Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel

Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel

Author: Hafsat Bature
Chapter 85 of 86
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,694 words Chapter 2 1,678 words Chapter 3 1,646 words Chapter 4 1,464 words Chapter 5 1,676 words Chapter 6 1,670 words Chapter 7 1,657 words Chapter 8 1,695 words Chapter 9 1,675 words Chapter 10 1,629 words Chapter 11 1,656 words Chapter 12 1,614 words Chapter 13 1,684 words Chapter 14 1,090 words Chapter 15 692 words Chapter 16 1,565 words Chapter 17 1,105 words Chapter 18 1,914 words Chapter 19 78 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 923 words Chapter 22 1,350 words Chapter 23 1,543 words Chapter 24 1,402 words Chapter 25 1,465 words Chapter 26 1,722 words Chapter 27 1,031 words Chapter 28 1,561 words Chapter 29 1,678 words Chapter 30 852 words Chapter 31 1,504 words Chapter 32 705 words Chapter 33 1,623 words Chapter 34 1,205 words Chapter 35 1,234 words Chapter 36 1,638 words Chapter 37 1,675 words Chapter 38 1,681 words Chapter 39 1,653 words Chapter 40 1,124 words Chapter 41 1,691 words Chapter 42 1,691 words Chapter 43 1,648 words Chapter 44 1,460 words Chapter 45 1,259 words Chapter 46 1,319 words Chapter 47 1,979 words Chapter 48 2,219 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,657 words Chapter 51 1,643 words Chapter 52 1,565 words Chapter 53 1,696 words Chapter 54 1,689 words Chapter 55 1,693 words Chapter 56 484 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 831 words Chapter 59 1,546 words Chapter 60 1,496 words Chapter 61 1,168 words Chapter 62 2,181 words Chapter 63 1,641 words Chapter 64 303 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 743 words Chapter 67 1,672 words Chapter 68 1,355 words Chapter 69 1,582 words Chapter 70 1,076 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,235 words Chapter 73 2,302 words Chapter 74 1,326 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 671 words Chapter 77 1,685 words Chapter 78 1,524 words Chapter 79 1,616 words Chapter 80 1,696 words Chapter 81 1,666 words Chapter 82 1,651 words Chapter 83 1,650 words Chapter 84 1,526 words Chapter 85 Reading now Chapter 86 1,487 words

