Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel
By Soyayyanovels
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel

Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel

Author: Soyayyanovels
Chapter 18 of 90
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 1,700 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 Reading now Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 1,700 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,700 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 1,700 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,700 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 1,700 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 1,700 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,700 words Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,700 words Chapter 62 1,700 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 823 words Chapter 83 2 words Chapter 84 1,700 words Chapter 85 1,700 words Chapter 86 1,700 words Chapter 87 1,700 words Chapter 88 1,700 words Chapter 89 1,700 words Chapter 90 478 words

bata iya jure kallan cikin k'wayar idanun sa, sosae taji dad'in yadda ya kalle tan, kafin ta dawo daga wannan kuma taji yace "Yawwah barka.." seta sake yin murmushi tana janyo plate ta fara serving nasa, Mummy da fitowar ta kenan daga d'aki ta kalli Muneerat dake zuba masa abinci cikin plate da gasken gaske, seta girgiza kae a ranta tana raya "Lallae soyayya me chanja mutum" dan kuwa tasan halin k'wuiwa irin na d'iyar ta ta, bata aekin komae cikin gida, koda abinci ne kuwa se dae a kawo mata idan an kawo kuma a zuba mata, ina ganin da da dama ma cewa zata yi a bata a baki. Plate d'in ta tura gaban sa sanda ta gama zuba komae a muhallin sa sannan ta koma kan kujerar tana fad'in "Bismilllah Yaya na" seya ajje wayar sa a gefen sa, sannan yaja plate d'in a hankali yace "Thank u" wani irin farr tayi da idanu tana jin dad'i mara misaltuwa, ko ba komae tasan tayi abin kirki tunda gashi wanda tayi dan shi d'in har godiya ya mata, zata so ace kuma wannan kwalliyar ma ya kalla yace tayi kyau da tafi kowa farin ciki, se dae tasan kafin ma ya kalle tan abu ne me wuya ballantana yace tayi kyau, wayar sa daya ajje tabi da kallo sanda ta kawo wani haske, tana jin kamar ta janyo wayar ta duba wani abu amma se dae ba zata iya ba musamman daya kasance idanun sa na wajen, se kawae ta cigaba da kallan had'ad'd'iyar wallpaper wayar tasa dake d'auke da tambarin "A" wanda ita har yanzu tayi tunanin ta fad'ad'a k'wak'walwar ta amma ta gaza gane abinda yake nufi da hakan "Uhmm Yaya na ya d'alibae?" tayi k'arfin halin fad'in hakan dan katse shirun daya wanzu a wajen na wasu mintuna dan tasan ko da zata shekara ba tace komae ba, shi shirun baze dame shi ba balle yace wani abun, d'an ta6e baki yayi gami da yamutsa fuska ta d'auka ma ba zece komae ba se kuma taji yace "Alhamdulillah, baza kiyi karatu bane?" yayi maganar sanda ya ajje spoon cikin plate d'in, bata bawa maganar daya fad'a muhimmaci ba seta kalli abincin daya keci da kallo sannan ta kalle shi sanda yake k'ok'arin mik'ewa tace "Wae har ka gama?" ta fad'a itama bayan ta mik'e tsaye cikin maraeraece fuska, sake yamutsa fuska yayi kana yace "Ehh, dama ba yunwa nake ji ba, kije kiyi karatun ki" ya fad'a yana d'aukar wayar sa, seta bishi da kallo sanda yake wucewa har ya fice daga d'akin, komawa tayi ta zauna tana jin