Ciki Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
KUKAN KURCIYA.....👇🏻🤕
*_Shugaban kasa Buhari yayi jawabi mai ban tausayi da kuma sanyaya jikin duk mai hankali, jiya Al-hamis a Bauchi._*
*_A ziyaran da shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kai birnin Bauchin Yakubu, shugaba Buhari yayi jawabai masu sosa rai dangane da makomar Kasar mu Nigeria da tsarin siyasar miyagun shugabanni 'yan jari hujja_*Shugaba Buhari yace: "Allah Ya sani bisa kokarin tunani na shine in tabbatar na dora Nigeria kan mizanin da zaku yi alfahari da ita nan gaba.*
*_Akwai wahala cikin kawo sauyi a Kasa , amma muna jure shi iyakar iyawar mu, ko makiya sun tabbatar mun dauki saiti kan makomar Kasar mu Nigeria, amma 'yan jari-hujja munyi musu laifin da bazasu yafe_*mana ba, laifin shine rufe musu kofofin sata, su ba damuwar su bane Nigeria ta kone ta babbake su sayar da tokan ta su gudu*, *Sun sako mu a gaba yanzu da dukkan karfin su suna bukatar a kyale su su wargaza 'dan abinda muka fara gyarawa.*
*_Basa fatan alheri ko miskala-zarratin wa Nigeria da al'ummar ta_* *_Babu wani zabi gare mu, zabi yana gare ku al'ummar Nigeria, idan kun gaskata kokarin mu ku sake zaban mu mu dora daga inda muka tsaya, hakan zai zama alheri gare ku, idan kuma kun karyata mu ku_* *koma gare su ('Yan jari hujja) su lalata makomar ku da Kasar ku.*
*_Amma tabbas wata rana zaku tuna na fada muku gaskiya, kuma na dora ku akan gaskiya, kuma na rike ku da gaskiya, zabi naku ne, kan makomar Kasar ku ba batun siyasa ce a raina ba wallahi face makomar ku nan gaba.."_*
Jawabin shugaban Kasa MuhammaduBuhari Hafizahullah
kenan.
Alherin Allah Ya kai ga shugaba Buhari
Allah Ka tsare manashi daga dukkan sharri
Allah Ka daukaka darajar sa duniya da lahira
Allah Ka bashi dukkan nasarar da yake nema
Allah Ka zama jagoran sa.
Bilyn Abdull
*_idan kagane ba buhari zakaimawaba, kanka zaka taimaka da yankinka, harma da addininka, Idan har mai hankali zai nutsu to zaigane 'yan arewane keta wannan haukan , saboda son mulki da hanyar Neman yin wawaso akan dukiyarmu kamar yanda suka saba abaya_*
_Wlhy 'yan arewa mu farka, domin kauda mak'iyanmu, wad'anda shekaru aru-aru basu kawo mana sauyi a arewarmuba, kuma wlhy yanzuma yaudararmu sukeyi bazasu gyaraba, shiyyasa suka KASA had'a hannu damai kishinmu sudawo da martabar Yankin mu, burunsu kawai kud'unmu, da mulkarmu_.
_mubar siyasar shirme, mukoma ta cancanta kamar yanda kudancin k'asarmu keyi😭👈🏻_
2⃣0⃣
Sunana na yanka Halematussa'adiyya, kasancewar sunan kakata naci iyayena ke kirana Ameerah.
Ni 'Yar asalin garin sokoto ce, amma yanzu muna zaune da iyayena a Kaduna, nima a Kaduna aka haifeni, mahaifina mutumin kirkine, yanada k'ok'ari wajen kare mana mutunci dukda bamai kud'i baneba.
Ga mahaifiyata kam Sam bahaka baneba, macece mai son birga da son mu'a mullah da hajiyoyin birni.
Mu 5 iyayenmu suka haifa, nice d'iya ta uku acikinmu, yayyena biyu Suwaiba da 'Daheera duk halin mama suka biyo, kuma suna bin hud'ubarta daki-daki, wannan yasa suka tashi a fand'are, abin nadamun mahaifinmu, amma bashida damar tankawa.
Awajena kawai yake samun sauk'i da sassauci, Dan bana k'etare zancensa, ahaka muka kammala secondary, yayinda nikad'aice nayi sauka acikinsu.
Mahaifinmu yakiramu tareda sanar damu mu fido mijin aure, yabamu watanni uku rak.
Nad'an shiga damuwa, saboda bana kula kowa, amma inada samari masu sona, ahaka nafidda Aminullah acikinsu, yayindasu Anty 'Daheera baba nata fama dasu, saida ya tsoratar dasu akan zai saki mama sannan suka kawo mazajen aure.
