Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Ciki Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel
Ciki Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Ciki Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel

Ciki Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel

Author: Bilyn Abdul
Chapter 24 of 41
About 7 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters

*Sosai* suke kiciniya, amma da alama John yabar ayshar ne kawai, Dan k'arfinta danashidai ba d'ayaba.
Aikam saida tagaji Dan kanta tahak'ura saboda galabaitar datayi, sai nishi takeyi da hura hanci.
John yatsira mata idanu yana murmushi, cikin harshen turanci yaja hancinta yana fad'in o baby!, kingafa kin wahalarmin da kanki, ina mamakin yanda zuciyata ke tausayinki da sonki, alhalin banta6a hakan gawata bak'ar fataba, amfaninku agareni naji dad'i daku, Ku nemomin kud'i, kumin bauta.
Amma ke tadabance acikinsu, wani lokacin har nakan fad'a tunaninki, anya ked'in mutum Ce?.
Harara Aysha ta dallah masa da manyan idanunta, sannan tamurgud'a bakinta, da Hausa tace, "a'a aljanace, kuma wata rana bak'ak'en fatar saisun zamemaka dodonni, saika zama bawansu, kud'in dasuka tara maka saisun koma nasu, jindad'in dasuke sakaka saiya zame maka masifa, mugu azzalumi haihuwar asara.
Shiru yayi yana kallon yanda bakinta ke motsawa, burinsa kawai ya d'and'anesa, bajin kalamanta yakeyiba, amma tabbas yanayinta yanuna rashin kunya take masa, amma bai damesaba, jin Aysha yakeyi daban acikin halittu, komai nata na burgeshi sosai, haryakanji kamarma nangaba zai iya aurenta, koyanzu dayakeson d'an d'anar zumarta amatsayin masoyiya zai aikata hakan ba wai Dan kwad'ayiba.
Yamatse Aysha tsam ajikinsa, yayinda itakuma jikinta ke rawa, tana karanto duk addu'ar datazo bakinta.
Abubuwan daya fara mata yasakata dagewa ta gallah masa cizo a damtsen hannunsa.
Uhchhhh! Yafad'a sabodajin azabar zafi, abinka dajikin bature harta hudamasa wajen da mayun hakwaranta.
Amma john yakasa sakinta, kam yarik'eta da d'ayan hannunsa, yayinda yake yarfe Wanda tacijeshi d'in.
Aysha kam sai dariya kecinta ganin yanda yake yatsina fuska dafad'in oooh baby, shiii!!.
Ganin tana masa dariya shima saiyayi dariyan, yad'auketa cak yana fad'in aii saina rama.
Ganin yanufi gado da ita yasakata sakin kuka dabashi hak'uri, amma ko'a jikinsa....

_______________________________
Yaya Fad'ima lfy kuwa?.
Anty Mamie tayi maganar tana kallon mama data dafe k'irjinta tayi shiru ajikin Fright. Dan suna kichinne suna girkin rana, kasancewar girkin mamane sai Anty Mamie ke tayata.
Wlhy Bilkeesu jinayi gabana yayi wata mummunar fad'uwa, ga girata ta haggu NATA harbawa da Sauri tun d'azun, dama da safe nayi wani mummunan mafarki akan AI'sha.
To muyita addu'a Yaya fad'ima, ALLAH yajishemu alkairi, amma ita ayshan tana inane wai nikam?.
Tana karatu.
To mucigaba damata addu'a ALLAH yakare manager ita ako inane.
Jin jina kai mama tayi, ak'asan zuciyarta kuma tanata addu'oi ga d'iyar tata dabatada takamaiman indama take ahalin yanzu, tunda gwaggo bintu bafad'a musu k'asar da ayshar zata tafiba.
Harsuka gama girkin sukuku mama take, haka tanufi d'akinta tayi alwala kasancewar lokacim azhur yayima.
Saida tayi nafila Raka'a biyu, tamik'ama ALLAH kukanta akan yakare mata marainiyar d'iyarta ako INA ta tsinci kanta, tayi kuka sosai a sujuda d'inta, hakama a sallar azhur taita mik'ama ALLAH kukanta...

