbi Umma ta ɗaga hannu sama ta na Addu'a.
"Allahumma Inniy Ad'uka Bi'ismikal Wa'hidul A'azzu wa Ad'uka Allahumma Bi'ismika Assamadu wa Ad'uka Bi'ismikal Azimil watari wa'ad'uka Bi'ismikal Kabiri Al'muta'ali Allazi sabata bihi Arka'ina ka kullaha. An takshifa Anniy ma' Asbahtu wa amsaitu fihi."
Ja'afaru Assadiƙu ya ruwaito daga magabatansa daga Annabi Muhammad (s.a.w) cewa, lokacin da yahudawa suka haɗu a kan kashe Annabi Isa Alaihissalam sai Jibril Alaihissalam ya zo masa ya lulluɓe shi da fukafukinsa sai Annabi Isa ya ga an rubuta a cikin fukafukin Aminul Wahayi.
Sai Annabi Isa (AS) ya faɗi haka sai Allah (SWT) ya yi wahayi izuwa Jibrilu Alaihissalam ce wa,
Ɗauko min bawana zuwa wajena."
Sannan Manzon Allah (S.A.W) ya ce
Ya ƴaƴan Abdulmuɗallib, ku roƙi ubangijinku da wanɗannan kalmomin, na rantse da wanda raina yake hannunsa, bawa ba zai yi addu'a da wanɗannan ba, don kuɓuta a cikinsa face Al'arshi ya girgiza ko kuma ubangiji ya ce da mala'iku ku shaida, haƙika na amsa masa waɗannan kuma na ba shi roƙon sa take a cikin duniyarsa da kuma nan gaba a lahirarsa."
Sannan ya ce da sahabbansa ku roƙa da ita, ba za a yi jinkirin amsawa ba.
Umma ta shafa ta ɗau charbi ba su tashi a gurin ba har sai da su ka yi sallar asuba daga nan su ka ɗaura da azkar.
Su ka ɗauko littafai Umma ta ƙara musu daga nan Umma ta ɗauko raguwan zam-zam ta juye a cup ta yi addu'o'i ta ƙara da ruwa ta ba su kowannen su sai da ya sha daga nan su ka fara aikin gida.
Wannan masar mai haɗi su ka yi breakfast da shi da ruwan lipton Umma ta ba Manaheer key ta gyara ɗakin Abba.
Shukrah ta yi wanka ta shirya Darraini ma haka Auta Umma ta yi mishi wankan bayan ta daga toilet su ka shirya tsaff Shukrah ta kunna turaren wuta.
Umma ta ta ji Manaheer shiru ta ce.
"Auta je ka duba mun kaga lafiya."
Auta ya fita ya shiga ɗakin Abba Manaheer na kwance ta na bacci a saman kujera kamar zai tashe ta ya fasa ya zo gurin Umma ya na dariya ya ce.
"Ta na can ta sa ki baki ta na bacci."
Umma ta yi dariya Shukrah ta ce.
"Yarinya kamar wata kasa."
Umma ta ce.
"Ai ma ta yi ƙoƙari."
Daga haka Umma fita ɗakin Abba ta je ta buɗe drawer kamar yanda ya faɗa mata jiya a waya kuɗi ta ɗauka ta fito parlour ta gyarawa Manaheer kwanciya ta fita.
Umma ta ake su cefane Auta ya bisu daga nan ta koma ɗakin Abba ta kwaso doya ta fito ta yi shimfiɗa ta fara gyara doyan.
Bayan ta gama gyarawa daman da raguwar gawayin jiya ta kunna wuta ta ɗaura ta gyara gurin da ta yi aiki ta koma ɗaki.
Umma ta na shiga wayarta ta yi ringing Abba ne yake kira.
Ta ɗaga su ka gaisa daga nan ya gaya mata a ɗaura girki da wuri bashi kaɗai bane Umma ta yi murmushi daga nan ya tambayeta yara ta ce.
"Na aike su kasuwa cefane."
Abba ya ce.
"Yanzu fisabilillahi yaran ne ki ka tura mun kasuwa?."
Umma ta yi shiru can Abba ya ce.
"Har da Manaheer ki ka tura kasuwar.?"
Umma.
"A'a ta na ɗakin ka ta na bacci."
Abba cike da rashin yarda ya ce tashe ta muyi magana."
Umma ta yi dariya domin ta gane nufin shi ɗakin Abba ta shiga ta tayar da Manaheer ta miƙa mata wayar ta fita.
Manaheer ta yi sallama Abba ya amsa ta gaishe daga nan ya ce.
"Kaiwa Umman ku wayar."
Manaheer ta kaiwa Umma wayar ta dawo ɗakin ta na cikin gyarawa Mama ta shigo Manaheer ta tsaya ta na kallonta.
Mama ta ce.
"Daman abu zan ɗauka munyi magana da Alhaji."
Manaheer ta yi dariya ta ce.
"Alhaji ya ce kar a bar kowa ya shigar mishi ɗaki."
Mama ta ɗaure fuska Manaheer ta ce.
"Ni ma shi ya bada umarnin in zo in gyara mishi ɗaki."
Mama ta tashi za ta shige bedroom ɗin Abba Manaheer ta tare.
"Dan Allah Mama karki jamun matsala a gurin Abba."
Mama.
"Sai fa na shiga ɗakin nan saboda ɗakin mijina ne kuma ko uwarki ba ta isa ta hanani ba."
Manaheer ta yi dariya ta ce.
"Wallahi tunda ki ka ce haka ba za ki shiga ba."
"Idan kuma kin dage to bismillah ga hanya amman wallahi kina shiga zan rufe da key har sai Abba ya dawo."
Mama ta san Manaheer za ta aika ta fita ta na masifa ta na zaginta Manaheer ba ta ce komai ta gama gyaran ta ɗauko air freshener a bedroom ɗin Abba ta sa ta ɗauko turaren wuta daga nan ta rufe ƙofar ta fita.
Ta samu Mama a tsaye a bakin ƙofar ɗakin su ta na ta zage-zage wai Umma ta na sa Manaheer na mata rashin kunya Umma na zaune a saman kujera ta na danna waya.
Manaheer ta zo wucewa ta gefen Mama ta yi magana yanda Umma ba za taji ba ta ce.
"Garin kwashe kwashen Abba ya ɗibo mana dangin yarbawa."
Mama ta fashe da kuka Manaheer ta waske ta shiga kitchen Umma ta kalli Mama cike da mamakin yanda ba ta gajiya da masifa ta ce.
"Dan Allah kiya haƙuri zanyi mata magana in sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba."
"Kuma karki ga laifin Manaheer Abba Shukrah ya ce kar a ba kowa keys ɗin ɗakin shi."
Umma bata san abin da Manaheer ta yi ba Mama ta yi ƙwafa ta ce.
"Wallahi in dai ina raye sai zaman gidan nan ya gagareku."
Manaheer ta yi tari
Mama ta kalli Manaheer ta ce.
"Muzuba ni da ku acikin gidan nan."
Mama ta wuce ɗaki Manaheer ta zauna a bakin kitchen taƙi shiga ɗakin kar Umma ta yi mata faɗa.
Shukrah Darraini Auta su kayi sallama su ka shigo Manaheer ta kalle su ta ce.
"Ashe kun fita ne naji gidan shiru kamar gidan mutuwa."
Auta ya ce.
"Kin gama sakin baki da hanci kina bacci."
Dukkansu sai da suka yi dariya harda Umma da ke fitowa daga ɗaki Manaheer ta ɓata fuska.
"Wallahi Auta karka bari in kama ka."
Umma ba ta bi takan ta ba tunda ta fahimci abokin faɗa take nema cefanen ta karɓa suka fara gyarawa Manaheer ta shiga wanka.
Yaro ne ya yi sallama ya shigo kanshi ɗauke da buhun gawayi Umma ta nuna mishi gurin da zai aje a kitchen Shukrah ta ce.
"Umma buhun gawayi ki ka siya.?"
Umma.
"Abbanku ya siya."
Shukrah.
"Hmmmmm."
Darraini ta sauke doyar ta buɗe ta ɗago ta kalli Umma ta ce.
"Umma doyar nan ta yi mana yawa."
Umma.
"Baƙi Abbanku zai yi."
Umma sun sha aiki doyan nan sakwara su ka yi da rabi rabin kuma suka soya da ƙwai Shukrah ta ɗibi wani ta yi yam balls dashi daga nan Umma ta haɗa lemon cucumber gidan ya na ta ƙamshi.
Mama harda leƙowa ƙamshi ya isheta bayan sun gama aikin wanka suka sake saboda rana ta yi lokacin Umma duk abin da ta dafa sai da ta zubawa Mama ta ce Shukrah ta kai mata.
Shukrah na fita Manaheer ta amsa ta je bakin ƙofar Mama ta ji suna ƙulla wani abun ita da Mimah Manaheer ta sa hannun ta buga ƙofar ta shiga da sallama.
Mama jin irin dukan da a kaiwa ƙofa sai da gabanta ya faɗi amman ta na ganin wanda ya shigo ta kau da kai ta ɗaura fuska.
Manaheer ta ce.
"Na yi sallama baku amsa ba kuma kun san sallama cikon addini."
Mimah ta yi tsaki Manaheer ta a'je zata fita Mimah ta ce.
"An gaya muku muna jiran wannan abincin naku ne."
Manaheer ba ta ce komai ba ta dawo ta ɗau plate ɗin da ta jero kwanika uku Mama ta yi wuff ta amshe plate ɗin saura kaɗan ya zube Manaheer ta yi dariya ta fita.
Mama ta kalli Mimah ta ce.
"Wannan yarinyar da kike ganinta ba hankali take dashi ba tsaff za ta koma da abincin."
Mimah.
"To idan ta koma da abincin sai me."
Mama bata ƙara cewa komai ba ta zauna ta buɗe kwanonin dake rufe ɗaya sakwara ɗaya doya da ƙwai sai yam balls gashi Umma ta zuba musu abincin da yawa.
Mama ko hannu ba ta wanke ba ta fara cin doyar ta na cikin ci Manaheer ta shigo ta a'je mata kwanon miya da kuma drinks ɗin da Umma ta haɗa har za ta fita sai kuma ta dawo ta ce.
"Hajiya Mama a na ta ba ciki hakkinsa."
Daga haka ta yi waje Mimah ta kalli Mama ta ce.
"Wai dan Allah maiyasa Manaheer ta rainaki.?"
Mama da ta cika baki da doya ta ce.
"Bari in gama cin wannan abin daɗin."
Mimah ta yi tsaki ta sauko ƙasa Mama ta kusa cinye doya da ƙwan Mimah ta ɗauke kwanon doyar ta ce.
"Kinci rabonki."
Mama ta janyo jug ɗin drinks ta ce.
"Taimaka ki ɗauko mun cup."
Mimah ta zumɓura baki ta fita ba ta jima da fita ba ta dawo da cups biyu ta a'je Mama ta zuba drink ta fara sha.
Mimah raguwar doyan ta ci ta ƙara da yam balls ta sha drink ta na sha ta na santi kaɗan suka bar yam balls ɗin drink ɗin tass suka shanye suna santi Mimah ta ce.
"Gaskiya Mama ki je ki koyi girki irin wannan."
Mama.
"Ni tunda na ke ban taɓa ganin mara kishin uwarta ba sai ke."
Mimah.
"Daga faɗin gaskiya."
Mama.
"Dan ubanki ni za ki gayawa gaskiya.?"
"Mama yaushe ki ka yi wannan girman da za ki dunga faɗa mun maganganu san ranki.?"
Mimah ta hawe gado ta na danna wayarta ko Abba bai san tana da waya ba.
Ku lura da wani abu guda ɗaya idan babba ya ja girman shi babu ta yanda ƙarami zai rainashi.
Babba ya ja girman shi karya dunga shigewa ƙarami saboda gudun raini.
Kamar dai Manaheer da Mama.
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Allah ka biya mana dukkanin buƙatun mu ya hayyu ya qayyum 🙏
Page 59~60
Manaheer ta shiga ɗaki bayan ta yi sallama suna zaune suna cin abinci sakwara da miya.
Manaheer kitchen ta shiga ta ɗibo doya da ƙwai ta haɗo da yam balls ta fito.
Ta zauna ta yi bismillah ta fara ci babu wanda ya kulata Auta ya zuba drink ya miƙa mata Manaheer ta karɓa ta na hararan shi.
Sun rigata gamawa Auta ya wanke hannu ya zauna kusa da ita ya ce.
"Aunty mai hanjin ziri a na ta zirarawa."
Manaheer ta yi banza dashi sai da ta gama cin abinci sannan ta miƙa mishi plate ɗin ta ce.
"Ɗan ƙaro mun yam balls ɗin."
Shukrah.
"Ki zuba su a ina.?"
Manaheer ta yi dariya ta ce.
"Ni fa yanda kuka san na watsar haka na ji."
Darraini.
"Hhhhhhhhhh daman akwai lafiyar ci."
Manaheer.
"Shiyasa na fiku kuzari da ƙiba."
Daga nan musu ya kaure tsakanin Darraini da Manaheer.
Khadija ta shigo da gudu ta rungume Manaheer.
Umma ta yi dariya ta ce.
"Lallai yau gidan nan akwai matsala ciwon kai biyu sun haɗu guri ɗaya."
Shukrah ta yi dariya Khadija ta saki Manaheer ta rungumesu ɗaya bayan ɗaya sannan ta rungume Umma.
Auta ya ce.
"Aunty Khadija kiji tsoran Allah."
Khadija ta saki Umma ta rungume shi ta ce.
"Banganka bane Autar Umma."
Daga nan ta gaishe da Umma ta ce.
"Abba ya ce a kai mishi key."
Da sauri Umma ta yi waje ta na cewa.
"Allah ya shirya ki."
Bayan fitan Umma ta gaishe da Shukrah Darraini Auta ya gaisheta daga nan aka dasa sabon fira.
Shukrah ta duba time ta ga har biyu da rabi ta tashi ta yi waje Darraini ta kalle su ta ce.
"Lokacin sallah."
Daga haka itama ta yi waje su kai alwala su kai sallah Umma ta shigo itama ta yi sallar daga nan ta kalli Shukrah ta ce.
"Ku kaiwa Abbanku abinci."
Shukrah Darraini Auta su ka ɗauki abincin suka yi waje Manaheer ta zubo sakwara da miya su ka zauna su na ci da Khadijah.
Su na ci Khadija na santi bayan sun gama Manaheer ta zubo yam balls ta miƙawa Khadija.
Khadija.
"Baki ƙaro mun da drink ɗin ba."
Manaheer ta yi dariya ta fita Shukrah ta dawo ta ɗau plate da spoons ta fita Darraini ta ɗau jug mai ɗauke da drink tabi bayan ta Manaheer ta shigo ɗauke da ƙaramin jug ta a'je a gaban Khadija.
Auta ya shigo ya kalli Khadija ya ce.
"Uncle ya ce ki je ki kwaso kayanki a mota."
Manaheer.
"Daman tare kuke?."
Khadija.
"Eh mana."
Bayan ta gama ci Manaheer ta sa hijjab suka fita da Khadijah fitan su bada jimawa suka shigo Manaheer janye da akwati Khadija kuma manyan ledoji guda biyu.
Sai da a kai la'asar uncle Nasser ya kira Umma ɗakin Abba.
Daga nan ya faɗa mata abin da Abba ya ce Umma ta yi murmushi ta kalli Abba ta ce.
"In sha Allah za a gyara."
Daga haka ta yi shiru uncle ya kira Auta dake zaune a tsakar gida.
Auta ya shigo ya raɓe jikin Umma uncle Nasser ya ce.
"Ba za kazo mu gaisa ba."
Auta ya duƙa ya gaisheshi uncle Nasser ya kama hannun shi ya zaunar dashi kusa dashi.
Uncle Nasser.
"Mudan maiyasa kake gudun Abbanku.?"
Auta ya duƙar da kai Abba ya ce.
"Ai babu wani dalili kawai iskanci ne."
Uncle Nasser ya yi murmushi ya ce.
"Ku bamu guri zamu yi sirri."
Abba ya fita ya shiga ɗakin Mama Umma ta nufi ɗaki.
Bayan fitansu uncle Nasser ya dinga lalaɓa Auta har sai da ya ɓude baki ya ce.
"Abba ne ya daki Aunty Manaheer ta faɗi shine Umma ta kai ta hospital."
Uncle Nasser ya yi shiru ya na tunani wato dai ciwon da Manaheer ta yi Abba ne sila dalilin hakan sauran yaran suke jin tsoron shi."
Uncle Nasser ya ɗauko leda a gefen shi ya miƙawa Auta ya ce.
"Ga tsaraban ka nan."
Auta ya ɗuka ya karɓa ya yi godiya Abba ya shigo da sallama Auta ya tashi ya fita uncle Nasser ya kalli Abba dake kallon Auta.
Abba ya zauna suka cigaba da tattaunawa duk da hakan Abba yaƙi janye ƙudirin shi na aurar da Manaheer saboda ya riga da ya yi wa yaron magana kuma yana jin kunyar cewa ya fasa.
Bayan sun gama suka fito uncle Nasser ya ƙara bawa Umma haƙuri daga nan yasa almajirai suka kwaso kayan abincin da yazo dashi,
Abba ya yi mamaki domin bai san da kayan ba uncle Nasser ya yi sallama ya tafi Abba ma kasuwa ya wuce,
Da daddare bayan sun gama cin abinci Khadija ta ɗauko ledojin da ta zo dasu ta miƙawa Umma daga nan ta ɗauko akwatin kayanta,
Leda ta ciro ta mayar ta a'je ta miƙawa Umma ledar ta ce.
"Kayan su Aunty Shukrah ne a ciki."
Umma ta buɗe ledar kayan sawa ne kala bibbiyu duka sababbi da ankon suna da wanda Aunty Maryam ta ɗinka musu dukkansu ɗaya shadda ɗaya lesi.
Umma ta buɗe nata ledar itama harda ankon a ciki lesi ne da kamfala kowanne da mayafi sauran tarkacen kuma namar suna ne da snacks masu yawa a ciki.
Umma ta yi murna sosai Khadija ta ɗauko wani ledar a cikin akwati ta miƙawa Umma ta ce.
" Kayan Mimah da na Auta a ciki."
Umma ta amsa ta buɗe ta ciro na Auta shadda ne yasha aiki harda babban riga ta a'je a gefe ta ce Shukrah juye namar ki ɗibarwa Abbanku da Mama.
Shukrah ta amsa Auta ya ɗauko plate da ƙaramin flas ta zubawa Mama a plate Abba a flas Umma ta ce.
"Khadija ɗauka ki kai wa Maman ku."
Khadija ta ɗauko ta kalli Manaheer ta ce.
"Dan Allah zo muje ki raka ni."
Manaheer ta bita suka fita Umma ta yi hakan ne saboda Khadija ba taje sun gaisa da Mama ba.
Daga nan ta raba taba kowa bayan sallahr isha'i suka yi shimfiɗa a tsakar gida harda Abba a na zaune a na fira Mimah ta fito da hijjab ta yi hanyar zaure Abba ya ce.
"Ina za ki je?"
Mimah duk ta bi ta ruɗe kafin ta samo amsar bayarwa Mama ta yi saurin fitowa daga ɗaki ta ce.
"Magani za ta karɓo mun a chemist."
Abba.
"Tun ɗazun ba ki san da hakan ba sai yanzu.?"
Mama.
"Yanzu na ji ciwon ya taso mun sosai dan Allah ka barta ta je."
Abin da ba su sani ba tun fara maganar su Mimah ta fice daga gidan.
Mama da ƙyar ta shawo kan Abba ya yarda amman da sharaɗin karta daɗe Mama waigowar da za ta yi ba Mimah ba alamarta Abba ya kaɗa kai Mama ta shige ɗaki jiki a sanyaye.
Zuwa 10 kowa ya watse Umma a ɗakin Abba ta kwana Manaheer da Khadijah su kaɗai su ka ji dawowar Mimah domin sun daɗe su na fira.
Lokacin da Abba ya tambayi Mama cewar "Mimah ta dawo.?"
Cewa ta yi ai ta daɗe da dawowa kuma ya san ba ta dawo ba kawai ya tambaye ne ya ga iya gudun ruwanta.
Ya kulle ƙofar gida ya shige ɗaki itama ta shige ɗaki 12:30am Mimah ta dawo kuma ta tabbatar lokacin sun kulle gida sai ta kira Mama a waya lokacin da Mama ke buɗe kofa Manaheer ta ji motsin taɓa ƙofar gidan.
Manaheer sai da ta bari sun shigo tsakar gida ta fita da ƙaton tocligh ta haske tsakar gidan ta na cewa.
"Subhanallahi waye ya shigo da tsakar daren nan."
Mama da takaici ya isheta ta ce.
"Uwarki ce shegiya munafuka."
Manaheer.
"Ashe ƴar lelane ta dawo makaranta."
Cewar Manaheer ta na dariya ganin Mama ta nufo ta yasa ta shige ɗaki da gudu ta kulle.
Khadija na kallon abin da ke faruwa ta na dariya da ga haka su ka kwanta bacci.
Mama ta yi ƙwafa ta ce.
"Zamu haɗe da ke wallahi za ki gane ba ki da wayyau."
Asuba ta gari.
Bari mu leƙa gidan Inna muga irin wainar da suke soyawa ita da ƴarta.
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Ina taya ɗaukacin al'ummar Annabi Muhammad murnar shiga watan maulud ubangiji ya bamu albarkar dake cikin wannan watar🙏
Page 61~62
Tun bayan rasuwar Baffa Inna ta matsa sai da aka raba gado ta amshe nata da na ƴaƴanta duk da hakan Abba ya dau nauyin gidan lokacin da ya samu karayan arziki nauyin gidan ya koma kan uncle Nasser komai shi yake yi daga baya Umar ya shigo ciki tare suke yin kowani irin hidima ya taso a gidan.
Ban da Isma'eel domin ko sun tambaye shi abu cewa yake yanzu kasuwar babu ciniki Isma'eel haushin Amina ya ke ji shi ya sa ba ya yiwa Inna komai.
