Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel

Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel

Author: Hafsat Bature
Chapter 52 of 86
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,694 words Chapter 2 1,678 words Chapter 3 1,646 words Chapter 4 1,464 words Chapter 5 1,676 words Chapter 6 1,670 words Chapter 7 1,657 words Chapter 8 1,695 words Chapter 9 1,675 words Chapter 10 1,629 words Chapter 11 1,656 words Chapter 12 1,614 words Chapter 13 1,684 words Chapter 14 1,090 words Chapter 15 692 words Chapter 16 1,565 words Chapter 17 1,105 words Chapter 18 1,914 words Chapter 19 78 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 923 words Chapter 22 1,350 words Chapter 23 1,543 words Chapter 24 1,402 words Chapter 25 1,465 words Chapter 26 1,722 words Chapter 27 1,031 words Chapter 28 1,561 words Chapter 29 1,678 words Chapter 30 852 words Chapter 31 1,504 words Chapter 32 705 words Chapter 33 1,623 words Chapter 34 1,205 words Chapter 35 1,234 words Chapter 36 1,638 words Chapter 37 1,675 words Chapter 38 1,681 words Chapter 39 1,653 words Chapter 40 1,124 words Chapter 41 1,691 words Chapter 42 1,691 words Chapter 43 1,648 words Chapter 44 1,460 words Chapter 45 1,259 words Chapter 46 1,319 words Chapter 47 1,979 words Chapter 48 2,219 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,657 words Chapter 51 1,643 words Chapter 52 Reading now Chapter 53 1,696 words Chapter 54 1,689 words Chapter 55 1,693 words Chapter 56 484 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 831 words Chapter 59 1,546 words Chapter 60 1,496 words Chapter 61 1,168 words Chapter 62 2,181 words Chapter 63 1,641 words Chapter 64 303 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 743 words Chapter 67 1,672 words Chapter 68 1,355 words Chapter 69 1,582 words Chapter 70 1,076 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,235 words Chapter 73 2,302 words Chapter 74 1,326 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 671 words Chapter 77 1,685 words Chapter 78 1,524 words Chapter 79 1,616 words Chapter 80 1,696 words Chapter 81 1,666 words Chapter 82 1,651 words Chapter 83 1,650 words Chapter 84 1,526 words Chapter 85 1,658 words Chapter 86 1,487 words

Wuri suka samu asamn garden chairs ɗin suka zauna auna facing juna, bin ta da kallo azmee tayi ganin tana ta faman murmushi, wato bakomai sehrish ke tunani ba fa ce ranar da zasu fara magana da baban yaya harsu shaku ssae su rinka zuwa garden ɗinnan atare suna kewaya wa, lumshe idonta tayi sbd wata iska da ta ratsa ta, aranta tana cewa "Ya Allah ka nunamin wannan ranar da raina da lafiya ta, ni da shi atare muna strolling Cikin farin ciki," 😥

"Me ki ke tunani ne"? Firgit sehrish ta yi jin maganar azmee a dodon kunnanta , cikin sauri tace "bakomai kawai ina mamakin haÉ—uwar gidan nan kamar a mafarki,"
Murmushi azmee tayi sbd sarai ranta ya bata cewa, tunanin ta na babban yaya ne,'

"Estate za'a mai dashi" cikin mamaki sehrish ta ce "dagaske aunty azmee? Amma zai fi kyau wlh girman yayi yawa,"
Azmee ta ce "eh naji da jima wa abbansu ya faɗi cewa za'a ƙara wasu part ɗin, yana so zai ware ma kowannansu nasa saboda baison in sunyi aure suyi nesa dashi, yace duk wanda yayi aure zai dawo ciki da matarsa, duk da sun mallaki gidajensu nakansu, amma shi yafi son hakan,"
Wani daɗi ne ya rufe sehrish, kamar anyi mata albishirin cewa itama zata kasance ɗaya daga cikin surukansa da zasu zauna agidan, 😒
Bayan sun É—anyi shiru na wani lokaci azmee tace "i have something to discuss wit u,'
"Menene aunty azmee" sehrish ta tambaya da É—an mamaki a fuskarta,
"Ko kinsan cewa a cikin sojojin gidan nan akwai wanda yasan cewa ke maca ce ba namiji ba !!"
A firgice sehrish ta mike hannu dafe da kirji tace "Who"? fuskarta da tsananin tsoro,
Dariya azmee tayi kafin tace " zan faɗa miki but firstly ina so ki mun alƙawarin cewa u will calm urself,"
Jiki a sanyaye ta koma ta zauna zuciyarta na bugu, tsoranta kar ace cikin jarababbun ne wato Fawan ko Twins,

"Aunty azmee wanene dan Allah.. .." tayi maganar tana haÉ—iye yawu,
Murmushi azmee tayi kafin tace "king of smile"
"Wanene haka azmee"? Ta tamvaya da mamaki,
"Oh baki gane ba tom nabaki satar amsa kije ki gano waya dace da sunan,'
duk iya tunanin sehrish bata gano wa azmee take nufi da *King of smile* ba, takasa samun natsuwa ta gano sa, sun jima suna fira bfr su koma ciki donyin sallar La'asar,
*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

~🔥the father of soldierd🔥~?

