Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel

Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel

Author: M Shakur
Chapter 25 of 31
About 18 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters

______Shi kuwa Farooq tsabar mamaki sai mutsuka ido yake yana budewa gani yake kamar a film yake kallon su.

can Daddy ya numfasa yace "dama kai niki jira yanzu nike cewa Umar yaje ya kira min ku  dan lokacin tafiya ta yayi".

"Siddeeqah". Daddy ya kira suna na cikin wata murya mai nuna ana jin tausayin wanda akai wa ita".

"na'am" nima nace bayan na zare hannu na daga jikin yaya na daga kai muka hada ido da shi.

Ya cigaba da cewa "shin kin amince zaki tafi makarantar kwana?".

Ina wasa da yatsaun hannu na nace "eh na amince Daddy".

Sai alokacin Momy dake tsaye ta zauna tana fadin "Alhamdu lillah Allah yasa hakan ne yafi alkairi".

Take yaya Sadeeq ya sauke ajiyar zuciyar da ko wannen mu sai da ya dago kai ya kalle shi, ni kuwa takaici ne ya kamani ganin yadda yake murna zai rabu dani sai kace zai rabu da musifa, lallai ma yaya tabbas zan nuna maka nima macace kuma zan iya yin duk wani abu da mata suke yi wajen burge mazajen su, sosai nayi nisa cikin tsara yadda abubuwa zasu kasan ce idan na girma, firgigit nai a dan tsorace na dawo hayyaci na  sakamakon tabani da kafa da yaya yai.

Daddy yace "Siddeeqah lafiya tunanin me kike yi haka? bayan na hana ki yin dogon tunani irin wannan, kina yar karamar ki  Ko so kike hawan jini ya kama ki? Ki mutu tun kamin lokacin ki yayi?".

Baki na narawa nace "A a Daddy insha Allah na daina daga yanzu".

Yace "Masha Allah, Allah yai muku Albarka ni zan tafi ki kula da kanki banda kula kwayen banza karatu ne ya kaiki shi zakiyi "

Nace "to Daddy nagode insha Allah bazan baku kunya ba".

Sai da ya sallami duka yaran gidan, dama Momy ya ruga ya sallame ta, kana yabi ko waccen mu da kudi masu kauri, Gaba dayan mu muka dunguma zuwa harabar gidan saboda muyiwa Daddy rakiya, saida muka ga tafiyar shi sannan muka dawo gida, Momy ta daura daga inda Daddy ya tsaya nasiha take min mai ratsa zuciya, jiki na duk yai sanyi, son Momy da kaunar ta yana dad'a ratsa ilahirn jiki da bargo na, saboda yadda take kula dani, da nuna min so da kauna.

Bayan ta gama min nasihar tace "naje na kara shiryawa".

Kallon Ummi da Khadija nai muka hada ido naga jikin su yai sanyi Umar kuwa harda kwalla, jiki na a sanyaye na mike  na haura sama ba wani wankan na sake ba kaya kawai na sauya  i zuwa riga da sikel na atamfa dinkin bai min yawa ba kuma bai kamani ba, sannan na dauko hijabi na nasaka, ko da na sauko a tsaye na samu Yah Sadeeq da Farooq da wani katon akwati a gaban shi, yana Murmushi yace "yauwa muje ko, ke muke jira".

tuni kwalla ta fara wanke min fuska ta nace "amma yaya baka kira min Inna ba".

Shafa keyar sa yai  yace "ai na manta gwara da kika tuna min".

Hannu yasa a aljihu ya ciro wayar sa, amma sai ya rasa wa zai kira sanin Inna babu waya a hannun ta dama da ta Farooq suke gaisawa "saida ya dan bata rai yace "kina da rigima Siddeeqah sanin kanki ne Inna bata da waya"

Goshi na dan dafe, tuna cewar batada wayar.

Yace "amma dai ki bari zan san abin yi tunda ni yau zan koma zan baki number ta idan kinje makarantar sai ki bama wata senior ta kirani sai na hada ku kuyi magana".

"to" kawai nace

har bakin get su Momy suka rako ni, in rungume wannan in saki wannan haka dai nan ta kuka Khadija da Ummi da Umar suna tayani, yayin da Momy ke bamu hakuri kamar kar mu rabu da juna saboda sabon da mukayi,  sabanin Jiddah da ko Allah ya kiyaye hanya bata ce ba sai kallon banza da take bi na dashi, tana cika tana batsewa, yi  nai kamar ban gan ta ba saboda yanzu ba lokacin fada bane a gurina.

