Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel
By Soyayyanovels
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel

Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel

Author: Soyayyanovels
Chapter 25 of 90
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 1,700 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 1,700 words Chapter 25 Reading now Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,700 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 1,700 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,700 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 1,700 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 1,700 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,700 words Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,700 words Chapter 62 1,700 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 823 words Chapter 83 2 words Chapter 84 1,700 words Chapter 85 1,700 words Chapter 86 1,700 words Chapter 87 1,700 words Chapter 88 1,700 words Chapter 89 1,700 words Chapter 90 478 words

su, tayi wasa da hankalin su, ta kuma nuna musu yawan shekaru ba shine wayo ba. .. Da sallama ya shiga d'akin yana sanye cikin wasu k'ananan kaya masu kyau da taushi, kan sa d'auke da facing cap data matuk'ar k'awata shigar sa ya fito yayi kyau abin sa, cikin sa'a seya samu Mummy har ma da Daddy a d'akin, ba k'aramin dad'in ganin hakan yayi ba, dan haka ya k'arasa ya zauna k'asan Carpet yace "Barkan ku da warhaka" "Barka kadae" suka had'a baki wajen fad'in hakan "Daddy dama inaso ne na shaeda maka yau zan koma Kano" "Kano kuma Likita? Wani abu ne ya faru?" seya girgiza kae kawae yana d'an lumshe idanun sa kad'an bece komae ba har zuwa sanda Mummy tace "Haba kae kuwa Raj, gaggawar ta me ce?" "A'ah Mummy.." shine abinda kawae ya fad'a, Daddy yace "Ko dae akwae abinda zaka yi ne acan d'in?" tambayar Daddyn ta matuk'ar yi masa dad'i dan haka da sauri ya furta "Ehh Daddy, akwae wani abu me muhimmanci da zan gabatar acan d'in.." "Toh shikenan babu damuwa, akwae maganar ma dama da zaku yi da Abbun naka.." be bawa zancen muhimmanci ba dan haka kawae abinda yace shine "Tohm" "Allah yayi maka albarka kaji Doctor, Allah kuma ya sanya albarka" shine abinda Mummy tace "Ameen" kawae yace duk da ita kan ta be gane akan maganar da take magana ba, ya dae fi tunanin itama taji labarin ajiye aekin da zeyi ne yasa take magana fatan alkhaeri, seya mik'e hannun sa d'aya cikin aljihun sa yace bayan yayi murmushi "Daddy bari naje na sake shiryawa" "Toh Raj, seka fito" daga haka ya fice daga d'akin. .. Ko jakar ta bata iya d'auka ba ta fad'a cikin gidan nasu da gudu tana kwad'a sallama da siririyar muryar ta, wani sanyi Umma taji ya ratsa ta jin muryar shalelen er tata, kafin ma ta kae ga k'arasowa Umman ta fito daga cikin d'akin ta, aekuwa tana shigowa ba tayi wata wata ba ta fad'a jikin Umman tana sakin dariya lokaci d'aya tana furta "Nayi kewar ki sosae Umma ta" murmushi Umma tayi ita kan ta tasan tayi kewar d'iyar ta ta sosae, dan haka itana ta rungume ta tana fad'in "Yanzu ae gani gaki koh?" seta jinjina kae har lokacin tana jikin Umma, sun kae wajen minti 1 a haka sannan Ayrah ta saki Umma tana fad'in "Umma ina Yah Sadeeq?" "Yana d'aki bacci yake" Umma ta fad'a tana kallan d'iyar ta ta "Umma wallahi yanzu Yah Sadeeq ya zama malalaci, kullum cikin bacci" ta fad'a lokacin data shiga d'akin nasa, seta hange shi kwance kan gadon idanun sa a rufe