Ciki Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
_____________________________
Agidam baffama yau gwaggo bintu da Anty zuwairah da yaran ta sukazo daga Lagos.
Gwaggo bintu dukta fita hayyacinta, gawani uban bak'i datayi, daka ganta kasan tanashan bak'ar wahala a hannun Anty zuwairah.
Ita kanta hajia babba kasa hak'uri tayi, saida tacema Anty zuwairah shin bintu ciwo tayi agidankine zuwairah?.
A'a Momy mikika ganine?.
Naga dukta fita hayyacintane cikin shekaru 2½.
Baki Anty zuwairah ta ta6e, wlhy mamy tak'idai kwantar da hankalintane, amma ban rageta da komaiba, kullum hankalinta yana gidannan, shiyyasama nakasa hak'uri zuwa lokacin meeting d'in Na tattata muka taho tunda dadyn Najwa ba yanan, kartaje ta mutumin agida.
Momy bata sake cewa komaiba.
Itama gwaggo bintu tuni ta lalla6a zuwa 6angarensu Na 'yan aiki, Dan batada cikakkiyar lafiyama, ko mutamen gidan bata shiga gaida kowaba.
Yaranma duk basa nan, masu aiki sun tafi, masu zuwa makaranta sun tafi, Ammah kuma tana Jigawa ma ita, mama da Anty Mamie kam kowacce tana'a 6angarenta, umme amarya Na wajen aiki itama.
Matansu ya Sultan ma suna nasu 6angare, dan ba kullum suke shigowa cikin gidanba dama.
Su iya hama duk sunyi mamakin ganin yamda gwaggo bintu tafita hayyacinta, amma basuda ikon tanbaya, Dan damacan tsoronta sukeji, bishirah ce taita bama gwaggo bintun kulawa, (itama tazama budurwa sosai) harma ansaka mata ranar aure, zata auri wani d'an uwansu a can Kaduna. Amma zai zauna da'ita a Suleja, anan yake 'yan kasuwan cinsa...................✍🏿
*_Fatan alkairi agareku, inafata ansha bikin sallah lafiya?, ALLAH ya maimaita mana ta bad'in bad'ad'ad'a, Yakuma gafarta mana ayyukanmu Marasa k'yau dasuka wanzu a cikin wannan shekarar, ALLAH ka gafartama mahaifanmu, ka yace musu, kabama marasa lafiyarmu lafiya, muda Muke da ita ka k'ara mana, ALLAH ka yaye ma kowa damuwarsa, ka kawo mana sauk'i cikin al'amuranmu Na yau da kullum, ALLAH ka d'ora musulinci akan kafirci, ka karya kafirci da kafirai, ka d'aukaka musulinci da musulmai, katsare mu muda addininmu daga hannun azzaluman duniya, ALLAH kaza6a mana shuwagabanni nagari, ka k'arama shugaban k'asarmu lafiya, ka kareshi ga dukkan Sharrin masu burin cutar mana dashi, ya ALLAH ka zaunar da k'asarmu lfy, ka shirya al'ummar musulmai Baki d'aya, kabamu damina mai albarka, ka tsarkake mana zukatanmu duniya da lahira._*
Ameen ya rabbi🤚🏻✋🏻😭
Barkanmu da dawowa, acigaba da gashi my Guy's😚😉.
😘😘😘
[8/24, 8:20 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_*
🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜
*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭
*_part 1_*
(littafi na d'aya📕)
_wannan gaisuwa takuce ku kad'ai 'yan group d'in *CIKI DA GASKIYA FAN'S* sak'onninku na isowa agareni, ina yinku 100%, ina sonku wallah, alkairin ALLAH yakai gareku._
😘😘😘❤❤
3⃣3⃣
Kwanan sa kusan uku kenan da dawowa k'asar amma baije gidaba, saboda wani aiki daya rik'eshi, wani mutumi sukesan kamawa, kuma yanada had'arin gaske, kasancewar sa tsohon d'an ta'adda.
Sun d'ana masa tarko sosai tun wajen wata 5 daya wuce, har yanzu ALLAH baisa ya fad'a a tarkonba.
Mutumin a Rivers state yake, cikin port-harcourt.
Cikin shirin Uniform d'in police interpol yake, yaukam da bindugu biyu yafito, kokad'an fuskarnan babu alamar sassauci, duk lokacin da ya khaleel yad'ora hular aikinsa yakan k'ara kwarjini da cikar haiba👮🏼♂.
Sosai Uniform kemasa k'yau, gashi dogo mai suffar k'arfi masha ALLAH, cikakken training daya yasamu yakansaka suffarsa tsorata mazanma ba mataba kawai, ga tsare gida irinnan jaruman ma'aikata nagartattu.
Cikin Nutsuwa yake tafiya, wadda hakan tamkar halittarsace, komai ya khaleel zai maka anutsuwarsa yake, komai zafin daya d'auka awajen aiki ko rikiCewar abubuwa kuwa.
