Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
A Tsakankanin Soyayya Part One Complete Hausa Novel
A Tsakankanin Soyayya Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Tsakankanin Soyayya Part One Complete Hausa Novel

A Tsakankanin Soyayya Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 29 of 71
About 7 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,076 words Chapter 2 703 words Chapter 3 1,721 words Chapter 4 1,657 words Chapter 5 1,697 words Chapter 6 1,115 words Chapter 7 1,422 words Chapter 8 1,221 words Chapter 9 1,677 words Chapter 10 1,680 words Chapter 11 829 words Chapter 12 1,538 words Chapter 13 920 words Chapter 14 1,677 words Chapter 15 1,467 words Chapter 16 1,618 words Chapter 17 1,305 words Chapter 18 1,812 words Chapter 19 665 words Chapter 20 1,776 words Chapter 21 1,291 words Chapter 22 699 words Chapter 23 1,465 words Chapter 24 1,641 words Chapter 25 1,588 words Chapter 26 1,030 words Chapter 27 876 words Chapter 28 1,086 words Chapter 29 Reading now Chapter 30 1,411 words Chapter 31 1,118 words Chapter 32 1,320 words Chapter 33 920 words Chapter 34 1,132 words Chapter 35 1,081 words Chapter 36 1,684 words Chapter 37 1,502 words Chapter 38 1,269 words Chapter 39 1,314 words Chapter 40 1,068 words Chapter 41 1,668 words Chapter 42 1,681 words Chapter 43 1,555 words Chapter 44 1,240 words Chapter 45 1,224 words Chapter 46 1,555 words Chapter 47 1,537 words Chapter 48 500 words Chapter 49 1,618 words Chapter 50 465 words Chapter 51 1,319 words Chapter 52 507 words Chapter 53 1,447 words Chapter 54 1,034 words Chapter 55 1,078 words Chapter 56 1,441 words Chapter 57 1,642 words Chapter 58 1,485 words Chapter 59 1,363 words Chapter 60 1,347 words Chapter 61 1,264 words Chapter 62 1,598 words Chapter 63 1,315 words Chapter 64 1,472 words Chapter 65 960 words Chapter 66 1,607 words Chapter 67 1,692 words Chapter 68 999 words Chapter 69 1,291 words Chapter 70 1,663 words Chapter 71 1,106 words

