Soyayyanovels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel

Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel

Author: Hafsat Bature
Chapter 23 of 86
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,694 words Chapter 2 1,678 words Chapter 3 1,646 words Chapter 4 1,464 words Chapter 5 1,676 words Chapter 6 1,670 words Chapter 7 1,657 words Chapter 8 1,695 words Chapter 9 1,675 words Chapter 10 1,629 words Chapter 11 1,656 words Chapter 12 1,614 words Chapter 13 1,684 words Chapter 14 1,090 words Chapter 15 692 words Chapter 16 1,565 words Chapter 17 1,105 words Chapter 18 1,914 words Chapter 19 78 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 923 words Chapter 22 1,350 words Chapter 23 Reading now Chapter 24 1,402 words Chapter 25 1,465 words Chapter 26 1,722 words Chapter 27 1,031 words Chapter 28 1,561 words Chapter 29 1,678 words Chapter 30 852 words Chapter 31 1,504 words Chapter 32 705 words Chapter 33 1,623 words Chapter 34 1,205 words Chapter 35 1,234 words Chapter 36 1,638 words Chapter 37 1,675 words Chapter 38 1,681 words Chapter 39 1,653 words Chapter 40 1,124 words Chapter 41 1,691 words Chapter 42 1,691 words Chapter 43 1,648 words Chapter 44 1,460 words Chapter 45 1,259 words Chapter 46 1,319 words Chapter 47 1,979 words Chapter 48 2,219 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,657 words Chapter 51 1,643 words Chapter 52 1,565 words Chapter 53 1,696 words Chapter 54 1,689 words Chapter 55 1,693 words Chapter 56 484 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 831 words Chapter 59 1,546 words Chapter 60 1,496 words Chapter 61 1,168 words Chapter 62 2,181 words Chapter 63 1,641 words Chapter 64 303 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 743 words Chapter 67 1,672 words Chapter 68 1,355 words Chapter 69 1,582 words Chapter 70 1,076 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,235 words Chapter 73 2,302 words Chapter 74 1,326 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 671 words Chapter 77 1,685 words Chapter 78 1,524 words Chapter 79 1,616 words Chapter 80 1,696 words Chapter 81 1,666 words Chapter 82 1,651 words Chapter 83 1,650 words Chapter 84 1,526 words Chapter 85 1,658 words Chapter 86 1,487 words

kanal yusif dai baice komai ba yau baya jin ƴ'an maganar sai dai in sunyi shiriritar tasu ya ɗan murmusa 😊
kallonsa khaleed yayi ganin yau yaƙi cewa komai don haka ya ɗanyi gyaran murya cikin zolaya ya ce "su yaya yusif ciki yana ta ɗauka ko magana babu,"
É—agowa yayi tare da É—an jefamar harara cikin sanyayyiyar muryarnan tasa yace"bana son shashanci fa, kar na sake jin wani yayi magana acikin ku"
Shiru su kayi tsit kowa ya natsu yana zubawa cikinsa,
Karar faÉ—uwar cokalin junaid ne yasa su dagowa suka kallesa, cikin sauri sehrish ta duka domin ta É—auko masa,
Zuƙunna wa tayi kasan table ɗin takai hannu zata ɗauko cokalin kenan !
Idonunta suka hango mata abunda su Twins ke yi, dayake suna facing ɗin juna shida jahaan, ƙafafunsu na maƙale dana juna sun harɗe su ,
girgiza kai tayi aranta tace"jaraba" ɗagowa tayi ta miƙa masa cokalin hararar ta yayi tare da cewa"change another spoon for me i can't use this one,"
mamaki ne ya kamata ganin inda cokalin ya faɗa a tsaftace yake, don ita ji take ko abinci za'a zuba mata a ƙasan wurin to tabbas zata sa harshe taci don ta shaida tsaftar wurin,
giɗa kai kawai tayi, ta ɗauko wani a inda suke jere ta miƙa masa, yasa hannu ya karba,
Sam ta gaza tsaida idanunta a kan wanda zata kalla cikinsu, kowa ta kalla kyau, shi dai kanal yusif wani irin sanyin kyau ne dashi ba fari bane tass wankan tarwaÉ—a ne, shi kuma khaleed tamkar É—an kasar Ethiopia, launin fatarsa yayi irin choculate É—in nan, da jabeer da irfan duk kalar fatarsu daya da yusif,
Amma in akazo wurin junaid, Ayaan da jahan da fawan farare ne tass kamar ka ta6a jini ya fito, natural white ne a tattare da junaid su twins kuma sunyi jawur, fawan kuma bai kaisu haske ba nasa mai yellow ne, dukkansu masha Allah suna da dogon hanci, ga kyawawan idanu ga kuma launin lips ɗinsu ga dimples ga kwantacciyar suma, duka dai 😇
Idonta yafi tsayawa akan junaid kallonsa take amma zahiri tunanin wayarsa take yi, har ranta bata ji daÉ—i daya canza security code É—insa ba, yanzu yaya zatayi ta kira su tsohuwa ?
É—aya bayan É—aya suka fara tashi kowa ya fi ce, wato wata irin motace jibgegiya ta sojoji idan suka hau ta, kowa sai yasan cewa Æ´an gidan Abban sojoji ne suka fito Saboda da wata irin jiniya suke janta,
Sehrish
gyara wurin ta shiga yi, ta tattara komai da sukayi amfani dashi ta wuce dasu kitchen, sai da ta wawwanke komai tsaf ta mayar dasu cikin kitchen shelves,
Sannan ta koma tana gyaggara dining table area É—in, ta tsaftace wurin sosai,
komawa tayi tana gyara babban falourn, ƴan goge-goge ƴan kakkabe kakkabe, da sauransu nan take wurin yayi tsaf, bakomai yake ƙara burgeta ba face komai nasu zaka ga launin sojoji ne (army colour) hatta teburin cin abincin da chairs ɗin dake zagaye dashi duk kafafunsu launin army ne, daga saman teble ɗin ne kawai glass,
Hatta 2 sets na royal sofa É—in dake a katafaren palourn suma army colour ne, haka sofa tables É—in duk launi É—aya, da sauran abubuwan, lallai wannan yaci ka gidan Abban sojoji.

