Soyayyanovels
A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel
A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel

A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 2 of 75
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,668 words Chapter 2 Reading now Chapter 3 1,699 words Chapter 4 1,648 words Chapter 5 1,670 words Chapter 6 1,655 words Chapter 7 1,687 words Chapter 8 1,693 words Chapter 9 1,635 words Chapter 10 1,666 words Chapter 11 1,676 words Chapter 12 1,593 words Chapter 13 1,694 words Chapter 14 1,642 words Chapter 15 1,664 words Chapter 16 1,676 words Chapter 17 1,636 words Chapter 18 1,661 words Chapter 19 1,625 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,655 words Chapter 22 1,668 words Chapter 23 1,673 words Chapter 24 1,674 words Chapter 25 1,662 words Chapter 26 1,687 words Chapter 27 1,662 words Chapter 28 1,622 words Chapter 29 1,691 words Chapter 30 1,696 words Chapter 31 1,634 words Chapter 32 1,659 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,649 words Chapter 35 1,669 words Chapter 36 1,656 words Chapter 37 1,583 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,676 words Chapter 40 1,695 words Chapter 41 1,693 words Chapter 42 1,696 words Chapter 43 1,695 words Chapter 44 1,638 words Chapter 45 1,673 words Chapter 46 1,511 words Chapter 47 1,684 words Chapter 48 1,663 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,664 words Chapter 51 1,697 words Chapter 52 1,698 words Chapter 53 1,629 words Chapter 54 1,667 words Chapter 55 1,657 words Chapter 56 1,690 words Chapter 57 1,664 words Chapter 58 1,682 words Chapter 59 1,692 words Chapter 60 1,663 words Chapter 61 1,644 words Chapter 62 1,660 words Chapter 63 1,694 words Chapter 64 1,638 words Chapter 65 1,676 words Chapter 66 1,647 words Chapter 67 1,695 words Chapter 68 1,678 words Chapter 69 1,649 words Chapter 70 1,597 words Chapter 71 1,634 words Chapter 72 1,667 words Chapter 73 1,699 words Chapter 74 1,637 words Chapter 75 946 words

Dawo wa d'akin tayi ta tashi Suhaima sanya mata kaya tayi sannan ta zuba mata garin a kofi ta mik'a mata, ai kuwa da sauri ta kar6a ta hau shan shi babu k'akk'auta wa.

Ido Umma ta tsura mata tana kallon kumbararriyar fuskar ta ta zuciyar ta fal tausayin su, tana nan zaune Aliyu ya shigo d'akin dakyar ya iya yin sallah sannan ya zauna, mik'a mishi nashi garin Umma tayi girgiza kanshi yayi yana cewa
"Umma ki sha kawai na k'oshi "
Girgiza kanta ita ma tayi idanun ta fal hawaye tace
"A'a Aliyu ka kar6a kasha idan kana son ganin kwanciyar hankali na "

Bashi da yanda zai yi ya kar6a ya fara sha a nutse, ita ma Umma ta d'auki ragowar tana sha, bankad'a labulen d'akin aka yi tare da shigowa ba sallama, babu wanda ya d'ago kan shi ya kalli kofar saboda sun san wane mai shigo wa d'akin a haka.

Ko kallon su bai yi ba ya shige k'uryar d'akin ya zauna saman gadon tare da bud'e kunshin tsire da gurasar da ya siyo ya hau cin abin shi hankali kwance, tuni d'akin ya d'umame da k'amshin naman da gurasar suka hau had'iyar yawu dukanin su har da Umma.

Abin ka da mai ciki akwai kwad'ayi gashi ba ci ake ba nan ta shiga had'iyar yawu akai akai haka ma Suhaima, kallon Aliyu yake yi zuciyar shi tana zafi na tsanar halayyan mahaifin nashi, tashi tsaye yayi tare da cewa
"Umma zan kwanta sai da safe "
Don idan bai fita daga d'akin nan ba zai iya had'iyar zuciya ya mutu saboda tsabar bak'in ciki, kallon shi Umma tayi tare da cewa
"Allah ya tashe mu lafia "
"Amin "
Yace tare da fice wa a fusace.

"shege mai zuciyar tsiya da bak'in hali "
Babu wanda ya tanka mishi har Suhaima bacci ya d'auke ta tana had'iyar yawu na son cin naman, kwantar da ita tayi tare da lullu6e ta da zani saboda lokacin hunturu ne.

