Ciki Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
*_Bayan sati d'aya_*
Zuwa yanzun Aysha tahak'ura da yunk'urin guduwa, dantabi dukkanin hanyoyin daya dace amma babu nasara, yawan kula da ita da bishirah keyi kuma yasata sakin jikinta sosai, Dan bishirah tagirmi Aysha dakusan 2years.
Yau tunda suka tashi suketa bautar girke-girke saboda zuwan ya khaleel k'asar, harma da Aunty zuwairah daga Lagos.
Su Aunty Amatullah kuma sai gobe idan ALLAH ya kaimu.
Zuwa k'arfe 2pm suka kammala komai, gidan yad'auki k'amshin girki dana turare, mafi yawan yaran gidan basu dawoba, wasu nawajen aiki, wasukuma basu dawo school ba.
Suma su Aysha 6angarensu suka dawo sukai wanka.
Wajen k'arfe uku Aunty zuwairah ta iso daga Lagos, yaran gidan basuwani damu da zuwantaba, saboda itama masifaffiyace kamar hajia babba, indai tazo gidan saita addabi kowa, k'annentane kawai suketa farinciki saikuma hajia babba.
Sudai su Aysha tunda suka gama shigarmata da kayanta ciki sukadawo harabar gidan suka zauna, karatun littafin *magana jarice* Aysha ke karanta musu itada bishirah, Dan bishirah batayi karatun bokoba ita. lokacin sallar la'asar nayi suka shiga ciki, bayan sun idar suka kuma dawowa wajen suka zauna, zamansu baifi da 10minutes ba d'an gwari ya wangale k'aton bak'in gate d'in gidan.
Jibga jibgan motocine bak'ak'e wulik keshigowa ajere harsu biyar.
Da sauri Bishirah tamik'e tana fad'in ya khaleel ya iso. Haka kawai Aysha tasamu kanta da fad'uwar gaba, innalillahi... Tashiga ambata, mutan gidan duksun fito harda aunty Mamie.
Saidai mutanen sauran motocin hud'u suka gama fitowa wad'anda ke sanye cikin bak'ak'en suit wulik sannan d'aya daga ciki yabud'e motar tsakkiya wadda tafi kowacce mota k'yau da tsari.
Bak'ak'en takalma sau ciki masu matuk'ar k'yaune suka fara bayyana, saikuma farar k'afar wandonsa.
Fitowarsa gaba d'aya tasaka Aysha ambatar masha ALLAH!! batareda tashirya fad'an hakanba.
Dogone sosai kuma k'ak'k'arfa, dukda yanacikin suit farare hakan baihana cikar haibarsa bayyanaba, yanada haske sosai amma baza'a kirasa fariba kuma ba bak'i baneba, yana matuk'ar kama da mahaifinsu Alhaji Abdallah, saidai kawai yafishi fari, kamar yanda dukkan sauran yaran suka fishi haske, shida Tasleem ne kawai kalarsu d'aya, sunmmafi kama da juna.
A 6angaren k'yawun fuska kam dolene kakirashi kamilalle, komai nashi masha ALLAH, a kwai hanci kam daidai da tsarin faffad'ar fuskarsa, gawani saje daya k'awata taswurar kamilalliyar fuskar tasa, bai tara sumaba kuma kansa ba kwal-kwal yakeba, yabar 'Yar kad'an data kwanta luf akan nasa tamkar mai sabon aski.
Agaskiya guy d'in yahad'u masu karatu, tako ina ubangiji yayimasa k'yak'yk'yawar hallitta Dan bashida makusa, idanunsa kawai abin sone ga kowacce mace, Dan gsky ba maza dukaba keda girman ido da haske irinna *Ibraheem Abdallah Rufa'ee (J!)*
Cikin takun k'asaitarsa yake nufo family nasa, saidai fuskarnan tasafa babu fara'a, amma kamala da dattako sun lullu6eta. Ammah ce tak'araso ta rungumeshi dafad'in oyoyo maigidana.
Yafita tsawo sosai, yarik'eta da k'yau yanamai farincikin ganin kakar tasu, suma yaran suka k'araso gareshi sunamai farinciki damasa sannu dazuwa.
Zame jikinsa yayi yak'arasa inda momy take itama ya rungumeta, my lovely son Sannu dazuwa.
Yauwa momyna I miss you, yafad'a yana d'agowa daga jikinta, hannunsa takama tana dariya, nima haka yarona ina kewarka kusadani.
Lallausan murmushinsa yasaki, sannan yanufi aunty Mamie dake tsaye itama tana murmushi.
Hark'asa ya duk'a yace Aunty barka da gida, munsameku lfy?.
Hannunta takai tashafa kansa, idanunta cikeda hawaye saboda tuni Rufa'ee ta datayi, tace lfy lau babana, kunzo lfy?.
