Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel
By Soyayyanovels
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel

Zazzafar Kauna Part One Complete Hausa Novel

Author: Soyayyanovels
Chapter 54 of 90
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 1,700 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 1,700 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,700 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 1,700 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,700 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 1,700 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 1,700 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 Reading now Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,700 words Chapter 62 1,700 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 823 words Chapter 83 2 words Chapter 84 1,700 words Chapter 85 1,700 words Chapter 86 1,700 words Chapter 87 1,700 words Chapter 88 1,700 words Chapter 89 1,700 words Chapter 90 478 words

maeda ta tasa halak malak, sannan yace "Ranar da kika dena so na, ki ka kuma sallamawa wata matar ni.." ba tare da ta shirya ba ta d'aga idanun ta ta juye su cikin na sa idanun sanda ya maeda fuskar sa ta koma aenahin ta sa, babu kuma alamar wasa a maganar da yayi se dae kuma yayi maganar ne a narke kamar kuma wani maraya, cigaba tayi da kallan sa kamar me nazari haka kawae taji jikin ta yayi wani mugun sanyi ga kuma wani irin rauni daya ziyarce ta lokaci guda, ita idan suna tare da shi mantawa take yi akwae wata mata a gefen su da itama take amsa sunan matar sa, se kuma ta sauke idanun ta sannan ta saka hannu ta d'auke k'wallar data tarar mata cikin idanu kafin ta sake kallan sa dae_dae lokacin da yake fad'in "Uhmm ko ba haka bane?" bata san sanda ta girgiza kae ba sannan ta bud'e bakin ta a nutse ta furta "Ni dae a'ah fa" ta k'are maganar a raunane, iska ya fesar daga bakin sa lokaci d'aya yana lumshe idanun sa, seya saka hannun sa duka biyun kawae ya rungume ta tsam cikin jikin sa ya d'ora ha6ar sa akan kafad'ar ta kana ya kae bakin sa saetin kunnen ta ya furta "Har yanzun kina sona ko kin bar wa wata ni?" dira k'afa ta fara yi lokaci d'aya tana fara tashi daga jikin sa "Ni dae Allah ka dena min zancen wata, bana so fa" murmushi yayi kana ya furta "Toh ki ce kina sona har yanzun" ya fad'a bayan ya saki wani k'awataccen murmushi "Ni fa ina son ka, ina son ka, ina son ka Allah kuwa" ta fad'a tana kae hannun ta kan fuskar ta ta rufe, tana kuma sake tura kan ta cikin jikin sa saboda yadda kalmar ta fito tun daga can k'asan zuciyar ta, wani irin sanyi ne ya shiga ratsa ilahirin jikin sa, ya lumshe idanun sa yana sake shigar da ita cikin jikin sa kamar ze maeda ta cikin sa, shi kad'ae ya san wani irin farin ciki da ya mamaye shi mara misaltuwa, ko babu komae ya gama da wannan matsalar itama, yanzu wadda yake so ya tunkara itace sasanta tsakanin Abba da Abbu. ... Da sallama ya shigo cikin gidan fuskar sa d'auke da mad'aukakin annuri, Umma da fitowar ta kenan daga d'aki ta k'araso ta kar6i ledar dake hannun sa "Sannu da zuwa Abban su" ta fad'a tana jin dad'in yadda ta gan shi d'in, dan da alama ko ba'a fad'a ba yau d'in wani gagarumin abu ya same su "Yawwah sannu ka dae.." ya fad'a yana neman waje ya zauna akan tabarmar dake shimfid'e