yadda wasu k'walla suka tarar mata a ido, dae_dae lokacin Mummy ta k'araso taja kujera ta zauna tana kallan ta tace "Muneerah meya faru?" seta d'ago idanun ta ta kalli Mummyn sannan tace "Mummy kinga fa abinda yaci, kamar dan ina wajen ne fa yak'i ci da yawa fa" "Ke waye ya fad'a miki haka Muneerah?" Mummy ta fad'a tana kallan ta, seta sake maraeraece fuska sannan tace kamar zata sanya kuka "Toh Mummy se yaushe ne zamu saba, har yanzu kullum jiya i yau" ajiyar zuciya Mummy ta sauke sannan tace "Uhmm Muneerah gajen hak'uri ne dake, idan ma kun saba idan ma baku saba ba aure ne dae kin san za'a yi shi koh? Ko kuwa kin ta6a ganin Daddyn ki yayi magana 2? Sun riga sun gama magana saboda haka ki kwantar da hankalin ki, ko ba yanzu ba zaku saba nan gaba" hannu Muneerah ta saka ta sake share k'wallar idanun ta sannan tace "Da gaske Mummy?" ta fad'a kamar zata yi kuka, murmushi Mummy tayi tana jan Muneerah jikin ta tace "K'warae kuwa Munee.." se a lokacin Muneerahn tayi murmushi tana jin wani irin farin ciki mara misaltuwa na mamaye ta, ji take kamar taje tace wa Daddyn nata idan za'a saka musu rana kada a saka da yawa, kae ita da zata iya ma da kanta za taje wajen Abban Rk d'in tayi masa maganar kar a saka ranar da yawa. ... Yana fitowa compound d'in gidan motar Daddy ta shigo gidan, seya k'arasa zuwa parking space d'in zuwa wajen motar, ya sanya hannu ya bud'e murfin motar inda Daddy ke zaune, Daddy ya fito yana murmushi yace "Ka dawo kenan Doctor?" murmushi Rk yayi kana yace "Ehh Daddy, barka da dawowa" "Yawwah" ya fad'a sanda yake mik'a masa brief case d'in hannun sa, hannu 2 Rk ya saka ya kar6a kana suka fara takawa zuwa d'akin Daddyn "Ya karatu ya kuma d'alibae?" Daddyn ya fad'a har lokacin suna tafiya "Alhamdulillah Daddy" Rk ya fad'a "Toh Allah ya taemaka" "Ameen" ya fad'a sannan suka cigaba da tafiya, seda suka shiga parlour sannan Rk ya ajje brief case d'in hannun sa kan kujera kana ya sake fad'in "Sannu da dawowa Daddy" "Yawwah.." Daddy ya fad'a yana sake jin k'aunar Rk d'in a ransa, d'aya daga cikin halayen daya sanya yake son aura masa Muneerah shine tarbiyyar sa, sosae hakan ke k'ara masa k'aemi wajen son cika wannan burin nasu shi da d'an uwan sa "Bari na wuce.." Rk ya fad'a "Tohm shikenan, idan da akwae wata matsalar seka sanar dani" Daddy ya fad'a yana bin Rk da kallo sanda yake ficewa daga cikin d'akin. .. Fitowar su kenan daga Capteria, su 3 ne a wannan karon, rana ta farko kenan data fara bin su Capteria saboda k'aryar su data musu yawa, ita kuwa ba er kowan kowa ba idan tace zata biye musu d'an kud'in da take dashi seta k'arar dashi a kwanaki k'alilan, dan haka take kama kan ta sosae, daga ita se Jidda se Ruks ne yanzun, tana sanye cikin abaya maroon colour da mayafin ta data yafa shi bayan ta saka wata kyakykyawar hula saboda kada sumar ta ta fito. Sun zo zasu gifta ta wajen wasu jerin reading chairs Jidda tace "Ko mu d'an zauna mu huta ne?" da sauri Ayrah ta girgiza kae sannan tace "A'ah ni kam na gaji" dan har ga Allah ta gaji so take ta zauna ta huta, idan da dama ma ta kwanta "Haka dae, Allah kuwa Ayrah kin fiya lalaci" Jidda ta fad'a tana kallan ta bayan ta jefa mata harara, murgud'a d'an k'aramin bakin ta tayi ba tare da tace komae ba, Ruks tace "Gaskiya dae kam, ya kamata mu huta" ganin su dae hutawar zasu yi ya sanya ta ta6e baki sannan tace "Ni dae na tafi.." ta fad'a tana yin gaba, suka bita da kallo