Jinjina kansa yayi kawai, danta Sosa masa inda kemasa k'aik'ayi, tatuna masa d'an uwansa Wanda suka tashi tamkar tagwaye, komai nasu tare sukeyi, aikine kawai ya banbantasu, yamik'e jiki asanyaye suka k'arasa ainahin falon gidan.........🖊
*ina yinkufa🙋🏻♀*😘🤧
[8/7, 7:37 AM] Aisha Galadima: *_Typing📲_*
🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜
*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭
*_part 1_*
(littafi na d'aya📕)
0⃣7⃣
Harsuka shige Aysha dasu bishirah nabinsa da kallonsun sha'awa, bak'aramar damuwa hakan yasaka Aysha ba, harda d'an kukanta sakamakon tuna nata ahalin itama, harga ALLAH tana kewar gida da 'yan uwanta, dama bikinsu Yaya Fhadeela take kwad'ayin zuwa kuma and'aga sainanda watanni uku.
Basu sake jin d'uriyar mutanen gidanba har dare, sai bayan isha'i ne aka aiko Nureedeen yakira Aysha da bishirah.
Da sallama suka shiga katafaren falon, dukda sunsan bama lallaine wani yajisuba, 'yan matan gidanne kawai ke kallon film. Su Aysha sukamusu sannu.
Duk suka amsa musu cikin k'yak'yk'yawar alak'a, dansu ba'a musu tarbiyyar wulak'anta 'yan aikiba.
Bishirah tace Anty Amal gamu.
Kai bishirah wayace ina kiranku?.
A'a dama Nuriddeen ne yace muzo, tonazata kokune ke kiran. Bamu baneba inagato Aunty ce ko Ummee, amma kuzauna ina zuwa.
Amal namik'ewa saiga Aunty Mamie tafito daga 6angarenta, Amal tace yauwa Aunty kece kika aika Nurri kiransu Aysha?.
Eh nice, suna inane?.
Aysha da bishirah sukataso suna fad'in gamu Aunty Mamie.
Yauwa kuzo muje nad'an sakaku wani aiki nan.
Aunty Mamie nagaba su Aysha nabinta abaya harzuwa 6angaren samarin gidan, Wanda yau shine farkon zuwan Aysha, Ya Zunnurain da ya Mujahedeen da Hafeez ne kawai afalon suna kallon kwallo, sai Musleem dakecan gefe yana duba books, da alama wani bincike yakeyi ko aiki.
Duk suka gaida Aunty Mamie, sannan ya mujahedeen yace Aunty Mamie baki aikomin maganinbafa.
O namanta wlhy Mujaheed, amma miyasa baka tunaminba? Haryanzu wajan namaka ciwone?.
Eh wlhy yanayi, d'azufa har zazza6i yakusa yasakarmin.
To ALLAH ya sawak'e, Hafeez jeka d'akina saman madubi kad'akko box d'inan kakawo masa yaduba.
To aunty, Hafeez yafad'a yana mik'ewa.
Su Aysha sukaima ya mujahedeen sannu, kansa kawai ya jinjina musu, danshima akwai d'ankaren miskilanci.
Aunty tace babanafa?.
Yana d'akinsa, cewar ya Zunnurain.
A'a ahakan kuma yazauna? Bayan yace, ''d'akin duk datti.
'Yar dariya mujahedeen yayi, to aunty aikinsan halin kayanki dai, amma baima dad'e dashigaba tunda yanzun muka dawo masallaci.
Ok, bara baduba, inasu Muhseen?.
Sunje wani waje shida ya Ramadan.
Sultan fa?.
baffah ya aikesa inaga.
Ok.
Anty tanufi d'akin khaleel, harta fara tafiya tagasu Aysha BASA binta, tace kutaho mana.
Saida tamasa Knocking sannan yabud'e k'ofar, sanye yake cikin wando da Riga ash colour, rigan mai bud'ad'd'en k'irjice, amma yasaka vest ak'asa, wandonma iyakarsa guywarsa, sai silifas bak'i ak'afarsa, wani ni'imtaccen turare yabigi hancin su Aysha, suduka saida suka lumshe idanunsu.
Yana ganin aunty Mamie yasaki murmushi, cikin girmamawa yace Aunty Mamie kece?.
Eh babana, d'akin za'a k'ara gyara maka nasan kana iya cewa kakasa barcima aciki.
Wlhy kamar kinsani aunty, yanzun Yakama shirin tafiya d'akin sultan nakeyi Dan nikam k'yank'yamin d'akinnan nakeyi, kokad'an ba'amasa wani gyaraba.
A'a babana, aiko nagasu Hasnah sungyara d'azun da safe.
'Dan tsaki yaja, yace Aunty miwad'an Nan yaran suka iya banda rashin mutunci yay maganar tareda komawa cikin d'akin, Aysha da bishirah sukabi bayansa shida aunty.
Mamakine yakashe Aysha, Dan itakam bataga wani dattiba awannan d'akin, gashinan Fe's, saidai 'Yar k'ura, wadda hakan yana nufin Wanda yay gyaran d'akin yanada gandar tsayawa k'alk'ale Abu, amma babu wani dattifa.
Aunty tace to babana gasunan zasu sake gyara maka, saika nuna musu ko.
To Aunty sufara da toilet.
More Hausa novels
A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Babban Gida Part 2 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Rayuwarmu Book One Complete Hausa Novel
By Saadatu
Search across the available chapters.