Soyayyanovels
A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel
A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel

A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 64 of 75
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,668 words Chapter 2 1,687 words Chapter 3 1,699 words Chapter 4 1,648 words Chapter 5 1,670 words Chapter 6 1,655 words Chapter 7 1,687 words Chapter 8 1,693 words Chapter 9 1,635 words Chapter 10 1,666 words Chapter 11 1,676 words Chapter 12 1,593 words Chapter 13 1,694 words Chapter 14 1,642 words Chapter 15 1,664 words Chapter 16 1,676 words Chapter 17 1,636 words Chapter 18 1,661 words Chapter 19 1,625 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,655 words Chapter 22 1,668 words Chapter 23 1,673 words Chapter 24 1,674 words Chapter 25 1,662 words Chapter 26 1,687 words Chapter 27 1,662 words Chapter 28 1,622 words Chapter 29 1,691 words Chapter 30 1,696 words Chapter 31 1,634 words Chapter 32 1,659 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,649 words Chapter 35 1,669 words Chapter 36 1,656 words Chapter 37 1,583 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,676 words Chapter 40 1,695 words Chapter 41 1,693 words Chapter 42 1,696 words Chapter 43 1,695 words Chapter 44 1,638 words Chapter 45 1,673 words Chapter 46 1,511 words Chapter 47 1,684 words Chapter 48 1,663 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,664 words Chapter 51 1,697 words Chapter 52 1,698 words Chapter 53 1,629 words Chapter 54 1,667 words Chapter 55 1,657 words Chapter 56 1,690 words Chapter 57 1,664 words Chapter 58 1,682 words Chapter 59 1,692 words Chapter 60 1,663 words Chapter 61 1,644 words Chapter 62 1,660 words Chapter 63 1,694 words Chapter 64 Reading now Chapter 65 1,676 words Chapter 66 1,647 words Chapter 67 1,695 words Chapter 68 1,678 words Chapter 69 1,649 words Chapter 70 1,597 words Chapter 71 1,634 words Chapter 72 1,667 words Chapter 73 1,699 words Chapter 74 1,637 words Chapter 75 946 words

Yana gama sha ya mik'e ya d'auki kayan shi ya rik'e mai dattin a d'ayan hannun ya fito waje kallon Suhaima ya d'an yi kan ya kalli Aunty Aliyah yace

"Auntyn mu nagode bari na d'an fita waje ko zanga Ashiru don bamu had'u ba tun da nazo "

"Toh Sabeer sai ka dawo, amman ina zaka tafi da kayan nan masu datti haka a hannu? "

D'an murmishi yayi yana cewa
"Anjima zan wanke su ne zan ajiye su a inda nake kwana "

Tausayin Sabeer ne ya kama Aunty Aliyah tasan bai ta6a tsammanin zai yi irin wannan kwatankwacin rayuwa ko zuwan da yayi na farko baya yin wanki Yah Aliyu ne yake had'a wa ya wanke musu da nashi.

"Sabeer kabar shi Suhaima zata wanke maka "

"A'a Auntyn mu kada na wahalar da Mata ta "
Ya k'arasa maganar fuskar shi d'auke da murmishi wanda ya k'ara mishi kyau.

'Yar dariya Aunty Aliyah tayi kan tace
"Mata manya ni ai ban ta6a ganin matar da take gudun mijinta ba akan wani abu da ya faru bisa kuskure "

"Kaiii Auntyn mu kada mu yi haka da ke waya gaya miki tana gudun mijinta? "

Ya fad'i yana satar kallon Suhaima wanda ta cika tayi fam,
"Ai abin a fili yake K'anina "
Daga jin dai yanda Aunty Aliyah ke maganar kasan ta tsokana ce, sai akayi sa'a Suhaima bata tanka musu ba, ajiye kayan Sabeer yayi kusa da k'afar Suhaima kan yayi wa Aunty Aliyah sallama ya fita daga gidan.

"Allah Aunty ki daina yi min haka taya ina zaman hutawa na ki had'a ni da wanki don Allah "Cewar Suhaima cikin turo baki.

"Haba K'anwata bansan ki da fushi mai yawa ba ki d'auka ki wanke mishi na tabbatar Allah zai rubuta miki lada tunda da auren shi akan ki "
Cewar Aunty Aliyah cikin rarrashin Suhaima.

