Soyayyanovels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel

Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel

Author: Hafsat Bature
Chapter 39 of 86
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,694 words Chapter 2 1,678 words Chapter 3 1,646 words Chapter 4 1,464 words Chapter 5 1,676 words Chapter 6 1,670 words Chapter 7 1,657 words Chapter 8 1,695 words Chapter 9 1,675 words Chapter 10 1,629 words Chapter 11 1,656 words Chapter 12 1,614 words Chapter 13 1,684 words Chapter 14 1,090 words Chapter 15 692 words Chapter 16 1,565 words Chapter 17 1,105 words Chapter 18 1,914 words Chapter 19 78 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 923 words Chapter 22 1,350 words Chapter 23 1,543 words Chapter 24 1,402 words Chapter 25 1,465 words Chapter 26 1,722 words Chapter 27 1,031 words Chapter 28 1,561 words Chapter 29 1,678 words Chapter 30 852 words Chapter 31 1,504 words Chapter 32 705 words Chapter 33 1,623 words Chapter 34 1,205 words Chapter 35 1,234 words Chapter 36 1,638 words Chapter 37 1,675 words Chapter 38 1,681 words Chapter 39 Reading now Chapter 40 1,124 words Chapter 41 1,691 words Chapter 42 1,691 words Chapter 43 1,648 words Chapter 44 1,460 words Chapter 45 1,259 words Chapter 46 1,319 words Chapter 47 1,979 words Chapter 48 2,219 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,657 words Chapter 51 1,643 words Chapter 52 1,565 words Chapter 53 1,696 words Chapter 54 1,689 words Chapter 55 1,693 words Chapter 56 484 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 831 words Chapter 59 1,546 words Chapter 60 1,496 words Chapter 61 1,168 words Chapter 62 2,181 words Chapter 63 1,641 words Chapter 64 303 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 743 words Chapter 67 1,672 words Chapter 68 1,355 words Chapter 69 1,582 words Chapter 70 1,076 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,235 words Chapter 73 2,302 words Chapter 74 1,326 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 671 words Chapter 77 1,685 words Chapter 78 1,524 words Chapter 79 1,616 words Chapter 80 1,696 words Chapter 81 1,666 words Chapter 82 1,651 words Chapter 83 1,650 words Chapter 84 1,526 words Chapter 85 1,658 words Chapter 86 1,487 words

Abba yayi mamakin ganinta tana shayar da yaron, bayan ita da kanta tace anemi mai raino don baxata shayar dashi nono ba inyazo duniya, da alama soyayyar yaronce ta kamata,

A lokacin itama maryam ta haifi nata yaron kyakkyawan gaske wanda duk cikin ya'yanta bamai kyansa, farinciki a wurin abba ba'a magana a lokacin yama rasa ina zai tsoma kansa, saboda ƙaunar yaran nasa da aka haifa masa,

Babban tashin hankalin shine, Alexandra ta tada 6alli akan cewa yaronta addininta zai biyo kuma tasanya masa suna Alex, nan fa hankalinmu ya tashi, kowa ya harzuƙa akan lamarin,

Ran abba ya 6aci sosai kamar yayi ihu, a ƙarshe daya takura mata akan cewa shifa yaronsa addininsa zai biyo, sai ta ɗauko masa wannan takardar daya sa hannu ajiki wadda akayi rubutu ajikinta da harshen spanish ta nuna masa,

Cikin rashin sanin ma'anar hakan yace "me wannan ke nufi"?
Dariya tayi masa tare da cewa " wannan takarda dace, ta yarjejeniya dake nuna cewa ka amince ƴa'ƴana su bi addini na! in har ka matsamin zamu shiga court ne ayi shari'a, kuma kada kayi tunanin zaka iya ɗauke takardarnan domin akwai copy ɗinta awurina ba ɗaya ba, signature ɗinka ne ajiki, 🙆

Hankalin abba fa ya tashi, bai ta6a dana sanin auren Alexandra ba sai alokacin domin takaisa ƙarshe, Ashe wayau tayi masa, tasan hakan zai faru shiyasa tayi rubutun da harshen spanish, shi kuma gudun rigima ya sa bai tambayi menene fassarar abunda aka rubuta ajiki ba kawai yasa hannu, 😥

yaso ya tada 6alli akan koma mai zai faru sai dai ya faru , amma maryam ta dakatar dashi takwantar mashi da hankali ta nuna masa cewa, inya bi komai asannu wata rana ita da kanta zata canza, canjin da har yau muke jira amma Alhamdllh an samu ci gaba,

Bakowa bane wannan yaron da ake tada jijiyoyin wuya akansa ba face Surgeon general Rafayet wato BABBAN YAYA,

tun yana jariri bai ta6a kuka da hawaye ba, kuma likitoci sun tabbatar da cewa lafiyarsa garas, amma momynsa har ƙasar waje ta fiddasa aka ƙara dubasa aka tabbatar mata da lafiyarsa, sannan ta yarda,

