Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Ciki Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel
Ciki Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Ciki Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel

Ciki Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel

Author: Bilyn Abdul
Chapter 5 of 41
About 6 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters

Alhaji Abdallah Rufa'ee jigawa shine cikakken sunan maigidan, d'an asalin jihar jigawane a garin ringim, ALLAH yayima mahaifinsa Malam Rufa'ee rasuwa dadad'ewa.
Alhaji Abdallah yana sana'ar saida carpets ne a babbar kasuwar wuse dake Abuja, ahankali ubangiji yacigaba da bud'a masa harkokinsa harya bud'e kamfaninsa na kansa, Wanda yasami had'in guywa da k'asar Turkey, Alhamdullah kasuwancinsa yabunk'asa matuk'a ak'asar, yanzu haka sunada reshen kamfanin a Kano, Lagos, sokoto, Jigawa.
Matansa uku da 'ya'ya 21.
Hajiya Laurah itace uwar gida, wadda sukan kira da hajiya babba, yaran kuma suna cemata (momy). cikakkiyar 'Yar bokoce dantayi karatu mai zurfi, ko kad'an hajiya laurah batason talaka, macece mai tunk'aho da tak'ama, shikansa Alhaji Abdallah nuna masa isarta takeyi, tad'auki aikinta sosai da muhimmanci, kokad'an babu maijin dad'in zama da'ita agidan, saboda halayyarta, musamman hajia Bilkeesu. Yaranta 6, Zuwairah, Shukurah, Ibraheem khaleel, Hameedah, Hasna, Husnah.
Sai Hajiya Bilkeesu, tanada yara 11, Rufa'ee, ALLAH yamasa rasuwa wata uku dasuka shige sakamakon had'arin mota zaije jigawa. Yanzu akwai 10 Sultan, Mujahedeen, Amatullah, Ramadan, Zunnurain, Muslim, Muhseen, Amal, Tasleem, UmmuNoor. Itakam tanada hak'uri, ga kawaici da sauk'inkai, kowa natane, batada k'yamar talaka, saima tazauna tayita hira da 'yan aikin gidan, gatada taimako, batayi karatu mai zurfiba, iyakarta Secondary aka aurama Alhaji Abdallah ita, tana yarinya d'anya, kobayan aurensu batacigaba da karatuntaba, danhaka bata aikin komai saina kula da mijinta da 'ya'yanta, wannan yasa suka taso cikin tarbiyya. Alhaji Abdallah nasonta sosai saboda k'yautatawarta agareshi da mahaifiyarsa. Yaran gidan nakiranta (Aunty Mamie).
Sai amarya hajia saudah, itamadai balaifi akwai girman kai, amma batakai hajiya babba ba, itamadai ma'aikaciyar Ce, Lauya ce maizaman kanta, ita wata irin mutumce dabata damu da damuwar kowaba, cikikam harda 'ya'yanta, (shiyyasa yaranta duk sunfi shak'uwa da Aunty Mamie) takan bama aikinta muhimmanci fiye da komai, kakan dad'ema baka ganta cikin lamuran gidanba, hajiya babba taso suhad'ema hajiya bikeesu kai itada hajia saudah, amma hajia saudah tace ita ba wannane agabantaba. Yaranta 4 Hafeez, Shuhudah, Maleekah, Nurudden. Itakuma suna cemata Ummee Amarya.
Mahaifiyar Alhaji Abdallah tana nan gidan taredashi, itace tsohuwar dakika gani, anabata kulawa sosai agidannan, babu maison abinda zai ta6ata, idan kika cire hajiya babba da 'ya'yan tokowa jiyake da'ita, ya khaleel ne kawai halinsa ya banbanta ayaran hajiya babba, danshi babu ruwansa.
Wannan shine tak'aitaccen tarihin gidannan. Kinada tambayane??.

