Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
_____"To". Nace wa Momy na nufi hanyar kitchen bayan na shiga na d'auko kular abinci da zobon da Momy ta hada mai akan wani madai dai cin tirai na d'oro su sanda na fito babu kowa a falon har Momy ta wuce d'akin ta saboda haka nima na haura sama sai da na fara zuwa daki na na sauya kaya na, saboda izuwa yanzu nima na fara sabawa da kayan baccin idan ba dasu ba bana jin dadin baccin saboda haka na sauya izuwa wata farar doguwar riga mai kauri ta bacci akwai wata yar baza mai kamar leshi a gaban ta ina sau yawa na nufi bangaren ya Sadeeq da yake dan nesa da mu saboda saikin bi ta wata kofa sannan zai sada ki da bangyaran sa dake dauke da falo da d'akuna 2 sai bayi da kitchen, nayi sa'a saboda kofar shiga a bude take ina murmushi na karasa ciki saida na gama karewa falon kallo sannan naja dogon tsaki ina ta'ba baki na ce "shi ko kunya baya ji daki sai kace na mace". A bude na bar kofar sannan na wuce bedroom din sa da shiga ta naga gado a gyare luf luf dashi ya lailaye zanin gadon sa ji nayi ina sha'awar hawa gadan saboda haka na ajiye kular abincin a kan wani teburi nayi sufa kan gadon😜 ina 'yan tsalle tsalle na ina dariya ni kadai
♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Tafe yake a kan hanya tunani ne fal a cikin zuciyar sa ya sa'ka wannan ya warware wancen duk da tuki yake yi amma yayi zurfi a cikin tunanin sa ta yadda bai san mai yakeyi ba Allah ne ya tsare sa da kuma kasan cewar ba akan babban titi yake ba ringing din wayar sa ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya lula firgigit Sadeeq yayi saida ya dafa kansa "ya Salam ni Sadeeq mai ke damu na haka wani irin tunani ne kuma akan me nike yin sa mtssss" .yaja dogon tsaki ba shida amsar tambayar sa saboda haka ya lalubi wayar sa da yaji tana ringing bai wani tsaya ya kalli sunan wanda ke neman sa ba yana dauka ya kara a kunne.
Daga d'ayan bangar akace "wallahi aboki baka da mutunci daka zuwa Abuja ganin Princess sai ka manta damu, munafuki amma da anyi magana kace baka son yarinya ka tsane ta".
"shege akace maka kowa mayen mata ne irin ka ka rasa dawa zaka hada ni sai da yar karamar yarinya wacce ko...".
"haba malam kada kacika min baki daga karshe kazo ka fada tarkon karamar yarin ya".
"Wa ni?!". Ya fada yana nuna kan sa da yatsan sa Kamar Farooq din yana ganin sa "Allah ya kyauta ai na fada mata duk sanda taji nace ina son ta kada ta taba yadda dani saboda ba da gaske bane".
Farooq baiji dadin yadda abokin sa yayi su'bul da baka ba saboda haka yace "uhm Sadeeq idan Allah ya tashi kama ka bazai maka kadan ba kuma gaskiya bazan ji tausayin ka ba koda zanji sai ka ji jiki, saboda duk abinda ka Shuka shi zaka girba dama na kira ne naji ya kake ya Momy tunda duk kuna lafiya sai da safe".
"Kaga Farooq kada ka kashe a kwai maganar da nike so muyi".
"Ina jin ka to"
"yanzu haka fa a hanya nike naje naga gimbiya ta, gaskiya babyn ta hadu tafi kyau a fili nike fad'a maka komai yaji zam-zam hhhmm nasan ba lallai ka yarda ba tunda kaki ko hotan ta ka gani amma tun na ganta na shiga wani yanayi".
"Haba Sadeeq daman wannan ce maganar da kace za muyi?.