*_Hafsat Bature_*
~(Boss Lady)~

Page 25-26

Ita kaÉ—ai take ta faman wannan aika ce aikacen saboda azmi bata jin daÉ—i headache ke damunta dama ta sanar da ita, zata sha magani ta É—an kwanta,
tunanin ta ynx yadda za ta goge waɗannan long stairs ɗin kullum wahalar su take ji, bin wurin tayi da kallo, wasu irin tagwayen bene ne masu double starcase ɗin nan, a zagaye suke, left & right , in kabi na hannun haggun zaka iya zagayo wa ka sauko ta hannun daman ka, a tsakanin su akwai space, a space ɗin nan zaka iya shiga ta tsakankanin benayen ka miƙi hanya anan zai kai ka bedrooms ɗin su Ayaan waɗan da ke a down kenan,
In kuma ka hau saman É—aya daga cikin stairs É—in zai kai ka , upstair in da ke akwai hanyoyin da zasu sada ka da jerin É—akunansu junaid, a kalla bedrooms É—in dake a gidan totally da wanda ke akwai mutane da wanda babu zasu kai 30,
Falo kuwa akwai manyan manya sunkai 9, kuma kowanne an ƙawata shi da attractive & expensive furnitures,
Amma babban cikinsu shine wanda kana shigowa ciki zaka fara cin karo dashi, main palour É—insu kenan
Ni nasan duk yadda zan kwatanta haÉ—uwar gidan nan ba kowa bane zai gane ba saini dana shirya kuma na gabatar
don hka just imagine it like the one u used to see in your dream, 🙅
tasha wahala sosai wurin gyara gyatan ɗakunansu don ma ba ɗauda kawai iya bedsheet ne zaka samu an yamutsa, sai kaya in an cire kaga anyi wurgi dasu ƙasa, wani ma don iyayi kayan nasa a saman mirror ta same su,
Bayan ta kammala dukan aiyukan, gajiya ta saukar mata bagatatan, ɗaki ta koma cike da jin ƙyanƙyamin jikinta,
Maballin rigar ta ciccire ta zame ta duka ta ajiye ƙasa, cire wandon tayi shima, sannan tasa hannu ta cire naɗin mayafin kanta, kafin tasa hannu ta 6an6are abunda take matse ƙirjinta dashi, tana ciresa taji wata irin iska na shigarta, gaba ɗaya boobs ɗinta a mugun taƙure suke, ba abunda ya same su, amma ƙan nipples ɗinta ba ƙaramin hurting ɗinta ya ke ba,
Ita kanta tausayin kanta taje ji, yadda ƙiri~ƙiri ta canza kanta daga mace zuwa namiji, duk tabi ta takure halittarta, hannu tasa ta cire ɗan gashin bakin da take mannawa, ɗago dashi tayi tana kallonsa tana matuƙar son ainihin halittarta ta mace,
gaban dressing mirror taje ta ajiye shi, toilet ta shiga tasakarwa ƙanta shower, ta haɗa hada hairs ɗinta ta wanke saboda ya fara tashi, gashi tana buƙatar tayi shaving, batasan ya zata yi, sauƙin bata da gashin armpit amma can under ɗinta kuwa akwai sosai,
ta gama yanke shawarar zata É—ebo shaving cream É—in junaid taga hada set na shaver gare sa, dama shine marainin wayan ta,
