Soyayyanovels
A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel
A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel

A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 3 of 75
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,668 words Chapter 2 1,687 words Chapter 3 Reading now Chapter 4 1,648 words Chapter 5 1,670 words Chapter 6 1,655 words Chapter 7 1,687 words Chapter 8 1,693 words Chapter 9 1,635 words Chapter 10 1,666 words Chapter 11 1,676 words Chapter 12 1,593 words Chapter 13 1,694 words Chapter 14 1,642 words Chapter 15 1,664 words Chapter 16 1,676 words Chapter 17 1,636 words Chapter 18 1,661 words Chapter 19 1,625 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,655 words Chapter 22 1,668 words Chapter 23 1,673 words Chapter 24 1,674 words Chapter 25 1,662 words Chapter 26 1,687 words Chapter 27 1,662 words Chapter 28 1,622 words Chapter 29 1,691 words Chapter 30 1,696 words Chapter 31 1,634 words Chapter 32 1,659 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,649 words Chapter 35 1,669 words Chapter 36 1,656 words Chapter 37 1,583 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,676 words Chapter 40 1,695 words Chapter 41 1,693 words Chapter 42 1,696 words Chapter 43 1,695 words Chapter 44 1,638 words Chapter 45 1,673 words Chapter 46 1,511 words Chapter 47 1,684 words Chapter 48 1,663 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,664 words Chapter 51 1,697 words Chapter 52 1,698 words Chapter 53 1,629 words Chapter 54 1,667 words Chapter 55 1,657 words Chapter 56 1,690 words Chapter 57 1,664 words Chapter 58 1,682 words Chapter 59 1,692 words Chapter 60 1,663 words Chapter 61 1,644 words Chapter 62 1,660 words Chapter 63 1,694 words Chapter 64 1,638 words Chapter 65 1,676 words Chapter 66 1,647 words Chapter 67 1,695 words Chapter 68 1,678 words Chapter 69 1,649 words Chapter 70 1,597 words Chapter 71 1,634 words Chapter 72 1,667 words Chapter 73 1,699 words Chapter 74 1,637 words Chapter 75 946 words

Cikin tsananin kuka Fatima tace
"Don Allah kayi hak'uri ka dawo mu zauna, kada ka mance ina da auren ka akai na, sannan kuma ga yaran k........."

Kafin ta k'arasa fad'in maganar ta, Umaru ya sanya hannu ya ture ta da k'arfi, ta fad'i da6ar a k'asa, tuni marar ta tayi wani mugun d'aure wa, da sauri Aliyu ya nufi wajen Fatima shi da Suhaima suna mata sannu, cikin hassala da rashin mutunci yace
"kada ki k'ara danganta ne da wad'annan shegun yaran, kuma zan tafi babu uban da ya isa ya hana ni tafiya "
Yana gama fad'in haka ya kad'a kanshi ya fita, cikin zuciyar shi wasai babu damuwa ko kad'an.

Dakyar Fatima ta iya gyara zaman ta, saboda mugun ciwon da marar ta yake, sakamakon ture ta da mijin nata yayi ta fad'i, wani irin zugi zuciyar ta take lokaci d'aya ta nemi hawaye ta rasa, ta kafe idon ta waje d'aya tamkar wata mara rai don ko motsin kirki bata yi.

Tun motsawar da tayi bayan ta fad'i, a hankali wani abu mai d'umi ya fara zubowa ta jikin ta, sai a lokacin ta motsa idon ta, zuwa kallon jikin nata, sai ta ga jini ne yake zuba sosai, alamar cikin nata yana cikin hatsari, koma yana daf da fita, sai a lokacin taji wani kuka ya zo mata mai k'arfi.

Cikin kid'ima Aliyu yace
"Umma jini a jikin ki, na kirawo miki Babaa lantana? "
D'aga kai kawai ta iya yiwa Aliyu saboda yanda take jin jikin nata, yayin da Suhaima take kuka sosai, saboda ganin halin da mahaifiyar tasu take ciki, da gudu Aliyu ya fice daga gidan har yana cin tuntu6e da dutse, yana saurin k'arasa wa gidan Babaa lantana mak'ociyar su, domin neman taimakon ta.........

Aishat A Muh'd ✍🏻
[2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 *A SANADIN SON KI* 💝

*Written by*
Aishat A Muh'd

♻ £xclusive Writer's Forum

Dedicated to my Sadeey SaNaz

PAGE 5-6

Da gudu Aliyu ya shiga cikin gidan Babaa Lantana yana kuka sosai, Babaa Lantana mak'obciyar su fatima ce, mutunci sosai suke yi, tana tsananin tausayin Fatima da yaran ta, ita da mijin ta shi yasa wani lokacin suke taimka musu da abin da Allah ya hore musu, don su ma ba wani kud'i suke dashi ba sai rufin asirin Allah, suna da yarinya d'aya mai suna Aliyah ta d'an girmi Suhaima da kusan shekara hud'u, ita kad'ai Allah ya basu rayayyiya cikin duk yaran da take haihuwa suke mutu.

