Soyayyanovels
A Garin Mu Part One Complete Hausa Novel
A Garin Mu Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Garin Mu Part One Complete Hausa Novel

A Garin Mu Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 75 of 93
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,685 words Chapter 2 1,666 words Chapter 3 1,665 words Chapter 4 1,675 words Chapter 5 1,662 words Chapter 6 1,665 words Chapter 7 1,671 words Chapter 8 1,699 words Chapter 9 1,683 words Chapter 10 1,675 words Chapter 11 1,689 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,691 words Chapter 14 1,666 words Chapter 15 1,686 words Chapter 16 1,673 words Chapter 17 1,662 words Chapter 18 1,654 words Chapter 19 1,693 words Chapter 20 1,688 words Chapter 21 1,662 words Chapter 22 1,664 words Chapter 23 1,690 words Chapter 24 1,695 words Chapter 25 1,680 words Chapter 26 1,605 words Chapter 27 1,606 words Chapter 28 1,682 words Chapter 29 1,662 words Chapter 30 1,688 words Chapter 31 1,695 words Chapter 32 1,689 words Chapter 33 1,683 words Chapter 34 1,678 words Chapter 35 1,643 words Chapter 36 1,686 words Chapter 37 1,654 words Chapter 38 1,674 words Chapter 39 1,662 words Chapter 40 1,656 words Chapter 41 1,676 words Chapter 42 1,662 words Chapter 43 1,698 words Chapter 44 1,661 words Chapter 45 1,598 words Chapter 46 1,679 words Chapter 47 1,677 words Chapter 48 1,657 words Chapter 49 1,679 words Chapter 50 1,675 words Chapter 51 1,698 words Chapter 52 1,689 words Chapter 53 1,625 words Chapter 54 1,653 words Chapter 55 1,622 words Chapter 56 1,679 words Chapter 57 1,659 words Chapter 58 1,694 words Chapter 59 1,630 words Chapter 60 1,688 words Chapter 61 1,697 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,673 words Chapter 64 1,655 words Chapter 65 1,666 words Chapter 66 1,694 words Chapter 67 1,671 words Chapter 68 1,696 words Chapter 69 1,694 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,655 words Chapter 72 1,695 words Chapter 73 1,697 words Chapter 74 1,663 words Chapter 75 Reading now Chapter 76 1,683 words Chapter 77 1,699 words Chapter 78 1,659 words Chapter 79 1,645 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,677 words Chapter 82 1,671 words Chapter 83 1,653 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,681 words Chapter 86 1,655 words Chapter 87 1,625 words Chapter 88 1,640 words Chapter 89 1,694 words Chapter 90 1,672 words Chapter 91 1,675 words Chapter 92 1,689 words Chapter 93 1,418 words

Dan Talo dai sai gwale ido ya ke, ya ga mamallakin motar, domin dukkan alamu sun nuna gidan shi motar ke tunkara, nan da nan kuwa ya miqe ya kade rigar shi da ta fara nannadewa saboda yawan zama da ake akai.

Mota na qarasa tsayawa a gidan shi ya karkata kai ya na kallon motar har sai da su Mubaraka suka fito, ba qaramin jin dad'in hakan ya yi ba, nan da nan kuwa ya yi gyaran murya, da qaramar dariya ya ce,

"Dama k'yale ku ai niyyi, ku qarqare qaryar ku, tun subahin munkayi waya da su suna tahe, Mubaraka ta dawo daga qasar waje, sanda na fadi maku ta tai qasar waje karatu mi kun ka kira ni? Zubairu ko? Tauuu yanzu wa ka qarya ni da ku? Nan nan gaba gare ku, gwauna ya aiko a basuwa hoton yarinyar ga za shi yi mata miji, kun ka qaryata ni, tauu ga dai shi ta dawo ko?"

Wani fad'i ya dinga yi, ya na qobarewa, shi a dole mai gaskiya, kuma yaran shi sun dangwalo azziqi.

Ya na daga cikin sharadin Lawwali kar Mubaraka ta kula kowa a waje, in ya ce kowa ya na nufin kowa, sai sun shiga gida.

Dan Talo na ta washe baki, ya na musu barka da zuwa, Mubaraka ta yi wuf ta fad'a gidan, Lawwali kuwa yanda ya daure fuska kawai ya isar wa da Dan Talo babban saqo, su na shiga ciki suka ji hayaniya kamar za a d'aga gidan, qarasa tsayawa suka yi a qofar shiga gidan, Lawwali ya nade hannun rigar shi, ya zuba hannayen shi a qirjin shi ya na kallon su, 'Yabbuga ta fi kowa zaqalqalewa, Lamishi kuwa ta yi kalar tausayi,yau ko masifar ma ta kasa.

