Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
بسم الله الرحمن الرحيم
_____Jin jina kai Inna tayi, sannan ta nufi hanyar d'akin da Momy take, ta 'kwan-'kwasa musu kofa, ta d'an jima a bakin 'kofar, kafin Momy ta bud'e ta fito, "ina kwana hajiya". Momy ta gaisar da hajiya
cikin sakin fuska Inna ta amsawa surukar ta "ya ba'kun ta?".
"Lafiya lau". Momy ta bata amsa,
"to alhamdu lillah".
A cewar Inna
ta dora da cewa "kiya 'kuri na tashe ki kina tsaka da bacci".
"babu komai Inna" cewar Momy,
Inna ta cigaba da cewa "daman Garba ne wai tun asuba yake ban d'aki". Har yanzu bai fito ba, Siddi'ka tace "yau kamar bashi ba yana tayin wasu abu irin na taba'b-'bu" shine nace "bari na tada ki muje bayin mugani ko lafiya".
Momy tace "Hajiya Inna badon karkice na raina ki ba da bazani ba tunda shi bayajin magana".
Inna tace "Ha'kuri zaki Aisha muje mugani ko lafiya kinga da ya idar da sallar asuba yake tafiya gurin aiki, amma yau shuru".
"To". Momy tace badon ranta yaso ba, tabi inna ban 'dakin
Koda su Momy suka 'kara sa bakin bayin sunan shi Inna takira "Garba Garba". kamar babu kowa a ciki, saboda bai amsa ba, saida Momy tace "sadeeq wai lafiyar ka?".
Da wata iriyar murya yace "wallahi Momy nima ban sani ba".
Tace "au daman kana jin Hajiya na kiran ka kayi shuru, saboda ka raina mutane, ai sai ka fito ka bawa mutane guri, saboda gari ya waye".
Yace "Momy bazan iya fitowa ba".
"saboda me?". Ta tambaya
Momy wlh yau Ban san me ke shirin faruwa dani ba, ko nayi gamo ne tun nafito sallar asuba na had'u da bala'i ko sallar ma banyi ba". 🤣
Salati suka hauyi Inna natafa hannu kace "baka yi sallah ba tom wai me kake yi a cikin bayin ne haka?". Cewar inna
Cikin jin zafin tambayar da Inna tayi mai Sadeeq yace "Wai baki ji nace ina cikin bala'i bane, amma kike sake tamba ta".
Momy ce ta daka mai tsawa "rufe min baki anan gurin ko na ci maka mutun ci, kuma kafito kabawa mutane guri suna son shiga bayan gida".
Sadeeq yace "Amma Momy...".
Katse shi tayi da "ko baka ji abinda nace maka bane?".
"naji". Ya fad'a a ta 'kaice,
d'an matsa wa suka yi nesa da bayin,
Ni kuwa da tun-tuni nike zaman jiran fitowar sa, da naji Momy tace "ya fito". Sai Na 'kara gyara zama na a kan kurer tsakar gida
Saida ya d'auki tsayin minti biyar kafin ya cire sakatar, ya bud'e 'kofar ya fito, babu ko riga a jikin sa, sai d'an gajeran wando, basu Inna kad'ai ba hatta ni da niyi zaman jiran fitowar sa, saida na tashi tsaye saboda yadda yayi wani iri, kamar ba yaya Sadeeq d'an gayu da 'kwalisa ba
Yayi wani wuji-wuji dashi idanuwan sa sunyi jawur se muts-tsuka su yake ga jikin sa duk ya karce sa da farce, harda shedan jini, ba 'karamin ciwuka yajiwa jikin sa saboda susa ba, hatta da fiskar sa bai bari ba akwai alamun karta, duk ya fad'a fuskar nan yayi zuru-zuru,
mamaki ne kwance a kan fuskokin su Momy
Momy tace "Wai sadeeq me ke damun ka haka kamar me borin jini?".
"Momy nima bansani ba". Ya bata amsa
Yanzu yaji sau 'kin 'kai-'kayin da jikin sa ke yi, sai dai rad'ad'in da fatar jikin sa ke mai,
"to ai saika je ko jallabiya kasa mutafi asbiti". Inji Inna,
"A a Inna ba sai kunje ba don asbitin gari zani kuma da nisa ku zauna a gida". Ya fad'a yana tafiya
ta kusa dani yazo wuce wa, saida muka yi ido hud'u dashi na kwashe da dariya🤣
kallan tsana yayi min, sannan yanufoni dagudu na mi'ke nanufi bayan Momy ina haki, biyoni yayi shima, da hannu Momy ta da katar dashi san-nan tace "amma walahi Sadeeq kaji kunya kanwar kanwar ka itace abokiyar yinka, ba dole ta raina ka ba,
Wallahi ka bada maza wuce kabani guri, kamin ki'kam a gaba kamar wani soja, Ko wannan iftila'in daka fad'a be isheka ishara karabu da yarinyar mutane ba". Momy ta fad'i haka tana nuna mai hanya da hannu
Badon yaso ba saidan yabi umarnin mahaifiyar sa,
had'a ido muka yi dashi nayi masa gwalo ina 'kara yin dariya ciki ciki😄
Yace "Zan kamaki yarinya wallahi zakiyi bayani".