Bayansa Joseph ne da Youseef, Samuel, Adams, Taheer, saikuma mutum uku wad'anda bansansuba kam, da alama dai cikin k'ananun ma'aikatan suke.
Da sauri d'aya aciki yabud'e masa motar, harya taka zai shiga saikuma yajuyo yana kallonsu, in serious tone yace, ''komai zakuyi kuyi da kula, saboda anguwar tanada jama'a, banason aikinmu yashafi wani mara laifi, so Ku kula.
Kowa zaiyi tafiyarsa shi kad'aine, Adams shiga muje.
OK sir!!! Suka fad'a tareda Salutes nasa.
Batareda maida murtaniba yashige motar ya zauna abaya, yayinda Adams & Emanuel ke a gaba.
Kwantar da kansa yayi jikin kujera ya lumshe idanu, addu'oin Neman nasara ga ubangiji kawai yakeyi, yayinda gefen zuciyarsa take masa hasashen idan ta kwa6e ko ansami nasara.
Daka gansa kaga tibiran mahaukaci, kokad'an babu wata hujja dakakeda ita wadda zaka nuna rauninsa da amsa sunan mahaukacin, zaune yake kusada wani mai shayi Wanda yakasance ba haushe d'an balaguro, gefe d'aya kuma mai gasa naman tsirene da balangu, dandazon matasane awajen anata hirar duniya, wasu ta siyasa wasukuma ta yanayin rayuwa, harma da masu ta ball.
Wani matashin saurayi dayaci indome yarage yamik'e zuwa gaban mahaukaci daketa zane-zane ak'asa, kaikace lissafin kud'i yakeyi kona shekarunsa.
Mik'a masa filet d'in yayi, babu musu ya kar6a, saidai maimakon yaci, saiya juye cikin bak'ar ledan buhu datake hannunsa akowanne lokaci, yamik'ama matashin saurayi filet d'in yana tuntsura dariya.
Girgiza kai kawai matashin saurayi yayi yakoma rumfar mai shayi ya zauna.
Wani yace nifa kunsan wani Abu?.
Akace a'a.
Tunda mahaukacin can yazo wajennan, kimanin watanni uku kenan, banta6a ganin yaci abinciba, komi zaka bashi saidai yazuba abuhun ledar can, kuma kullum anan yake kwana.
Wlhy gaskiyanka ne, amma k'ila yanaci mune bama maida hankali shiyyasa bama ganewa.
Wani yace, nifa tausayi yake bani, ruwan shekaran jiya duk akansa yak'are.
Wlhy haka yakeyi, ammafa ni a kwanakin baya sonayi nad'an rud'e, sainaga mahaukacin daya fara zama awajennan tamkar yafi wancan d'in suffar k'arfi dad'an tsawo? Danni farkonma zuwansa ban yarda mahaukaci baneba.
Ashe bani kad'ai nakula da hakanba, kasan ALLAH nima sainake ganin tamkar ba wannan baneba Wanda yafara zuwa, ni wannanma baifi sati 2 ba nafara ganinsa anand'in, saikuma na daina ganin wancan.
Kudai kuna masa kallon tsorone, k'iladai aljanunsa ke canjashi, wani matashin saurayi ne mai wannan maganar, tun d'azu kuma baisaka baki a hirarba sai yanzu, yanata danna waya abinsa.
Jin shigowar sak'o yasaka ya khaleel bud'e shanyayyun idanunsa, wayar yad'auka yaduba, cikin d'an rikita yace, "Adams akwai matsala kenan?".
Da sauri Adams yace sir! Matsalarmi kuma? Naga komai yana tafiya yanda muka tsarashi.
Hakane, amma wai mutanen wajen sun fara tantama akan Mahfouz, yanzu katura masa sak'o yabar wajen, yaje inda muke had'uwa zanzo na samesa.
OK sir!, Adams yafad'a yana k'ok'arin tura sak'o da wayarsa.
Sunata hirar mahaukaci, Wanda ko alamar yasan misuke fad'a baiyiba, kamar an tsikaresa sukaga yatashi yana lalube-lalube abuhunsa, barin wajen yayi yanata surutai kamar yanda yasaba, babu Wanda yadamu dabarinsa wajen, harya 6acema ganinsu.
Mintuna kamar 20 dabarinsa wajen saigashi yadawo, yanata 'yan surutansa, yakoma inda yasaba zama ya zauna.
Mai Nama yace kai jama'a, ALLAH kuwa nafara gaskata maganar guy d'incan daya tashi, kugafa mahaukacin nan yanzu.
Suduka kallonsu suka maida kansa, yanata zane-zane ak'asa, mai shayi yace kakula yanzu kuma yad'an k'ara tsaho da k'iba, kai aljanima shaid'anine, babu abinda baya iyawa, kai Malam wannan bawan ALLAH da k'alau yake aii wlhy bak'aramin namiji za'ayiba.
