Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel

Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel

Author: M Shakur
Chapter 23 of 31
About 14 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters

       ___Ya dauki tsayin lokaci a haka yana kallon tsala tsala cinyo yin nata, daka bisani ya mike yana mai jin haushin kansa ko me yagani a jikin wannan kwailar yarinyar? Haka ya tambayi kanshi ganin bashida amsa yaja dogon tsaki "mtssww" duk abinda Sadeeq yake yi Siddeeqah bata san inda kanta yake ba.

Izuwa lokacin cikin nasa yai masa sauki sosai sai dan abinda ba a rasa ba

Dukan kafar ta ya shiga yi kamar a mafarki taji ana bugun ta a tsorace ta bude ido ganin Sadeeq ne yasa ta dan ji sanyi a ranta

Dube dube ta fara sai alokacin ta tuna ashe a falo ta kwanta, dirowa tayi daga kan kujerar ta wangale baki tayi hamma Sadeeq harda toshe hanci yayi saboda da tayi hammar bata kare bakin ta ba wai kada yaji wari,  tayi mamakin ganin sa amma sai bata nuna nasa ba ta bige da cewa "wash".

A yatsine Sadeeq ya dube ta wallahi shi har cikin zuciyar sa ya tsane ta mtwssss ya kuma Jan tsaki a karo na biyu, afili yace "wallahi Daddy bai kyauta min ba daya aura min yarinyar nan"

Duban sa itama tayi tace "aikin banza wai harara a duhu, kaje ka fada masa man".

Bata karasa fada a gaban sa ba ta ruga da gudu saboda tasan duka ne zai biyo baya, ta ko yi sa'a dakin Ummin abude yake tana fadawa ta maida kofar ta rufe kana ta fara maida numfashi daka bisani tabi lafiyar gado.

Da takaicin ta Sadeeq ya mike
Ko kadan babu laka a jikin sa  ahankali ya ke tafiya har ya haura sama ya shiga makwancin sa

*** * * * * * * * *

Bayan ta gama gyara bra dinta ta dubi Sumy tace "dan zuge min zif din". Da "to". Sumy ta amsa kana ta zuge mata kamar yadda ta bukata.

Basu jima ba sai ga Lubancy ta zo, tana ganin Zuby tare da Sumy tayi kicin-kicin da rai, sarai Zuby ta gane nufin Lubancy amma sai ta basar tace "yauwa dama tun dazu ke nike jira muje ko".

Ba tare da Lubancy ta tanka mata ba tayi gaba asakarce Zuby ta bi bayan Lubancy da kallo kana ta maida kallon ta ga Sumy tace "am mata mu mun tafi sai idan mun hadu wani satin".

Sumy ta ce "to".

Koda suka fito bakin get din sun tarar da Zuly na jiransu amoto saboda haka basu wani tsaya bata lokaci ba suka shiga Zuly tajasu suka dau hanya

Tafiya suke babu mai kula dan uwan sa Zuby aka fara saukewa saboda unguwar tasu tafi kusa, kana tayi musu sallama ko da tazo bakin get din ta rasa ya zatayi saboda tasan mai gadi yanzu bacci yake yi, can ta sauke ajiyar zuciya da sauri ta fiddo wayar ta daga cikin jakar ta number Mama ta shiga laluba Mama dake safa da marwa a dakin ta taji ringing din wayar ta da sauri taje ta dauko kana ta duba screen d'in saboda taga wace me neman nata.