Har wannan lokacin Inna ba ta ƙaunar ƴaƴan Mama duk da ubangiji ya nu na mata gaskiya.
Amman ita gani take asiri aka yi wa Isma'eel shiyasa ba ya tausaya musu Amina sai aukin tara zawarawa amman har yanzu ba ta samu wanda ya yi mata ba a cewar ta mijin da yafi na Fatima kuɗi za ta aura.
Ackin wannan ya na yin Inna ta ce wa Amina.
"Zama guri ɗaya lalura ne gwara ki ɗan dinga ziyarar ƴan uwanki ko Allah zai sa ki sa mu miji"
Duk da cewar Amina ba ta zama a gida gaba ɗaya yau ta na gidan suna gobe ta na gidan biki.
Inna ta ce.
"kishirya ki je gidan Aliyu ko kwana biyu kiyi"
Amina ta ɓata rai ta ce.
"Haba Inna ta ya ya zanje gidan ya Aliyu bayan yanzu babu wannan kuɗin da ya ke gadara da shi ni dai gaskiya ba zanje ba"
Inna ta ce.
"To kar ki je ki zo mu zauna a gidan tun da na ga zaman gidan bai isheki ba"
Amina.
"Gaskiya ba na son zuwa gidan ya Aliyu ko dan wancan mara kunyar yarinyar"
Inna.
"Ai idan kinje gyara mata zama za kiyi domin ina da labarinta a gurin Aisha"
Amina.
"Ina laifin ki ce inje gidan Fatima ko gidan ya Nasser"
Ina ta tashi ta shige ɗaki Amina ta bi bayan ta daga nan su ka shirya yanda za a yi.
Amina ta je gurin bokan da yake musu aiki ya ba ta maganin farin jini ta na dawowa ta zuba ɗaya a turare ɗayan kuma ta kwaɓa lalli da shi.
Da daddare ta siyo sticker ta manna asuba ta gari.
Gidan Abba.
Da safe tun kafin yaran su tashi Umma ta gama breakfast a cewarta sun sha aiki da yawa.
Bayan sun yi breakfast su ka gyara gidan Umma ta na zaune a ɗakin Abba su na fira Abba ya ce.
"Anjima masu gyara zasu zo"
Umma.
"Allah ya kawo su lafiya"
Daga nan Abba ya tafi kasuwa Umma ta koma cikin yaran ta suna ta fira.
Lokacin ɗaura girki suka haɗu dukansu harda Khadija su kayi dambun kuskus ya sha kayan lambu bayan sun gama su ka ƙara shiryawa su ka yi sallah sannan suka zauna cin abinci Khadija tana ta santi.
Suka gama cin abinci Manaheer ta gyara gurin sallama su ka ji a ƙofar gida Umma ta ce.
"Auta jeka dubo ko masu gyara ne"
Auta ya fita bai jima ba ya dawo ya ce.
"Wai masu gyara ne zasu duba guri"
Umma ta ce.
"Jeka shigo da su"
Suka shigo suka gama ganin gidan sannan babban cikin su ya kalli Auta ya ce.
"Kira mun Mamanka"
Umma ta fito bayan sun gaisa mai gyara ya ce.
"Zamu ɗan duba cikin ɗakunan ku idan ba damuwa"
Umma cike da mamaki take kallon mai gyaran domin Abba bai gaya mata cewar harda ɗakunan su za a gyara ba.
Umma ta koma ɗaki ta gayawa yaran su shirya masu gyara za su shigo duba guri.
Yaran duka suka fita tsakar gida Auta ya musu jagora har cikin bedroom bayan sun gama gani ta buɗe musu ɗakin Abba nan ma suka gani suka fito suka tafi ba tare da sun duba ɗakin Mama ba.
Cike da mamaki Shukrah ke tambayar abin da ke faruwa Umma ta faɗa musu yanda su ka yi da Abbansu kafin ya fita.
Mama ta fito daga ɗaki tana ƴan waƙe -waƙen da ta saba Umma ta shige ɗaki yaranta suka take mata baya.
Bayan sallahr isha'i Abba ya na zaune a tsakar gida shi da iyalanshi gaba ɗaya suka haɗu su kaci abincin dare harda Mama da ƴarta.
Bayan sun gama cin abinci yaran suka gyara gurin suka zauna aka cigaba da fira Abba ya kalli Umma ya ce.
"Nayi suriki fa."
Umma ta ce.
"Wani surikin ka ƙara yi?"
Abba.
"Ɗazun bayan na je kasuwa wani matashi mai suna Salisu ya same ni kan cewa ya ga ɗaya daga cikin yarana yana so."
Mama.
"Uhmmmm"
Abba.
"Shine yazo neman izinin magana da ita idan ban yi mata miji ba"
Abba.
"Kuma na bashi dama gobe idan Allah ya kai mu zai zo su ga juna"
Umma.
"Allah ya sanya alkhairi."
Mama.
"Baka faɗa mana wanda yake so ba"
Abba ya yi dariya ya ce.
"Idan ya zo gobe idan Allah ya kai mu za kuga wanda yake so."
Daga haka firan ya watse Mama ta kama hannun ƴarta suka shige ɗaki.
Bayan shigar su ɗakin Mama ta ce.
"Na san ma kece ya gani ya na so ba wata ba saboda duk cikin su kin fisu iya kwalliya da iya magana"
Mama taci gaba da cewa.
"Kuma kina kwalliya ki yafa gyale su kuma kullum yawo da hijjab kamar matan limamai"
Mimah ta yi dariya Mama ta ce.
"Idan baka sa gyale ba ta ya ya mazan za su ganka har suce su na sonka"
Daga nan suka fara shirye-shiryen taron baƙo.
Umma bayan sun koma ɗaki ta yi musu sai da safe ta tafi ɗakin Abba Manaheer ta kalli Shukrah ta kwashe da dariya Shukrah ta ce.
"Kefa wani lokacin baki da isashen lafiya."
Darraini ta yi dariya ta ce.
"Allah ya shirya ki Manaheer"
Khadija ma ta hau dariya Shukrah ranta ya ɓaci ta ya ya zasu sata a gaba da dariya kamar ta zama mahaukaciyya.
Shukrah ta ce.
"Wai dan Allah me ya sa kuke mun dariya?"
Manaheer.
"Saboda kece wanda Abba yaƙi faɗa mana ko wacece"
Shukrah.
"Uhmmmm ni kuma na san ba ni ba ce"
Su ka dage akan cewa itace amman Shukrah taƙi yarda data ga suna son sa mata ciwon kai ta shige bedroom ta rabu da su.
Ganin ta basu guri suma suka bita bayan kowacen su ta yi alwala har Khadija.
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Happy maulud masoya manzon Allah s a w ubangiji ya bamu albarkar dake cikin wannan watan 🙏
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu 🥰
(Ta Batulu)
Page 63~64
Da safe bayan sun gama aikin gida suka zauna su na hutawa suna fira jefi-jefi Umma ta na ɗakin Abba Mama ta ɗaga labulen ɗakin ta ce.
"Mallamai kun ishe mu da hayaniya kamar gidan biki"
Manaheer ta yi saurin cewa.
"Allah ya taimaki hajiya Maman mu"
Darraini da ta kasa riƙe dariyar ta da sauri ta shige bedroom Shukrah ko kallo ba ta isheta ba.
Mama.
"Amina ki kayi wa dariya bani ba fitsararrun yara marasu kunya"
Daga haka ta yi gaba daman neman dalili ya kawota.
Mama ɗakin Abba ta shiga yana zaune suna fira da Umma.
Mama ta nemi gurin zama ta ce.
"Daman gurinka na zo Alhaji"
Abba ya zuba mata ido ya na jiran ta faɗa mishi ƙaran wanda ta kawo.
Mama.
"Gaskiya idan an yi girki a gidan nan ba a zuba mana yanda zai ishe mu domin ni rabon da in ci abinci in ƙoshi acikin gidan nan koni na manta abinci ne yanda kasan za a ba wa mage"
Abba ya kalli Umma
Mama ta yi saurin cewa.
"Ni dai a raba girki kowa ya dinga yin nashi kawai yafi alkhairi"
Abba.
"Gaskiyar magana babu wace ta isa ta sa ni in raba girkin gidana'
Abba ya kalli Mama ya ce.
"Ni ba na son tashin hankali tun da kin ce ƙara kika kawo ba sai ki zuba ido ki gani ba"
Mama.
"Alhaji ba abinci ake zuba ma na acikin gidan nan ba face ƙanzon ƙasan tukunya wanda ya kama ya yi baƙi"
Abba bai tanka mata ba harta gama faɗar maganarta bayan ta fita Abba ya mai da hankalin shi gurin Umma ya ce.
"Shin dagaske ne abin da ta faɗa."
Umma.
"Idan da gaske ne mai ya sa duk tsawon lokacin nan bata taɓa kawo maka ƙara ba sai yanzu?"
Abba.
"Ni dai kawai tambayarki na yi dagaske ne abin da ta faɗa."
Umma ranta ya ɓaci ganin ya yarda da abin da ta faɗa ba tare da bincike ba amman ta shanye ɓacin ranta ko ba komai a samanta yake.
Abba.
"Gaskiyar magana ba zan lamunci haka acikin gidana ba"
Umma.
"Tun da kayarda da abin da ta faɗa to kafin ka yanke hukunci dan Allah ka yi bincike"
Abba.
"Wani irin bincike zan yi bayan a gabanki ta faɗa ballan ta na kice sharri ta yi miki"
Umma.
"In sha Allah daga yau na cire hannuna a girkin gidan nan"
Daga haka ta fita Mama na tsaye a bakin ƙofa Umma ko kallonta ba ta yi ba ta nufi ɗakin ta daman girkin Mama ne.
Mama ta yi wuf ta faɗa ɗakin ta samu Abba ya na shirin fita kasuwa bayan ya gama shiryawa ya bata kuɗin cefane ya fita Mama ta daɗe a ɗakin kafin ta rufo ƙofar ta fita.
Mama ɗakin Umma ta nufa ta na kar kaɗa makulli Umma na zaune suna fira fuskanta cike da farin ciki Mama ta ji ranta ya ɓaci ita da ta so ta zo ta same ta cikin ɓacin rai shine zata ganta cikin farin ciki.
Umma ta yi murmushi ta na kallon Mama Manaheer.
"Hajjiya Mama ikon Allah."
Mama ta watsa mata harara ta ce.
"Ku zo ku yi mun cefane dukan ku."
Manaheer ta yi dariya ta ce.
"To hajjiya Mama idan ma harda girkin kike so duk za muyi."
Umma ta kama hannun Auta suka shige bedroom Mama ta bi ta da harara Manaheer ta kalli Mama.
Khadija ta ce.
"Mama kawo kuɗin."
Mama.
"Ku barshi kawai bana so zan aiki Mimah."
Manaheer ta ɗau buta ta yi waje Shukrah ta kaɗa kai ta shige bedroom parlour ya rage daga Darraini sai Khadija Mama ta yi waje ta na cika ta na batsewa.
Manaheer daman ba toilet zata shiga ba ta na ganin Mama ta nufo hanyar ɗakinta ta gyara tsayuwa sai da ta zo dab da ita sannan ta ce.
"Hajjiya Mama ikon Allah mata a gurin Alhaji."
Tana gama faɗar hakan ta shige toilet ta kulle ƙofa Mama ranta ya ɓaci ta rasa inda zata sa kanta saboda ɓacin rai ganin tsayuwar ba zai fisheta ba ta shige ɗaki ta ɗau wayarta.
Ta kira Abba ringing ɗaya ta ji ya ɗaga wayar tun kafin ya yi magana ta riga shi.
"Alhaji ban samu yaron da zai mun cefane ba."
Abba.
"Mimah fa.?"
Mama.
"Ta je gidan lalli."
Abba.
"To ba ga yara a gidan nan ba ki aike su mana."
Mama.
"Na yiwa Manaheer magana ta ce ba za ta je ba kuma ni bansan wanda zan aika ba daman na ga Manaheer itace ƙarama acikin su"
Abba.
"Ki aiki Darraini ta siyo miki."
Daga haka ya yanke wayarshi.
Abba ya kira Umma bayan ta ɗaga wayar sai da jikin shi ya yi sanyi domina ba haka ta saba amsa wayarshi ba amman sai ya share ya ce.
"Darraini ta je ta yi cefane."
Umma na jin haka ta kira Darraini ta miƙa mata wayar Darraini ta karɓa ta fita lokacin Manaheer ta shigo Darraini ta buɗe maganar gaba ɗaya yanda za su ji abin da zai ce.
Abba ya ce.
"Darraini ki je ki karɓi kuɗin cefane gurin Maman ku ki siyo mata."
Daga haka ya yanke wayar ya kira Mama ya ce.
"Ki kaiwa Darraini ta siyo miki."
Abba ya yanke wayarshi Mama ta fita ta na ran gaji da jiki ta shiga ɗakin Umma ta tsaya a bakin ƙofa ta ce.
"Manaheer in ji Alhaji ya ce ki zo ki yi cefane."
Wannan karan ba iya Manaheer ta yi dariya ba harda Umma dake kwance a ciki sai da abin ya bata dariya Shukrah dake zaune kusa da Umma murmushi ta yi.
Mama.
"Ya ina magana kuna mun dariya kamar kunga mahaukaciyya.?"
Manaheer.
"Hajjiya Maman mu ikon Allah yanzun nan Alhaji ya kira ya ce Anty Darraini ta je ta karɓi kuɗin cefane ta siyo miki."
Mama sai da ta ji kunya amman ta fuske ta yi gaba ta na cewa.
"Ina jiranki."
Mama ta na shiga ɗaki Amina ta yi sallama hannunta janye da ƙaramin akwati ɗakin Mama ta nufa.
Darraini ta sa hijjab Khadija ma haka a bakin ƙofar ɗakin Mama suka tsaya Khadija ta yi sallama.
Mama ta fito ta lissafa musu abin da za su siyo mata ta koma ɗaki gurin Amina.
Bayan sun gaisa Mama ta ce.
"Ya na ganki da akwati kamar wata mai hijira."
Amina.
"Kwana biyu zan yi."
Mama ranta ya ɓaci amman bata nu na ba daga nan Amina ta yi kwanciyarta Darraini basu jima da fita ba suka dawo.
Har sun tsaya a bakin ƙofa Khadija ta shige ɗakin bayan ta yi sallama Amina kwance a saman two seater tana bacci.
Darraini ma ta shigo ɗakin idonta akan Amina dake bacci kujeran da take kwance akai ƙofa yake kallo Mama ta fito daga bedroom ta na hararan su.
Khadija ta miƙa mata kayan cefanen ta fita Darraini ma haka.
Bayan sun shiga ɗaki Manaheer na zaune a kujera tana game Khadija ta ce.
"Kunyi baƙuwa fa a gidan."
Manaheer ta mayar da hankalinta gurin Khadija ta na cewa.
"To ina ruwan mu da ita.?"
Khadija.
"Anty Amina daga saminaka."
Ba Manaheer kaɗai ba hatta Shukrah sai da ta ji faɗuwar gaba Umma rintse ido ta yi ta na jin faɗuwar gaba.
Umma ta san halin Amina sosai macece mara son zaman lafiya Manaheer ta ce.
"Lallai gidan nan zai kama da wuta."
Darraini jiki a sanyaye ta nemi gurin zama Umma ganin yanda jikin su ya yi sanyi ta ce.
"Shukrah muna da raguwar kayan cefane."
Shukrah ta duba ta kalli Umma ta ce.
"Eh."
Umma.
"Ki dafa mana abin da ya dace."
Khadija ta shigo bedroom ɗin ta ce.
"Dan Allah Aunty Shukrah dambun tsaki."
Umma.
"Kin iya ci.?"
Khadija.
"Eh mana ina son dambun tsaki."
Shukrah.
"Ai ko za ki sha aiki domin babu mai ta yaki.
"
Manaheer da shigowarta kenan ta ce.
"Zan ta ya ta."
Shukrah.
"yanzu dai ku ta shi lokaci na ƙurewa."
Umma.
"Ki duba ki gani idan akwai tsakin masaran."
Shukrah.
"Eh akwai."
Daga haka suka fita Umma ta bayar da kuɗi a siyo alayyahu da kabej cucumber da gyaɗa.
Ba a dauki dogon lokaci ba suka gama girkin Shukrah ta shiga wanka Darraini ta gyara gurin Manaheer ta yi wanke-wanke bayan Shukrah ta fito Khadija ta shiga.
Khadija ta fito Darraini ta shiga Manaheer na kwance a two seater bayan Darraini ta fito Umma ta shiga daga nan su ka yi alwala su kai sallah.
Manaheer ta zubo abinci a babban plate Umma ta kalleta ta ce.
"Manaheer ba ki yi wanka ba."
Manaheer.
"Yunwa na ke ji sai mun gama cin abinci."
Daga haka suka fara cin abincin bayan sun gama Manaheer ta ƙaro Auta ya na ta tsokanarta.
Manaheer ta gama cin abinci ta ɗau ruwan wanka ta kai toilet ta fito ɗaki ta shiga Umma ta ce.
"Ya za ki dawo ɗaki bayan kin kai ruwan wanka toilet.?"
Manaheer.
"Mantuwa na yi."
Ta shige bedroom bata jima ba ta fito ta yi hanyar toilet bucket ɗin data kai ruwa toilet ta ganshi a bakin ƙofar toilet an fito mata dashi da kwandon wankan.
Cike da mamaki ta ƙarika ta duba da kyau ta ga bucket ɗin ta ne kuma babu kowa a toilet ɗin.
Manaheer ba ta ce komai ba ta mayar da bucket ɗin da kwandon wankan ta kulle ƙofar bata jima da kullewa ba ta ji a na dukan ƙofar toilet ɗin kamar za a cire.
Manaheer ta leƙo da kai daman bata fara wankan ba Amina ta gani a bakin ƙofar toilet ɗin da sauri Manaheer ta kulle ƙofar.
Amina.
"Wallahi idan baki fito ba sai na shigo na jawo ki waje."
Manaheer ko sauraronta ba ta yi ba ta gama abin da take ta buɗe ƙofar ta fito.
Tun kafin Amina ta yi magana Manaheer ta ce.
"Lah Aunty Amina yaushe kika zo?"
Amina ta ɗaure fuska ta ce.
"Dan iskanci kin shige toilet kin yi zamanki."
Manaheer.
"Dan Allah kiya haƙuri big Aunty."
Amina ta shige toilet Manaheer ta wuce ɗaki shigarta ɗaki bada jimawa ba Amina ta yi sallama ta shigo hannunta ɗauke da flas ɗin abinci Umma na zaune a two seater.
Darraini na zaune kusa da Umma Manaheer Khadija Auta suna zaune suna game a wayar Umma.
Darraini ta miƙe ta shige bedroom Amina ta zauna kusa da Umma suka gaisa ta yi mata ya gajiyan hanya daga nan ta aje flas ɗin hannunta.
Shukrah ta fito suka gaisa Amina ta ce.
"A na nan zaune a gida ba aure."
Manaheer.
"Big Aunty aure lokaci ne."
Amina.
"Ke kuma waya ambaci sunanki.?"
Manaheer.
"Ni naji kamar kin ce Manaheer a na nan zaune a gida ba aure."
Amina ba ta ce komai ta yi waje Umma ta ce.
"Manaheer dan Allah ki rufa mun asiri ki fita daga sabgar Amina."
Manaheer.
"Umma ita har ta na da bakin yiwa mutum gorin aure shekarunta nawa ba auren."
Umma.
"Ni dai ki fita sabgarsu dan Allah."
Manaheer.
"In sha Allah."
Shukrah ta shige bedroom ko kallon abincin ba su yi ba har zuwa bayan isha'i lokacin Abba ya dawo.
Kamar kullum an shimfiɗa tabarma su na zaune bayan sun gama cin abinci Mimah an sha kwalliya da lalli Abba ya kalli Amina ya ce.
"Amman ba gobe za ki koma ba .?"
Amina.
"Zan ɗan kwana biyu."
Mimah ta shige ɗaki ta fesa turare ta dawo ta zauna Manaheer ta yi murmushi yaro ne ya yi sallama ya ce.
"Wai a na sallama da.........?
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Allahumma Sali Ala Sayyadina Muhammad Wassalim 🥰
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Gaisuwar ban girma Anty Lele 🥰 Allah yaqara wa rayuwa albarka🙏
Sis Prettyn Jajirtattu ƙawar alkhairi ubangiji yaƙara basira 🙏
Page 65~66
Mama ta yi saurin cewa.
"Ga ta nan zuwa." Tun ba ta jira abin da yaron zai faɗa ba.
Abba ya kalli yaron ya ce.
"Wane aka ce ka kira.?"
Yaron.
"Shukrah."
Da ga haka yaron ya yi waje Mama hankalinta ya ta shi Manaheer ta yi dariya Umma ta harare ta Abba ya kalli Shukrah da ba ta da niyyar ta shi ya ce.
"Ba ki ji abin da aka ce ba.?"
Manaheer ta kama hannunta su ka shige ɗaki Mama ta kama hannun Mimah su ka shiga ɗaki bada jimawa ba Shukrah ta fito ta kalli Umma.
Umma ta yi murmushi Shukrah ta fita Amina ta ta shi ta shiga ɗakin Mama da ga nan taro ya watse.
Mama hankalinta ya tashi Mimah an sha kwalliya da lalli Amina ta shigo ta kalli Mama ta ce.
"Daman wancan yarinyar ta na da saurayi."
Mama.
"Aa ba ta da kowa."
Amina.
"Wanda ya aiko kiranta fa.?"
Mama cike da takaici ta yi banza da ita Amina ganin haka ba ta ƙara cewa komai ba ta shige bedroom ta yi kwanciyarta Mama ta bi bayanta da harara.
Mimah.
"Yanzu ki na ganin abin da Abba ya yi amman kin ka sa cewa komai."
Mama.
"Kwantar da hankalinki shalele ba dai ki na son shi ba.?"
Mimah ta ce.
"Bari in leƙa in duba saurayin sannan kuma in duba irin motar da ya zo dashi."
Mama ta ce.
"Tunani mai kyau."
