Ciki Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
______________________________
Da yamma meerah takira Aysha akan sun dawo, zuwa anjima zasuzoma nan gidan su gaida su mama.
Sosai Aysha take farinciki, dantayi missing d'insu sosai, da murnarta ta sanarma mama da yaya fadeelah.
Suma sunyi farinciki, dandanan aka shirya abincin tararsu.
Bayan sallar magriba kuwa saigasu, Aysha da Ifteehal da anty meerah suka rungume juna, sunacike da murnar sake had'uwa, tasakesu takoma kan mom, itama tayi kewar ayshar, su Safwan ma suka rungumeta, ya Naufal yanata murmushi dabin Aysha da kallo.
Saida tagama murnar ganinsu sannan tace ya Naufal I miss you.
Oh sai yanzu kika san dani?, kofa kirana awaya bak'yayi?.
Hannu tasaka tarufe fuskarta🙈, sorry yayana, amin afuwa, wlhy murnar ganin su mamane ya mantar dani.
Maheer dake gefe shida shakur yace habawa yarinya, ALLAH saina rama nima.
Wayyo ya Maheer d'ina, inata kewarka, inata kewarka kamar nayi tsuntsuwa nazo Kd.
Bakinsa yata6e yana mata hararar wasa, to sarkin tsari, nibama wajenki nazoba dama, mama nazo gaidawa.
Aff nasan saikamafi kowa kewata ALLAH, dojewa kawai kakeyi.
kafin yabata amsa Shakur yace beauty kin k'ara k'yau da girma.
Ita saima yanzu tagansa, gidan su yazo, shiyyasa bazata masa wulak'anciba, tayi y'ar dariya tana kallonsa, da gaske ya Shakur?.
ALLAH kuwa beautyna.
Baki tad'an ta6e taigaba tana kar6ar Raudat dake hannun ya Naufal.
Dad da baffah suka k'araso, daka gansu kasan sunsan juna dama.
Mazan 6angaren baffah suka shiga, matan kuma 6angaren Anty Mamie, dan tace itace uwar y'ar.
Ansha hirar yaushe gamo, yayinda su mom suka saki jiki dasu mama saboda tarbar mutunci dasuka samu.
Aysha taja anty meerah d'aki ta zayyane mata komai gameda Auren mama da baffah.
Sosai meerah tayi murna, tace yauwa Aysha wannan shine matakin farko nacikar burinmu, amma ina gwaggonki?.
Nima Tunda nazo gidan bangantaba, bankuma tambayaba, kinsan abin saida taka tsantsan, yanzudai sonake nafara ganin Bishrah, awajentane kawai zansamu dukkan bayanan danakeso.
Gaskiyane, ammafa nayi farinciki da kowa yakasa ganeki agidanan.
Wlhy nima haka Anty meerah, hakan yana cikin nasarar aikinmu shima.
Aikamdai, ya khaleel fa?.
Baki Aysha ta ta6e, yana nan shima, Aysha takwashe yanda sukai dashi a shoprite dakuma had'uwarsu agidan.
Dariya sosai Anty meerah tayi, lallai Aysha kinyi jarumta sosai, ammafa karki yarda yasan kina sonsa, ki kama kanki sosai.
Tab yo Anty meerah hauka nakeyi, rashin kunyarma dakiga ina masa ganinai yana Neman shiga hancina, amma karki damu zan sake takune, saidai damuwata mama da kawu bilyamin.
Wai bazanje bautar k'asaba aure za'amin, ni basusan inada buruka agabanabane.
Dariya meerah tayi, cikin tsokana tace, kawai kice ya khaleel yafito musha shagali abinmu💃🏻.
Kai Anty meerah, kema hadake ko?, nifa koda nake sonsa bawai inason aure baneba yanzu.
Hhhhh to shikenan maida bakin, yanzu dai kawo kunnenki kiji wani Abu.
Matsawa Aysha tayi, cikin rad'a meerah takema Aysha magana, wannan yasa banji misuke magana akaiba🤕.
Fitowata nayi nabarsu awajen.
A 6angaren su baffah kuwa sunata hirarsu da dad, sunsan juna tuni, baffah yakira ya khaleel awaya yazo suka gaisa, dad sai mamaki yanda khaleel d'in yakoma yakeyi, Dan rabonsa dashi tun bai wuce 18years ba.
Dad yace andai ajiye iyali ko?.
K'asa ya khaleel yayi dakai yana murmushi.
Baffah yace baiyiba, inata fama, amma kuma insha ALLAH Ana gab dayi.
Da sauri ya khaleel yad'ago yana kallon baffah, cikin tsinkewar zuciya ya maimaita maganar ta baffah a zuciyarsa, _ana gab dayi!_, to gabda yin me?.