ganin cewa babu kowa gidan daga ita sai azmi wadda ke can kwance tana sharar bacci, hakan yasa ta yanke shawarar cewa yau zata sakata ta wala, don haka ta shirya tsaf cikin riga t-shirt white colour da black trouser, sai da ta tabbatar ta matse ƙirjinta kamar yadda ta saba, sannan ta aza gashin bakin da take sawa, lalubawa tayi cikin jakar kayanta dayake ba duka kayan ta zuba cikin wardrobe ɗinba, anan tasamu hular da hajjaju ta siya mata, irin wannan hular da ake kira da tashi da kwakwa,
sai da ta tabbatar ta naÉ—e gashinta cikin ta cunkushe ta matse shi sannan ta kifa hular a saman kanta, sai gashi ta fito fes kamar É—an saurayi,
Ita kanta ba ƙaramin daɗin jikinta taji ba, fitowa tayi ƙafarta sanye da takalmi roba na maza,
Kama hanyar É—akin junaid tayi, cikin sauri take tattaka matattakalar stair É—in, a gajiye ta iso É—akin tura sa tayi ta buÉ—e ta shige,
Komai tsaf a tsanake dama ita ce tayi gyaransa, cikin jin daÉ—i ta wuce cikin toilet É—insa, agaban bathroom cabinet ta tsaya, anan taga jerin tsaddun mayukansa, duk wani abu na gyaran jiki akwashi kai kace na macene ba na namiji ba,
Tsawa tayi tana tunanin me yakamata ta ɗauka, tunani ta shiga yi " kodai kawai na tsaya anan nayi shaving ɗin inyaso in na gama in tsaftace masa wurin yadda bazai gane ba sai in samu in lalla6a in fi ce, saboda in na ɗaukar masa zai iya gane wa, ƙarshe ya kamani a matsayin 6arauniya, ya zanyi ni," ta fada tana ƙarewa wurin kallo
hannu tasa ta É—auko roban shaving cream É—in ganin yana da kusan guda uku yasa ta yanke shawarar ta É—auki É—aya bazai gane ba, sai ta haÉ—a da shaver guda biyu, tun da taga yana dasu dayawa a cikin ledarsu,
ruƙo su tayi a hannun ta saboda haɗama irin tamu ta bil'adama zuciyarta ta raya mata cewa mai zai hana ki haɗa da shampoo saboda wanke kai ga kuma sabulai masu ƙamshi sannan kina buƙatar turare na fesawa a jiki,
Murmushi tasaki jin wannan zancen na zuciyarta,
A fili tace "abun sai na samo wurin da zan zuba su baxan iya É—auka ba a hannu na,
Fitowa daga bathroom ɗin tayi ta shiga neman wurin da zata sa kayan, a nan tasamu wata shopping bag, ƴar jakar nan ta siyayya, komai cikin sauƙi take ganin sa,
Komawa cikin toilet É—in tayi ta shiga jidar kaya tana zurawa aciki, Sam bata tunanin cewa sata take yi ita ina gani take kamar ta zama Æ´ar gida in ta É—auka halal ne.

A gajiye ya shigo cikin gidan jikinsa sanye da kayan kwallo riga da gajeran wando, yellow colour ba ƙaramin kyau sukayi masa ba, hannunsa riƙe da kwallo yana ɗan bugata a hannunsa, kafin ya rungumo ta a ƙirjinsa, cikin sauri ya haye upstair yana isa kofan ɗakinsa, yasa ƙafarsa ya harba door ɗin ta buɗe,
Saboda tsananin firgice sai da tasaki kayan dake rungume a ƙirjinta, zo kaga tashin hankali, daga cikin toilet ɗin take jin shigowarsa, tuni ido ido ya raina fata musamman da taji tabbas shine ɗin dai ya shigo, ana dara ga dare yayi 🙉

End of Chapter 23Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next