Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel

Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel

Author: M Shakur
Chapter 17 of 31
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters

______Sun d'auki kusan mintuna goma shabiyar a haka batare da d'ayan su ya yi 'kwa'k'kwaran motsi ba sai sautin bugun zuciyar Sadeeq dake sauka fat fat, Siddeeqah kuwa duk da akwai na'urar sanyin dake saka cikin motar saida tajike da gumi sharkaf, idanuwan ta suka dad'a fitowa waje. dago raunannun idanun sa yayi da suka koma launin gwauta saboda tsabar bacin rai ya sauke su akan na Siddeeqah, da sauri ta maida kanta kasa tana wasa da y'atsun hannun ta zuciyar sa ce take ingiza sa da ya shake mata wuya wata zuciyar kuma ta ce masa "Kul Sadeeq ka kashe gawar da ba taka ba, ka bud'e mata mota ta fita" haka kuwa akai yabi shawarar zuciyar da ta gar gad'e sa soboda haka ya bude mata murfin motar Siddeeqah naji ya bud'e tayi sauri ta bude murfin ta fito har tana neman dungurawa a kasa soboda yanayin Sadeeq d'in yayi mugun bata tsoro da sauri da sauri take tafiya jefa kafar ta kawai take batare da tasan inda take jefewa ta ba, ji tai ta ci karo da mutum a tsorace ta ja da baya ganin Sadeeq ne yabiyo ta d'ayar hanyar da ake iya haduwa da Wanda yabi ta gaban gida, yanda taga yanayin sa har yafi d'azun firgitar wa idanuwan sa sun kara yin jaa kamar Jan gauta, nufo ta ya fara yana d'an Murmushi yana shafa sajen sa, 'kafa mai naci ban baki ba gudu ta fara shima ya mara mata baya cikin ikon Allah saiga Momy a harabar gidan da alamar wani abu take nema saboda idanuwan ta a kasa suke, da gudu Siddeeqah taje bayan ta ta 'boye tana nishi "ke lafiyan ki kuwa daga ina haka kamar an koro ki?". Momy ta fad'a tana duban Siddeeqah Bata lura da Sadeeq ba, da hannu Siddeeqah ke nuna mata inda Sadeeq yake sai alokacin Momy ta dube sa, washe baki yai ya wayance yace ma Siddeeqah "ba dai kin ki bari na kama ki ba nima zan rama yarinya, waifa Momy ce mata nayi ta jirani mu taho tare shine ina gama faking ta rigani fitowa shine nabi bayan ta da ta hango ni sai tafara gudu nima shine na biye mata". Siddeeqah kamar sakarya haka ta saki baki da hanci tana kallon shi lallai ya iya tsara labari,

cikin gamsuwa da abinda ya fad'a Momy tace "ai da baka biye mata ba yarinya ce, amma gaskiya kun dade ko ka kaita wani gurin ne? Daddyn ku na ta kiran ka a waya baka dauka munyi tunanin ko ba lafiya ba hankali ya fara tashi".
"Wallahi lafiya lau Momy layi muka tarar a gurin saloon d'in, amma me ya fito dake naga kamar wani abu kike nema?".

"to babu damuwa, eh wallahi d'an kunnen Jiddah ne  guda daya ya fad'i sanda suka dawo daga asbiti".

Tace "anan ya fad'i shine nace bari na duba ko zan gani".

"haba Momy ke da kanki ina sauran yaran gidan?".

"Suna ciki Khadija ta ce ta gaji zata shiga ta huta dan ko abincin rana bata ci ba, Umar kuma yana tare da Jiddah, Ummi kuma tun safe ban kuma ganin ta ba".

"Kibar neman haka Momy muje ciki ba rabon ta bane kawai sai asai mata wani".

"dama a cikin irin tsarabar da Bilkeesu ta kawo musu ne alokacin da ta dawo daga India daham ne yanada tsada sosai yanzu ita kadai ce ba ta da".

"Momy ita ta jawa kanta".

Siddeeqah kamar ruwa ya cinye ta Momy ce ta kama hannun ta tace "muje ciki yau na girka abinda ki ka fi so a bincin gargajiya".

"dan Allah fa Momy?".

"zan miki 'karyane?".

"a a Momy".

Ta fad'a tana rufe fuskan ta da tafin hannun ta ahaka suka karasa cikin gidan Siddeeqah na mamakin Sadeeq,

Yayin da shi kuma ya ji haushin ganin  Momy a harabar gidan batare da ya ma Siddeeqah matsiyacin duka ba dan so yayi ya mata dukan ban kwana saboda ba lallai ya kuma haduwa da ita ba har sai ta dawo hutun makaranta, yanda bazata manta dashi ba

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Kamar wacce tayi karya takai ta komo tarasa ina zata sa kanta dafa kafad'ar ta akai da han zari ta dago kanta ganin Lubancy ce Kawar ta yasa Zuby sauke ajiyar zuciya tace "kawata kin zo a dai dai dan dama yanzu nike shirin zuwa gidan ku wallahi ina cikin tashin hankali nasan babu Wanda zai fitar dani saike".

"haba ke kuwa kinada ni kike cewa kina cikin tashin hankali kin manta wace ni kin manta kirari na? Bari na na tuna miki".