"Eh amma da akwai d'ayar nafi zumud'in wannan shiyasa na fara fada maka ita" kuma kasan nace "Momy ce take nema na ashe akan makarantar yarinyar nan ne to shine nike so ka nema mata admission a makarantar da Sadiya take saboda na cewa Momy na gama komai tafiya ta rage".
Shuru Farooq yayi na wasu yan da'ki'ku alamar nazari can ya numfasa yace "haba Sadeeq wai meke damun ka meyisa kake son ka kuntatawa yarinyar mutane wani irin makarantar kwana ana zaune 'kalau don Allah kajanye wannan maganar kaji tausayin ta
Har yanzu fa Siddeeqah yarinya ce karama na tabbatar ma batasan maye aure ba da tasani wallahi da...". Bai karasa maganar ba Sadeeq ya dakatar dashi da cewa "malam don Allah ba shawara na tambaye ka ba
Dan kaga na biyo ta hanyar ka shine zaka tozartani idan baza kaimin ba kawai ka fadamin"
"Allah ya huci zuciyar ka". Farooq ya fada kana yace "aji nawa za a sata?".
"Ko js1 ne asata ba matsala ta bace zan fi son haka saboda na more soyayya ta da Baby na kan tagama karatun"
Farooq nason yace wani abu amma gudun kar yakara laifi yace "babu damuwa zanyi kokari insha Allah ko js2 su kaita".
Daga haka sukayi sallama
Bayan Sadeeq ya gama faking din motar sa ya fito jinsa yake wani iri saboda haka ya haura sama bai kai ga shiga dakin ba yaga kofar abude yayi mamaki bai gama tsinkewa ba sai da ya shiga bedroom din sa ran sa a mugun bace ya karasa kan gadon da niyar fusgo ta amma sai yaji kamar an soka masa kibiya a cikin sa bai san sanda ya zube a kan gadon ba numfashin sa nafita da sauri da sauri Siddeeqah garin juyi ta wurga wa Sadeeq kafa ransa bace ya wurga mata harara, tuna aikin banza yayi tunda bacci take yi ya shiga kwala mata kira "ke ke uban wa ya ce ki shigo nan?"
Siddeeqah da kamar a mafarki taji ana kiran ta a firgice ta bude idanuwan ta suka sauka akan na Sadeeq dake mata kallon tuhuma fuskar sa a murtuke babu alamar wasa yace "dan uban ki uban wa yace ki shigo min daki?".
Siddeeqah gaba daya ta rike ce bakin ta na rawa take fadin "lah yah...!".
"Yayan uban ki zakiyi bayani wallahi bazaki sauka ba sai na yi ball da ke".
'Kokarin tashi yake amma cikin sa ya kara murde sa nan take ya rike cikin yana kiran sunan Allah a rude Siddeeqah ta 'karasa gurin sa ta kama hannun sa "yaya yaya meke damun ka haka me yasameka?".
A wahalce Sadeeq yace "cikina". Kama hannun ta yayi ya dora a kan marar sa ji tayi kamar akan shocking ya d'ora mata hannun saboda haka tayi sauri ta janye yaya bari naje na kira Momy saboda ni bansan mai zan maka ba, zata sauka kenan Sadeeq ya kama hannun ta idon sa a rufe yake cewa "kar ki tafi ki banni kizo dan Allah kada ki tafi" cikin karfin hali ya janyo ta ya matse ta a jikin sa yana fitar da numfashi da sauri da sauri
Gaba d'aya jikin Siddeeqah rawa yake ta kasa fahimtar mai Sadeeq din yake nufi da haka kokarin saka mata hannu a riga yake Allah ya bata sa'a ta kwace daga rukon daya mata tace "karamin mara mutunci, ashe daman kai dan iska ne to bari kaji ni ba yar iska bace inace daga waje kake to ba kaje gurin 'yan iskan naka bane?"
