Ciki Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
####
Suma dai su Aysha karatu natafiya musu yanda yakamata Alhamllah kam, Aysha ank'ara girma sosai, tazama big girl abinta, yanzu tana shekara ta 16, takusa shiga 17. Amma idan kaganta saika d'aukama takai 18 saboda jindad'i da kwanciyar hankalinsu data samu, takanyi tunanin gida, wani lokacin takansha kukanta saboda kewar su mama da 'yan uwanta, meerah da ifteehal sukan lallasheta danuna mata ladan mai hak'uri, aganinsu aii komai yazo k'arshe, tunda Dady yace dasun kammala karatunsu nanda shekara 1½ dakansa zai maidasu Nigeria, wannan yasama Aysha tak'ara maida hankalinta sosai ga karatun.
Bata kula kowa, Dan it's ko aboki namiji batashi a school, inhar baka ganta tareda ifteehal ba to zaka ganta tana karatu ko latsa waya, Maheer ne kawai Aysha take sakewa dashi bayan Naufal data d'auka amatsayin babban wa.
Son ya khaleel kam yana nan mak'ale a zuciyarta, kullum k'ara girma yakeyi dasakin rassa, amma ta danne kayanta bats amince kowa yasaniba.
Meerah da ya Naufal kam soyayya mai k'arfi tashiga, 100% iyayensa sun amince masa ya auri meerah.
Acewar Dady aii zaiyi jihadi ne, kuma meerah ba it's tasaka kanta a wannan halinba.
Kiwa yayi farinciki da wannan had'i, karfa Sholy da ifteee da maheer suji labari, sosai suke arinciki.
*_bayan shekara 1_*
Aysha sanye cikin bak'in dogon wando, ta d'ora jar riga wadda takai mata har guywa, hakama rigar sanyinta ja mai k'yalli, tayane siririn bak'in gyale akanta, sosai tayi k'yau, danta k'ara girma da cikar hallita, komai nata Na babbar mace yagama bayyana.
Ya Naufal daya fito daga d'akinsa yace oya lil sholy ina iftee kuzo Na saukeku inada wajen zuwa.
Kai ya Naufal, nikam tunda bikinku yamatso kaida Anty meerah duk kunwani rud'ar da kanku, idan sauri kakeyi kabamu key d'in kawai mutafi.
No kumuje Na ajiyeku kawai, idan kuma zaku jira maheer ne to nawuce abina, dadyma yau bazaije aikiba.
Tab broth munada exams fa yau, inamu inajiran sarkin barcin can. Iftee dake fitowa saga d'aki tafad'a.
Gaba ya Naufal yayi abinsa, tofa zanwuce abina.
Da Saudi sukabi bayansa.
Tunda suka shigo makarantar yau gaban Aysha keta fad'uwa, ga girarta ta dama sai harbawa takeyi, addu'oi taitayi azuciyarta.
Kasanceaar itada ifteehal kiwa da abinda yake karanta yasa basa tare ayanzu.
Gama exams d'insu kenan Aysha tafito amatuk'ar gajiye, tafiya take kamar zata fad'i, ga yunwa, class d'in su ifteehal tanufa Dan bata iya cin abinci saida ita, tunda tazo school d'in batada k'awa sai ifteehal, sauran duk k'awayen hello hii ne, garama wata 'Yar Nigeria mai suna Khursum, itama bawani sakin jiki ayshan tayi da itaba, saboda tsaro, Dan haka kawai halayen Khursum d'in basa birge Aysha, kullum kuma Anty meerah tana nuna mata tayi taka tsantsan da mutane, saboda tasan su John bawai sun daina Neman su baneba.
Kan Aysha ak'asa tana danna waya domin kiran ifteehal saitaji kawai tayi karo da Abu.
Da sauri tad'ago tana kallonsa, fad'uwar gaba, tsinkewar zuciya, daskarewar jini duk suka riski Aysha alokaci d'aya.
Cikin mamaki take kallonsa, ko'a mafarki bata ta6a tunanin ganin mai kama dashibama awannan lokacin........... ✍🏿
*_kowaye Ayshar tagani?.🤔_*
*_I love you all_*🙌🏻🙌🏻🙌🏻🙌🏻😘😘😘.
[8/17, 10:10 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_*
🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜
*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭
*_part 1_*
(littafi na d'aya📕)
_Alkairin ALLAH ya iso agareku 'yan group d'in *MAMAN SHUEIM NOVELS & MAMAN SHAHEED FAN'S & UMMU NOOR NOVELS WORlD* ina godiya sosai da k'auna._.