sannan suka nemi waje suka zauna. A hankali take tafiya zuciyar ta fall cike da tunanin Umman ta, sosae take jin kewar ta musamman a kwanakin nan duk da kullum se sunyi waya, amma ta k'agu ta gan ta "Raj!!" taji an ambata daga bayan ta, wanda kiran sunan ya gama fita ne da bugun zuciyar ta, take a lokaci guda taji bugun zuciyar ta ya sauya, suna ne da zata iya kiran sa da extra ordinary one, sannan kuma tun daga wancan lokacin bata sake jin me irin sunan ba ballantana tayi tsammanin ko suna ne yazo d'aya, "ko dae shine?" ta tambayi kan ta, wannan tambayar data yiwa kanta ya sanya har bata san lokacin data juya da wani irin sauri ba tana wuwwulga kyawawan idanun ta cikin harabar makarantar, dae_dae lokacin data hango wani ya k'arasa shigewa cikin wata hamshak'iyar mota, cikin sakannin da basu wuce 5 ba motar ta bar wajen, ji tayi kamar sun tafi da duk wani kuzari da numfashin ta, ta lumshe idanun ta tana jan numfashin ta a nutse ko zata samu ya dawo dae_dae "Raj!" yanda aka fad'i sunan ya sake dawo mata cikin kwanyar ta, seta sake bud'e idanun ta tana fatan ace taga Raj d'in ta a gaban ta, toh koma dae kunnen ta ne ke mata gizo?..... Mhiz Innocent....... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* *TITAN'S OF TALENT* Page 017_018 ___A hankali ta sauke numfashi tana sake lumshe idanun ta, ganin da tayi ta tsaya ne akan hanya ya sanya ta jan k'afafun ta ta fara takawa zuwa Hostel, da k'yar ta iya k'arasawa cikin d'akin saboda yadda jikin ta yayi wani irin mugun sanyi haka zalika k'irjin ta ya mata wani irin nauyi. Ajiye littafin hannun ta tayi sannan ta haye kan gadon ta taja pillow ta kwanta tana lumshe idanun ta "Raj!" ta sake fad'a akan la66an ta, cikin lokaci k'ank'ani rayuwar su ta baya ta fara dawo mata cikin kwanya kamar wadda ake haskawa, wata irin kewa ta musamman ta shiga ratsa ta, tana jin ina ma ace ta gan shi, ina ma ta sake ganin shi a rayuwar ta ko da sau d'aya ne, ko ina ya shiga? Ina yake? Meyasa bata sakr ganin sa tun wancan lokacin ba? Se yanzu ta tsaya tayi wa kan ta wad'annan tambayoyin wanda ada k'uruciya bata bar ta tayi ba, tabbas Raj d'in wani mutum ne na musamman a rayuwar ta wanda bata tunanin har abada zata ta6a mantawa da shi, koda kuwa bata sake ganin sa ba a kafatanin rayuwar ta, ko idan ta gan shi zata gane shi? Tana zaune a haka kamar me shirya film duk wani abu daya faru a rayuwar su tana k'ok'arin tuna su, duk da wasu abubuwan da dama ta manta saboda yanayin shekarun ta a wancan lokacin har zuwa sanda Bahijja ta shigo cikin d'akin, ta kalle ta yadda take juyi daga wannan 6angaren gadon zuwa wani 6angaren "Lafiya kuwa Ayrah?" seta bud'e ido da sauri yadda ta tsorata dan sam bata san da shigowar Bahijjan ba kawae maganar ta taji, ganin ta ya sanya ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "Ehh.. Yanzu kika shigo?" "Ehh yanzun nan" Bahijja ta fad'a tana zame mayafin jikin ta, Ayrah ta koma ta kwanta dan sosae take jin dad'in tunanin da take yi. *** *** *** .. Littafin ta ta d'auka ta sake karantawa sannan ta rufe, Ruks dake kusa da ita tace "Wae Ayrah gaba d'aya littafin kike k'ok'arin karancewa ne? Test ce fa ba exam ba" ta fad'a dan tun jiya data farka cikin dare taga Ayrahn na ta karatu, shiru Ayrahn ta mata har seda ta gama zuba littafan ta cikin jaka sannan tace kamar bata son yin maganar "Ae

End of Chapter 18Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next