Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel

Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel

Author: Hafsat Bature
Chapter 1 of 86
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 Reading now Chapter 2 1,678 words Chapter 3 1,646 words Chapter 4 1,464 words Chapter 5 1,676 words Chapter 6 1,670 words Chapter 7 1,657 words Chapter 8 1,695 words Chapter 9 1,675 words Chapter 10 1,629 words Chapter 11 1,656 words Chapter 12 1,614 words Chapter 13 1,684 words Chapter 14 1,090 words Chapter 15 692 words Chapter 16 1,565 words Chapter 17 1,105 words Chapter 18 1,914 words Chapter 19 78 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 923 words Chapter 22 1,350 words Chapter 23 1,543 words Chapter 24 1,402 words Chapter 25 1,465 words Chapter 26 1,722 words Chapter 27 1,031 words Chapter 28 1,561 words Chapter 29 1,678 words Chapter 30 852 words Chapter 31 1,504 words Chapter 32 705 words Chapter 33 1,623 words Chapter 34 1,205 words Chapter 35 1,234 words Chapter 36 1,638 words Chapter 37 1,675 words Chapter 38 1,681 words Chapter 39 1,653 words Chapter 40 1,124 words Chapter 41 1,691 words Chapter 42 1,691 words Chapter 43 1,648 words Chapter 44 1,460 words Chapter 45 1,259 words Chapter 46 1,319 words Chapter 47 1,979 words Chapter 48 2,219 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,657 words Chapter 51 1,643 words Chapter 52 1,565 words Chapter 53 1,696 words Chapter 54 1,689 words Chapter 55 1,693 words Chapter 56 484 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 831 words Chapter 59 1,546 words Chapter 60 1,496 words Chapter 61 1,168 words Chapter 62 2,181 words Chapter 63 1,641 words Chapter 64 303 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 743 words Chapter 67 1,672 words Chapter 68 1,355 words Chapter 69 1,582 words Chapter 70 1,076 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,235 words Chapter 73 2,302 words Chapter 74 1,326 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 671 words Chapter 77 1,685 words Chapter 78 1,524 words Chapter 79 1,616 words Chapter 80 1,696 words Chapter 81 1,666 words Chapter 82 1,651 words Chapter 83 1,650 words Chapter 84 1,526 words Chapter 85 1,658 words Chapter 86 1,487 words

💖💖💖💖
💖💖💖
💖💖
💖 *ABBAN SOJOJI* 💖
💖💖
💖💖💖
💖💖💖💖

```The father Of Soldiers```

Story
&
Written
by
*_Hafsat Bature_*
~(Boss Lady)~

Dedicated to my beloved sisters. 😍

Special thanks to Fadeela Lamido & Sadeeq Abubakar. Wannan littafin sadaukarwa ne a gare ku, jinjina ta musamman.

Proud Of My First Novel💋

Warning banyarda wani yayi amfani da wani sashe na littafina ba, kada a ta6amin komai na littafina in kuma mutun yayi shi da Ubangiji 😇

Sa'an kada ki karanta Littafin nan in har yakasance lokacin Sallah ne !!! ko kuma lokacin da iyayenki suka saki aiki ko mijinki, in har kikayi hakan wlh ke zata shafa 👌

*Page 1-2*

Hannu tasa ta toshe kunnenta saboda ta gaji da jin masifar da Buzun maigadin yake ta surfa mata, "Ke wannan idan mayya ce kika kama mutun wallahi sai an yi da kyar za a samu magani."

"Na she miki hajiya ba ta nan kullum sai kin zo, ba ki da zuciya ne kare ya lashe ko? Yarinya karama da ke sai taurin kan tsiya, da wasu kwala-kwalan idonki kamar na kwarton mazuru, kina kallon mutane da su ba kunya ko? Kai ga d'an iska!"

Dagowa ta yi a hankali tana kallon sa jin cin mutuncin da yake yi mata , idonta ne suka ciko taf da kwalla, kananun labbanta suka soma kyarma, tuni yanayin fuskarta ya canza.
Duk a tunaninsa yarinyar za ta mayar masa da martani saboda ya san yaran zamanin nan ba ka taba su su yi maka shiru, zuba mata ido ya yi kuri yana kallon ta. Gani ya yi tana ja da baya a tunaninsa tafiya za ta yi tabar wurin amma sai ta samu wuri a jikin bangon gidan ta tsugunna tare da kifa kanta a saman guiwowinta sannan ta soma rera kuka mai tsuma zuciya.

