A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
_gobe insha Allah zaku ga next pag fan's_
Aishat A Muh'd ✍🏻
[3/31, 5:55 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI*
Written by
Aishat A Muh'd
Dedicated to my Sadeey SaNaz
*PAGE 79-80*
Washe gari kuma shine ranar dinner d'in da friend d'in Sabeer wato Muusaddiq ya shirya musu don haka Suhaima ma ranar ma wajen azahar driver ya d'auke ta sai gidan Jiddah ita da wasu friends nata guda 5 wad'anda suka yi islamia dasu kuma kawayen ta na cikin unguwa, lokacin da suka k'arasa ma Jiddah bata nan ta tafi gidan su nan suka zauna a palour suna hirar su mai aikinta ta shirya musu abubuwa ci dana sha ta kawo musu sai after la'asar Jiddah ta yakice jikin ta dakyar ta taho gidan don sun yi waya da Suhaima sun zo.
*_8:40pm_*
Wata had'add'iyar mota black sai shek'i take da ganin ta kasan sabuwa ce tayi parking a compound d'in gidan Jiddah, ko mintuna biyar bata yi da parking ba sai ga su Suhaima sun fito wow masha Allah nace ganin yanda Suhaima tayi wani masifar kyau cikin wata gown har k'asa take ja sosai hannun rigar dogo ne har karshen hannu peach colour ne mai d'an haske tana da adon flower's manya shima kalar peach ne da kyallin duwatsu silver ajiki, sai abin nad'in kanta peach ne mai d'an duhu sai veil mai d'an girma an yafashi a saman kafad'un ta, tana sanye cikin shoes hill peach da purse nata itama kalar takalmin tasha wata sark'ar gold babba mai d'an girma a wuyanta haka ma hannun ta warwaron gold ne kowanne hannu guda hud'u hud'u tasha heavy makeup irin na bride, fuskar ta sai wani shek'i take kyau iyakar kyau Suhaima tayi shi sai tashin wani sanyayen k'amshi take yi ajikinta mai rikita mutum ya rasa irin perfumes d'in da akayi amfani dashi, tana tafiyar ta a nutse yayi da wasu kawayen ta biyu suke rik'e da karshen gown d'in ta inda yake jan k'asa suka nufi motar da ango yake, suma friends nata biyar sun sha gayun su cikin wani material pink da blue sun yi kyau kam ba laifi, Jiddah ma ta shirya cikin wata gown ta material pink colour tayi kyau itama hannun ta yana rik'e dana mijinta Khaleel shima yayi kyau cikin wata lallausar shadda fara.
Tun da suka taho Sabeer ya saki baki da hanci yana kallon Babyn shi yanda ta koma tamkar ba ita ba, duk da yasan Babyn shi mai kyau ce ko batayi kwalliya but wannan kyan da tayi na daban ne har baisan lokacin da ta shigo motar ba sai jin daddad'an k'amshin turaren ta cikin hancin sh.
Wata ajiyar zuciya ya sauke mai d'an k'arfi baisan lokacin da ya rik'o hannun ta ba d'aya ya d'ago fuskarta da d'ayan hannun yana mata wani irin kallo da eyes nashi wanda suke a wani lumshe lumshe, bakin shi yakai saman goshin ta yayi kissing d'in shi sannan ya cika fuskar ta yana cewa
"Masha Allah "
Abin da ya fad'a kenan a lokacin da suka bar harabar gidan Jiddah but still hannun shi yana cikin nata yana wani irin murza su a hankali, ita kuma Suhaima kunya ce ta kama ta sosai ganin abin da Sabeer yayi mata wanda bai ta6a kwatanta yi mata sai yanzu kuma tasan kwalliyar tace ta burgeshi sosai.
Sabeer bakin shi yayi mishi nauyi ya kasa magana saboda wani irin abu da yake ji yana ratsa shi a cikin kowanne lungu da sako na jikin shi, da haka suka k'arasa wajen da za'a gabatar da dinner d'in kallon ta yake tamkar yau ya fara ganin ta.
A d'an sace Suhaima ta kalle shi yasha wata shadda milk colour mai d'an duhu milk d'in sai aikin jikin rigar brown zare akayi amfani dashi har da babbar riga karo na farko kenan da Suhaima taga Sabeer cikin shigar manyan kaya sai taga yayi mata kyau ya k'ara mata wani girma da kwarjini a idanun ta har da hula milk and brown ne kai Sabeer ya had'u kawai ta ko'ina gaskiya Suhaima tayi dacen miji haka shima yayi dacen mata sun dace da junan su sosai.
Motar su tana k'arasa wa wajen tayi parking but basu fito ba suna zaune aciki, sai da Jiddah suka k'araso sannan suka fito hannun su na sark'e waje d'aya suna gaba Jiddah da Khaleel, Musaddiq da Mufidah a bayan su sai kuma friends na Suhaima su biyar d'in nan a bayan su.
Wajen yasha decoration na peach, red, pink and white ko'ina sai kyalkyali yake ga mutane duk an zazzau suna zaman jiran shigowar ango da amarya wani slow music ke tashi na wakar india ta Piya O Re Piya Tere....., itace ke tashi a wurin suna shigowa kallo ya dawo kansu sai fesa musu wani spray mai kyalkyali ga wasu furanni farare da ja da ake watsa musu a jikin su har suka k'arasa inda zasu zauna wata kujera ce d'aya mai d'an fad'i da zasu zauna daga bayan su kuwa wani k'aton frame ne yasha decoration an rubuta anyi zanen heart sai aka rubuta S-S ajiki wato Suhaima and Sabeer.
