Soyayyanovels
A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel
A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel

A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 1 of 75
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 Reading now Chapter 2 1,687 words Chapter 3 1,699 words Chapter 4 1,648 words Chapter 5 1,670 words Chapter 6 1,655 words Chapter 7 1,687 words Chapter 8 1,693 words Chapter 9 1,635 words Chapter 10 1,666 words Chapter 11 1,676 words Chapter 12 1,593 words Chapter 13 1,694 words Chapter 14 1,642 words Chapter 15 1,664 words Chapter 16 1,676 words Chapter 17 1,636 words Chapter 18 1,661 words Chapter 19 1,625 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,655 words Chapter 22 1,668 words Chapter 23 1,673 words Chapter 24 1,674 words Chapter 25 1,662 words Chapter 26 1,687 words Chapter 27 1,662 words Chapter 28 1,622 words Chapter 29 1,691 words Chapter 30 1,696 words Chapter 31 1,634 words Chapter 32 1,659 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,649 words Chapter 35 1,669 words Chapter 36 1,656 words Chapter 37 1,583 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,676 words Chapter 40 1,695 words Chapter 41 1,693 words Chapter 42 1,696 words Chapter 43 1,695 words Chapter 44 1,638 words Chapter 45 1,673 words Chapter 46 1,511 words Chapter 47 1,684 words Chapter 48 1,663 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,664 words Chapter 51 1,697 words Chapter 52 1,698 words Chapter 53 1,629 words Chapter 54 1,667 words Chapter 55 1,657 words Chapter 56 1,690 words Chapter 57 1,664 words Chapter 58 1,682 words Chapter 59 1,692 words Chapter 60 1,663 words Chapter 61 1,644 words Chapter 62 1,660 words Chapter 63 1,694 words Chapter 64 1,638 words Chapter 65 1,676 words Chapter 66 1,647 words Chapter 67 1,695 words Chapter 68 1,678 words Chapter 69 1,649 words Chapter 70 1,597 words Chapter 71 1,634 words Chapter 72 1,667 words Chapter 73 1,699 words Chapter 74 1,637 words Chapter 75 946 words

[2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 *A SANADIN SON KI* 💝

*Written by*
Aishat A Muh'd ✍🏻

♻£xclusive Writers Forum

*Dedicated to my Sadeey (saNaz)*

*PAGE 1-2*

Wata mata ce durk'ushe a filin tsakar gidan tana faman risgar kuka, har da shashshak'a kamar zata sume saboda tsabar kukan da take yi, sakamakon fad'an da mijin ta yake mata, gefe d'aya kuma yaran ta ne su biyu namiji da mace suna rungume da junan su, suna taya kan su da mahaifiyar su kukan tausayin kansu.

Tsinkar muryar mahaifin nasu naji cikin tsantsar 6acin rai da rashin mutunci yake cewa
" tun da abin haka ne zan tafi na bar muku garin gaba d'aya, na sha fad'a miki ni bana son haihuwa kwata kwata, ban shirya yin ta yanzu ba saboda bana son ta, ga kuma shegen bak'in talaucin da muke ciki, amman ke kamar kaza kina haihuwa babu dad'e wa ki dad'a samun wani cikin ni na gaji "

Ya k'arasa fad'i yana wani sauke numfashi, sakamakon hayagagar fad'an da ya gama yi cikin d'aga murya da tsawa, hararar matar tashi yake da 'ya'yan nashi, zuciyar shi cike da mugun tsanar su, ji yake kamar ya shak'e su, su mutu ko ya huta da ganin su.

Cikin shashshak'ar kuka matar tace
"Kayi hak'uri maigida, ni kaina ba ni na bawa kaina haihuwar ba, Allah ne ya bani su taya zan butulce mishi wajen zubar da cikin da ba shege ba ne, ka tuna haihuwa rahma ce wasu da kud'in su nema suke basu samu ba, amman kai da Allah ya bawa kyauta kana neman butulce mishi"

Ko gama rufe bakin ta bata yi ba ya d'auke ta da wani azababban mari har guda biyu bisa kyakkyawar fuskar ta, sake durk'ushe wa tayi tana rik'e da fuskar ta inda ya mare ta, hawaye ne kawai yake zuba a idanun ta.