Da kyar yaya ya lallashe ni na shiga mota inajin raina babu dadi, tuni daman yah Farooq ya shiga sannan shima sadeeq din ya shiga mai gadi ya wangale get muka fice, su Momy nayi mana Allah ya sauke ku lafiya.

Yaya Farooq ne ke tukin yayin da Sadeeq ke kujerar me zaman banza ni kuma ina gidan baya ji nike gabad'aya rayuwar ta dagule min tafiya ta fara yin nisa dan barci har ya fara dauka ta

* * * * * * *

Zaune take kan dan madaidaicin gadon ta hannun ta rike da wayar ta sai cije lebe take tana tsaki wai ita Sadeeq zaiki dagawa waya to wallahi bai isa ba tun da yace yana son ta sai ya aureta, ta fada afili yayin da tayi  kwafa.

Number Lubansy ta danna kira har tafara ringing sai kuma ta kashe saboda tasan itama fushi take da ita baza ta d'auka ba, idan tana son su shirya sai dai fa ta shirya taje gidan su, gashi ita kuma yanzu bata jin zata iya fita saboda zuciyar ta babu dadi, safa da marwa ta cigaba da yi gabad'aya ta rasa me zatai, can ta tuna da group din su na madugo association aran ta tace "bari na dan hau online ko na samu na rage damuwa" gefan gadon ta zauna kana ta dauko wayar ta shiga cikin whatsapp din nan ta tarar da sakonni masu yawa amma duk bata tsaya bi ta kansu ba, abinda ya kaita kawai shi take so tayi, bayan ta shiga cikin group din a hankali tafara karanta sakonnin da akayi bata nan bata jima tana duba chart d'in ba ta fahimci fada a keyi, sakamakon wata da tayi left cikin sauri da sauri ta cigaba da duba sakonnin har zuwa inda aka tsaya da firar take ta fahimci Sumy ce tai left kuma ana kyautata zaton yar leken asiri ce gabad'aya hankulun officials da members din kungiyar a tashe yake saboda idan asiri ya tonu ba karamin yaki za ai ba, tuni Zuby ta shiga cikin firan inda har take bada labarin tayi magana ma da yarinyar har take ce mata "hajiya Tubalas ce ta kawo ta"

Hajiya Tubulas da jin an ambace ta, ta shiga auna ashar tana cewa "kada ayi mata sharri ita yanzu ko wuqa a ka sa mata a wuya a kace ta siffan ta kammannin Sumy to sai dai a yanka ta dan bata san ta ba".

Shugabar kungiyar madugo tace "ya kamata a hada meeting na gaggawa saboda a kawar da wannan gagarumar matsalar".

Tubulas tace "gaskiya bazai yuyu ba saboda a cikin dokokin kungiya ba a meeting sai ranar litinin din da tazo a cikin karshen wata, kuma kunga yau talata 28 ga wata, nasan kunsan cewa  karya doka daya ta wannan kungiyar dai dai yake da tonuwar asirin mu gabaki daya".

Sai alokacin Turai ta tuna da wannan dokar kuma gaskiyar Tubulas ne karya daya daga cikin dokokin kungiya babban laifi ne dan har gwara su dauwama a cikin wannan tashin hankalin da suke ciki, amma abin dubawa anan shine wata uku da suka wuce duka watan bai kare da litinin ba, kuma da alamar wannan ma ba da litinin zai kare ba, tunda yau talata.

Duk kannin su sunyi na'am da batun Tubulas saboda haka suka ce a nemo wata mafitar amma haka sukai ta fama duk inda suka bi sai suga babu hanya

Zuby dai gajiya tai ta sauka daga online din tana mamakin yadda Sumy ta ci amanar su, tasan tabbas kungiya bazata bar ta a haka ba sai ta dauki mummunan mataki akan ta.