Ajiyar zuciya Aysha tasauke, cikin kafe bishirah da kallo tace, tambayata biyuce zuwa uku. Tafarko suwaye sauran yara uku danagani dakuma 'yanmata biyu?.
Dariya Bisheerah tad'anyi, cikin tsokana tace Ashe kinfahimci labarin sosai?, 'yan mata biyu dakika gani, Hamdiyya da Naseeba yaran k'anin Alhaji Abdallah ne, uncle Ma'aruff, suma suna nan zaune awajen Aunty Mamie, karatu sukeyi anan sudasu Amal.
K'anan su uku kam yaran aunty Amatullah ne, 'yan uku, suna k'asar Japan itada mijinta, shine aka kawosu nan gidan saboda school.

Jinjina kai Aysha tayi alamun gamsuwa, tacigaba da fad'in yaran hajiya babba fa? Dan uku nagani yanzu agida?.
Eh, biyu sunyi aure, Anty zuwairah tana Lego's itada mijinta, sai Anty Shukurah tananan abuja, amma yanzu suna kasar Jordan shekara uku kenan, wai mijin natane yake karo karatu, yaya khaleel kuma bansan takamaimai k'asar dayakeba, Dan shi yanzu zai iya cemikima yana Najeria, anjima kuma kiji yabar k'asar, haka yake yawo k'asashen duniya saboda yanayin aikinsa.

"Aikin mi yakeyi?."

Wlhy ban saniba Aysha, amma naji sunacewa ko d'an sandane, kamardai haka naji su iya hama nafad'a kwanaki. Amma kwanannanma zakiji yazo k'asar saboda hutun k'arshen shekara dakuma meeting na family dasukeyi.
Shiru Aysha tayi, Dan haka kawai tasamu kanta da fad'uwar gaba, Bishirah ta ta6ata tareda fad'in shikenan kin gama tanbayar taki?.
Jiki amace Aysha tad'aga mata kanta, kafin Bishirah tace wani Abu kiran da Rabi kemusu yakatseta.
Atare suka amsamata, sannan suka fito inda take.
Kichin suka shiga domin tanadar abincin rana, yaran gidan sunkusa fara dawowa, yaukuma aikin hajia saudah ne. Itakam tanama wajen aikinta.
Duk ranakun aikinsu itada hajiya babba 'yan aikine keyin komai, sa6abanin Anty Mamie dakan tsaya ayi komai da ita, shiyyasa yaran kanyi farincikin aikinta, Dan koba komai zasuci mai dad'i da tsafta...............🖊

nagaji bara nahuta😏😢, kuma inajin yunwa😋, muhad'u a page 6 guys😉

*I love you all my lovely fans*😍
[8/7, 7:37 AM] Aisha Galadima: *_Typing📲_*

🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜

*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭

*_part 1_*
(littafi na d'aya📕)

*_Dolene namik'o sak'on jinjina da godiya agareku 'yan group d'ina, ALLAH yabar zuminci, inajinku sosai aruhina, inayinku irin tamau-tamau d'innan, I love you so much_*😘😉

0⃣6⃣

Gaban Aysha sai fad'uwa yakeyi sakamakon kiran da hajia babba ta aiko karime Tamata. harsuka shiga falon tana addu'ar daduk ta iso bakinta.
Hajiya babba nazaune tareda wata hamshak'iyar mace, daganinta kasan naira ta zauna.
Karime tarissina tana fad'in hajia ga Ayshar nan.
Kai kawai hajia babba ta gyad'ama karime alamar taji.
Karime nafita daga falo Aysha ta durk'ushe tana gaishesu, babu Wanda ya amsa acikinsu, saidai suna binta da kallon k'urullah, musammanma bak'uwar ta hajia babba. bayan kamar 4mnt hajia babba tace, ''aminiya kingantafa, ai zata iya nake gani?.
Wani murmushin k'asaita hajia khaltum tasaki, tagyara zamanta tana k'arema Aysha kallo lungu da sak'o, Aminiya ai zancenma zata iya labarine, zan iya cemiki tunda muke business d'innan baki ta6a samun hajaba irin ta wannan lokacin, ai young girls irin wad'annan su ake so dama, ALLAH kad'ai yasan irin ribar daza'a samu anan 👉🏻🙎🏻‍♀tayi maganar tana nuna Aysha datayi k'asa dakai tamkar munafuka.
Amma jikinta sai tsuma yakeyi saboda tsoro da firgicin zaurencen Nasu hajia babba, ko kad'an Aysha bata fahimtar komai a zancensu, saidai tanaji ajikinta ba alkairi baneba, addu'oin Neman tsari tafara a can k'asan zuciyarta......
Hajia khaltume takatseta da fad'in yarinya yasunanki?.
Muryarta Na rawa tace Aysha.

