Soyayyanovels
A Wata Masaurautar Part One Complete Hausa Novel
A Wata Masaurautar Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Wata Masaurautar Part One Complete Hausa Novel

A Wata Masaurautar Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 11 of 27
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters

A nan Abdullah yasan ko 'yar wace masarautarce yakuma fahimci matsayinta awurin sarki." Yau Monday Bilkisu tak'are shirinta tsaf." Domin zuwa makaranta." afterdress ce sanye a jikinta, ta yafa mayafinta, tayi kyau sosai kamar balarabiya." Wayarta tad'auka takira Safeenat tace "hello sister kinshirya nabiyo tanan mutafi." Safeenat dake kwance cikin yanayin ciyo, tace "sister banasamun zuwa makarantar nan banada lfy daciyon ciki nagwana jiya." Bilkisu ce "subhanallah, sister Allah yabaki lfy idon nadawo zanbiyo nadiba jikin naki, sukayi sallama Bilkisu tafito tanufi makaranta." Prince zaune a kan motarsa, yasha bak'in glass a fuskarsa." kallon duk wadda keshigowa yake d'aya bayan d'aya." duk wadda keshigowa makarantar a kan fuskarsa yake." fatansa Allah yahad'ashi da Bilkisu, shikad'ai yasan irin abunda yashirya mata a rayuwarsa." A can ya hango shigowarta.' tafiya takeyi cikin natsuwa da k'asaita da littafai rik'e a hannu ta." Yana hangota ya duru a kan motar, ya zagaya, yashiga mortar, yafige motar da k'arfi yayi cikin Bilkisu , saida yazo gaf da ita sannan ya faka motar yafito." Bilkisu tsaye tayi takasa tafiya sai kallo tabisa dashi." bata ankaraba saiji tayi and'aure mata baki anturata a mota." Writing Fareeda Bashir A WATA MARAUTAR.. Writing by Ummu Safwan PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S Page2 Tafiya sukeyi, bakinta a d'aure, idanunta sai zubarda hawaye sukeyi." Saida suka shiga wata unguwa wadda babu hayaniyar mutune a cikinta." Unguwar tsit kakeji kamar babu bel'adamar dake rayuwa a cikinta." Parking yayi a dai dai wani katafaren gida, wadda babu kowa a cikinsa."fitowa yayi ya bud'e get dakansa sannan Yashigar da motarsa a ciki." A guje yanufi wurin ajiye motoci." Tsayawa yayi yabud'e murfin mota ya fito." Ya zagaya wurin zaman Bilkisu sai zubarda hawaye takeyi." Ya finciko hannuta da k'arfi yafito da ita, jaye yake da hannunta, harsuka k'arasa shiga cikin gidan." Wani d'aki yanufa da ita, wadda yake ya motse. kaya ne ko'ina a watse." A ranta tace turk'ashi yau dai Allah kad'ai zai fissheni a hannun mugun mutumin nan." Gashi k'azamin banza, duk k'asaitarsa, dawani kwalliya tasa, ashema gidansa babu komai a cikinsa sai k'azanta." Ya katsemata tuninta dayace zaki fad'amin inda Abdullah yake ko saina aikata abinda nayi niya a kanki."? Inkasheki inkashe banza." Domin babu wadda yaga a lokacinda na d'aukoki, bare kiturowa mutane banzayen fadawanki masu kama da samudawa." Magana yakeyi idanunsa sunkad'e sunyi jajir, cikin b'acin rai yace bazaki bud'i baki kiyi magana ba bare kifad'amun a 'inda kika kaimun Abdullah." Bilkisu sai kallonsa take sama da k'asa, domin ita a yanzun Allah ya ciremata jin tsoransa a rayuwarta." Shima ita yake kallo cikin mamaki, Tace "karyane wlh baka isa kakashiniba sai dai idan lokacina ne yayi." Abdullah bazan fad'i inda yakeba harsai ka d'an d'anni bak'in cikin daka sanyani na tsawon wani lokaci." don hka kabani hananya nafita nayi tafiyata, tunkafin warin wannan d'akin yayimun illah." Cikin b'acin rai yanufuta a fusace, ya had'a bayanta da bango hannunsa a kwalar rigarta ya matseta yana ce mata. "Ina Abdullah? Iyee ina Abdullah nace?" Tafita hanyacinta don tsabar tsoro da firgitar abunda yayimata a rayuwarta babu namijin daya tab'ayi mata abinda yayi mata yanzun." Ta runtse idanunta hawaye na fita daga idanunta, Ya