Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
So sai Siddeeqah take dariya harda rike ciki, tana ayyana yadda zata gyara ma Jiddah zama dan wallahi ta daina daukar rainin hankali
Take Umar ya mara ma Jiddah baya yana mamakin kiyayyar da suka ma juna kamar ba 'yan uwan juna ba
A zaune ya sami Jiddahn a kan kujera sai cika take tana batsewa tana ganin sa ta daure fuska tace "mai kazo yi wuce ka bani guri munafuki ni zaka raina ma hankali a gaba na za ka dunga yiwa waccan yar kyauyen magana? Har da ce mata aunty saboda munafurci na cin ka". Ta karasa maganar tana nuno masa inda nike
shi dai Umar bai ce mata komai ba sai mamaki ma da ta kara bashi
Jin kamar ana hayaniya Momy ta fito da Alamar daga bacci ta tashi, a dai dai lokacin Ummi ta fito daga kitchen hannun ta dauke da plate din abin ci, kallon mu Momy ta shiga yi daya bayan daya, daga karshe ta sauke su akan Jiddah tayi mata kallo irin na gar gadi, ba tare da tace mana komai ba ta koma ciki abin ta
Ummi kuwa zama tai a dinning din tana fadin "wash Allah na".
Kallon ta nayi nace "kefa raguwa ce daga dafa Indomie sai kizo kina wash kamar wacce tayi abin a zo a gani?".
"Bazaki gane bane". Ummi ta fada tana kai lomar Indomie
Shi kuwa Sadeeq tun sanda suka shigo ya haura sama soboda yana bukatar ya huta, dan Zuby ba karamin bata mishi rai tayi ba sosai yake mamakin ta dan shi baya son rashin kunya musamman ma idan yasan ya girmi mutum, to yana so a girma ma shi, a gogan hannun sa ya cire tare da lalubar aljihun sa ya ciro wayar sa ya aje a kan madubi kana ya shiga cire kayan jikin sa, wannan ita ce dabi'ar Sadeeq a duk sanda zai shiga wanka sai ya fara cire kayan sa a bedroom sannan ya ke shiga bayi, to bayan ya shiga ya dauki kusan mintuna 43 a cikin bayin yana cuda jikin sa ya zuba wancan ya zuba wannan sai da yaji kam shin ya mishi yadda yake so, sannan ya fito daga cikin kwamin wankan ya zo gurin da tawul yake a rataye ya daura a kugun sa kana ya dauki karami ya shiga goge kansa daga haka ya fito.
* * * * * * *
A ban garan su Zuby kuwa bayan sun gama fasikan cin su suka shiga wanka nan ma sai da suka bata mintoci suna kissing din juna kamar wasu mata da miji Zuby ta manta da wani Hallita mai suna Sadeeq saboda Lubancy ba baya ba wajen romance ta iya solon makirci da Jan hankali kala-kala.
Bayan sun fito daga wankan ne suka shafa mayuka masu kam shi tare da fesa body sprea riga da wando Zuby ta dauko a cikin durowar ta kana ta duby Lubancy tace "sweety wani kalar kaya zan fiddo miki?".
"My love duk wanda kika dauko min zan sa". Lubancy ta fada cikin salo mai Jan hankali
To bayan sun gama shiryawa suka shiga fesa turaruka masu sanyin kamshi gami da daukar hankalin wanda duk a ka gibta ta kusa dashi.
Hijabi suka zum bula har kasa tare da saka safa a kafar su ke idan ki ka gansu zaki rantse mutanen arziki ne.
Falo suka fito inda suka tarar da Mama zaune tana kallon BBC World news, ta maida gabadaya hankalin ta da nutsuwar ta akai
Kamshin turaran tilon diyar ne ya dawo da ita ga barin kallon TV,
kallon su tayi cikin sakin fuska tace "kar dai har zaki tafi?".
Mama ta fada tana duban Lubancy wacce ke tsaye tana dan Murmushin tace "Eh Mama zan tafi dama sako na kawo mata".
Kallon Zuby Mama tayi ta ce "iya rigima ina zuwa kuma? ko rakiya zaki mata".
"Eh mama". Zuby ta bata amsa a takaice
To babu damuwa ki dawo Lafiya amma gaskiya yau kar ki dade kin San Abban ki yana gari, motsi kadan yace "kina ina?". Sai dai nayi masa karyan kan ki na miki ciwo kina bacci kin kuma ce kar a tashe ki har sai kin tashi, fek kiss Zuby ta mannawa Mama a goshi tana fadin "Allah ya bar min ke Mama na I love you". "Love you too". Mama ta fada tana dariya irin ta-su ta manya da yike ita ma irin gogag-gun iyayan nan ne, kuma ta san da duk wani abu da diyar ta-ta take aika wa asali ma ita ce ta sata akan hanyar
* * * * * * * *
To a bangaren Sadeeq kwance yake a kan makekyan gadon sa idon shi a rufe kamar mai bacci amma kuma ba bacci yake ba a duniyar tunani yake.
Wayar sa ce ta shiga ringing amma be da niyar dauka har kiran ya katse saida a ka sake kira a koro na biyu ya bude raunan-nun idanun shi ya lalabi wayar ganin sunan Farooq na yawo akan screen d'in wayar ya danna picking kana ya kara a kunne
daga can ban-garen Farooq yace "kai bana son iya shege tun dazun nike kiran ka baka dauka ba, ba yan kasan haka kawai ba zan dunga kiran ka ba".
"Ina jin ka to". Sadeeq ya fad'a yana cin magani
Farooq ya kwashe da dariya yace "dan iska wannan ji da kan naka ba shi zai sa a dunga maka abinda ka ke so ba, ni dai kasan ba tsoran ka zan ji ba ko?".
Cikin jin haushin kalaman Farooq Sadeeq yace "malam ya i she ka haka ka fadi abinda ya kawo ka ina jin ka".
Farooq yace "akan maganar makarantar matar ka ne na gama magana da wannan abokin nawa da yake koyar wa a makarantar ya sama mata admission yace maganar aji sai idan an kaita sun mata interview zasu gane ajin daya dace da ita, saboda haka daga yau zuwa kowace rana zaku iya kaita dan har register yai mata ".
Shiru Farooq yayi ko Sadeeq din zai ce wani abu amma sai yaji a kasin haka,
Bayan wasu yan daki ku Sadeeq yace "ka gama?".
Cikin takai cin abokin nasa Farooq yace "dan iska insha Allah wannan yarinyar da ka ke rainawa sai ta zame maka ciwan ido, yana gama fad'ar haka ya kashe wayar sa
Aje wayar sadeeq yayi gami da daga kafada alamar ko in kula ya tabe baki a can cikin zuciyar sa yana jin dadin zai rabu da ala ka kai
NI DA YAYA SADEEQ
˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙
More Hausa novels
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel
By Oum Yasmeen
Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Ciki Da Gaskiya Book 1 Complete Hausa Novel
By Ubeera
Search across the available chapters.