Ciki Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Cikin sand'a take fitowa daga 6angaren nasu, kaikace sata zatajeyi, ahaka tafito babban falo, ananma shuru kowa yashige d'akinsa, ya Ramadan ne kawai zaune yanata danne-danne a lap-top, da alama wani akin yakeyi, kuma aikin yayi matuk'ar d'aukar hankalinsa.
Ahankali tabi bayansa tashiga ta kicin, ta k'ofar baya tafice, tsakar gidan ko'ina k'wanyar yake da hasken lantarki, ta tsakanin motocin dake barbaje a harabar gidan tarink'abi, kasancewar yaran gidan kowa yana gida, ya khaleel ne kawai bama ya k'asar (amma suna saran dawowarsa a yau).
Koda ta'isa k'ofar gate d'an gwari nakan benci sai zabga gyangyad'insa Na k'addara yakeyi, tazabga tsaki tareda shurin k'afarsa, firgigit yafarka yana niyyar saka ihu, da sauri tace, "ALLAH kamin ihu sainasa baffa yakoreka, kajimin wawan mutum.
Tuni d'an gwari yanutsu danjin muryar mufeedah, amma jikinsa haryanzu k'yarma yakeyi, ta balla masa harara tana fad'in dallah bud'emin k'ofa.
Kamar d'an gwari zai fasa kuka yace, " madam duk randa Alhaji yagane kina fitan dare zai punishing d'ina, ki tausayamin".
Yama kasheka ina ruwana, munafiki idanhar bakaine zaka fad'aba waye yasan ina fita, wlhy duk randa hakan tafaru sainasa ankashemin kai, kai har uwarka saina saka ankashe, kadai San banida kirki, bud'emin k'ofa jio, shashasha mara lissafi, kadamu mutane da wannan banzan hausar naka Mara dad'in ji.
Jikin d'an gwari narawa yabud'e mata k'aramin gate tafita.
Tana fitowa tacire k'aton hijjabin jikinta, daga ita sai guntun siket iya cinya, tasaka riga maikama da best ko cibiyarta bata rufeba, shigar tata saikace 'Yar basketball.
Kad'an tabar jikin gidan nasu ta tadda wata farar mota 'Yar k'arama, bud'ewa kawai tayi tashige abinta.
Hi! babe. Tafad'a tana wani far da idanu.
Woow!! zumata kinyi k'yau, yau wankannan Na musammanne, nima zanyi biya Na musamman kam.
Still tayi far da idanunta, cikin salon tantiranci tace ka cancanci fiye da hakama, wlhy kodagani sai 👙kace nazo maka zanzo, kai ko tsirarane.
Wata dariyar jin dad'i yayi, yace, ''kina cikin aikina wlhy, my Mufeey, zumata kenan".
Ya akayi yau? Naga kinfito da wuri.
Kabari kawai, aii boss ya khaleel baya nan, kuma bansan miya saka 'yan gidan barci da wuri hakaba, Momy kuma itace da baffah shiyyasa duk nasami fitowa akan lokaci.
Dariya yaytayi tajin dad'i, tun'a mota suka fara masha'arsu.
(Nace, "ALLAH ka shiryemu, Momy gafa abinda kike gudun, dama masu iya magana kance, *Ciki da gaskiya* wuk'a bata hudashi🤷🏽♀).
_______________________________
Har yanzu kan yana ciwo my Noor?.
A'a ya daina ma tun d'azun wlhy, yanzukam saidai baya, shima kad'an-kad'an, zuwa anjima ma zakaji shima ya daina.
To ALLAH yak'ara afuwa, babyna dai yana baki wahala.
'Yar dariya meerah tayi tareda kallonsa, tace, "karka damu, ai zan ramane".
Shima dariyar yamata, yana fad'in kokuma kirame ba, wlhy nifa da Dady zaima yarda dakawai muntafi ki haihu a Nigeria, naga lil sholy tak'agara ayi tafiyarnan, tunifa tagama had'a kayanta.
Dolene taso zuwa gida, nikaina hak'uri kawai nakeyi, shekara 9 ba kwana tara baneba, amma nafison saina haihu, sai dai kawai naje musu da d'a ko 'ya.
Cikin murmushi ya Naufal ya sumbaci goshinta, yana fad'in ALLAH ya saukeki lfy to, aii duk yanda kikeso haka za'ayi, kece mai mulkin Naufal zuciya da rayuwa.
Meerah tayi murmushin jin dad'i, d'an box d'in zoben Aysha Na diamond tad'akko, tace nikam Ring d'innan zaiyi nawa a kud'in Nigeria dana nan k'asar?.
