Soyayyanovels
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel
By Soyayyanovels
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel

Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel

Author: Soyayyanovels
Chapter 20 of 90
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 1,700 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 Reading now Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 1,700 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,700 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 1,700 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,700 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 1,700 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 1,700 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,700 words Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,700 words Chapter 62 1,700 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 823 words Chapter 83 2 words Chapter 84 1,700 words Chapter 85 1,700 words Chapter 86 1,700 words Chapter 87 1,700 words Chapter 88 1,700 words Chapter 89 1,700 words Chapter 90 478 words

ya bawa tambayar ta ta muhimmaci ba yace "Zaki tafi ne?" a shagwa6e ta furta "Haba haba kae kuwa Yaya na, ni fa hira nazo na taya ka" kansa ya d'an dafe dan shi yana jin kamar ciwon kae take k'ok'arin saka masa, a yayin da ita a 6angaren ta tana yin komae ne dan saboda ta burge shi, jin da tayi bece komae bane ya sanya ta fad'in "Ohk muje na raka ka" ta fad'a tana murmushi "No babu buk'ata" ya fad'a yana d'aukar key d'in motar sa yayi gaba ita kuma ta rufa masa baya zuwa wajen, ya shiga motar sa yayin da ita kuma ta shiga ta ta kowanne ya tada tasa. A hankali take takawa fuskar nan ta ta kamar wadda aka yiwa duka, se cika take tana batsewa, wayar ta ce tayi k'ara ta zaro ta daga cikin hijab d'in jikin ta sannan ta d'aga tana karawa a kunnen ta, daga can 6angaren Yah Sadeeq yace "Ayrah.." "Na'am Yah Sadeeq" ta fad'a tana d'an tura bakin ta gaba kad'an, daga can 6angaren yayi murmushi kana yace "Yau kuma waya ta6a min k'anwa ta? Ko dae wannan likitan ne?" daga inda take ta d'an yi murmushi jin yadda Yah Sadeeq d'in ya gano hakan da wuri, ko da yake hakan ba abin mamaki bane dan kusan koda yaushe k'orafin ta baya wuce akan Rk "Shi ne" ta fad'a tana sake kwa6e fuska kamar tana gaban sa "Wae ni kam meyasa doctorn nan ya takurawa k'anwa ta ne?" "Oho masa" kafin Yah Sadeeq d'in yace komae ta sake fad'in "Yah Sadeeq ina Umma?" "Umma na gida, idan na koma zan kira ki In Allah ya yadda se ku gaesa" bata san sanda wani murmushi ya su6uce mata ba, haka suka cigaba da hira da yayan nata cike da k'aunar juna. ... Ita da Jidda ne cikin Cafe d'in, mutumin ya kalle su sanda Ayrah ke fad'in "Pls kayi mana kaaji" seya jinjina kae sannan yace "Ohk, amma zan je na samo mae idan zaku jira ni" "Babu matsala.." Ayrah ta fad'a tana neman waje ta zauna, dae_dae lokacin da mutumin ke shirin fita daga wajen yayi dae_dae da lokacin daya shigo cikin madaedaecin Cafe d'in, yana sanye cikin wata kyakykyawar riga da bluen jeans wad'anda suka matuk'ar yi masa kyau, kamar koda yaushe yanzu ma kan sa babu komae se kwantacciyar sumar kan sa da koda yaushe kamar ana k'ara mata shek'i ne da kyau, dakatawa mutumin yayi da murmushi kan fuskar sa yana fad'in "Doctor.. doctor barka da zuwa" yayi maganar yana mik'a masa