💋💋💋💋💋💋💋💋
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ
ﺭﺍﻓﻴﺖ💞💞💞💞💞

ﻗﺼﺔ ﻛﺘﺒﻬﺎ ﺣﻔﺼﺔ ﺑﺎﺗﻮﺭ🌹🌹

_Story & written by_

*Hafsat Bature Moh'd*

~BossLady~ 💋

*page 68*

..........SEHRISH...........................
bayan ta kammala sallar la'asar, kimtsawa tayi kafin ta fito ta wuce kitchen tayi mamakin jin shiru alamun duk sun fita ne, tunanin ta ko'ina Babban yaya ya ke, ta lura baya fita sai dai azo a same shi in da ya ke, tun kafin azmee ta iso, sehrish ta fara É—auko abubuwan da zasu yi amfani dashi, doya ta fara ferewa tasan suna yawan amfani da ita, tana aiki tana É—an murmushi, sa6anin da tana aiki cikin damuwa saboda tunanin halin dasu Hosana da Jahad su ke ciki, zuwan big bro ya canzawa sehrish rayuwa gaba É—aya,

Sam bata ji shigowar azmee ba, sai dae muryarta taji "Sannu da ƙoƙari rishi hakan ya burgeni,"
murmushi sehrish tasaki tare da cewa "Yawwa aunty azmee ina wurina,"
"Lafiya lou ta faɗi tare da shige wa ciki domin fara gudanar da aiki, cikin lokaci ƙankani kitchen ɗin ya fara kamshin abinci,

"Wani kalar abinci ki ka fi so"? Azmee ce ta jefa mata wannan tambayar yayin da ta ke zuba kayan ƙamshi acikin sauce ɗin da ɗaura, sehrish tace "farar shinkafa da jar miya ina son abincin nan sosai aduk lokacin da akayi mana shi a gida zumuɗi muke yi kamar hauka saboda muna jimawa bamu ci ba, shine abinci mafi daɗi a wurin mu," ta karasa maganar muryarta a sanyaye ba don komai ba sai don tuna wa da hosana, a lokacin da su ke tare da mahaifiyarsu duk in akayi musu tuwo tafi kowa mita ta rinƙa sababi tana cewa "oumma wai mu kullum tuwo kullum tuwo, da rana ayi tuwo, da daddare ma tuwo, in safe tayi ma ɗumamen tuwo, ni wlh nagaji zanje gidan makwabciya in ciyo shinkafa da jar miya hada ma wasilla zata samun, "

Hawaye ne suka soma koƙarin zubowa a fuskar sehrish tunawa da rayuwarsu ta baya,

"Ni kuma nafison Tuwo arayuwata miyar ku6ewa da busasshen kifi wayyo daÉ—i in inaji kunne na har motsi ya keyi, musamman in ya kasance É—umame ne,"

Azmee sai zuba ta keyi sam bata lura da sehrish ba wadda, take matsalar kwalla, jin shesshekar kukanta yasa azmee saurin ƙarasowa inda take tana faɗin "subhanallahi sehrish meke faruwa ne ? Cikin sauri sehrish ta dai dai ta natsuwarta,
Murya na rawa tace "ba komai aunty azmee, zafin albasar da nake yankawa ne, ya shiga ido na,'
"Eyyah sannu barshi na ƙarasa kawai,"
"A'a aunty azmee aikin zaiyi miki yawa, zan idasa,'
"Sehrish akwai ayyuka dayawa ba dole sai wannan ba, kibarmun yankar albasar ki kula da miyar dana É—aura,"
"Shikenan aunty azmee amma kafin nan, ayimun uziri zan shiga toilet,"
"Shikenan ba damuwa kije kawai,"

Cikin sauri sehrish ta fice, saboda tana so tasamu space ta matse hawayen dake son zubo mata, tana shiga bedroom É—inta, ta fashe da matsanancin kuka, a gefen gado tazauna tana matse hawaye,
Cikin murya kuka tace "Ya' Allah ka karemun ƴan uwana, aduk inda su ke, ka sauƙaƙawa rayuwarsa, Hosana da jahad kowane yanayi zan shiga na rayuwa duk mun daɗinsa I will neva forget about you, i will keep praying for u till d rest of my life 😭

haka ta dinga addu'o'i akansu, sai daga baya ta tuna da azmee wadda ta baro a kitchen tana aiki, cikin sauri ta shiga toilet, agaban wash basin ta tsaya, ta kunna fanfo ta wanke face É—inta sannan ta fito,

