Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel
By Soyayyanovels
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel

Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel

Author: Soyayyanovels
Chapter 8 of 90
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 Reading now Chapter 9 1,700 words Chapter 10 1,700 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 1,700 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,700 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 1,700 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,700 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 1,700 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 1,700 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,700 words Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,700 words Chapter 62 1,700 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 823 words Chapter 83 2 words Chapter 84 1,700 words Chapter 85 1,700 words Chapter 86 1,700 words Chapter 87 1,700 words Chapter 88 1,700 words Chapter 89 1,700 words Chapter 90 478 words

ya k'araso a hankali ya rik'o hannun Ayrahn dake cigaba da girgiza kae yace cikin rarrashi "Ki taho mana kinji" ya fad'a yana janyo ta, a hankali hannun nata dake rik'e da nasa ya shiga zamowa daga sama zuwa k'asa har zuwa sanda ya zama tafin hannun su ne kawae cikin na juna, Raj ya rik'e hannun nata sosae yana kallan k'wayar idanun ta dake cigaba da zubar da hawaye, Yah Sadeeq be kalle su ba ya jata ya d'auke ta kawae a hannun sa, abinda ya sanya hannun su rabuwa dana juna kenan kuma dae_dae lokacin da Ayrah ta saki kuka me k'arfin gaske cikin kukan tana fad'in "Yah Sadeeq Raj, Yah Sadeeq Raj" be bi ta kanta ba se kwantar da kan nata da yayi a kan kafad'ar sa amma tak'i kwanciya ta cigaba da kukan ta kamar ranta ze fita, a haka yayi gaba. Lumshe idanun sa yayi sanda Ummeen sa ta d'ora hannun ta akan kafad'ar sa, yana jin wasu k'walla na tarar masa a cikin idanun sa, Ummee tace "Kada kayi kuka fa" kamar ma zuga shi tayi se kuwa hawayen suka cigaba da zuba yana saka hannu yana goge su, Umma data mik'e tace "Toh bari mu tafi" "Allah ya tsare Hajiya.." Inji Ummee "Ameen" Umma ta fad'a tana yin gaba... Tunda suke tafiya kukan take yi tana cigaba da ambatar sunan Raj, se rarrashin ta Yah Sadeeq keyi amma tayi kamar bata san yana yi ba, ta cigaba da rera kukan ta tana yi tana sauke ajiyar zuciya, seda suka kusa isa tasha sannan bacci yayi awon gaba da ita a kafad'ar Yah Sadeeq... Motar da zata kaesu Kano direct ita suka samu tana shirin tashi mutane 2 kawae ake jira ta tashi, ganin su Abba ya sanya su dakatawa kwandasta ya kalli Abba yana tambayar inda zeje, Abban ya fad'a masa sannan ya bud'e musu motar, Umma ce ta fara shiga sannan Yah Sadeeq daya zauna a maleji, kana Abba ya kalli wajen da yayi ragowa sannan ya kalli Abbu dake tsaye rik'e da kayan Abban yace bayan ya kalli kwandastan "Ae mu 2 ne kuma naga saura wajen mutum 1" kwandastan ya kalli Abba kana yace "Shawara idan zaka d'auka ku raba motar, idan yaso wasu su tafi yanzu wasu kuma idan wata za taje kanon seta d'auke su" Take Abba yayi na'am da shawarar ya kalli Abbu yace "Ko mu barsu su tafi, mu kuma ma taho?" Abbu yace "Alhaji kar a samu matsala tunda kaga basu ta6a zuwa kano ba se wannan karon.." "Hakane kuma" Abba ya fad'a yana tunanin mafita "Meze hana kuyi gaba ni sena taho daga baya?" Abbu