_bilyn Abdul tana yinku_😄🙌🏻
😍😍😘😘
3⃣0⃣
Sanye yake cikin suit blue, sunyi masifar yimasa k'yau, k'yawun haibarsa da nagartaccen annuri yana nan, babu abinda ya canja agareshi. Saima k'yawu da kwarjini dataga yak'ara mata, fuskarnan ad'aure tamau kamar yanda tasanta ashekarun baya.
Kallon ido cikin ido sukaima juna, kowannensu saida tsigar jikinsa ta tashi, Aysha tayi azamar janye dara-daran idanunta daga kallon rikitattun nasa.
Bakinta yamata nauyi, tama rasa mizata furata, farin cikin ganin ya khaleel zatayi kokuma kuka? wanne yadace agareta arin wannan ranar?, gata ga abin sonta Wanda baimasan tanayiba.....
Maganarsace takatse mata tunaninsa, muryarnan tasa maisaka marajin magana nutsuwa tadaki dodon kunnenta, cikin harshen turanci yake maganar, dan baimayi zaton yarinyar tasan wani yare hausaba a duniya.
K! hankalinki yana a tsakkiyar kaine dabakisan abinda ke a gabankiba?.
Ba halin Aysha ne rashin kunya gana gaba da itaba, amma a yau saita samu kanta da murgud'ama ya khaleel d'in baki, tana magana k'asa-k'asa cikin k'unk'uni.
Da Hausa takeyin maganar, amma bayajin mitake fad'a, saibakinta daketa motsawa ya tsirama mayun idanunsa.
Bata ankaraba taji anbige mata baki, hannu tasaka da sauri tadafe bakin nata saboda zafin dataji ya ratsata, kafin kacemi hawayen sunfara gudun zirnaniya a kumatunta.
Yaja siririn tsaki yana hararta, saida yara6a ta gefenta zai wuce sannan yace, ''gobema kisake ma wani rashin kunya".
Wlhy ALLAH ya isana, Aysha tafad'a cikin harshen Hausa.
Tsayawa yayi cak daga tafiyar dayakeyi, baiji mitaceba, amma saiyaji tamkar Hausa tayi, kai kodai kunnenane yajiyemin k'arya?.
Ya khaleel yafad'a yana waigowa inda Aysha take.
Saidai tuni tayima nisa dawajen, amma kamar ance tajuyo, saigata ta waigo, suna had'a ido tamasa gwalo dasaka hannayenta a kunne kamar yanda yara keyi idan Suna tsokanar 'yan junansu😂.
Da d'an gudunta tashige bayan wasu samarin d'alibai ta 6uya.
(Ho Sholyn Anty meerah🤣🤣🤣)
Samun kansa yayi dasakin murmushi, tunda yake baita6a had'uwa da shashashar yarinya irin wanga d'iyaba, yakuma Jan k'aramin tsaki tareda juyawa yacigaba da tafiya, har sannan murmushin yakeyi Wanda shikansa baima San namiyeba.
Aysha naganin yatafi tafito daga gun 6uyanta, wani nishad'i nadaban takeji ayau d'innan, tadad'e batayi farincikiba a rayuwarta, wai yau itace tareda ya khaleel, tabbas tasanma bai ganetaba, to yama za'ayi yaganeta, tunda ko'a wancen lokacin bawai ta Isa yawani tsaya kallonta baneba, ita tundama take dashi basu ta6a kallon ido cikin idoba sai yau, ta lumshe idanunta tanamai tuna kwayar idon ya khaleel d'in maicikeda kwarjini da abubuwa masu wuyar fassara ga ma'abocin kallonsa.
Tasanma yanzu yadad'e dayin aure, k'ilama harda 'ya ko d'a, jitai wani bak'in cikin ya soki k'irjinta, taja tsaki tana fad'in yoni INA ruwanama da aurensa mtsowww.
Kekam wakikema tsuk'a?.
Cewar ifteehal data iso wajen Aysha da idanunta ke a lumshe har yanzu.
Da Sauri Aysha tabud'e idonta, tab yaushe kikazo?.
Yaza'ayi kisani, nifa sometimes kina bani mamaki, kina Acting like mai soyayya wlhy, shin kodai kinfad'a tarkon wanine a k'asar tamu?.
Harara Aysha tazabgama iftee, a'a Auren wani nakeyi k'arewar soyayya, ni muje muci abinci yunwa nakeji parrot kawai.
Tsaki iftee tayi, tayi gaba tana fad'in ai gwamma dani parrot ce, kekuma dutsi ko?.
Aysha tayi murmushi, Dan tasan ifteehal tashaki haushine, bataso ayshar nace mata parrot.
Gaba d'aya yau duk Wanda yaga yanayin Aysha yasan tana cikin farinciki, harma mom takasa hak'uri ta tambayeta.