Ganin sunan shalelen nayawo akai yasa Mama tai saurin dagawa gami da karawa a kunne, daga can bangaren Zuby tace "Mama a bude min kofa". Daga haka ta kashe wayar bata dade ba sai ga Maman tazo ta bude mata, tana shiga Mama ta maida get  din ta tura ahankali Zuby zatai magana Mama tai sauri ta tashe mata baki tun kan su karasa falon Zuby ta cire nikabin fuskar ta cikin sanda suka wuce falon basu zarce  ko ina ba sai dakin Zuby kana Mama ta maida kofa ta rufe, Masifa Mama ta shiga zazzagawa inda sabo Zuby ta saba saboda indai Abba nanan to fa haka Mama ke yi sai da ta gama kana Zuby ta dubi Mama tace "haba Mama wai meyisa ki ke min irin wannan ne? Ni gaskiya bana so ki sani a gaba ki tai min masifa sai kace yarinya karama".

Dafa kafad'ar Zuby tai tace "kin dai san halin Abban ki duk da nace kin ce kar atashe ki nan yai ta zuwa yana buga kofar ki yana ambatar sunan ki yanzu haka nasan idon sa biyu dan sanda na baro sa yana bayi dan ya dauro alwala maza canza kayan ki ki kwanta zanje na ce masa kin tashi".

Mama na gama fadar haka ta fice daga dakin, a gag-gauce Zuby ta canza kayan kana ta kwanta ta rufu da bargo kamar mara lafiya

Ko da Abba ya shigo tambayar ta yashiga yi me ke damun ta kin sha magani? Haka dai yai ta mata tambayoyi yace "ko na kira miki Dr khamis ne?". Tace "a a Abba". Yace "to ya jikin naki". Kamar mara lafiyar gaske yadda ta marairai ce fuska tace "Abba da sauki sosai fa". "Allah ya kara sauki amma baki fada min meke damun ki ba". Tace "wallahi Abba ciwan kai ne mai tsanani ga jiri da nike gani shiyasa dana sha magani na kwanta nace kar a tada ni". Kan nata ya taba babu wani zafi yana Murmushi yace "Alhamdu lillah kan da sauki tunda gashi jikin naki babu zafi". Tace "Eh Abba". Mama ce ta shigo hannun ta dauke da karamin kofi akan wani dan karamin tebur ta ijiye kana ta zo ta dan yaye bargon Zuby tace "daure ki tashi ki kurba shayi ne nayi miki irin wanda kike so". Abba yace "ai kuwa kin kyauta Mariya miko min na bata". Da jin  haka Zuby ta dan yunkura ta mike tana dan ciza leben ta na kasa tace "Abba zan sha da kaina  a miko min". Abba bai baro dakin ba sai da ya tabbatar da lafiyar diyar sa.

* ** * * * * * * * * *

Washe gari da misalin 9:00am na safe gaba-daya mutanen gidan a farke suke Momy ce da kanta a kitchen sai khadija da Ummi da suke taya ta aikace-aikace yayin da Suwaiba keta share-share da goge-goge Jiddah kuwa da Alama bata tashi ba, Siddeeqah kuwa hango ta nayi cikin shigar material ja da ratsin bulu dinkin doguwar riga, kasan cewar bata da kiba bai kama mata jiki ba kuma ko hoda bata shafa a fuskar ta ba, bata iya daura dan kwalin zamani ba saboda haka tayafo sa  a kanta, gyaran gashin jiya duk ya tuje ya zame daga dunot din da akai mata, saboda gyashin ta irin mai santsi din nan ne ahankali take saukowa daga step din,

Yayin da Sadeeq yake tawowa cikin sauri-sauri dan shi Sam bai lura da mutum ba, amma ita ta ganshi tana ta kokarin kaucewa amma ina, saida ya ture ta tayi taga-taga zata fadi bakin ta na rawa takasa yin ihu kamar yadda ta saba saboda firgita, sai alokacin Sadeeq din ya lura cikin zafin nama ya kamo ta ya janyo ta kirjinsa kokarin hada hannayen sa yake ya rungume ta tayi sauri ta ture shi cikin tsiwa tace "malam na fara gajiya da wannan iskancin naka ko ka dauka kowa dan iska ne irin ka? to ka kiyaye ni wallahi dan ko hannu na ka kuma tabawa ka taba Allah ya isa, ina fatan ka gane". Tana gama fadar haka tai saukowar ta dama shi haurawa zai yi