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un kawai yake maimaitawa, baffah yana lura da halin dayake ciki, aransa yayi dariya yana fad'in d'an jakar uba aii maganinka zanyi wannan karon.
Tundaga nan ya khaleel yadaina saka baki a hirar, dama can eh, a'a Ce maganar tasa.
Sai around 11 suka bar gidan, tuni sabo yashiga tsakaninsu da mutan gidan, kowa yayi aboki kuma.
Aysha harda 'yan kwallanta, taso ace tafiyar dazasuyi Sokoto gobe harda ita aciki wlhy.
Bayan tafiyarsu suka dawo d'aki, mama sai yaba kirkin bayin ALLAHN takeyi, suna d'an hirar zuwan bak'in wayar mama tayi wringing.
Ummah ce, Dan haka tad'auka da murmushi, Yaya ina yini? Kune da daddare haka?.
Wlhy kuwa fad'ima, ya yarana?.
Lfy lau suke, duk gasunan muna tare dasu, bak'i akayi yanzu suka tafi, mama tabama Ummah labarin zuwansu mom.
Sosai Ummah taji dad'in hakan.
Ummah tace munfara maganar bintu dake d'azu wayata tamutu, shiyyasa nakasa hak'uri nak'ara kiranki yanzu.
Au wlhy kuwa Yaya, tana nan babu lfy, abinda yasa kenan banmata maganar Aysha ba, sonake ta warke, Dan inason jin wasu bayanai daga gareta, Dan tareda Bilkeesu mukaje dubata ranar, shiyyasama nakuma k'yaleta.
Hummm abin mamaki, yakamata kam ki bincikar mana ita, kidubafa tunda tatafi da yarinyar nan bata kuma zuwa kano ba, kuma kince tunda kikaje gidan baki ta6a ganintaba.
Wlhy kuwa yaya, shiyyasa kawai naji yakamata nasan wani Abu, sainake ganin kamar kawai lauje cikin nad'i bamu saniba, tunda tace mai gidanne yabiya kud'in karatun, harma da y'ay'ansa ciki, kuma banga wannan alamarba, hasalima babu Wanda ya nuna yasan Aysha agidan.
Lallai maganarki gaskiya akwai lauje cikin nad'i, yanzudai bara nabarki saida safen.
Ki gaishe da jama'ar gidan.
To zasuji yaya, nima agaidamin yarana.
Bayan sunyi sallama fadeelah tace mama wai miya farune?.
Babu komai fadeelah.
Ina ayshar kuma?.
Tashiga wanka.
OK, kijeto ki kwanta, nasan k'awayen naki nacan nazuba ido.
Jin jina kai fadeelah tayi, tamik'e, dama ummuhanee nawajensu Hamdiyya, tafita zuciyarta na waswasi akan abubuwa dayawa, saidai batasan yazata kama lamarinba harya zama hujja agareta.................✍
❤❤❤❤😘😘😘😘😍
[8/29, 6:44 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_*
🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜
*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭
*_part 1 🔚_*
(K'arshen littafi na d'aya📕)
*_Alhmdllh masoyan ciki da gaskiya, wannan shafin nakune aduk inda kuke, ngd sosai da k'aunar dakuke nunama buk d'in, ALLAH yabar zuminci, nima ina sonku da k'aunarku over wlhy._*
❤❤❤❤😍😍😍😍😍😍😍😘😘😘😘.
4⃣0⃣
Duk zungurar da mama tayima Aysha adaren jiya saboda gwaggo bintu, Aysha tak'i cewa uffan, kuma tadage akan ba nan gidan suka zaunaba sanda ta d'akkota.
K'yaleta mama tayi, Dan batason Aysha ta fahimci wani Abu, saidai batasan ayshar tagane komaiba.
Saidai tunaninta ina gwaggo bintun?.
Washe gari bayan sun kammala break fast Aysha tazare jikinta zuwa 6angaren masu aikin gidan, shiga tayi tamkar mai neman wani Abu, Rabi da iya hama kawai ta taras a falo suna kallo, aranta tace ana nandai da hali.
Suna ganinta suka hau washe baki, Rabi tace ko ana kiranmu ne?.
Murmushi Aysha tayi, cikin basarwa tace, "a'a, kawai zan wuce garden ne najiyo dariyarku, shine nace bara Nagano miya baku dariya haka?.
Iya hama tagyara zama tana fad'in wlhy babu komai. film ne muke kallo.
Aysha takalli TV n, Indian hausane suke kallo, batace komaiba tafito, can cikin garden tashige, takira wayar Anty meerah, bayan sun gaisa ta shaida mata bataga alamun gwaggo bintu na gidanba, Dan d'akinta arufe yake, kuma bataga bishirah ba.