Tashi tayi tare da nufar gefen gadon k'arfen nata ta kwanta a can k'arshe tana mai tunanin makomar rayuwar su a gaba, ga cikin ta da yake k'ugin yunwa da haka bacci ya fara d'aukan ta, can cikin baccin nata taji mijin nata na lalubar ta alamar akwai abin da yake nema a wajen ta, wasu hawaye ne masu zafi suka dunga fita a idanun ta, duk dare ta saba da wannan halin mijin nata gashi ba abinci kirki yake basu ba, shi yasa kullum take tashi jiki ba kwari a gala6aice, tana kuka shi kuma yana sha'anin gaban shi har zuwa lokacin da ya rabu da ita ya juya mata baya, ba dad'e wa ta fara jin saukar minsharin shi, dakyar ta iya mik'e wa ta fito zuwa band'aki tayi wanka don bata iya bacci a haka, tana fito wa ta ga Aliyu zaune a tsakiyar gidan ga tsananin sanyin da ake zabga wa cikin mamaki tace
"Aliyu lafiya? "
D'ago kanshi yayi tare da cewa "Umma na kasa bacci ne, zuciya ta rad'ad'i take min "
Ya k'arasa fad'a hawaye na fita a idon shi, cikin tausayin shi tace
"kayi hak'uri Aliyu komai tsanani yana tare da sauk'i, bana son kana sa damuwa a ran ka wani ciwon ya kama min kai, kasan kai ne mai taimakon mu, yanzu tashi kayi alwala kayi sallah tare da addu'a, ka mik'a wa Allah buk'atun ka "
Tana nan tsaye yayi alwala sannan ya shige d'akin shi, tukunna ta juya ta shige d'akin ta kwanta, jikin ta babu k'arfi da ita ma nafilar zata yi ta fad'a wa Allah matsalar ta, amman duk da haka sai da ta janyo carbi ta fara istigifari tare da salatin Annabi (SAW), da haka bacci mai k'arfi ya d'auke ta...........

*** **** ***

*ASALIN LABARIN SU*

Aishat A Muh'd ✍🏻
[2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 *A SANADIN SON KI*💝

*written by*
Aishat A Muh'd

♻ £xclusive Writers Forum

*Dedicated to My Sadeey (SaNaz)*

*PAGE 3-4*

Umaru direba miji ne a wurin Fatima, auren so da kauna suka yi don sai da suka d'an jima suna soyayya kafin su yi aure.

Bayan sun yi aure ne suna zaman su lafia cike da so da kulawar junan su, don ma bai fiye zama a gida ba tun da direba ne shi suna tafiye tafiye zuwa garuruwa daban daban, amman hakan bai hana shi kula da ita ba sosai kwatsam ana haka sai Fatima ta samu ciki tun daga lokacin ta rasa gane kan Umaru don gaba d'aya ya canja mata, duk wata kulawa da yake bata ya bari.

Saboda sam shi baya son yara gaba d'aya wahala ne rainon su kawai, yayi rarrashin da ban bakin don kawai Fatima ta yarda a zubar, amman sam tak'i yarda saboda tana matuk'ar kaunar yara sosai, ganin tak'i yarda da buk'atar shi na zubar da cikin yasa shi fara gallaza mata tare da yi mata wulak'anci da rashin mutunci kala kala.

Amman duk Fatima ta shanye wannan wahalar da yake bata har zuwa lokacin da Allah ya sauke ta lafiya ta samu d'a namiji inda ya ci sunan shi Aliyu, saboda rashin babu ko suna ba'a yi ba balle yiwa yaro yanka kamar yanda ake yi a al'adance, saboda iyayen Fatima basu da k'arfi su ma kuma waje ba d'aya ba don suna da d'an nisa a tsakanin su, tun kafin ta haihu da Umaru ya sanya k'afa ya bar garin bai dawo ba har sai da tayi wajen wata biyu da haihuwa sannan ya dawo duk da kuwa yaji labarin haihuwar.

Nan ya bi ya tsani Aliyu ko kad'an baya kaunar yaron, ga zafin talauci da ya kunno mishi kai saboda motar da yake aiki da ita mai shi ya kwace abar shi, sai buga buga da yake faman yi.