Mimah ta sa turare ta yafa gyale ta fita daidai lokacin da Auta ya fito da jug ɗin ruwa Mimah ta tsayar da shi ta tambaye shi wa zai kai wa ruwa Auta ya ce.
"Aunty Shukrah zan kai wa."
Mimah ta amshi ruwan ta ce.
"Jeka abinka."
Auta yaƙi yarda Manaheer dake tsaye a bakin ƙofa tun fitowar Auta ta ce.
"Auta ba ta jug ɗin ka dawo."
Auta ya sakin mata plate ɗin da aka ɗaura jug a kan Shi.
Mimah ta harari Manaheer ta yi waje bayan ta shiga zauren harda sallama Shukrah da baƙon su na zaune a saman wani carpet wanda Abba ya shimfiɗa tun bayan da ya shigo gida domin ko Shukrah a kai ta samu baƙon.
Mimah ta gaishe shi ta a'je plate ɗin ta yi waje 5 minutes ta dawo ta shige ɗaki Mama.
"Wani irin mota ki ka gani.?"
Mimah ta yi dariya ta ce.
"Ko keke ban gani a ƙofar gida ba."
Mama ta yi tsaki ta ce.
"Har yanzu ki na son shi.?"
Mimah.
"Allah ya kiyaye na barwa Shukrah."
Mama ta yi dariya su ka tafa kamar ba ƴa da uwa ba.
Shukrah ba ta jima ba ta dawo hannunta ɗauke da carpet da plate mai ɗauke da jug ta shiga ɗaki dukkan su a parlour ta same su Manaheer ta fara tsokanarta Darraini na tare mata Shukrah bedroom ta shige Umma ta kalli Manaheer ta ce.
"Allah ya shirya mun ke."
Daga haka ta bi bayan Shukrah ta same ta zaune a saman gado ta na ta zabga murmushi Umma ta yi farin ciki da ganin haka.
Umma ta zaune tun kafin ta tambaye ta Shukrah ta fara gaya mata yanda su ka yi da saurayinta mai suna Hamza.
Shine wannan da ya yi mata siyayya lokacin da aka kwantar da Manaheer a hospital Umma ta yi na'am da shi duba da yanda ya samu shiga a gurin ƴarta.
Bayan duk sun kwanta bacci Shukrah idonta biyu Manaheer daman ba ta bacci da wuri ta kalle ta.
"Soyayya ruwan zuma."
cewar Manaheer Shukrah ta lumshe ido kamar ta na bacci Manaheer ta gaji da surutun ita ma ta kwanta a haka har bacci ya kwashe su.
Kwana biyu da faruwan hakan masu neman auren Shukrah sun kawo kayan sa rana kamar yanda Abba ya buƙata.
Abba ya zauna da ƴan uwanshi su ka tsaida lokaci 5 month Mama sai habaici take za su ga abin da Umma za ta ƙulla.
Umma ta toshe kuninta kamar ba ta jiba hutun Khadija ya ƙare Umma ta haɗa mata kaya daidai gwargwado Abba ya kai ta ta sha ta hau mota.
Bayan kwana biyu Umma ta ci gaba da sana'ar sai da turare sosai ta ke samun ciniki Shukrah saurayinta ya sai mata babban waya smart 9 yanzu har ta online Umma na sai da turare.
Har yanzu Mama ba ta san wanda Shukrah za ta aura ba ita da Amina gani suke Abba ya samo talaka ne ya bashi sadakarta.
Hamza duk lokacin da zai zo zan ce gurin Shukrah bai taɓa zuwa da ko keke ba kullum a ƙafa ta ke ganin shi farkon haɗuwar su ma a ƙafa ta ganshi.
Kayan sa ranar da ya kawo ba wasu na arziki ba ne shi ya sa Mama habaici ya ƙaru Umma babu ruwanta ita babbar addu'arta Allah ya sa ya zamo miji na gari ita ƙyale ƙyalen duniya ba sa burgeta.
Su na zaune su na fira a tsakar gida Amina ta fito daga ɗakin Mama ta kalli Manaheer ta ce.
"Wanki na ya taru."
Manaheer.
"A kira miki almajirin ƙasan layin mu ya iya wanki sosai."
Amina.
"Kin ji na yi miki maganar almajiri.?"
Manaheer.
"Na ji kamar kin ce mun a ina ake kai wankin kaya."
Amina.
"Ba na son iskanci ya ina miki magana ki na mayar mun da amsa kai tsaye."
Manaheer.
"Allah ya wuci zuciyar Umma."
Amina.
"Idan kin ga dama ki biyo ni ki kwashi wankin nawa kuma wallahi idan ki ka wanke bai fita ba sai kin sake wanke su."
Manaheer ta sa ki baki ta na kallon Amina Umma na ɗaki ta na kwance ba ta san abin da ke faruwa ba.
Amina ta yi gaba ta na tunanin Manaheer ta biyo ta yaron ya da ya yi sallama shi ya ɗauke mu su hankali.
"A na kiran Manaheer a waje." In ji yaron Shukrah ta ce.
"Ga ta nan zuwa."
Manaheer ta sa hijjab ta yi waje Darraini ta yi dariya Shukrah ta ce.
"Manaheer sai dai shiriyan ubangiji."
Bayan fitan Manaheer ta kalli Auwal sama da ƙasa ta ce.
"Dan Allah mallam karka sake zuwa gidan nan domin wallahi na ga ji da kawaicin da na ke maka."
Auwal.
"Subhanallahi waya ɓata ma gimbiyata rai za ta sauke fushin a kaina.?"
Manaheer.
"Wane ma sunanka.?"
Ta tambaye shi cike da rainin wayyau Auwal.
"Yanzu sunan mijin na ki ma ba ki sa ni ba wannan ai abin kunya ne."
Manaheer.
"Karka ɓata wa kanka lokaci tun wuri ka nemi matar aure amman ba ni ba domin wallahi ban isa aure ba."
Auwal.
"Kar ki damu gimbiyata ni ma ban isa aure ba wallahi hajjiya ce ta takura mun amman guda nawa nake ɗan yaro na da ni."
Manaheer.
"Hanji ne kai ba yaro ba."
Auwal.
"Duk da ban san dalilin ɓacin ran ba amman dan Allah a sassauta mun gimbiyata."
Manaheer ta na shirin magana Abba ya shigo zauren Auwal ya ɗuka ya gaishe shi Abba ya miƙawa Manaheer makullin ɗakin shi ya ce.
"Duba cikin drawer ki ɗaukon mun wasu takardu."
Manaheer ta amsa ta fita har za ta shiga ciki ta ji abin da Abba ya ke cewa da sauri ta dawo ta tsaya ta in da ba za a ganta ba.
Abba ya kalli Auwal ya ce.
"Ba na son yawan zance idan ka koma ka turo mun iyayenka mu tsaida maganar aure."
Auwal ba ki har kunni Manaheer ta na gama ji ta shige ɗakin Abba ta ɗauko ta kawo mishi Abba ya karɓa ya na ƙara jadaddawa Auwal cewa kar ya manta.
Bayan fitan Abba Auwal ya kalli Manaheer ya ce.
"Amaryata."
Manaheer ta shanye ɓacin ranta ta yi murmushi cike da yaudara ta ce.
"Yaushe za ka turo iyayenka."
Auwal.
"Daman na san ki na sona gimbiyata ni ko yanzu ki ka ce a shirye na ke."
Kafin Manaheer ta bashi amsa Amina ta shigo zauren ko gyale babu ta ce.
"Zo ki wuce ki yi aikin da na sa ki." Manaheer ta ce.
"Yanzu zan zo."
Amina ta tsaya ta ce.
"Sallame shi mu wuce."
Manaheer ta kalli Auwal ta ce.
"Baby zan shiga gida ga shi kuma ban gaji da jin dadaɗan muryanka ba. "
Auwal.
"Kar ki damu gimbiyata amarya ta ni ma zan yi kewarki sosai da sosai dan Allah ki kula mun da kanki please."
Amina cike da takaici ta shige Manaheer ta dawo da kallonta gurin Auwal ta yi mishi kallo mai cike da gargaɗi kafin ta ce.
"Ganganci ne auren wanda ba ta sonka."
Daga haka ta shige gida ta barshi Auwal ya sa ki ba ki ya ce.
"Kaga yarinya sai ka ce mai iskokai."
Amman zan yi maganinki ba ki san waye Auwal ba da ga haka ya kakkaɓe rigar shi ya yi gaba.
Manaheer ɗaki ta shige ta kwanta a saman kujera ta na lumshe ido Umma ta fito da ga bedroom ta kalleta ta ce.
"Har baƙon ya tafi.?"
Manaheer.
"Eh kaina ke ciwo."
Umma ta kawo magani ta ba ta da ga haka ta yi waje gurin su Darraini ta nufa Auta ya shigo hannun shi ɗauke da baƙin leda ya miƙawa Umma ya ce.
"Gashi in ji saurayin Anty Manaheer."
Wash typing ba daɗi wallahi kuma ka gama ba likes ba comments ba share
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Allahumma Sali Ala Sayyadina Muhammad Wassalim 🥰
Written by
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Page 67~68
Umma ta amsa ledar da Auta ya miƙa mata Amina ta fito tsakar gida ta kalli Daraini ta ce.
"Ina Manaheer ta ke.?"
Darraini.
"Ta na cikin ɗaki."
Amina ta shiga ɗakin Umma Manaheer na kwance hannu dafe da kai Amina ta fara masifa ta na zagin ta Umma ta shigo ɗakin hannunta da ledar da Auta ya kawo ganin Manaheer na kwance hannu dafe da kai ga zufa ta ko ina ya na gangaro mata.
Umma ta a'je ledar a kusa da ita ta kama hannun Manaheer ta ce.
"Har yanzu kan bai faɗa ba.?"
Manaheer ta ka sa magana Amina ta ce.
"Wallahi ko hospital za ku kai ta kafin ku ta fi sai ta yi mun wankin da na sa ta."
Umma.
"Amina wannan wani irin rashin imani ne yarinya na cikin wannan halin amman ki ke maganar ta zo ta yi miki wanki."
Amina.
"Kin ga mallama ban yi da ke ba kuma wanki ne wallahi sai ta yi."
Umma.
"Amina fita da ga cikin ɗakin nan tun kafin ranki ya ɓaci."
Amina.
"Ɗaki dai ba da ga gidanku ki ka zo da shi ba gida kuma na yaya na ne."
Manaheer ranta ya gama ɓaci ga ciwon kai ga Amina na ƙara mata da hayaniya Manaheer ta miƙe ta nufi gurin Amina Umma ta ce.
"Manaheer ina za ki je a wannan halin da ki ke ciki.?"
Manaheer ba ta saurari zan cen Umma ba ta na zuwa ta shaƙe wuyan Amina da hannu ɗaya Amina Umma ta yi ta yi ta ƙwaci Amina a gurin Manaheer amman ta ka sa Umma ta nufi ɗakin Mama hankali tashe.
Ta na zuwa ta faɗa ɗakin ta kamo hannun Mama Shukrah ganin Umma riƙe da hannun Mama su ma su ka ta ke mata baya su na shiga ɗakin su ka tsaya su na kallon Manaheer ga Amina sai kakari ta ke yi.
Umma hankali tashe ta ce.
"Dan Allah ku zo ku ta yani mu ƙwace ta."
Mama da gudu ta fita Umma ta din ga roƙan Manaheer amman ta ƙi sakin ta Daraini ma hakan amman Manaheer ko buɗe ido ma taƙi yi Shukrah ta matsa ta kama goshin Manaheer ta karanta mata ayyatul kursiyu da sauri ta buɗe idanunta da su ka rine ta na shirin kai duka su ka haɗa ido da Shukrah Manaheer ta sa ki Amina ta yanke jiki ta faɗi.
Da sauri Umma ta riƙo ta Daraini ta ɗibo ruwa ta yayyafawa Manaheer raguwar kuma ta ba wa Amina ta sha saboda wahala da ƙyar ta ke iya numfashi Amina anji shaƙa.
20 minutes Manaheer ta buɗe ido Amina ta na ganin ta buɗe ido da rarrafe ta fita ɗakin babu wanda ya lura da ita sai Shukrah da Auta.
Su ka taimaka mata ta ta shi ta zauna a kujera, Umma ta zauna kusa da ita.
"Manaheer mai ke damunki.?"
Umma.
"Kai na kamar zai fashe jiki na sai ciwo yake mun kamar ba nawa ba."
Har zuwa dare Manaheer na kwance babu lafiya, bayan dawowar Abba da daddare ya na zaune da ga shi sai matan shi sun sa shi a tsakiya.
Abba ya kalli Umma ya ce.
"Ina yaran suke.?"
Su na ɗaki gurin Manaheer ba ta da lafiya Abba.
" Allah ya ba ta lafiya."
da ga haka bai ƙara cewa komai ba, Mama na shirin kai gulma su ka haɗa ido da Manaheer da ta fito za ta shiga toilet, Mama ta rufe baki ta kau da kai.
Manaheer bayan ta fito da ga toilet ta yanke jiki ta faɗi da sauri Umma ta ƙariƙa gurin ta na kiran sunan Shukrah, ku san a tare su ka fito su ka taimaka mata ta shiga da Manaheer ɗaki.
Abba ya bi bayan su hankali ta she a bedroom su ka kwantar da ita, Abba ya ce.
"Daman jikin ya yi zafi ne haka.?"
Umma.
"Uhmmmm ni ban ma san ta yan da zan yi maka bayani ba."
Mama ta shigo ɗakin ta ce.
"Alhaji Amina ba ta da lafiya."
Abba ya da ka wa Mama tsawa ya ce.
"Da wanne zan ji da wannan ko da wan can.?"
Mama za ta ƙara magana Abba ya ce.
"Fita ki bani guri."
Mama ta fita Abba ya kalli Umma ya ce.
"Bari in kira mai chemist ɗin can ya duba ta."
Umma.
"Ina ganin kamar ba ciwon hospital ba ne."
Abba.
"To idan ba ciwon hospital ba ne ciwonki ne.?"
Umma ta yi shiru yaran su ka fice daga room ɗin Abba ya ce.
"Ba na son jajibe jajibe kar ki kwaso mun bala'i ki mannawa ƴata."
Umma ta faɗawa Abba abin da ya faru tsakanin Amina da Manaheer Abba ya ce.
"Wato ki na nufin jinnu koh.?"
Abba.
"Wallahi kar in ƙara jin wannan maganar a bakin ki."
Da ga haka ya yi waje Umma ta ɗauko ruwan zam-zam ta yi addu'o'i ta ba ta ta sha Abba ya ce.
"Sa mata hijjab zan shigo da doctor." Fitar Abba bada jimawa ba su ka shigo tare da doctor ya duddubata ya koma shago ya kwaso drip da injection ya sa mata.
Doctor ya kalli Umma ya ce.
"Yanzu za ta yi bacci in sha Allah."
Abba ya kama hannun doctor su ka fita sai da su ka je shago ya bada table's sannan Abba ya ce.
"Ba ka gaya mun abin da ke damunta ba."
Doctor.
"Zazzaɓi ne kawai sai ƴar damuwa da ta sa a ranta."
Abba ya biya kuɗin ya amso magungunar ya tafi gida, ya na shigowa su ka haɗe da Mimah za ta fice.
Koda ta ga Abba ba ta fasa fita ba ta raɓa ta gefen shi za ta wuce Abba ya fincikota ya zabga mata mari, Mimah ta fashe da kuka da sauri Mama ta fito da ga ɗaki.
Abba ya ce.
"Wallahi ba zan lamunci gantali a cikin gida na ba."
Mama za ta yi magana Abba ya ce.
"Duk irin yawon da ta ke yi da gantalin da ta ke yi a gari, ina da labari kawai na ɗaga mata ƙafa ne."
Abba ya fara faɗa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, kuma duk da haushin kuɗin da ya kashe na maganin Manaheer.
Amina ta fito da ga ɗakin Mama Abba ya kalleta ya ɗaure fuska, Amina ta matsa kusa da shi ta na hawaye ta ce.
" Ya Aliyu ɗazun bayan fitan ka Manaheer ta zage ni ta ci mun mutunci, harda cewa na zo na tare musu a gida saboda na rasa mashin shini."
Abba ya rasa in da zai sa ranshi saboda ɓacin rai.
Ya kalli Amina ya ce.
"Manaheer ɗin da ba ta da lafiya kike magana.?"
Amina ta fashe da kuka ta ce.
"Babu irin zagin da ba tai mun ba ɗazun."
Abba ya ce.
"Dan Allah ba na son tashin hankali, yanzu dai faɗa mun abin da ki ke so ayi."
Amina.
"Ban da lafiya ne tun safe ko abinci na kasa ci"
Abba ya ba ta 5k ya ce.
"Kije chemist."
Da ga haka Abba ya shige ɗakin Umma, Mama ta kama hannun ƴarta su ka shige ɗaki.
Amina ta yi waje ta na dariya.
Like and share
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Allahumma Sali Ala Sayyadina Muhammad Wassalim 🥰
Written by
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Page 69~70
Abba ya miƙawa Umma maganin ya fita ranar babu wanda ya yi bacci sai Auta dukkanin su kwana suka yi su na ibada.
Manaheer da asuba ta ta shi Shukrah ta taimaka mata ta yi alwala ta yi sallah Umma ta yi addu'o'i a cikin ruwan zam-zam kamar yan da ta saba yi kowace safiya suka sha daga nan kowa ya kama aikin shi.
Auta ya shigo da baƙin leda ya miƙawa Umma ya fita.
Shukrah sun je gaishe da Abba daga nan su ka gaishe da Mama.
Bayan sun dawo Manaheer ta je ta gai da Mama daga nan ta shiga ɗakin Abba ta same shi zaune a saman carpet ya na ƙirga kuɗi.
Abba ya ɗaue fuska Manaheer ta gaishe shi ta nemi gurin zama Abba ya kwashe kuɗin shi ya zuba su a cikin aljihu Manaheer ta ce.
"Abba kuɗin karyawa."
Abba.
"Su ke nan ƴan canjin na siyo miki magani jiya dan haka ku je ku yiwa Annabi salati s a w."
Manaheer ta kalli aljihun da ya zuba kuɗi a ciki Abba ya ce.
"Ba kuɗi na ba ne."
Manaheer.
"Abba ka san menene.?"
Abba ya ɗaure fuska shifa ya riga ya gama kashe kuɗi jiya da daddare dan haka yau ya sha alwashin ko sisi ba zai bayar ba.
Abba.
"Kin sha maganinki.?"
Manaheer.
"Ai ban ci abinci ba."
Abba.
"Ita Umman ta ku amfanin mai take da ba za ta nema muku abin da za ku ci ba.?"
Manaheer.
"Na ji kaina ya fara ciwo bari in je in kwanta."
Abba.
"Ki tabbatar kin sha magani kar ki sa ni a sara."
Manaheer.
"In sha Allah."
Da ga haka ta fita bayan shigar ta ɗaki Umma ta miƙo mata ledar da Auwal ya kawo jiya waya ce a ciki sabuwa smart 8.
Manaheer ta yi murmushi ta jona a charge daman sun kawo wuta.
Umma ta shiga ɗakin Abba su kai sallama ya ba ta kuɗin cefanen dare, da rana ba girki saboda ya kashe kuɗaɗen shi jiya ga maganin Manaheer ga Amina 5k.
Bayan fitar Abba Amina ta fito tsakar gida ta na harare-harare.
Umma ta dama kunnin gyaɗa sukai breakfast da shi daga nan Manaheer ta sha magungunar ta sukai wanka su ka shirya sannan su ka dasa fira.
Auta na ba su labarin yan da Amina ta fita da rarrafe Manaheer har da hawaye saboda dariya, Umma ta na ciki ta na zuba turaren wuta a wani babbar leda.
Bayan Umma ta gama haɗawa, ta ba Daraini ta kaiwa matar da ta siya daga nan ta ba ta kuɗi ta yi cefane.
Manaheer ta yi shimfiɗa a tsakar gida ta na zaune su na fira Amina ta fito ta na ra ta ya jaka Mimah na bayanta an riƙo gyale a hannun gyalen ma yanzu an wuce level ɗin ya fawa sai dai a riƙo shi a hannu.
Manaheer sai da ta ba ri sun zo tsakiyar gidan ta ce.
"Big Anty ina kwana."
Amina.
"Da ban kwana ba za ki ganni."
Manaheer.
"Da ga abin arziki."
Amina.
"Manaheer wallahi idan kika ƙara shiga sabgata a cikin gidan nan sai na tijaraki."
Manaheer.
"Kamar ki na jirace da ni."
Mimah da ta ga abin ba na ƙarewa ba ne ta kama hannun Amina ta ce.
"Dan Allah Aunty Amina ki rabu da ita ki zo mu wuce."
Da ga haka su ka yi waje Shukrah da ta zauna ku sa da Manaheer ta ce.
"Wai dan Allah ba za ki dai na shiga sabgar da babu ruwanki ba.?"
Manaheer.
"Aunty Shukrah wani irin anko kike ganin ya da ce mu fitar."
Shukrah ta yi banza da ita daga nan su ka cigaba da fira da Auta, har lokacin da Daraini ta kawo cefane macaroni Shukrah ta dafa suka ci da rana.
Bayan sun gama cin abinci Abba ya kira waya ya ce Shukrah ta raka Manaheer chemist ayi mata allura.
Manaheer na jin maganar allura ta yi tsalle ta ce.
"Wallahi ta warke."
Umma ta yi ta yi amman Manaheer ta ce.
"Ta ji sauƙi."
Mama ta fito sanye da hijjab ta kulle ƙofa ta fita.
Kuɗin cefanen da Abba ya bayar Umma ta miƙawa Shukrah ce.
"Ga yi nan kuyi cefane ku ɗaura, idan kun gama ba sai kun kirani ba."
Shukrah ta karɓi kuɗin su ka yi kamar yan da ta ce tuwon shinkafa miyar kuɓewa ɗanye.
Da daddare Abba ya na zaune a na fira ya kalli Umma ya ce.
"Manaheer ta je an yi alluran.?"
Tun kafin kowa ya yi magana Amina ta ce.
"Ba ta je ba."
Manaheer ta yi murmushi Abba ya ce.
"Shukrah ɗauko hijjab ki ra ka ta."