a hankali ta buÉ—e kopan ta fito cikin sanÉ—a, gabanta ne ya faÉ—i da ta hango su gaba É—aya sun hallara a babban palorn cikin tashin hankalin rashin junaid, har sun fara yanke sha'warar fara kiran friends É—insa da sauran Æ´an uwa aji koya je can,
Dafe zuciya sehrish tayi tabbas kuwa in tabi ta entry É—in main palor zasu tambaye ta jin ba'asin ina xataje, don haka tayi deciding ta canza hanya cos there's many doors acikin gidan da zaka iya fita compound É—in gidan,
Ja da baya tayi a hankali dama slippers ne a ƙafarta marasa sauti, cikin sanɗa ta lallaba, ta miƙi doguwar hanyar da zata sada ta da backyard ɗin gidan,
Taci sa'a akwai Key ajikin ƙopan jikinta na kerma tasanya hannu ta murɗa key ɗin kopan ta buɗe, ahankali ta zura ƙafa ta fuce,
tsoranta kada security guard ɗin dake strolling acikin gidan su ganta a daren nan tana shawagi tabbas sai sun tuhume ta, gashi ko'ina na gidan Haske ne 6ayau kamar rana saboda fitilun kwan da aka ƙawata shi dasu masu hasken da kyan gaske kamar rana,
A hankali sehrish ke tafiya kamar 6arauniya, har Allah ya shigar da ita cikin garden É—in kai tsaye wurin da garden chairs É—in suke ta tunkara,
tunkan ta ƙarasa ta Hango mutun a ƙanƙame saman kujera ya kifa kansa saman table ɗin gabansa, gaba ɗaya jikinsa sai kermar sanyi yake na tashin hankali,
Zaro ido sehrish tayi cikin tsananin tashin hankali ta watsa aguje inda yake gabanta na faÉ—uwa, tabbas kuwa Junaid ne, dafe kanta tayi tare da cewa "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un !!! Nashiga Ukuna ! Junaid meyasa !!!!!
Cikin tashin hankali tayi maganar tuni hawaye sunzo mata shar a face É—inta,
Matsawa tayi dab dashi tasa hannu ta bubbuga table É—in dake gabansa murya a mace take ambaton sunan shi "Junaid...junaid...,'
Wani irin dogon numfashi yaja hatta yatsun hannayansa kerma suke yi, ko eyes É—insa bai iya buÉ—ewa tabbas yaji Muryar sehrish amma sam yagaza bata amsa, so yake yayi mata magana taje ta sanar da wani daga cikin gidan yazo ya taimaka mishi ya tashi amma ya gaza, saboda sautin muryarsa baya fita, Lips É—in ma nasa rawa suke yi kaf kaf,
Bin ziraran yatsun hannun shi tayi da kallo ganin suna kerma kaf ! kaf !! Hakan ya tabbatar mata da cewa Junaid idonshi biyu, sanyi ne yakamashi ssae,.
Cikin sauri sehrish ta cire mayafin da take naÉ—e gashin kanta dashi ta rufa ma junaid abayansa, duk da mayafin bai da wani kaurin da zai masa magani,
Zubewa tayi saman guiwarta agaban table É—in, saitin fuskarshi dake kwance saman table É—in tace "Junaid meyasa? Why pls? meyasa zaka cutar da kanka har haka? dan Allah ka buÉ—e idonka junaid, ka tashi mu tafi,'
Daker numfashinsa ke fita sam sehrish batayi tunanin tana 6ata lokaci ba wurin agaza masa,
So yake ya buÉ—e idonsa ya kalle ta amma sam ya gaza, sai kerma eye lids É—insa suke yi,
Hawaye ne kawae ke fita a idon Reesh, tana cikin wannan zuƙunnan karaf idonta suka sauka akan Hancinsa da Jini ke ɗigo wa,
Waro ido tayi waje a firgice ta fashe da kuka tare da faÉ—in "Junaidd...!!! innalallahi wa'inna ilaihirraji'un nashiga ukuna Wayyo Allah !!!
A zabure ta miƙe ta juya da gudu don taje ta sanarwa Aunty azmee wata'ƙil ta taimaka wurin sanar dasu halin da Romeo yake ciki don azo ataimake shi karya mutu,
Har Tayi nisa da gudun nata muryar shi ta ratsa kunnan ta "Sehrishhhhhhhh," cikin wata irin matacciyar murya wadda ta galabaita yyi maganar,
A razane ta dakata tare da juyo tana kallon shi, samun shi tayi ya buɗe idonshi waɗanda suka rune jawur daker yake ƴunƙurin tayar da jikinsa da dukkan sauran ƙarfinsa,
Cikin tsananin tausayi sehrish ta koma da gudu wurinsa tana faÉ—in "junaid,' tashi yayi zaune yana fidda numfashi a hargitse muryarsa na rawa yace "ki taimaka mun numfashi na zai iya É—auke wa, ki goyani ki kaini wurin Abbana,'
É—an zaro ido tayi tana kallonsa can kuma tayi tunanin ae junaid bazaiyi nauyi ba, ba wani girman jiki gare shi ba, duka nawa yake
daddagewa sehrish tayi ta tsugunna masa tare da cewa "hau muje," daker junaid ya sauko ya faɗo bayanta tare da ƙanƙameta yana numfashi a sama sama,
Jigumm sehrish tayi saboda wani abu da taji ya yi mata yawo ajikinta,
"Ki tashi mana so kike na mutu ko," junaid ne yayi maganar daker cikin shagwa6a, bawan Allah,
Da iya ƙarfinta na ƙarshe, daker sehrish ta miƙe tana tangal tangal zata faɗi amma ta hana hakan, ta dake ta cije ta miƙi hanyar fita daga garden ɗin da junaid goye abayanta kamar wani ƙaramin yaro, ya lafe abayan sehrish ɗinsa, tana jin numfashinsa a gefen wuyanta saboda nan hancinsa yake, tana jin yarda junaid ya ƙanƙame mata stomach ɗinta saboda ta nan ya zagayo da hannayensa,
Cikin sa'a ta fuce dashi daga garden ɗin kuma ba wanda ya ganta har ta shige dashi cikin ƙopan da ta fito, yanzu tunaninta shine yarda za'ae ta haɗa junaid da ƴan uwansa batare da wani ya ganta ba, tsayawa tayi tana wannan tunanin aikuwa junaid ya fashe mata da kuka mai sautin gaske yana cewa "wai bazaki shiga dani ba so kike na mutu ko,' duk yarda sehrish taso ta hana junaid magana abun ya faskara sai ma ya ƙara sautin kukan wanda hakan ya janyo hankalin Mutanen gidan dake a falo,
. gaba É—ayansu sunji kukan junaid da muryarsa, har haÉ—a baki suke yi wurin cewa "Kai wannan ae kukan junaid ne !!,'
gaba ɗayansu suka nufi hanyar da suka jiyo muryar junaid yana kuka yana yima sehrish faɗa akan taƙi ta motsa takai shi ɗakinsu,
Jin takon takalmansu alaman sun tunkaro wurin yasa sehrish shiga tashin hankalin, gashi ta cire mayafinta, hular kanta ta karkace dogon gashin kanta duk ya barbazo waje, ae kuwa a firgice ta saki Junaid ya faɗi ƙasa tumm !tayi saurin zame mayafinta dake jikinsa, kamar aljana tayi Wuff ta boye a wani saƙo hannunta dafe da saitin zuciyarta,
Junaid kuwa ganin sehrish ta jefar dashi ƙasa ta gudu yasa shi ƙara sautin kukan nashi ya karaɗe ko'ina yadinga burgima a ƙasa yana faɗin "wayyo Allah na, ta jefar ni !! bazaki zo ki goyani ba ki maida ni wurin Abbana ba, Wlh saina tona miki asiri tunda kikai mun hakan.......' sam junaid fa baya cikin hayyacinsa yake waɗannan maganganun, sehrish kuwa saboda ruɗin abunda junaid yace, tuni futsari ya kufce mata ta cikin wandonta ya soma zuba zirrrrrrrrrr ! Mai zafin gaske cije le6enta tayi tare da runtse idanunta,