"....An fadi d'in barayin banza barayin wofi, talauci ku kad'ai ke fama da shi? Daga zuwa bukin suna sai a nemi atamfa a rasa? To waye ya dauke  ta in ba ku ba? Tunda ku na amince ku zauna qofar mai jego kar dangin mijin ta su shiga suyi sata, to walle biyan ta za ku yi, dan ba bar maku za mu yi ba"

" 'Yabbuga ni ta ce fa Lamishi, aminiyar ki, ni ki ka wa d'iban albarkar ga? Akan atamfar da ko dubu biyat bata kai ba? Ke mance har kyautar Suhwa (super) sai da na miki? Ranar bikin yaron nan ba abinda baki sata kin kai gidan ki kin boye ba, ko aza ki kai bamu sani ba? A gidan nan kin sha zuwa ki ci abinci ki qoshi ki tai, wa ya taba cewa ki biya?"

"Ki na barin yi min gori ki biya ni atamfa ko sai na maki d'iban albarka yanzun ga?"

Haushi ya gama cika Dan Talo, dan kuwa su na b'ata masa lokaci, ya matsu a gama gaggaisawa, in Lawwali zai tafi a bashi dan wani abu, kutsawa zai cikin gidan Lawwali ya dakatar da shi.

Jikin katangar gidan nasu da ba ta wani cika tsayi ba Lawwali ya jingina,ya ci gaba da kallon haukan da suke.

Mubaraka ta rasa me zata yi ta jawo ra'ayin su, ta na tsaka da tunani, ta tuna me ya kamata ta yi, magana ta fara qoqarin yi wa Lawwali, kawai sai ta hau tari, ta dinga tari ba qaqqautawa, nan da nan kuwa hankalin Lawwali ya tashi, ga hayaniya ta masa yawa, ya na ma tambayar Mubarakan me ya same ta ba ta ji, da ya juya ya daka musu wata gigitacciyar tsawa, gaba dayan su suka juya a matuqar firgice, su ka kalle su, shi kuwa da ya ji an yi shiru, kama Mubaraka ya yi ya na tambayar ta lafiya take tari?

"Yah Auwal zan....sha...ruwa, tari na ya sarqe ni,"

Da sauri ya fita mota, dan dakko mata ruwa,hankalin 'Yabbuga in ya fi cikin garin Zamfara to ya tashi, rasa inda zata saka kan ta tayi, Lamishi kuwa me zatai banda dariya tace,

"Shi kenan ma, tsaya ki karbi kuddin atamfar ki da ki ka mana sharrin sata,"

"Habaa Lamishi, ke ba ki san wasa ba halan, wasa ta ni kai miki, bari ma ki ga na tai gida, Dan Jummaa bai ko hita aiki ba"

Ta sa kai zata bar gidan kenan taga Lawwali na dawowa, da ihu da kururuwa ta koma ciki, ta ja turmi, ta haye katangar gidan, ta dira a maqota, duk kurjewar da ta yi bai dame ta ba, maqota kuwa na ganin mace ta dira cikin gidan su,suka d'iba da mugun gudu, kowa na takan shi,basu san me ya diro da ita ba, ko ta kan su bata bi ba, ta arce sai gidan ta.

Lamishi da Mai Buruji na ta sheqa dariya.

Mubaraka ta shiga suka hau dariyar a tare, ko da Lawwali ya shiga ya gan su tare sai ya juya ya yi d'akin shi.

Duk dakin ya yi matuqar yin datti da qura, duddubawa ya yi duk an dauke masa abubuwa masu mahimmanci, har kayan sawa da takalmi.

Ya na nan tsaye ya na tunanin rayuwa, ya dinga jiyo dariyar su Mubaraka, da mahaifan nashi,can kuma ya ji Mubaraka na bada hakuri, da sauri ya bar dakin ya fita.

"Menene ke faruwa?"

Cikin qoqarin maida kwallar ta ta ce,

"Babu komi"

A tsawace ya ce,

"Menene na ce? Waya tab'a ta?"

Lamishi ce ta ce,

"Yo gani nayi ta dawo daga tahiya ba ko tsaraba, hannu na dukan cinya, kuma dai nasan bata kasa sanin irin halin talaucin da muke ciki, abinci ma gagarar mu shi kai, dan rashin tausayi irin naku, kun bi duniya kun....."

