Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Cikin shagawaɓewa tace.
“But I have already found the woman, musulma Mai addini kamar yadda ka buƙata. Dan Allah Farooq ka karɓi abun nan da zuciya ɗaya please”
Kafaɗar sa ya ɗaga tare da ware hannayensa alamar shi kenan.
Hugging ɗinsa tayi tare da narke masa tana sakar masa sabbatu, shi kuma daman can in dai Hanifah zata biye sa to yafi ƙaunar wannan rayuwar soyayyar fiye da komai a duniya . Duk son sa da abinci haka suka lalace a wurin suna ta abu ɗaya.
***************
BAHIYYAH
Firah muka sha sosai muna ta tsara yadda zamuyi da likita kamar yadda ya faɗa mana cewa da zaran an samu kuɗin zai shige mana gaba a shirya yi mata aikin. Mama ma jefi jefi ta kan ɗan sako bakinta kaɗan. Gaba ɗaya da ka kalle mu kasan cewa cikin kashi saba'in kashi talatin na daga cikin damuwar mu ya tafi da ikon Allah.
Sai da aka gama sallar Isha mijin malama yazo ya gaida Mama, malama ta faɗa mishi abinda ake ciki ya nuna farin cikin sa yayi mana addu'a sannan suka fita zuwa gida.
A bakin get ɗin asibitin na tsaya nace.
“Malama dama akwai maganar da nike so in sanar miki.”
Tsayawa tayi shi Kuma uncle Idris yayi gaba wurin mashin ɗinsa ya tsaya jiran mu.
Kallon ta nayi tare da marairece murya na riƙe hannun ta nace.
"Malama akwai abinda na ɓoye ban faɗa muku ba. Matar tace ba a ƙasar nan zatayi renon cikin ba kuma dole in amince in tafi tare da ita, to na san idan na faɗa kai tsaye hankalin Mama na iya tashi ni kuma bana son abinda zai ɗaga mata hankali a halin yanzu”
Jinjina kai Malama tayi alamar abin babba ne tace.
"Dole kuma sai tare da ke Bahiyya? Anya zan yarda da wannan matar kuwa?”
Cikin magiya nace.
“Malama dan Allah kada ki ce a'a please, wallahi nayi imani ba zata cutar dani ba, gobe fa da kanta tace zata zo nan, kuma na faɗa miki babbar Aminiyar maman Khadijat ce idan har ba ta kirki ba ce maman Khadijat ba zata haɗani da ita ba. Malama wannan hanyar ita kaɗaice hanyar da zan iya ceto rayuwar mahaifiya, ba zan iya bari wannan damar ta wuce ni ba, domin idan Mama ta mutu wallahi ni kaina rayuwata tazo Ƙarshe, kawai abinda nike so da ke shi ne ki tayani da addu'a kuma ki kula min da Mama ta da Ƙanwata, shekara kamar kwana ce take cikin Ikon Allah zaki ga shekara ta zagayo, in sha Allah kuma zaku same ni mai kiyaye wa”
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace.
“Bahiyya duk don saboda mahaifiyar ki kika yarda da ɗaukar wannan kasadar, dole zan kirashi da kasada domin ba ki san ina zaki ba kuma baki san mi zaki tarar ba, amma koma minene ina miki fatan tsarin ubangiji a duk inda kike, tunda har saboda mahaifiyarki kika ɗauki wannan nauyin in sha Allah ubangiji zai saka miki da abinda baki yi tsammani ba domin uwa ta sha gaban komai da albarkar ta zaki yi nasara a rayuwar gwagwarmayar ki in sha Allah. Zan kira Hajiya Rasi'a zuwa gobe in sha Allah domin in ƙara tabbatarwa daga gareta”
Rungume ta nayi ina hawaye nace.
"Na gode sosai Malama, kema in sha Allahu ke da mijin ki, tsaya mana da kuka yi sai ubangiji ya saka muku ta inda baku zata ba, domin da ace ubangiji bai haɗamu da ku ba ban san wace irin rayuwa zamu faɗa ba.”