ya lullu6e rabin jikin sa da bargo, se tayi murmushi tana jin dad'in ganin sa sannan ta k'arasa ciki tana fad'in "Yah Sadeeq ka tashi, na dawo" kamar daga sama ya jiyo muryar lilin ta sa, dan haka a hankali ya bud'e idanun sa se kuwa ya sauke su a kan ta, murmushi suka sakarwa junan su sannan Yah Sadeeq yace "Yanzu kuka shigo?" "Ehh Yah Sadeeq nayi kewar ka wallahi" ta fad'a tana 6ata fuska, dariya yayi yana jin dad'in ganin k'anwar ta sa dan shi kan sa yayi kewar ta irin sosae d'in nan "Nayi kewar rigimar nan taki Auta" ya fad'a har lokacin yana murmushi "Kae Yah Sadeeq rigima kuma?" ta fad'a har lokacin dae tana 6ata fuska gami da tura baki "Toh shikenan dae ya hanya?" ya fad'a yana k'ok'arin tashi zaune, shi kan sa baya so ta gane karaya ce a k'afar sa dan ya riga yasan halin ta yanzun nan zata fishi shiga damuwa, se akayi sa'a ma tace "Yah Sadeeq kayi baccin toh, idan ka tashi se muyi hirar" ta fad'a tana kallan sa, seya koma ya kwanta ba dan yana tunanin ze iya baccin ba sannan yace "Toh shikenan Auta.." "Yawwah Yah Sadeeq" ta fad'a tana ficewa daga d'akin tana fad'in "Umma kin ga lalacin Yah Sadeeq d'in koh? Ya sake komawa baccin" ta fad'a tana k'arasawa tsakar gidan, dae_dae lokacin da Umma take fad'in "Za dae a tantance malalacin" turo d'an k'aramin bakin ta tayi sannan tace "Kae Umma" dariya Umma tayi tana fad'in "Toh shikenan, ina Abban?" "Aou" ta fad'a bayan ta kae hannun ta kan bakin ta sannan tace "Allah sarki Umma k'anwar Zaenab ce ta rasu shine ya tafi za'a kae ta" "Innalillahi wa inna ilaehi rajiun, ashe ta rasu? Toh Allah ya ji k'an ta, ashe ba mazauniya bace" Umma ta fad'a tana tuna yarinyar data rasun wadda ba tafi wata 5 da haehuwa ba, k'arasowa Ayrah tayi ta zauna kan tabarmar da Umma ta shimfid'a, seda Umma ta zauna sannan ta d'ora kan ta akan cinyar Umman tace "Umma nazo muku da wani albishir, amma bazan fad'a ba se Abba ya dawo" "Wane albishir ne wannan?" "A'ah Umma se Abba da ya dawo" Ayrahn ta fad'a tana sake gyara kwanciyar ta kan cinyar Umma "Toh shikenan, ya exam ya karatun?" "Umma komae Alhamdulillah fa" ta fad'a tana murmushi, daga haka suka cigaba da hira, Umma nata jin labaran da Ayrahn ke ta bata, wani tayi dariya wani ta girgiza kae cike da ganin wautar Ayrahn, se dae lokaci lokaci ta kan yi shiru ta saki murmushi me k'ayatarwa idan ta tuna Rk, Umman na lura da ita amma har lokacin tak'i fad'awa Umma komae game da albishir d'in da tace zata yi musu, dan haka itama ta mata shiru kawae tana cigaba da saurarar hirar da take mata. ... A 6angaren Rk kuwa dab da maghrib ya isa gidan nasu cikin motar sa, k'atuwar harabar gida dake d'auke da manya manyan motoci a gefe guda, shuke shuke da sauran abubuwa na burgewa, kae tsaye parking lot d'in ya wuce da motar sa yayi parking nata dae_dae lokacin da wani ya k'araso da sauri yana fad'in "Barka da dawowa yalla6ae" ya fad'a yana duk'awa "Barka, a shigar min da kaya ciki" shine abinda Rk ya fad'a yana wucewa cikin tafiyar nan tasa ta nutsuwa hannun sa d'aya cikin aljihun sa, tafiya me tsayi ce yayi kafin ta sada shi da aenahin inda d'aku nan masu gidan yake, yayi murmushi sanda ya ganshi a k'ofar Parlourn Ummeen sa, babu 6ata lokaci ya sanya k'afar sa cikin k'aton hamshak'in Parlourn da sallama, Ummee na zaune kan kujera hannun ta d'auke da remote tana shirin chanja channel yayi sallama, seta ajje remote d'in akan kujera tana kallan sa sanda wani k'awataccen murmushi ya su6uce a fuskar