Nuna ta yayi da d'an yatsan shi, cikin masifa yace "bana buk'atar jin shawarar ki ko wa'azin ki, idan baki bi maganar da na fad'a miki na ki zubar da wannan cikin ba, to wallahi zan bar garin don ban shirya rainon 'ya'ya ba, naji ma da uban talaucin da ya dame ni"

Yana gama fad'in haka ya juyo kan yaran, tsawa ya kwantsama musu ba shiri suka shige d'akin uwar ta su da gudu, jikin su na 6ari na tsoron mahaifin nasu.

Tsaki yaja tare da cewa "shegun 'ya'ya da munafurcin tsiya da sun ga uwar su na kuka, su ma zasu fara kukan 'yan iska kawai "

Yana k'arasa fad'in haka ya sake makawa matar tashi harara tare da jan tsaki ya kad'a rigar shi ya fice fuuuu a fusace kamar ya hantsila saboda sauri.

A hankali yaran suka d'aga labulen d'akin suna lek'en ko mahaifin nasu ya tafi, saboda jin shirun da suka ji, ganin ya fita ne yasa su fito wa da sauri suka nufi inda mahaifiyar su take tsugunne tana kukan nata.

Rungume ta suka yi suna rarrashin ta da tayi hak'uri ta daina kuka, daman sune masu rarrashin nata idan uban nasu ya gama yi mata rashin mutunci.

Dak'yar ta iya mik'e wa tsaye suka shiga cikin d'aki, zama suka yi akan tsohuwar tabarmar su wadda ke shimfid'e a k'asa, kallon yaran nata tayi cikin matuk'ar tsantsar kaunar su tare da mugun tausayin su, ta kamo hannun su ta had'a waje d'aya tare da bud'e bakin ta tace

"Aliyu ga amanar Suhaima nan ko da bayan rai na ina son ka kular min da ita, bana son tayi kukan maraicin na, ina son ku tsaya tsayin daka ku nemi ilimi saboda inganta rayuwar ku ko da bana raye, ina son mahaifin ku yayi alfahari da ku a gaba, ku kasance cikin yi wa mahaifin ku biyayya a duk abin da yace muku, ku cigaba da addu'a watarana sai labari komai zai zo ya wuce kamar ba'a yi ba."

Cikin kuka Aliyu yace
" Umma ki daina furta cewa zaki mutu ki bar mu, zamu rayu da ke Umma insha Allah, kuma zan rik'e k'anwa ta da kyau zan kula ta da ita Umma duk wani kyautata wa da bata farin ciki zan bawa Suhaima a cikin rayuwar ta."

Ya k'arasa fad'i hawaye na zuba a idanun shi, cikin zuciyar shi tsanar mahaifin shi taf a ciki, Suhaima da bani wayo ne da ita ba sosai, kallon su kawai take tana kuka.

Nan Umma ta janyo Suhaima jikin ta, rarrashin ta take har ta yi shiru sai sauke ajiyar zuciya da take, kafin kuma ta bud'e baki tace
"Umma ni yunwa na ke ji."

Umma kallon Aliyu take shima kallon Umman yake, cikin zuciyar su suna tunanin me zasu bawa Suhaima a yanzu taci, don basu da komai a gidan daman wani lokacin Aliyu ne yake fita yin 'yar sana'a ta k'arfi ya nemo musu abin da zasu ci, idan kuwa ta uban nasu ne kuwa gwara su mutu da yunwa akan ya basu abin da zasu ci.

Gaba d'aya ba wanda yayi k'arfin halin bawa Suhaima amsa, jin haka ya sanya ta fashe da kuka don ko karya wa basu yi ba gashi yanzu azahar tana kok'arin yi, cikin rarrashi Aliyu ya janyo hannun ta yana goge mata hawayen fuskar ta yace
"yi hak'uri 'yar k'anwa ta yanzu zan fita na samo miki abin da zaki ci, amman kada kiyi wa Umma kuka kin ji "
Gid'a kanta tayi tana mai had'iye kukan nata, da sauri Aliyu ya fita daga d'akin, yayin da Umman ta bishi da kallon tausayi, yaron da bai fi ace yana k'ark'arshin kulawar iyayen shi ba amman shine yake kula da kanshi, mahaifiyar da k'anwar shi, saboda rashin dace da samun managarcin uba a gare su.

Tun Suhaima na jiran Aliyu har bacci yayi awon gaba da ita a jikin Umma tana mai tsotsan 'yan yatsun ta a bakin ta, sai da bacci yayi k'arfi sannan Umma tayi mata shimfid'a ta kwantar da ita.