Kar6ar box d'in Naufal yayi, itakuma meerah ta tsura masa idanu dansan fahimtar wani Abu.
Bud'e box d'in yayi, yafiddo Ring d'in sai k'yalli yakeyi, d'an murmushi yayi, batareda yace komaiba yamaida Ring d'in a box d'in yarufe.
Meerah tace, " ya haka kuma?".
Kamar ya?.
Tanbayarkafa nayi kud'insa, amma babu amsa kamayar ka ajiye.
Eh, namayarne saboda bansan kud'inba, ke inama kika samu zoben?.
Meerah tad'anyi shiru, sai zuwa can tace, ''wanine yata6a banishi, shine kawai yau naganshi akaya na d'auko.
Shiru yayi bai tankaba, saima kanta daya d'auke daga cinyarsa yamik'e abinsa, kinga bara naje wajen Dady muyi magana, Dan inason mufara tura kayanmu kafin lokacin tafiyar mu, inasaran zuwa next week k'ilan ki haihu insha ALLAH Dan EDD d'inki yakusa cika.
bai jira cewartaba yafice abinsa.
Binsa meerah tayi da kallon mamaki, kenan da gaske shine yabada Ring d'in wa Aysha?.
Tayi murmushin takaici, tareda share guntun hawayenta, ALLAH ya tabbatar da alkairi tafad'a tana mik'ewa da k'yar, insha ALLAH bazata zama shashashar maceba wajen hana mijinta abinda yakeso, Dan batasan mi ALLAH ya shiryaba akan hakan.
Tundaga ranar bata kuma yimasa maganar ba, tamaida ma Aysha zoben kuma, sati uku tsakani meerah tatashi da nak'uda.
Tasha wahala kam hardai ALLAH yabata ikon haihuwar d'iyarta mace, mai matuk'ar kamada kakarta mom, meerah bak'a Naufal bak'i, amma ALLAH ya azurtasu da haihuwar baturiyar yarinya mai kamada mahaifiyar Naufal, shi bai d'akko kamannintaba d'iyarsa ta d'akko.
Fad'amuku farin cikin da familie d'innan sukayi 6ata lokacine, kamarma Aysha taji labari, jitake tamkar yayarta uwa d'aya uba d'aya ta haihu.
Yarinya taci suna Zainab sunan mom, zasuna cemata (Raudah) to ALLAH ya raya Raudah, bawani taron suna akayiba, amma sund'anyi party acikin gida, dangin Momy kuma da abokan arzik'in ya Naufal duk sunzo, hakama gayyarsu Aysha da Maheer, hardasu iklas da Safwan.
Watannin Raudat biyu a duniya suka fara shirin tahowa k'asarsu ta haihuwa Nigeria.
Fad'a muku zumud'in da Aysha keyi a lokacinma 6ata lokacine, amma nabaku dama Ku k'iyastama zuciyarku.😄
________________________________
Yau kam mama da Anty Mamie da Abashiyya da Aymana da gayyar 'yan matan gidan, Shuhuda, Amal, Hamdiyya, Naseeba, maleeka, Tasleem, UmmuNoor, Nuriddin, suka shirya zuwa Kano sunan Fadeela data haihu, Dan ita bata haihu ba sai yanzun, Hafsat kam tanada yaro d'aya harda ciki yanzu.
Har 6angaren hajia babba Anty Mamie taje, tace, su Hasnah sushirya suma aje dasu, amma sukace bazasujeba, wai sunada lectures a ranar, hajia babba Na zaune tanajinsu amma batace komaiba.
Mamie ma bata maida kaiba barema abin ya6ata ranta, dama dankar ace sunware sukad'ai sun tafi shiyyasa tafad'a.
Hafez da Musleem ne suka d'aukesu suka tafi, ita Ammah dama tana can, tun haihuwar da kwana d'aya tayi gaba.
Sosai baffah yahad'a shatara ta arzik'i akaima fadeela, harma dasu Ummah, akwati biyar yacika da kayan arzik'i, banda kayan haihuwa da Anty Mamie tahad'a Ammah tayi gaba dasu.
Gidan duk sai yayi shiru babu dad'i, Umme Amarya ma tabada turmin zani uku da kayan jarirai 5 sai 'yan tarkace tace akaima fadeela.
Amma hajia babba ko yajinta babu, hakan ko kad'an bai damu mama ba, Dan dama bata sa akaba.