a tsakar gidan, wucewa kitchen Umma tayi ta ajje ledar hannun ta sannan ta dawo tsakar gidan itama ta nemi waje ta zauna "Ina wannan yaron?" kallan d'akin Yah Sadeeq Umma tayi kana tace "Yanzun nan ya shiga d'aki, ina ga be ji shigowar ka ba... Sadeeq.." Umma ta k'arasa maganar cikin d'an d'aga murya tana kallan d'akin Yah Sadeeq d'in "Na'am Umma" Yah Sadeeq ya fad'a yana fitowa daga cikin d'akin hannun sa d'auke da wayar sa, shima k'arasowa yayi ya nemi waje ya zauna sannan yace "Abba sannu da zuwa, ashe ka dawo?" "Yawwah Sadeeq, wallahi kuwa na dawo" "Ruqayyah wani abun kirki ne fa ya same mu" Abba ya fad'a yana murmushi bayan ya maeda duban sa kan Umma "Toh ikon Allah, Abban su meya same mu?" ajiye wayar sa Yah Sadeeq yayi a gefen sa dan jin abinda Abban ze fad'a dan dama missed call d'in Rk ya gani a wayar ta sa yana k'ok'arin kira kuma Umma ta kira shi "Alhaji Wada ya sakar min shagon nan gaba d'aya, ni zan dinga kula da shi kawae dae ya had'a ni da wani yaron sa da suka dad'e tare suna kasuwanci" ya k'arasa maganar yana jin dad'i har cikin ran sa "Kae Alhamdulillah" Umma da Yah Sadeeq suka had'a baki wajen fad'a "Allah ya saka masa da alkhaeri Abba, amma naji dad'i sosae wallahi" inji Yah Sadeeq, addu'a suka shiga jerawa dukan su suna kuma yiwa mutumin addu'ar k'arin arzik'i me amfani cike da jin dad'in yadda ya faranta musu. Se bayan sun gama tattaunawa sannan Yah Sadeeq ya d'auki wayar sa ya kira Rk, dab da zata tsinke ya d'aga wayar "Yah Sadeeq An yini lafiya?" shine abinda Rk ya fad'a, murmushi Yah Sadeeq yayi kafin yace "Wae ba zaka dena wannan Yah Sadeeq d'in ba fisabilillahi?" shima murmushin yayi me d'an sauti kamin yace "Ae yayan ne dole na girmama ka" "Toh shikenan, ya aeki?" "Alhamdulillah" Rk ya fad'a "Masha Allah, d'azu naga kiran ka bana kusa ne" neman waje Rk yayi ya zauna kafin yace "Ohk ehh, dama ina so naji inzo in d'auke ka ne? Ko kuma na tura maka address d'in?" seda Yah Sadeeq ya d'an yi jim kad'an kafin yace "Tura min Address d'in kawae.." "Ohk, a gaeda su Abba" Rk ya fad'a yana katse wayar. Kallan Umma yayi dake zaune kusa dashi yace "Umma yaushe zamu je gidan Auta?" ya fad'a yana murmushi, shi kan sa be ta6a kawowa a ran sa Autar ta su za tayi aure yanzu ba, musamman saboda ga6untar ta da wautar ta, se gashi ikon Allah yanzu haka tana gidan ta "Gidan Auta kuma Sadeeq?" Umma ta fad'a tana rik'e ha6ar ta, kafin yace komae kuma ta d'ora da "Rufa min asiri kada a fara yawo dani cikin gari, dududu ma yaushe akayi auren har da zan je?" "Haba Umma babu fa komae dan kin je" girgiza kae Umma tayi kafin tace "A'ah a'ah ba dani ba, kae dae kaje ka gano min d'iya ta, idan kaje kamar naje ne" jinjina kae Yah Sadeeq yayi yace "Shikenan Umma.." ... Daga cikin d'akin ta ta fito sanye cikin doguwar rigar abaya, ta d'aura mayafin a kan ta, ba dan taji zuwan Auntyn ta ta ba babu abinda ze saka ta sanya kayan, da sauri ta k'arasa ta rungume Aunty Zeenahn dake tsaye cikin parlourn hannun ta d'auke da er k'aramar trolley "Oyoyo Aunty na, naji dad'in zuwan ki wallahi" ta fad'a cike da mad'aukakin farin ciki, dan kuwa har cikin ran ta tayi matuk'ar farin ciki da zuwan Auntyn musamman yadda ya kasance tunda suka yi waya da Auntyn bata sake zuwa d'akin nasa ba kamar yadda ta umarce ta, se dae shi idan yazo zezo yaji idan bata