Aysha tace lah babu komaifa mom exams d'in yaucedai tayi dad'i sosai.
Meerah dake zaune gefen mom dama suna list d'in abinda zasu Sayo Na shirin bikin ya Naufal d'in da meerah sukeyi.
Ta kalli Aysha tana nazarinta, ko kad'an bata yarda da zancen Na Aysha ba, zuwa yanzun kam saidai tabama wani labarin Aysha amma badai abataba.
Itama ayshar ganin kallon da Anty meerah kemata yasakata mik'ewa tashige d'akinsu itada ifteehal.
Mirmushi kawai meerah tayi, tacigaba da abinda takeyi.
______________________________
Taheer gobe idan ALLAH ya kaimu zamubar k'asarnan, Dan bincike ya tabbatarmin yarinyar ba d'iyarsa baceba, amma akwai yarinyarsa wadda matarsa tarasu tabari tana nan America Tana karatu, kuma daga nan Canada yawucene Domin dubata itama.
Ayanda ita wannan yarinyar take nunamin kamar d'iyar tasa batajin magana, so babbar hanyar dazamu sami bayanai akansa sosai shine d'ayanmu yayi soyayya da yarinyar ta kwana goma kacal.
OK Na fahim ceka, amma ina ganin awannan fagen kaiyakamata kataka rawar gani, Dan babu macen dazakace kanaso bata sokaba, saboda yanayin k'arancin lokacin damuke dashi.
Harara ya khaleel yasakarma youseef, amma bakada hankali alhaji, kaima kasan wannan ganganne wlhy.
Dariya suka yi suduka, Taheer yace, "boss ALLAH kuwa gaskiyar youseef, kaine kawai zaka samu damar samun zuciyarta cikin k'ank'anim lokaci, Dan nasan wlhy tun a zuwan farko zata amince maka.
Indai sainine zanyi soyayya da yarinyar nan to Ku tabbata bazamu kama Alhaji Alasan kwangila a nanba kuwa, kuma wannan itace damarmu ta k'arshe akansa.
Taheer kaine zakayi soyayya da ita.
Yana gama fad'a yatashi yashige d'aki.
Binsa kawai sukayi da kallo suduka, Taheer ya sauke ajiyar zuciya yana maida kallonsa ga youseef, anya kuwa j yanada lfy youseef?.
Miyasa kace haka kaikuwa Taheer?.
Gani nayi ko kad'an mata basa agaban j, tunda nake dashi banta6ajin yayi hirar maceba wlhy, kaduba yanda mata ke mutuwa akansa ammashi ko kallon arzik'i basu isheshiba, yakai lokacin dazai buk'aci mace kusa dashi amma banta6a ganin j yarik'e hannun wata yarinyaba ALLAH kuwa.
nida kai duk muna Neman mata, amma koda wasa wannan harkar bata ta6a birge j ba, saima fad'a dayake mana akullum akan muji tsoron ALLAH.
Humm hakane gaskiyarka Taheer, ALLAH bazan 6oye makaba abin nadamuna, Dan sosai ina k'aunar j, inajinsa tamkar d'an uwana najini bawai aboki ko oga a wajen aikiba kawai.
d'azu damuke jiransa amota cikin makaranta, sainaga kamar yatsaya da wata yarinya.
Ashe ka kula, nima nagansu, nadaiyi shirune kawai, amma nasan koda zamu tambayesa yanzu zaice babu komaine kawai.
Mugwada tambayar tasadai to, idan mun samu amsa to, kasansa maganarma ta kud'ice awajensa.
Dariya Taheer yayi yace Oga J kenan, shidai komai nasa yanada banbancin tsari dana sauran jama'a.
Ya khaleel kam wanka yakeyi hankalinsa a kwance, saidai tunanin yarinyar data masa gwalo yakasa barin zuciyarsa, murmushi yaketa saki aduk lokacin da zuciyarsa ta tariyo masa murgud'a bakin data masa da gwalo, ahankali ya furta mara kunyar banza kenan, ya ture tunaninta da k'arfin tsiya ya maye gurbinsa dana Alhaji Alasan kwangila, wanda sukebi tundaga Nigeria domin son kamashi, yaja wani dogon tsaki, a zuciyarsa ya furta kazo hannu aii insha ALLAH, duk Wanda yafad'a tarkon Ibraheem Abdallah dama yad'auka yagama shiga uku kawai.
Yasaki lallausan murmushinsa dasai yagadama yakeyi yana saka rigar wanka pink.
Haka kawai yakejin nishad'i tun lokacin dasuka had'u da yarinyar nan, shirmenta yayi tasiri a zuciyarsa, batareda yasan daliliba.
More Hausa novels
A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Babban Gida Part 2 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.