Sun isa kano lfy, d'akin mama Nada suka sauka, Wanda Umma tasaka aka gyarashi fes, gidan ya canja sosai, saboda gyaran da mama tasaka akai masa tuni. Dama tabama Ummah jari tanata juyawa, ga mijinta itama mutumin kirki, yarik'e Umma da yaransu da daraja, ko'a haihuwarnan ta fadeela dukkan abinda uba keyi saida yayi. Bayan Wanda kawu bilyamin yayi shima, hakama Umma duk abinda uwa yakeyi tayishi. Dan haka koda sukazo sun tararda komai ready.
Su Amal ma basu dad'e ananba suka kwashi kayansu sai gidan fadeelah mai jego, a can suka taradda Ammah, Dan itace ke zaune da Fadeelah.
Hafsat ma tana gidan. Aikam nan sukaita shan shargallensu, duk wani aiki da dangin mai jego kanyi a daren suna su sukayishi, babu ruwansu da k'yamar talaka, sunshige cikimsu Ruk'ayya k'annen mijin fadeelah anata harkar arzik'i, Ammah taji dad'i sosai, Dan ita tsohuwace tagari. Maison k'arfafa zuminci dakuma girmama mutane.
Wannan yasaka take alfahari da Anty mamie, saboda k'yak'yk'yawar tarbiyyar da yaran suka samu daga gareta, kowa yabonsu yakeyi awajen taron.
Washe gari jaririya taci suna Ummu-hanee, saimuce ALLAH yaraya fadeelah.
Wajen Ummah aka dawo da'ita wankan jego.
Kwanansu mama hud'u akano suka tafi Jigawa, Dan duba inna, tayi murnar ganinsu itama sosai, kwanansu biyu suka koma Abuja, Ummulkhairi tanata zabga kuka saitabi mama, dama tun a Kano taketa dama-dama da ita, 'yan uku kam kamar ta cinyesu, itama tayi k'anne, ta tashi daga autar mama😀tunda gasu Khaleefa, (yarinyar tayi girma sosai itama).
___________________________
Akwana atashi babu wuya wajen mai duka, dagari ya waye saikaga rana tayi, babu dad'ewa kaga dare yarufa, sati kam yazama tamkar kwana, yayinda wata yazama sati, shekara batada wahalar zuwa saidai muce ALLAH yasa mucika da imani.
Ayaune jirginsu Aysha yasauka k'asarsu ta haihuwa, wato Nigeria. Yanda kasan bak'auya haka Aysha takoma, gaba d'aya gani tayi k'asar ta sauya mata, sun sauka a Abuja, amma ko kusa Aysha bata ganeba, tabar k'asar tanada shekaru 14, tadawo cikinta tanada shekaru 17 dawasu watanni, cikin hikima tayita share hawayen farinciki, babban burinta shine taganta a Kano kawai, to amma Dady yace, "anan Abuja zasu sauka agidansu, sai bayan sun huta zasu rakasu itada meerah, kowacce taga iyayenta.
Meerah kam sosai takeyin kuka tun'a jirgi, saida ya Naufal yayta lallashinta, da nuna mata muhimmancin yarda da k'addara, k'yak'yk'yawa ko mara k'yau.
Sun sauka agidansu Naufal d'in dake a Garki Area 7, gidane mai matuk'ar kyawu da girma, yayi k'ura sosai kasancewar ba zama sukeyi acikinsaba, dama ya Naufal ne yafi zama a Nigeria, shima kusan shekaru uku kenan rabonsa da k'asar, garama Dady yazo shekara 1½ kenan, gidan dake makwaftaka dasu suka shiga, sosai akaita murnar zuwan nasu, Annan sukayi salloli dacin abinci. 'Yan aikin gidan kuma sukaje sunata tik'ar gyaran agidansu Naufal d'in.
Bayan sun gama suka koma can.
Aysha sai gimtse fuska takeyi saboda yaron gidan daya dasamata ido da kallo tamkar yasamu television, sai balla masa harara takeyi da murgud'a baki.
Amma ko'a jikin Shakur, danshikam Aysha tagama tafiya da imaninsa.
Har gidan yarakosu dazasu taho, sai wani dama-dama takeyi da Aysha yanama Raudat dake hannunta wasa.
Daga k'arshe da Aysha taga yatasa rayuwarta agaba saita mik'a masa Raudat d'in.
Ifteehal kam mizatayi banda dariya, Dan komai dake faruwa akan idonta itada meerah, shikam Maheer dariyar mugunta yay tayima Shakur d'in, Dan shima yadad'e yana nuna alamomin so ga Aysha amma tana shareshi danuna masa bama ta fahimceshiba.
More Hausa novels
A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Babban Gida Part 2 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Rayuwarmu Book One Complete Hausa Novel
By Saadatu
Search across the available chapters.