ya katsewa Abban tunanin da yake, Abba ya d'aga kae ya kalle shi kana yace "Babu matsala?" "A'ah babu matsala" Abbu ya fad'a yana murmurshi, mik'a hannu Abba yayi da niyyar kar6ar kayan hannun Abbu, kwandastan yace "Yalla6ae cikin wajen nan wallahi babu wajen da zaka ajiye jakar nan, ko a jikin ka zaka rik'e zaka takura ne kuma ka takurawa mutane" Abba baya son dogon zance dan haka yace "Bud'e min bayan motar na saka to" "Ae da mutane a ciki" sauke numfashi Abba yayi yana tunanin meya kamata yayi yanzun, seya tsinto muryar Abbu na fad'in "Toh Alhaji kona taho maka dasu?" kallan Abbun Abba yayi sannan yayi murmurshi yace "Toh shikenan, yanzu zaka jira zuwan wata ne?" "Ehh In Sha Allah Alhaji, Allah ya tsare.." Abbu ya fad'a "Ameen Ameen, Allah ya tsare dukkan mu" "Alhaji lokaci fa na tafiya" kwandastan ya fad'a yana kallan Abba, kallan Abbu Abba ya sake yi sannan yayi murmurshi ya koma ya shiga cikin motar sannan kwandastan ma ya shiga, Abbu ya sake yi musu addu'a sanda drivern motar ke k'ok'arin tashin ta, be bar inda yake tsaye ba seda motar tasu ta tashi. Tafiyar awanni suka yi suka isa garin na Kano zuwa lokacin Ayrah ta tashi daga bacci ta cigaba da kukan ta, tayi kukan harta gaji ta hak'ura se ajiyar zuciya da take ta saukewa daga k'arshe wani baccin ya sake d'auke ta a jikin Yah Sadeeq dan shi kad'ae ne ze iya rik'e ta saboda yadda su Umman suke a matse a inda suke zaune, se a lokacin Abba yayi dana sanin k'in tahowa da motar sa, daya sani ya kae ta gyara saboda matsalolin da take bashi a kwanakin nan, ganin tafiyar tasu me nisa ce ya sanya be taho da ita ba ko dan gudun matsala.... Sanda suka isa Kanon kae tsaye gidan da Alhaji Maton ya nemar musu suka isa, su Umma ne suka fara shigewa cikin gidan ita da Yah Sadeeq yayin da Abba ya tsaya ya lalubo wayar sa dan tuntu6ar Abbu yaji ko shima ya taho d'in dan yana ganin kamar wannan d'in nauyin sa, yana so kuma ya sanar dashi idan be samu motar ba ya bari se gobe kada yamma tayi masa a hanya, kiran farko da yayi ta shiga ta soma ringing, se dae har kiran ya katse ba'a d'auka ba, hakan ne yasa Abban ya sake kiran layin se dae ga mamakin sa se suke fad'a masa wayar tana a kashe ne, ya riga ya yaddarwa zuciyar sa matsalar network ne tunda a yanzu yayi kira na farko ta shiga yanzu kuma a kashe dan haka ya sake trying number sedae abinda yanzu kuma take fad'a masa shine kwata kwata ma ba zata shiga ba....... *Zarah Bint Yusuf (Mhiz Innocent)* https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* *TITAN'S OF TALENT* Page_006 ___Sosae tsoro ya kama Abba, a ransa yana fatan ba wani abin ne ya faru ba "Lafiya kuwa Abban su?" Umma da fitowar ta kenan ta fad'a tana kallan Abban da damuwa ta gama bayyana akan fuskar sa, kallan ta yayi sannan yace "Na kira layin Kabeeru ne da farko ta shiga yanzu kuma ta dena shiga" Abban ya fad'a "Ae Ina tunanin yanzu yana cikin mota ne, babu mamaki ko shiyasa kaji wayar a kashe" d'an murmushi kad'an Abba yayi sannan yace "Babu shakka ma haka ne" itama murmushin ta maeda masa sannan tace "Ya kamata muje ciki koh?" Babu musu yabi bayan Umman da tayi gaba zuwa cikin gidan daya kasance madaedaeci, gida ne haka me k'ofa da d'aku na 4 a cikin sa, 1 parlour wanda ya kasance shine na Umma sannan d'akin gado shi kuma shine na Abba, sannan ragowar d'aku nan da suka kasance madaedaeta su kuma Yah Sadeeq da Ayrah kowannen su ya d'auki