A lokacin da yana yaro yayi tashen ƙiwuya, ya tsani bakar fata indai launin fatarka ba fara bace irinta mahaifiyarsa tofa kun raba jaha,

Duk bala'inka baka É—aukarsa, hatta mahaifinsa dake mutuwar son shi, bai yarda da shi duk da hasken fatar abban nasa, tsakaninsu sai dai kallo daga nesa , sai kuma in yana bacci uban ya lalla6a yaje ya zuba mishi ido yana kallonsa,

Shi kuma yaron da maryam ta haifa, ba kowa bane fa ce Marshal omer tazarar satittika ne a tsakaninsa da Rafayet,

Tun suna yara omar ke son wasa da rafayet, amma bai yarda dashi ba duk da kasancewar omar fari ne sosai kamar balarabe, yabiyo mahaifiyarsa Maryam bafullatana,

Gashi shima rafayet ɗin yana son Omar amma tsakaninsu sai dai daga nesa a rinka jefawa juna murmushi 😊

daya ƙara wayau hankali ya fara shigarsa, wata irin shaquwa ce ta shiga tsakaninsa da omar, duk da momyn shi bataso yana hulɗa dasu,
kai har takaiga idan dare yayi sai ya saci hanya daga bedroom É—insa izuwa nasu, ya haye saman gadonsu wurin omar ya kwanta kusa da shi,

Shima omar ɗin harya gane idan dare yayi, yazauna yaƙi bacci yayi ta zaman jiran rafayet, har sai yazo sannan su kwanta tare suyi bacci,

Maryam kaÉ—ai ce ta lura da hakan, ita dai ba ruwanta, tana son rafayet tanajinsa kamar É—an cikinta, haka zata je tayi musu addu'a tashafa musu kawunansu,

Ranar da alexandra ta gane hakan akan idonta, taga rafayet ya shiga ɗakinsu omar tsakar dare , aiko washe garin ranar tarinƙa zabga masifa har sai da kowa ya gaji,

Bayan wannan lokacin maryam taci gaba da haihuwa a inda ta sake haihuwar namiji again wanda yaci sunan shi najeeb, gaya nan kuna kallonsa, wato captain najeeb,
daga shi kuma sai Kanal yusif shima gashi nan zaune, daga yusif kuwa sai commender haroon, daga haroon sai Captain adams,

daga adams sai khaleed daga shi kuma sai jabeer da irfan, haka ta haifesu, daga nan ne ta dakata,

A bangaren Alexandra kuwa shiru sbd tace ta kammala nata, abba najin baƙin cikin musamman inyaga Ya'yansa zasu masallaci sun haɗu su duka amma babu rafayet acikinsu,

Ya so ya sake tada 6alli akan yaron, saboda yana da hanyar da zai kwaci kayansa daga faɗawa daga halaka, amma mahaifiyarsa tayi masa tatass akan cewa lokacin da ya aurota dawa yayi shawara, taja masa kunne akan cewa kada ya kuskura ya ƙara tankawa akan alexandra,

A dolensa yaja bakinsa yayi shiru bisa umarnin mahaifiyarsa,
A karshe ya koma yana nuna mata soyayya don yaja hankalinta, y rinƙa binta sau da ƙafa,

dalilin komawar Rafayet us da zama ba kowa bane face wan mahaifiyarsa mr donald, mugun son rafayet yake kamar hauka, duk weekends sai yazo nigeria don kawai ya gansa, kai daga baya ma sai ya kai sau 3 yake zuwa a week sam baya gajiya da zarya daga us zuwa 9ja, ran abba yayi matuƙar 6aci, har dai wata rana ya tambayi donald yace masa wai shi bai da ƴa'ƴa ne? da buɗen bakinsa sai cewa yayi, shiya riga da yayi plan ƴa'ƴa biyu yake so arayuwarsa, yanzu ya samu ya'yan kuma dukkansu mata ne, guda biyun ,

abba tamkar ya shaƙe shi haka yaji, wato tunda yasamu biyun duk mata, shiyasa ya dakata bayan yasan cewa yana son ɗa namiji,

Ba yadda abba ya iya haka ya zuba ma sarautar Allah ido 👀 haka donald zaizo yaita kashe ma rafayet kuɗi shida omar, kamar hauka bai gajiya,

bayan wannan kuma abba yaji yana son ya sake samun ƙaruwa da Alexadra, yaje cikin lalama yayi mata magana, sai yaga tana dariya abun ya ɗaure masa kai ,

gyara murya tayi tare da cewa " na amince zan sake haifa maka Æ´a'Æ´a har 3 amma bisa sharaÉ—in cewa zaka amince Alex ya koma wurin É—an uwana Donald da zama gaba É—aya, don na fi yarda da ya zauna can sbd zai fi samun tarbiya, zai wataya ya samu rayuwar Æ´anci,
.(wai tarbiya a us 😂)