Abba ya na rufe baki yaro ya yi sallama ya ce.
"A na kiran Shukrah a ƙofar gida."
Abba ya kalli Daraini ya ce.
"Ta shi ki ra ka ta."
Shukrah ta ɗau carpet ta fita Manaheer ta na tura baki su ka tafi chemist, bayan sun fita Abba ya ce.
"Gobe idan Allah ya kai mu za a fara gyaran gidan nan."
Mama.
"To mu kuma a ina za ka a'je mu."
Abba ya yi banza da ita ya ce.
"Za a fara da ɗaki na idan an gama sai ɗakin Amina."
Mama dai ba haka rai ya so ba su na nan zaune Manaheer ta shigo Daraini na bin bayanta ta na dariya.
Abba ya sallami kowa ya shige ɗaki ƙarfe 9 dai dai Shukrah ta shigo.
Sai da su ka zo kwanciyya Shukrah ta ce.
"Umma wai Hamza ya matsa sai na je na gai da hajjiyar su."
Umma.
"To mai ki ke ce mishi.?"
Shukrah.
"Ba zan iya zuwa ba shine ya ce in tambayeki."
Umma.
"Ni dai ban amince ki je ba."
Manaheer ta riga kowa bacci da ga nan su ka yi alwala su ka kwanta asuba gari.
Bayan wani lokaci har an gama gyara ɗakin Abba a na gyara ɗakin Umma yanzu haka gidan da ga Mama da ƴarta sai Amina.
Umma ta roƙi Abba su ka tafi Saminaka shi ma da ƙyar ya bari da sharaɗin a na gama gyaran ɗaki za ta dawo.
Umma a gidan iyayenta ta sauka gidan akwai ƙanin mahaifinta a zaune, hasalima Umma ta matsa mishi a kan sai sun dawo nan da zama shi da yalanshi.
Aunty Maryam ta zo sun jima su na fira zuwa yamma ta tafi, ɗakin da Umma ta sauka ciki da parlour ne sai toilet a ciki.
Kwanan su uku Aunty Fatima ta zo da ƙaton cikinta haiwuwa yau ko gobe, zuwa yamma driver ya zo ɗaukarta.
"Shukrah haɗa kayanki mu tafi." Cewar Anty Fatima.
Umma za ta ga ya wa Abba Anty Fatima ta ce.
"Wallahi ki na ga ya mishi ba zai yar da ba."
Haka nan Umma ta rufe baki su ka tafi, bayan tafiyan su da kwana biyu Aunty Rabi'a ta zo ta yini su kasha fira da Manaheer.
Zuwa dare Umar ya zo bayan sun gaisa da Umma ya sauke musu kayan abinci, taliya shinkafa macaroni kayan tea da sauran kayan buƙata na rayuwa, da ga nan ya ɗauki matar shi.
Washe gari Umma ta shirya su ka tafi gidan Inna, bayan sun gaisa Inna ta ce.
"Ita Shukrah ta girma yanzu babu ruwanta da mutane."
Umma.
"In sha Allah ta na nan zuwa."
Zuwa sallar azahar Umma ta yi musu sallama ta tafi gida,
Tsakanin gidan su da gidan Inna babu nisa dan haka a nan tabar Daraini da Manaheer.
Bayan sun yi sallah su ka zauna su na fira,
Inna ta harari Manaheer ta ce.
"Kin wani zura mun ido kamar mayya."
Manaheer.
"Astagfirullah Inna ko ni mayyace ai jikinki babu tsokar da zai isheni."
Daraini ta yi dariya su na cikin haka Isma'eel ya shigo, duk da cewa bawai sun saba dashi sosai ba ne,
Amman su babu ruwansu kowa na su ne.
Manaheer ta washe baki ta ce.
"Barka da zuwa uncle."
Isma'eel.
"Saukar yaushe.?"
Manaheer.
"Mun kwana biyu da zuwa."
Su ka gaisa ya gaishe da Inna da zai fita ya ce.
"Manaheer ɗauko hijjab ki biyo ni."
Bayan fitan su Daraini ta ce.
"Ni fa yunwa na ke ji."
Inna.
"Aiko ba ni da komai a ɗakin nan."
Daraini.
"Ai ko gida za mu wuce yanzu."
Inna.
"Babu inda za kuje sai kun yi mun wanki da girki."
Daraini.
"To idan mun gama mai za ki bamu, tun da kin ce ba ki da abinci."
Inna.
"Yanzu wankin ma sai na biya ku saboda gantalewa.?"
Daraini ta yi kwanciyarta ta na danna wayar Umma, Manaheer ta yi sallama ta shigo hannunta ɗauke da manyan ledoji guda biyu.
Bayan ta zauna Daraini ta buɗe ledojin kaji ne a ciki guda biyu manya sai kayan miya da kayan cefane,
Ɗayar ledan kuma sweet biscuits drinks da sauransu.
Daraini ta ce.
"Gaskiya uncle ɗan aljanna ne."
Inna da ta ji haushin kayan da Isma'eel ya bayar ta ce.
"Ni kuma dan uban mutum ya kai ni wuta."
Manaheer ta yi dariya suka gyara kayan miya su ka niƙa a greater Daraini ta ɗaura miya.
Inna ta zauna a tsakar gida ta kasa ta tsare.
Manaheer ta ce.
"Inna ba ki bayar da shinkafar da za a dafa ba."
Inna.
"Idan Aliyu ya kawo sai ki zo ki ɗiba."
Manaheer ta yi dariya ta ce.
"Shi ma lokacin ya na da shi ai ya na bayarwa, ba tare da an tambaya ba."
Inna ta yi banza da ita har suka gama miya Inna ta hana shinkafar da za su dafa.
Su ka yi alwala su kai sallahr la'asar daga nan,
Manaheer ta ɗauko babban flas guda biyu ta raba miyan biyu ta zuba wa Inna ɗaya ta juye musu ɗaya.
Su ka gyara gurin sannan su ka ɗau miyar Manaheer ta ɗau ledarta suka yi wa Inna sallama su ka tafi,
Inna baƙin ciki kamar ya kasheta amman haka ta daure ta buɗe flas ɗin da Manaheer ta a'je mata, miya ne ya ji kaji sai tashin ƙamshi ya ke Inna ta ce.
"Da na sa ni na ba da shinkafar ko gwangwani 4 ne su dafa,
yanzu ina zan samu abin da zan haɗa da wannan miyar."
Inna ta ɗau flas ɗin ta shiga ɗaki ƙarshe dai da bread ta ci ta haɗa da tea.
Bayan sun fita da ga gidan Inna Daraini ta ce.
"Amma tsowuwar nan ƴar bala'i ce."
Manaheer.
"Har da rikicin tsufa ke damunta."
Bayan sun shiga gida Umma na zaune ta na yan kewa Auta ƙumba.
Manaheer ta a'je flas ɗin hannunta Daraini ta fara buɗe flas ɗin da ake a'je abinci.
Shinkafa ne white aciki Umma ta ce.
"Lafiya."
Daraini.
"Yunwa mu ke ji."
Umma ta ci gaba da abin da ta ke,
Manaheer ta ɗauko plate su ka cika da shinkafa daga nan ta janyo flas ɗin da ta zo da shi, ta zuba miya su na ci su na firan Inna.
Bayan sun gama cin abinci Manaheer ta miƙawa Umma ledar da ta shigo dashi.
Umma ta amsa ta buɗe bayan ta ga abin dake ciki Manaheer ta miƙa mata flas ɗin da su ka shigo da shi.
Umma ba ta yi mamakin hanasu abincin da Inna ta yi ba domin halin Inna babu wani sabon abu a ciki.
Da yamma su ka ci bread da miya su ka haɗa da tea, bayan sun gama su ka dinga firan Inna har bacci ya ɗauke su, Umma ta na ta ibada har akai sallahr asuba,
Manaheer ta fara ta shi sannan ta ta shi Daraini Umma ta tayar da Auta bayan sun idar da sallah,
Suka yi karatun Qur'ani da gari ya yi haske su ka je gaishe da mutanan gida, bayan sun dawo su ka yi breakfast Manaheer ta gyara ɗaki Daraini ta gyara tsakar gida Auta ya wanke toilet,
Bayan sun gama aikin su ka zauna su na hutawa yaro ya yi sallama ya gaishe da Umma sannan ya ce.
"Inna ta na kiran Daraini da Manaheer."
Umma.
"Ka ce mata gasu nan zuwa. "
Manaheer.
"Umma ko wanka ba mu yi ba."
Umma.
"Ki rufa mun asiri dan Allah ki ta shi ku tafi."
Daraini ta sa hijjab ta fita Umma ta kalli Manaheer da ke zaune ko motsawa ba ta yi ba.
Umma.
"Yaushe na fara wasa da ke.?"
Manaheer ta fara kuka Umma ta sa ki baki ta na kallonta.
Umma ta na mamakin kukan ta domin ita ba ta ga abin kuka ba.
Manaheer itafa da gaske ta ke yi ba ta son zuwa gurin Inna.
Like and share sannan kuyi comments
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Allahumma Sali Ala Sayyadina Muhammad Wassalim 🥰
Page 71~72
Umma ta ce.
"Manaheer zo ki wuce ki tafi."
Manaheer ta share hawaye ta fita Umma ta yi ta gumi ta na tunanin lamarin Manaheer.
Manaheer ta shiga gidan bakin ta ɗauke da sallama Daraini na wanki a tsakar gida, Inna ta na zaune a saman darduma a ƙofar ɗakinta.
Manaheer ta gaishe da Inna ta na turo baki Inna ta ce.
"Sai yanzu ki ka ga damar zuwa."
Manaheer ba ta ce komai ba Inna ta ce.
"Ki shiga ɗakin ki gyara mun."
Manaheer ta shiga ɗakin Inna kaya ne ko ina ga tayis ɗin ya dafe, Manaheer ta ce.
"Wannan ɗakin kamar ba mutane ke rayuwa a ciki ba."
Inna.
"Dabbobi ne ke rayuwa a ɗakin."
Manaheer ta kama baki ta fara gyaran bedroom, bayan ta gama ta gyara parlour dattin da ta fitar kamar ɗakin kuturwa.
Bayan ta zubar da sharan ta kalli Inna ta ce.
"Inna yanzu a cikin ɗakin nan ki ke rayuwa, bakya tsoran wani cutar ta kama ki.?"
Inna.
"Idan kin gama zagin nawa kije ki gyara mun toilet domin na san ba ki gyara ba."
Manaheer ta shiga toilet ɗin babu laifi bai yi datti kamar ɗakin ba.
Bayan ta gyara toilet ɗin ta janyo wani babban kwano a ƙasan gado.
Dambun nama ne cike da kwanon kamar ba a dibar shi Manaheer ta cika farin leda ta aje a saman one seater ta haɗa da hijjab ɗin ta.
Inna ta kira Manaheer ta ce.
"Ki zo ki share tsakar gidan."
Manaheer ta fito daga ɗaki ta na cewa.
"Yanzu dan Allah da bamu zo garin nan ba waye zai yi miki duk wannan aikin.?"
Inna.
"Ubanki Aliyu shi zai yi."
Manaheer ta yi sharan ta gyara toilet ɗin tsakar gida, kuma har lokacin Daraini na wanki ba ta gama ba.
Inna.
"Kitchen ɗin sai na roƙa za ki gyara.?"
Manaheer da ta fara gajiya ta ce.
"Inna yunwa na keji."
Inna ta ce.
"Ita wanda ke aikin ƙarfi bata ce ta na jin yunwa ba sai ke, to ni ban da abin da zan ba ki."
Manaheer ta yi dariya ta ce.
"Hutawarki lafiya kakus."
Da ga haka ta gyara kitchen ɗin ta shiga ɗakin Inna ta diɓo indomie guda 4 manya, ta haɗo da eggs guda 6 ta ɓoye dambun namar da ta ɗiba ta fito.
Inna bata lura da Manaheer ba har ta fice 20 minutes ta shigo da baƙin leda.
Inna ta ce.
"Yaushe ki ka fita ban ganki ba.?"
Manaheer ta zauna kusa da Inna ta buɗe ledar ta ce.
"Indomie na siyo mana da eggs."
Inna ta washe baki Manaheer ta kalli Daraini ta ce.
"Aunty Daraini dafa mana indomien in ƙarika miki wankin."
Daraini ta shiga kitchen ta kunna wuta Inna ta ce.
"Akwai kayan miya a kitchen ɗin da mangyaɗa."
Daraini ta yi dariya domin ta ga lokacin da Manaheer ta fita da wani abu a cikin hijjab, kuma ta na da tabbacin wannan indomien a ɗakin Inna ta ɗiba.
Manaheer ta kalli wankin ta ga da yawa kuma lokacin biyu saura.
Wanki ɗai ɗai ta dinga yi har ta gama ta gyara gurin, Inna ta na samata albarka ta na washe baki za a ci banza.
Daraini ta zubo indomie a plate biyu ɗaya ta sa eggs guda 2 ɗayan kuma guda 4, ta aje mai eggs 2 a gaban Inna.
Ɗayan kuma ta aje musu a kusa da Inna suka zauna Inna ta ce.
"Manaheer duba ƙasan gado na, za ki ga lemu ki ɗibo guda 3."
Manaheer ta kalli Daraini suka yi dariya bayan ta shiga ta duba ƙasan gadon drinks ne wajen katan biyar, ita ɗazun ma ba ta lura da shi ba.
Manyan ta ɗauko guda 2 ɗayan kuma ta ɗauko ƙarami ta aje wa Inna ƙaramin ta aje musu manyan.
Bayan sun gama cin abincin suka gyara gurin, daman Daraini ta ɗaura ruwan zafi a wuta.
Bayan ruwan ya yi zafi Manaheer ta yi wanka da ga nan ta yi sallah Daraini ma haka, Manaheer ta kai wa Inna ruwan wanka toilet.
Bayan ta fito ta shirya suka zauna a tabarma Inna ta na basu labarin kakanin su, har a kai sallahr la'asar su na gidan.
Bayan sun idar da sallah Manaheer ta ce.
"Inna zamu tafi gida ko za a ɗaura miki girkin dare."
Inna.
"Zanci bread da miya."
Manaheer.
"Inna dan Allah ki dinga cin abinci."
Inna.
"Ina tausayawa masu kawowa ne."
Manaheer.
"Sun kawo miki ne domin ki dafa kici bawai ki adana ba."
Inna.
"To ai yanzu yamma ta yi."
Manaheer.
"Ko taliya sai mu dafa miki."
Inna.
"Aa ba zan ci taliya ba."
Daraini.
"Kuskus."
Inna.
"Yauwa ku dafa mun fari sai in ci da miya."
Zuwa 5 na yamma sun gama komai Inna ta zuba musu abincin a flas Manaheer ta ce.
"Na ga dambun nama a ɗakinki ɗazun ina gyaran ɗaki."
Inna ta ɗaure fuska ta ce.
"Na san kin ɗiba koh.?"
Manaheer.
"Eh na ɗiba mana shine na ce zan gaya miki kar in ci abin da ba a bani ba."
Inna.
" Ai ko yanzu ɗin bada sa ni na ki ka ɗiba ba."
Manaheer.
"Ai idan na gaya miki ba za ki bani ba."
Inna.
"Saboda kin mai da ni marowaciyya."
Manaheer.
"Tsohuwa mai ran ƙarfe."
Inna.
"Ya zanyi da halinki ai dole in yi haƙuri."
Manaheer.
"Ni fa na yanke shawaran zan dawo nan da zama, kafin mu koma gida."
Inna.
"Allah ya kiyaye ni wallahi ba na ɓukatar ki."
Daraini ta yi dariya ta ce.
"Na tafi gida tun da na ga firan na ku ba mai ƙarewa ba ne."
Da ga nan su ka yiwa Inna sallama su ka tafi gida, suna hanya Manaheer na bawa Daraini labarin yanda ta ga kayan abinci a bedroom ɗin Inna.
Har suka ƙarika gida suna labarin Inna Umma ba ta ɗakin sai Auta da ke games a wayar Umma.
Manaheer ta ce.
"Ina Umma.?"
Auta.
"Ta na cikin gida."
Zama su ka yi su na cicgaba da fira har zuwa lokacin da a ka kira magrib lokacin Umma ta shigo, su ka yi sallah suka zauna karatu har zuwa isha'i.
Manaheer ta miƙawa Umma flas ɗin da Inna ta zuba musu abinci, Umma ta yi mamakin jin cewa Inna ce ta basu abincin, amman ba ta nu na musu ba ta ce.
"Auta ɗauko plate."
Bayan Auta ya kawo plate ɗin Umma ta juye abincin ta aje musu.
Bayan sun gama cin abinci Manaheer ta fara hamma Auta ya ce.
"Da alama yau ba fira."
Manaheer.
"Ba wannan maganar."
Da ga haka ta yi alwala ta shige Daraini ma haka, Umma ta shigo ta ce.
"Gobe idan Allah ya kai mu za kuje gidan Rabi'a."
Daraini ta ce.
"To."
Da ga haka Umma ta fita Auta ya na kallo Umma ta na karatu zuwa 10 Umma ta amshi wayar, su ka yi alwala Auta ya kwanta Umma ta hau darduma ta yi nafila ta kwanta.
Asuba ta gari.
Ɗakin da Umma ta sauka daman na ta ne akwai komai da komai na buƙata aciki, daman ƙanin mahaifinta ya tsara hakan idan ta zo garin sai ta sauka a nan.
Bari mu leƙa gidan Abba mu dawo.
Ta Batulu ce ✍️
Like and share sannan kuyi comments 🥰
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Allahumma Sali Ala Sayyadina Muhammad Wassalim 🥰
Happy maulud masoya manzon Allah s.a.w ubangiji ka biya mana dukkanin buƙatun mu saboda manzon Allah s.a.w.
Page 73~74
Gidan Abba tun bayan tafiyar Umma Mama ta ƙara miƙe ƙafa zuwa gurin boka ya ƙaru ita babban burin ta Umma kar ta dawo, yawo gidan boka har da Amina kuma duk gurin da su kaje ba su dace ba.
A ƙarshe dai talatu ta yiwa Mama hanyar wani boka a garin Zaria, ko da su kaje gurin shi ya faɗa musu raba Umma da gidan Abba abu ne mai matuƙar wahala, amman zai yi musu aiki a kan Abba wanda hankalinsa zai ɗauke da ga kan Umma da ƴaƴanta.
Amina kuma ya ba ta maganin farin jini Mama ta ce.
"Dan Allah."
Boka ya daka mata tsawa ya ce.
"Da kin san Allah babu abin da zai kawo ki gurin mu asararriya."
Talatu jiki na rawa ta ce.
"Ka ya haƙuri asararre ɗan asararriya."
Boka ya kwashe da dariya har sai da ɗakin ya amsa ya ce.
"Tambaɗaɗdu asararru."
Talatu ta ce.
"Godiya muke."
Mama ta ce.
"Sai maganar yaran da za su yi aure."
Boka.
"Mijin za a kashe ko kuma a haukata shi?."
Wa'iyyazubillahi babu wani mai ka shewa sai Allah ubangiji ka tsare mana imanin mu.
Mama.
"Aa kawai a fasa auren su yi baƙin jini su rasa masoya."
Boka ya yi ƴan dube duben shi ya ce.
"Wannan aikin ya na da wahala kuma za a kashe kuɗi da yawa."
Mama.
"Ko nawa ne zan biya."
Boka.
"Ki bari sai sun dawo garin aikin zaifi tafiya daidai."
Da ga nan boka ya yi surutai ledoji uku su ka faɗo ya miƙawa Mama guda biyu ya ce.
" Wannan ki zuba mishi a cikin abinci, ɗayan kuma ki barbaɗa a gurin zaman shi."
Mama ta amsa boka ya ce.
"Za ki mallake shi sai yanda kika yi da shi, amman fa akwai babbar matsala."
Mama.
"Wani irin matsala ne.?"
Boka.
"Karki barshi ya sha koda ruwa ne a ɗakin matar shi, domin in dai kika bari hakan ta faru komai zai warware."
Mama.
"Zan kiyaye."
Boka ya miƙawa Amina ɗayan maganin ya ce.
"Ki zuba shi a cikin man shafawa ki dinga amfani da shi."
Amina ta karɓa ta yi godiya talatu ta amshi maganin kasuwa da zasu fita boka ya ce.
"Ku fita da tsalle kar ku taka mun yara su na wasa."
Da tsalle suka fita kamar wasu kwaɗi 😂😂
Mota suka hau zuwa Jos su na tafe suna fira fuskar Mama cike da annuri.
An gama gyara ɗakin Umma yanzu ɗakin Mama ake gyarawa Mimah da Mama da Amina su na gidan talatu, Mimah yawo sai abin da ya ci gaba.
Idan Mama na yi mata faɗa talatu cewa ta ke yi.
"Barta ta yi lokacin ta ne."
Mama ta bawa Abba shawaran ya bari idan aka gama gyaran gidan gaba ɗaya sai su koma har da Umma.
Babban burin Mama Umma ta bar gidan da zama kuma duk in da taje babu rabuwa ake gaya mata, amman har yanzu ta ƙi haƙura.
Mimah na zaune a tsakar gida ta na charts ƙawarta ta yi sallama ta shigo, Mimah ta ce.
"Sofy daga ina.?"
Wanda a ka kira da Sofy ta ya mutsa fuska ta ce.
"Da ga gida."
Daga nan suka fara fira wayar Mimah ta yi ringing ta ɗaga bayan ta gama magana ta yanke wayar.
Mimah ta ce.
"Sofy dan Allah zo ki ta yani girki."
Sofy.
"Wa za ki yiwa girki?."
Mimah.
"Mama ta kira ni yanzu ta ce in ɗaura musu girki, please Sofy."
Sofy ta aje hijjab ɗin ta suka fara girki su na yi su na firan saurayin Mimah, Ɗan shila wanda suka haɗu da shi a gurin partyn ƙawarsu, tun da ya ɗaura idon shi a kan Mimah ya kamu da ƙaunarta.
Tun daga ranar suka fara soyayya da farko Ɗan shila yaso lalata, Mimah amman taƙi yarda, babu irin kuɗin da baya kashe mata amman Mimah ta ce.