_____________________________
John NATA bidirinsa da Aysha, wadda har shid'ewa takeyi saboda azabar kuka dakiran sunan ALLAH yakawo mata agaji, saida yakai inda yake kwad'ayin zuwan saikuma yadakata yatsaya yana kallon ayshar ransa a6ace, yaja wani wawan tsaki tareda tureta gefe yasauka a gadon.
Ganin haka yasaka Aysha sauka da gudu tashige bathroom tasaka key.
Dubawa tayi danson ganin miya dakatar da john daga yunk'urin keta mata haddi? Bata ta6a tunanin zata tsiraba kam a yau.
Jini tagani sosai ajikinta, tasauke ajiyar zuciya mai k'arfi da mik'a godiyarta ga ubangijin talikai, lallai ubangijine yayi belin ta tunda ya k'addaro zuwan period d'inta alokacin dabatayima tunaniba, a lissafin tama sai next week yakamata yazo mata.
Takuma k'an k'ame jikinta da john yagama rabata da suturarta, kukan farinciki tak'ara fashewa dashi, saida tayi mai isarta sanan tashige cikin 🛀🏻 tana wanka, yayinda hawaye kecigaba da zirara akumatunta har yanzu. Duk inda hannunta yakai tatuna john yata6a saitace ALLAH ya Isa tsinanne haihuwar asara, ALLAH ya wargaza rayuwarka fiye da yanda kake wargaza ta 'ya'yan jama'a, ya ALLAH kahana wannan kafirin farinciki arayuwarsa😭, dagashi harsu hajia babba.
Sama sama take jiyo kuka, wannan yasakata tsayawa tsam tana saurare, jitaifa da gaske kuka akeyi acikin d'akin, saita fito daga cikin kwamin wankan tazo jikin k'ofa tana lek'awa tajikin 'Yar k'ofar da'aka tanada domin hakan.
Zaro manyan idanunta tayi waje tana fad'in innalillahi Ngozi!.
Amma john d'innan mugune.
Tarintse idanunta tausayin yarinyar nasake shigarta, jitake sautin kukan Ngozi tamkar ana watsa mata garwashin wuta a sassan jikintane.
Yarinyar sai kiran Jesus takeyi da dadynta harda momy da brother d'inta, saboda azabar datakesha a wajen john.
Ganin tadamasa da Sha'awar da Aysha tayi, gashi kuma tana period, shikam yanada k'yank'yami, wannan yasaka yabar ayshar, to amma bazai iya hak'uraba, saiyasa aka kawo masa yarinyar da Anty kubra tazo da ita shekaran jiya, wadda zasuyi kaid'aya da aysha, dafarko yarinya tayi muk'uy tana jin dad'in wasanni da john keyi da ita, shiyyasa Aysha batasan wainar da'ake toyawaba sai ihunta taji kawai.
Haka Aysha takasance, ita kuka a bayi Ngozi kuka a hannun john, har saida taji shiru sai shashshekar kukan Ngozi kawai.
Cikin sand'a takuma lek'awa kamar muna fuka, saitaga babu john ad'akin sai Ngozi dake kwance share-share kamar sabuwar gawa.
Ahankali tabud'e tafita bayan tasaka farar rigar wanka, tanad'e kanta da k'aramin towel.
Koda taga halin da Ngozi take ciki saita durk'ushe takuma sakin kuka mai tsuma zuciya, dayanzu ita john yayma wannan cin mutunci, dayanzu ita ya kacaccala haka kamar saniyar watanda.
Ngozi sai d'aga ma Aysha hannu take alamar ta taimaketa, muryarta ko fita batayi sosai saboda ihun datasha.
Aysha tamatsa kusada ita tana cigaba da zubarda kwallah, ahankali takamata Ngozi tayunk'ura zata tashi, azaba tasakata kiran Jesus!!!!!!!!!.
Itama Aysha saita kwalla k'ara kawai, danta tsorata.
Adaidai lokacin Anty glory da Lola da Anty kubra suka shigo d'akin dagudu, yayinda meerah datasha uban kuka take binsu abaya, Dan ita azatonta angama wargaza tanadinta akan Aysha.
Gaba d'aya su Lola suka kwashe da dariya ganin abinda ke faruwa.
Amma banda meerah data nufi Aysha tana fad'in my lil miya faru dake? Miya faru? fad'amin.
Jikin meerah Aysha tafad'a tasaki kuka, cikin kuka tace, "babu komai Anty meerah, amma jibi yanda yakusa kashe Ngozi, k'aramar yarinya saboda z......
Da sauri meerah ta toshe bakin Aysha gudun kada tamusu bankad'a, Dan furucinta daidai yake da Dana Sani.