Kai tsaye Abba yace ya amince dalili kuwa shine ya gaji daganin rafayet ba sallah ba salati ba karatun ƙur'ani, kwara ma yayi nesa dashi zaifi samun salama,

Amma shima yace yana da sharaÉ—i guda É—aya, tace tana sauraronshi,

Abba yace "yaran da zata haifa mashi dole su bi addininsa wannan karan,'

Batayi masa gardama ba tace ta amince, a wannan lkcn ALexandra ta ajiye aikinta gaba É—aya, sbd ta mallaki komai takeso a ynx, tayi mai isarta ynx lokacin hutun rayuwarta ne acewarta,

A nan ne kuma cikin ikon Allah ta samu ciki, a inda ta haifi twins tagwaye wato Ayaan da jahan, kyawawan gaske Allah ya zuba musu kyau, abba yayi farin ciki sosai, da aka tashi sa masu suna akexandra tace Za6i na wurinta, sbd a yarjejeniyarsu bai ce zaisa ma yara suna ba, don haka tasanwa Ayaan (John) Jahan kuma (James) kowa ya zuba mata ido 👀

daga su kuma ta ƙara samun ciki inda ta haifi fawan shima tamkar sauran wurin kyau, kyakkyawan gaske Fari sol, a inda tasanya mishi suna (Michael) nan Ma kowa ya zuba mata ido 👀

Bayan shine ta dakata da haihuwar gaba ɗaya, nan fa abba yasa rigimar cewa haihuwa uku tace zata yi masa, ita kuma tace ae inya lissafa da twins da fawan ƴa'ƴa uku kenan, ba dole sai ta yi ciki uku ba, Allah ya kawo mata cikin sauƙi,

Rigima ta 6alle a tsakaninsu daga ƙarshe da Abba yaga ba riba sai ya koma yana lallashinta akan ta taimaka masa ta haifa masa last born, uhmmmmm

A lokacin maryam tana ɗauke da cikin autanta na ƙarshe wanda a wurin haihuwarsa ne ta rasa rayuwarta, bakowa bane fa ce Talal,

Aunty azeema ta faÉ—i tana nuna sa, jikinsa yayi mugun sanyi, tuni hawaye sun zubo masa, haka sauran ma duk jikinsu ya mutu,

Ita kuwa alexandra dakyar abba ya samu ta haifa masa last born É—insa,
Wanda ya tafi da zuciyar kowa, da irin kyawunsa, shi na musamman ne, kowa rububinsa yake tun yana yaro yake fama da athma, ko ban faÉ—a ba kunsan ko wanene, mahaifiyarsa tasa mashi suna ROMEO, a inda mukuma muke kiransa Junaid,

Ansha wahala sosai kafin alexandra ta kar6i musulunci, a inda sunanta ya canza daga Alexandra zuwa FATIMA, kowa yayi tunanin cewa tayi imani da Allah ne, ashe ita bada son rantaba takar6i addinin,
Takurawar abbace,

dalilin barin alexandra nigeria tsakaninta da mahaifiyarmu ne basu shiri, hajiyarmu ta tsane ta ba don komai ba sai don yadda take wahalar mata da É—anta,

Duk in tazo abuja gidan abba sai sunyi cece ku ce, tun daga ranar da hajiyarmu ta buÉ—e baki tace ma Alexandra musuluncin ta ba kar6a66e bane, ta musulunta a banza domin kota mutu wuta zata shiga,

Ran Fatima ya 6aci sosai jin wannan maganar hakan yasa, ta koma addininta kai tsaye,
shiyasa ba a so in mutun ya shiryu arinƙa ƙyamatarsa ko kuma ana goranta masa, sbd gudun irin hakan ynx gashi ta koma yar gidan jiya, a ƙarshe da hajiyarmu ta Tsananta mata da baƙaƙen maganganu, ranta ya 6aci sosai

Wannan shine silar da fatima ta koma ƙasar Australlia da zama wurin danganin mahaifiyarta can sydney, babban tashin hankalin ma tabar masa jinjirin yaro batare da idasa shayar dashi ba,

Junaid yaga rayuwa, naso na É—auke shi,amma azmee ta nuna cewa tana so ta shayar dashi, shiyasa nabarmata sbd nima ina shayar da talal da mahaifiyarsa ta bari,

Rafayet ya musulunta ne a sanadin omar, saboda duk ƙarshen wata donald yana kawosa su gaisa da mahaifinsa, a haka ahaka har suka ja ra'ayinsa duk da ansha wuya kafin asamu ya kar6a, abba yaji daɗi sosai a lokacin, shima kuma donald yayiwa abba alƙawarin cewa bazai ta6a takurawa rafayet akan addininsa ba, zai bashi ƙwarin guiwa duk da kasancewar shi mabiyin addinin catholic,

End of Chapter 39Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next