"Ya bari su yi aure."
Ko da ya ce mata zai turo iyayenshi gidan su Mimah cewa ta yi.
"Ba yanzu ba."
A haka dai suke tare da ita duk da cewa ta sakar mishi jikinta ya na yin komai da ita, amman ta ce.
"Ba ta yarda da zina ba."
Ɗan shila ya yi ya yi Mimah ta amince da shi amman taƙi amincewa, abin da Mimah ba ta sa ni ba Sofy tsohuwar budurwan shi ne.
Sunan shi Yusuf amman friends ɗin shi Ɗan shila suke ce mishi, Sofy na tare da Mimah ne domin cimma wani ƙudiri na ta.
Mimah ba ta iya girki ba dan haka ta sakar wa Sofy aikin ta ɗau wayarta, babu jimawa Sofy ta gama aikin ta yi wanka Mimah ta sanja kaya, daman da kayanta a cikin jaka ta zo.
Bayan Mimah ta yi wanka ta zubo musu abinci su na fara ci wayar Mimah ta yi ringing, cike da iyayi ta ɗau wayar Ɗan shila ne ya kira ta ya na gaya mata cewar ta shirya zai zo ya ɗauke ta daga haka ya yanke wayar.
Mimah ta kalli Sofy ta ce.
"Wallahi beb ya cika rigima."
Sofy ta yi murmushi ta ce.
"Mai yafaru?."
Mimah.
"Wai in shirya zai zo bada jimawa ba."
Sofy.
"To mene ne a ciki ai hakan ma shine dai dai."
Mimah.
"Ba za ki gane ba Sofy wallahi beb ya cika rigima da yawa, kullum idan muka haɗu da ƙyar yake ƙyaleni."
Sofy.
"Dan Allah ki waye mana yanzu an dai na ya yin wannan abin da kike, sai ka ce wata ƴar ƙauye."
Mimah.
"Ni fa ba zan iya wannan ƙazamin rayuwar ba."
Sofy.
"Ni ma ba na ce ki yi bane amman shawara na ba ki."
Mimah ta yi shiru ta na kallon Sofy.
"Na ga ya na sonki sosai kuma aurenki zai yi, to mene ne abin damuwa dan Allah." Inji Soft.
Mimah.
"Kinga mu bar wannan maganar yanzu dai bari in je in shirya kafin ya ƙariso."
Mimah ta shiga ɗaki Sofy ta harare ta ta na jan tsaki.
Comments and share
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Allahumma Sali Ala Sayyadina Muhammad Wassalim 🥰
Page 75~76
Mimah ta fito sanye da riga da wando rigar ya matseta sosai cibi a buɗe, wandon kuma tree kwater.
Sofy ta ce.
"Kina wuta muna binki da petur."
Mimah ta yi dariya za ta ɗaura after dress a saman kayan Sofy ta ce.
"Haba dan Allah wannan ai ƙauyanci ne."
Mimah.
"Kin san dai ko giya na sha ba zan iya fita a haka ba."
Sofy.
"Ki sa dogon hijjab har ƙasa."
Mimah ta yi shiru Sofy ta dafa kafaɗarta ta ce.
"Wai dan Allah yaushe za ki dai na abu irin na ƙauyawa."
Mimah.
"Ba za ki ganeba."
Wayar Mimah ta yi ringing ta kalli Sofy ta ce.
"Har ya ƙara so."
Sofy cikin dubara ta karɓe after dress ɗin hannunta, Mimah ta sa hijjab suka fita bayan ta kulle gidan, ta miƙawa mai shagon ƙofar gida makullin ta ce.
"Dan Allah ka aje wa Inna talatu."
Mimah ta nufi gurin wata mota ash colour ta buɗe gaban motar ta shiga, ta na shiga matashin da ke gaban motar ya rungumeta, chocolate colour ya na da jiki ba laifi kuma ya na da tsawo,
Mimah ta ce.
"Ka bari mana."
Ɗan shila.
"Haba mana beb kin san na yi kewarki da yawa."
Mimah.
"Ba ni kaɗai ba ce dan Allah ka dai na."
Sofy ta buɗe gidan baya ta zauna suka gaisa da Ɗan shila daga nan ya kunna motar suka tafi, haɗaɗɗen hotel ya kai su bayan ya yi parking.
Suka fito gurin cin abinci suka nufa Sofy ta ce.
"Ni dai gida zan wuce."
Mimah.
"Yau ba za ki ci kazar bane.?"
Sofy.
"A siya mun in tafi dashi."
Suka zauna a kujera Mimah ta kalli Ɗan shila ta ce.
"Besty za ta wuce gida."
Ɗan shila.
"Ok bari inje in karɓo mata abin da tafi buƙata."
Bayan ya tafi Sofy ta ce.
"Gayen nan ya na sonki da yawa."
Mimah.
"Kamar yanda na ke son shi."
Sofy.
"Dan Allah Besty ki daina wahalar da gayen nan, karfa ya ce ya fasa."
Mimah.
"Kina nufin in bashi kaina.?"
Sofy.
"To idan kin yi hakan mene ne a ciki, ai duk cikin soyayya ne."
Mimah.
"Gaskiya ba zan iya ba."
Daga haka babu wanda ya ƙara magana a cikin su, Ɗan shila ya ƙariko hannunsa ɗauke da babban leda, ya miƙawa Sofy daga nan suka yi sallama da Mimah.
Bayan Sofy ta tafi ɗan shila ya kama hannun Mimah suka nufi ɗakin da ya kama.
Tabbas Mimah sakacin iyaye ya jefata a wannan halin, domin da ace Abba ya tsare musu ci da sha da kuma tufatarwa baza ta tsinci kanta a wannan rayuwar ba, sannan kuma Mimah bata jin magana, sannan duk iskancin da ta ke yi ba ta yarda ya kusance ta ba.
Abba sau biyu yake bada abinci a cikin gidan shi wani lokacin kuma sau ɗaya, suttura kuma daga shekara sai shekara, a wannan rayuwar da muke ciki ka tsare ma ƴaƴanka komai da komai ya aka kaya ballantana ka sakar wa budurwa hidimar kanta, bayan ba ita ta haifi kanta ba sannan kunga Mama ba ta sana'ar komai, dan Allah iyaye mu kula,
Ƴaƴa da dukiya amana aka baku kuma lallai za a tambayi yanda kuka tafiyar da amanar da aka baku,
Cikin halayen Abba da na rubuta wallahi akwai masu irin halin, wani ma kwatakwata baya bayar da abinci a cikin gidan shi wannan halin Abba da na rubuta dagaske ne wallahi na so in rubuta ai nihin labarin amman wani dalili nawa yasa na sanja da har na fara rubutawa sai kuma na sanja shawara, shiyasa na zaɓi in rubuta halayen Abba kawai, ɗan shila ya na yiwa Mimah hidima sannan ya na fanshewa a jikin ta.
Allah ka haɗamu da iyaye nagari. 🤲
Ɗan shila bai mayar da Mimah gida ba sai 6 saura na yamma, kafin ya ajeta sai da ya yi mata shopping, sannan ya kai ta har ƙofar gida.
Mimah ta jima acikin motar kafin ta fito duk da hakan Ɗan shila bai barta ba domin har zaure ya rakata hannun shi ɗauke da ledojin da ya yi mata siyayya.
Kamar ba zasu rabu ba domin sai da suka jima a zauren sannan ya fito ya shiga mota, Mimah ta shiga gida hannunta ɗauke da ledoji, babu kowa a tsakar gidan ɗakin da suke zaune da Mama ta shiga.
Daman gidan ɗaki biyu ne ciki da parlour toilet ya na waje kitchen ma ya na tsakar gida.
Mimah ta yi sallama Anty Amina ce kawai a ɗakin Mama ta na gurin Abba, tunda tsakanin su babu nisa.
Aunty Amina.
"Sai yanzu ki ka ga damar dawowa daga yawon na ki."
Mimah ta tura baki ta ce.
"Aunty Amina rayuwar nan kowa tashi ta fisheshi a ke yi."
Aunty Amina.
"Rashin kunya za ki yi mun daga faɗa miki gaskiya."
Mimah.
"Aunty Amina daman kin san gaskiya.?"
Amina ranta ya ɓaci ta tashi ta fita Mimah ta ce.
"Wai har ta na da bakin gayawa mutane gaskiya."
Bayan wani lokacin Mama ta gama aikin da boka ya sata kuma ta yi nasara, duk da cewa wani lokacin Abba yana mata gardama, amman ta kama shi a hannunta.
An gama gyaran gidan har sun koma gida ya yi kyau, dukka ɗakunan two bedroom ya mayar kowani ɗaki da toilet a ciki, kuma kowace anyi mata kitchen ajikin ɗakinta, Abba gate ya sa yanzu gida harda pampo, ko ina ya sha tayis.
Amina ta samu wani saurayi har sun gama daidai tawa.
Umma bata san wainar da ake soyawa ba Manaheer yanzu haka ta zama ƴar lele a gurin Inna, saboda kullum sai sun je gidan sun yi mata aiki, kuma idan zasu tafi Manaheer da abincin da za su dafa take zuwa.
Abin da Inna bata sa ni ba duk kayan abincin da Manaheer take zuwa dashi a ɗakinta take ɗiba idan za su tafi gida, Inna akwai ta da rowa ga san banza da ya yi mata yawa, kuma sai gashi ta haɗu da Manaheer.🤣
Fan's Aunty Barrister ta ce mun Ta Batulu.
"Banda dogon typing 😂😂😂🏃
Ta Batulu ce ✍️
Comments and share
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Allahumma Sali Ala Sayyadina Muhammad Wassalim 🥰
Page 77~78
Umma satin su uku a Saminaka Abba ko plsh bai mata ba,
Aunty Fatima ta na can ta na yiwa Shukrah gyaran jiki.
Manaheer Daraini sun je dangin Umma na kusa da na nesa, Umma bata zauna haka ba ta na yin sana'ar turare kamar yanda ta saba, sai ya zamana ta fi samun customer a nan garin.
Kayan abinci duk ƙarshen wata Umar ya na aje musu ba su da matsalar komai.
Uncle Nasser ya kira Abba a waya ya tambayeshi har yanzu bai gama gyaran gidan ba.
Abba ya ce.
"Akwai ɗan gyare gyaren da nake shiyasa ban ce su dawo ba."
Uncle Nasser.
"Aisha ta na ina.?"
Abba.
"Ta dawo tun tini."
Uncle Nasser ya ce.
"In sha Allah nan da sati ɗaya zan sa su a mota, na san zuwa lokacin an gama komai."
Abba.
" Allah ya kai mu."
Daga haka suka yi sallama kwana biyu da yin wayarsu yaje ya samu Umma ya gaya mata yanda suka yi da Abba.
Umma ta yi murmushi domin ta na da labarin komawar Mama a bakin wata customern ta da taje gidan amsar turare, Umma ta zuba mishi ido ne ta ga iya gudun ruwanshi.
Umma ta ce.
"Sai na gama ziyarar dangina sannan zan ta fi."
Uncle Nasser ya daɗa bata haƙuri sannan ya tafi kwana ɗaya tsakani Umma ta kira wayar Abba, lokacin suna tare da Mama bayan sun gaisa daga nan ta nemi izinin zuwa gurin danginta domin tun da tazo garin ba taje ko ina ba.
Abba.
"Allah ya kiyaye hanya." daga haka ya yanke wayarshi.
Kwana biyu dayin wayarsu ta shirya ta ta fi ziyara dangin mahaifinta ƴan buta kafin a shiga Saminaka garin yake, suna da nisa sosai tsakanin Saminaka da garinManaheer Daraini a gida ta barsu daga ita sai Auta suka tafi.
Kwanan Umma uku ta dawo gida ƴan uwan mahaifinta sun ji daɗin ziyarar da ta kawo musu, dan haka suka haɗa mata shatara na arziki.
Dawowar Umma da kwana biyu ta ta fi kaduna dangin mahaifiyarta sun yi murna sosai, yayar mahaifiyarta da suke uba ɗaya Hajiya Fatima har kuka sai da ta yi.
A gidan Hajiya Fatima ta sauka mijinta hamshaƙin ɗan kasuwa ne ya jima da rasuwa ƴaƴanta biyu maza Yahaya Ibrahim, duk sun yi aure suna zaune a gidan part uku ne ɗaya na Hajiya Fatima sauran na yara.
Sun raba dare suna fira daga nan ta tambayeta dalilin da yasa bata zo da yaran duka ba domin da Auta kawai ta tafi, Umma ta ce.
"In sha Allah suna nan zuwa."
Umma da zata dawo Hajiya Fatima ta sai mata kayan ɗaki kayan kitchen kamar na budurwa, Umma har kuka sai da ta yi ranar da zasu dawo Hajiya Fatima ta amshi address ɗin Umma da number wayarta ta ce.
"Nan da kwana biyu company za suje su kai miki kayanki har gida."
Umma da zata dawo yaran Hajiya 50k suka bata Auta kuma harda sababbin kaya masu kyau Hajiya Fatima ta siya mishi.
Kwanan Umma biyar da dawowa ta kwashi yaran duka suka tafi gidan Isma'eel daga nan su kaje gidan Rabi'a, har yamma suna gidan da ya Umar ya dawo ya kai su gida ya yi musu sallama domin nan da kwana uku zasu wuce.
Washe gari Umma taje gidan Aunty Fatima gidanta masha Allah ga ƴan aiki tako ina, bayan sun gaisa Aunty Fatima ta kira Shukrah.
Umma ta yi mamakin yanda ta ga Shukrah gaba ɗaya ta sauya, sun jima suna fira da Aunty Fatima bayan la'asar suka tafi Aunty Fatima ta saiwa Daraini babbar waya irin ta Manaheer, Shukrah kuma sababbin kaya ta ɗinka mata akwati ɗaya mijinta kuma ya bata 50k.
A daren suka haɗa kayansu Umma ta kira Hajiya Fatima wanda take cewa Mama, bayan sun gai sa ta sanar da ita jibi idan Allah ya kai mu zata wuce gida, sun jima suna fira kafin ta bawa yaran suka gaisa.
Bayan sun gama magana Hajiya Fatima ta kira company ta ce.
"Zuwa gobe idan Allah ya kaimu su kai kayan kuma dan Allah su shirya ɗakin yanda zai yi kyau." Ta tura musu da address ɗin.
Da safe bayan sun gama duk ayyukan gida suka ta fi gidan Inna harda Shukrah da Umma, Inna ta na zaune a tsakar gida ta na jin redio ta amsa sallamar su ta na hararan Manaheer.
Bayan sun gaisa Umma ta yi mata sallama Inna ta ce.
"Har kun gaji da zaman kenan.?"
Umma bata ce komai ba Inna.
"In banda rashin wayyau irin naki mai zai sa ki kwaso ƙafa kizo ki zauna har tsawon wannan lokacin."
Manaheer.
"Gyaran gidan a ke yi shiyasa muka zo ziyarar dangi."
Inna.
"To kunyi ƙoƙari." Masu ziyarar dangi.
Inna ta kalli Shukrah ta ce.
"Ita kuma wannan koɗaɗiyar sai yanzu ta ga damar zuwa."
Manaheer.
"Faɗi gaskiya dai ko dai kinga ta fi ki kyau ne kika cemata koɗaɗiyya."
Inna.
"Allah ya tsareni itama wannan hasken da ta yi mai ne."
Umma ganin firan baya ƙarewa ta ce.
"Inna bari inje in cigaba da haɗa mana kayan mu."
Inna.
"Uhmmmm."
Bayan fitan Umma Manaheer ta ce.
"Hajiya Inna yau mai za a dafa.?"
Inna.
"Ai kayan abincin sun ƙare."
Manaheer ta sa hijjab ta ce.
"Bari inje gurin uncle Isma'eel in karɓo."
Bata jira cewar Inna ba ta yi waje Darraini na ta ƙunshe dariya Shukrah na zaune ta na dana waya, 20 minutes Manaheer ta shigo da manyan ledoji guda biyu ta kalli Daraini ta ce.
"Bismillah."
Daraini ta matsa Manaheer ta buɗe ledar biscuits ne manya manya a ciki da drinks ɗayar ledar kuma ta ce.
"Wannan kuma tsaraba ne uncle Isma'eel ya bamu."
Inna.
"Tun da kika zo garin nan kike karya ma yaron nan jari."
Manaheer.
"Idan bai yi mana ba wazai yiwa babu ɗa babu jika."
Inna ta fashe da kuka ta ce.
"Yanzu Manaheer a gaba na kike zagin Isma'eel, kina nufin baya haihuwa.?"
Manaheer ta miƙawa kowa drink ɗin da biscuits ɗin ta yi banza da Inna.
Sai da suka yi sallar azahar sannan Manaheer ta ce.
"Inna zamu wuce."
Inna.
"Allah ya kiyaye hanya."
Manaheer.
"Daman zan gaya miki wata magana."
Inna.
"Ni fa bani da abin da zan baku."
Manaheer ta yi dariya ta ce.
"Kayan abincin da nake zuwa dashi ina dafawa, kina tunanin daga waje nake zuwa dashi to a nan nake ɗiba nake dafa mana muna ci tare dake."
Shukrah da ta gaji da tsayuwa ta yi waje Daraini ma haka Inna ta fashe da kuka ta ce.
"Shiyasa tun farko jinina bai haɗu dana Amina ba ashe ba haka kawai ba, sai kuma mene kika aikata bayan wannan.?"
Manaheer.
"Yanzu dai ki kawo mun tsaraba in tafi."
Inna ta na kuka ta ce.
"Bari in ɗauko miki."
Manaheer na ganin ta miƙe ta yi waje da gudu ta na dariya.
Inna ta yi ƙwafa ta ce.
"Da kin sa ni ki bari in ta shi kika ga yanda zan yi dake."
Washe gari suka tafi gidan uncle Nasser Aunty Maryam ta yi murna da ganin Umma Khadija kuma ta janye su Manaheer ɗakinta, Umma har zuwa dare tana gidan sai da uncle Nasser ya dawo suka yi sallama ya basu 20k Aunty Maryam kuma 10k da zasu tafi Khadija harda kuka.
Da safe Umma ta yi sallama da muta nan gida ƙanin mahaifinta ya bata wani babban gora ya ce.
"Wannan maganin tsari ne kusha keda yara."
Bayan la'asar Umar ya kai su tasha drop ya biya musu har ƙofar gida saboda yawan kayansu, har da kayan abinci ya siya musu Umar sai da yaga tashin su sannan ya koma kasuwa.
Mama washe garin ranar da Abba ya yi waya da uncle Nasser ta tafi Zaria.
Mama zaune a gaban boka ta na kora mishi jawabi.
Boka.
"Gaya mun abin da kike so."
Mama.
"Ba na son ta dawo gidan gaba ɗaya."
Boka.
"Dole zata dawo."
Mama.
"Ina son su yi baƙin jini a idanun mai gidan daga ita har ƴaƴanta."
Boka.
"Ko da mun yi aiki ya kamata ba zai daɗe ba."
Mama.
"To mai yasa hakan.?"
Boka.
"Ta na da yawan ibada daga ita har ƴaƴanta."
Mama.
"Ka taimaka mun."
Boka.
"Taɓa matar nan abu ne mai wahala."
Mama.
"Ina son Manaheer a samata rashin jin magana da yawace yawace idan ta kama ta daina kwana a gida, sannan kuma wanda yake zuwa gurinta a kora shi."
Boka.
"Zanyi iyakar iyawata."
"Ungo wannan maganin ki barbaɗa a in da zata zauna ko kuma ki zuba a in da kika san zata taka." Cewar boka yana miƙawa Mama baƙin leda.
Boka ya ƙara miƙa mata wani ledar ya ce.
" Ki barbaɗa a ƙofar gida lokacin da kika tabbatar da cewar zasu shigo gidan."
Mama ta yi godiya har ta miƙe zata tafi boka ya ce.
"Akwai matsala."
Like and comment sannan ku yi share
Nayi kewarku ƴan amanata😘
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Allahumma Sali Ala Sayyadina Muhammad Wassalim 🥰
Page 79~80
Boka.
"Babbar matsalar shine maganin bai da makari."
Mama ta washe baki ta ce.
"Ba damuwa."
Boka.
"Ki kula da kyau domin wannan maganin ya na da matuƙar haɗari."
Mama.
"Zan kiyaye."
Boka.
"Idan kin koma ki yiwa yarinyar ki aure tun ba ta jawo miki magana ba."
Daga haka bai ƙara magana ba Mama hankali tashe ta fita ta kamo hanyar Jos tsakanin Jos da Zaria tafiyar 4 hours.
Kwana biyu da dawowar Mama daga Zaria ta hana Mimah fita ko ina Abba ya yi faɗan har ya gaji amman Mama ta toshe kunnenta, Amina ta kawo saurayinta sun gai sa da Abba ya yi mishi tambayoyi ya ce.
"Idan da gaske kake sonta ina son ka turo mun iyayenka, domin ba na buƙatar yawan fira."
Amina ta ga yawa saurayin ita bazawara ce mijinta ya rasu ne kuma ba ta taɓa haihuwa ba.
A ranar da Umma za su dawo Abba ya kira ƴan uwanshi dukkansu ya faɗa musu maganar auren Amina, uncle Nasser ya ce.
"Ka turo mun da address ɗin shi."
Abba ya tambayi Amina address ɗin Isa ta tura mishi da shi ya turawa uncle Nasser.
Lokacin da company suka je kai kayan da Hajiya Fatima ta siyawa Umma, Abba ya na gida suka yi sallama da shi bayan ya fito suka gai sa daga nan suka faɗa mishi abin da ya kawosu kamar yan da Hajiya Fatima ta faɗa musu.
Abba ya kalli kayan baki sake yana mamakin a in da Umma ta samo kayan company, haka ya shanye mamakin shi ya yi musu jagora zuwa cikin gidan ya buɗe musu ɗakin ya fita.
Mama ta na bacci lokacin suka shirya ɗakin tsaf harda labulaye da ƙaramin dining table mai kujeru biyar, komai sun aje shi a in da ya da ce kujerun maroon da ratsin baƙi labulayen ma haka carpet ɗin shima maroon ne da ratsin baƙi.
