Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel
By Soyayyanovels
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel

Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel

Author: Soyayyanovels
Chapter 73 of 90
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 1,700 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 1,700 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,700 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 1,700 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,700 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 1,700 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 1,700 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,700 words Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,700 words Chapter 62 1,700 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 Reading now Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 823 words Chapter 83 2 words Chapter 84 1,700 words Chapter 85 1,700 words Chapter 86 1,700 words Chapter 87 1,700 words Chapter 88 1,700 words Chapter 89 1,700 words Chapter 90 478 words

babu wata mafita se kawae ta mik'e a hankali cike da mutuwar jiki ta fice daga d'akin zuwa tsakar gida cike da fatan kada ta samu kowa, ae kuwa addu'ar ta ta ta kar6u dan kuwa babu kowa d'in hakan ne ya sanya ta k'arasawa ta shige toilet d'in har lokacin idanun ta cike da k'walla. Ta d'auki wajen minti 30 a toilet d'in sannan ta fito aekuwa se ta ji yanzun tafi jin dad'in jikin ta fiye da ko yaushe. Ko da ta fito ma bata samu kowa a tsakar gidan ba hakan ne yasa cikin sauri ta shige d'akin ta, doguwar riga kawae ta zura ta haye kan gado ta duk'unk'une cikin bargo kamar me jin sanyi. Zuwa can se ga Umma ta shigo cikin d'akin da sallama, ta kalli kan gadon, ganin da tayi alamar Ayrahn tayi bacci ne ya sanya ta fad'in "Ashe har tayi bacci" Sarae taji abin da Umman ta fad'a amma ta sake lafewa kan gadon dan bata kuma san da wane ido zata kalli Umman ba. .. Washe_gari Abbu, Rk da Muneerah suka sauka a Zaria, kae tsaye gidan su Muneerahn suka wuce, suka gaesa da Mummy da Daddy, ba wani dad'ewa suka yi anan d'in ba suka bar Muneerah suka wuce gidan da suka saba sauka idan suka zo dukan su. .. Washe_gari da ya gama shiryawa cikin k'ananan kaya wad'anda suka matuk'ar yi masa kyau, jikin sa babu abin da yake yi se tashin k'amshin turaren sa me dad'in shak'a, se ya fito parlourn gidan, anan ya samu Abbu da tulin takaddu a gaban sa yana dubawa, ya k'arasa ya nemi waje ya zauna suka gaesa da Abbu, yana shirin jan takardun Abbu yace "A'ah ka je kun gaesa da Daddyn Muneerah kuwa?" girgiza kae yayi kana yace "Abbu ae na ga mun shiga jiya" murmushi Abbu yayi sannan yace "A'ah fa Raj, yanzun fa sirikan ka ne, ko babu komae hakan girmamawa ce a gare su, musamman kuma da ya kasance ba kae kad'ae kazo ba" baya son zancen yayi tsayi hakan ne ya sanya shi fad'in "Toh" daga haka ya mik'e walking majestically ya fice daga d'akin. .. A parlour ya tadda Daddy da Mummy, ya k'arasa ya nemi waje ya zauna kana yace, "Barka da safiya Daddy" "Barkan ka dae likita, ka kwana lafiya?" ya jinjina kae yana fad'in "Lafiya k'alau Alhamdulillah" "Toh Madallah" daga nan kuma se suka gaesa da Mummy, itama ta amsa masa kamar yadda Daddyn ya amsa masa. Mik'ewa