ƙarar shigowar motoci taji, a lkcn da take ƙoƙarin barin ɗakin, nata cikin sauri tadawo ta tsaya agaban window ɗin da tasaba leƙe, janyen labulen tayi ta zuge glass ɗin tana kallonsu,

Motocinsu ne a jere, bayan sunyi parking wani Soja black american gabjejan gaske, ya fito ta gaba tare da buɗe mashi mota, a hankali ya zuro kafarsa dake sanye cikin slippers ɗin *Gucci* sun hau ƙafarsa raɗau ba ƙaramin kyau su kayi masa ba, idasa fitowa ya yi zuba mishi ido sehrish tayi sam batasan time ɗin daya fita ba, ashe baya gidan,
Sanye ya ke da V-neck shirt light green color, sai dogon wando Army trouser, surar nan fa tafito raɗau bai matuƙar jan hankali, sumar kansa mai tsayin nan tasha gyara na musamman ta zubo masa abaynsa ya ɗaureta,
Ba shi kaÉ—ai bane tare da abbansu su ke, da Kanal yusif,
gaba ɗaya jikin Sehrish ya gama mutuwa, zuciyarta ta gama narkewa, tafiyarsa ma kawai abun kallo ce, ta majiya ƙarfi *Rafayet* tamkar Zaki ya ke, wanda ke mulkar namun dawa a ƙarƙashinsa,
Zuge glass ɗin window tayi, tare da cije le6enta, sam bata gajiya da kallonsa, cikin sauri ta fito ta wuce kitchen saboda tasamu damar ƙare masa kallo in sun shigo,'
"Sannu da dawowa ya idon nake"? Azmee ce tayi mata wannan tambayar,
"Alhamdulillah ae sun dawo dai dai aunty azmee," sai faman murmushi take tana Æ´an kame-kame,
Shigowa su kayi atare suna É—an ta6a fira, anan main palor É—in suka samu wuri suka zauna, abbansu na facing É—insu yayin da shi da Kanal yusif suke zaune a 3 seater,
Murmushi abbansu ya ke ta faman saki ba don komai ba sai don jin daɗin zuwan Babban yayan, musamman yau da suka yawata atare, duk da kin sakin fuskarsa da kuma ƙarancin maganarsa, _muryarsa tsada gare ta, saboda daɗinta shiyasa wata'kil ya ke rowarta_ (nace ba, da zai faɗi farashinta dana ƙulkula nasiya😂)

Hannunsa na riƙe da wayarsa, yana daddanawa, bazan faɗi ƙirar wani company bace, sbd wata irin haɗaɗɗiyar waya ce, very expensive wadda takasance mallakinsa, kuma sunan sane ajikinta wato (SGR) ba mai iya controlling ɗinta sai shi duk bala'in mutun, saboda sometimes da Voice ɗinsa take amfani, daga ya faɗi abu zata nuno masa, 😔

gyaran murya abbansu ya yi tare da cewa "Ina magana," a hankali ya É—ago da sexy blue eyes É—insa ya aza akan abban nasu tare da cewa "Am all ears,"
Abba yace "Ina so kayi mun promise É—in cewa har ka bar nigeria, bazaka ta6a kowa ba kayi shiru da bakin ka salin alin ka tafi cikin salama dan Allah,'
wani irin kallo babban yayan ya ke wa abban nasu jin abunda yace, hannu ya kai tare da ajiye phone ɗinsa saman table ɗin da ke front ɗinsa, ya jingina bayansa jikin royal sofa ɗin, tare da aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya, duk abban nasu na kallonsa burin sa ya ji amsar da zai basa,
murmushi kawai kanal yusif ya ke yi wanda ke ta faman danna wayarsa, amma kunnansa nakan maganar da suke yi,
É—an ta6e small lips É—insa ya yi kafin yace "*IMPOSSIBLE*" atakaice,
Sauke ajiyar zuciya abban yayi dama yasan amsar kenan,
Cikin takaici yace "Oh sai kayi kenan"?
"Eh" ya bashi amsa ba wasa,
Jinjina kansa yayi tare da cewa "ni narasa gane tsakanin kai da Momynka Alexandra waya fi wani taurin kai, kafiya da ji da izza,'
da buÉ—en bakin babban yaya sai cewa ya yi "Ita,"

End of Chapter 52Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next