Bayan sun gama shirya ɗakin suka shirya kitchen kamar yan da Hajiya ta faɗa musu, bayan sun gama komai suka rufe suka bawa Abba makullin suka tafi.
Abba ya buɗe ɗakin yana kallo abin sai da ya bashi tsoro ganin irin dukiyar da a ka narka a ɗakin, kuma iya sanin da ya yi wa Umma bai taɓa sanin su na da masu kuɗi a familyn su ba.😂
Ya yi ta kiran wayar Umma taƙi shiga haka nan ya rufe ɗakin ko Mama bai faɗawa ba ya ta fi kasuwa.
An kai kayan yau washe gari Umma ta taso.
Tafiyar rabin awa suka ƙarika har ƙofar gida driver ya kai su kamar yan da suka yi da shi.
Shukrah ta na ta kallon gidan Umma ta kalli driver ta ce.
"Dan Allah ɗan tsaya in duba."
Umma ta fi ta ta na kallon gate ɗin gidan Manaheer ta shige gidan da sauri bayan ta buɗe ƙaramin ƙofar shiga gidan.
Amina ta fara gani a bakin ƙofar ɗakin Mama ta na waya.
Manaheer ta fita har lokacin drive na tsaye Daraini ta ce.
"Munyi ɓatan kai."
Manaheer ta fara sauke kayan su ta na cewa Umma.
"Nan ne gidan ba makuwa mu ka yi ba."
Drive ya taimaka musu suka kwashe kayan su zuwa tsakar gidan da babu kowa, har bakin ƙofa ya kai musu sannan ya ta fi Manaheer ta nufi ɗakin Abba lokacin su na zaune da Mama su na fira.
Manaheer ta yi sallama ta shigo gaban Mama daman "Yau zasu dawo." Cewar Mama a cikin zuciyarta.
Manaheer ta duƙa ta gaishe da Abba sannan ta gaishe da Mama.
Abba ya miƙa mata makullin ɗakin ta fi ta Mama tabi ta a baya.
Manaheer ta buɗe ɗakin Umma ta fara shiga Shukrah na bayanta.
Umma ta tsaya cak ta na bin ɗakin da kallo Shukrah ma haka Daraini ta shigo janye da kayansu a cikin akwati, ita ma ta ƙame ta na kallon ikon Allah Manaheer ta shigo da Auta.
Manaheer ta dinga bin ɗakin da kallo idonta ne ya sauka a gurin wani babban picture dake manne a bangon ɗakin.
Ta ƙarika gurin picture ɗin ta ciro Umma da Auta sai wata Hajiyar Allah sun sata a tsakiya su na dariya.
Manaheer ta ƙara shiga ruɗu yaushe a ka yi wannan picture ɗin.
Daraini ta matso ita ma ta gani Manaheer ta kalli Auta ta ce.
"Auta zoka faɗa mana wacece wannan."
Auta ya karɓi picture ɗin ya miƙawa Umma dai-dai lokacin Abba ya shigo.
Umma ta shafa picture ɗin hawaye na bin fuskanta ta kalli yaran ta ce.
"Yayar mahaifiyata Hajiya Fatima."
Abba ya yi ajiyar zuciya ya fita Umma ta kalli yaran ta ce.
"Bari mu yi sallah mu wuta, sai in baku labarinta."
Bayan sun shirya kayansu kayan abincin suka aje a kitchen suka yi sallah suka yi wanka Manaheer ta fito da biscuits ɗin da uncle Isma'eel ya basu da drinks.
Bayan sun gama ci Shukrah Darraini Auta suka je gaishe da Abba da Mama.
Bayan sun gai sa da Abba suka shiga ɗakin Mama, su na zaune ita da Amina da Mimah babu wanda ya amsa sallamar Shukrah ta gaishe su, bata jira jin amsar su ba ta fi ta Daraini ma haka Auta yabi bayansu.
Bayan fitan su Mama ta kalli Amina ta ce.
"Ki na ganin abin da idona ke gani.?"
Amina.
"Gyaran jiki a ka yi mata na amare."
Mama.
"Ki na ganin yarinya ta buɗe ki ce mun gyaran jiki a ka yi mata."
Amina.
"Ni ban ma lura ba."
Mama cike da takaici ta ta shi ta fi ta, bayan komawarsu ɗaki Umma ta fi ta ɗakin Abba ta shiga.
Bayan sun gai sa take ba shi labarin Hajiya Fatima da yan da suke da ita Abba ya na ta kau da kai, bayan ta gama faɗa mishi ta miƙe Abba ya ce.
"Mun tsai da lokacin bikin Shukrah nan da sati uku."
Umma.
"Allah ya kai mu lokacin ai kamar yanzu ne."
Mama ta yi saurin barin jikin window ɗakin Umma ta zauna a parlour suka sata a tsakiya, daga nan ta basu labarin Hajiya Fatima da yanda take a gurinta.
Da daddare Mama ba ta basu abinci ba tae suka sha suka zauna zaman fira, Manaheer ta sa ci jiki ta fita ɗakin Abba ta shiga bayan ta yi sallama.
Abba ya na cin abinci Mama na gefenshi Manaheer ta gaishe su ta kalli Abba ta marairace fuska ta ce.......
Likes and share sannan kuyi comments
Ta Batulu ce ✍️💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Allahumma Sali Ala Sayyadina Muhammad Wassalim 🥰
Page 81~82
"Abba yunwa muke ji."
Abba ya ce.
"In zo in baku abincin a baki ne.?"
Manaheer ta ce.
"Abba ai bamu gama idon abincin ba."
Abba ya kalli Mama ya ce.
"Ba ki basu abinci bane.?"
Mama ta fara kame kame duk da ta kama shi a hannu amman wani lokacin komawa yake asalin Aliyun shi.
Abba ya daka mata tsawa ya ce.
"Ya ina miki magana kina neman samun ciwon kai."
Mama cikin karfin hali ta ce.
"Abincin ne bai kai ba shiyasa."
Manaheer ta fara hawaye ta ce.
"Abba tun karin safe ne a cikin mu."
Abba ya kalli Manaheer fuska cike da mamaki ya ce.
"Da rana bata baku abinci ba.?"
Manaheer ta ce.
"Eh."
Abba ya ta shi ya fi ta kitchen ɗin Mama ya buɗe ya ga wani babban flas cike da abinci, ya ɗauka ya shiga ɗaki Mama na zaune in da ya barta ya miƙawa Manaheer ya koma ya zauna.
Manaheer ta karɓa ta yi godiya ta fita Abba ya ce.
" Da rana abincin da kika ɗiba harda nasu amman saboda haɗama kin dafa kin hana su."
Mama ta ce.
"Alhaji wannan fa abincin da ka basu namu ne ni da su Amina."
Abba ya ce.
"Sai kusha tea ku kwanta."
Mama ta fashe da kuka jikin Abba ya yi sanyi ya dinga rarrashin ta ya na bata haƙuri, Mama ta ɗauke abincin Abba ta fita da shi daman bai ci da yawa ba.
Dalilin da yasa Mama kuka namar da Abba ya kawo babu wanda ta zubawa sai Abba shima bada yawa ba, sauran ta kwashe ta zuba a flas ɗin da Abba yaba Manaheer.
Manaheer ta shiga ɗakinsu ta aje flas ɗin ta kwaso spoon da plate Umma ta ce.
"A ina kika samo wannan.?"
Manaheer ta ce.
"Abba ya ce in kawo."
Daraini ta buɗe flas ɗin ta ce.
"Da alama rago a ka yanka."
Manaheer ta leƙa flas ɗin gaba ɗaya nama ne a saman abincin, ta kwashe da dariya harda hawaye Shukrah ta yi mata kallo mai cike da zargi.
Manaheer ta yi kamar bata ganta ba a plate ta zuba ta ware nata daban, Manaheer duk ta fi su ci.
Rabi shinkafa rabi nama bayan sun gama cin abincin Mama ta yi sallama ta shigo, ganin irin dukiyar da a ka narka sai da numfashinta ya ɗauke na 5 minutes.
Kafin ta ƙirƙiro murmushin ƙarfin hali Mama suka gaisa da Umma ta yi mata ya gajiyar hanya daga nan ta fi ta.
Da suka zo kwanciya Umma ta ce.
"Gobe idan Allah ya kai mu zan kira dilalliya ta sai wancan kayan ɗakin." Tsofaffin kayan ɗakinta.
Shukrah ta ce.
"Eh hakan ma ya yi sai ki ƙara jarin turare."
Manaheer ta ce.
"Aa ki siya mana katifa mu aje a wancan ɗakin da babu komai a ciki."
Umma ta ce.
"Ni ma nayi tinanin haka saboda baƙi."
Daga haka babu wanda ya sake magana a cikin su, duk sun yi bacci amman banda Umma da Manaheer domin kwana suka yi a saman darduma suna ibada.
Da safe Umma bata jira Abba ba daman tazo da kayan abinci ga wanda Umar ya siya musu ga wanda dangin mahaifinta suka haɗa mata doya dankalin turawa dankalin hausa barkono kayan miya da sauran kayan abincin ƙauye.
Manaheer ta soya dankalin turawa da ƙwai suka haɗa tae bayan sun yi breakfast Shukrah ta gyara ɗaki Daraini ta share tsakar gida, Mama bata gyaran gidan kuma bata sa Mimah ta yi.
Sun gaishe da Abba zasu fi ta Manaheer ta ce.
"Abba kuɗin karyawa."
Abba.
"Ai tun da kika dawo na san ba zan taɓa hutawa ba, ɗan kiɓar nan da na yi duk sai ya zube."
Manaheer ta ce.
"Allah ya taimaki Abban mu."
Abba ya ce.
"Yau ban ta shi da ko sisi ba hasali ɗakin ku zan zo na san kun yi abin karyawa."
Manaheer ta ce.
"Raguwar abincin jiya muka ci."
Abba ya ce.
"Idan na fi ta na karya a waje."
Umma ta shigo ɗakin suka gaisa da zai ta fi kasuwa ya miƙawa Umma makullin ɗakin, Umma ta ce.
"Kuɗin cefane."
Abba ya ce.
"Gaskiya ban da kuɗi ki ara mun zan bayar."
Umma ta ce.
"Ni ma banda kuɗi."
Abba ya ce.
"Ita ƴar uwan mahaifiyar na ki bata ba ki ko sisi ba.?"
Umma ta ce.
"Eh."
Abba ya ce.
"To ki ɗanyi dubarbaru na mata mana a samu abin da za a ci a gidan."
Mama ta yi sallama ta shigo ta miƙawa Abba kuɗi ta ce.
"Na ji ka na cewa baka da kuɗi ga wannan ko za ayi cefane."
Abba ya washe baki ya ce.
"Ƴar aljanna."
Ya amsa ya ƙirga 10k ne ya miƙawa Umma 3k ya fi ta.
Mama ta kalli Umma ta yi dariya ta fi ta bayan 1 week da faruwar haka Abba ya tara su ya ce.
" Mai son Manaheer ya same ni a kasuwa ya bani haƙuri, mahaifiyar shi ta yi mishi mata."
Mama rai fes sannan Abba ya ce.
"Uncle Nasser ya ce shi ne uban yarinya, zai yiwa Shukrah kayan ɗaki."
Mama ta ce.
"Haba Alhaji ai hidimar sai ya yi yawa."
Abba ya ce.
"Ni ma haka na ce mishi har ya nu na mun ɓacin ranshi."
Daga haka taron ya watse daman da safe ne Mama ta shiga ɗaki ta ɗauko maganin da boka ya ce, ta zuba a in da su Umma za su wuce.
Mama ta zuba a bakin ƙofar ɗakin Umma lokacin Manaheer za ta fito, ganin haka sai ta koma ɗaki ta kulle ƙofar ta ciki.
Umma ta na bedroom ɗin yara suna waya da Hajiya Fatima, Shukrah Daraini suna zaune a parlour babu wanda ya lura da abin da ta aikata.
Manaheer ta ɗauko zam-zam ta zuba a cup ta yi addu'o'in karya sihiri ta zuba ruwa a cup ɗin ta fi ta.
Ƙofar ta buɗe bakinta ɗauke da addu'a ta yi bismillah ta yayafa ruwan addu'o'in da ta yi gaba ɗaya ƙofar ɗakin sai da ta yayyafa.
Da yamma Abba ya shimfiɗa tabarma a tsakar gidan yaran duk suna zaune Manaheer ta ta shi ta shiga ɗaki, Mama ta faki idon mutane ta zuba maganin a gurin da Manaheer ta ta shi.
Wayar Mimah ta yi ringing ta ta shi ta shige ɗaki 10 minutes Mimah ta fito, saboda tsokana gurin da Manaheer ta ta shi ta nufa za ta zauna.
Mama ta ce.
"Karki kuskura ki zauna mata a guri."
Ko kafin Mama ta rufe baki Mimah ta riga da ta zauna.
Mama ta fara masifa ta na zagin Mimah lokacin Manaheer ta fito ɗauke da plate da fruits a ciki.
Mama ta kalli Manaheer ta ce.
"Allah ya isa tsakanina dake."
Daga haka Mama ta fashe da kuka ta shige ɗaki, Abba ya kalli Manaheer ya ce.
"Mai kika aikata.?"
Manaheer ta ce.
"Ni babu abin da na aikata."
Umma jikin ta ya yi sanyi ta kalli yaran ta ce.
"Ku ta shi mu ta fi ɗaki."
Manaheer ta ajewa Abba fruits ɗin a gabanshi ta ce.
"Abba ga shi na yanka maka."
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Allahumma Sali Ala Sayyadina Muhammad Wassalim 🥰
Page 83~84
Abba ya karɓi plate ɗin ya ce.
"Allah ya yi albarka."
Umma ta riga kowa shiga ɗaki yaran suna shigowa Umma ta ce.
"Manaheer kiji tsoran Allah ki faɗa mun abin da kika aika."
Manaheer ta ce.
"Umma kina ganin lokacin da na ta shi, wallahi ban aikata komai ba."
Shukrah ta ce.
"Umma ina zargin wani abin ta ƙula shine ya koma kan ta."
Daraini ta ce.
"Ni ban ga Manaheer ta ce komai ba hasalima ɗaki ta shiga ɗauko fruits Mimah ta zauna a gurin da ta ta shi, ina tunanin maganar Aunty Shukrah a kwai gaskiya a ciki."
Umma ta yi shiru daga haka suka shige bedroom bayan sun yi alwala suka kwanta, Manaheer na zaune ta na charts Umma ta shigo ta ɗau wayar ta.
Hajiya Fatima ta kira ta gaya mata an tsai da lokacin biki daga nan suka ɗan yi fira ta yanke wayar.
Dangin mahaifinta ta kira ta gaya musu Manaheer ganin hankalin Umma ya ɗauke ta ɗau buta ta fice.
Ɗakin Mama ta nufa har lokacin ta na kuka Anty Amina da Mimah sun na ta rarrashin ta amman taƙi yin shiru.
Mimah ta shige bedroom Anty Amina ta ce.
"Dan Allah ki gaya mun abin da ya faru ko zan iya ba ki shawara."
Mama ta faɗa mata abin da ya faru Amina ta fara salati ganin haka Mama ta fashe da kuka, Amina ta ce.
"Gaskiya akwai matsala."
Mama.
"Gobe idan Allah ya kai mu zan yi samakon zuwa gurin boka."
Manaheer da ke tsaye a gaban window ɗakin Mama sai da ta yi hawaye ashe abin da ta aikata kenan shi ya sa hankalinta ya ta shi.
Manaheer ta shiga ɗaki suka cigaba da fira asuba ta gari Manaheer ta dage da addu'o'i tun daga lokacin ko guri za ta zauna sai ta yi addu'a, ƴan biki sun fara zuwa Khadija ta zo suna ta shirye shirye har lokacin Abba ya ha na Mama fi ta unguwa.
Mama hankalinta ya ta shi gashi Mimah ba ta jin maganarta ga yawace yawace a gari, biki saura sati 1 aka kawo lefe dozing 2 harda zenare a ciki Mama ta ƙara ruɗewa domin duk cikin su babu wanda ya yi tunanin haka.
Hamza mahaifinshi kasuwanci yake yi na gwagwalai da zenare ya jima ya na neman wanda za ta so shi domin Allah bai samu ba sai yanzu, su biyu mahaifinsu ya haifa daga shi sai ƙanwarshi Nadiya.
Ango dubu ɗari biyu ya bayar na gyaran jiki ana saura kwana uku biki Hajiya Fatima ta sauka, Aunty Maryam sun zo tare da Aunty Fatima daga baya Umar ya kawo Rabi'a.
Duk events ɗin da a ka yi da su a ka yi a na gobe ɗaurin aure Umma ta yi walima, a ranar da daddare Hamza ya bawa Shukrah kuɗin kwalliya dubu ɗari.
10:00pm aka ɗaura auren a kan sadaki dubu ɗari biyar Umma anko suka yi ita da ƴaƴanta shadda doguwar riga yasha aiki, sun yi kyau sosai Anty Maryam sai tsokanar Umma ta ke yi.
Umma ta yi ƙoƙari sosai domin ko Abba daya ga kayan da ta yi sai da ya yi faɗa, Mama baƙin ciki kamar ya kasheta Mimah bata gidan tun da aka fara hidimar biki.
Mama hankalinta ya ta shi kawai ƙarfin hali ta ke yi har Inna sai da ta zo.
Da daddare a kazo ɗaukar amarya Shukrah ta sha kuka Umma sai da ta yi hawaye da ƙyar aka rabata da jikin Umma.
Dangin Umma sun yi mata ƙoƙari sosai Hajiya Fatima ta kawo zannuwan gado labulaye flasks masu kyau abubuwan suna da yawa, Umma ta samu alkhairi a gurin ƴan uwa da abokan arziki harda costumer masu siyan turaren wuta.
Gidan Shukrah ya haɗu ma sha Allah gidan na zaman mutum ɗaya ne tree bedroom ne uncle Nasser ya zuba mata kaya masu kyau, duka ɗakunan sai da ya cika mata da kaya, Mama harda ita a ka zo kawo amarya data ga daular da aka zuba sai da ta yi kuka saboda baƙin ciki.
Make-up artist ta zo ta shirya amarya da ƙawayenta Shukrah bata da ƙawaye daga ƙaninta sai Khadija.
Dinner abokan ango suka haɗa bayan an kawo amarya a ka zo da mota a ka kwashe su har da su Inna da Amina Anty Fatima da Rabi'a matar Umar ga Anty Safiyya ita ma ta zo.
Bayan MC ya yi jawabi ya gayyato babban abokin ango ya bayar da ta ƙai taccen tarihin ango, daga nan ya buƙaci babbar ƙawar amarya ta fito.
Manaheer ta fito ta na taku ɗai-ɗai masha Allah kamar ka sace ta ka gudu dogon hancinta irin na Abba fuskanta cike da gashin gira, doguwar riga tasa pink da ratsin fari takalmi fari gyalen ma haka.
Manaheer ba ta yi dogon jawabi ba ta koma ta zauna anko suka yi su uku Daraini Khadija da Manaheer.
Zuwa ƙarfe 11:00pm
A ka ta shi ango ya wuce da amarya gidan sa, abokan ango suka a kwashe iyayen amarya da ƴan uwanta.
Babbar abokin ango ya ɗauki su Manaheer zuwa gida, bayan sun sau ka ya tsai da Manaheer ya ce.
"Dan Allah ko za ki bani number sistern ki."
Manaheer ta ce.
"Dare ya yi yanzu ka dawo gobe idan Allah ya kaimu."
Daga haka ta shige gida kwana biyu da biki Mama ta ta fi Zaria, saurayin Amina ya turo iyayen shi an tsaida sati 2 tun da ba budurwa ba ne kuma har lokacin Inna ba ta koma Saminaka ba.
Mama a gaban boka ta fashe da kuka sai da ta yi mai isarta ta ce.
"Aiki ya ɓaci yanzu haka yarinya na ta bar gida."
Boka ya ce.
"Ba sai da na gargaɗeki a kan haka ba."
Mama ta ce.
"Ka taimaka mun ina cikin wani hali."
Boka ya ce.
"Ni dokata ba na yin aiki in karya."
Da ƙyar boka ya amince zai karya aikin da ya yi amman da sharaɗin sai nan da sati 1 sannan Mama ta ce.
"Duka aikin da ka yi mun babu wanda ya ci."
Boka ya ce.
"Laifin kine wannan."
Mama ta ce.
" Ina zargin Manaheer ke karya mun aiki, ya kama ta na fara kawar da ita kafin in dawo kan mahaifiyarta."
Boka ya ce.
"Wallahi yarinyar nan ta ɓata abu ne mai wahala, amman zan yi miki aiki na ƙarshe a kanta, ko da me take ta ƙama wannan karon ba zata gujewa tarkona ba."
Likes and share
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU💖💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
I'm sorry two days kun jini shiru, banda lafiya ne amman yanzu alhamdulellahi.
Allahumma Sali Ala Sayyadina Muhammad Wassalim 🥰
Page 85~86
Mama ta ce.
"A sama ta ciwon hauka."
Boka ya ce.
"Ba zan sa mata ciwon hauka ba, zan sa mata laluran da za a rasa gane kanshi."
Mama ta ce.
"Eh hakan ma ya yi, suna can suna naiman magani kafin su farga na gama dasu gaba ɗaya."
Boka ya ce.
"Wannan aikin ya sha ban ban da sauran."
Mama ta ce.
"Ko nawa ne zan iya ka shewa, in dai buƙatata za ta biya."
Boka ya ce.
"Za mu siyo baƙin jaki, da baƙin alade sannan."
Mama ta katse shi ta ce.
"A taimaka mun in bada kuɗi a siyo."
Boka ya ce.
"Kuɗin aikin ki dubu ɗari da ashirin."
Mama ta ce.
"Zan yi ƙoƙari in kawo, yanzu ga dubu hamsin."
Boka ya amshi kuɗin ya ce.
"Nan da kwana 7 dai-dai wannan lokacin zan aje miki magani a ɗakinki, idan kika ɗauki maganin ki kwance ki samu ƙwarya ki juye duka maganin a ciki, ki ɗibo ruwan rijiya 4 ki zuba a cikin ƙwaryan."
