Soyayyanovels
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel
By Soyayyanovels
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel

Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel

Author: Soyayyanovels
Chapter 13 of 90
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 1,700 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 Reading now Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 1,700 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,700 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 1,700 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,700 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 1,700 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 1,700 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,700 words Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,700 words Chapter 62 1,700 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 823 words Chapter 83 2 words Chapter 84 1,700 words Chapter 85 1,700 words Chapter 86 1,700 words Chapter 87 1,700 words Chapter 88 1,700 words Chapter 89 1,700 words Chapter 90 478 words

sa ya sauya cikin k'ank'anin lokaci "Wacece wannan yarinyar?" ya fad'a sanda wani malami a cikin makarantar ya k'araso yana gaeda shi, amma shi sam be lura ba hankalin sa na kan Ayrah ne, da mamaki malamin ya kalli inda ya nuna da hannun sa yace yana kallan Alhajin "Wa kenan yalla6ae?" "Wata farar yarinya data shiga Office d'in nan yanzu ita da wata.." "Ohk wae Ayrah Ibraheem Khaleel?" "Ayrah!" ya ambata a fili, "kamar yadda sunan ke da dad'i haka mamallakiyar sunan ke da kyau" ya ayyana a ransa kafin a fili yace "K'warae wacece ita?" "D'aliba ce a makarantar nan.." malamin ya fad'a yana mamakin jin tambayoyin dake fitowa daga bakin Alhajin "K'arin bayani.." Alhajin ya fad'a yana kafe Malamin nan da jajayen idanun sa da suka kasance na halitta, seda yaja numfashi kad'an sannan ya furta "Hadda ita dae a cikin wad'anda suka ci qualifying, so yanzu akwae wani important issue ne yasa principal kiran su" ganin dae baze samu wani cikkaken information daga wajen sa ba ya sanya shi fad'in "Ohk ya yanayin k'wakwalwar ta yake?" seda ya d'an yi shiru sannan yace yana murmushi "Gifted, a cikin ajin su ita ke d'aukar first position koda yaushe" "Thank u" Alhajin ya fad'a yana mik'awa Malamin hannu suka gaesa sannan yayi gaba, drivern Alhajin ne ya matso kusa dashi kansa a k'asa yace "Yalla6ae kana buk'atar wani abu ne?" "A'ah.." ya fad'a yana kallan wanda ya fito daga cikin motar yana maeda waya cikin aljihu, da alama waya ya gama yi a cikin motar, shima kamar Alhajin zasu yi shekaru kusan d'aya se dae banbancin kamanni, dae_dae lokacin da Ayrah ke fitowa daga cikin Office d'in se dae wannan karon ita kad'ae ce, Alhajin ya kalli abokin sa Alhaji Baba yace "Wannan yarinyar ta min" bin Ayrah Alhaji Baba yayi da kallo kana ya dawo da duban sa kan Alhaji yace "Wannan abar?" jinjina kae yayi yana cigaba da binta da kallo harta 6acewa ganin sa "Wannan ae se dae ka raene ta yalla6ae.." Alhaji Baba ya fad'a yana kallan sa "Babu damuwa zan raene tan, daga yanzu zuwa sanda zata gama Secondary School, zan kashe ko nawa ne a kanta nasan ka gane abinda nake nufi.." murmushi Alhaji Baba yayi kana yace "Kana tunanin wannan yarinyar zata aure ka?" "Meze hana? Ina da wani aebun da 'ya mace zata guje ni ne? Musamman ma irin wannan da take zuwa makarantar talakawa irin wannan?" Alhajin ya fad'a yana kallan Alhaji Baba "Iyayen ta fa?" "Me kud'i suke yi? Ina tunanin ka manta nace zan kashe ko nawa ne a kanta koh?" Alhaji ya katse shi da fad'in hakan "A nemo min wace ce ita, su waye iyayen ta, menene burin su na rayuwa, dukka zan cika musu shi komae girman sa.." ya fad'a yana kallan drivern sa.... *_Doctor RK is coming...._* Mhiz Innocent..... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* *TITAN'S OF TALENT* Page 011_012 ___"Sir mun binciko maka wacece ita" cewar wani d'an matashi daya shigo cikin wani hamshak'in parlour daya gaji da had'uwa, murmushi Alhajin yayi yana kallan sa sannan yace "Good job Muttala, wacece ita? Menene burin nasu? Yaya iyayen ta suke?" gyara zama matashin saurayin da aka kira da Muttala yayi kana yace "Kamar yadda muka tsammata talakawa ne futuk yalla6ae, kuma idan iyayen nata nada buri toh be wuce na d'iyar tasu tayi karatu ba" "Sure? Kuma kana nufin ka bincika da kyau?" Alhajin ya fad'a "Sosae kuwa ranka ya dad'e, idan da k'ari dae toh se dae ko a bawa baban nata jari, dan wallahi ranka ya dad'e da gani yana shan kebula" ya fad'a yana wani maraeraece fuska kamar wanda yaga wani abun mara dad'i, se kuma ya sake gyara zama yace "Amma wani hanzari ba gudu ba yalla6ae, ina ga da zan iya bada shawara da nace kar ka fara tarar abin daka haka, a fara da ita yarinyar saboda gudun matsala" jinjina kae Alhajin yayi cike da gamsuwa da maganar Muttalan yace "Hakane, yanzu abinda nake so, ayi duk abinda ya dace akan karatun yarinyar, kome take buk'ata zan samar mata shi, kada ayi sanya akan wannan al'amari kuma bana so a samu matsala" "Babu damuwa Alhaji..". Muttala na fita daga d'akin kae tsaye makarantar su Ayrah ya wuce direct ya tafi wajen Principal ya sanar dashi sak'on Alhaji, sosae shi kansa Principal yayi mamakin jin wannan lamari amma tunda abin na manya ne seya dena ganin laefin sa, ya maeda hankali wajen sanar dasu abinda Ayrahn ke buk'ata daya danganci makaranta.. Da sallama ya shigo cikin gidan, duka suka amsa masa sanda yake k'arasowa cikin tsakar gidan da suke zaune, Ayrah dake kwance kan cinyar Umma tana kalmashe mata dogon gashin kan ta me santsi, Umman ta mik'e ta k'arasa wajen Abba kafin ya gama shigowa, ta masa sannu da zuwa sannan suka k'araso suka zauna a tsakar gidan "Matso ina zaune na k'arasa miki kalbar.." Umma ta fad'a tana kallan Ayrah data d'auki mayafi ta yafa a kanta, seta kwa6e bakin ta sannan tace kamar za tayi kuka "Don Allah Umma a bari haka nan" harara Umma ta jefa mata, Abba dake kallan su yayi murmushi sannan yace "A'ah abar Auta ta huta haka nan, kinga ma nazo miki da wani albishir.." ya fad'a yana sanya hannun sa cikin aljihu ya d'auko kud'i sannan ya mik'a mata yace "Ga kud'in nan sun samu" ya fad'a yana murmushi, hannu biyu Ayrah ta saka ta kar6a sannan tana murmushi ta kalli Umma kana ta maeda duban ta kan Abba tace "Abba Albishirin ka.." Seya kalle su su duka kafin yace "Albishir kuma? Ikon Allah... Toh goro.." yayi maganar duka a lokaci d'aya, Ayrahn ta cigaba da fad'in "Abba PC da kansa yasa aka kira ni ya fad'a min wae an biya min kud'in ma saboda k'ok'ari na" ta k'arasa fad'a da k'ayataccen murmushi akan fuskar ta, shiru na wasu en sakanni kafin Abba yace "Ikon Allah, toh Masha Allah Auta, Allah ya k'ara miki k'ok'ari Uhmm?" "Ameen Abba" ta fad'a tana mik'a masa kud'in hannun ta, seya sanya hannu ya maeda kud'in cikin hannun ta sannan yace "Ki rik'e su a wajen ki bana so na kashe, in case koda wata matsalar zata taso, duk da bama fata ma" seta mik'awa Umma kud'in tace tana Kallan Abba "Allah ya k'ara arzik'i Abba.." ..... A cikin en tsukun su Ayrah suka zana NECO, sun