A madafa Aliyu ya tarar da Babaa Lantana tana sauke abinci daga kan murhu, d'ago kanta tayi da sauri ganin yanda aka shigo mata gida kai tsaye babu sallama, mamaki ne ya kamata ganin Aliyu ne ya shigo yana kuka, cikin mamaki tace
"Aliyu lafiya, mai ya faru kake kuka? "
Cikin rawar murya da hakin gudun da yayi yace
"Babaa Lantana ki taimaka mana, Inna ce bata da lafiya gashi ji...... '
Kafin ya k'arasa maganar da yake yi ne, tuni Babaa Lantana ta d'auko fallen zanin ta na atampa a saman igiyar shanya ta lullu6a shi a kanta, ta fita da sauri shima Aliyu ya bi bayan ta, har suna rige rigen shiga gidan.

Cikin d'akin suka shige da sauri inda Fatima da Suhaima suke, Fatima sai murk'uk'usun azabar ciwo take tana hawaye, yayin da Suhaima take zabga kuka da k'arfi don ganin halin da Innar su take, da sauri Babaa Lantana da Aliyu suka k'arasa inda take, ganin halin da take ciki ne ya sanya Babaa Lantana cewa
"Subhanallah Fatima 6ari ne sannu Allah ya baki lafiya "
Kallon Aliyu tayi tace
"Aliyu kama hannun Suhaima ku fita tsakar gida "
Girgiza kai Aliyu da Suhaima suka yi lokaci d'aya, kafin Aliyu ya iya cewa
"Babaa Lantana kiyi hak'uri ki bar mu a wurin Innar mu "
Itama girgiza kai tayi tare da cewa
"A'a Aliyu kayi hak'uri ku je waje "
Dakyar Babaa Lantana ta shawo kan Aliyu ya kama hannun Suhaima suka fita waje, suna waiwaiyar Innar su, da batasan halin da take ciki don ta fara fita a hayyacin ta.

Bayan fitar su ne Babaa Lantana ta fara yiwa Fatima dabarin su irin na zamanin da, ganin abin yana kok'arin gagarar ta ne ya sanya ta fito waje inda Aliyu suke raku6e waje d'aya, kallon su tayi wani tausayin su ne ya kamata dakyar ta iya cewa
"Aliyu kayi sauri kaje ka kirawo Ladi ungozoma "
Gid'a kanshi yayi sannan ya fita da gudu, ita kuma Babaa Lantana ta koma cikin d'akin wajen Fatima, ta bar Suhaima anan zaune tana kuka.

Babu dad'e wa Aliyu ya dawo Ladi ungozoma tana bin shi a baya, d'akin da Fatima take ciki ya iya nuna mata da d'an yatsan shi, Ladi ungozoma kuwa wadda ke d'auke da k'aramin buhu a hannun ta na kayan aikin ungomanci irin na zamanin da, ta shige cikin d'akin.

Duk yanda suka yi kok'ari wajen kada cikin Fatima ya zube, sai da cikin ya zube sai dai jini yak'i tsayawa sai zuba yake, nan dai ungozoma ta bayar da maganin da za'a jik'a mata ta sha, sannan Babaa Lantana ta biya ta kud'in ta, ta had'a kayan nata ta tafi.

Babaa Lantana sai da ta gyara jikin Fatima tsaf da d'akin, sannan ta kirawo Aliyu da Suhaima don su zo wajen ta, sannan ta tafi gida don d'ebowa Fatima abinci don ba k'aramin gala6aita tayi ba sosai, tun da ba wani abincin kirki take samu ta ci ba, da sannu Allah zai saka ita da yaran ta a wajen Umaru, tabbas yaci amana bai rik'e amanar da Allah ya bashi ba ya azabtar da su, duk don son rai irin shi nashi.

Suna shiga d'akin wajen Fatima suka nufa, zama suka yi a gefen ta gaba d'aya sun zuba mata suna kallon ta tamkar yau suka fara ganin ta.