hannu, Rk ya mik'a masa hannu suka gaesa shima da wani tsadadden murmushi akan fuskar sa, Jidda data ga shigowar sa sanda ta mik'e tace "Barka da wannan lokaci Sir" "Barka" yayi maganar har lokacin hannun su na cikin na juna shi da mutumin "Bari naje pls Ayrah, me zan siyo miki?" murmushi tayi kana tace "Mango" dariya Jidda tayi k'asa k'asa sannan tace "Nima bansan meyasa na tambaya ba bayan na san ina tare da mayyar mangoro Ayrah!!" ba saurarar su yake ba kuma be damu da kallan wadda ta gaeshe shi ba amma tabbas wannan maganar ta sauka cikin kunnen sa har be san sanda yayi sauri ya d'aga kae ya kalli Jiddan ba, ita kuwa sosae hakan ya mata dad'i har da chanja tafiya ko da ta janyo hankalin sa, se dae abinda bata sani ba sam bema kalli fuskar ta ba balle akae ga kallan tafiyar ta, bega wadda take bayan ta ba saboda ita Jidda ta taso zata fita ne, kafin kuma ya maeda duban sa wajen seya jiyo mutumin nan na fad'in "Raj pls bari na d'an je na samo mae zan yi wani aeki ne, idan babu damuwa a jira ni pls" yayi maganar yana murmushi, se kawae ya d'aga masa kae yana lumshe manyan idanun sa, shi kuma yace "Toh nagode" yayi maganar yana bin bayan Jidda data fita, tunda taji sunan da mutumin nan ya ambata ta d'aga dara daran idanun ta ta kalli wanda aka kira da Raj d'in, bata san sanda ta mik'e ba har handout d'in dake kan cinyar ta ta zame, shima ita yake kalla yana so ya bar k'wak'walwar sa tayi aekin daya dace, cikin en sakannin da basu wuce 2 ba idanun su suka sark'e cikin na juna, a lokaci guda zuciyoyin su suka buga wanda har seda Rk ya d'an lumshe manyan kyawawan idanun sa, yanayi ne da be ta6a jin sa akan kowacce d'iya mace ba, wani sabon al'amari ne daya dad'e yana bashi mamaki, dukkan su se suka kaasa d'auke idanun su daga cikin na juna duk da yadda hakan ke azalzalar zuciyoyin kowannen su, sun kae tsawon minti 1 a haka kafin Ayrah tayi watsi da duk wani tsoro, wasu wasi tare da taraddadi ta watsa su gefe sannan ta tattaro jarumta kana ta d'aga yatsan ta dake rawa kamar me, ta nuna shi sannan ta bud'e bakin ta daya mata wani irin nauyi bayan ta lumshe idanun ta sanda wasu kyawawan hawaye suka zuba akan fuskar ta ta furta.... Mhiz Innocent..... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* *TITAN'S OF TALENT* Page 019_020 "Raj!?" ta k'arashe maganar da sigar tambaya, lumshe nasa idanun yayi daga cikin nata yana jin yadda zuciyar sa ke azalzalar sa na k'ara k'aemi, cigaba tayi da kallan sa har lokacin bugun zuciyar ta be koma dae_dae ba jira take kawae ta tabbatar, taji daga bakin sa cewar da gaske shine Raj, a hankali ya jinjina kan sa sannan da muryar sa wadda ta d'an shak'e shima saboda tsananin mamaki yace k'asa k'asa, wanda idan ba dan babu hayaniya a wajen ba da ko ita da take a cikin wajen ba zata ji ba "Ayrah!!?" seta shiga jinjina kae da sauri wasu hawaye na cigaba da ambaliya akan kuncin ta sannan lokaci guda kuma ta saki wani murmushi duk da har lokacin bata dena kukan ba, ta kaasa daurewa, ta kaasa cijewa, har izuwa lokacin wani irin azalzala zuciyar ta ke yi tana wani irin zillo dan haka cikin k'ank'anin lokaci da kuma sauri ta k'arasa ta rungume shi lokaci guda tana runtse idanun ta ko zata ji sauk'i daga abinda take ji a cikin zuciyar ta, k'irjin ta ya cigaba da bugawa da sauri da sauri kamar wadda tayi gudu, kamar wani soko ya tsaya kawae bayan sauke