Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Bayan an gama shirya komai kwana biyu tsakani muka tattaro kayanmu da Mama muka dawo nan asibitin. Ɗaki ne aka bamu mai zaman kansa wai shi amenity, komai akwai cikin ɗakin tamkar kana gida zaune.
Bayan Malama ta koma gida na zo na zauna kusa da Mama na kalle ta da murmushi a fuskata na saƙala hannuna cikin nata nace.
“Mama na! Ina sonki, Ina matuƙar sonki ina alfahari da ke Mama. Haƙiƙa duk mai haƙuri yana tare da Allah, ubangiji ya dubi maraicin mu ne yaga bamu da wata mafita shi ne ya turomana agaji ta hannun wannan baiwar tasa mai cike da albarka. Alhamdulillah! Allah shi ne abin godiya, Allah ya ji ƙan Baba da Rahma. Haƙiƙa kin kula dani kin bani tarbiyya da ke da Baba iya gwargwadon iyawarku na yi miki alƙawarin zan kare mutunci na a duk in da na shiga a faɗin duniya komai wuya komai tsanani.”
Murmushi ta sakar min itama tana mai gyaɗa kanta a hankali ta buɗe bakinta murya can ƙasan maƙoshi tace.
“Allah yayi muku albarka Bahiyya, yadda kuka ji ƙaina kuka tausayamin ina roƙon ubangiji ya baku rayuwa mai albarka ya baku mazaje na gari ko bayan bani a duniya”
Kallon ta na sake yi tare da jin nauyin kalmar ta ta ƙarshe a ƙirjina tamkar an ɗoramin falalen dutse nace.
“Mama kullum na tambaye ki sai kice zaki faɗamin Mama, dan Allah ki faɗamin mi yasa muka kasance mu huɗu kawai a duniyar mu? Ga shi mun rasa Baba duniyar mu ta sake canzawa zuwa mu uku kacal, shin mi yasa Mama ba zamu iya komawa ƙasar mu ba?”
Girgiza kanta tayi tare da haɗiye wani yawu mai ɗa ci a maƙogwaronta tace.
"Bahiyya ba ina ɓoye muku bane don wani abu, babu kalma ɗaya mai ɗaɗin saurare a cikin wannan mugun labari, domin idan har na sanar dake zaki yi ta damuwa ne a banza, zaki tsani dangin Mahaifin ki tsana ta har abada, sannan kuma zaki yarda cewa tsakanin 'ƴan uwa na jini babu amana. Ki bar wannan maganar Bahiyya”
Shiru tayi tare da juyamin baya alamar bata son ma zancen ganin haka yasa nima na kama baki na nayi shiru tare da tattara kaya na fita na kira Nuhaira nace ta dawo in da take.
***************
Tunda aka shiga da Mama na je na ɗoro alwala na fara jera nafila ina ta kai kuka na a wurin mai duka akan ya taimake mu yasa ayi lafiya a ƙare lafiya,yayinda Nuhaira da Malama suke girke a bakin ɗakin suna zaman jira.
Wannan likitan doctor Sam ba musulmi ba ne amma yayi mana abinda tsawon rayuwar mu ba zamu manta da shi ba, komai ake yana nan tare damu yana taimaka mana.
Ƙarfe biyu na rana aka fito da Mama daga ɗakin tiyata zuwa ɗakin hutu. Muna nam jugum jugum muna ta kallo aka yi mata duk abinda ya kamata ayi mata na bayan fitowa tiyata.
Mu kuma muna nan muna ta aikin kula da ita duk da cewa bata cikin hankalin ta yanzu.
Ku san Ƙarfe biyar na yamma ta farfaɗo wanda ni kai na da nake kusa da ita bana jin mi take cewa, muna cikin murnar kawai muka ga ta fara fisge numfashi ƙirjin ta na sama da ƙasa, jikin duk ya ɗau mazari, a gigice na nufi waje wurin nemo likita, yayin da Nuhaira ta shiga rera kuka mai ban tausayi........