"a a barshi ban manta ba kai na ne ya kulle na rasa mai yake min dadi, sai yanzu dana ganki na ji sauki a raina nasan ke a wurin ki ba komai bane soboda na shiga matsalar da tafi wannan kuma kin mini maganin ta".

"yauwa yar gari  ashe baki manta da wace ce kike tare da ita ba".

Zuby tace "kawa ta mu zauna na baki labarin abinda ya sa na shiga cikin tashin hankali nan".

Saida Lubancy ta je ta  bude karamin fridge din dake dakin ta dauko goran lemu sannan ta dawo ta zauna a bakin gado tace
"ina jinki".

"ina wannan gayen da nike baki labari Wanda na had'u dashi a Instagram kwanaki kin tuna shi?".

"Eh anyi haka na tuna to mai ya faru dashi ko shima an fad'a masa halin ki ne".
Lubancy ta fad'a haka tana duban kawar ta

"ko daya kawata nan take Zuby ta kwashe duk abinda ya faru ta fad'a ma Lubancy,

tsaki Lubancy taja kana tace "wallahi Zuby kina bani mamaki d'an karamin abu duk ki bi ki tada hankalin ki ba kin ce   yana soki ba?".

"Eh yana sona na gani a cikin 'kwayar idanun sa".

"kuma kince yarinyar suna kama".

"wallahi suna masifar kama abinda ya bani haushi" da yace" min 'yar mai gadin su ce baki ga yarinyar ba kama da larabawa take yi".

Lubancy tace "dadi na dake gajen hakuri, da kin bisa a yadda  yace idan ma da wata a 'kasa zamuji daka baya, kince kina son sa kuma auren sa zakiyi kin tafka kuskure da kika ce masa karya yake saboda shine gaba dake, amma ko nan gaba ki kiyaye kisan kalar maganar da zaki dunga gaya  masa, Zan san yadda zamu bullo wa lamarin, saboda nima yanzu tawa ce ta kawo ni tun jiya da muke chart kika fad'a min kin gama period naji kamar nayi tsun tsuwa nazo saboda nayi missing d'in ki ".

"Kawata kenan wallahi bakida hakuri". Zuby ta fad'a tana zuge zif d'in rigar ta,

ita ko Lubancy dama doguwar riga ce ta zumbulo sai undies da ta saka nan take ita ma ta cire doguwar rigar tayi cilli da ita ta kamo Zuby suka 'karasa cire ma juna kaya,

sosai Lubancy ta rikice saboda Zuby Allah ya yi mata baiwar komai bata da makusa a halittar  jikin ta shine ke rud'an maza da kuma matan da suke neman junan su

sakonni suka fara aika wa junan su sosai suke romance suna ihu. Babu inda basa tabawa a jikin junan su

Wa'iya zu billah lallai halin Zuby sai ita baza taso Sadeeq ya sani ba dan shi kamilar mace yake so ya aura,
ja musu 'kofar nayi ina takaicin rayuwar Zuby

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Ina cin danbun ina side yatsun hannu na Ummi na hango tana saukowa daga sama. Dinning din tazo ta zauna da alamar daga bacci ta tashi saboda yadda idanuwan ta sukayi, kallo na tayi tace "maiyar dambu sai kace kin samu wani abun dadin, ko naman kaza baki masa irin wannan santin, ni kuma wallahi na tsane sa dole nike ci nasan Daddy ne yasa Momy tayi dan shima yana son dambu".

Nace "yarinya da kinsan kalan dadin da nike ji alokacin da nike cin dambu da ko magana aka ce ki min bazaki ba saboda idan zan baki amsa a cikin santi zan baki, yanzu dai bari na gama sai ki sake maimaita abinda kika fad'a".

Ummi tace "tab sai na tsaya har sai kin gama kamar yarinyar ki bani da wannan lokacin bari naje ko Indomie na dafa dan yau ba zanci danbun ba".

"ke dai kika sani idan za a shekara ana jera yin dambu babu abinda zai dame ni".

"uhm". Ummi ta fad'a ta nufi hanyar kitchen

Umar ne tafe rike da hannun Jiddah ahankali suka karaso gurin, Umar yai sauri ya ja mata kujera tai saurin dakatar da shi da fad'in "Umar mai kake shirin yi haka to wallahi na daina had'a gurin zama da wannan 'yar kauyen muje falo idan ta gama sai nazo muci".

Kallon ta nayi na kwashe da dariya nace "da alamar har yanzu bakin ki bai mutu ba".

Umar na kalla nace "wai ka nuna mata madubi kuwa? na tabbatar da  taga yadda nayi mata da ko suna na taji an ambata gaban ta ne zai fad'i dan Allah idan bata ga ni ba maza je ka d'auko saboda ina son ta san ruwa ba sa'an kwando bane".

"Aunty Siddeeqah dan Allah ku daina wallahi banajin dadin hakan ko kadan". Umar ya fad'a kamar zai rushe da kuka

ganin haka yasa nace "to shikenan kanina ya wuce amma kaja mata kunne kasan ni duk Wanda yai min kan kara na itace nake masa".

Umar yace
"Aunty Jiddah muje".

A masifan ce Jiddah ta kwace hannun ta fuuu ta wuce falo ta zauna tana kananun magan-ganun da ita kadai tasan mai take cewa

🤙 _Hy guys please don't forget to comment vote and follow me on Wattpad join my group on Telegram please please please_ 🥰

NI DA YAYA SADEEQ

˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

End of Chapter 17Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next