k'ara matseta ya kuma matso da fuskarsa daidai tata yana wani huci, zakifad'amun inda Abdullah yake ko saina kasheki?" Ta katse shi dacewa, "hannunka a k'irjina!" Ta fad'i hakan cikeda shagwab'a kuma cikin sanyin murya wadda ke k'unshe da wahala." Besan lokacinda ya saketaba, dashima ya gano hannunsa a kan k'irjinta yake." Ya ciji leb'ensa na k'asa a ransa kuwa haushinta ya k'ara kamashi so take tayi suducing d'inshi?" Tambayar da yakeyiwa kansa kenan, Lallai yarinyar nan tayi nisa, ganinta zata iya jan hanlinsa ne kome take nufi?" Duk Kansa yakeyiwa wad'an tambayoyin, a zahiri kuma yanunata da yatsa yana Jamata kunne kokifad'i inda kikai Abdullah ko na d'aukar maki kwankwaran mataki a kanki yanzun nan." Karfin hali tayi domin ta tsorata da ganinsa cikin wannan yanayin, idanunsa sunkad'e sunyi jajir Tace "malam kabud'emun k'ofa nafita bana iya k'ara minti d'aya a cikin wannan k'azamin d'akin. Tanufi wurin k'ofar da niyar tabud'e tafita, saiji tayi ya fisgota ya had'ata a bango ya matseta gam ajikinsa, saiwani numfashi yake fitarwa kamar wani zaki." Tuni hankalin Bilkisu yatashi, tarufe idonta, tana fad'in SUBHANALLAHI!" Ina kikasanta? Ashe kinsan Allah?" To wlh duk Baki fad'i Inda kika kai Abdullah ba zakiyita zama a nan gidan, Har sai ranar da kikafito da Abdullah sannan kema nasakeki, Muguwa kawai, aibashi yayi maki laifiba, ni ne nayaki laifin, meyasa bazaki d'auki mataki a kaina ba sai a kansa?" Kina tunin ninafi k'arfinki kenan shiyasa zaki sanya samudawan fadawanki sutafi da Abdullah Kisakesa mana, ni sai kisanya a kamani." Magana yakeyi amma bata tankashi, Ya kuma kuluwa, yajaye a bakin k'ofar d'akin yaturata a kan katifa, Yabud'e k'ofar d'akin yafita, yasanyawa k'ofar key yayi tafiyarsa ya barta nan." Bahijja da Fahad soyayya tayi nisa domin har ansanya ranar da maimartaba zaitafi yola neman auren Bahijja k'arshen watan nan." writing By Fareeda Bashir A WATA MASARAUTAR....... Writing by Ummu Safwan PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S Page2 Kwana d'aya babu labarin gimbiya Bilkisu hankalin jakadiya duk yatashi, Tanufi gidansu Safeenat domin duk a tunaninta suna tareda Safeenat, Saima taji labarin Safeenat batasamu zuwa makarantaba saboda bata da lafiya, Ba jakadiya k'adaiba gaba d'aya hankalin iyayen Safeenat saida yashi , Domin abbansu Safeenat fitowa yayi daga gida yana salati yashiga motarsa nufi neman Bilkisu." Safeenat kuwa kuka tashigayi kwana d'aya babu Bilkisu babu labarinta, Saitafara tunanin ko prince Adnan ne yasanya a d'auketa, domin d'aukar fansar abunda taimasa, Wata zuciyar kuwa na gargad'inta da bazai iya sanyawa a d'auke ta ba." Bilkisu kuwa ya kulleta a d'aki yayi tafiyarsa, sai dai duk bayan a'wa biyu zaizo domin ganin koda tayi nadama tafad'a masa inda Abdullah yake, Amma babu alamar nadama a fuskarta, sai dai ya tarar da ita tana games a wayarta hankalinta a kwance babu damuwa a tareda ita, haushinta ya lunlub'eshi yace "wato ita wannan yarinyar batada niyar nadama tafad'i inda takai Abdullah kenan?" Ya kai hannunsa zai fisge yawar dake hannunta k'irar 1phone tayi saurin b'oye wayar a bayanta, Ganin zai iya murd'eta ya kwace wayar a hannunta , tatura wayar cikin rigarta, shi kuma ganin ta tura wayar a rigarta, yayi mata wani kallo, Yace "shed'aniya ni babu abunda zanyi dake, kidaina wani tura waya a riga, wato d'azun kinji dad'in nahad'a jikina da nake shine yanzun kike Neman nasanya hannuna a cikin rigarki, saboda kina jarabanbiya, to Allah yakiyayeni babu abunda nake iyayi dake, kitafi can kinemi dai dai dake, ninafi k'arfinki babu abunda zanyi dake, Yaja wani dogon tsaki malama kifito mun da Abdullah nasakeki kikama gabanki ." Ta kallesa