Ansaka mana biki wata 11 saboda baba yasamu kammala yimana kayan d'aki.
Bikinmu yarage saura wattani hud'u ALLAH yayma baba rasuwa, sakamakon had'arin mota daga Kano zuwa Kaduna.
Mutuwar baba tata6ani matuk'a kuma najigatu nida sauran k'annena biyu baza.
Amma gasu mama da su Anty Suwaiba bahaka bane, domin sufa duniya sabuwa fill, ko arba'in d'in rasuwar baba ba'ayiba mama ta aika gidan samarinmu cewar tafasa aurar damu.
Dan acewarta bamu gama morar kanmuba bazamuje muyita bautawa k'artan banzaba, nashiga tashin hankali Aysha, Dan alokacin auren kawai nake buk'ata kasancewata mace mai yawan sha'awa.
Rashin mafita yasakani dagewa dayawan azumi domin kame kaina daga halaka.
Humm awata ranar laraba nadawo daga islamiyya agajiye saboda inazuwa hadda alokacin, saina tararda su mama sunbaje kud'i afalo suna irga, kud'ine masu shegen yawa, tsoron kud'in yasakani zaro ido waje da tambayar ina suka samu?.
Mamace cikin hasala tace satowa mukayi Dan ubanki.
Shiru nayi, jiki a sanyaye nashige d'aki domin cire uniform d'ina.
Damuwar ganin kud'innan tahaifarmin dayawan kuka, na tabbata bata k'yak'yk'yawar hanya su mama suka samu kud'inba, to amma tambayata itace a ina suka samun?.
Bansaniba, wannan yasaka nasama zuciyata salama, sati biyu da kawo kud'inan akafara gyaran gidanmu, gyara kuma namasu kud'i ahannu, aikam kamar jira 'yan anguwa keyi akafara surutu mahaifiyarmu tasakamu karuwanci, dama shiyyasa ta lalata aurenmu.
Maganarnan tana k'onamin rai, amma banida amsar gamsar da jama'a, Dan nima bansan tushen kud'inba.
Hummm inafad'a miki Aysha ranar saiga wata hamshak'iyar hajiya tazo gidanmu, dakaga matar nan kasan kud'i sungama zaunawa agareta, sunyi maganganunsu da mama, daga k'arshe aka kirani, wai matar nan tad'auki nauyin karatuna zuwa turai, tunda takarduna sunyi k'yau.
ALLAH sairki rashin Sani, sainaita tsallen murna, Dan aganina zanbar gidanmu da abubuwan bak'inciki suka tare aciki.
Cikin k'ank'anin lokaci aka gama mana komai, muka cane k'asar India.
Wannan tafiya itace tazamarmin tushen nadama da Dana Sani. Itace ta wargatsa rayuwata daduk wani tanadina, itace ta zama hajijiya dake wajiga zaren rayuwata ayanzu, tayi maganar tana kuka maicin zuciya.
Aysha ma natayata.
Tacigaba dafad'in munsauka k'asar india, hajia Fanta Ce takawo mu, intak'aicemiki dai bantashi nadama ba, saida john yaketa haddina adaren Dana kwana 2 dashigowata k'asar India, saida suka shayar dani kayan maye a drink sannan yayi yanda yaso dani, nayi kuka nakuma yi bak'inciki.
Ashe ba makaranta zanyiba, kawoni akayi nayi karuwanci kawai, ankawonine domin cin amanar ubangijina.
Abubuwa sun kwa6emin Aysha babu mai lallashina ko tausaya min, tun ina d'ari-d'ari da harkar har zuciyata takarye saboda bak'incikin mahaifiyata nafad'a tsundum, na tabbata tasan komai amma tabadani aka taho dani wata k'asar, Aysha mahaifiyata fa, wadda duk duniya tafi kowa sanin zafina, kaico da hali irin nami Mamana.
Meerah tafashe da kula.
Aysha bata hanataba, saida sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru.
Meerah tace, ayshan shed'anci da shagala yasakani daina sallah, nadaina azumi, na daina karatun alkur ani, dukna maye gurbin wad'annan da shaye-shaye, kwana a club, wlhy Aysha har blue film anta6ayi dani.
Bak'aramar zabura Aysha tayi da jin furucin meerah ba.
Cikin tsoro tace, ''Anty meerah da gaske?.
Murmushi mai ciwo meerah tayi, tacije le6enta nakasa, tareda fad'in humm Aysha kedai abar kaza cikin gashinta kawai, ni k'arancin tunanina nayi hakane dundan aita d'orama mahaifiyata zunubi, tunda itace silar komai.