Bayan an zazzauna ne kuma Jiddah ta bud'e taron wajen da addu'a sannan ta bayar da tak'aitaccen tarihin amarya da harshen turanci bayan ta gama Musaddiq ma ya tashi cikin tafiyar kasaita Mufidahn shi mak'ale dashi yaje shima ya bayar da tak'aitaccen tarihin ango Sabeer sannan kuma akan nemi ango da amarya su fito su d'an taka rawa.
Suna tsaye wajen da aka tanada don yin rawa hannun Sabeer d'aya zagaye da kugun Suhaima d'ayan hannun kuma yana rik'e da d'ayan hannun ta ita kuma hannun ta yana zube saman kafad'un shi da haka suke d'an jujjuyawa don babu wanda ya iya wata rawa acikin su, sun birge mutane sosai yana mata magana kasa k'asa saitin kunnen ta bayyana mata irin tarin son da yake mata yake yi.
Jiddah ce da Khaleel suka fara zuwa wajen suka fara yi musu lik'i nan Musaddiq da Mufidah suka taso suma daga nan sauran mutane suka fara yi musu lik'i, can na hango My Biebie dee, my Sadeey, Ummu Safwan, Zahra da sauran fan's suna faman lik'a musu 'yan five five a kunyace suke yi saboda babu mai lik'a k'asa da five hundred sai su lol 😂.
Nan daidai aka cigaba da gudanar da dinner har zuwa lokacin da za'a yanka cake, Sabeer na rik'e da Babyn shi suka k'arasa wajen cake d'in wanda ya kasance hawa 5 ne yasha decoration sosai na white da peach, Suhaima ta rik'e knife na yanka wa Sabeer ya d'ora hannun shi saman nata nan suka yanka sannan Suhaima ta gutsuro cake d'in sai da ta d'an russuna k'asa sannan ta sanya mishi abaki a d'an kunyace tayi hakan tana yin murmishi.
Shima Sabeer murmishin yake kafin ya sanya hannun shi ya d'ago ta tsaye tukunna ya d'an rungume ta a jikin shi ya bata cake d'in da d'an juice a cup daga k'arshe ya bita da kissing a cheek d'in ta sai d'an ihun birgewa mutane ke yi suna yi musu tafi daga haka suka koma wajen zaman su.
Sannan aka fara ciye ciyen abubuwan ci da sha wanda aka shirya su na alfarma, Sabeer ne ya kallo Babyn shi cikin wani salon kallo yace
"Baby nah i luv U, i really luv U bazan iya rayuwa babu ke ba ina fatan addu'ar Allah ya bar min ke har iyakar tsayin rayuwa ta "
D'an murmishi Suhaima tayi kawai, hannun ta ya rik'o wanda ke rik'e da cup da juice aciki ya kai bakin shi ya d'an kur6a kad'an kafin yace
"Baby baki ce komai ba fah, yanzu gobe kamar haka na zama ke kin zama ni babu zancen jin kunya kuma, kodan ma kunyar bin ta zanyi duk inda take na cire ta ko ba haka ba amarya ta? "
Kamar k'asa ta tsage Suhaima ta shige haka take ji lallai Sabeer ya fitsare da yawa, yanzu ma yana mata haka balle gobe an d'aura musu aure sai kuma abin da yafi haka nan taji gaban ta ya fad'i, yana kokarin sake magana Musaddiq ya k'araso yana cewa
"Ango kazo ayi pic's don dare nayi my wife ta gajiya zamu tafi gida"
Tashi suka yi nan aka fara d'aukan picture's sosai da mutane, nan na d'an kutsa na samu aka d'auke mu pic's da ango da amarya sannan na samu wani table na zauna a gajiye nake lik'is, d'an waigawar da zanyi ba sai na hango su My Sadeey, My Biebie dee, Zahra, Ummu Safwan ana faman kiciniya da cinyoyin kaji bakunan su yayi dumu dumu da maik'o amman basu san da hakan ba, wani huci na saki mai zafi ganin zasu sanya ni jin kunya idan aka tambaye ni wadannan wane ya gayyace su idan aka nuna ni dole naji kunya kuwa don haka harara na dalla musu sannan na d'auke kai na lol🤣😂, gaskiya naji dad'i sosai ganin yanda fan's na ASANANDIN SON KI sunyi k'arar zuwa wannan bikin na Sabeer da Suhaima mun sha hira dasu sosai gashi har da ankon su na daban suka yi daga k'arshe muka yi sallama dasu don ni bayan amarya zan bi don na cigaba da d'auko muku rahoto yanda zata kasance nayi musu fatan komawa gida lafiya.
Sai wurin 12am na dare aka tashi daga wannan dinner d'in Jiddah tayi tayi da Sabeer yabar Suhaima su tafi gida tare ya 6ata rai tare da cewa
"Ke ni fah kin dame ni Jiddah ranki zai 6aci cinye ta zanyi kome, nace zan kawo ta har gida? "
Zum6ura baki Jiddah tayi had'e da cewa
"Toh gaakiya kada ku dad'e sannan ayi ahankali ba'a d'aura ba don naga rawar kanka ta fiye yawa"
Fad'in Jiddah tana tafiya tana maganar k'asa k'asa kamar gunguni don bai ma ji k'arshen maganar ta ba.
More Hausa novels
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel
By Oum Yasmeen
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Search across the available chapters.