A Wata Masaurautar Part One Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Root Entry WordDocument 0Table Data Copied By YAYA HAYAT (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion Cool novel, makeup and kitchen1 AND Cool novel, makeup and kitchen2 WHATSAPP NO: +2347039625239 A wata masarautar.... Writing by. Ummu Safwan https://hausanovels001.com.ng Bissimillahi Rahamirrahim Page1 zaune take tana kuka a gaban abbanta tana basa hakuri, Abba don Allah kayi hakuri kabarni nabar jaharnan natafi can inda ba a sanniba nayi karatu, Abba kataimakamun Sai a lokacin Abba yyi kyaran murya yace gimbiya bilkisu naji, bukatarki, meye dalilinki dabakyasonyin karatu a jaharku? Gimbiya bilkisu ta sunkuyar dakai kasa, tace Abba banason ace ni diyar sarkice, kona hada wani abu da masarauta, nisantana da masarautarmu shi xaibani kwanciyar hankali da kwarin gwaiwar yin karatuna. Sai a lokacin Ammi tayi magana toh memartaba kadiba abunda gimbiya bilkisu tace, kabarta tabar garin takoma can inda ba a santaba tayi karatun, tunda batason asan ko ita wacece Pls Abba kamata abunda takeso kasan halin gimbiya bilkisu tun tana karama ra ayinta daban yake da yayan gidan nan, gimbiya bahijja ce take magana. Sai a lokacin memartaba sarki yyi mgna yace na yarda dake bilkisu, nayarda kije garin kano kiyi karatunki idon kuma bakyason kano to kije adamawa, Ta dago kanta daga sunkuye tana murmushi nanuna jindadinta, Abba garin kano xantafi domin a canne naji ance akwaisu da karama bako, Yace bamatsala Allah yyimki albarka ya tsareki a duk inda kike. Gaba daya palon ya amsa da amin kowa yana murmushin jindadi bayan kowa yamike xaitafi dakinsa saisukaji , memartaba yace xakije tareda jakadiya domin ta kula da lafiyarki, Sai tabata fuska idanunta suka fara hawaye, Abba don kar asan koni wacece xanbar gombe xuwa kano karatu, kuma Abba sainaje da jakadiya Anty bahijja ce ta lakucemata hannu alamar ta yadda da abunda Abba yace, tace to Abba na yarda amma da sharadi ajawa jakadiya kunne idon mukatafi kada ta yarda tadinga sunkuyamun a gaban mutane, domin itace xata xama a matsayin ammi ta Sarki ne yyi murmushi tare da ammi sukace munji daina kukan, saitayi murmushi kowa yana murmushi sukatafi makwancinsu Memartaba yabada umurni a kiramasa jakadiya, waxiri yatafi a guje ynakiran jakadiya, Jakadiya kuma kodataji kiran waxiri gabanta yashiga faduwa domin idon taji waxiri nayimata irin wannan kiran to tabbas tasan sakone daga wurin sarki, gabantane yashiga faduwa saicewa takeyi a xuciyarta to ita metayi? Daxaisanya memartaba ya aiko a kirata? Waxiri tagani yanafadamata sakon sarki, tashitayi tabi bayan waxiri xuwa fadar memartaba sarki mai adalci, tanashiga fada jakadiya takai gaisuwa ga sarki fadawa saicewa suke sarki ya amsamki jakadiya amintanciya ga sarki, Sannan sarki yyi kyaran murya yafadamata dalilin dayasanya aka kirawota yanason takulamasa da gimbiya bilkisu domin xa a turata karatu kano, kuma tare xasu tafi nan dai yafadata yanda sukayi da gimbiya bilkisu, jakadiya ta sunkuyar da kai kasa tace angama ranka ya Dade Allah yajadaran sarki mai adalci duk abunda kace hka xa ayi ranka ya Dade, tatashi tafita Akabarshi da ammi suna tantauna maganar tafiyar gimbiya bilkisu Gimbiya bilkisu yace ga abdulrahaman, suna xaune a garin yola a wata masarauta mai adalci, sarki abdulrahaman yagaji sarautane a wurin mahaifinsa, masarautace wadda basu yarda da xulunciba, suna daraja talakawansu dabasu hakkinsu shiyasa yankin yola suke alfahari dashi fadawansa sukejidashi suna kuma ganin girmansa sabda yana adalci a tsakaninsu. Sarki abdulrahaman yanada mata hudu, ta farkon sunanta sarauniya