Kallo d'aya mutum zai mata yasan bata da ishashshan jini a cikin jikin ta, saboda yanda tayi wani fari sosai, gashi ta rame sosai dakyar take iya motsi ma, kallon yaran nata tayu tana daga kwance, wani tausayin sune ya kamata, a hankali wasu hawaye suka shiga zubowa daga idanun ta, bud'e bakin ta tayi wanda ya bushe saman le6en yayi fari tace
"Aliyu ga Suhaima nan koda na mutu ka rik'e ta cikin amana, ina horan ka da ka tsaya tsayin daka ku nemi ilimi, don zama da jahilci bashi da amfani, sannan kada ku ce zaku ji haushin mahaifin ku, ku cigaba da yi mishi biyayya koda ya dawo wajen ku, ku kasance cikin yi mishi addu'a Allah yasa ya gane gaskiya, yasan 'ya'ya rahma ne, komai runtsi ina son ka kasance da Suhaima kada ka guje ta, duk laifin da tayi maka kayi hak'uri kai babba ne "

D'an dakatawa tayi ta had'iyi yawu sannan ta d'an yamutsa fuska saboda jin yanda marar ta take wani murd'awa wa, cikin kuka Aliyu ya kamo hannun ta yace
"A'a Inna baza ki mutu ba, zamu rayu tare da junan mu, don Allah ki daina wannan maganar Inna, hankali na yana tashi wani tunani yana d'arsuwa a zuciya ta sannan gaba na yana fad'uwa "

Wani d'an murmishi Fatima tayi tare da cewa
"Kayi hak'uri d'ana ni kaina bansan dalilin yi maka wad'annan maganganun ba, ina son duk lokacin da mahaifin ku ya dawo ku sanar dashi na yafe mishi duk abin da yayi min, nima kuma ya yafe ni idan nayi mishi wani laifin a zaman mu, Allah ya albarkaci rayuwar ku, Allah ya raya min ku ya baku ilimi mai amfani ya kuma kare min ku a duk inda kuke 'ya'yana, ku rik'e Babaa Lantana da Baba Adamu a mataayin iyayen ku, don mutanen kirki ne kuma zasu rik'e ku tamkar Aliya 'yar su, duk abin da suka baku shawara kuyi amfani da ita don nasan baza su baku mummunan shawara ba Allah yayi muku albarka "

Fatima ta k'arasa fad'in haka tana hawaye sosai, nana Aliyu da Suhaima suka sake fashe wa da kuka sosai, ana cikin Babaa Lantana ta shigo d'akin turus taja ta tsaya ganin su da tayi suna kuka, jikin ta ne yayi sanyi sannn wasu hawaye na tausayin su ya zubo mata, wayance wa tayi tare da fakar idon su don kada su ganta ta goge nata hawayen sannan ta k'arasa inda suke tace
"Haba Fatima taya zaki na saka su a gaba kina kuka suna yi, ke da zaki rarrashe su ki kwantar musu da hankali "
Murmishin yak'e kawai Fatima tayi, nan Babaa Lantana ta rarrashe su dakyar suka yi shiru, sannan ta basu abincin suka fara ci hannu baka hannu kwarya.

Sannan ta d'ago Fatima a hankali ta kara mata kofin madarar shanu mai d'umi a bakin ta, a hankali Fatima take kur6a har ta gama shan kusan rabin kofin, sannan ta zame bakin ta a bakin kofin tana girgiza wa Babaa Lantana kai alamar ya ishe ta.

Sauke kofin tayi a k'asa ta ajiye, tukunna ta d'auko kofin maganin da aka jik'a ta bawa Fatima tasha, bayan ta gama ta kwanta tana mai mayar da ajiyar zuciya, ita kad'ai tasan abin da take ji cikin jikin ta.

Babu dad'e wa bacci ya d'auke ta, fito wa suka yi zuwa tsakar gidan gaba d'ayan su don kada ayi hayaniya ta tashi, Babaa Lantana da Suhaima suka fara kimtsa gidan da yake Fatima bata sangartar da ita ba, tana d'an sata aikace aikacen da zata iya wanda baifi k'arfin ta.

Aliyu kuwa fita yayi a gidan don zuwa neman wani aikin da zai siyo wa Inna lemo da kankana don tasha, tun da yasan mara lafiya yafi son cin kayan itatuwa fiye da komai.

Babaa Lantana tana wanke wanke ne Aliya d'iyar ta ta shigo gidan, nan ta kar6i aikin da Babaa Lantana take yi ta cigaba da yi, gefe d'aya Suhaima nayi mata dauraya.

Lokacin da Farima ta farka daga baccin jikin ta da d'an dama don ta iya tashi taje band'aki da kanta, sai dai har zuwa lokacin jini yana zuba a jikin ta, amman ba mai yawa sosai ba, sai bayan ishsha Babaa Lantana ta tafi gida, ta bar Aliya anan wurin Fatima ko zata na taimaka mata da wani abin a yafi k'arfin Suhaima.

End of Chapter 3Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next