Isowa su kayi gaba ɗayansu sunyi mamakin ganin junaid baje a ƙasa yana burgima sai faman sambatu yakeyi yana faɗin "wlh saina tona miki asiri kowa ma yasani Allah,' cikin kuka da shagwa6a yake maganar,
Atare suka haÉ—a baki suna cewa "Junaid ! ina ka shiga muna ta nemanka? Kai da wanene ? Ta ina ka shigo,'
Jin muryoyinsu yasa shi dakatawa yana kallonsu idonshi biji biji sam bai gane su wanene akanshi,
Murya na kerma yace "ita ce ta shigo dani, ta goyani kuma ta jefar dani ƙasa ta boye acan wurin,' yayi maganar yana nuna inda sehrish ta 6oye,
Tuni temperature ɗin jikin sehrish ya ɗau wani irin mahaukacin zafi, nan take wani futsarin ya sake zubo mata na tashin hankali, tuni zufa ta gama wanko mata sharkaf wandon jikinta kuwa ya jiƙe sharr,
Babu abunda take furtawa Acikin zuciyarta fa ce "La'ila ha illah anta subhanaka inni kuntu minal Zalimin,'

Gaba É—aya idonsu ya kai inda junaid ya nuna musu,
"Ah Wannan Fa aikin shaiÉ—anun aljanu ne kubarmin kawai A ya neh nayi maganin Æ´an Iskan," acewar haroon
Yana maganar ya nufin wurin,
Sgr bai tsaya jin bayanansu ba, hannu kawai yasa ya ɗago junaid dake kwance, ya ɗauke sa kamar wani ƙaramin yaro ya aza shi a ƙafaɗarsa, ya juya batare da ce musu komai ba ya wuce dashi part ɗinsa,
Shi dae abbansu ajiyar zuciya kawai yake saki tunda Allah ya dawo masa da Baby junaid É—insa lafiya, kallon sauran yayi tare da cewa "Kowa yaje ya kwanta, koma mekenan gobe zamu duba,"
Juyawa su kayi gaba ɗayansu kowa na faman sauke ajiyar zuciya suka wuce rooms ɗinsu, ban da haroon wanda ke faman sakin murmushin mugunta, domin kuwa ya hango ƙafafun sehrish masu sanye da wannan slippers ɗin nata na ƴan gado,
Bayan kowa ya bar wurin, sehrish tayi tunanin ta lalla6a ta wuce ɗakinta, dama idonta na runtse a hankali ta buɗesu gaf taga fuskar haroon a kusa da tata, wage baki tayi zatayi Ihu yayi saurin sanya hannunsa ya toshe mata baki yana faɗin "Ƴar shila, ae dama nasan kece ja'ira, na hango waɗan nan ƙafafuwan naki masu kama dana Zabbi,'
Tsananin bakin ciki ne ya cika sehrish ganin mutumin da ta tsana,
A faɗace tasanya hannunta tare da Buge nasa, da gudun gaske ta wuce shi ta faɗa bedroom ɗinta tana shessheƙar kuka, datse ƙopan tayi gudun kada haroon yasamu damar faɗo mata,
Jingina jikinta tayi jikin ƙopan bayan ta rufe, tana kuka mai cin rai, ta ƙara jin tsanar haroon a ranta hada shine yaja mata barin junaid yayi ta faman jiran ta a garden gashi hakan yayi masa Illah ssae, duk inta tuna ɗigon jinin junaid da tagani daga hancinsa, sai taji wani irin ba daɗi aranta,
Ta jima jikin kopan kafin daga bisani ta wuce toilet ta tu6e wandon daya jiƙe sharkaf da futsari tasa shi a bucket ta wanke sa, sannan ta shanya shi a siririyar rigiyar dake a toilet ɗin, wadda akayi ta domin shanya panties, da hanging ɗin kaya, bayan ta kammala tayo wanka sannan ta fito ta canza wasu kayan riga da wando
daga bisani ta haye saman gadonta tana sauke ajiyar zuciya, shigewa tayi cikin bargo tana dariya lokaci guda da ta tuna abunda junaid yaso yayi mata a yau da ta shiga uku kuwa, daker bacci 6arawo yayi awon gaba da ita,

End of Chapter 85Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next