Inna tace"Ai gashinan alhakin tane wannan abin da ke faruwa da kai, saboda Allah ba azzalimi ne ba saidai bawa ya zalinci kansa".
"Kwarai ma kuwa". Momy tace
Jikin sa babu 'kwari ya wuce mu, tashi nayi nima nakoma d'aki, saboda na gabatar da sallar a subahi, sai a lokacin nayi sallar takwas saura, ina idar wa ko kan sallaya ban sauka ba nahau rawa da juyi, saboda na rama a binda sadeeq yayi min gado na koma saboda yau bazan je 'yar kasuwa yin tsokanar safe ba bacci zan koma
♾️♾️♾️♾️♾️
Abangaren sadeeq kuwa koda yaje asbiti, kulawa ta mu samman suke bashi saboda asbitin su na 'yan sanda yaje har gado aka bashi sannan aka saka mai ledar 'karin ruwa, saboda yana bukatar ruwa ajikin sa
Harda allurar bacci a kamai saboda ya sami hutu
♾️♾️♾️♾️♾️
Koda na farka daka bacci 'karfe sha d'aya saura11:00am naji dadin baccin sosai domin ya ragemin damuwa
Kamar yadda nasaba idan natashi bacci mi'ka nayi babu ko salati, na sauka daga kan gadon, na d'auki brush d'ina na fito tsakar gida nayi, san-nan nanufi falon hajiya, acan na iske su Khadija suna cin waina da miya,
zama nayi kusa da Momy nace "ina kwana Momy".
"lafiya lau". Tace min "kin tashi lafiya?".
Nace "eh Momy lafiya lau". Saboda ni bana son doguwar gaisuwa
Tace "ba inda ke miki ciwo?".
kai na d'aga mata
"madallah" ta ce masha Allah haka ake so
Inna na kallah naga ta tasa kwad'an zogale da kuli a gaban ta sai kaiwa baka takeyi, d'an Murmushi na sakar mata, ita ma ta maido min
Kana na gyara zama, na saka hannu a kular wainar su Khadija, ina ci ina lumshe ido saboda dad'i
Nace "Inna wai wannan wainar wane gida ce".
Tace "ta gidan su fulera ce matar d'an tsoho".
"Haba koda naji". Nafad'i yaka yayin da nike kai lomar waina a baki na
"Kice kinyi santi" Murmushi nayi kawai na cigaba da aikawa cikina
Umar ma cewa "yayi ni rabon da naci
Waina me dad'in wannan wallahi na manta".
"Umar duk santin ne haka". Inji Khadija
Yace "ai kokema kinyi tunda naga kun-nen ki d'aya sai rawa yake yi".
Kowa a d'akin saida ya dara
♾️♾️♾️♾️♾️
Bayan Sadeeq ya farko daka nan-nauyan baccin da ya d'auke sa, jikin sa babu kwari ya tashi, a za filo a bayan sa yai kana ya jingi na, yana jin gaba d'aya jikin sa na mai ciwo, ga wata yunwa da ta ad'da beshi da kasala
Likatan ne yazo ya zauna agaban shi dayike a bokin sa ne kuma shima d'an sanda ne, yace "wai Sadeeq dame kai amfani ne?".
d'an shiru yayi kafin yace "nidai a binda nasani natashi da a suba lafiya ta 'kalau amma bayan na d'auki buta ta, naje bayi na dowo nafara jin yana yi na yana can zawa, koda na fara alwala ko fiska ban gama wan kewa ba, tsarkin da nayi yafara damu na,
Sai nasa aka kai min ruwan wanka, to na 'kar-'kare maka zance, daka zuba wannan ruwan a jikina kid'an ya sauya salo, sai azabar ta 'karu bayan na sa a mi'ko min sabulun wanka, ba ba nasha wuya fa sosoi, tun asuba nike a cikin bayi nine har 'karfe takwas saura, wannan raunin duk ni najiwa kaina, saboda 'kyai-'kayin da jikina yake min idan ban sosa ba bana jin dad'i".
Dariya sosai Dr Farooq yakeyi, Sadeeq yace "Kai Farooq banason iskanci fa nifa ban baka labari don kayi min dariya ba, sai dan kayi aikin ka".
Dr Farooq yace "ba ba wallahi labarin naka ne gunin ban dariya, sai kace a cikin shirin film".
Duka Sadeeq yakai wa Dr Farooq d'in, amma sai ya kau ce yana fad'in "shege kasamu kenan d'azun kamar wani lagwani kana ta num-far fashi kamar baza ka kai aniji ma ba".
Sauko wa Sadeeq yayi daga kan gadon, Dr Farooq yai saurin mi'kewa, d'akin suka fara za gayewa, Farooq d'in ya'ki barin sadeeq ya kamasa,
Dan kansa Sadeeq d'in da ya gaji ya ha'kura, ya janyo kujera ya zauna yana maida num-fashi, ruwan sanyi Dr Farooq ya d'auko a ciki firiji ya mi'ko masa, yana fad'in "maganin d'an iska kenan gobe ma ka 'kara".
Sadeeq d'in amsa kawai yayi be kula sa ba
NI DA YAYA SADEEQ
بسم الله الرحمن الرحيم
More Hausa novels
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel
By Oum Yasmeen
Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Ciki Da Gaskiya Book 1 Complete Hausa Novel
By Ubeera
Search across the available chapters.