Kallon da Lawwali ke mata ne ya sa maganar ta maqalewa a wuyan ta, Dan Talo kuwa ji yake kamar ya buga mata mari sai kumatun ta sun fi na Hameeda tashi (lols) duk za ta bata masa shirin qorafin da yake tafe da shi a lissafe, yanzu in ran shi ya ɓaci ya fita a hasale wazai bashi sisi?

"Wai ku yaushe ne za ku yi hankali?....shin dan Allah na tambaye ku, ku ne iyayen mu kuwa? Kun san ma'anar haihuwa kuwa? Kun san wane ne d'a ko d'iya kuwa? Ina su Jameelu? Ko kun san ina da labarin irin barnar da su Jameelu suke yi yanzu na sace-sacen kayan mutanen unguwa? Iyaye kala kala ne a duniya tabbas, akwai iyaye nagari, masu kula da d'iyan su, ta bangaren ,ciyarwa,tarbiyya,tuwahi,ilimi, da duk abinda ya kamata, Sannan akwai iyayen banza, irin ku, baku kula da tarbiyyan d'iyan ku, ballantana abinda za su ci, ba ku san ku basu ilimi ba, balle sutura, da ku da iyayen da ke kai d'iyan su almajiranci,ba su san cin yaran su ba, balle shan su, ba su san a wanne hali suke kwana ba,da ruwa da sanyi da zahi, ciwo da halin qunci, duk basu san ya d'iya suke ba, baku da bambanci,duk d'aya kuke, a zato na tunda kun ka ga baku gammu  ba na tsahon wannan lokacin, za ku neme mu, za ku damu, ku na nan ba ma cikin ran ku ma, burin ku, mu je mu kewayo, mu kawo maku kuddi ko? Kuddi kuka so ko? Yunwa kuka ji ko? Ina zuwa"

A haukace ya nufi garken awakin Dan Talo, ya bude su, sun kai guda tara, ai kuwa suka fita a guje, Dan Talo na ihu, Lamishi na Ihu,dan akwai uku nata a ciki.

Har qofar gida ya raka awakin ya kalli abokan  Dan Talo ya ce,

"Duk wanda ya kama shi tafi da su gidan shi, na bashi,"

Ai kuwa kamar qananan yara haka dattijan nan suka kwasa a guje su na bin tumakin nan, Dan Talo kuwa sai fadi ya ke ya na kumawa

"Walle ban bayar ba, ku bar min bisashe na"

Komawa Lawwali ya yi ya ce,

" kun gane ta nan, ta san darajar ku, ta na son ku, ta na qaunar ku, shi ne dalilin da yasa ta dage sai mun taho ta gan ku, kun san me nake aikatawa, amma ko a jikin ku, ita kad'ai ce ta damu da yi min nasiha, da addu'a dan na bar abinda ni ke, ku fa?....kun san me, ba zan taba yahe muku ba har abada, sai Allah ya tsai da  mu a gaban shi, ya ji dalilin da yasa ku ka  haife mu, ku ke walaqanta mu, ku ka barmu a lalace haka, sai Allah ya saka muna, ba iyaye na taqama da tsinuwa ba, komi ta yi maki, mai kyau, ko kure ki tsine mata, ki hada ta da mummunan kalami, ke san me ya same ta a dalilin kalaman ki?...."

Da sauri Mubaraka ta zube a gaban shi, ta na kuka,ta na bashi hakuri akan kar ya tona mata asiri, dan kuwa tonon asiri ne wannan, tun da ta san iyayen ba wani son ta suke ba.

"Bari na sanar da ita fatan da take maki kullum na kiyi gantali, baki yi gantali ba,gantalin ne yasame ki, inda ki ke, ko ke san cewa an yi mata fyade? Ki na da labari ko baki da shi?"

Mubaraka ce ta rushe da wani irin kuka mai matuqar ban tausayi, shi kan shi bai san hawaye na zubar masa a idanun shi ba, zuwa jikin rigar shi, tsabar qarfin fitar su.

Bai san ya zai fahimtar da su, ya yake jin baqin ciki a cikin zuciyar shi ba, duk wani irin bayani da zai yi ba zai bayyana yanda ya tsane su ba, Dan Talo da ya shigo ya ji kalaman Lawwali sai da ya zauna dabar a qasa, Lamishi da Mai Buruji Kuka, Mubaraka kuka,  dariya Lawwali ya yi ya share hawayen shi ya ce,

"Lallai ku na da abun mamaki, menene kuma na  kuka? Fyaden da an ka yi ma diyar ku? Ko kasancewar d'an da kun ka haihwa na kisan mutane da hannayen shi? Ko kuwa salwantar da rayuka da dukiya, da mahallin mutane da gudan jinin ku ke yi, shi ke sa ku kuka?

End of Chapter 75Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next