Kofar dakin ta taji ana bugawa da sauri taje ta bude ba tare da ta tambayi wanda yake buka kofar ba, koda ta bude Lubancy ce ta shigo tana wani shan kamshi bakin ta dauke yake da chingom tana taunawa yana kara kas-kas, haka dai tai ta yamutsa baki tana yauki, bayan Zuby ta maida kofar ta rufe tazo ta rungume ta tana cewa "aminiya nayi missing din ki". Lubancy taso sharewa amma saita kasa saboda a matse take tuni itama ta rungumo ta tana sauke ajiyar zuciya, basu tsaya wata wata ba suka shiga cire ma juna kaya suka fada kan gado suna nishi tuni suka fara shafe-shafen juna suna sauke ajiyar zuciya.

idan kida ya sauya rawa ma canza ta ake yi, ganin abin yafi karfi na yasa na fito daga dakin naja musu kofa, ina yi musu adduar Allah ya shirya su dan wannan dabiar bata mutanen kwarai bace, wace irin musifa ce wannan da mace take neman yar uwar ta mace yayin da shima namiji yake neman dan uwan sa namiji, shiyasa annoba bazata rabu damu ba saboda aduk lokacin da akasumu saukar annoba to sabon Allah ne yai yawa akasa, kuma duk masu wannan dabiar a wuta zasu dauwama, indai basu tuba sun daina ba.
wa'iya zu billah.

* * * * * * * *

Yunwar da ta fara kwakular ciki nane ta tashe ni daga nannauyen baccin daya dauke ni, na manta a mota nike saboda haka nai mika gami da yin juyi, ai kuwa cikin rashin sa'a na fada sakon mota inda ake saka kafafu, ihu na fara ina kiran sunan yaya da duk ya bi ya gaji sai mita yake wai Farooq baya gudu ". Shi kuma Farooq na cewa" in ba sama kake so na tashi ba ai wannan gudun ya isa ".

Ihu na ne ya katse musu firar su da sauri yaya ya juyo da kansa cikin motar yana fadin "subhanallah garin yaya haka ta faru maza tashi". Ya karasa maganar yana zuro da hannayen sa da kyar na iya temaka masa ya daga ni, bayan na gyara zama na akan kujera nace "yaya wai har yanzu bamu kai ba ni na gaji yunwa nike ji". Na karasa maganar cikin sigar shagwaba, nuna min Farooq yai yace "duk laifin shi ne kwata kwata baya sauri tafiya yake kamar wanda yake tsoran taka kwalta".

Nace "to ni yaya yunwa nike ji"

Yace "to bari mu karasa can gurin ina kyauta ta zaton karamar kasuwa ce sai muje baza'a rasa abin tabawa ba". Ya fad'a yana nuna min wani guri da nike hangen mutane

"To" Nace yayin da na hada kaina da gwuiwa ta

Ba mufi minti 7 ba muka karasa bakin gurin, kasuwa ce yar karama mata da maza sai zurga zurga sukeyi, yara da manya Farooq yace "banda abinka Sadeeq me zamu samu anan da zamu ci?".

Yace "mu fita ahaka ba zamu gane ba kuma can ma kamar masallaci ne mayi sallar azahar.

Yah Sadeeq yace" ki zauna a mota bari mu fita mugani ko zamu samu abinci".

Ban bashi amsa ba suka fita harda rufe motar

Basu wani jima ba sai ga Yah Farooq ya dawo da kwano a hannun shi da kwarya, bayan ya bude motar ya miko min na amsa, shi kuma ya juya 

Koda na bude kwanon danbu ne na gani yaji gyada da zogale yayin da ita kuma kwaryar fura ce acikin ta me rai da lafiya

Ba tare da nayi bismillah ba na shiga cin danbun, duk da yawan danbun saida na kusan yin rabin shi saboda ina mutukar son danbu a rayuwa ta, bayan na koshi kuma na dauki kwaryar fura itama na fara sha saida naji na cika cikina dam, sannan na hakura ba don bakina ya koshi ba sai don cikina da ya koshi

Gyatsa nike so nayi kozan dan ji dadin ciki na amma taki zuwa.

Can saiga su yaya nan sun dawo hannun Yah Sadeeq dauke da gorar ruwa bayan sun zauna yace "kin rage dan bun?".

Nace "eh".

"yauwa miko wa Farooq danni bazan ci ba furar zan sha ai itama kin rage?"

"eh nace yayin da na miko mai kwanon danbun dana furar

A mota suka ci bayan sun gama  suka je suka mayar da kwanon da kwaryar

Daka bisani muka kuma daukar hanya

" Nace yaya amma dai mun kusa zuwa ko?"