To Aysha wakike ganin zaki tambaya batareda ya zargi komaiba?.
Tab aikam hakan zai zama Matsala, danni bansan mi mama keson ganowaba, jiyafa titsiyeni tayi damuka kwanta.
Tofa, saifa munlura sosai, Dan inhar suka gano dakansu za'a wargaza mana aiki. Kiyi k'ok'ari Sanin Inda gwaggo bintu take ko bishirah, sune kawai murfin rife sirrinmu, Dan su hajia babba hatsibi baine.
Karki damu zan k'ara himma insha ALLAH, k'arfe NAWA zaku wuce birnin Shehu?.
Saida yamma ma, zamubi jirgin 5pm ne.
OK zankiraki, ammafa dole musake secret numbers, wasu zasu iyamana bincike a wayoyi su wargaza mana aikinmu Anty meerah.
Nima nayi tunanin haka Aysha, amma kibari mudawo daga soskot.......
Motsin dataji abayantane yasakata saurin kashe wayar, tajuyo da sauri, gabantane yafad'i Dan ganinsa tsaye abayanta, hannayensa zube cikin aljihun wandonsa Na bak'in jins, yanda yakafeta da mayun idon nan nasane yasakata aro sabuwar nutsuwa ta yafama kanta, sannan ta had'e fuska tareda kauda kai daga kallonsa.
Mamaki tabasa, yarinyar abubuwanta sunfara bashi tsoro, kullum da Sabon salo zaka ganta, yaukuma a sahun munafunci yaganta, yo idanba munafinciba mizai kawota k'arshen garden yin waya? Duk yawan d'akunan gidan.
Ra6awa tayi tagefensa zata wuce yace, "k!.
Shiru tamasa tacigaba da tafiyarta.
Tsawar daya Daka matace tasakata tsayawa cak, bak'aramin wakitawa y'an hanjinta sukayiba, damacan dauriya takeyi, Dan atsorace take da tunanin koya ji mitake fad'ane, dama akuma kamar yana mata zargin wani Abu daban, tunda ranarma ya tambayeta ko an turota lek'en asirinsane?, hawaye suka cika mata idanu, amma tayi jarumtar tsaidasu.
Batasan yak'araso Inda takeba, saida alamun tsayuwarsa taji kusada ita, wannan yasakata d'an d'agowa tasaci kallonsa, idanunsa k'yam akanta, ahankali ta janye NATA tareda lumshesu.
Shima saiya kauda Kansa daga kallonta yana furzar da huci abakinsa.
Baki yabud'e zaiyi magana wayarsa data fara wringing takatsesa.
Cirota yayi daga aljihun wandonsa yakara akunne.
Hello Youseef miya farune?.
J! Kana inane?.
Ina gida mana, miya faru kake magana akid'ime haka?.
J! Kayi sauri, ina k'auyen Dutsen Alhaji, nabiyo bayan Barau modibbo ne, please kayi Sauri.
What!!, barau modibbo fa?.
Kasan mikake fad'ama? da gaske kakeyi kuwa?.
Wlhy da gaske nakeyi j!, tundaga airport nake binsa, naje raka Abbah zai tafi Egypt ne, naga Barau modibbo ya sauka a jirgin dayazo daga Spain.
OK OK ina zuwa, kakira su Ema.... Kace muhad'u acan, basai sunzo d'aukataba zanje dakaina.
Da sauri ya kalli Aysha dake tsaye har yanzu tana sauraren wayar tasa, please maza d'akina cikin drowan gefen gado ki d'akkomin bindiga da key d'in mota, maza da sauri.
Yama manta waya aika, saboda akid'ime yake.
Hajia babba dake k'ok'arin shigowa garden d'in tatsaya cak, jin wayar da ya khaleel keyi tayi mugun kid'imata, ta maimaita sunan cikin matuk'ar razana, *BARAU MODIBBO!!* lallai yau k'arya zata k'are musu, umarnin dataji yana bama Aysha ne yasakata juyawa da sauri 6angarenta, akid'ime tad'auki waya tashige bedroom d'inta, harda kullewa, wayar hajia Khaltum takira, number busy.
Tasaki wani irin tsaki, jikinta har rawa yakeyi.
A hanzarce Aysha tadawo d'aukeda guns guda biyu, ta lullu6esu dawani hanky d'insa gudun kada wani yaganta.
A harabar gidan ta isakeshi yana yaye tamfol da aka lullu6e dawata azababbiyar mota mai k'yau da tsari.
Ya kar6a cikin hanzari, yashige motar, aguje yafigeta, ganin haka d'an gwari yabud'e gate da sauri.
More Hausa novels
A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Babban Gida Part 2 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.