Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
____Washe gari da misalin 'karfe 11am na rana a lokacin Su Khadija suna makaranta, Momy ma ta fita ma'kota gidan wata 'kawarta Hajiya Nafisa, amma tace ba zata dad'e ba, zaune nike ni kad'ai a falo kan kujera ina kallon TV
Ya Sadeeq ne ya shigo bakin sa d'auke da sallama koda yaga ni ce zaune a falon sai ya gimtse bai 'karasa sallamar ba ya d'aure fuska kamar bai ta'ba dariya ba, ni ma nayi kamar ban ganshi ba, tsawa ya daka min "dan ubanki baki iya gaisuwa bane ko nan d'in gidan uban ki ne? Ko da yike shima ubanki' tarbiyar bata ishe sa ba bare kuma kema ya baki".
Inajin zafin gorin da Sadeeq yake mini har cikin raina a lokuta da dama
ya cigaba da cewa "idan ba mummunar 'kaddara ba mai zanyi dake kucaka ki kalle ki, ki kalle ni, kin tafka babban kuskure da kika yarda Daddy ya hada auren nan zan shayar dake madarar azaba gida na zai zame miki tamkar kabari ke koda sunana ki kaji an ambata sai gaban ki yayi mummunan faduwa, saboda bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane, ki fara tunanin yadda zaki rubuta littafi mai suna *NIDA YAYA SADEEQ* saboda irin zaman da zakiyi a cikin gida na ya isa ki rubuta".
Duka wannan maganar da Sadeeq yayi kaina a 'katsa wasu hawaye masu zafi suna gan garo mini, narasa mai nayi wa Sadeeq da har ya tsane ni haka? Ban ta'ba tunanin tsanar da yake ce wa yayi mini ta kai har haka ba,
Ban tanka masa ba illa mi'kewa da nayi na nufi hanyar sama na fara taka steps kenan ya da katar dani ta hanyar fadin "na tsane ki Siddi'ka na tsane ki, kuma bazan taba sonki ba a duk sanda ki kaji nace ina sonki to kada ki ta'ba yadda dani saboda yaudarar ki zanyi ba gaskiya bane". 😭
Hawaye masu 'kuna suka cigaba da gangaro min a haka na 'karasa haura steps din, Suwaiba da ke faman dafa abinci a kitchen taji duk abinda ya faru tsakani na da Sadeeq
'Dakina na shiga na fad'a kan gado, hawaye mai zafi yana zuba daga ido na, ni da kaina ina jin tausayin kaina saboda a sani na da yaya Sadeeq bai ta'ba cewa zaiyi baiyi ba duk abinda yace zaiyi to sai ya aikata sa.
A cikin kukan na d'aga hannaye na sama na ce "ya Allah ka bayyana mahaifiya ta a duk inda take a fadin duniyar nan, ya Allah kasa tana a raye saboda inaso na rayuwa tare da ita, ya Allah kada kabama wani bawan ka sa'ar cutar da ita".
Mama. Na fad'a haka yayin da na d'aga kaina sama ina kalla, "bansan maye dalilin ki na cewa ko bayan babu ranki a daura wa 'yarki aure da Sadeeq ba, nayi alkawarin ni Siddi'ka zan zauna da Sadeeq koda kuwa hakan na nufin zai zama ajali na ha'k'kin ki ne nayi miki biyayya a sanda kike a raye da kuma sanda rai yai halin sa, tabbas zan bi duk wani umarnin da kika bani, Mama ta ina sonki". Na 'kare maganar da wani irin kuka mai tsuma zuciya
Allah sarki Siddi'ka ni kaina ta bani tausayi ban san sanda na saki waya ta tafad'i a kasa ba saboda ido na ya cika da hawayen 😭 tausayin halin da take ciki da 'kyar na samu na daidai ta kaina na d'auki waya ta na fita daga d'akin naja kofar na rufe
Momy ce zaune ita da Sadeeq a falon 'kasa, sai zazzaga masifa takeyi "Sadeeq kabi duniya a hankali ko ta d'aga ka zata aje ka, Wallahi Sadeeq ina guje maka ranar da zakayi ladama amma kuma ladamar zata kasan ce da ita gwamma babu saboda ka makaro, ka kasa d'aukar kaddarar ka a yadda tazo maka".