" eh mun kusa bai fi sauran mu 30 minutes ba mu karasa, ya nuna min wata katan ga da muke ta shigewa yace "nan kinga duk makarantar ce, zaro ido nai nace" kai yaya gari guda haka ".

Yace" eh har tafi haka girma bari muje ki gani".

Haka dai nai ta yiwa Sadeeq surutu yana biye min duk da fuskar sa babu wal-wala amma duk tambayar da nai masa yana bani amsa, a raina nike cewa "nasan yana tsoron nace na fasa ne shiyasa yake amsa min".

* * * * * * * * * * *

Aban garen Zuby kuwa bayan sun gama sheke ayar su tashi sukai suka shiga wanka kamar kullum nan ma saida suka bata lokaci suna tsotse-tsotse kana suka fito fiskokin su dauke da nishadi suka shirya cikin wata doguwar riga me ruwan kwai tana da laushi matuka Lubancy tace "ina zamu yau?"

Zuby tace "gurin shakatawa man, yauwa naga baki hau online ba meyisa".

Lubancy tace "banida data ne, wani abun ya faru ne ?"

Zuby tace "kwarai ma kuwa ina wannan yarinyar da kika sameni ni da ita jiya?".

Tace "eh na tuna ta".

Zuby tace "ashe yar lekan asiri ce yanzu haka tayi left a kungiya kuma ni fa cemin tai Tubulas ce ta kawo ta ashe karya tai min".

Lubancy tace "nifa shiyasa tun na kalli yarinyar naji batai min ba kwata-kwata kuma yanzu wani matakin aka dauka?".

"Har yanzu dai ba'a samu mafita ba kasancewar wa'innan tsinannun dokokin kungiyar na aiki, ke nifa abun ya fara isa ta gashi yanzu wlh ina cikin damuwa" Zuby ta fada tana sauke ajiyar zuciya

Kusa da ita Lubancy ta matso ta ce "kawa ta me ke damun ki fada mun naji ko zan iya miki magani".

Nan Zuby ta kwashe labarin komai yadda sukai da Abba ta fada mata hankalin Lubancy a mutukar tashe tace "da matsala gaskiya ya zama dole a fada wa yan kungiya saboda su taimaka mana da shawara kinsan a ka'ida ko aure kai baka daina wannan harkar da zaran ka bari kungiya zata tona maka asiri kuma kinga Maheer ba kalan mazan da zasu dauki haka bane".

Gwauran numfashi Zuby ta sauke tace "wallahi kawa ta shiyasa duk na bi na damu amma dai mu dan jinkir ta kafin mukai maganar kungiya idan Abba ya dawo zan roke shi".

Lubancy tace "to Allah yasa a dace".

"Ameen" ta fada yayin da ta mike ta dauki katon hijabin ta gami da fiddo nikabin ta a jaka tace "kawa tashi ki shirya mu tafi".

"To" Lubancy ta fada yayin da itama tai shiga kamar yadda Zubyn tai kana suka fito

Mama Mama Zuby tai ta kwala mata kira daga can ciki Mama ta amsa

Zuby tace "kina ina ne Mama?"

tace "ina kitchen"

Shiga kitchen din sukai inda suka tarar da ita tana nuna ma mai aiki wani abun gasa kaza da aka siyo shi sabon yayi.

Fuskar Mama dauke da fara'a tace "sai ina kuma?"

Lubancy tace "wallahi Mama mun gaji da zaman gidan ne shine zamu fita ba jimawa zamuyi ba".

Tace "to adawo lafiya"

"Allah yasa".

* * * * * * * * * * *

Wangala-wangalan get yaya Farooq ya wuce guda biyu, kana yai tafiya marar tsayi a bakin wani guri yai farkin danaga an rubuta staff room, kasan cewar na iya karatu amma ban san ma'anar shi ba,

Shiru yadan ratsa mu kana yaya Sadeeq yace "mu sauka man".