shafe satittika suna gabatarwa, sosae Ayrah ta dage wajen yin karatu ko dan ta cika burin iyayen nata na son tayi karatu, a kwanakin sau da dama takan hana kanta bacci dan dae tayi karatun, har wani lokacin se Umma ta saka ta tayi bacci sannan take hak'ura da karatun tayi baccin.. .. Tun d'azu bacci ke ta barazanar d'aukar ta amma take ta basarwa dan jira take Abba ya dawo saboda tun d'azu ya fita a dalilin rasuwa da akayi a cikin layin nasu, bata k'ara minti 5 a zaune ba kuwa ta jiyo sallamar sa daga tsakar gida, seta tashi zaune tana janyo d'an kwalin ta daya sa6ule daga kanta ta yafa shi ta zubo dashi gaba sannan ta fito tsakar gidan "Abba sannu da zuwa.." ta fad'a bayan ta nemi waje ta zauna akan tabarmar dake shimfid'e a tsakar gida "Yawwah Ayrah.." Abba ya fad'a yana kallan ta, seta cigaba da zama har zuwa sanda Umma ta fito daga kitchen d'auke da plate a hannun ta wanda ta yiwa Abba kwad'on salad a cikin sa "Sannu" ya fad'a yana kallan ta da murmushi kan fuskar sa, Ayrah tace "Abba.." yace "Na'am" ya fad'a yana kallan ta yadda take lumshe manyan fararen idanun ta da alama bacci take ji "Abba dama zuwa nayi na fad'a maka.." seya cigaba da kallan ta sannan yace jin tayi shiru "Ina jin ki" "Wae gobe idan Allah ya kaemu ance muje da wani d'an gidan mu za'a min registration na Jamb" sosae Abban ya cigaba da kallan Ayrah, I zuwa yanzu haka kawae yaji rashin yadda ya d'arsu a ransa, dan haka dole yayi wani abun "Shima cewa suka yi zasu biya miki?" seta jinjina kae kawae "K'arfe nawa?" "Wae kafin k'arfe 2 dae.." seya jinjina kae shima kafin yace yana janyo plate d'in gaban sa "Toh shikenan, Allah ya kaemu gobe inaso naje wajen principal d'in ku" "Toh Abba seda safe.." ta fad'a tana mik'ewa, Umma ta bita da kallo sanda take shigewa d'akin ta bayan ta mata seda safe, seta dawo da kanta wajen Abba tace "Amma gaskiya makarantar nan idan hakane suna da kirki, kuma hakan ba k'aramin k'arawa d'alibae k'warin gwuiwa zeyi ba" "Sosae kuwa" Abba ya fad'a a ransa dae yana tunani ne. Washe_gari Abba tare suka fita da Ayrah zuwa makarantar tasu, sanda suka shigo cikin makarantar da k'afar su suke takawa zuwa ciki, jefi jefi Abba kan d'an yi mata tambaya ita kuma ta amsa masa, har zuwa sanda suka k'arasa inda office d'in principal yake, a dae_dae lokacin da Alhaji ke fitowa daga cikin office d'in principal d'in nasu yayi dae_dae da lokacin da wayar Abba ta fara ringing, seya zaro ta daga cikin aljihu yana barin wajen zuwa baya dan amsa wayar saboda hayaniya, yana juyawar shi kuma Alhajin ya ida fitowa, a take idanun sa suka yi tozali da kyakykyawar fuskar ta sanda take tsaye a wajen tana jiran Abba ya dawo su shiga Office d'in tare, seya bita da wani mayattacen kallo da idanun nasa yana jin yadda zuciyar sa ke bugawa saboda k'aunar yarinyar "Yalla6ae.." wani dake gefen sa ya fad'a, se ya d'an yi firgigit ya juya yana kallan mutumin sannan ya rufe idanun sa ya bud'e kana ya saki murmushi yace a hankali "Idan na ganta wallahi ina loosing control d'ina ne.." yayi maganar sanda suke barin wajen zuwa inda motocin su ke ajjiye, suna wucewar Abba kuma ya ida wayar sa ya k'araso yana kallan Ayrah yace "Muje..".... Da sallama suka shiga Office d'in, principal dake zaune ya kalle su sannan yayi murmushi ganin Abba fad'i yake "A'ah sannun ku da zuwa" ya fad'a kamar wanda yaga wani hamshak'in mutumin, shi kansa Abba seda abin ya d'an so bashi mamaki amma ya fuske ya nemi waje ya zauna yayin da Ayrah ta

End of Chapter 13Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next