Daga haka boka ya yi shiru Mama ta na zune ta na sauraron shi.
Boka ya ce.
"ki bawa yarinyar ki ta sha a tsaye."
Mama ta yi godiya za ta tafi boka ya ce.
"Aikin da ki ka yiwa mijinki ya warware gaba ɗaya."
Mama hankali tashe ta ce.
"Boka ka taimaka mun."
Boka ya ce.
"Babu abin da zan iya yi miki a yanzu."
Mama ta hau mota zuwa Jos, abin da ya faru bayan fitan Mama daga gida.
Manaheer ta ɗauko cup cike da ruwan zam-zam, ta miƙawa Umma ta ce.
"Umma yi mun addu'a in sha."
Umma ta ce.
"Ba ki da lafiya ne.?"
Manaheer ta ce.
"Wani abu nake ji yana mun yawo acikin jikina."
Umma ta karɓi cup ɗin ta yi addu'o'i sosai ta miƙawa Manaheer.
Manaheer ta karɓa ta rufe ta aje shi a gurin bedroom ta shiga ɗauko waya, zuwa lokacin duk ƴan biki sun watse.
Bayan shigan Manaheer Abba ya yi sallama ya shigo, ya zauna a gurin da Manaheer ta ta shi.
Umma ta ce.
"Na yi tunanin ka fita."
Abba ya ce.
"Na yi mantuwa ne."
Abba ya aiki Umma ɗakin shi bayan ta fita Auta ya shigo da sallama, ganin Abba a parlour ya ta fi ya zauna kusa da shi, ya kwantar da kai a jikin shi.
Abba ya yi murmushi ya ce.
"Da alama yau abin ya motsa."
Auta ya ƙara kwantar da kan shi a jikin Abba.
Manaheer ta fito Abba ya ce.
"Ɗauko mun ruwa in sha."
Manaheer ta ɗauko wannan cup ɗin ta miƙawa Abba.
Abba ya yi bismillah ya sha dai-dai lokacin Umma ta shigo.
Ta miƙawa Abba jakar da ta ɗauko, Manaheer ta kalli Auta ta ce.
"Ikon Allah."
Abba ya ce.
"Babu ruwanki da shi."
Umma ido ta zuba musu, ta na fatan wannan ya na yin da take ganin Abba ya tabbata.
Abba ya fara zufa ya kalli Umma ya ce.
"Jiri nake gani."
Umma hankali tashe ta ce.
"Baka da lafiya ne.?"
Abba ya ce.
"Lafiya ƙalau na shigo."
Auta ya shige bedroom ɗin su Daraini Manaheer ta bi shi a baya.
Abba ya kalli Umma ya ce.
"Ɗan taimaka mun in kwanta."
Umma ta taimaka mishi ta kai shi bedroom ɗin ta saboda parlour za a iya yin baƙi.
Umma ta na zaune ta na kallon Abba dake ta faman bacci.
Mu koma bayan kaɗan bayan dawowar Umma bada jimawa ba Aunty Fatima ta haiwu na miji Abdulwahab, Umma ba ta samu zuwa suna ba amman ta turo yaran da abin suna.
Sai da aka yi sallahr azahar Abba ya farka ya yi alwala suka ta fi massallaci da Auta.
Lokacin Mama ta dawo Aunty Amina a na ta shirye-shiryen biki, Inna ta yi ta yi Amina ta biyo ta su koma gida amman taƙi.
Abba sai da ya yi kwana biyu ya na fama da ciwon kai, Mama ta sanja salo Mimah ta kan leƙo gida time to time amman ba ta kwana, idan Abba ya yi wa Mama magana sai ta ce.
"A hostel ta ke kwana saboda karatu."
Mama ba ta son a san halin da Mimah ta ke ciki, Umma ta zaunar da Abba ta ba shi shawarwari masu kyau, kuma ya yi na'am da shawaran da ta kawo.
Abba ya fara sauyawa gaba ɗaya yanzu ya na kulawa da su dai-dai gwargwado, saboda ya na da labarin Mimah da irin rayuwar da ta ke yi, shima ya san ya na da laifi sosai amman ya zubawa Mama ido ya ga iya gudun ruwanta.
Biki saura kwana uku Isa ya kawo lefe akwati 4 kaya cike da kaya Amina ji da kai ya ƙaru.
Babban abokin Hamza Abubakar ya nemo number Daraini tun ba ta sauraron shi har ta ba shi damar zuwa gidan su, shine ya dawo da su gida bayan an ta shi daga gurin dinner bikin Shukrah.
Manaheer ta lallaɓa Umma ta basu kuɗin saloon Abba kuma ya bayar da kuɗin lalli.
Manaheer duk ta fiso dogon gashi amman sun fita haske, lallin da a ka zanawa Manaheer ja da baƙi ne ya yi kyau sosai lallin ya zauna a skin ɗinta.
Manaheer ta fito za ta amsa waya ta ji ta yi karo da wani abu saura kaɗan ta faɗi, har ta rufe ido ta ji an riƙota.
Manaheer jin bata faɗi ba yasa ta buɗe idonta, a kan kyakyawar fuskan shi idanunta ya sauka.
Ganin ta buɗe ido ya yi saurin sakin ta ya na mata faɗan tafiya bata kallon gabanta.
Manaheer ta duƙa ta ɗau wayarta da ta faɗi ƙasa ta yi gaba.
Gurin saloon ɗin ta koma ta samu Daraini na jiranta Manaheer ta biya kuɗi suka ta fi.
Tun fitar su zuwa shigar su napep a kan idon shi, har ƙofar gida sai da ya bisu bayan ya tabbatar nan ne gidan su ya ta fi.
Ta Batulu ce ✍️
Like and share
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Allahumma Sali Ala Sayyadina Muhammad Wassalim 🥰
Page 87~88
Bayan sallahr magrib Manaheer ta ɗauko wayarta, ta na duba screen ɗin wayar ta ganta a fashe.
Ta fara tunanin abin da ya faru ɗazun Manaheer ta yi ajiyar zuciya ta mayar da wayar ta aje.
Gabaɗaya screen ɗin wayar ta lalace kuma bata lura ba sai yanzu.
An ɗaura auren Amina da angonta Isa gidanta masha Allah domin ba laifi ya na da rufin asiri, matar shi ɗaya kuma bata taɓa haihuwa ba.
Isa irin mazajen nan ne masu maƙon tsiya gaba ɗaya babu ruwanshi da iyalanshi kasuwanci kawai ya sa a gaba, hatta abinci baya bayarwa a dafa a cikin gidan shi, matar shi Asiya ita ke ciyar da kanta duk da cewa yana da kuɗin kawai dai baya bayarwa ne yana tunanin idan kullum ya na bayar da abinci da kuɗin cefane arzikin shi zai yi ƙasa. 😂😂
Abdulwahab ya turo iyayensa sun nema mishi auren Daraini, uncle Nasser ya ce.
"Su ɗan jira zai neme su, idan ya gama bincike."
Da daddare kamar yanda a ka saba bayan an gama cin abinci yaro ya yi sallama ya miƙawa Abba leda ya ce.
"Ga shi a bawa Manaheer in ji wani a waje."
Abba ya tsaida yaron ya buɗe ledar waya ce Samsung 71 Abba ya ce wa yaron.
"Muje ka nuna mun wanda ya baka."
Bayan fitan su Mama ta kalli Manaheer ta ce.
"Yanzu dai kowa ya san maza basa yiwa budurwa hidima dan Allah."
Manaheer ta ce.
"Ƙwarai kuwa sai dai su gayyace ta zuwa in da suke, ko kuma su kama mata ɗaki su aje ta."
Umma ta dakawa Manaheer tsawa Mama ta fashe da kuka ta ce.
"Manaheer ni kike wa sharri."
Manaheer ta ce.
"Ni fa ba dake nake yi ba, kawai na kawo miki misalin abin da ya ke faruwa ne."
Bayan fitan Abba ya samu saurayin a tsaye jikin motar shi, ya na ganin Abba ya duƙa suka gaisa daga nan Abba ya ce.
"Bawan Allah ko dai ka yi mantuwa ne."
Saurayin ya ce.
"Idan ba damuwa dan Allah zamu iya magana."
Abba ya koma gida ya ɗauko carpet ya shimfiɗa a zaure suka zauna, bayan sun ƙara gaisawa mata shin ya ce.
"Sunana Mujaheed Ibrahim chanji."
Abba ya ce.
"Ba dai alhaji Ibrahim chanji ba, wanda na ke jin sunan shi a gidan television.?"
Mujaheed ya ce.
"Mahaifina ne."
Abba ya ta shi ya shiga ciki ruwa ya ɗauko a fridge ɗin Umma faro ya ɗauko mai sanyi ya haɗo da cup ya fito, Manaheer ta bishi da kallon mamaki Mama ta ce.
"Lallai wannan baƙon ya na da muhimmanci."
Abba ya aje ruwan Mujaheed ya yi godiya, bayan ya sha ruwan ya kalli Abba ya ce.
"Dan Allah ka ba ni auren Manaheer, idan ba ka yi mata miji ba."
Abba ya ce.
"Ban yi mata miji ba, amman ina son ka bani ɗan lokaci zan neme ka."
Mujaheed ya yi godiya ya kawo kuɗi ya bawa Abba da ƙyar ya amsa, bayan Mujaheed ya tafi Abba ya shiga gida.
Ya na shiga Mama ta fara tambayar shi Abba ya miƙawa Manaheer wayar ya ce.
"Jeki sa wayar a charge."
Manaheer ta amsa fuska cike da murmushi Abba ya kalli Umma da Mama ya ce.
"Kun san alhaji Ibrahim chanji.?"
Mama ta ce.
"Ina jin labarin shi a gari."
Umma ta ce.
"Ni dai ban san shiba."
Abba ya ce.
"Shine ya kawo wannan wayar a bawa Manaheer."
Mama ta ce.
"Uhmmmm mutumin da ba a ganin shi kwatakwata, saboda shiɗin ba mazauni ba ne shida iyalanshi."
Abba ya ce.
"To yau gashi a ƙofar gidan Aliyu ya zo neman aure."
Mama ta yi dariya ta ce.
"Ko dai mai gadin shi ne ya yi maka basaja."
Abba ya yi banza da ita Mama ta kwashe da dariya ta shige ɗaki.
Abba ya faɗawa Umma yanda suka yi da Mujaheed, Abba ya ce.
"Dalilin da yasa na ce zan neme shi, zamu yi magana da sauran ina tunanin gwara a haɗa bikin guri ɗaya, Daraini ma saurayin ta a shirye yake gwara ayi lokaci ɗaya a wuce gurin.
Umma ta yi fatan alkhairi Manaheer bayan shigarta ɗaki ta jona charge Auta ya na zaune yana karatu, burin Umma ya fara cika ta mayar da Auta school.
Daraini na kwance a two seater ta na waya Manaheer ta ɗau wayar Umma ta kira Shukrah, ya na fara ringi a ka yanke.
Shukrah ta kira Manaheer ta ɗaga wayar ta ce.
"Allah ya taimaki Aunty amarya."
Shukrah ta yi dariya ta ce.
"Allah ya shirya ki."
Manaheer ta ce.
"Dan Allah kin yi kewata kamar yanda na yi kewarki.?"
Shukrah ta ce.
"Ina zan yi kewarki bayan tun da kuka kawoni baku dawo ba."
Manaheer ta ce.
"Wallahi Umma ta ha na."
Sun jima suna fira a nan Manaheer ta ke ba ta labarin saurayin Daraini Shukrah, ta yi murna sosai kuma ta ji daɗi Auta ya amsa wayar suka gaisa daga nan, suka yi sallama.
Umma ta shigo ɗakin sun ɗan taɓa fira kafin su kwanta, Umma darduma ta shimfiɗa ita da Manaheer suka yi nafila kafin su kwanta.
Washe gari Abba ya tafi Saminaka da rana Mama ta yi girki, bayan ta gama ta shiga ɗaki ta na shiga ta ga baƙin leda a tsakar ɗakinta.
Mama ta ji tsoro amman da ta tuna yau kwana 7 da zuwa gurin boka ta ɗau maganin ta ɓoye.
Bayan ta raba abinci ta miƙawa Umma ta rufe ɗakinta ta fita.
Mama bata dawo gida ba sai da ta samo ruwan rijiya, 4 bayan ta dawo ta haɗa maganin kamar yanda ya ce ta yi, daman ta siyo ƙwarya tun a hanyar ta na dawowa gurin boka.
Mama ta ɗau wayarta ta kira Mimah ta na jin an ɗaga ta fashe da kuka ta yanke wayar, Mimah ta yi ta kiran wayar amman an ƙi ɗagawa, daga baya ma da ta kira wayar a kashe ta ji.
Mimah ta nufo gida hankali a tashe.
Bari mu leƙe in da Mimah ke kwana.
Ta Batulu ce ✍️
Like and share
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Page 89~90
Mimah saurayinta ɗan shila ya kama mata ɗaki, babu irin hidimar da ba ya yi mata amman har yanzu Mimah ta hana shi kanta.
Addu'ar iyaye na da matuƙar tasiri a gurin ƴaƴan su, Abba ya na tsaye da addu'o'i a kan ƴaƴan shi musamman Mimah da ba ta yi sa'ar uwa ba.
Lokacin da Abba ya dawo hayyacin shi ya ga irin rayuwar da Mimah ta ke yi hankalin shi ya ta shi, kuma ya san ya na da laifi a lalacewar rayuwar ta.
Abba ya samu limamin da ke jan sallah a unguwar su ya faɗa mishi abin da yake faruwa, limamin ya yi wa Abba nasiha mai tarin yawa, sannan kuma ya faɗa mishi hakkin ƴaƴa a kan iyayensu, tun daga tasowar su har zuwa gidan auren su.
Abba sai da ya yi hawaye saboda irin sakacin da ya yi.
Tun daga ranar Abba yasa a din ga yiwa Mimah addu'o'i da saukar ƙur'ani, shima kuma ya dage ba dare ba rana sannan ya na yawan bayar da sadaka.
Wannan dalilin yasa ɗan shila bai yi nasara a kan ta ba, ga shi dai ta sakar mishi da jikin ta babu abin da ba sa yi amman ta hana shi kan ta.
Dan Allah iyaye mukula da yiwa ƴaƴan mu addu'o'i,
Mimah ta shigo gida hankali tashe ta na zuwa ta samu Mama zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya, Mimah ganin haka ta juya za ta fita Mama ta ce.
"Wallahi kina ƙara taku ɗaya ban yafe miki ba."
Mimah ta tsaya cak Mama ta fashe da kuka, Mimah ta saki baki tana kallon ta domin ita ba ta ga abin kuka ba.
Mama kuka take yi tun daga zuciyarta domin abin ya fara isarta, Mimah ta nemi gurin zama ta zauna.
Mama ta gama kukan ta ɗauko wannan ƙwaryan ta miƙa mata.
Mama ta ce.
"Maganin tsari na karɓo miki."
Mimah ta ce.
"Gaskiya ba zan sha."
Mama da ƙyar ta lalaɓa Mimah ta sha maganin bayan ta sha Mama ta zuba mata abinci, ta na gama ci ta fara wani irin amai baƙin ruwa kawai ke fitowa ta hanci da baki.
Mimah ta yi 5 minutes ta na fitar da wannan ruwan kafin ya dakata, Mama ta taimaka mata ta yi wanka ta kwanta ba ta jima da kwanciya ba ta yi bacci.
Da la'asar Abba ya dawo gida lokacin Mimah na zaune a bakin ƙofar ɗakin su, Abba ya yi farin cikin ganinta.
Kwana biyu da faruwan haka Mimah ta natsu sosai Abba ya na amso mata rubutu, kuma ta na sha yanzu ko fita ba ta yi ta na zaune a gida abokin ɗan shila ya kira ta a waya yake ba ta labarin, ɗan shila da Sofy sun yi hatsaniya har ya soke ta a ciki, ta na gadon asibiti juyin duniya Mama ta ha na ta zuwa haka nan ta haƙura.
Shukrah mijinta ya ɗauketa sun bar ƙasan Abba ya bawa Abdulwahab da Mujaheed daman turo iyayensu a tsaida rana, Manaheer suna gaisawa da Mujaheed domin har charts suna yi.
An sa rana one month Daraini da Manaheer, a hankali Mujaheed ya siye zuciyar Manaheer.
Kuma har zuwa lokacin Mama bata yarda cewa yaron alhaji Ibrahim chanji ba ne.
Mama ta kai wa boka cikon kuɗin shi boka ya ce.
"Ta je ta kawo gashin kan Manaheer."
Mama ta dawo gida ta na tunanin in da zata samu gashin kan Manaheer, Mimah ta sa ki jiki cikin ƴan uwanta duk da cewa basu cika jituwa da Manaheer ba, amman kuma ta na zama cikin su a yi fira.
Manaheer na tsifa ta kalli Daraini ta ce.
"Dan Allah ki taimaki ƙanwarki."
Daraini ta yi banza da ita Mimah ta ce.
"Idan mutum na son a taya shi tsifa ya ce mun Anty, Manaheer ta harare ta."
Zuwa can da ta ji wuya ta ce.
"Dan Allah Anty Mimah ki taimaka mun."
Hatta Umma dake fitowa daga ɗaki sai da ta yi dariya, Daraini ta ce.
"Kowa ya tuba dan wuya ba lada."
Umma ta ce.
"Kin ji Mimah karki ta ya ta."
Manaheer ta marairace fuska Mimah ta ce.
"Bari in ɗauko abin ta je gashi."
Mimah ta shiga ɗaki ta ɗauko cum na ta ce gashi da abin tsifa, bayan ta fito Manaheer ta kalli hannun Mimah ta ce.
"Wannan gashin fa."
Mimah ta ce.
"Ina tunanin Mama ta yi tsifa ta manta da shi."
Manaheer ta miƙa mata na hannunta ta ce.
"Yi mun da wannan."
Mimah ta aje cum ɗin da ta ɗauko a jikinta a na cikin tsifan a ka tsiyace da Mimah da Manaheer.
Manaheer na ta faɗa wai Mimah na jan mata gashi saboda mugunta.
Daraini ta ce.
"Wannan ya na daga cikin dalilin da yasa ba na taya ki tsifa."
Mimah ta mayar da cum ɗin ta aje ta fita Mama ta fito daga bedroom, ta leƙa waje ta ga Manaheer na tsifa.
Ta kalli Mimah ta ce.
"Da zaman da kike yi dama kin taya ta."
Daraini ta yi dariya ta ce.
"Ai yanzu Mimah ta mayar da cum ɗin ɗaki, kin san Manaheer ba a mata abin arziki."
Mama jin haka ta shige ɗaki daman da safe ne kuma ba girkin ta ba ne.
Mama cum ta ɗauka ta nufi hanyar Zaria boka ya yi dariya ya ce.
"Aikin ki zai kammala nan da kwana biyu, kamar dai wancan lokacin za ki ga saƙo a ɗakinki, idan kika ɗauki saƙon ki aje a in da zata wuce da zaran ta tsallaka abin zai ɓace da kanshi, daga nan aikin ki ya kammala boka ya fashe da dariya Mama ta yi godiya ta tafi.
Kwana ɗaya da faruwan hakan Aunty Fatima ta yi waya a tura mata amare ta fara musu gyaran jiki, daman sana'ar da take yi ne harda shago mijinta ya buɗe mata.
Umma ta ce.
"Zan yi magana da Abban Shukrah, duk yanda muka yi zan faɗa miki."
Suka yi sallama da Aunty Fatima bayan kwana ɗaya, Mimah na share parlour ta tsinci laya a tsakar ɗaki.
Mimah ta kai hannunta za ta ɗauka.
Ta Batulu ce ✍️
Like and share
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Allahumma Sali Ala Sayyadina Muhammad Wassalim 🥰
Page 91~92
Har ta ɗaura hannunta a ka bige hannun Mimah ta kalli wanda ya bige mata hannu Mama ta ce.
"Wallahi idan ba ki daina shiga abin da bai shafe ki ba sai na saɓa miki."
Mama ta ɗau layar ta ɓoye Mimah jikinta ya yi sanyi da lamarin mahaifiyarta, yanzu gaba ɗaya tsoro take bata.
Mimah tun dawowar ta gida take ɗaukar karatu a gurin Umma da daddare.
Umma ta faɗawa Abba yanda suka yi da Aunty Fatima, kuma ya amince da hakan.
Bayan sallahr la'asar Manaheer na waya a tsakar gida Mama ta fito Mimah ta bi ta a baya, Mimah tun da ta ga laya a cikin ɗakinsu ta fara zargin mahaifiyarta da shirya wani abun.
Mama ta yar da layar a gaban Manaheer Mimah na tsaye a bayan ta, Mimah ta yi murmushi ganin Mama zata juyo ta yi saurin ɓoyewa.
Manaheer bayan ta gama wayar ɗakin Abba ta nufa, Mimah ta yi ajiyar zuciya ganin bata taka wannan layar ba.
Manaheer ta shiga ɗakin Abba daman da makulli a hannunta, Mimah ta nufi gurin da layar yake.
Ta yi kamar zata taka Mama ta yi saurin fitowa ta dakatar da ita, Mimah ta ƙunshe dariyar ta daman da gan-gan ta yi Mama ta ɗauke layar ta na hararan Mimah.
Da daddare duk suna zaune a saman tabarma Abba ya kalli Mama ya ce.
"Gobe idan Allah ya kaimu, Daraini da ƙanwarta zasu tafi gidan Fatima."
Mama ta yi murmushin ƙarfin hali ta ce.
"Tun yanzu za su ta fi."
Abba ya ce.
"Eh saboda lokacin bikin ba mai tsawo bane."
Mimah ta ce.
"Abba dan Allah zan bisu, nima in ga family na."
Abba ya ce.
"Daman ba ki taɓa zuwa ba."
Mama ta ce.
"Amman kin san jarabawa kuke yi koh.?"
Abba ya watsa mata harara Mama ta yi shiru, Abba ya kalli Mimah ya ce.
"Ki shirya gobe idan Allah ya kaimu ku tafi tare."
