Soyayyanovels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel

Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel

Author: Hafsat Bature
Chapter 47 of 86
About 9 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,694 words Chapter 2 1,678 words Chapter 3 1,646 words Chapter 4 1,464 words Chapter 5 1,676 words Chapter 6 1,670 words Chapter 7 1,657 words Chapter 8 1,695 words Chapter 9 1,675 words Chapter 10 1,629 words Chapter 11 1,656 words Chapter 12 1,614 words Chapter 13 1,684 words Chapter 14 1,090 words Chapter 15 692 words Chapter 16 1,565 words Chapter 17 1,105 words Chapter 18 1,914 words Chapter 19 78 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 923 words Chapter 22 1,350 words Chapter 23 1,543 words Chapter 24 1,402 words Chapter 25 1,465 words Chapter 26 1,722 words Chapter 27 1,031 words Chapter 28 1,561 words Chapter 29 1,678 words Chapter 30 852 words Chapter 31 1,504 words Chapter 32 705 words Chapter 33 1,623 words Chapter 34 1,205 words Chapter 35 1,234 words Chapter 36 1,638 words Chapter 37 1,675 words Chapter 38 1,681 words Chapter 39 1,653 words Chapter 40 1,124 words Chapter 41 1,691 words Chapter 42 1,691 words Chapter 43 1,648 words Chapter 44 1,460 words Chapter 45 1,259 words Chapter 46 1,319 words Chapter 47 Reading now Chapter 48 2,219 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,657 words Chapter 51 1,643 words Chapter 52 1,565 words Chapter 53 1,696 words Chapter 54 1,689 words Chapter 55 1,693 words Chapter 56 484 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 831 words Chapter 59 1,546 words Chapter 60 1,496 words Chapter 61 1,168 words Chapter 62 2,181 words Chapter 63 1,641 words Chapter 64 303 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 743 words Chapter 67 1,672 words Chapter 68 1,355 words Chapter 69 1,582 words Chapter 70 1,076 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,235 words Chapter 73 2,302 words Chapter 74 1,326 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 671 words Chapter 77 1,685 words Chapter 78 1,524 words Chapter 79 1,616 words Chapter 80 1,696 words Chapter 81 1,666 words Chapter 82 1,651 words Chapter 83 1,650 words Chapter 84 1,526 words Chapter 85 1,658 words Chapter 86 1,487 words

Sehrish dake a tsorace jiki na rawa ta lallaba ta taso, daga ita sai yar shirt wadda takai mata dai dai guiwa, ba dogon wando jikinta, sai santala santalan kafafuwanta,
Jikin window ta karasa tasa hands dinta dake ta faman kerma ta janye labulen tare da zuge glass din windown, zuba ido tayi tana hangen Zugar sojojin dake a cikin gidan kai kace yaki ne ya taso,
A hankali take lumshe idonta tare da budesu tana kare wa mutanen dake wurin kallo, sam sojojin da sukayi masu kawanya basu bari tagansu ba,
Sai da soldiers din suka dare biyu tare da bude masu hanya sannan sehrish ta samu damar hangensu, Marshal omar ne a gaba sai Mg osman a bayansa sai Captain adams ne, a hankali take kallonsu a ranta tana fadin "wanene babban yaya acikinsu, inaji araina cewa tabbas shine ya dawo,"
Bata idasa tunaninta ba eye balls dinta suka sauka akanshi, kasancewar duk yafi su tsayi nesa ba kusa ba, Allah yayi mishi tsayi, sumar kansa ce tafara hangowa wadda ke kwance luf a bayansa da gefen forehead dinsa, zuciyarta ta dinga ji tana mata wani irin mugun bugu, bata da tabbacin cewa shine, amma ba karamin razana tayi ba da irin kyansa, duk da bata samu damar ganinsa da kyau ba, amma irinsu ko daga nesa ana shaida kyansu, kamar tauraro haka yazama acikin taurari 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