Shi dai Sadeeq jin Momy kawai ya keyi amma baiga wata ranar ladamar da zata zo mai ba kuma ma ladamar ba akan kowa ba sai akan Siddi'ka yaji takaicin kalaman Momy, saboda har cikin ransa ya ke jin kiyayyar Siddi'ka
tace "dama akan maganar makarantar Siddi'ka ne yasa nace kazo tunda kai ba kayi hankalin haka ba, kasan dai an koma hutu, so nike ka kaita makarantar su Khadija saboda akwai koyarwa sosai kuma kaga tana da saurin d'aukar abu bazata sha wuya ba".
Yana sosa 'keyar sa yace "Momy gaskiya ni boarding school zan kaita acan katsina nama gama komai yanzu haka ranar lahadi zan kaita".
Momy bataji dad'in abinda Sadeeq ya aikata ba tare da ya nemi shawar ta kona Daddy ba, saboda haka tayi mai fad'a sosai kuma tace "bata yadda ya kai Siddi'ka boarding ba".
da yake Sadeeq ya iya dad'in baki kamar d'an siya sa yasan kalaman da zai fad'a ayi saurin yarda dashi, nan take ya siye Momy da da-d'a-d'an kalamai har ta amince masa
A zahiri Sadeeq 'karya ya keyi saboda bai yi mata register ba dama yana da burin yin hakan saboda bai son ya kaita jeka kadawo yasan su Momy zasu takura masa amma boarding sai idan anyi hutu tazo, ko babu komai zai samu sau'kin abun
Bugu da kari yana san ya shigo da batun auren sa da Zuby nan bada jimawa ba, saboda a halin yanzu soyayya mai 'karfi ta shiga tsakanin su sun aminta da junan su har sunyi alkawarin aure duk da basu taba ganin juba ba yau Sadeeq zaije ganin ta saboda itama anan garin Abujan take, saboda hud'uwar da zaiyi da masoyiyar sa ne 'karfin zuwan nasa Abujan domin yana matukar 'kaunar Zuby kuma yana da muradin ganin ta.
Momy ce ta katse shurun da cewa "kuma aji nawa za a sata?".
"Momy yadan ganta da yadda suka gwada ta kinsan yarinyar kwata kwata ba tada 'kwa-'kwalwa yanda kika san dusa haka kanta yake Allah dai yasa ko JS1 ne su d'auke ta".
"Js1 fa kace Sadeeq! Ina laifin 2 idan 3 bai samu ba, to ban lamun ce ba banyarda ba kayi duk yadda za kayi ta gama prmry
School fa, kai kan ka shaida ne akan makaranta da ta gama, kuma kada na 'kara jin kace bata da 'kwa-'kwalwa zan sa'ba maka".
"Uhm" dai Sadeeq yace wa momy
Daga haka ya mi'ke "Momy ni zan fita a kwai wani aiki da zanyi zuwa anjima zan dawo zan kwana biyu anan kafin na koma ".
♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
𝑫𝒂 𝒃𝒂𝒛𝒂𝒓 𝒌𝒖 𝒏𝒊𝒌𝒆 𝒓𝒂𝒘𝒂 𝒎𝒐𝒔𝒐𝒚𝒂 𝒏𝒂💃 𝒊 𝒍𝒐𝒗𝒆 𝒚𝒐𝒖 𝒂𝒍𝒍
Addua
_Ya Allah ina rokonka da dukkan kyawawan sunayen ka ka kiyaye duk wani musulmi daka shiga mawuyacin hali kabamu lfy me amfani kasanya mana haquri da juria ya Allah ka kwantar mana da hankulanmu ya Allah kada kabamu ikon butulcemaka koda ka jarabcemu 🙏_
NI DA YAYA SADEEQ
٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·
More Hausa novels
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel
By Oum Yasmeen
Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Ciki Da Gaskiya Book 1 Complete Hausa Novel
By Ubeera
Search across the available chapters.