Takai kusan 2min atsaye chak awurin takasa matsawa sai rawa da jikinta keyi, kafin ahankali ta janye hijabinta tana kallon wajen, mai keken dayazo wucewa ta tare da sauri dan kunya takeji bana wasaba yanda kowa ke kallonta a wurin, shigewa tayi tace "express road zani" tada keken yayi yaja sukai gaba har express road yasauketa tafito dari biyu ta dauko tamikamai tajuya da gudu Yusuf zai tsaya yimata magana tabude kofa ta shiga abinta, Fatima sai kallonta take kaman yau tafara ganinta, backyard tawuce straight ta bude staff toilet ta shiga da gudu tarufe kofan tabude tap ruwa na zuba tafashe da kuka sosai tana taushe bakinta she's so angry, Aliyu ya mugun bata mata rai, ita wata irin mutum ne da ta tsani dizgi a bainar jama'a tun tana yar yarinya, ko dukanta Ammi zatayi inhar tamata agaban mutane saitai kusan kwana biyu bata fitaba taita kuka agida dan tanada kunya, kuma inhar Ammi tadaketa agaban jama'a kozata kasheta bazatai kuka ba saita daure sai jama'a sun tafi saitafara kuka, batason amata fada agaban mutane she's just naturally like that abin gets to her ne emotionally, shine Aliyun nan da bamata sanshi ba yakama yana mata tsawa kaman wata yarshi harzai mareta, sosai tafashe da kuka, cikin kuka sosai tabude jakanta taciro wayarta hanunta har rawa yake ta shiga contact dinshi ta danna ma number shi delete ta ijiye wayan takara kifa kanta awurin tana kuka sosai, jin ana shirin bude kofa yasa da sauri ta deba ruwan ta shiga wanke fuskarta, Fatima ce tashigo bayin tana hararanta tazo gefenta gaban wash hand basin din tana dan rera waka. "angwada nawa yace bayayi, da akaje gidan namiji saiya kadomu yace bazai bayarba shine muka gudo bayi muna kuka ahayye nanaye" Aneesa najin ta amma ba tace mata komiba, gama wanke wanke hannun tsokana Fatiman tayi tazo zata wuce tana waken ta ta bangaje Aneesa zata wuce, cikin tsananin fushi Aneesa ta fizgota batai wata wataba ta daga hannu ta daura mata clean mari, ihu Fatima tayi zata rama Aneesa tasa kafa ta kwashe ta sai kasa, tabita kasa ta kara daura mata wani marin tace "nasha gayamiki kifita daga harkana kinki, mene miki kika bangaje ni, ba fada kikeso ba zan koya miki hankali yau" takara zuba mata wani mari ta hade hannayen Fatiman ta murde su da karfi, ihu Fatima tayi, gwabe bakinta Aneesa tayi ta tashi daga kan cikinta tace "ki kara tonana" taja hijabinta da wayanta da jakan tafita daga bayin cikeda fushi, Fatima kasa tashi daga kasan tayi ta daga murya tace "wlh sainaga bayanki aduniyan nan Aneesa, sainaci mamanki dan ubanki, wayyo Allah na reshen bayana" dafa bango tayi tamike tsaye da kyar da sauri ta kakkabe jikinta dan batason Yusuf yagane Aneesa ta kayar da ita akasa ta wanwanke hanunta daya baci da kasa tawuce tafita daga bayin ta shiga store kitchen tabiyo Aneesa ta tsaya abakin kofa tarike kugu tace "ni kika mara Aneesa? Wlh sainaga bayanki aduniyan nan zaki ga" cikin masifa sosai dan ranta abace itama Aneesa yake tawani buga bowl din dake hanunta akan table ta kalli Fatima tace "ga fili gamai doki ubanki kafasa, kin zaci ke kadai kika iya hauka ko, sainaci ubanki" tafinciki bowl din tai kofan da gudu inda Fatiman take tsaye da gudu Fatima tafice ganin Aneesa ta haukace mata tana haki Ashe Aneesa ta iya fada haka, tsayawa Aneesa tayi abakin kofa tarufe kofan da karfi tana masifa. "dakin tsaya kiga inban kakkarya kasusuwan jikin ki da kwanon nan ba, da wlh saina kwaba cake dinan da namomin jikin ki" taja tsaki ta tsugunna jikin kofan Aliyu nafado mata arai sosai sama da dama, takai kusan 1min a tsugunne kafin tamike tashare hawayen daya zubo mata ta mike tawuce ta debo flour, kana ganin yanda take aikin kasan ranta abace yake.

Wuraren five na yamma yatashi daga baccin da tsananin ciwon kai, ahankali yabude ido ya yaye bargon da Dady yarufe shi dashi hanunshi dayaji yamai tsami ya kalla yaga an shafamai mai, dan murmushi yayi dan yasan aikin Dady ne ahankali yatashi ya zauna yana kallon wayarshi dake kusada side lamp ijiye, kafe wayar yayi da ido yanaji kaman yadauka yakira Aneesa, kawad da kanshi yayi da sauri daga kallon wayan yamike tsaye ahankali yana yatsine fuska yana tafiya ahankali, bathroom ya shiga yadauro alwala yafito, dadduma ya shimfida yay salla yadade kan dadduma yay shiru yana kallon wayar ahankali yamike tsaye ya linke dadduman yawuce yafita, abinci ya ganni kan dining ko kadan baijin cin komi, kitchen dinshi yawuce yabude fridge sliced fruits dinshi dasukai sanyi sosai ya kalla su yakeso yaci but baida karfin ci baida apatite, cup yadauka yadauko yogurt ya zuba farm fresh strawberry flavour yacika cup yamaida sauran fridge yafito yazauna kan dogon kujera yana kallon tashan kwallon dake aiki yakai cup din baki yana kurban yogurt din sanyin yogurt din na sanyaya mai wuya hakan yasa yasake relaxing tareda lumshe ido, fuskar Aneesa yagani tanamai murmushi.
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah🙌: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤

_✍🏿M Shakur_

2️⃣0️⃣ & 2️⃣1️⃣

_How to subscribe_
_*zaki turo 300 ta account number na 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting. Zaki iya turo katin MTN na 300 for those dabasu da bank*_

_Today is the DAY!!! I must give you my sincere, warm and outstanding shout out to my VIP group, you people are not just Very Important people you guys are my BLOOD_

_The amount of love, patient and understanding danake samu daga wurinku is beyond tunanina, ina karatun exam ina exam I don't get much time to type you guys supported me, oh my God, I mean o-h m-y G-o-d, am blown away da iskan kaunar ku, I Love my VIPs_

_Oh Hello, wanna join my VIPs and be having frequent updates? VIPs na are matured folks yo, manyan mata, issassu masu ji da kansu 😎 marasa son jira, masu rike alkawari, chat me up a pc if you want to join too_

Sosai tunanin Aneesa ya addabi zuciyar shi, ahankali yabude ido ya kalli yogurt din dake hanunshi ahankali yace "she's a Nubian princess" knocking kofar da akayi tareda shigowa yasa yadaga kai ya kalli kofa, Rauda ce ta shigo tanamai murmushi, rabonshi da ita tun ranan daya kwatota daga hannun Khamis, tsareta da ido yayi ganin ta ramemai duktai wani iri, shiru yayi baice mata komiba dan haushinta yakeji danta mai karya ranan, karasawa cikin dakin tayi ta zauna gefenshi ahankali tana wasa da yatsunta ahankali tace "good afternoon Ya Aliyu" gyadamata kai yayi batare dayace komiba ya cigaba da kurban yogurt yana kallon TV, shiru tayi tana wasa da yatsunta saikuma takara dago kai ta kallai ganin yaki kallonta yasa duk taji wani iri, ahankali tadaura hanunta kan nashi takama hannun shi tarike, dago kai yayi ya kalleta, lankwashe kai tayi murya chan kasa tace "am sorry Ya Aliyu bazan karama karyaba wlh, kunyan fadama da Khamis zamu fita nake saisa ban fadama gaskiya ba, am sorry kaji please" ganin yanda duktai wani iri tana shirin mai kuka yasa ya gyadamata kai dan ko kadan baijin surutu yau baijin dadin kanshi shima, bedroom dinshi yanuna mata yace "daukomin wayana" tashi tayi da gudunta tai bedroom dinshi, bata wani jimaba tafito rikeda wayanshi karban wayan yayi yaduba yaga ba miss calls ba message, baida any notification, dan lumshe ido yayi zuciyarshi namai badadi ya ijiye wayan ahankali kan kirjinshi, Rauda dake kallon fuskanshi ne tace "menene Ya Aliyu? Are you expecting something ne awayan?" batare daya bude ido ba murya chan kasa yace "nevermind" ji yayi ma yogurt din ya isheshi hakan yasa yamikama Rauda kofin, karba tayi tawuce kitchen tana shan ragowan daya rage, ta ijiye ta fito tadawo kusada shi ta zauna, yanda taga duk yay wani iri yasa takama hanunshi tace "Ya Aliyu wai menene? Bakada lafiya ne? Kai wani iri sosai wlh yau, are you okay Ya Aliyu kona kira Dr?" girgiza mata kai yayi yana mikewa tsaye yace "go and pray ana kiran salla" daya daga cikin sweet din dake cikin wani flower bowl dake kan center table dinshi ne tadauka tana folding legs dinta akan kujeran shi tace "ni am off salat" yatsine fuska yayi ya dungure mata kai batare dayace komiba, dariya tayi tana jefa sweet din abaki ya harareta yawuce ya shiga bayin falo ya dauro alwala yafito yabude kofa yawuce mosque yana tafiya ahankali.

End of Chapter 29Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next