hadixa wadda takasance diyar sarkin xamfara ce, Allah ya albarkacesu da yaya uku danta na farko sunansa abdulrahaman wadda yaci sunan sarki, sai ta biyu gimbiya bahijja sai kuma ta uku itace gimbiya bilkisu, tun daga bilkisu sarauniya hadixa wato ammi bata kuma samun haihuwaba Sai hajiya xainab ita kuma yayanta duka matane, subiyar ta Haifa Sai halima ita kuma yayanta hudu duka mata. Sai Aisha yayanta biyu mace da namiji Yayan sarki abdulrahaman goma sha hudune, mata sha biyu, maxa biyu Shiyasa suka dauki tsanar duniyar nan suka dora a kan ammi sbda a ganinsukeyi da sarki yyi murabus to abdulrahaman xai mikawa sarautar domin shene babban dansa namiji, Acikin yayan sarki mata kuwa su goma sha biyu yayan ammi sunfita daban da sauran, musaman gimbiya bilkusu, wadda gaba daya rywarta daya da sarki shiyasa yafisonta acikinsu domin gimbiya bilkisu akwai tausayin talakawa Motocine jere suna jiran fituwar gimbiya bilkisu domin rankiyarta makaranta, tafito tareda Abba da ammi da kuma bahijjah suna gaba sai ita da prince Adull suna daga baya suna mgna, a can ta hango motoci sunyi layi duk ita suke jira, tana kawowa gafda motocin taja tatsaya tareda kallon maimartaba Tace Abba tafiya xakayine? Naga duk anjeramaka motoci, Sai yyi murmushi yace duk yan rakiyarki ne gimbiya bilkisu, Nantake tabata fuska gskiya ni Abba baxasu biniba, Abba inason inyi ryuwa irin ynda kowa keyi a makaranta Batare da ansan koni wacece ba, Abba don Allah kayi hkri idon nabatamaka, Abba kace sutafiyarsu kawai banason rakiyar. Sai a lkcin prince abdull yyi mgna, Abba kabani key din motar natafi na kaita da kaina, idon ka amince Ammi tace abdull tafiyarka batareda batakan tsaroba a kwai matsala, ammi ta hasala wai ita dolene sai anyimata yanda takeso Bahijja tace ba hka xa ayiba bilkisu kishiga kutafi idon akakusa kaiwa sai yaya abdull ya karbi key hannunsu sai yakarasa dake mkrantar shi kuma saisu jirasa, ko hkan meyimkiba? Sai a lokacin tayi Murmushi ta rungume bahijja, shiyasa nakesonki Anty bahijja,kowa yyi dariya, sukashiga mota sai mkranta, garin kano tadabo dandin Hausa koda me kaxo anfika Lov u all A wata masarautar.... Writing by Ummu Safwan 07066214433 Page2 Mmy ce a bangaren prince adnan tana kokarin shiga dakin barcinsa, fadawa suka hanata shiga, yarima yabada umurni kar a bar kowa ya shigarmasa daki domin yanada bukatar hutu, Ummi ce taxo wucewa ta wurin, saitaji fadawa na gardama, saitadawo domin taji meke faruwa? Aikuwa taga Ashe mmyce fadawa suka hanata shiga dakin yarima Ummi ke tambayarta meyakawota sashen yarima adaidai wnn lkcin ? tunda tasan halin yarima sarai. Mmy na xubarda hawaye tanafadawa, ummi, wurin prince naxo shine yabada umurni kar a bar kowa yashigar masa daki, sabda yana bukatar hutu. Ummi tadafa kafadar mmy tace tafiyarki barni nashiga dakin naga abunda yake tsinanawa da har xaisanya a hana mutane shiga, tana kaiwa wnn tawuce, basuyi yinkurin hanataba domin sunsan mahaifiyar sace. Kwance yake a kan makeken gadonsa, barci yakeyi cikin kwanciyar hankali, dakagansa kasan yaji ddin barcinsa, ummi CE tsaye a kansa tana kallonsa ta ynda yke barcinsa cikin kwaciyar hankali, ya manta lkcin makaranta ya kusa,bayan daxun yagama fadamata cewa yau sunada test a class dinsu Ummi takai dubanta a kan makeken agogon bangon dake like a dakin nasa, taga karfe 3:30pm bayan yafadamata cewa karfe 4:pm xasufara test din, nan tashiga tashinsa dakyar tasamu ya mafalka, da masifa bude idanunsa kenan saiyaga ummi a kansa yyi murmushin dole, Ummi yaushe kika shigo? Ya xa ayi kasan shigowata kabude Baki da Hanci kana barci, Kaduba lkci kagani ynxun karfe nawa? Ba test naji