Baa Boren Namiji Book One Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
PAID BOOK
#500via 7084653262 Binta Umar Opey bank ko 0542382124...Binta Umar gtbank.
*GARKUWAR MATA*
*BINTA ABBALE*
[12/12, 9:46 AM] Bintu: *BA A BORAN NAMIJI!!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A.*
*ADVERT*
Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/JrVGCbG7R8SFurApPbPilB
*SAMIES KITCHEN*
The Best Chartering Service🥗🥘.
*KANO STATE: NO4 ZOOROAD HOUSING ESTATE*
*Jama'a Samies kitchen wurin fita kunya ne da kece raini. Wuri ne ingantace da ya amsa sunansa domin sharewa ma'abota karamci hawaye a yayin da wata hidima ta same su. Bari na jaddada muku SAMIES KITCHEN Ya samu sheda da lambar yabo gurin cika alkawari da karrama jama'a. Kada na cika ku da surutu bari na tafi kai tsaye domin sanar daku ainihin abinda ya sa nake kwad'aita muku 'kulla alaka da su. Wato SAMIES KITCHEN sun 'kware wajan shirya girke girke na gida dana waje. Sun yi shura wurin 'karbar order daga kowane sassa a fad'in Najeria. Suna yin abincin biki, abincin suna, abinci taro, abincin saukar al'kur'ani, order domin yin Birthday. Sun gwanance sosai wurin yin cima iri-iri da kayan ma'kulashe duk domin fita kunyar abokan hurd'arsu. Sannan ba su tsaya iya nan ba suna hada-hadar sayar da manya manyan leces 'kananu da manya kowane irin na'ui. Suna bud'e dilolin leces irin namu na gida (mama ta mutu) kala daban daban. Ana samun kayansu da inganci tare da farashi mai sau'ki. Domin neman karin bayani sai a tuntubi wannan lambobin.*
*08173037544 ko 07044417448*
5&6
Kansa ya girgiza ya kama hanyar fita yana sa'be babbar riga sai kace sabon limami.
Na yun'kura na tashi na fita zuciyata a 'kuntacce na shiga kicin domin lalubar abinda zan sa a bakina. Kicin din kace-kace babu gyara kudaje sai tashi suke yi ina kuma jin muryar Jummai mai yi mana wanke-wanken da shara a gurin Nafisa suna hira da dariya.
Raina ne ya 'baci ainun domin na san tabbas da Yaya Rabi'u ya lura da k'azantar kicin din a kaina zai sauke bala'i duk da ya san ba ni nake da alhakin hakan ba, zai ce ai ni ce babba amanar gidansa a hannuna take.
Kofar Nafisan na nufa na iske su a zaune durshen suna hira. Baffah da 'yan'uwansa suna zaune du'kun-du'kun da d'aud'a Nafisa ta yi wa Yaranta wanka tana shafa musu mai.
Babu fara a fuskata muka gaisa sama-sama, na ce." Jummai kin ga kicin kuwa 'kudaje sai bi sukeyi kwanuka duk sun bushe kina zaune kina hira ga sharar tsakargida da gate duk ba ki yi balle ki wanke band'ukuna, lokacin nan fa takaitacce ne, har yaushe ki ka kammala wannan aikin ki ka d'orawa Yara abincin rana, kuma kin riga kin san islamiyarsu ba su da wasa gaskiya Jummai ki canza idan ba haka ba zan sanar da maigidan halin da ake ciki domin wannan shine karo na uku."
Cikin ya'ke ta ce." Yi ha'kuri Uwar dakina bisimillahi bari na tashi na yi aikin da yake gabana.
Nafisa ta dakatar da ita babu fara'a a fuskarta ta ce." Wai Ummi girki ki ne ko nawa da za ki shigar mini hurumi?"
Jim na yi ina kallonta kafin na ce." Girki ki ne amma ba sai na yi miki 'karin bayani ba kin san komai.
Sunkuyar da kanta ta yi tare da cewa" Ni fa ki daina yi mini katsaladan ina ganin mutuncinki, ranar girkinki bana sa miki Ido saboda haka babu ruwanki Jummai dai ni na kira ta muna magana kuma ba ke ki ke biyanta albashi ba."
Murmushin takaici na yi na ce." Sai ki fad'awa Mijinki idan ya ce na zare hannuna daga kanku dama haka na fi bu'kata."
Ta bugi kirji tana fad'in." Ni fa ba Nadiya ba ce wallahi, kin san ni sarai idan ki ka yi mini ba zan saurara miki ba, ya kamata ki fahimci wannan, zaman aure ki ke yi, zaman aure nake yi, na lura kawaicin da nake yi miki ba kya gani amma idan ba rashin mutuncin ba ina ruwanki da shiga abinda bai shafe ki ba."
Tsaki na ja na kalli Baffah dake zaune yana had'awa 'kannansa jirgin Leda na ce." Ku ta shi Baffah mu je ayi wanka."
Da sauri ta ce." A banza dama ai babban burinki ki kore mu daga gidan, kin kori uwarsa kina kinibibi, ai wallahi Kulsumu tuntuni na dawo daga rakiyarki, ki juya mana miji sannan ki juya mu to ni wallahi ba ki isa ba, kin yi tsararo! Kuma zama daram a gidan Rabi'u."
Ban tanka mata ba saboda ganin yadda Yaran sukayi tsit! suna kallonmu, kawai na yi gaba ina fad'in" Baffah ku biyo bayana ayi wanka, ke kuma Jummai wata'kila shan ruwanki ne ya 'kare a gidan tunda gulma da munafurci ki ka zo yi."