duk yadda sehrish taso ta kare ma wannan da ta hango daga nesa kallo hakan baiyu ba, bakomai take tunawa ba sai wannan hoton na cikin wayar junaid datake yawan gani, tabbas wannan shine na cikin wayar wato BABBAN YAYA,"
zuge glass din tayi tare da janyo curtains din ta rufe, murmushi kawai take sakarwa kanta tare da ajiyar zuciya at same time,
Tarasa ina zata sa kanta don farin ciki, sai faman sakin fara'a take kamar wacce aka ma Albishir da gidan Aljanna 😂
Tarasa tsaye tarasa zaune tarasa ina zata tsoma ranta, tsilli tsilli haka take yawo da yan kafafuwanta cikin room din nata,
A can ciki kuwa lokacin da suka shigo, hankalin Amani ba karamin tashi yayi ba ✨✨✨✨•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·
_Warning ❗❗❗ko da gigin wasa banyarda wani ya ta6amin littafine ba kamar canza wani sashe na labarin nan ba , ko haɗa document ko makamancinsu, in hakan ta faru kuma wlh mutun bazai ji da daɗi ba, duk inda yake a faɗin duniyar za'a samomin shi koda aljani ne ba mutun ba_😡

*page 59 to 60*

A can ciki kuwa lokacin da suka shigo, hankalin Amani ba karamin tashi yayi ba data fara cin karo da marshal omar, duk tabi ta zuzuce, a hankali tace ma aunty babba wadda ke kusa da ita a tsaye tace "Shine "? girgiza kai aunty babba tayi tare da cewa "wannan Shine marshal omar, ki zuba ido kawai bama saina fada maki gashi ba kina ganinsa zaki gane sa da kanki,"
tun kan Amani tace wani abu Babban yaya ya shigo cike da wannan tafiyar tashi ta Qasaita, wani irin bugu taji zuciyarta tayi juyawa tasake yi ta kalli aunty babba wadda idonta ke akansa ko kyaftawa basuyi,
Cikin tsantsar farin ciki kanal yusif yayi sauri zai hugging din omar, dakatar tashi omar yayi da cewa "bari na fara kwasar Albarka wurin Abbana tukunna," murmushi su kayi gaba dayansu especially Abban nasu, karasawa yayi tare da rungume abban nasu, so tightly hannu abban yasa yana bubbuga bayansa yace "I really really missed u my guys" omar yace "i missed u too my daddy,'
Mg osman kam wurin su Bg abuhaisam ya karasa suka shiga rungume juna ana ta faman gaishe gaishe, bayan omar ya gama da abbansu ya koma yana rungume sauran,
gaba daya idon abbansu ya koma kan Rafayet wadda ko kallo bai ishe su ba, kawai bedroom dinsa yake kokarin tunkara,
Cikin sauri bg abuhaisam yace "kai ina zuwa........? dakatar dashi abban yayi daga yi masa magana, kowa binsa da ido yayi,
Cikin sauri junaid ya shiga gabansa don ya riga sa isa sbd key din na hannunsa, can upstairs katafaren bedroom dinsa yake mai hade da palour, Aljannar duniya ce aka shimfida,
tunkan ya karaso Junaid ya bude masa, ya shige ciki, an kawata shi sosai sehrish ce zata fada mana ya haduwarsa yake, 😝
"Amma abba anya Rafayet bai fara shaye-shaye ba? Kalli yadda yabi ta gabanmu ko kallo babu, atlease ko kai ae ya kamata ya tsaya ya gaisar ko,"? abuhaisam ne yayi maganar ransa ya baci sosai,
Aunty azeema tace "kada ku damu indai rafayet ne dakansa zai fito,"
Zama su kayi a saman royal sofas din suna kara gaggaisawa da juna, hankalin Omar bai kwanta ba da yanayin abban nasu, kuma yasan duk akan babban yayan ne, ya kwalfa rai akansa yasaran daya shigo shi zai fara runguma amma sai yaga akasin hakan,
Aunty azmee ce ta shigo musu da abunsha itama da fara'a a fuskarta, tabi su tana musu sannu da zuwa, tare da mika musu abun sha,
Cikin rashi kwarin jiki abban nasu yace "am really glad to see you, ina godiya ga Allah daya dawo mun daku lpy, amma nayi mamakin jin cewa tare da su Omar zaku zo ina ABUSUFYAN din?