Bai ce mata komai ba kuma baiyi kokarin bin ta ba, saboda atunanin sa idan sun rabu yau ba lailai ya sake haduwa da ita ba saboda haka zai daga mata kafa duk rashin kunyar da zatai mai bazai tanka mata ba

"Momy ina kwana". Siddeeqah ta fada lokacin data karasa kicin inda Momy ke wanke fatatus

Cikin sakin fuska Momy ta juyo ta kalleni kana tace "lafiya lau yan makaranta har kin shirya?".

"eh Momy".

"yau ba saikin tayani ba kije falo ki zauna ga Umar can sai kuyi fira kamin mu gama, saboda kada kayan ki su baci kije makaranta a dunga yi miki dariya".

"to nace" na fito falo inda na tarar da Umar shi kadai a zaune, kusa da shi na zauna kana nace "Umar". Da sauri ya dago kai ya kalle ni, na cigaba da cewa "da gaske dai makarantar kwana yaya zai kai ni, shikenan bazan kuma sake ganin ku ba sai na dauki tsawan lokaci, wallahi ni an cuce ni an raboni da Inna gashi yanzu kudun da nike gani nike jin dadi za'a rabani da ku". Tuni kwalla ta fara zubomin ban damu na share ba saboda kukan shine ya kamaceni a wannan lokacin, sosai Umar ke lallashi na amma Sam naki sauraren sa kuka na nike wuy-wuy, acikin wannan halin Daddy yazo ya isko mu Tambayar Umar ya shiga yi abinda yasani kuka Umar bai boye masa komai ba ya fad'a masa, Daddy ya ce "haba mai gaskiya indai akan makarantar da zaki tafi ne kike kuka to an fasa babu inda zaki ai na dauka da yardar ki zai kaiki ashe gaban kansa yayi".

Karaf maganar da Daddy yayi sai a kunnen Sadeeq saboda saukowar sa daga sama kenan kan yakara so falon kasa ya tsinkayi kalaman Daddy

Cije leban sa yayi da karfi bai saki ba saida yaji zafi afili yace "wannan wace irin yarinya ce mai naci da taurin kai, yanzu mai take nufi ya riga yagama tsara yadda komai zai tafi, amma yanzu Daddy yana neman ya kofsa masa".

Bayan ya kara so falon har kasa ya tsugunna ya gaida Daddy ba yabo ba fallasa ya amsa mai

Kana Sadeeq din ya nemi kujera ya zauna yana kitsa abubuwa da dama a cikin ransa

Haka itama Siddeeqah babu abin da zuciyar ta bata raya mata game da Sadeeq ba, sai yanzu take kara tabbatar wa da zuciyar ta cewa tabbas fa yaya ba son ta yake ba, idan ba haka ba mai yisa bai kai daya daga cikin kannan sa ba? Bata da wannan amsar amma tabbas ita ko za'a kashe ta bazata wannan makarantar ba ta gwaumace ta mutu a jahilar ta

* ** * * * * * * * *

Kwance take kan gado tayi dai-dai abinta da ganin ta hankalin ta kwance yake sai sharar baccin ta take.

Ringing din wayar ta da ake kira shiya ta data daga nannauyen baccin daya dauketa tun jiya dan ko Sallar asuba batayi ba.

A firgice ta farka ta lalubo wayar ta daga karkashin filo bata tsaya duba wanda yake kiran nata ba ta d'auka ta kara a kunne, daga muryar sa ta gane Abba ne, ban san me yace mata ba naji tace "to Abba gani nan ".