*Oum Ameer*
💝 *BAHIYYA*💝
*ADABI WRITERS ASSOCIATION*
*BY*
*AMINA IBRAHIM*
*(OUM-AMIR)*
*BAHIYYA NOVEL ƊIN KUƊI NE KIBIYA 500 TA WANNAN ASUSUN 3132703269 FIRST BANK AMINA IBRAHIM SAI KI TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08068974831*
*FREE PAGE*
*BABI NA GOMA SHA BIYU*
......... A Irin yadda muka ga jikin Mama ya rikice bamuyi tunanin likita zai kai ga shigowa ba ruhinta bai bar gangar jikin ta ba. amma cikin ikon Allah sai gashi a hankali bayan likitan sun shigo sunyi iya yinsu ta dawo normal.
Kulawa mai kyau Mama ta samu tun daga doctors har zuwa nurses da mu kanmu, Alhamdulillah! Aiki ya yi nasara domin Mama ta samu lafiya sosai tamkar ba ita ce a mawuyacin hali a kwanakin baya ba. Saida muka kwashe sati biyar masu kyau sannan aka bamu sallama da kuma lokacin follow - up a kai a kai domin gujewa matsala bayan an ɗora ta akan tsarin maganin da ya dace. Kuma doctor Sam ya tabbatar mana cewa daga yanzu har abada ya dawo likitan ta duk lokacin da taji wani sauyin yanayi a jikin ta zata iya zuwa gare shi.
Gida mai daɗi. Tunda muka koma nayi sallar zuhr bacci ya ɗauke ni sai bayan asr sosai na farka da wani irin tsoro, domin mafarkin dai kamar ko yaushe babu daɗi, wanda har ya zame min jinin jiki wanda a yanxu sai dai inyi addu'ar da manzon Allah (S. A. W) ya koyar da mu, in ci gaba da abubuwan gaba na.
Bayan kwana biyu.
Zaune muke mu uku muna cin abinci a faranti ɗaya, ni, mama, Nuhaira. Mama ta kalle ni tace
“Bahiyya Malam Maharazu shiru, rashin samun sa a waya ya dame ni”
Cikin alhini nace.
“Wallahi kuwa mama. Abin da mamaki, ki duba duk tsawon lokacin da kika ɗauka a kwance har aka miki aikin nan ace har yau babu labarinsa abun akwai alamar tambaya, ni jiki na yana faɗamin ba lafiya ba”
Nuhaira ce tace.
“Wai Mama da ke da Baba kunce Baba Maharazu ɗan uwanmu, to mi yasa shi yake iya zuwa Nijar ɗin mu ace bamu iyawa?”
Girgiza kai mama tayi tace.
“Aminin babanku ne haƙƙun, tun suna yara suke abota har kasuwanci ya kawo su nan tare suka fara zuwa Nigeria, kuma tare suka kasance har mutuwa ta ɗauki babanku. Abokan taka ce ta haɗa su ba jini ba, saboda haka ba inda ƙaddarar Mahaifin ku ta shafe shi. Tun kafin ya auro ni yake xuwa nan, bayan mun aure ya dawo dani lokaci zuwa lokaci munkaje gida mu dawo, a lokacinda na haifi Ishaq yayanku kenan, Malamam yaga cewa ga ɗawainiya ta ƙaru ya kamata ace ya mallaki gidan kansa ya daina haya wanda ni kaina naga dacewar hakan domin ga sayen abinci ga kuɗin haya ga lalurar yaro ta ƙaru,daga haka sai muka yanke shawara cewa idan na tafi kai musu jariri, zai sayar da gonar guda biyu da ƙannen sa ke nomawa sannan a bashi nashi gadon Mahaifin su da ya bari. Tunda muka je kowa yake murnar zuwan mu kamar ko yaushe amma tunda yayi wa su Amadu zancen gona da kuɗin sa shikenan zance ya canza. Tun yana can ya so a siyar suka dage da lallai ya kamata ya koma wurin kasuwar sa su kuma idan suka sayar daga baya sai su haɗa komai su je da kansu su kai masa, tunda dai