Tsayawa ya yi yana kallon ta, da alamun nadama a tattare da shi, har cikin zuciyarsa yake jin bai kyauta mata ba, yana Musulmi da shi ya gaza fahimtar yar karamar yarinyar da ke zarya kullum a bakin gate din gidan, bai taba tambayar kansa dalilin da yasa yarinyar take zuwa wurin ba. Ba irin korar karen da bai yi mata ba amma hakan bai sa gobe taki dawowa ba.

Jiki a sanyaye ya matsa inda take ya tsugunna a gabanta ya ce, "Kai kukan ya isa haka! Dago ka gaya mini mene ke damun ka me yasa kake zuwa kullum kana neman hajiya?"

Dagowa ta yi fuskar nan ta yi jaga-jaga da hawaye ga majina cikin shesshekar kuka ta ce, "Ina zuwa neman hajiya ne saboda na ji an ce tana taimakon 'yammata ta sama masu aikatau ana biyan su kudi."

Jim ya yi yana kallon ta kafin ya ce, "Kai ko mai yasa kake neman aiki karamin yaro da kai gidanku ba manya ne?"

Girgiza kai ta yi, "A'a babu kowa, ba mu da kowa, ni da 'yan uwana ne kuma ba su da lafiya an kwantar da su a asibiti, kuna likita ya ce aiki za a yi musu, ba ni da kudin aikin saboda suna dayawa, shi ne nake so na samu aikin da zan yi ina samun kudin da zan tara a ayi musu aiki kada su mutu su bar ni ni kadai!" Karasa maganar ta yi tare da mayar da kanta kasa tana kuka.

Yanzu ya gane dalilin da yasa yarinyar ta nace sai taga hajiyar, a cikin zuciyarsa ya ce, "Baiwar Allah tana shikin damuwa karama da ita. Oh amma yana da tunani mai kyau!"

Riko hannunta ya yi tare da cewa, "Share hawayen ya isa haka, zan taimaka maka ka ga Hajiya, taso mu je ka zauna saman benchi ka ji."

Mike wa ta yi ta bisa, a tare suka zauna saman bencin, jim suka yi na d'an wani lokaci kafin ya ce, "Ka yi shiru kaji ka daina kuka Allah shi ne gatan bawanSa ko mutun bai da kowa indai ya yi imani da Allah shi ne zai zama gatansa, ka shi gaba da addu'a 'yan uwanka za su samu sauki har ku yi wasa da su."

Murmushi ta yi saboda ta ji dadin maganarsa, hannu ya kai ya dauko ruwan bunun da yake dafawa a saman 'yar butarsa, dama akwai karamin kofi guda biyu da yake amfani da su wurin zuba shayin.
Lekensa ta dinga yi tana kallon 'yar butar karfen da yake dafa shayin da ita, ta burge ta musamman abin da ke cikinta. Kofin ya dauko ya tsiyaya mata a ciki, mika mata ya yi. Hannu biyu ta sa ta karba don rabon ta da ta ci wani abu a cikin ta tun jiya. Sannan shi ma ya zuba wa kansa a d'ayan kofin yana kurba yana ba ta labarin gizo da koki.

Sam ba ta gane me yake cewa, d'an ruwan bunun da ya ba ta ya dauke mata hankali saboda dadinsa musamman daya sanya sugar a ciki, a hankali take kurbarsa, kusan so uku tana shanyewa yana kara mata, a karshe ya ce "Aradun Allah shegen ci ne da kai ga shi harka shanye mini ruwan bununa, idan hajiya ta samo maka aiki ka fara yi sai ka biya kudin shayina."

Murmushi ta saki tana sauraron shi tana mamakin yadda yake suffanta ta da namiji, ga shi shi dai ba makaho ba sarai ya gan ta da kayan mata a jikinta,
har marece ya yi hajiya ba ta dawo ba, da lokacin sallar Azahar ya yi da kansa ya bude musu kofar dake a jikin gate din suka shiga. Ruwa ya debo musu a buta, suka yi alwala tare sannan ya shimfida musu tabarma, shi ya ja su sallar yana gaba tana daga bayansa.
Bayan sun gama , suka ci gaba da zama a saman sallayar yana jan cazbi a hannunsa ita kuma ta shiga tunanin duniya, a haka har La'asar ta yi suka sake kabbara sallar, tun kafin su sallame yake jin karar motar hajiya alamar ta iso.

Dadi har cikin ranta yau dai Allah ya yi za ta gana da hajiyar nan, yana sallame sallar da sauri ya tashi ya bude mata kofa, ta shigo da dankareriyar motarta, wucewa ta yi da motar zuwa wajen ajiya. Zuge kofar ya yi sannan ya bi motar hajiyar a baya yana mata kirari kamar yadda ya saba.