" Ba komai Bahiyya ki koma ciki, dare yayi sai da safe in sha Allah, go be ma ba zan fita school ba, nan zan zo in sha Allah sai muga yadda za'a yi”
Daga haka mukayi sallama suka wuce ni kuma na koma ciki...........
*OUM AMEER*
💝 *BAHIYYA*💝
*ADABI WRITERS ASSOCIATION*
*BY*
*AMINA IBRAHIM*
*(OUM-AMIR)*
*MI KI KE JIRA NE ER UWA DA HAR YANZU BAKI YI PAYMENT BOOK ƊIN BAHIYYA BA??? ZANEN ƘADDARAR SU NE ZAI SOMA DAGA LOKACINDA AKA DASA SPERM ƊIN FAROOQ DA ƘWAN HANIFAH A MAHAIFAR BAHIYYA WANDA AKE KIRA SURROGACY A KIMIYANCE.WAI MIYE DALILIN SURROGACY ƊIN NE? DALILIN RASHIN LAFIYA NE?? A'A!! DUNIYA CE KAWAI TAYIWA HANIFAH DAƊI TAKE GANIN ITA SAM BA ZATA IYA HAIHUWA BA DOMIN DAUKAR CIKI DA HAIHUWA DA RENO SUNA CANJA HALLITAR MACE. SHI KUMA FAROOQ HAIHUWA YA KE SO, TO FA!! SHINE TA YANKE WANNAN SHAWARAR SABODA TA NEMAWA MIJIN TA FARIN CIKI, YAYINDA BAHIYYAH TA FAƊA KOMAR HANIFAH IDO RUFE TANA NEMAN KUƊIN DA ZA'A YIWA MAHAIFIYARTA AIKI, TO WANE ALFANU HANIFAH ZATA CIMMAWA? SHIN HAƘAR TA KUWA ZATA CIMMA RUWA KO KUMA TAYI SHUKA NE A IDON MAKWARWA????? KU BIYO NI IN SHA ALLAH TAFIYAR BABU DANA SANI*
*BAHIYYA NOVEL ƊIN KUƊI NE KIBIYA 500 TA WANNAN ASUSUN 3132703269 FIRST BANK AMINA IBRAHIM SAI KI TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08068974831*
*FREE PAGE*
*BABI NA GOMA SHA ƊAYA*
BAHIYYA
Kwana nayi ina abu ɗaya wato tunani da zullumi, gaba ɗaya jin nike can ƙasan zuciyata na karaya domin tunda nike ban taɓa nisa da iyayena ba ko sau ɗaya sai yau da na amince da ƙudurin wannan matar, ba wai ina nadamar hakan ba ne a'a, nisantar ahlina da zanyi shine ya tsaya min a rai. Taya zan iya rayuwa babu Mama a tare dani har na tsawon shekara ɗaya? Wace irin rayuwa zan tarar a can? Wai ƙasar waje kamar yadda naji ta faɗa, Hmm!.
Abubuwan da suka yi ta cizon ƙahon zuciyata kenan gashi ina Allah Allah gari ya waye ni dai in ga an biya kuɗin aikin nan an yi mata a lokacin ne hankalinmu zai kwanta.
Kiran sallahr Farin ko a masarrafar sauraro na ya sauka, da sauri na miƙe na ɗoro alwala na zo bayan na kambala raka'atanul Fajr na zauna na yi ta addu'ar samun nasarar aikin Mama da kuma zaɓin mafi alkairi a cikin rayuwar da zanyi ta shekara ɗaya.
Da wuri na je gida na shiryo mana abin karyawa na ɗauko wa Nuhaira tufafi kamar yadda ta buƙata.
Ƙarfe tara a Office ɗin doctor Sam tayi min, cikin farin ciki na shiga shaida ma cewar na samo kuɗin aikin Mama, shima congratulations ya shiga furta min tare da faɗin in bari ya kira asibitin yaji yaya za'a yi.
Muna nam sai ga malama ta zo abinda take shaidamin shine tayi ta neman layin maman Khadijat baya shiga ga shi har 10:00am tayi amma Hajiya Hanifah shiru.
Bayan mun gama tattaunawa da likitan ɗakin da mama take kwance muka koma muka ci gaba da tattaunawar a can.