Yah Farooq ya fara fitowa sannan sai yaya Sadeeq, bayan ya fito yazo ya bude min kofa yace "fito mun kawo, bayan mun fito office-office mukai ta shigewa har muka isa wani office dan madai-daici, shiga mukai da sallama dauke abakin su yaya, inda muka sami wani malami a zaune da takardu a gaban shi yana ta dubawa, da alamar shine abokin yah Farooq ganin su yaya Sadeeq ya aje abinda yake, yah Sadeeq ya mika masa hannu, yana Murmushi ya amsa, hakama yah Farooq bayan sun gama gaisawa yai musu nuni da su zauna akan wasu kujeru da aka tanade su saboda baki,

Babu abinda nike sai zaz-zare ido ina kara shigewa yaya.take naji bazan iya zama a wannan dokar Dajin ba gaskiya to wai ma in banda  abun mutane taya za azo dokar daji ayi gini ace wai makaranta, ni dai gaskiya bazan zauna ba.

Da turan ci malamin yai min magana, ban san me yake nufi ba yaya Sadeeq yace " ya sunan ki yace?"

Nace "Siddeeqah Suleiman".

Yace "suna mai dadi, ku tashi na raka ku ofishin shugabar makarantar".

"to suka ce yayin da suka mike a tare, muka fito ina ta ganin dalibai na wucewa dai-dai haka, wani office din muka kuma shiga ba laifi ofishin babba ne kuma an dan kawata shi wata mata ce muka gani zaune akan kujera fuskar ta sanye da sirrin gilashi, matar ta manyan ta fara ce sosai kamar ka taba jini ya fito, dagani hutu ya zauna a jikin ta, tana da kyau dan irin doguwar fuskar nan gare ta tana da manyan idanu da dogan hanci ga dan karamin bakin ta, sanye take cikin kayan alfarma tana dan juya kan kujerar da take zaune, da Sallama muka shiga, fuskar ta dauke da fara'a ta amsa kana ta nuna mana kujeru tace mu zauna,  tunda na kalli matar naji ina son ta ban taba haduwa da wanda naji ya kwanta mi  arai lokaci daya kamar ta ba,

To abangaran Hajiya Amina ma haka lamarin yake dan kuwa tana kallon Sadeeq da Siddeeqah taji gaban ta ya fadi, ga kuma kwarjinin da sukai mata har taji  son su da kaunar su ya shiga ranta.

Tana dariya tace "Malam Naseer suwaye wa'innan?".

Yace "ai ranki shi dade sune wa'inda na miki maganar su wannan itace kanwar tasu da akai ma register".

Tace "masha Allah" yan mata ya sunan ki?" Hajiya Aisha tai maganar tana kollon Siddeeqah

"Siddeeqerh" na bata amsa yayin da muka hada ido ta sakar min Murmushi tace "sunan ki babban suna ne kuma nima sunan yarinya ta babba ce".

Nace "Ammi da gaske kema kina da yarinya me suna na?".

Bani da na fadi sunan ba ita kanta Hajiya Aminan yanayin ta ya nuna taji dadin yadda na kira ta, shi kuwa yah Sadeeq mamaki ne ya kama shi.

Tace "da gaske nike yata amma a halin yanzu bama tare".

Nace "to Ammi tana ina?".

Idon Hajiya Amina ne ya kawo kwalla ganin haka yasa yah Sadeeq yace "ke Siddeeqah ya isa haka kin cika tambaya".

Jikina a mutukar sanyi nace "Ammi ki yakuri na daina".

Handkerchief ta d'auka ta dan yi sama da glass din ta ta share kwallar data cika mata ido tace "babu komai yata".

Ya Sadeeq ta kalla tace kai ya sunan ka?". Nai sauri nace "Sunan shi Sadeeq yaya na ne kuma dashi Daddy ya daura min aure yace Wai alkawarin kanwar shi ne data...".

"Ke!!!" Yah Sadeeq ya daka min tsawar da saida naji hantar cikina ta kada a tsorace na dago kai na kalle shi inda na hangi tsan tsar bacin ran sa, ture ni yai daka kusa dashi ya tashi ya fita  fuu kamar zai tashi sama.

Farooq yace "ranki ya dade ki yaquri haka yake zuciya gare sa".

Hajiya Amina da ke saka abubuwa barkatai a ranta tace "ba komai, amma abinda ta fada gaskiya ne dan ta tuna min da wani dana shima haka yake kamar wannan?".

Farooq yace "eh gaskiya ne".