Captain adams ne ya bashi amsa da cewa "daga can wurinshi muka wuce us sbd mu tafo atare," jinjina kai abban nasu yayi tare da cewa "hakan yayi kyau,'
"Nima naji dadin ganin ku sosai, dalilin dayasa na tsaya nace dole saina ga ya'yana,' murmushi su kayi jin abun da aunty azeema tace,
"Muna tayaku murnar dawowa cikin koshin lpy ni da yar uwata Amani,' aunty babba ce tayi maganar, mg Osman yace "munji dadin ganin ku gaba daya, Allah yabar zumunci," suka amsa da ameen,
Idon aunty azeema nakan abba wanda jikinsa ke kerma zuciyar ta motsa, jiki ba kwari ya mike tsaye tare da cewa "yakamata ku shiga ciki ku huta, zuwa anjima, nima bari naje ciki,'
Cikin sauri ya wuce room dinsa, da hanzari aunty azeema tabisa,
Yana shiga ciki gaban mirror ya tsaya, idonsa sunyi jawur ransa yayi mugun baci,
Shigowa tayi tana fadin "haba yaya Hussein meyasa ?, duk don sbd da abun da Rafayet yayi yasa ka shiga wannan halin,"
Juyowa yayi muryarsa na rawa tamkar zai yi kuka yace "meyasa zaimun haka ? gaba daya na kwallafa rai akansa, yaushe rabon dana sa shi a ido na? Amma yadawo shine ko kallona baiyi ba? meyasa yake son azabtar dani ne da soyayyarsa kamar yadda mahaifiyarsa tayi mun !? yayi mgnr ne tamkar zaiyi kuka,
(Dama ko acikin gida dan banza yafi shiga rai 😂)
Cikin sanyin murya Aunty azeema tace "Am sorry yaya na, kamar yadda kke son ganinsa shima haka yakeson ganin ka, ni na tabbata akwai dalilin hakan, u shouldn't worry ur seft abt him, "
dagawo su kayi jin tura kopa, marshal omar ne ya shigo, yabiyo abbansu ne sbd shima ya lura da halin daya shiga,
Karasawa yayi inda suke yana cewa "daddy duk akan rafayet ne wannan ? Amma kasancewa sarai ba haka yake maka ba, rafayet bfr mu shiga jirgi yayi ma kansa allura, sbd aikin dayasha kasan yadda yake kamar enjine baya gajiya da aiki, allurar ce bata sake shi ba, just calm dowm ur mind dakansa zai zo ya same ka,in ya samu natsuwa"
ajiyar zuciya abban yasaki jin abunda omar ya sanar dashi, har yaji sanyi aransa,
Murmushi aunty azeema tasaki tare da cewa "ynx hankali ya kwanta ko, zamu iya komawa ciki ko ? Murmushi shima yasaki atare suka fito,
Yinin ranar gidan ya cika fam saboda zuwan SGR Da Marshal omar, mutane kamar kyankyasai sai bullowa suke yi abokanan arziki da kuma yan uwa, da sauransu hada su karare irinsu Hafsat bature yan shisshigi gayya soɗi, 😥
Duk wannan budurin da ake yi Babban yayan na can ciki a hakimce, yana sharar bacci cikin natsuwa, gashi kowa tambayarsa yake yi ina Babban yaya, Ina Sgr, ina rafayet amma shiru, ba wanda yayi attempting zuwa ya tashe shi saboda ba wanda ya isa ya tashe shi yana bacci, mutun yaji naushi alkur'an 😂
Dole fa sehrish ta fito aiki yayiwa azmee yawa, don haka tunkan ma azmeen ta buÉ—e ta, tayi gaggawar zura dogon wandonta, ta gyaggyara kanta da gashin bakinta,
kamar barauniya haka ta fito, tana tafiya cikin sanÉ—a ta tsorata da yawan mutanen da tagani, gasu nan bakake da farare kowa dai masha Allah,
Bama wanda ya lura da ita, direct kitchen ta wuce, abun ya bata mamaki ganin junaid tsaye aciki aunty azmee ta jera masa abunsha a tray cikin cups , alamar cewa hada shi ke taimaka mata wurin share ɗinsa wa bakin, saukin kan junaid na bata mamaki he'a so Special 😍