Firar mu ke amma gaba ɗaya yanzu hankali na ya dugunzuma ya koma kan Hajiya Hanifah, ƙirjina sai dukan uku-uku yake ganin ta kai har zuwa wannan lokacin bata zo ba, kar dai ace fasawa tayi? Wayyo Allah na....
Ban tantance cewa kuka nake ba sai da naji Malama na faɗin.
"Subhanallah! Bahiyya lafiya kuwa?”
“Matar nan fa har yanzu bata zo ba Malama, kada ta canja niyyarta gashi har sha biyu tayi.”
“Kwantar da hankalinki haba, in sha Allah tana tafe”
Daga haka ban sake cewa komai ba na yi shiru cikin raina ina faɗin Allah yasa haka.
Ba mufi minti ashirin da gama maganar ba sai gashi an aiko ɗan aike cewa ana nema na a Office ɗin doctor Sam.
Ko da naje zaune take a office ɗin suna magana da ita da turanci da alama maganar aikin Maman ce suke yi.
Na jima a tsaye kafin nan suka gama ta juyo ta kalle ni kai tsaye tace.
"Aikin ki ya kambala, na cika nawa alƙawarin saura naki”
Murmushin nasara na saki ina faɗin.
“Nagode na gode Allah ya saka da alkairi....” daga haka na fita da gudu naje na kira Malama da Nuhaira suka zo.
Kallon halittar ta Nuhaira ta tsaya yi tana mai ƙara tsinkewa da lamarin ta domin ba ƙaramar mace ta gani ba, tasha wasu riga da wando, rigar bakin guiwa ne sai wando plazo tayi ɗan ƙaramin rolling ɗin nan na manyan matan nan, ko mai hassadar ka idan ka kalli Hanifah sai ka sara mata, fatar luwai-luwai ga faranta mai ɗaukar hankali ga wanka komai na ta manyan mata. sai zubo mata addu'o'i take tamkar wata zararrariya bayan ta gama ne Malama ta kalle ta Itama tace.
“Mungode sosai Hajiya, Allah ya saka miki da mafificin alkairi...”
Sai yanzu tayi murmushi tace.
“Ba komai ai dani da Rasi duk ɗaya ne. Allah yasa a dace.”
Daga haka ta miƙe ta fice ni kuma na bi bayanta har bakin motar ta. Ba tare da ta kalle ni ba tace.
"Na gama nawa, idan kin shirya ki zo wurin wannan doctor ɗin naku zai sadaki da ni, bana so ki bar ni na tsaya jira da yawa”
“Ɗan risinawa nayi duk da cewa bata kallo na nace”
" In sha Allahu ba zan jima ba daga zaran an kambala zaki ji ni”
****************
NATIONAL HOSPITAL ABUJA,
CENTRAL BUSINESS
DISTRICT, ABUJA.
Wannan ita ce asibitin da aka shirya za'a yiwa Mama aiki nan da kwana huɗu mai zuwa.
Bayan an yi booking likitan yace sai nan da sati shida za'a aikin, but ganin condition ɗinta ya zama emergency doctor Sam ya shige mana gaba aka yi postponding ɗinsa zuwa kwana huɗu.
Kukan farin ciki na fashe da shi a lokacinda malama ta ke sanar min an gama biyan kuɗin aiki har da kuɗin magani, sannan akwai 500k daga maman Khadijat inji ita Hanifah ɗin. Sannan kuma tace bayan shi ko da ace an gama aikin idan akwai wata matsala za'a neman ta kai tsaye ta hanyar doctor sam, sannan kuma tace idan anyi nasarar aiki an bata sallama akwai million biyu da za'a bawa Mama daban ta ci gaba da kula da kanta da Nuhaira kafin na dawo, tunda likitan ya gaya mata cewa ni ce babbar 'ƴarta duk wani rabin nauyin ya rataya ne a wuyana yasa ta ƙara mana da wannan kuɗin na daban. Nan Malama ta ji ta saki jiki da ita tayi amanna da kirkin ta tare da yi mata addu'a.
More Hausa novels
Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.