Ina jin hargowarta tana fad'in." Ba ki isa ba wallahi Jummai zama daram dam! sai ke ki fita ki bar mata gidan. " Takaici ya kama ni, dama ai mai hali ba zai fasa halinsa ba, lokacin muna biyu Nafisa ba irin cin mutuncin da ba ta yi mini ba, sai ta kai ni bango wani sa'in nake turmusheta na daki kayana Yaya Rabi'u yazo ya yi ta shari'a, ta kama hanya ta tafi gidansu wai ta yi ya ji saboda na doke ta, idan ya yi biko ta'ki ta dawo sai ya rabu da ita ya shiga sabgoginsa, da k'afafunta take dawowa saboda iyayenta ba su da karfi wasu daga cikin 'yan uwanta ma a k'arkashinsa suke cin abinci, kuma da yake Ubanta dattijo ne duk abinda zai shiga tsakaninmu ba ya goya mata baya, saboda sanin halinta sai dai ma ya ba ni ha'kuri ya tattaramu ya yi mana nasiha har mijin namu gabad'aya.
Ina ko'karin kunna wuta Jummai ta shigo tana soki burutsu duk a 'ko'karinta na kare kanta ta kar'bi ashanar da take hannuna tana gyara bakin buhun gawayi zata zuba a korfoti take fad'in na je na zauna yanzu za ta d'umama ruwa ta yi wa yaran wanka.
Kafin ma na yi magana Baffa ya yi caraf ya amshe Yana fad'in "Munafuka wallahi sai na fad'awa Babanmu maganar da na ji kuna yi akan Mama har kuna k'yalkyala dariya ai duk na ji abinda ku ke fad'a ke da Ummansu Walida."
Jummai ta diririce ta fara kame-kame. Yaron ya cigaba da za'kulo zance wanda ya d'aure mini kai mutu'ka wato dama amincin da yake tsakaninsu na gaibu ne suna yin hakan ne domin su kai ni kasa wai Nafisa yau ita take farinciki da fitar Nadiya har tana addu'ar Allah ya sa ta tafi kenan ba za ta dawo ba.
Na yi sauri na daka masa tsawa jin yana ko'karin zaginta saboda tana musantawa, Baffa ba k'yalle ba ne, ba shi da kunya uwarsa ma bai bari ba balle wani.
Na kalleta duk ta muzanta sai zare Ido take yi na ce " Jummai kin ba ni kunya wallahi, ai idan duniya da gaskiya ba za ki zauna a ci naman Nadiya dake ba idan an yi duba da irin hidimar da take yi miki a gidan nan cikinmu babu wadda take kwatantawa, ba gori zan yi miki ba daga gidansu Nadiya duk shekara kina da Zakkah ta bayar da sunanki, sannan da Azimi kina da buhun shinkafa da gero bayan wanda maigidanmu zai ba ki, da sallah kina da turmin atamfa da kudin d'inki duk daga gidansu Nadiya, idan ban mance ba kuwa Nadiya idan ta tashi bayar da kayanta dana Yara ke take had'awa d'auri guda ki d'auka ki kai garinku amma yau dake aka zauna ana cin dunduniyarta.
"Billahil-lazi 'karya yake mini Uwardakina kwarankwarsa dubu ban......Katse ta ya yi yana fad'in." Wallahi Ummi karya take yi Munafuka ce domin har ji na yi suna cewa wai kin wanke wandonki kin bawa Babanmu ya sha a ruwa kece ki ke sarrafa shi, sai umarnin da ki ka bashi."
Jummai ta yi tsuru-tsuru tana zare Ido.
Hakan ya tabbatar mini da gaskiyar maganar Baffah dama kuma yaron da wuya ya yi k'arya, kusan halinsu d'aya da ubansa rashin tsoro da kafiya da taurin zuciya!
Na kalleta tana sinne kai na ce." Jummai yi maza ki kunna wuta zan yi wa tufkar hanci.
Ido jawur ta ce." Dan zatin Allah ki rufa mini asiri kada ki sa a kore ni wallahi zan kiyaye gaba, zan kula da aikina.
Tausayi ta ba ni ganin yanda take shirin fashewa da kuka, tabbas idan na fad'awa Yaya Rabi'u abinda ya faru babu makawa sai ya sallameta 'karshe ya had'a mata da cin mutunci tunda na san hali.
Na ce." Jummai wannan ya zama na farko kuma ya zama na k'arshe kada ki kuskura ki sake ke'bewa da wata daga cikinmu ki yi gulma idan hakan ta sake faruwa a bakin aikinki."
"Zan kiyaye wallahi ba zan 'kara ba." Cikin nadama ta yi maganar. Na ce." Ki d'ora musu ruwan wanka idan kin sauke sai ki dafa mini indomi biyu.
Ta amsa da sauri ta fara ko'karin rura wuta.
Yaran na ja d'akina muka zauna ina ta kwakwkwafar Baffah akan maganar kada ya fad'awa Babansu ko Mamansa, da 'kyar na shawo kansa ya yi mini al'kawarin babu wanda zai fad'awa a cikinsu. Sai hankalina ya kwanta domin ina fargabar maganar ta fita wani rikicin ya 'balle wata'kila itama Nafisan yana iya kora ta gidansu muddin ya ji murna take da fitar Nadiya a yadda hankalinsa ya tashi da faruwar hakan bai 'ki gabad'aya mu fita mu bar masa gidansa ba muddin Nadiya tana ciki.
More Hausa novels
Ig Ajeemal Book 3 Complete Hausa Novel
By Sajida Niger
Zee Yar Bariki Part One Complete Hausa Novel
By Zee Usman Kumurya and Fateemerh Zahra Eadress (Real Farhana)
A Cikin Rayuwa Part One Complete Hausa Novel
By Zainab Bature (Zeelaluh)
A Tsakankanin Soyayya Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
A Zato Na Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Search across the available chapters.