wata doguwar ajiyar zuciya, yana jin yadda ta rik'e shi sosae da alama tsananin farin ciki ne ya sanya ta hakan, wani sassanyan murmurshi ne ya wanzu akan kyakykyawar fuskar sa sannan akan la66an sa ya furta "Har yanzu dae bata chanja ba" hannun sa ya saka ya zame ta daga jikin sa sanda take kuka me d'an sauti, a hankali ya k'arasa ya zaunar da ita kan kujerar wajen sannan ya saki hannun ta a ransa yana furta "Astagfirullah" a kunnen ta abinda ya fad'a d'in ya sauka duk kuma se taji wata matsananciyar kunya ta kama ta, ta kaasa controlling kan ta a lokacin, ta rasa abinda za tayi taji sauk'i, farin ciki da kuma mamaki gami da son tabbatar da abinda ta gani ne ya sanya ta rungume shi ba tare da wani tunani ba, yana tsugunne akan k'afafun sa daga k'asan inda take yana cigaba da kallan kyakykyawar fuskar ta, shi kan sa har ya zuwa lokacin ya kasa dena mamakin shin da gaske Ayrah ce? wannan d'in Ayrahn sa ce? Dae_dae lokacin ta d'ago jajayen idanun ta ta sauke su a kan sa farar fuskar nan tayi jawur haka zalika a d'an shagwa6e ta kalle shi, be san sanda wani murmushi ya su6uce masa ba, babu shakka ita d'in ce, kuma har yanzu halayen ta na nan "Da gaske Raj d'ina ne kae?" ta sake tambaya dan har lokacin tana tantama ne, musamman yadda tasan Raj d'in ta basu da hali, amma wannan tana ganin sa ne mutum me kud'i, a yadda ma taji ana kiran sa kamar likita ne in dae ba tayi mistake ba, idanun sa ya kashe mata wanda hakan ya sanya ta saurin kauda nata idon tana jin wani irin bak'on al'amari da tunda take bata ta6a jin sa akan kowanne d'a namiji ba, yanayin da take ji a yanzun wanda ke tafiya da dukkan wani bugun numfashin ta "Raj Kabeer" yayi maganar yana mik'ewa ya zauna gefen ta dan ya sake tabbatar mata da shi d'in ne ba wani ba, a hankali ta sake lumshe idanun ta tana jin wani irin dad'i na cigaba da ratsa ta, ita kam yau wace irin rana ce me muhimmaci a wajen ta? Wace irin ranar farin ciki ce a gare ta wadda a cikin ta taga Raj, yau gata ga Raj d'in ta bayan tsawon wasu shekaru? "Meyasa baku sake zuwa gidan mu ba?" tayi maganar tana langa6ar da kae gami da kallan sa, se dae a wannan karon bata kalli k'wayar idanun sa ba, kafin ya kae ga cewa komae me Cafe d'in yayi sallama ya shigo wajen, da mamaki ya kalli Rk dake zaune kujera d'aya da wata 'ya mace, abin ya matuk'ar bashi mamaki har hakan seda ya bayyana akan fuskar sa amma ya maaze yace "Doctor!!" dukan su suka kalle shi dan sam basu san da shigowar sa ba saboda yadda suka shagala da son jin abubuwa da dama daga kowannen su "Pls jira ni a waje!!" Rk ya fad'a bayan ya d'an kalli Mutumin, cike da mamakin dae ya furta "Ohk.." sannan yayi waje ya nemi waje ya zauna har lokacin yana cigaba da mamakin Rk d'in, kamar bashi ba.. "Bansani ba, nima bansan dalili ba" yayi maganar a ransa yana zurfafa tunani ko ze gano dalilin da yasa basu je gidan su Ayrahn ba amma ya kaasa, ita tunda ta gano shine Raj duk wannan tsoron nasa da take ji se taji kamar ya tafi, gaba d'aya ma ta manta shi a matsayin Rk kawae tana masa kallan Raj ne "Kullum ina tunanin ka, amma baka ta6a zuwa waje na ba" tayi maganar kamar zata saka kuka, d'an shiru yayi yana cigaba da kallan ta sannan yace bayan ya lumshe idanun sa "Ban san a ina zan same ki ba Ayrah, ki min uzuri pls.." yana

End of Chapter 20Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next