A Wata Masaurautar Part One Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
ita saboda kyawawan halayennta da kuma daraja d'an adam." Adnan yace " 'yar wace masarautarce?" Waye ubanta?" Kuma A wane gari suke gudanar da mulkunsu?" Duk a jere yajerawa Abdullah wad'an nan tambayoyi, Abdullah ya wurgamasa harara, yace " kobaka tambaye niba nad'aukoma labarai da d'umi d'uminsu, Zakasan kowacece Bulkisu amma kabarni nashiga gida nahuta zuwa anjima sai muhad'u kasha labari." Yana kaiwa nan yayi tafiyarsa yabar Adnan a nan tsaye yashiga tunani, Saida Abdullah yakai k'ofar gida ya waigo yaga Adnan tsaye yana tunani, Yace gaskya prince baka kyautamun ba, dakasanya a kafito dani daga cikin daular mulkin gimbiya Bilkisu, Domin gaskiya da bakai bane danace kamar kanajin bak'incikin ganina a cikin daular masarauta Yana kaiwa nan yashigewarsa gida Yabar prince Adnan tsaye yana tunani." Writing by Fareeda Bashir A WATA MASARAUTAR... Writing by Ummu Safwan PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S page 2 2 Prince Adnan kasa tafiya yayi a k'ofar gidansu Abdullah, Domin gaba d'aya Abdullah mamaki yake bashi lokaci d'aya ya firgice masa har yake iya fad'a masa Magan ganu a kan Bilkisu, Motarsa Yakoma ya zauna yana tunanin sauyawar da Abdullah yayi, Kiran sallar azahar ne yafito dashi daga cikin motar, yanufi masalanci dake kusa da gidansu Abdullah domin yayi sallah, Yasan dolene Abdullah yafito domin yayi sallah, daga nan yabafashi labarin kowacece Bilkisu, 'yar wace masarautace shine kawai abunda yakeso yasani a bakin Abdullah." Shiru kakeji har a'ka kammala sallah bega Abdullah ba, dibe dibe yashigayi koda zaiganshi amma beganshi, Yanke shawara yayi yashiga cikin gidansu kai tsaye yayi masa dabarar da zai fanyace masa komai a kan Bilkisu, Domin yanda yaga kan Abdullah namasa rawa ko aika yaro yayi yakirashi yasan bazai fitoba." Kaitsaye yanufi gidan tare da sallama, Mamarsu Abdullah ya tarar tsakar gida tana arwala, Ya durkusa k'asa ya gaida ita, ta amsa masa cikin fara'a da sakin fuska, Tace "Adnan dawowa kayi ne?" Yaufa bazaman lafiya amininka yadawo, Adnan yayi murmushi ya sosa kai, yace "Ummu yana ciki kuwa?" Ummu tace "yana d'akinsa shiga katashesa lokacin sallah yayi yana kwance, Adnan ya mik'e yashiga d'akin Abdullah dake kwance saman makekeyar katafarsa yana shak'ar barci, Adnan yashiga tashinsa yana bunbugar k'afarsa, Abdullah yabud'e idonsa a hakanli yakai dibonsa ga maitashinsa yana cikin jin dad'in barcinsa, Ai kuwa yayi ido biyu da Adnan Zurbur yamike zaune yana mai kallon Adnan Yace "dama nasan kaine, domin babu mai katsemin jin dad'in duniya sai kai, To yanzun da katasheni me kakeso naimaka?" Adnan yayi murmushin dole domin a xahirin gaskiya maganganun da Abdullah yake fad'a masa sunayimasa ciyo a rayuwarsa amma baya nuna masa, saboda yana buk'atar yabashi labarin Bilkisu wadda ya dad'e yana nema." Danne zuciyarsa yayi, yace "sorry abokina tashi lokacin sallah ne yayi kana kwance kanata shak'ar barci, Kuma kasan kwana biyu nayi missing d'inka, Bilkisu ta d'aukemun kai." Jin ya ambaci sunan Bilkisu Abdullah yamik'e zaune yana murmushin jin dad'i a fuskarsa, Wadda yabawa Adnan mamaki." Abdullah yace "wlh kuwa nima nayi missing d'inka abokina bari nayi sallah kasha labari da d'umi d'uminsa." Adnan yayi murmushin dole, yace "yawwa my friend ayi mana addu'a." Dariya yayi ya d'auro alwala ya shinfid'a darduma tayar da sallah, Adnan na kallonsa." Bayan ya idar da sallah ne Ummu tagabatar masu da abinci, Damun shinkafane yasha kayan lambu da busanshin kifi, Adnan yakai dibansa ga abincin, yaga kalar abincin da Addah take dafa masu duk ranar juma'a, Filet d'in abincin yajawo a gabansa yana mai had'iyar yawu, Soma cin abincin yayi yana mai kallon Abdullah domin ya matso yafad'a masa asalin wace ce Bilkisu, Yana gudun yafayiwq Abdullah maganar, Yace yafasa gayamasa, domin ya fahimci dawowarsa wani rashin mutunci yakeji dashi, Besan abunda ya hango a masarautar su Bilkisu ba, Wadda shi a masarautarsu basu dashi." Ya kuma kallonsa yace "abokina baka bani labarin zamanda kayi da fadawa ba?" Abdullah yayi dariya yace "bari kawai prince nasha wuya, Kuma daga baya nasha dad'i, domin kuwa abincin damukece tare da fadawa kamar abincin da sarki yakeci, Bari kawai prince ai mulki da daraja d'an Adam na masarautar su Bilkisu, Sannan kullum cikin farin ciki muke kwana mutashi cikinsa sab'anin nan, Prince yayi saurin katsesa zuciyarsa nayimasa tafasa, yana yabun kirkin wata masautar da batasuba, kuma abunda yakeso yafad'a masa bashi yake fad'a masaba
More Hausa novels
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A D U N I Y A Ta Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Search across the available chapters.