d'aya, se kitchen da ban d'aki, babu laefi gidan yayi kyau duk da ba wani girma gare shi ba amma an masa k'yale k'yale wanda suka k'awata shi. Kae tsaye cikin d'akin Abban suka nufa wanda shima yake d'auke da d'an madaedaecin ban d'aki a cikin sa, Umma ce ta taemaka masa yayi wanka kafin ya fito su d'an zazzagaya gidan, kukan Ayrah data jiyo daga parlourn nata ne ya sanya ta fad'in "Ya ilahy" "Toh rigimatu ta farka kenan" Abba ya fad'a yana murmushi, mik'ewa Umma tayi ta fita daga d'akin dae_dae lokacin da Yah Sadeeq shima yake shirin shiga d'akin, ganin Umma ya sanya shi fad'in "Alhamdulillah, Umma gwara ki rarrashi abar ki" ya fad'a yana juyawa yayin da Umma ta shige cikin d'akin, k'arasawa Umma tayi ta zauna inda Ayrah ke zaune ta kamo ta cikin jikin ta tace "Kiyi hak'uri kiyi shiru kinji Auta" "Umma Raj" Ayrahn ta fad'a tana kallan Umma da jajayen idanun ta, lumshe idanu Umma tayi a ranta tana cigaba da mamakin irin wannan shak'uwa tace "Shikenan za'a kira Abban sa ya kawo miki shi kinji?" seta cigaba da kallon Umman kamar me nazari se kuma tace "Umma ze zo?" murmurshi Umma tayi kana tace "Ehh ze zo" "Kuma in be zo ba na dena kula shi" ta fad'a cike da sakarci tana ta6e baki, girgiza kae Umma tayi "Toh shikenan, kukan ya isa haka Uhmm?" ta fad'a tana kuma shafa bayan ta, cigaba tayi da sheshshek'ar ta har zuwa sanda ta gaji tayi shiru a jikin Umman... Wajen k'arfe 7pm na daren ranar Umma ta shiga d'akin Abba, seta tarar dashi zaune kan gadon, a hankali ta k'arasa ta zauna tana kallan sa tace cikin nutsuwa "Abban su lafiya kuwa?" d'an gyara zama yayi sannan yace "Haka nan kawae nake jin kamar ba lafiya ba, ina tunanin zan koma in bincika dan har yanzu layin sa baya shiga, kuma yaci ace yanzun dae ya iso cikin garin nan" cikin kwantar da murya kuma dan ta k'ara bawa Abban k'warin gwuiwa ya sanya ta fad'in "In Sha Allah yana lafiya, lafiyar ce kuma ta 6oye shi.." "Allah yasa" Abba ya fad'a. Tun Abba na kiran layin Abbu har ya gaji ya hak'ura ya cigaba da addu'ar Allah yasa Abbun yana lafiya, duk kuma yabi ya takurawa kansa yana ganin kamar duk abinda ya samu Abbun shine sila, haka dae Umma ta dinga bashi baki akan ya kwantar da hankalin sa amma har zuwa dare babu kiran Abbu.. Washe gari Abba ya kasa sukuni dan haka tunda yayi sallahr Asuba ya shirya cikin wani yadi me kyau ya kalli Umma dake kallan sa "Har yanzu hankali na ya kasa kwanciya Ruk'ayya, gwara naje na duba da kae na" jinjina kae Umma tayi dan itama yanzun ta fara d'an shiga cikin tsoro gwara Abban ya duba ko lafiyar ce ta 6oye Abbu, amma dan ta sake kwantar masa da hankali tunda tafiya zeyi ya sanya ta fad'in "Hakan ma yayi Abban su, Allah ya tsare hanya..amma yadda nake ta tunani dae babu mamaki motar da zata zo zuwa Kano ne be samu ba shiyasa ya bari se yau ina ga" murmurshi Abba yayi kafin yace "Toh banda abun Kabeeru ae ya kira ni ya fad'a min ko dan kada hankalin mu ya tashi dukan mu" "Hakane Abban su, In Sha Allah lafiyar ce ma" "I hope so" Abba ya fad'a sanda yake d'aura agogon hannun sa. Sanda ya fito daga d'akin yayi dae dae da lokacin da Ayrah ke fad'in daga toilet d'in tsakar gida "Umma na gama" k'arasawa Umma tayi zuwa cikin toilet d'in ta yiwa Ayrahn tsarkin fitsarin da tayi sannan suka fito tare, da gudu ta isa wajen Abba tace hannun ta rik'e da nashi

End of Chapter 8Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next