"Aunty kawai naga alama yanzu kin fi son shi da ni "

"Tabd'i kinsan dai Suhaima son da nake miki na daban shak'uwar mu da ke ma ba d'aya ce da ta Sabeer ba dukkanin ku matsayin k'annena ba don na girmi Sabeer ba, ina son ku had'a kanku da Sabeer ne da zarar Aliyu yaga haka duk fushin da yake dashi zai daina, Allah ya gani ina sonki da Sabeer wallahi gashi yana ban tausayi jiya da dare ji ruwa da aka tafka amman kusan akanshi ya k'are ga sanyin waje da duhu dalilin da ya tashi da mura kenan don tun da na tashi da asuba nake jin tarin shi da atishawa yana yi kuma duk wannan abun yana yi ne saboda A DALILIN SONKI Suhaima ya kamata kiyi tunani sosai kisan Sabeer masoyin ki ne na gaskiya "

Tana gama fad'in haka ta tashi ta wuce don cigaba da aikin ta yayin da tabar Suhaima cikin wani irin yanayi wanda lokaci d'aya ta fara jin haushin Sabeer yana raguwa cikin zuciyar ta.

Cikin sanyin jiki ta tashi ta fara wanke mishi kayan fes ta wanke su ta shanya saman igiya sannan tayi alwala ta tafi d'aki don yin sallah, bayan ta idar ne tana nan kwance saman abin sallahr Aunty Aliyah ta shigo cikin shirin tafiya suna tace

"Suhaima ni zan tafi idan Yayan ki da Sabeer sun dawo ga abinci nan a foodflaks ki zuba musu "

"Kaiii Aunty yanzu ki fasa tafiya dani? "

"Kiyi hak'uri Suhaima bazai yiwu mu tafi tare ba saboda baki tambayi mijin ki ba amman zan dawo da wuri kafin mangarib insha Allah "

"Toh Aunty adawo lafiya "

"Yawwa K'anwata haka nake son ji kin fad'a "

Tashi tayi suka fito har k'ofar zaure ta rakata ta tafi sannan ta rufe gidan ta wuce ta zuwa d'akin ta, kwanciya tayi kawai maganganun Aunty Aliyah ne suke dawo mata, da taga tunanin ba mai k'arewa bane ya sanya ta tashi taje ta had'a wuta a dutsen guga ta zauna ta gogewa Sabeer kayan shi tsaf ta d'auke su taje ta ajiye mishi saman jakar shi.

Tana zama kenan taji ana buga k'ofar gidan tashi tayi taje tana tambayar wane sai taji muryar Yayanta Aliyu bud'e k'ofar tayi tana murmishi tace

"Yayah sannu da dawowa? "
Shima fuskar shi d'auke da murmishin yace
"Yawwa Suhaima ya zaman gida ke kadai don nasan Aliyah ta tafi gidan suna koh? "

"Eh Yaya ta tafi sai ni kadai duk tsoro ya kama ni "

"Ai dama ke matsoraciya"
Cewar Yah Aliyu yana dariya cikin shagwa6a tace
"Kaiii Yayah aikuwa ni jaruma ce "

Hannun ta ya kamo suka k'arasa cikin gidan yana biye mata, bayan yayi wanka ta zuba mishi abinci yana ci suna hira yana bata labari akan harkar karatun shi tana yi mishi addu'ar Allah ya taimaka, yana tsaka da cin abincin Sabeer ya shigo gidan bakin shi d'auke da sallama.

Sanin muhimmancin sallamar ne ya sanya Yah Aliyu amsa mishi ko k'arasa shiga tsakar gidan bai yi ba ya juya zuwa cikin zaure ya shimfid'a tabarma ya zauna akai kawai, wani tausayin shine ya kama Suhaima wanda ya sanya ta binshi da kallon tausayi, ashe duk wannan kallon da take binshi dashi Yah Aliyu yana kallonta shima girgiza kanshi yayi kawa ya cigaba da cin abincin shi.

"Ki zuba mishi abinci ki kai mishi "
Ya furta hakan kamar bashi yayi maganar ba, aikuwa tsam ta mik'e da sauri taje kitchen ta zuba mishi tare da d'iban ruwa ta kai mishi, duk abin da take Yah Aliyu yana kallon ta yana kula da yanayin ta, bayan ta dawo daga kaiwa Sabeer abinci ta wuce d'akin ta kawai.

Ahaka har aka kwashi tsayin sati biyu Sabeer na kwana a zaure har zuwa yanzu babu wata kyakkyawar fahimta tsakanin shi da Aliyu, ga wani irin tari da zazza6i mai zafin gaske da yake yi da cikin dare baya iyayin wani cikakken bacci duk yabi ya rame sosai yayi bak'i ga rashin aski duk gashi ya cika mishi fuska ko abincin kirki baya iya ci, gashi kirjin shi yayi mishi wani irin nauyi gashi tsakiyar damina akai ana samun ruwa akai akai sosai.