Bata tashi a lokacin ba sai da takara kusan 13 minutes sannan ta tashi tsaye tana mika da hamma da Alamar baccin bai isheta ban daki ta fada tayo wanka a gurguje bayan ta fito ta shafa nayukan ta kana tasaka atamfa riga da zani rafa ta dan fesa turare mai sanyin kamshi ta daura dan kwalin ta ta fito cas da ita, saida ta kalli kanta a madubi irin wanda yake nuna mutum daka sama har kasa kana tayi Murmushi ta fito dakin ba tare da tayi sallar asuba ba, wannan dama dabi'ar ta ce hada sallah ko ba abinda take yi bazata taba yin sallah akan lokaci ba sai lokacin ta ya fita an shiga na wata

A falo ta sami Mama da Abba suna karya wa akan dinning zama ita ma tayi kusa da Abbah aka shiga karya wa da ita suna dan taba fira akai-akai.

Bayan sun gama mai aikin su Ramatu ta zo ta kwashe kwanukan, kana Abba ya koma kan kujera ya zauna "shalele tashi ki dauko min rimot". Abba ya fad'a yana duban Zuby da mikewar ta kenan a kan dinning da "to". Ta bashi amsa bayan ta miko mai zama tayi kusa dashi akasa tana ja mai yatsun kafa, saboda tasan Abbah nasan haka

* * * ** *** * *
Kowa na karya wa amma ban da Siddeeqah da tayi tagumi ta tsurawa filet din gaban ta ido Wanda yake a cike da soyayyan dan kalin turawa da kyau

"Momy tace Wai ke kuwa lafiyan ki lau gaba daya yau ban gane miki ba ko akwai abinda ke damun ki ne?". Ga dukkan alamu hankalin ta baya tare da ita saboda tayi zurfi cikin tunani, lura da haka yasa Khadeeja dafa kafad'ar ta tace "sisi wai maye haka irin wannan tunanin kina yar karamar ki".

Fir gigit Nadawo daga duniyar tunanin da na Lula ba tare da na gano nazarin da nayi ba.

Kallo na Momy tayi kana ta kawar da kai Daddy yace "ci abincin kinji ki daina irin wannan tunanin babu kyau nasha fada miki".

Kai na gyada kana na fara cin abincin haka nai ta turawa kamar ina cin magani haka nike jin dan danon abin cin .

Bayan mun gama kan mu tashi daga dinning din Daddy ya kalli Sadeeq yace "kai Sadeeq na soke tafiyar Siddiqah zuwa makarantar kwana ba dani ba za'ai wannan zalincin kaji na fada maka wannan ai zalinci ne, na dauka da yardan ta kayi komai ashe san zuciyar ka ka aikata, na baka daga nan zuwa lokacin da zan yi tafiya ka lallashe ta idan ta yar da to idan kuwa bata yarda ba sai dai ka kaita wacce yan uwan ta suke zuwa, kada kuma ka man ta zuwa anjima zan tafi bayan azahar ".

Daddy na gama fadar haka ya bar gurin

Saboda kaduwa har da zufa ke karyo wa Sadeeq Sam baiyi tsammanin abin zai kai haka ba, kallo na yayi muka hada ido na banka mai harara, cije Leban sa na kasa yayi nima nayi yadda naga yayi, Momy na lura damu bata ce komai ba ta Mike zata bar dinning din yaya Sadeeq yai sauri yace "Momy dan Allah kiyi wani abu akai kice wani abu please nasan Daddy na jin maganar ki".

Tace "kaga Kaga ka fita ido na tun wuri kayi abinda Daddyn ku yace maka dan yanzu kayan sa zan je na shirya babu ruwa na ni".