da damuwa ya wuce nasa d'akin, sosae yaji dad'in yanda ta dena shishishige masa d'in, ita kuwa takaeci ne kawae yake isarta idan taga ya bar mata d'akin ya koma na sa. "Oyoyo daughter me, naga kin sake fresh?" Auntyn ta fad'a bayan ta sake ta, d'an ta6e baki tayi kamin tace "Kae Aunty.." tayi maganar tana maeda duban ta kan Bahijja dake tsaye tana kallan su "Ashe tare kuke tafe, sannun ku da zuwa.." "Yawwah sannu dae Muneerah" Bahijja ta fad'a tana neman waje ta zauna, itama Aunty Zeenah zama tayi tana kallan Muneerah data nemi waje itama ta zauna "Me kike nufi? Mu d'auko hanya tun daga Zaria sannan kice babu abinda kika yi mana?" hannu ta saka a kan ta ta d'an sosa sannan tace "Kae Aunty, kin san fa dama ba wata gwana bace ni a wajen nan, kuma dama in dae yana gida shi ke siyo mana abinda zamu ci, shi kan sa be damu da se nayi girki ba shiyasa ma nima bana damuwa" kallan ta kawae Aunty Zeenah ke yi har ta gama maganar sannan ta shiga jinjina kae "Lallae dole sena tashi tsaye a kan ki Muneerah, dan na lura shashasha ce ke.." 6ata rae Muneerah tayi ba tace komae ba. Mik'ewar da Bahijja tayi ne ya sanya dukan su suka kalle ta "Ina zuwa?" Aunty Zeenah ta fad'a "Gidan su k'awar nan tawa da nake fad'a miki mana Aunty, na mata alk'awarin ina shigowa Kano zan je gidan su ne.." rik'e baki Aunty Zeenah tayi tana kallan ta "Ke ni fa bana son yawo, kada ki saka Abban mujaheed yace zeyi fad'a na bar ki kin fita" (Bahijjan er k'anwar mijin Aunty Zeenah ce wadda suke matuk'ar d'asawa tun tuni, da farko zuwa gidan kawae take ta tafi, daga k'arshe ma seya kasance kawae ta koma wajen ta da zama) "Allah Aunty bazan dad'e ba" "Shikenan kiyi da jiki dae.." "Tohm sena dawo" Bahijja ta fad'a tana ficewa daga d'akin, maedo da duban ta kan Muneerah Aunty Zeenah tayi tace bayan ta gyara zama "Ina mijin na ki?" ta6e baki ta sake yi kafin tace "Yana asibiti, aekin kwana ze yi, se gobe zaki gan shi" "Toh yayi, yanzu dae muje ki samar min wani abun in ci kafin mu fara abinda ya kawo ni" mik'ewa Muneerah tayi kana ta amsa da "Toh" daga haka suka wuce kitchen d'in tare. ... Duk da ba wani sanin yadda garin yake Bahijja tayi ba hakan be hana ta d'aukar mota ba kawae ta sanar da shi inda ze kae ta kamar yadda ta gani a rubuce, inda akayi sa'a mutumin ya san wajen sosae, dan haka bata sha wahala ba ya kae ta har k'ofar gidan, da taemakon kwatancen da Ayrah ta tura mata. Sauka tayi daga Napep d'in ta biya shi kud'in sa sannan ta k'arasa tayi knocking gate d'in dake a rufe. Da mamaki Ayrah dake zaune a cikin d'akin ta ta sake kasa kunne dan tabbatar da knocking d'in da take ji, a iya sanin ta shi kad'ae ke shigowa cikin gidan, bayan shi babu wani dake shigowa, shi kuma idan yazo se dae kawae taga shigowar shi, to amma kuma yau se gashi taji ana knocking, kamar ta share se kuma ta mik'e dama da hijab a jikin ta ta fito, a hankali ta cigaba da takawa zuwa compound d'in gidan har zuwa sanda ta isa dab da gate d'in sannan ta tsaya "Waye?" ta fad'a a hankali cike da d'an tsoro tsoro, jin muryar ta ya sanya Bahijja sakin murmushi ganin ba tayi 6ata ba "Ni ce, Bahijja ce" ta fad'a dan ta k'agu Ayrahn ta bud'e k'ofar, seda ta saki ajiyar zuciya sannan ta saka hannu ta bud'e k'ofar, murmushi ne ya

End of Chapter 54Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next