Sadeeq jin maganganun yayi kamar ta watsa mai garwashin wuta saboda zafin su gashi baya jin zai iya tashi bare yayi maganin rashin kunyar ta
Saida ta rike 'kugun ta ta dawo gaban sa ta dan jujjuya tayi fari da idanuwan ta tace "karamin d'an iska to duk abinda kayi min sai na fada wa Momy saboda tun muna yara ake jamana kunne akan mukula da maza shine a waje ba a lalata ni ba yanzu kai ka lalata ni" take ta fashe da kuka tana fadin "na shiga uku yaya Sadeeq yayi min ciki innalillahi wa innah ilaihi rajiun Allah kagani ni ba yar iska bace shine ya taba ni waiyo Allah Momy zata yanka ni yaya Sadeeq ka cuce ni azzalumi Allah sai ya saka min". Ta kara rushewa da wani irin kuka mai ban tausayi
Sadeeq bai fahimci mai Siddeeqah take nufi ba shidai yasan ana ce musu ko hannu suka bari namiji ya rike musu zasu dauki ciki to yana ga shiyasa yanzu take cewa yayi mata ciki😂 bai san sanda dariya ta kubuce masa ba, sai yanzu yake kara tabbatar da yarintar Siddeeqah kallan ta yayi suka hada ido tana rike da 'kugu tana jijjiga 'kirji
a yanzu yaji saukin murdawan da marar ke mai saboda haka ya kamo ta cikin zafin nama tana ta zizzille wa, bayan ya daidai ta natsuwar sa ya koma mata Sadeeq din da tasani ada yace "ke dan uban ki ni kike cewa dan iska?" ta tsorata da yadda taga yanayin sa saboda haka ta shiga yi masa magiya da bige bakin ta
Yace "babu ruwana ki daina buge bakin ki idan kina so kada na zane ki to kija bakin ki kiyi shiru da abinda ya faru a tsakanin mu ko Khadeeja kada ki fadama mata bare Momy idan kika yi haka kin tsira saboda nima bani nayi miki ba aljanu na ne suka miki kuma kin san aljani bai san a dunga talla da abinda ya aikata. Sai ya makantar da ke ko ya kurman taki saboda haka kija bakin ki kiyi shiru kuma ki tabbatar babu wanda ya ganki a lokacin da zaki fita daganan ".
Bakin ta narawa tace "to yaya". Sai alokacin ya sake ta ta nufi kofar futa daga bedroom din duk ta daburce dan kwalinta ma acan ta manto shi gashin kanta yayi yar batsa, sai yanayin ta ya nuna kamar bata cikin hayyacin ta tafiya take tana sand'a a haka ta fito daga ban garen sa tana gaf da shiga dakin Ummi taji ance "daga ina kika fito?". A dabur ce Siddeeqah ta juyo ta kalli Momy da ta tsura mata idanu, cikin in ina Siddeeqah tace "daga dakin yaya nike dazun dana kaima sa a binci na tsaya kallo har bacci ya kwashe ni sai yanzu da ya dawo ya tashe ni".
"Amma ya na ganki a furgice yayi miki wani abu ne?". Da sauri Siddeeqah tace "babu abinda yayi min saboda daga bacci na tashi".
Saida Momy ta kare mata kallon tsaf tace "kada ki boye min idan yayi miki wani abun fa kada daga baya azo asami matsala ki fada min gaskiya". Siddeeqah naso ta fadawa Momy abinda ya faru tuna kashedin da Sadeeq yayi mata yasa tace "Allah Momy babu abinda yayi min ki yadda dani Momy". Badan Momy ta yadda ba tace "jeki kada ki manta da adduar bacci".
"To Momy saida safe"
"Allah ya tashe mu lafiya
Ina jiran kyawawan comment dinku fans 💖💕💋
NI DA YAYA SADEEQ
˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙
More Hausa novels
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel
By Oum Yasmeen
Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Ciki Da Gaskiya Book 1 Complete Hausa Novel
By Ubeera
Search across the available chapters.