Daga haka babu wanda ya kuma furta wata kalmar

Malam Naseer ta duba tace "Malam jeka dasu office dinka kaina ya fara min ciwo ka bata ajin da ya dace da ita"

"To" yace muka fito, yah Sadeeq na hanga acan jikin mota, harara ya wurga min nima na rama harda murguda baki, a zuciya ta nike cewa ba zai taba canzawa ba".

Bayan mun zauna a office din

Malam Naseer yace "

"A jin ki nawa a makarantar da kika baro?"

Nace "Js 1"

"Shekarun ki fa?"

"sha hudu 14" na bashi amsa a takaice

Wata farar takadda ya dauko ya danyi rubuce-rubuce kana ya shiga yin magana da turanci yah Farooq na bashi amsa bayan sun gama ya miko min wata yar takadda yace "zan sa students su zo su tafi dake yanzu hostel din ku, dan yanzu dalibai suna aji ana karatu amma ke bazaki samu damar yin karatu yau ba saboda an kusa tashi ".

" to" nace bayan na amsa takaddar

Bayan mun fito da gudu na isa gurin yah Sadeeq na kan kame shi ina kuka nace "yaya yanzu tafiya zakai ka barni? saboda ba ka kaunata, kalli fa kaga ni dai na fasa bazan iya rayuwa anan ba".

Rage tsayin sa yai ya tsugunna yace "kowa da haka ya saba kema zaki saba karatu ne kuma ba'a samin sa a sauki saboda haka ki jure sannan banda rashin kunya dan akwai ban banci tsakanin makarantar kwana da ta jeka ka dawo, idan senior tace kiyi kiyi banda kin ji dan idan kika ce zaki rashin kunya wuya zaki ci".

Hawaye ne masu zafi suka cigaba da wanke min fuska na kara rungume shi, yah Farooq yazo yace "sake shi Siddeeqah, ki hakuri ba wani jimawa zaki ba zaku tafi hutu".

Ban sake shi ba na cigaba da kuka na "da kyar ya Sadeeq ya dago ni yana cewa" nace ya isa haka ki daina kuka muje na baki number na kuma insha Allah idan na samu lokaci zan zo na duba ki, kuma idan lokacin ziyara yai su Momy zasu zo".

Nace "to yaushe ne ziyarar?".

"an kusa". Ya bani amsa yana Jan hannu na muka nufi gurin mota

Bayan motar  ya bude ya fiddo wannan katon akwatin kana ya maida ya rufe

Yace "yauwa wannan shine akwatin ki duk abinda kike so akwai a ciki".

Kanshi ya dan dafa yace "Farooq munyi mantuwa fa"

"ta me?". Farooq ya tambaya

"Uniform din ta mana".

  yace "a haba na dauka ka dinka mata ne bari naje in karbo".

Cikin office din da muka baro ya koma bai wani jima ba sai gashi ya dawo da leda a hannun sa

Wasu students ne guda uku suka zo inda muke da turanci suka gaida su yaya suka ce Sir Nazeer ne yace muzo mu kaita hostel din ta, yah Farooq yace "to gata nan dan Allah amana ku kula mana da ita".

"insha Allah suka ce".

Kana ya Sadeeq ya ciro kudi ya bani nace "bana so yaya wanda Daddy ma ya bani suna gida na baro su".

Yace "ki amsa ki nada bukatar su".

Duk yadda yaso na amsa ki nai ba yadda ya iya wasu kudin ya ciro yabawa yan matan yace "wannan naku ne ku raba wannan kuma nata ne idan tanada bukatar wani abun sai ku bata".

"To" suka ce yayin da suka shiga Jan akwati na

yah Sadeeq yace ce "to Siddeeq zo ki amsa number kada na manta mota ya shiga ya dauki memo da biro ya rubuta number ya miko min na amsa

yace" sai na dawo duba ki Allah ya bada sa'a".

Ameen yah Farooq yace inda shima ya shiga mota hannu nai ta daga musu har saida naga sun Kule min sannan na daina na kalli wa'innan yan matan guda uku nace "ina zamu yanzu?"

Ba wanda ya tanka min suka cigaba da Jan akwatin da kamar na daina bin su sai dai nace bari naga gudun ruwan su

* * * * * * * *

Follow

Comment

Vote

NI DA YAYA SADEEQ

·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·

Not edited

End of Chapter 25Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next