Gsky kam, irin wad'annan suka damk'eka aii saidai lahira Dan babu mai kwatarka kuwa.
Suna cikin hirar mahaukaci saiga wasu ratsa-ratsan motoci sunshigo anguwar.
Wannan bawani sabon Abu baneba ga 'yan anguwar, akwai wani gida kad'an da rumfar mai shayin, kullum haka suke ganin manyan motoci nashigi da fici agidan, kowa yasan wani gawurtaccen tantirine agidan, amma kasancewar baita6a cutar da 'yan anguwarba shiyyasa ba'a damu dashiba, ko police shakkar zuwa anguwar sukeyi, Dan sosai ake tsoron anguwar a garin na port.
Kallone yakoma sama lokacinda mahaukacin nan yaje gaban motar farko yakwanta a akan titin, sunyi horn d'in duniya yak'i tashi, ganin haka boss d'in yafito a fusace.
Hakama dukkan yaransa da bodyguard d'insa.
Har d'aya ya saita bindiga zai harbeshi boss ya dakatar dashi tahanyar d'aga masa hannu.
K'arasawa yayi gaban mahaukacin yana lek'en fuskarsa.
Wata wawura mahaukaci yayma boss.
Kunsan abin mamaki da al'ajab😨😨kuwa??.
Bindigace a hannun mahaukaci ya saita kan boss d'in dashi, yayinda yake fad'in kuna motsawa saina alburushe kansa wlhy, kowa ya ajiye bindigarsa.
Shiru sukayi basu ajiyeba, kowa sai huci yakeyi, 'yan anguwa kam anyi irko-cirko ana kallon ikon ALLAH, masu tsoro kuwa tuni sunsha agida.🏃♀
Boss d'in ya jinjinama yaransa kai alamar su sauke bindugunsu, wasu sun ajiye, amma wasu basu ajiyeba.
Alokacine matashin saurayi mai cewa aljanu suke canja mahaukaci yak'arso wajen, yagaggun kayan yafara yagewa daga jikin mahaukacin.
🤥Bakowa baneba face ya khaleel, k'asan kayan haukarsa kam Uniform d'in aikinsane, sai alokacin su taheer da police masu yawan gaske suka fara fitowa daga ma6oyarsu, nanfa aka fara musayar wuta, tsakanin 'yan ta'adda dasu ya khaleel.
Kowa Yakama gabansa yana Neman ma6oya, bakajin komai a anguwar sai k'arar harbe-harbe ketashi.
Wai idan bakayi bani waje, inji masu iya magana.
🏃♀🏃♀🏃♀🏃♀.
Misalin awanni biyu aka d'auka anguwar a hargitse, ansamu nasarar kwamushe wasu yaransa, wasunsu kam an iza k'eyarsu barzahu, wasu kuma sun sami harbi da raunuka, acikin 'yan sandama wasu sun sami harbi, wad'an da aka kama duk aka zubasu amotoci, Ambulance 🚑kuma takwashe police d'in dasuka samu rauni, Dan dama da guzurunsu sukazo.
Saida ya khaleel ya tabbatar an kammala iza k'eyar kowa sannan, shida sauran jiga-jigansa irinsu Adams kawaine awajen, Samuel yasamo masa ruwa yafara wanke fuskarsa daya shafe da bak'in Abu, hakama Mahfouz.
Sai asannan 'yan anguwar sukad'an fara fitowa, suma masu k'arfin halin kenan.
Sun shiga cikin gidan, bincike sosai sukayi, dukkuwa abinda suke buk'ata sun samu, suka fito kowa yanufi mota.
Sai kallonsu akeyi, wani yace, "wlhy ko rantsuwa zanyi babu kaffara aciki, wancan (ya khaleel) shine Wanda yafara zuwa wajennan a matsayin mahaukaci, sati biyune dasuka wuce aka canja da wancan (Mahfouz).
Gaskiyar ka wlhy, hakane.
Ya khaleel dake jinsu yayi murmushin k'asaita, sannan yataka yashige motar da'aka bud'e masa.
Tabbas ya khaleel ne yafara zuwa a matsayin mahaukacin, sati biyu dasuka wuce wani aiki yataso masa zuwa Saudia shine Mahfouz ya maye gurbinsa.
Tunda suka tafi kwance yake kawai ajikin kujera, duk abinda yafaru sai dawo masa yakeyi azuciya tiryan-tiryan, lamarin tamkar shirin film ko novel, baita6a tunanin zasu samu sauk'i hakaba wajen kama tantirinnanba saboda had'arinsa, amma Alhmdllh ALLAH ya sauk'ak'a komai, dukda and'an sha gimurzu dai.
Ahaka suka isa hotel d'in dasuka kwana, kafin da yamma jirginsu ya tashi zuwa Abuja.
More Hausa novels
A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Babban Gida Part 2 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.