Aliyu na da watanni 10 cif, Fatima ta sake samun wani cikin nan Umaru bak'in ciki ya isheshi, a lokacin babu irin cin mutuncin da bai yiwa Fatima daga k'arshe sai da yasan yanda yayi ya zuba mata maganin zubar da ciki a lemo, ya bata tasha babu dad'e wa ciki ya zube nan farinciki fal cikin zuciyar shi, yayin da Fatima bata zarge shi ba ta d'auka kawai 6ari ne tayi nan ta cigaba da rainon Aliyu wanda uban bai ta6a d'aukan shi ba, ko kallon mutunci baya yi mishi saboda tsabar tsanar da yayi mishi kamar ba shine uban shi ba.

Bayan zubewar ciki ne ya dawo da d'an bata kulawa kafin daga k'arshe kuma wani cikin ya sake bayyana a jikin Fatima, wannan karon ma zubar mata da cikin yayi wanda sai a lokacin Fatima ta ankara da hakan, nan tayi kukan bak'in ciki da takaici na abin da mijin nata yake yi mata na mugunta.

Sai da Umaru ya zubar wa mata da ciki sau uku bayan haihuwar Aliyu, ana hud'un ne kuma bai samu nasarar zubar wa ba har aka haifo Suhaima, sai da Suhaima tayi shekara 5 sannan ta sake samun wani cikin wanda har Fatima ta fitar da ran sake haihuwa ganin shekarun Suhaima sun d'an ja, kwatsam ta samu wannan cikin wanda ya sanya Umaru dana sanin auren Fatima a rayuwar shi ga talaucin da yake fama dashi mai tsanani.

Har zuwa yanzu babu abin da ya canja daga tsanar da yake yiwa Aliyu, Suhaima da kuma cikin da yake jikin Fatima, daman abinci ba basu yake ba komai na abin da ya rataya a wuyan shi na hakk'in matar shi da yaran shi baya yi, kanshi kad'ai ya sani idan ya samu kud'i zai ci mai dad'i a cikin shi, wani lokacin agaban su zai ci abin shi sai dai su yi ta had'iyar yawu, amman ko kad'an ne bazai ba su ba, sai dai da dare ya bi ya tak'ura wa Fatima da buk'atar shi, bayan kuma ko abincin kirki baya bata wani lokacin ma tun karyawar safe har zuwa daren ba zata samu cin wani abincin kirkin ba, haka zai bi ya gala6aitar da ita shi yasa kullum sake rame wa take ga jiki babu k'arfi.

Ban da uban dukan da su Aliyu da Suhaima suke sha a hannun shi, don kusan akan su yake huce haushin shi, har zuwa lokacin da Aliyu ya fara fita d'an aikin k'arfi yana d'an samun wani abin wani lokaci ya siyo musu abin da zasu d'an sa a cikin su, ko kuma idan makobcin su idan anyi girki da d'an yawa suna taimaka musu saboda sun san halin da suke ciki, bama iya su kad'ai ba kusan k'auyen gaba d'aya ma sun gane halin da suke ciki.

*** *** ***

*CIGABAN LABARI*

Haka su Fatima suka cigaba da rayuwar wahala a hannun mugun mijin ta uban yaran ta, da ita da yaran nata don gaba d'aya had'a wa yake ya ci musu mutunci son ran shi.

Kamar yau da sassafe suna zaune cikin d'aki, a gaban su garwashin wuta ne a cikin kasko suna jin d'umi, duk sun yi jigum jigum Fatima da Aliyu suna tunanin hanyar da zasu bi don su samu abin da za'a karya dashi, yayin da Suhaima kuma ta fara hawaye saboda yunwar da take nuk'urk'usar ta.

Bankad'o labulen d'akin aka yi aka shigo, kamar kullum ba wanda ya kalle shi, cikin sauri ya wuce uwar d'aki ko kallon inda suke bai yi ba, babu jimawa ya fito hannun shi rik'e da jakar kayan shi kaf.

Kallon matar ta shi yayi tare da cewa
"to ni Fatima tafiya zan yi, kuma bansan ranar dawowa ta ba, watak'il na dawo ko kuma na tafi kenan, tun da kin k'i yin abin da nake so, zan tafi zan yi nesa da rayuwar ku, zan bar ki ke da yaran ki."

Tun da ya fara magana Fatima take kallon shi tana kuka, yana k'arasa maganar shi ya sanya kai zai fice zuwa waje babu alamar damuwa a fuskar shi, da sauri Fatima ta rik'o rigar shi cikin kuka ta fara cewa
"yanzu tafiya zaka yi ka barmu? "
Babu wata damuwa yace
"tabbas tafiya zan yi, bazan zauna bak'in cikin 'ya'yan ki ya kashe ni ba, tun kafin lokaci na yayi "

End of Chapter 2Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next