Suhaima tana tausayin Sabeer ganin yanda ya koma har kuka take a 6uye, Aunty Aliyah tayi tayi dashi Ashiru ya rakashi chemist yak'i zuwa yayin da Yah Aliyu yake ce mishi ya tafi gidan su bazai iya zaman nan ba tunda shi ba d'an wahala bane kawai ya sakar mishi k'anwar shi, Sabeer idan yaji haka sai kawai yayi murmishi kawai shi ciwon da yake damunshi da k'in kulashi da Suhaima take yafi komai d'aga mishi hankali.

Kamar yau tun kafin mangarib ake ruwa har zuwa bayan sallahr ishsha bai tsayaba sai dai idan lokacin sallah yayi ya d'an tsaya, Sabeer yana tukunkune a zaure yana rawar sanyi sosai ga tari da yake faman yi idanun shi sunyi ja sun k'ara fitowa sosai saboda tarin da yake yi zuwa can kuwa numfashin shi ya fara d'auke wa kafin daga bisani ya tuntsire a k'asa yana jan numfashi dakyar.

Suhaima kuwa tana zaune a d'aki sai faman kukan zuci take tasan Sabeer yana can yana fama da dukan ruwan wani tausayin shine yake ratsa mata zuciya tana fitar da hawaye.

Yah Aliyu kuwa da Aunty Aliyah sai fad'a suke tana fad'a mishi idan Sabeer ya mutu mai zai cewa iyayen shi wannan horan haka ya isa duk yaro yabi ya rame yayi bak'i ga rashin lafiyar da yake fama da ita nasan zuwa yanzu yayi horan da bazai sake maimaita abin da yayi ba.

"Aliyah ana dole ne nace ya rabu da ita kuma bani na ce yazo ba fah ya zauna ra'ayin shine to ni mene ruwana "

"Haba Yah Aliyu nasan ka da tausayi zuciyar ka mai kyau ce kayi hak'uri ka yafe mishi, baka ganin yanda Suhaima ma ta shiga damuwa kada ka shiga hakk'in su fah da yawa tana son mijinta shima yana son matar shi don me yasa baza ka hakura ka bashi matar shi ba kuma na tabbatar kana son Sabeer ya kasance da Suhaima har k'arshe rayuwar ta, bakasan abin da Allah ya 6oye ba kawai ni a shawara ta ka bashi matar shi don Allah Yah Aliyu "

Cewar Aunty Aliyah tana kama hannun shi fuskar ta tab da hawaye, shiru Yah Aliyu yayi yau Aliyah ta tunasar dashi abubuwa da dama, take yaji zuciyar shi tayi sanyi ya kalli Aliyah yace

"Naji na amince zan bashi matar shi "

Wani dad'i ne ya ratsa zuciyar Aunty Aliyah tayi murmishi tana cewa
"Ko kaifa Yah Aliyu naji dad'i sosai don Allah yanzu ka taso muje ka ce ya koma d'akin Suhaima "

Hannun shi yasa ya ja hancin Aliyah yana cewa
"Toh Mata tagari angama taso mu tafi "

Ya mik'e tsaye yana murmishi tare da kamo hannun Aliyah suka fito zuwa zaure, sai dai suna shiga zauren hankalin su yayi masifar tashi ganin yanda Sabeer yake jan numfashi dakyar yana rik'e da kirjin shi ga kuma tarin da yake.

Da sauri suka k'arasa inda yake Yah Aliyu ya tashe shi zaune tare da rik'e shi yace
"Sabeer me yake damun ka? "
Kallon Yah Aliyu yayi kafin yayi luuu da eyes nashi kamar wanda yasha kwaya bashi da k'arfin bud'e baki yayi magana ma, ganin haka ya sanya Yah Aliyu d'ago shi yana rik'e dashi suka k'arasa d'akin Suhaima.

Da sauri Aunty Aliyah take buga k'ofar d'akin Suhaima tana kiran sunan ta, a firgice Suhaima ta duro daga saman gado tare da bud'e k'ofar nata.

Kafin tayi magana Yah Aliyu ya shiga da Sabeer cikin d'akin tare da zaunar dashi ya juyo ya kalli Suhaima wadda sai rarraba ido take hanaklin ta atashe yace

"Kiyi maza ki cire mishi kayan jikin shi ki canja mishi bari naje na samo mishi magani, Aliyah kije ki dafa mishi tea da kayan k'amshi ki dafa da lemon tsami a ciki "

End of Chapter 64Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next