kace ke garekuba? Yana diba lokaci yatashi da sauri yafada tolet yyi wanka, koda yafito ummi ta tafiyarta tabashi wuri yashirya. Yana fitowa a gurguje ya shirya yasanya kananun kaya, sunyimasa kyau, ya dauki key din motarsa yafito domin tafiya makaranta, duk inda ya wurga bayi sai kaimasa gaisuwa sukeyi ko kallonsu bayayi, suma basudamu da hkanba domin idon da sabo sunsaba da halinsa. prince adnan kenan, Birnin kano garine mai yalwar mutane, acikin garin a kwai wata masarauta wadda sarki Bashir yake tsaye tsayendaka domin yaga ya amsarwa talakawansa hakkinsu. Sarki Bashir yanada mata biyu Matarsa ta farko hajia nafeesa haihuwarta daya namiji saidai bexo da raiba, tundaga lokcin ko batan wata bata kuma yiba, Mahaifiyar sarki ta matsamasa akan yakara aure, hka ya amince, ya aure diyar kaunarta maryam, ansha shagulgular biki amarya maryam Tatare a gdan sarauta, bikinsu da wata biyu tasamu ciki, sarki yyi murna da samun cikin maryam, ko ba komai xaisamu magajin sarautarsa, Baking ciki awurin hajiya mafeesa kuwa ba a mgna, domin duk duniyar nan bbu wadda ta tsana samada maryam da kuma Addah, domin cewa takeyi duk munafurcin Addah ne, datasanya sarki yayi aure. Haihuwar maryam ta farko ta haifi danta namiji, Wanda yaci sunan fahad, yaro mai kama da mahaifinsa, kamarsu data da sarki, sarki ya dauki son duniyar nan yadorashi a kan fahad Fahad Nada shekara hudu, ta kuma samun wani cikin tahaifi adnan, sarki yyi murna da haihuwar adnan domin anyi shagulgular biki irin na gdan sarauta. Fahad da adnan suntaso cikin kulawa da gata domin sarki bayason abunda ya tabasu, Adnan shine karami, amma bayajin magana ga miskilanci da qasaita, da ixxah, Takai takawo fahad shine babba amma kamar shine karami. Yanada shekara shidda ta haifi yarta mace, taci sunan fareedah, tundaga lkcin bata kuma haihuwaba fareeda itace autar sarki Bashir, Motocine suka tsaitsaya nesa da makarantar, prince abdull da gimbiya bilkisu tareda jakadiya suka karasa makarantar, wurin shugaban mkrantar suka wuce dama yasan da xuwan nasu, maimartaba yyiwa shugaban mkratar bayin xuwan nasu. Domin maimartaba yaturawa shugaban mkratar kudi yanemawa gimbiya bilkisu madaidaicin gida inda data xauna tare da jakadiya. Prince abdull tareda bilkisu da shugaban mkratar suka fito daga office, xairakasu gdanda akasayawa bilkisu domin ta xauna tayi karatunta. Isarsu gdan kenan Prince abdull ya kalli gdan ya kuma kallon bilkisu yace mata, ke ynxun kinfison xama a irin wnn rywar? Murmushi tayi tace yaya abdull a halin yanxun addu'arka nake nema Allah yabani abunda nafito nema, baice mata komaiba daga kafadarsa yyi alamar taji xata iyane Yyimata sallama tare da fatan alkhairi yatafiyarsa, yabarta tare da jakadiya. Prince adnan ne tareda yarima fahad yayansa, cikin mota direba na tukasu, tsaki kawai adnan keyi, yanayi2 yana dibon agogon gwal dake sanye a hannunsa, yajuya ya kalle fahad dayake kallon kwalta, ynajinsa yana tsaki amma yakyalesa, Sai a adnan ne yajuyo da fuskarsa yana kallon fahad yace yaya nakusan latti fa, sai lokacin fahad ya kallesa yyi mgna. Yace Kaine adnan bakajin mgna, ai INA ganin kasanda xakuyi test din amma kashige daki kadinga barcika harda wani sanya fadawa sutsareka don kar a tasheka, Allah danice ummi baxan tashekaba kyaleka xanyi tunda bakada son karatu, bnda ummi tatasheka dakayi lorxing din test din gabadaya, niyanxun taimako daya xan iyayimaka shine dama direba ajiyeni xaiyi, nan gaba kadan, nashiga motata
More Hausa novels
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A D U N I Y A Ta Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Search across the available chapters.