Farinciki ya sa ta kasa rufe bakinta sai faman murmushi take yi, ba ta tashi daga samman sallayar ba, zama ta yi tana jiran maigadin ya yi wa hajiyar maganarta. Bude mata motar ya yi ta fito, ma sha Allah irin matan nan ne masu jiki 'yar dumurmur da ita, ta ji hutu fara ce tas amma da alama tana karawa da man bleaching, jikinta na sanye da tsadadden leshi shudi wanda aka yiwa ado da stones, ba karamin kyau ya yi mata ba. Ta kashe daurin kallabinta, hannunta na sanye da diamond rings, haka sarkar wuyanta ta diamond ce, kwalliya ce sama-sama a fuskarta tana da dara-daran idanu ga hanci dogo, tubarkalla, sai jan-baki da ta shafa ja ne.

Cikin girmamawa ya ce, "Barka da isowa hajjaju makkatu!"

Ya mutsa fuska ta yi da alamun gajiya a tare da ita ta ce, "Yawwa Aku sarkin dumi akwai wanda ya zo ba na nan?" Ta yi maganar ne a yayin da take bude kofar motar ta baya, saboda ba ita kadai ta zo ba akwai 'yammatan da ta zo da su daga kyauye.

Maigadin ya amsa mata da cewa "E mutane sun zo sosai amma duk ban rike shunansu ba na dai ce musu ba ki nan kin yi tafiya, sai dai akwai yaro d'aya da ya zo neman ki kullum shai ya zo yau dai na ce mashi ya jira ki dawo."

D'aga idonta ta yi tana hangen 'yar yarinyar da ke sanye da hijab saman sallaya, mayar da idonta ta yi kan 'yammatan da ke zaune cikin motar, ganin ta bude musu motar amma sun ki fitowa, tsaki ta ja tare da cewa, "Kwana za ku yi ne a cikin motar?"

Washe baki su ka yi wata mai surutu a cikinsu ta ce, "Hajiya wallahi dadi motar nan ga wani sanyi da ke ratsa zuciyata kamar kada na fito."

Girgiza kai hajiyar ta yi tare da sakin guntun murmushi ta ce, "Ai irin wannan sanyin da kuke sha na A.C ne kuma in mun shiga ciki ma akwai A.C ko ina."

Cike da jin dadi suka fito daga motar su biyar ne, kai ka ce wadanda aka kwato ne daga bakin kura kayansu sun yi uban squeezing, ga shi riga daban zane daban dankwali daban, takalman kafafuwansu wari da wari ne, ga wata irin kwalliya da suka dambara a fuskarsu, janbaki ya sauka daga saman labbansu har kumatunsu, kamar wasu mayu. Ga black point din da suka diddiga a hancinsu har izuwa goshinsu, sai faman soshe-soshen kai suke.

A haka take dauko su daga kauyen kayau ta gyara su ta sama masu gidanje aiki, a nan take samun kasonta ita ma.
Kallon buzun ta yi ta ce "Ka shigo mini da yarinyar."

Sannan ta kalli 'yammatan ta ce "Mu shiga ciki amma kusa ni duk wacce ta yi mini hauka kauyensu zan mayar da ita ta je can ta ci gaba da tallar fura a bakin kasuwa."

Cikin falo ta shiga da su a daidai lokacin ita ma yarinyar ta biyo su, nan fa suka fara kalle-kalle ganin yadda wurin ya hadu, har kokawa suke yi wurin yunkurin hawa saman lumbutsa-lumtsan kujerun da ke a ciki, dakatar da su ta yi ta hanyar yi musu tsawa, "Kul! Kada wacce ta hau mini saman kujeruna, ga carpet nan shimfide ku zauna, haba ku rinka abu irin na mata mana."

Nutsuwa suka yi kowacce ta samu wuri ta zauna, ita da ma ba iri su ba ce da wayewarta wuri ta samu ta zauna ita kadai, yayin da su kuma suka cunkushe wuri daya kamar kifin gwangwani. Shiga ciki hajiyar ta yi tana kwalama mai aikin ta kira, "Larai, larai! Ina kika shiga haka gida sai ka ce ba kowa?" Karasowa ta yi tana hamma alamun daga barci ta tashi.

"Sannu da dawowa hajiya, wallahi barci ne ya yi awon gaba da ni da ma na sha maganin mura saboda ta takura mini."

End of Chapter 1Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Login to Save Next