ta tace tana k'arasawa inda yake "Oyoyo Oyoyo.." k'arasawa yayi inda take yayi hugging nata sannan ya zauna a k'asan kujerar yace cikin girmamawa "Ummee barka da wannan lokacin" "Barka dae ya hanya?" "Hanya Alhamdulillah" ya fad'a dae_dae sanda aka k'walla kiran Sallah a masallacin su dake jikin gidan nasu, se yayi saurin mik'ewa yana fad'in "Ummee bari naje" "Toh Raj seka dawo" ta fad'a tana bin sa da kallo har lokacin da murmushi kan fuskar ta. A harabar gidan suka yi kaci6us da Abbu dake sanye cikin wata dakakkiyar bluen shadda d'inkin babbar riga data matuk'ar yi masa kwarjini "Welcome my Son" Abbu ya fad'a yana bud'a hannun sa, Rk ya k'arasa yayi hugging mahaefin nasa sannan yace "Barka da wannan lokacin Abbu" "Barka dae Raj, ka dawo ashe? Mu wuce masallaci dae tukunna" babu 6ata lokaci suka wuce masallacin dake jikin gidan su, ana Sallahr Isha'i Rk ya koma gida saboda yadda yake so ya watsa ruwa a jikin sa yayin da ya bar Abbun a masallaci. Cigaban nan wajen yana page 1, yanzu haka mun ji TUSHEN LABARIN MU dan haka zamu d'ora ne da CIGABAN LABARI.... ... "Shin yanzu kin san wanene Raj d'in da kike magana a kan sa? Waye mahaefin sa? Meya aekatawa rayuwar ku? Mahaefin ku ya amince masa ya bashi amanar da be ta6a bawa wani ba amma daga k'arshe ya wulak'antashi ya tozarta shi yayi wancakali da duk wannan amanar, mahaefin ki ya d'auko shi daga rana ya sanya shi a inuwa amma daya tashi dame ya saka mishi? Seya d'auki mahaefin ki ya jefa shi cikin ranar shi kuma ya cigaba da rayuwar sa ba tare da tunanin halin da zamu iya shiga mu dukan mu ba, Yanzu haka Sadeeq na kwance ne a d'aki sakamakon karayar daya samu ana buk'atar a masa aeki amma babu kud'in aekin, mahaefin Raj ya cuci Abban ku, ya raba shi da dukiyar sa, takaddun sa masu muhimmanci, uwa uba kuma shine silar shigar mu cikin kowanne hali, silar abinda ya aekatawa mahaefin ku ne ya janyo masa hawan jini, ya cuce mu mu kan mu akan son zuciyar sa, ta yaya zan miki wannan bayanin a wancan lokacin ki fahimta? Ina k'wak'walwar ki take ta k'arfin fahimtar wannan zancen?" Umma ta k'arashe maganar tana kallan Ayrah da tunda ta fara maganar ba tace komae ba, idanun ta gaba d'aya Umma suke kalla har lokacin tana cigaba da tuno maganar Umman cikin kunnuwan ta wanda take jin su kamar amsa kuwwa suke mata a kunnen ta, dan kuwa duk da Umman tayi shiru hakan be hana ta cigaba da jiyo sautin muryar Umman a kunnen ta ba, kunnen nata ya mata wani duumm kamar wadda ta kurumce banda sautin muryar Umman babu abinda take ji har yanzun, bata ma sani ba ko Umman ta cigaba da fad'a mata magana ko tayi shiru ne ita dae bata sani ba, abinda kawae ta sani maganganun nan da suka sanya ta cikin sani irin shock da kuma hutun da k'wak'walwar ta ta tafi na wucin gadi su kad'ae keta dawo mata, jikin ta wani irin rawa yake yi kamar me jin sanyi, duk da idanun ta ba'a rufe suke ba amma se take so ta sake bud'e su tarr ko dan ta cigaba da kallan Umman da yanzun take ganin ta dishi dishi, gaba d'aya ta kasa koda bud'e bakin ta ne ballantana ta furta wani abun, koda yake idan ta bud'e d'in ma menene za tace?? Mhiz Innocent...... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* *CHA PTER ONE* *TITAN'S OF TALENT* Page 027_028 ___Ganin da Umma tayi har lokacin Ayrah ta gaza furta komae ya sanya ta sanya hannu ta share idanun ta itama da k'wallar ta gama tarar mata,

End of Chapter 25Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next