taja wani dogon tsaki, tayimasa kallon sama da k'asa, Tace "mezanyi dakai, dibeka, me gareka wadda harnake sha'awar had'a jikina da kai, tanuna masa d'akinsa dayi wani kaca kaca da kaya tace " k'azami kawai." Tace Abdullah bazan fad'i a inda yakeba domin har yanzun bangaji da ganinka cikin k'unci da bak'in cikin rashin ganin Abdullah ba." Yace "a she kema zama bek'aremaki a gidan nan ba kenan, Domin mundun bakibada umurnin a sake Abdullah ba nima kisani bazan tab'a sakinki ki koma gida ba, Kuma kisani abincin da nake kawomaki daga yau na daina, Sai dai kizauna da yunwa idon kikaji wuya zakiyi bayani da bakinki inda kikai Abdullah, Ganin yanda yake magana sai wani cincira yake cike da b'acin rai da bak'in ciki, kamar ba Adnan d'in da tasani ba, Dariya tashiga yimasa tana nunasa da hannu tana dariya harda rik'e ciki, Haushi da bak'in ciki ya kuma lunlub'esa, Ya d'aga hannu alamar zai daketa meya tuna oho sai ya sauke hannun yana cizon yatsa, Sai yafita d'akin a fusace yaja k'ofar d'akin da k'arfi yasanya makulli ya kulleta yayi tafiyarsa." Ganin ya kuma kulleta bayada niyar sakinta bare takoma gida, Duk hankalinta yatashi tana tunanin jakadiya, tasan yanzun duk inda take tana cikin tashin hankalin rashin ganinta kwana d'aya dabatayiba Idon kuma tayi yunkurin shedawa maimartaba to Tabbas hukuncine zai hau kanta watak'ila harta rasa rayuwarta, wadda idan hakan yafaru bazataji dad'i a rayuwarta ba." zubur tamik'e tsaye da tuna da Safeenat tasan yanzun labari ya kai a kunnesu na b'atanta Suma tasan tabbas basa cikin kwanciyar hankali a wannan lokacin." Wayarta ta d'auka takira fadawanta tace tana buk'atar a sakar mata Abdullah yanzun nan, Suka amsa mata da to angama ranki ya dad'e, Suka sakesa, suna kewar juna domin d'an zamanda sukayi da Abdullah sunshak'u dashi sosai, Wadda shi kuma Abdullah beso aka sakesaba ko dan saboda kalar abincin dayakeci irin na masarauta, Sai yashiga tunani a zuciyarsa, gaskya betab'a ganin masarautar da fadawa suke daula haka, sai a wannan masarautar, inama shima a maidashi cikin fadawan yaci gaba da rayuwasu, da ya bautawa masarautarsu Bilkisu, Domin zama taredasu ya fahimci me'ake nufi da sarauta, Kuma ya fahimci k'aramci da daraja d'an Adam irin na masarautarsu Bilkisu A haka dai yabar wurin fadawan, yana kewarsu, yana mai tsinewa Adnan a rayuwarsa domin yasan shine silar sanyawa a sakesa, domin yaga kwana biyu beganshiba, saikace a tare a ka haifemu." Yaja wani dogon tsaki yayi tafiyarsa." Adnan yana k'ofar gidansu Abdullah yana kwantarwa da mahaifan Abdullah hankali a kan cewa insha Allahu gobe Abdullah zaidawo gida, ba b'acewa yayi ba yanan cikin k'oshin lafiya da kwanciyar hankali, Begama rufe bakinsaba sai ganin Abdullah yayi a gabannsu yana dariya, yayi kyau yayi k'iba har wani shek'i yake, yana masu dariya, yanufi mahaifansa ya rungumesu cikin jin dad'i, suma sai murna sukeyi naganin tilon d'ansu, Prince baki yasaki yana kallon Abdullah yana mamakin kwana biyu, yaga yayi kyau kuma yayi k'iba. Gefe yajanyeshe yana kallonsa cike da mamaki, yace "Abdullah wai meke faruwa ne?" ina fatan muguwar yarinyar bata sanya anyimaka illah ba?" Yakaiwa Adnan harara yace gaskiya ka daina cewa gimbiya Bilkisu muguwa, domin ita ba muguwa bace, illah maison alkhairi da daraja d'an adam, Ni wlh a baya d'aukar da nake mata wata wuk'antanciyar 'yar talaka marasa galihu a she ba haka abun yakeba, Adnan yasaki baki da hanci yana kallon Abdullah cike da mamaki, Yace "gimbiya kana nufin Bilkisu 'yar sarki ce?" Abdullah yace kwarai kuwa, 'yar sarki ce, wadda mahaifinta da masarauta gaba d'aya suke alfahari da

End of Chapter 11Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next