Jikinsa na sanye da t shirt red colour sai trouser black colour, abun ba'a magana,
Sallama tayi ta shiga da murmushi a face dinsa ya dago yana kallonta, itama kawai saita tsinci kanta da sakar masa murmushi,
"Sannunku da aiki aunty azmee, am so sorry ban samu fitowa da wuri ba, because of sleepless night shiyasan ya,' ta faÉ—i tana wasa da yatsun hannunta,
"Babu komai ae, ga Junaid nan yana tayani, tun da ynx kin fito sai mu fara shirin lunch, tunkan time ya kure mana,"
karasawa tayi gaban junaid tare da kai hannu ta rike tray din dake a hannunsa tace "Bari naje na kai musu,"
"A'a ki barshi kawai, zan kai" ya bata amsa cikin sanyin murya,
"A'a bai dace ace É—an masu gida yana aikin daya dace ace Æ´an aiki ke yi ba,"
ta faÉ—i tana kokarin janye tray din daga hannunsa,
"Ae ni nace zan iya just leave me to do it ba wani aiki bane mai wahala kawai kaiwa zanyi,"
"A'a ni dai kabarshi pls zan yi tunda nazo"
Zuba musu ido Aunty azmee tayi baƙaramin burgeta su kayi ba,
"Kun ga ya isa haka, junaid ka bashi yakai musu kaje ciki nasan anata neman ka,"
kallon ta yayi suka haÉ—a ido, ya É—an murguÉ—a mata baki kafin yabi ta side dinta ya wuce, ajiyar zuciya ta saki,
Idasa jera mata drinks din azmi tayi sannan ta juya tashiga ciki zuciyarta na bugawa tsoranta kada ta ci karo da Babban yayan nasu, duk da har ynz bata shaida shi ba,
Haka Sehrish ta shiga zarya cikin manyan bakin nan tana miƙa wa kowannansu abunsha, tun tana yi cikin daɗin rai har tafara fidda gumin gajiya, bayan ta kammala suka shiga aikace aikace a kitchen na preparing Lunch,
Lokaci guda kamshi ya gauraye ko'ina, girki na musamman suka shiga yi, abinci iri iri, namu dana kasashen waje, musamman sbd Babban yaya bakowane kalar abinci yake ci ba, sai an tabbatar da tsaftar maiyinsa da kuma amfaninsa a lafiyar jikin mutun,"
Dama azmee ce ke masu girkin sun saba da delicious dinta, sbd sun shaida kwarewarta, da kuma tsaftarta da lafiyar abincin ta,
tana lura da duk wani motsin sehrish wani murmushi data ga tana saki kamar gonar auduga, cikin nishaÉ—i take aikinta, zumudin son ganinsa take,
mutane sun rage sosai ya raga saura mu na cikin gida kawai, su marshal omar sun samu damar shiga cikin rooms dinsu domin hutawa,
Aunty babba da Amani sun shige cikin daki baki cike da gulma, tsaitsaye su kayi,
"Wai dama haka Babban yayan yake ? Ya ilahi aunty ya hada komai da nake bukata ajikin É—a namiji meyasa tun farko baki haÉ—a ni dashi ba sai Abbas"?
Murmushi aunty babba tasaki kafin tace "idan kura na maganin zawo tafara yiwa kanta mana ! Kinsan irin haukan da nayi at the first day dana fara sashi a eyes É—ina, Allah sai da nayi regretting auran Ishaq, Rafayet shine irin namijin da nake kwaÉ—ayin samu ! Amma kaddara ta riga fata,"
Jinjina kai Amani tayi tana kallon auntyn tata, acikin zuciyarta tana tunanin meyasa bata haÉ—a ta da babban yayan ba ko marshal omar, Amma take yi wa Hayaam tanadinsa, kodan ta kasance ita shakikiyarta ce?

End of Chapter 47Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next