Girgiza kai Aysha tashigayi, cikin kula tace, "Anty meerah kinyi kuskure, ba'a gyara 6arna da 6arna, kinyi sakaci dakika bar ALLAH, Barin sallah shine mak'asudin ruguza dukkan rayuwarki, barin azumi da karatun alkur'ani sune dalilin haddasuwa k'unci ya yawaita aduniyarki.
Dakinsani kin kar6i k'addararki tafarko saboda fyad'e aka miki, bacikin hankalinki kika aikataba, kifa Sani yanzu ba mama kad'ai ake rubutama zunubiba hardake kanki, tawani fanninma kinfita wlhy.
Anty meerah kituba tunda lokaci bai k'ure mikiba, ki gyara mu'amullarki da ALLAH tunkan yakamaki da azabarsa, kiyi gaggawar farkawa daga nannauyan barcinki tunkan mutuwa tazo ta d'aukeki, wlhy kikabar duniya ahaka wuta zakije, saboda kindaina sallah, kindaina azumi, kindaina karatun alkur'ani zancen ALLAH, Anty meerah banbancin kafiri da musulmifa sallah, duk Wanda yabar sallah yayi asarar daza'a shekara dubu anamasa jaje.
Please Anty meerah😭😭😭😭😭 kicanja, kinada sauran lokaci, karki bari yawuce abanza agareki Dan Alfarmar mazonmu.
Itakanta meerah kuka takeyi kamar zata shid'e, suka rungume juna itada Aysha suna kuka mai cin rai da zuciya, saida sukayi mai isarsu sannan Aysha tafara bana meerah NATA labarin.....
Sosai meerah ta girgiza da labarin Aysha, cikin raunin murya tace, "Aysha sun yaudareki keda iyayenki, babu wani karatu dasuka kawoki ko kula damai ciki, sunkawokine kiyi karuwanci, danki samamusu kud'i.
Nasan hajia kaltume sosai, itama dila ce ta safarar yara, hajia babba cedai gasky ban saniba, inaga sune dillalan zaune masu samo yara subayar, wad'an nan sunfi kowa samun kud'i, Dan inhar suka samo yarinyar za'a d'auki hotonta aturama su hajia fanta, sai sukuma suturama wad'anda ake kaima yaran k'asa-k'asa irinsu Anty Glory kenan, sumafa zasu saka hoton yaranne akasuwa, idan ansamu Wanda yataya to zai biya mak'udan kud'i, hardana jirgi da duk wani cuku-cuku daza'ayi kafin kisamu nasarar baro k'asarki, kinsandai Yanda yankinmu na Africa yagama lalacewa da cin hanci da rashawa, su sunsan hanyar dazasubi abaro k'asar dake, ak'asashen turai kuwa kowaccenmu da abinda yakawota ake sakawa, wasu karatu, wasukuma abubuwane daban-daban, amma mafi yawanmu karatune.
Wannan millions kud'in dasuka tura shine za'aita rabawa tundaga kan iyayenki, dillaliyar data samoki, dakuma wadda zata fiddoki k'asar.
So wani yabiyane kizauna dashi natsawon shekaru biyu ko d'aya, harma uku, wasu kuma sau ma 1 kacal, karki d'auka wai 'yan Nigeria kawai ake kawowa, a'a 'yan k'asashen Africa ne daban-daban.
Wannan shegen john d'in dakike gani, duk yarinyar da'aka kawo shike fara amfani da ita, inhar wajen Anty glory aka kawota, idan yay amfani dake saiya had'aki dawani kuma, dagananfa ke harka tabud'e miki, zakije kiyi harkokinkima kisamu kud'inki kisa ajaka.
Aysha nayadda babu abinda yakai addu'a daraja da kariya, lallai addu'a da maida lamarinki ga ALLAH ya d'oraki akan azzauman nan har suka yanke shawarar kaiki makaranta, Queen tacemin tanada shekaru 13 aka kawota amma wannan baihana john kaca-kaca da itaba, dukdama su yawancinsu dasaninsu sukazo.
Amma kinga ke aranar saiya hak'ura yabarki, wlhy john tantirine dakike ganinsa, kariyar ALLAH ce kawai tahana ya6alle k'ofar yayi yanda yaso dake.
Kicigaba da godema ALLAH.
Sannan kada kisa wasa akaratun dazasu sakani kiyi, kitsaya kiyi domin zai amfanemu.
Insha ALLAH zan ku6tar dake dakud'in Dana tara, kedai kisaka himma, kicigaba da kare mutuncinki, karki biyema k'awaye dansuma suna taka rawar gani wajen wargaza tarbiyya, ballan tanama anan turai da 'ya'yamsu suke 'ya'yan ido, tunda komai kayi su awajensu 'yancine.
More Hausa novels
A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Babban Gida Part 2 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.