abin dole yana da jan lokaci, ni tunda naji sun fara mishi wannan hanya hanyar nace mishi ban yarda da su ba, amma abin ka da ɗan uwa yace min ai ba matsala, nayi sallama da iyayena da mahaifiyarsa kamar ko yaushe muka shirya muka dawo gida. Bayan dawowar mu saida akayi rabin shekara babu su Amadu babu dalilin su, tun babanku baya magana har ya fara tuntuɓa ta da zancen kai tsaye nace mishi ai saida nicce kada ka yarda dasu tun farko kace ba haka ba, ƙarshe muna nan Abu wasa wasa har aka shekare, daga nan ya yanke shawarar sake komawa yaji ina zance ya kwana, to tunda Malam ya sa ranar tafiyar nan ya kwanta wani irin mummunan ciwo wanda idan mutum ya kallesa ba zai sa ran zai ƙara kwana ba, mukayi ta yawon asibiti duk a banza, watarana sai nace mishi Malam ko dai zaka je Nijar ɗin ne daga can ka nemo magani ko Allah zai sa a dace. Sai ya girgiza kansa yace min shi yanzu ya bar zancen Nijar ɗin nan sai dai wani lokaci kuma, in faɗa muku cikin ikon Allah tunda yace ya janye tafiyar sa muka nemi ciwo muka rasa, abu kamar wasa. Muna nan kuma aka ɗauki lokaci ya sake saka ranar tafiya sai ga ciwo ya dawo kamar ba zai yi rai ba, to daga nan sai muka fara tsora ta, da kaina nace malam ka janye tafiyar nan har wani lokaci yace min ai ya bar zancen kuma shi ya ma cire rai da wannan tafiya, shima tun daga nan ciwo ya warke, haka haka tun bamu gasgata ba har muka yarda cewa akwai wani abu a ƙasa...”
Cikin tsananin firgice wa da ruɗewa nace.
“Mama karki ce min don Baba ya nemi haƙƙinsa ne Su Baba Amadu suka aikata mishi haka, kina nufin asiri suka mai kenan??”
Kuka take mai tsuma rai cikin raunatattar murya.
“Bahiyya wannan abun ba Babanku kaɗai suka yiwa ba, har da ni, domin shine silar da yasa har yau ban sake komawa tushe na ba, kuma ko yanzu ban isa nace zan tafi ba ni kaina, kuma abin da ya bamu tsoro, firgici da ban al'ajabi muka kasa warware shi har Mahaifinku ya bar duniya shine 'ƴan uwana da na Mahaifinku har yau babu wanda ya sake neman ina muke yau shekara ashirin da shida kenan rabon mu da gida, a wurin Malam maharazu kawai muke samun labarin su, a ta hannunsa ne Malam ya samu labarin rasuwar mahaifiyarsa, Nima a wurin shi na samu labarin rasuwar iyayena, da sauran Labaran dangi na daɗi ko akasinsa....”
Jikina sai ɓari yake ina wani irin kuka mai ban tausayi, cikin ruɗewa nace.
“Yanzu Mama akan abun duniya, suka rabaku da dangin ku?? Saboda abun duniya Mama! InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Kai duniya ina zaki damu,'ƴan uwanka uwa ɗaya uba ɗaya sune zasu aikata maka wannan mummunan aika aikar saboda wani ban zan abun duniya wanda dole watarana sai an barsa”
In banda kuka babu abinda Mama da Nuhaira suke, lallai tabbatas zancen Mama haka yake banga wani abun burgewa ba a cikin wannan labarin wanda har na koma ga Allah ba zan manta sa ba. Dafa kafaɗarta nayi nace a hankali nace.
More Hausa novels
Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Search across the available chapters.