Anty glo.....tadafa bayan Aysha tana dariya, sholy kardai ki rud'a kanki, nasan kema gab kike dakar6ar irin wannan sak'on, dakin hak'urama yamiki yau dayanzu kin wuce wajen, nakula tsorone dake.
Shimadai mamakin d'aga miki k'afar dayakeyi nake wlhy.
Babu Wanda ya tanka tsakanin Aysha da meerah.

Lola tad'auki Ngozi zuwa d'akinta, danta taimaka mata wajen kimtsa jikinta, su Anty glo...kuma suka fita suna dariyar shak'iyanci.
Aysha tarakasu da harara da tsinuwa azuciya.
Zanin gadon dayay kaca-kaca da jini meerah tafara nad'ewa zuciyarta Na k'una.
Aysha tace, ''gsky Anty meerah bazan kuma kwana a bedsheet d'innanba, kawai asakashi abola.
Shiru meerah Tamata, Dan ita hankalinta yatafine ganema musu mafita domin ku6tar da ayshar.
Ganin Anty meerah bata tankaba itama Aysha saitayi shiru...

____________________________
Wlhy band'auki kud'innanba, kuji tsoron ALLAH yarannan, dagirmana kudinga muzantani, har abin yakai yau da d'oramin sata? Gwaggo bintu tak'ara maganar da fashewa da kuka.
Baki Najwa tamurgud'a mata, yo inbake kika d'aukaba wanene? Momy dai tasan bamu ta6a mata sataba ehe😏.
Hakamasu Ebera basu ta6amana sataba saida kikazo gidannan akayi yau, Dan haka wlhy kifiddama momy kud'inta kafin muyi miki 'Yar zazzage.
Gwaggo bintu tafashe da kuka tanata rantse-rantse, su Huzaifa kam sai k'yalk'yata dariya sukeyi sunga gwaggo bintu Na kuka.
Anty zuwairah tace jeki, anjima zan nemeki.

Kamar munafuka haka gwaggo bintu tafita tana kuka, wai yau yaranda tayi jikoki dasune suke cimata mutunci, itadai wlhy zanman gidannan ya isheta, gara tasan abinyi, wlhy barin gidannan zatayi bazata zaunaba, anya kuwa ba hak'k'in marainiya baneba yafara kamata?.
Can gefe tasamu tanata kuka, da dana sanin kuskurenta, gashinan tanaji tana gani zaman gidan datakejin dad'i ya gagareta, shiyyasa akace *_CIKI DA GASKIYA WUK'A BATA HUDASHI!_* lallai wannan zance gaskiyane, inhar kanada gaskiya komai rintsi hankalinka a kwance yake.
Ita gata rashin gaskiyar yahanata kwanciyar hankali.😰
Yanzu miye mafita? Kodai taje Kano tafad'ama mama gaskiya? Asirinsu hajia babba ya tonu kawai.
Kai wannan gangancine kuma, su hajia babba sunfita k'arfin aiko a k'asarnan, Dan sunada d'aurin gidi sosai, gasu masu arzik'i, kada taje reshe ya juye da mujiya kuma.
Kai yanzu miye mafita?.
Wata zucia ta
ce addu'a.
Hakane kuma tafad'a tana kad'a kai.

_____________________________

John kam yak'i tafiya yana nan, jira yakeyi Aysha tagama period danya d'auki alk'awarin cika burinsa awannan karon, ganin Surar Aysha yasa bazai iya d'aga mata k'afaba.

End of Chapter 24Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next