Ta na gama fada ita ma ta bar wurin

Ya mutsa fuska ta nayi nima kana na Mike tsaye nayi mika harda dan ihu na hada kana na bar gurin ina dariya kasa kasa, nasan Sadeeq ya tsani haka da ace Daddy bai ce sai na yarda ba da tuni ya kai min duka

Shikuwa Sadeeq mamaki yake yadda karamar yarinya kama ta ta iya makirci

Tashi yayi ya haura sama dakin sa ya shiga kana ya dauki wayar sa daya barta akan gado kan kujera ya koma ya zauna kana ya shiga danna nambobin Farook ya ko ci sa'a ringing 3 Farooq ya dauka kiran, daga can ban garen Farooq yai sallama inda Sadeeq bai amsa masa sallamar ba, kusan ita ce dabi'ar sa ba kowa yakewa sallama ba, kuma ba kowa yake amsa wa ba, sai cewa da yai "Malam kana ina ne?".  Ya bashi amsa da "gani na kusan shugowa Abuja dan wallahi anyi min transfer zuwa Yobe shiyasa nazo na dauke ta na kaita da wuri nima na samu na shirya".

"kamar dole a kasa sa yai magana a dakile yace yobe fa kace to Allah ya tsare".

Ran Farooq bace yace "dan iska saboda ba kai bane aka mawa dole kayi min isgili, insha Allah kai ma sai anyi maka in dai transfer ce ruwan dare ce, dan wannan sabon matemakin kwamishinan bashida kir ki".

Ko a jikin Sadeeq yace "to sai me ai dama aiki nace zanyi kuma idan anyi min transfer din akan aiki ne kaga kuwa mai zai dame ni?".

Cikin jin haushin kalaman sa Farooq yace "babu, dama yanzu baza kasan inda matsalar take ba sai nan gaba".

"Am kaga dama akan yarinyar can na kira ka".

"Wace yarinyar?". Farooq ya tambaya duk da ya gane akan Siddeeqah Sadeeq yake magana amma sai yai masa bariki

Cikin kosawa da maganar Sadeeq yace "wai meyisa ka fiye surutu ne kafi son aita maimaita magana daya, bayan kasan yanzu bani da wata matsala da ta wuce waccan yar kyauyen".

Cikin zolaya yace "kai malam ni bana son gulma ka fito kayi min bayani sai kace matar ka amma sai wani boye-boye ka ke".

"amma kai ba karamin dan iska bane ni zaka raina wa hankali sai anjima na ma fasa fada maka abinda zan fada".

Farooq na dariya yace "matsalar ka ce wannan, nan da 15 minutes zan kara so insha Allah kace mata ta shirya".  Yana gama fada bai jira amsar Sadeeq ba ya kashe wayar

* * * * * * * * * *
"Shalele".

"Na'am". Abbah

Wai kuwa kin tuna aboki na Dr Usman da yake da zama a dubai?".

" Eh Abbah ".

"yauwa kin San ai yana da d'a, da yake karatu a kasar misra?".

"eh Abba kan ya tafi ma ai yana zuwa nan ko ba Maheer ba?".

"shi fa ashe baki manta dashi ba na dauka kin manta dashi to kinsan shi kadai Dr ya mallaka kamar yadda nima ke daya na mallaka".

"eh hakane Abba".

"Masha Allah na zauna ni da Dr din munyi magana har mun gama yanke hukunci zamu hada ku aure kar shen watan nan zai dawo dan ya kammala karatun sa a harkar kasuwan ci, kuma da ya dawo sai biki babu bata lokaci".

"amma Abbah".

"abba me? Shalale a wannan karon ko sau daya ki daure kiyi min abunda nike so, duk da nasan kina da Wanda kike so amma ni wannan ne zabi na".

Yana gama fadar haka ya mike gabad'aya Zuby jin ta take kamar ba ita ba saboda tasan Maheer mutum ne mai shegen sa ido da taka tsan tsan akwai shi da tsoran Allah kuma yana son mace mai addini dan yasha fada mata, shin ma cewa yayi yana son ta Ko kuwa dai iyayen su ne suke son su hada auren?
Tashi tai daga zaunan da take ta shiga yin safa da marwa tana zagaye dakin, a haka Mama ta shigo ta cin mata

* * *

Please
Comment
Follow me
Vote
I love you all Allah ya bar zuminci da kauna

NI DA YAYA SADEEQ

·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

End of Chapter 23Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next