yayi bayan sun gama gaesawar yace a nutse "Bari na wuce Daddy, dama nace bari na zo mu gaesa ne" "A'ah tafiya kamar yaya kenan Raj? Ka bari mana ka karya" Mummy ta fad'a tana kallan sa duk da yadda har yanzu haushin sa be sake ta ba tun bayan zuwan Muneerah gida, kawae dae tana yin komae ne saboda a gaban Daddy ne. D'an murmushi yayi kana yace bayan ya shafi sumar kan sa "A'ah Mummy a k'oshe nake, Na gode" yayi maganar yana soma tafiya. Da sauri Daddy yace "A'ah kae kana ji na? Dawo ka zauna ka ci abincin, ko yaya ne ka ta6a yafi baka ci ba" ba dan ya so ba ya koma ya zauna kan kujera. Mummy ta mik'e tana fad'in "Toh ae ka ga gwara ya zauna d'in" tayi maganar ba dan tana buk'atar jin amsa daga bakin wani ba, hakan ne yasa tayi hanyar kitchen. Mik'ewa Daddy yayi yana fad'in "Bari na fita, zuwa anjima zan neme ka" "Toh" shine abin da Rk ya fad'a yayin da Daddy ya fice daga d'akin. D'aukar wayar sa yayi ya soma dannawa, dan zaman kwata_kwata be masa dad'i ba kawae dae ya zauna ne saboda kada su ji babu dad'i, a karo na barkatae ya sake kiran layin Ayrah amma har yanzun bata d'aga ba, "Shett!" ya fad'a akan la66an sa yana d'an lumshe idanun sa. Wajen mintina 5 se ga Muneerah ta taho sanye cikin doguwar riga hannun ta d'auke da k'aton tire da abubuwa a kan sa, se da ta k'araso sannan ta ajje akan carpet d'in d'akin, kana ta kalle shi tana fari da idanun ta cike kuma da jin dad'in ganin sa "Baby ga abinci nan, ka sauko mu ci" se a lokacin ya san da zuwan ta saboda yadda ta taho kan ta tsaye babu ko sallama, se ya gyara zaman sa yana kallan ta, ya d'auka hakan ze sa ta gyara ko tayi sallamar ko kuma ta gaeshe shi se dae ya ji ba tace komae ba hakan ne ya sanya shi fad'in "Kin tashi lafiya?" Farr tayi da idanun ta tana jin dad'in tambayar ta sa kana tace "Lafiya k'alau na tashi, da kuma k'arin k'aunar ka Baby" "Madallah" ya fad'a yana k'ok'arin wanzar da annuri akan fuskar sa kada ya zama miji mara adalci a tsakanin matan sa, kafin kuma ta sake cewa komae ya ajje wayar sa gefen sa kana ya sauko daga kan kujerar zuwa k'asa. Tun kafin ya k'arasa zama Mummy ta sakko daga stairs da d'an sauri ta kalli Rk tace "Daddyn Muneerah be kira ka ba?" girgiza kae yayi kamin yace "A'ah.." "Ohk be san meyasa kiran yak'i shiga ba, se ta waya ta ya kira, yace yana jiran ka a Parking space ka d'an yi sauri" "Tohm" ya amsa da hakan yana mik'ewa a nutse ya fice daga d'akin. ... A d'aya 6angaren kuwa shigowar ta d'aki kenan daga kitchen inda ta d'ora tea ta dawo, a hankali ta k'arasa ta nemi kan gadon ta ta zauna, d'ora kan ta tayi akan pillow tana lumshe idanun ta, gaba d'aya a en kwanakin nan bata samun sukuni idan bata zauna tayi tunanin sa ba, gaba d'aya tunanin sa ya uzzura mata, komae take tunanin sa take yi. Wayar ta da koda yaushe bata bi ta kan ta ta d'auka ta soma dubawa, tama manta da rayuwar ta hakan ne yasa ko tunanin za'a kira ta ma bata yi ba, se dae ga mamakin ta se taga tulin missed calls daga number sa, cike da zumud'i ta dannawa layin na sa kira fuskar ta d'auke da mad'aukakin murmushi, tana fatan ya d'aga ta ji muryar sa ta kuma ji yadda zaman sa ke gudana a Zarian. .. Ringing d'in da ta ji yana fita daga wayar sa ne ya sanya ta sake kallan wayar a karo na barkatae, ba tun yanzu ba hannun