Nice name!.

Cewar hajia khaltume. Daga nan suka sallami Aysha tatafi.

Tana tafiya 6angarensu tana sharar kwalla, haka kawai taji tana tausayin kanta, gashi su hajia babba sun gargad'eta kada tasanarma kowa kiran dasukai mata, inba hakaba komi yabiyo baya ita tajama kanta.
Gaff taci karo da Abu, dasauri tad'ago kanta, amma kafin tasan wata bige ansauke mata Marika har biyu.
Dafe kuncinta tayi saboda azaba, ke Dan ubanki bak'ya ganine?....
Maganar matashiyar Husnah ta katseta.
Dan ALLAH kiyi hak'uri Anty Husnah wlhy bankula baneba, Aysha tayi maganar tana durk'usawa ak'asa, haryanzu hannunta Na dafe a kuncinta.
Muhseen yak'araso inda suke da sauri, yace k Husnah lfy kuwa?.
Cikin huci tace wai 'Yar iskar yarinyarnan hartakai ta bangajeni, Muhseen.
kiyi hak'uri to, tayi kuskure amma bazata sakeba, ke Aysha bata hak'uri.
Hak'uri Aysha takuma bata cikin kuka.
Hasnah taja tsaki sannan tara6a gefen Aysha tashige, harda takama Aysha yatsun kafa.
Aysha tafashe da sabon kuka dantaji zafin takawar. shikansa Muhseen yaga takawar da Husnah tama Aysha, danhaka ya rintse idanunsa yayinda Aysha tafashe da sabon kukan, tabashi tausayi sosai, yace kiyi hak'uri kinji, watarana sai labari, idan kina tafiya kiringa kula.
Aysha ta jinjina kanta tana share hawaye, sannan tamik'e.
Lafiya kuwa ya Muhseen?.
Kallonsa yayi yace babu komai Hafeez, Husnah Ce tamari Aisha wai ta bangajeta, shine nake lallashin ayshar.
Itadai kawai zalincinta yamotsa, Dan nasan babu yanda za'ayi Yarinyar ta bangajeta tana sane, ALLAH ya sakamata.
Ameen dai Hafeez.

Yinin yau zumbur Aysha ad'aki tayisa, kowa ya tambayeta saitace batada lafiyane, itakam sokawai take tasamu hanyar guduwa daga gidan, Dan bazata zauna acutar da'itaba.
Babban tashin hankalintama shine gwaggo bintu, kokad'an bata cika damuwa da lamarintaba yanzu, yau d'innanma kowa yazo yaji damuwarta amma banda ita, takuma fashewa da kuka mai ban tausayi, lallai tayarda maraici daban yake, Inda mahaifinsu Nada rai waya Isa yamusu koda kallon kaskanci, tatuna gidansu da rayuwa irinta family nata....
Haka taita kuka mai tsuma rai, hardai zazza6in gaskiya yasaukar mata.

Bishirah ce taita kula da'ita har zazza6in yasauka, koda tatashi da safe taji sauk'i sosai, saidai damuwa da fargabar abindasu hajia babba suke kullama rayuwarta gashikuma takasa sanarma koda bishirah ne saboda tsoron gargad'in dasukai mata.

End of Chapter 5Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next