Tashi tayi ta fito zuwa tsakar gidan tsintsinya ta d'auka ta laushi ta fara share filin tsakar gidan, tana yin sharar idanun ta na zubar hawayen tausayin kansu, wani 6angare na cikin zuciyar ta addu'a take yi tare da godewa Allah a halin da ta tsinci kanta a ciki, k'addarar tace ta auren wannan mugun mijin nata mara tausayi, mai butulce wa Allah da baiwar 'ya'ya biyu da ya bashi ga cikin na uku a jikin ta.

Tun da Aliyu ya fita bai dawo gidan ba sai daf da mangarib, hannun shi rik'e da 'yar k'aramar leda bak'a, Suhaima na ganin shi ta mik'e da gudu ta k'arasa inda yake tare da kar6ar ledar hannun shi tana duba wa.

Garin kwaki ne a ciki sai k'ullin sugar, kallon shi tayi fuskar ta d'auke da murmishi tace
"Yaya mun gode Allah yasa ka samu sana'a kana samun kud'i kamar yanda Yayan k'awata yake aiki yana samun kud'i yana siyo musu abin dad'i "

Cikin murmishi ya shafa kanta tare da cewa "Amin 'yar k'anwa ta ki cigaba da yiwa Yayan ki addu'a da Umman ki ."

"Toh Yaya ina yi kullum idan nayi sallah, amman bazan yiwa baba ba tun da shi mugu ne yana dukan Umman mu, kuma yana zagin mu da dukan mu kullum, nima na tsane shi kamar yanda yace baya son mu ya tsane m........ "

Kafin ta k'arasa fad'in maganar taji an zabga mata wani wawan mari wanda yasa ta hantsila k'asa, ledar garin kwakin ta baje a k'asa ta tarwatse cikin dandaryar k'asar tsakar gidan.

Ashe basu ankara da shigowar baban nasu ba gidan, yaji abin da Suhaima ta fad'a shine yayi mata wannan marin da ko babba aka yiwa sai haka, cikin rashin imani ya kama Suhaima ya hau dukan ta kamar Allah ya aiko shi, Umma tana d'aki idar da sallahr mangarib d'in da tayi kenan tana sauri ta fito don ta jawa Suhaima kunne ta daina wad'annan maganganun, don lokacin da dawowar uban su gida yayi, sai kawai taji saukar dukan da yake yiwa Suhaima runtse idon ta tayi da k'arfi hawaye na fita a cikin su tana mai addu'ar Allah yasa kada yayi mata bugun da zai illata ta.

Yana dukan ta cikin fushi yana cewa "shegiya tsinanniya daman ni ai ba son ku nake ba, da zaki ce baza ki min addu'a ba sai uwar ki da Yayan ki, na tsane ku bazan ta6a kaunar ku 'yan iska matsiyata "

Cikin kuka Aliyu yace "Don Allah Baba kayi hak'uri ka dai na dukan ta, ka ga Suhaima yarinya ce k'arama ba zata jure dukan nan ba "

Sakin Suhaima yayi yana haki kamar wanda yake jibgar k'atu, harara ya dalla wa Aliyu tare da cewa
"Don uwar ka ni zaka fad'a wa gaskiya koh ?"

Kafin Aliyu ya ankara tuni Baban ya kawo mishi duka nan ya had'a su ya dunga duka kamar Allah ya aiko shi, sai da yayi musu lilis tukunna ya ce
" yanzu na fara dukan ku 'yan iska, Allah yasa ku mutu na huta da ganin ku"
Da sauri Umma ta runtse idon ta tana rushe wa da kuka jin mummunan kalaman da uban su yake yiwa 'ya'yan ta wanda ba yau ta saba jin su a bakin shi ba.

Yana gama fad'in haka ya fice daga gidan yana fad'a kamar wani ta6a66e, Umma tana jin yana fita ta fito waje da sauri zuwa wurin 'ya'yan nata da suke kwance magashiyan a k'asa suna kukan azabar dukan da aka yi musu.

Nan Umma ta rasa me zata yi musu kawai sai ta had'a ruwa mai d'umi ta fara yiwa Suhaima wanka, daman ta d'ora ruwan tun kafin mangarib, sai da ta gama yi mata wanka ta gasa mata jikin ta, tukunna ta kai ta d'aki ta kwantar da ita, sannan ta dawo wajen Aliyu ta kai shi band'aki tare da ruwan wanka tace
"kayi hak'uri Aliyu na, maza kayi wanka ka gasa jikin ka "
Gid'a mata kai kawai ya iya yi, sannan ta fito ta tattara garin kwakin da ya zube ta tsince shi tukunna ta jik'a musu.

End of Chapter 1Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Login to Save Next