ta ke yawan yi mata k'aek'ayi akan wayar sa, se dae yau d'in abin da ta gani na yawo akan screen d'in wayar ya sanya ruwan jikin ta ya tsotse, man kan ta ya tsiyaye, haushi da takaeci suka nemi kada ta. Ganin sunan na cigaba da yawo akan wayar ne ya sanya ta saurin jan wayar a fusace ta d'aga tana karawa a kunne. Ajiyar zuciya Ayrah ta sauke dan ita a tunanin ta shine ya d'aga wayar, se dae jin shirun da tayi ya sanya ta soma kokwanto, yayin da ta 6angaren Muneerah tayi shiru ne ba dan wani abun ba se dan kada jin muryar ta ya saka wadda ta kira wayar tak'i cewa komae, ba tare da fahimtar komae ba Ayrah tace, "Assalamu Alaek" ta fad'a cikin siririya kuma daddad'ar muryar ta idanun ta a lumshe tana jin yanda zuciyar ta ke ta azalzala da son jin muryar sa. Cike da bala'i da masifar da ke cin Muneerah gami da zallar 6acin rae ta soma fad'in, "Toh Mayya er talakawa, wato duk da mun bar ki anan dan mu taho nan mu shak'ata amma baki k'yale mu ba d'an naci irin naku na talakawa koh? Yanzu kam kar ki zata ban san ko ke wacece ba kike nuna min kamar ke wata ce ada, bayan ke d'in ba kowa bace, idan kuma kina tak'ama ke wata ce fad'a min wanene uban ki a cikin garin nan?" Shiru Ayrah tayi bayan ta bud'e idanun ta da sauri, tana cigaba da saurarar maganar Muneerahn cike da mamakin yadda akayi ta d'aga wayar Rk d'in, zame wayar tayi daga kunnen ta ta kalli numbers d'in dake jere ta sake karantawa, tabbas wannan d'in number sa ce, se kawae ta cigaba da kallan number kamar me k'irga yawan su ko kuma me son gane adadin sakannin da ke tafiya a cikin wayar. Ita sam ba maganganu mara sa dad'i da Muneerahn ke fad'a ne suka ta6a ta ba, yadda ta ji ta amsa wayar sa bayan yana wani garin daban, ya kuma shaeda mata ba shi da Muneerahn zasu je ba, se dae kuma ga dukkan alamu sun nuna tare da Muneerahn suka tafi, yanzu haka suna tare tunda ga shi shi be samu damar d'aukar wayar ta ta ba se Muneerah, ita kuma ga ta tana zaune ko oho kenan? "me hakan ke nufi?" Ta tambayi kan ta wayar na sa6ulewa daga hannun ta ko ina na jikin ta na rawa. "Shin kin san ta yadda aka samu dukiyar da kike tunk'aho da ita? Idan nace miki duk wani arzik'i da kike tak'ama da shi kun same shi ne dalilin mahaefin Ayrah ya zaki ji?" Muneerah ta tsinto muryar Rk yana magana muryar sa a matuk'ar cunkushe, kafin ya saka hannu ya kar6e wayar dake kunnen ta yana cigaba da bin ta da kallan da na kasa fahimtar wane iri ne. A razane Muneerah ta d'aga idanun ta ta kalle shi dan bata ta6a tsammanin ze shigo yanzun ba.. Mhiz Innocent... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 054 ___Cigaba da kallan sa Muneerah tayi cike da mamakin abin da ke fitowa daga cikin bakin sa, se dae ta gaza furta komae. A yanda ta ga ran sa ke a 6ace bata yi tunanin ze sake bud'e baki yayi magana ba se dae ga mamakin ta se ya sake fad'in maganar da ta ida d'aure ta da jijiyoyin jikin ta. "Kada ki sake kuskuren ta6a min waya bare a kae ga kin d'aga ta. Har kuma wae kina da zarrar yiwa wata gori, da kin san idan da mahaefin ta ya so kae ku k'ara se kin yi nadama da baki bari bakin ki ya furta irin wad'annan kalmomin ba. And last warning..." se ya d'an numfasa kamin ya d'ora da "Ba'a

End of Chapter 73Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next