Mama ta faki idanun su ta aje layar bakin ƙofar ɗakin Umma, Manaheer da fitowarta kenan, ta ji wayar Umma na ringin ta ɓata fuska.
Ta koma ta ɗau wayar Shukrah ta gani a screen ɗin wayar, Manaheer ta zauna ta ɗaga wayar sun jima suna fira, a nan take gaya mata Hamza ya mayar da ita school.
Manaheer ta yi mata fatan alkhairi bayan sun gama wayar ta fara game da wayar, Mama dake tsaye a ba kin ƙofa ganin Manaheer shiru ta ƙi fitowa, ya sa ta yi mantuwa da layar da ta aje ta faɗa ɗakin.
Mimah na lura da abin da ya faru Mama ta taka layar ba tare da ta lura ba Mimah ta ta shi ta nufi ƙofar ɗakin Umma, ta na zuwa ta fara dudubawa amman babu layar ya ɓace Mimah hankalinta ya ta shi, ɗakin Umma ta shiga .
Ta na shiga ta samu Mama na yiwa Manaheer daɗin baki, Mama ta janyo ta zuwa waje Mimah na bin su a baya, dai-dai gurin da ta aje layar Manaheer ta bi Mama ta yi ajiyar zuciya.
Manaheer ta zauna a ka cigaba da fira da ita har zuwa 10 dai-dai fira ya watse, bayan sun shiga ɗaki Mimah ta kalli Mama ta ce.
"Dan Allah wani irin laya ne ki ka aje a ƙofar ɗakin Umma.?"
Mama ta ɗaure fuska Mimah juyin duniya Mama ta ƙi cewa komai, Mimah ta share hawayen fuskanta ta ce.
"Ba Manaheer ta taka layar ba."
Mama ta ce.
"Mai kike nufi.?"
Mimah ta ce.
"Kece ki ka taka layar a madadin Manaheer."
Mama ta watsa mata harara Mimah ta ce.
"Shiyasa a kace idan zaka gina ramin mugunta, ka gina shi dai-dai kai."
Mama bata ɗauki maganar Mimah da muhimmanci ba, ganin haka ta rabu da Mama ta yi kwanciyarta.
Bayan kwana biyu Daraini da Manaheer sun tafi Saminaka harda Mimah.
Umma ta gayawa ƴan uwanta sa ranar biki Hajiya Fatima ta ce.
"Ki bar mun hidimar kayan kitchen, karki siya musu komai."
Daga haka ta yanke wayar saboda ta san halin Umma za ta iya saka mata kuka.
Mimah a Saminaka ta ka sa sakin jiki saboda bata saba ba, Aunty Fatima ta sa drivernta ya kaita gidan ƴan uwa, suma sun ji daɗin ganinta.
Har kwana sai da ta yi a gidajen ƴan uwa, tun zuwanta garin, Usman yake biye da ita.
Mijin Aunty Fatima ya ɗauko shi daga garinsu ya sa shi a makaranta, yanzu haka ya gama karatu ya na aiki da Mijin Anty Fatima.
Tun saukar su Saminaka Khadija ta tare a gidan Aunty Fatima,
Mujaheed dubu ɗari biyar ya bayar kuɗin gyaran jiki, ta turawa Umma da kuɗin duk da cewar Hajiya Fatima ta ce. "Kar ta siya komai na kitchen."
Amman sai da ta siya Abdulwahab dubu ɗari biyu ya bayar, itama ta turawa Umma da kuɗin.
Biki ya na ta ƙaratowa Mama ta fara ciwo a tsaitsaye, yau ciwon kai gobe ciwon ciki jibi ciwon ƙafa, ciwuka dai kala kala.
Saura kwana huɗu biki a ka kawo lefe Daraini dozing 2 kayan ta masha Allah, komai ya ji a ciki harda sarƙar gwal a ciki.
Manaheer dozing 3 harda kyautar mota ba sai na tsaya zayyano muku kayan da ke cikin akwatin ba, domin wannan page ɗin ya yi kaɗan gurin zayyano muku kayan ciki.
Biki saura kwana 4 Hajiya Fatima ta sauka, sun yi magana da Umma a kan abincin da za dafa.
Hajiya Fatima ta bawa Umma shawaran a bayar a dafa a waje.
Mujaheed ya sauke musu katan katan ɗin lemu da shinkafa da sauran abubuwan buƙata, amaren sun dawo ranar da Hajiya Fatima ta sauka.
Umma ta miƙawa Hajiya Fatima ragamar komai na bikin.
Zuwa wannan lokacin hankalin Mama ya daɗa ta shi ganin irin dukiyar da a ka narkawa Manaheer.
Babu shiri ta garzaya gurin boka, domin a war gaza bikin gaba ɗaya.
Ta Batulu ce ✍️
Like and share
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
Page 93~94
Mama zaune a gaban Boka ta fashe da kuka Boka ya zuba mata ido kafin ya kwashe da dariya, ya ce.
"Daman na gaya miki yarinyar ba za ta taɓu ba, amman ki ka dage dole sai an taɓa ta."
Mama ta share hawayen fuskanta ta ce.
"Na a je mata layar ta taka amman,har yanzu shiru."
Boka ya janyo wani ƙaton kwano ya zuba ruwa, ba da yawa ba a ciki ya kalli Mama ya ce.
"Matso kiga babban kuskuren ki."
Mama ta matsa gaban shi Boka ya rufe ido ya na wasu irin yare, bayan ya gama ya tofa acikin kwanon.
Sai ga video abin da ya faru Mama ta fashe da kuka, tabbas itace wanda ta taka layar ba Manaheer ba.
Boka ya ce.
"Kuma gashin da ki ka kawo mun ba gashin ta bane."
Mama ta zaro ido ta ce.
"Gashin kanta na kawo maka."
Boka ya ƙara yin yanda ya yi ɗazun videon abin da ya faru ya bayyana, Mama ta ce.
"Kin kashe ni Mimah."
Boka ya ce.
"Ki yi sauri ina da aiki."
Mama ta share hawaye ta ce.
"Ina son a tarwatsa wannan bikin gaba ɗaya."
Boka ya ce.
"Wannan aikin mai sauƙi ne."
Mama ta ce.
"Daga nan Manaheer ta haukace ta bi duniya, kar a sake jin labarin ta."
Boka ya miƙa mata wani gora ya ce.
"Ki tabbatar kin watsa a gurin da suke zance da samarin su."
Mama ta karɓa ta ce.
"Boka ya zan yi da laluran jikina."
Boka ya ƙara miƙa mata wani ƙaramin kwalba kamar turare ya ce.
"Ki watsawa Manaheer a jiki, ko ta wani irin hali."
Mama ta karɓa boka ya ce.
"Maganinki ya na tare dake, kuma ya na da matuƙar wahala."
Mama ta ce.
"Zan yi duk abin da ya dace in dai zan samu lafiya."
Boka ya ce.
"Dole sai kin bawa Aljani kanki."
Mama duk da ta ji tsoro amman zuciyarta ta riga da ta bushe, Mama ta amince boka ya kwanta da ita.
Wa'iya zubillahi ubangiji ka tsare mana imanin mu 🙏
Bayan komai ya kamala boka ya mikawa Mama garin magani ya ce.
"Ki zuba a cikin ruwan wanka."
Mama ta amsa ta yi godiya boka ya ce.
"Idan ki ka ƙarayin kuskure kar ki nufo inda nake, domin duk aikin da nake miki da kanki kike ɓatawa."
Mama ta ce.
"In sha Allah zan kiyaye."
Boka ya daka mata tsawa ya ce.
"Da kin san Allah ba za ki taɓa zuwa in da nake ba."
Mama ta ba shi haƙuri Boka ya sallameta kwana ɗaya da faruwan, haka Mama ta yi wanka da maganin da Boka ya bata amman duk da haka ta na jin ciwon a jikin ta.
An fara events ɗin biki amare sun yi kyau an yi kamu an yi ƙauyawa day, dinner kuma sai an kai amare ɗakin su.
A na gobe ɗaurin aure Mama ta yi nasaran zuba maganin da Boka ya bata, sai dai matsalar da a ka samu ranar da ta zuba maganin, Mimah ta tsaya a gurin ita da Usman.
Hajiya Fatima ta hana amaren zance da angwaye, Shukrah ba ta zo bikin ba saboda ba ta da lafiya ga makaranta, har kuka sai da ta yi mijin ya rarrashe ta, amman ta ƙi haƙura ya kira Umma a waya ya haɗa su, Umma ta rarrashe ta ta kwantar mata da hankali.
Ranar ɗaurin aure da safe Mimah ta gama shiryawa cikin kayan da Abba ya yi musu anko, ta fara duba turare bata gani ba har ta haƙura zata fita.
Ta hango kwalbar da Boka ya bawa Mama Mimah ta yi murmushi ta ɗauko ta na buɗewa Mama ta shigo ɗakin, hankali tashe ta kalli Mimah ta ce.
"Karki sa ba turare bane."
Mimah ganin yanda Mama ta tayar da hankali ya sa ta ce.
"Ƙamshin ne ya yi mun daɗi."
Mama ta matsa za ta karɓa kwalbar Mimah ta ce.
"Allah zan juye duka a jikina."
Sanin halin ƴarta ya sa ta yi baya Mama ta ce.
"Na karɓo ne maganin mayu."
Mimah ta ce.
"To bari in shafa tun da maganin mayu ne."
Mama ta ce.
"Mimah yaushe na zama abokiyar wasanki.?"
Mama ta nufi Mimah da nufin ƙwace kwalbar,
Mimah ganin haka sai da ta bari ta zo gab da ita, sannan ta sa ki kwalbar ya faɗi ƙasa ya fashe."
Mama ta saka ihu cikin ficewar hayyaci ta rufe Mimah da duka ta na tonawa kanta asiri Khadija da ta shigo kiran Mimah, ta ji maganganun da Mama ke faɗa.
Daman wayar Manaheer na hannunta kawai ta danna record, Abba ne ya shigo ya samu Khadija laɓe a bakin ƙofa.
Khadija ganin Abba ya sa ta yi baya da sauri, Abba ɗakin ya shiga har lokacin Mama na dukan Mimah, ita kuma ta na tsaye ta ƙi motsawa.
Abba ya ƙwaci Mimah ya fara faɗa Mama ta yanke jiki ta faɗi a gurin.
Abba ya kira Aunty Amina ya ce.
"Kamata ki fito da ita waje."
Aunty Amina ta kama ta Abba ya fita ya samu Umar ya ce.
"Ɗauko mota ka kai Aisha asibiti."
Khadija sai da ta taimaka mata suka fito da Mama, Umar ya tuƙa suka tafi asibiti, ƴan biki suna ta hidimar su ba wanda ya kula su.
Ƙarfe 11 dai-dai dubanin jama'a suka shaida ɗaurin auren Daraini da Manaheer, ɗaurin auren da ya samu halarta manya manyan ƴan kasuwa, can na hango ya Salis m Reza yana ta baza babbar riga kamar shine angon 😂
Da daddare a ka tara amaren guri ɗaya an yi musu nasiha mai ratsa zuciya, Aunty Maryam ta shigo ɗakin ta ce.
"Motar ɗaukar amarya sun iso."
Umma sai da ta yi kuka an zo fita da Manaheer ta yanke jiki ta faɗi, Aunty Fatima ta yi saurin tare ta daman ita ce a kusa da ita.
An yayyafa mata ruwa amman ba ta farfaɗo ba, Umma ta ɗauko zam-zam ta yi addu'o'i ta shafawa Manaheer a fuska.
Manaheer ta yi ajiyar zuciya.
Ta Batulu ce ✍️
Like and share
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Allahumma Sali Ala Sayyadina Muhammad Wassalim
Written by ✍️
Jagaban Jajirtattu
(Ta Batulu)
End 95~96
Manaheer ta buɗe ido jikinta sai rawa ya ke yi, Umma ta kalleta ta ce.
"Assalamu Alaikum."
Manaheer ta amsa, Umma ta ce.
"Lafiya muna cikin taro za ki zo ki wargaza mana farin ciki."
Manaheer ta ce.
"Mun zo ta ya ƙawarmu murnar aure ne."
Umma ta ce.
"Mun gode za ki iya tafiya, kuma dan Allah idan kin tafi karki dawo."
Manaheer ta yi atishawa sai uku ta kwanta Umma ta bata raguwar addu'o'in da ta yi, bayan ta sha a ka fita da ita.
Aljannar duniya haka ƴan kawo Amarya ke ta faɗa, Hajiya Fatima har cikin ɗaki ta shigar da Manaheer.
Bayan sun yi sallar isha'i make-up artist ta yi wa Manaheer kwalliya, Khadija na gurin Manaheer, Mimah kuma gurin Daraini.
Motar da zai kwashe su zuwa gurin dinner ya kariko, Hajiya Fatima ta kama hannun Manaheer ta sata a baya.
Bayan sun ƙariƙa gurin ta ji an riƙo hannunta, Mujaheed ne yasha babban riga iri ɗaya da shigar jikinta, wedding gown blue da farin mayafi da jaka, kayan jikin angon blue ne an yi aikin fari a jiki.
Mujaheed ya kama hannunta suka shiga hall ɗin, kujera 4 Daraini da Abdulwahab sun riga su zuwa, Mujaheed ya zaunar da Manaheer shima ya zauna.
Mimah ta samu halartar gurin duk da ka san cewar Mama na hospital amman sai da tazo gurin.
Mimah ta bayar da tarihin Daraini a ta ƙaice, Khadija kuma ta bayar da na Manaheer.
Daga nan aka fara shagali wani keɓantacen guri na mussaman na hango, da sauri na ƙarasa sai naga ashe kungiyyar Jajirtattu ne suma sun samu halartar bikin.
Na shiga filin rawar can na hango Pending Amarya ana ta kwaso shockey, Pending Diamond na bayanta.😂
Ina shirin ficewa daga filin idona ya hango mun Barrister an dage sai rawa ake yi, ita da Pending Queen.😂
Sis Meerah da Autasssssss sun riƙe hannun juna, suma dai rawar suke yi abin ya ƙayatar.
Ido na ya hango mun Yaya na ɗan amana S Reza, a tsakiyar abokan ango babbar rigar a hannu.😂
11 dai-dai taro ya watse angwaye suka tafi da amarensu gida, Mimah kwana biyu Usman ya daina kulata.
Tun ta na damuwa itama ta share ta cigaba da addu'a, ƴan biki sun watse Hajiya Fatima ne kawai bata koma ba,
Hospital
Doctor sun yi bincike basu gano ciwon dake damun Mama ba drip kawai suke sama ta, kwana 4 da biki aka sallamo ta.
Mama ta yi baƙin ciki matuƙa amman duk da hakan bata saduda ba,
Hajjiya Fatima sai da ta bawa Umma jari sannan ta ta fi gidan ya rage daga Mimah sai Auta, shima Abba ya kai shi boarding school.
Bayan wasu watanni Mama ta kwanta ciwo sai dai a kwantar a tayar, kuma fa har lokacin bata gane gaskiya ba.
Mimah yanzu a ɗakin Umma ta ke kwana kakan Mimah ita ke jinyar Mama.
Abba arzikin shi ya ƙara bunƙasa Shukrah har yanzu basu dawo ƙasar ba, Manaheer mijinta ya ɗauketa sun koma in da yake sana'a London.
Daraini kuma an tura mijinta wani course America ya ta fi da matar shi, Mama da ta samu labarin abin da ya faru jikinta ya ƙara tsanani ta fara tonawa kanta asiri.
Bayan kaɗan kwana biyu da yin biki Manaheer ta ɗauko wayarta ta na dubawa, a nan ta ci karo da record ɗin da Khadijah ta ɗauka, ranar yini ta yi kuka da zazzaɓi Mujaheed juyin duniya ta faɗa mishi damuwarta, ta ce.
"Ina jin kewar gida ne."
Manaheer ta bar abin a cikin ta ba tare da ta sanarwa da kowa ba, hasalima wayar Umma ta aika ma dashi bayan ta goge komai na cikin wayar, Mujaheed ya siyo mata iPhone sai ta bawa Umma wannan.
Mama duk abin da ta ƙula sai da ta faɗa Abba ya yi baƙin ciki, amman ƙaddara ta riga fata.
Abba ya saki Mama saki 2 duk irin rarrashin da Umma ta yi amman Abba ya ce.
"Wallahi ba zan zauna da mai yin shirka a gidana ba."
Mama ta na kuka ta kwashe kayan ta Abba ya siyar da gidan ya koma Saminaka da zama gaba ɗaya, gidan shi kusa da uncle Nasser.
Amina ta yi nadamar halinta kuma ta roƙi ƴan uwanta gafara, yanzu haka suke ɗaukar nauyin ta Isa babu ruwanshi da sabgarta.
Inna ta yi hankali kuma ta tara yaran gaba ɗaya ta nemi yafiyar su, bayan shekara 2 Manaheer ta biyawa uncle Nasser da Umma kujerar hajji.
Mujaheed kuma ya biyawa Abba da uncle Umar, Hamza ya biyawa uncle Isma'eel, masha Allah kan family ya haɗu.
Umma burinta ya cika ta aurar da ƴaƴanta lafiya, yanzu babban burinta ta aurar da Mimah Abba har kuka sai da ya yi.
Sun je aikin hajji lafiya sun dawo lafiya Mimah zata auri, wani ɗan unguwarsu Khadija kuma zata auri yaron dake aiki tare da mahaifinta, lokaci ɗaya aka saka ranar bikin.
Shukrah yarinyar ta ɗaya Manal Daraini da Manaheer tsowon ciki, kuma har zuwa lokacin basu dawo ba.
An fara hidimar biki Shukrah ta yi zuwan ba zata Umma ta rasa in da zata ajeta saboda murna, da rana Manaheer ta sauka da ƙaton cikinta, Umma ta rungume ta jama'a suna ta tsokanarta da yamma Daraini ta sauka.
Umma ganin ƴaƴanta a guri ɗaya kuma dukkanin su rayuwa ta yi musu, har kuka sai da ta yi.
Kayan kitchen suka haɗu su 3 suka siyawa Mimah da zannuwan gado, Mimah har kuka sai da ta yi.
Umma ta yi farin cikin ganin sun haɗe kansu yanzu.
An fara hidimar biki Manaheer ta fara naƙuda, Aunty Maryam ta sata a mota Shukrah ta tuƙa suka kai ta hospital, basu jima da zuwa ba ta haifi twins duka maza.
Doctor ya dubata ya ga ba matsala ya rubuta takaddar sallama, a ɗakin Umma aka aje Manaheer Inna ta dawo gidan Abba da zama.
Anyi biki lafiya amare sun tare a ɗakinsu ranar suna yaran sun ci Hassan da Hussain, anyi shagali iya shagali jama'a da yawa sun halarci sunan, da daddare Daraini ta fara naƙuda kafin a kai ta hospital ta haiwu na mace.
Manaheer ta bawa big Anty jari domin ta kula da rayuwarta, yaran uncle Isma'eel uku biyu maza mace ɗaya.
Uncle Umar yaranshi 4 mace ɗaya maza 3, Auta ya girma yanzu haka yana ɗaura diploma ne, Mujaheed ya kai shi kasar waje.
Hajiya Fatima tun da Manaheer ta haiwu ta tare a gidan ita ke kulawa da masu jegon, ranar suna yarinya ta ci Amina suna kiranta da pretty.
Har yanzu Mama ta ƙi haƙura da yanda ubangiji ya tsara ita babbar burinta ta ga bayan Manaheer.
A hanyar zuwa gurin wani boka Mama ta gamu da hatsari ta rasa ƙafafunta, ubangiji kasa muyi kyakyawar ƙarshe.
Alhamdulellahi Ala Rasulillahi 🥰
A nan na kawo ƙarshen labarin RAYUWAR MU ubangiji ka bamu ikon aiki da darasin da labarin ya koyar.
Banyi wannan labarin domin cin zarafin wani ko wata ba.
A guji juya mun labari ta kowace irin siga domin ba zan lamunta ba.
Gaisuwar ban girma da addu'ar neman da cewa duniya da lahira.
Oum Ihsan mummyn Jajirtattu
Yusuf Gumel mallamin Jajirtattu Allah yasa kufi haka alfarmar Annabi Muhammad s a w 🙏
Jini yafi ruwa kauri,
Aunty Ma'aza
Sofy gaye iyayen gayu 😂
Gaisuwar girmamawa.
Aunty Maryam Anas Brando 🥰
Aunty Lele 🥰
Autar Jajirtattu 🥰
Sis Meerah 🥰
Barrister 🥰
Pending Amarya 🥰
Pending Queen 🥰
Pending Diamond 🥰
Autasssssss 🥰
Na saukar da wannan littafin ga mutane uku masu muhimmanci a cikin rayuwar Ta Batulu 🥰
Ya Salis Reza madubina abin koyi na 🥰
Muhammad Karim (MK) jagorana
Aliyu H Ishaq (fast class) masoyin gaskiya sanadin shi na iya rubuta Allah yasaka da alkhairi.
Kalmomin da zanyi godiya sun yi kaɗan sai dai in ce muku ubangiji ya biyaku da gidan aljanna, Allah ya baku dukkanin abinda kuke nema duniya da lahira ubangiji yasa ku gama da iyayen mu lafiya.
Allah ya sakawa iyaye na da gidan aljanna lallai kuɗin abin alfahari na ne.
Besty Ta Rasulu 🫶 Allah ya bar ƙaunarmu,
Sweet sis🫶 Allah ya gafartawa Baba,
Tawan🫶 ubangiji ka bamu miji na gari,
Ta Musamman ciwon kai na, 😂
Aunty Maryam Kd masoyiyyar Ta Batulu,
Saaduhhh 🫶 masoyin Saadeh 😂 na gode,
Bebyn baby Bestyn Besty Nooriyya Ta, Annabi Allah ya bar ƙauna,
Ƴan Amanata 😘 TA BATULU HAUSA NOVELS ina yinku over,
Dama wanda namanta ban ambaci sunan su ba na gode ƙwarai da soyayya, sai mun haɗu acikin sabon novel ɗina mai zuwa muku bada jimawa ba.
Ta Batulu ce ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT