Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel

Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel

Author: Hafsat Bature
Chapter 63 of 86
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,694 words Chapter 2 1,678 words Chapter 3 1,646 words Chapter 4 1,464 words Chapter 5 1,676 words Chapter 6 1,670 words Chapter 7 1,657 words Chapter 8 1,695 words Chapter 9 1,675 words Chapter 10 1,629 words Chapter 11 1,656 words Chapter 12 1,614 words Chapter 13 1,684 words Chapter 14 1,090 words Chapter 15 692 words Chapter 16 1,565 words Chapter 17 1,105 words Chapter 18 1,914 words Chapter 19 78 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 923 words Chapter 22 1,350 words Chapter 23 1,543 words Chapter 24 1,402 words Chapter 25 1,465 words Chapter 26 1,722 words Chapter 27 1,031 words Chapter 28 1,561 words Chapter 29 1,678 words Chapter 30 852 words Chapter 31 1,504 words Chapter 32 705 words Chapter 33 1,623 words Chapter 34 1,205 words Chapter 35 1,234 words Chapter 36 1,638 words Chapter 37 1,675 words Chapter 38 1,681 words Chapter 39 1,653 words Chapter 40 1,124 words Chapter 41 1,691 words Chapter 42 1,691 words Chapter 43 1,648 words Chapter 44 1,460 words Chapter 45 1,259 words Chapter 46 1,319 words Chapter 47 1,979 words Chapter 48 2,219 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,657 words Chapter 51 1,643 words Chapter 52 1,565 words Chapter 53 1,696 words Chapter 54 1,689 words Chapter 55 1,693 words Chapter 56 484 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 831 words Chapter 59 1,546 words Chapter 60 1,496 words Chapter 61 1,168 words Chapter 62 2,181 words Chapter 63 Reading now Chapter 64 303 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 743 words Chapter 67 1,672 words Chapter 68 1,355 words Chapter 69 1,582 words Chapter 70 1,076 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,235 words Chapter 73 2,302 words Chapter 74 1,326 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 671 words Chapter 77 1,685 words Chapter 78 1,524 words Chapter 79 1,616 words Chapter 80 1,696 words Chapter 81 1,666 words Chapter 82 1,651 words Chapter 83 1,650 words Chapter 84 1,526 words Chapter 85 1,658 words Chapter 86 1,487 words

*Hafsat Bature* 😎*🪄🪄🪄ABBAN SOJOJI🪄🪄🪄*

*Mallakin*

*💋Hafsat Bature Moh'd💋*

*❤‍🔥BossLady❤‍🔥*

*Junaid was the heart beats of my story not because i loved him so much, zaku shaida hakan*

~page 76-~

Murmushi hosana tayi daga kwancen da take tana kallonta, miƙa mata hannunta tayi tare da cewa "pls taimakamin na tashi kasala nake ji ajiki,"
Ruƙo hannunta jahad tayi daker ta miƙar da ita tsaye, tana faɗin "wash Allah ba dole ki ji kasala ba, kinci uban abinci kin kuma zo kin kwanta," acewar Jahada,
Wuce wa hosana tayi tare da shigewa toilet É—in, tana jiyo muryar jahad tana cewa "Hosana akwai shampoo ciki pls ki wanke wannan mahaukacin gashin kan naki, mara tsari nasan ki da taurin kai, bakisan wanke sumar kan ki, ko nazo na taya ki wanke wa.."? ta tambaya tana jiran amsa,
"Banso,' ta cikin toilet É—in tabata amsa, dafe kai jahad tayi tare da cewa "Oh God!!" saboda tasan hosana bazata ta6a yarda ta wanke sumar kanta ba, kuma bata so wani ya wanke mata, shiyasa kullum gashin kanta a cukurkuÉ—e yake, gashi duk tafisu yawan gashi da cukowa, duk da kowa da yawan nasa,
jahad na zaune saman stool gaban mirror tana shafa cream ajikinta, sai ga saude tashigo da sallama, da fara'a a face É—inta tace "wow masha Allah, tubarkallah wannan dogon gashin fa kamar na larabawa," tayi maganar tana kallon sumar kan jahad wadda ta zubo mata har wurin waist É—inta,
Cikin jin kunya jahad ta sunnar dakai, saude taci gaba da cewa "duk da nake bafullatana, nima ina da gashi amma bai kai ko rabin naki ba, ke wata ƙabila ce ? Jahad tace "BUXUWA,"
Saude tace "No wonder, shiyasan ya, hakan na nufin cewa ku Æ´an niger ne ko?
"Mahaifiyar mu buzuwa ce Æ´ar niger, amma mahaifin mu bafullatani ne É—an nan,"
saude tace "Wow wow!, haba ! ae dole kyau ya haÉ—u a wurin nan, dole kuyi kyau yara," murmushi kawai jahad ke saki, ganin yadda saude ke zuzuta su duk da itama É—in kyakkyawa ce,
Wuce wa ciki saude tayi ta buÉ—e wardrobe É—inta, riguna ta É—auko musu dogaye sun sha guga ninkakku, ta ajiye musu asaman gadon sannan tace "Gashi nan kusanya rigunana ne, duk da nasan sunyi muku tsayi sosai,"
"Mungode sosai aunty, Allah yasaka da alkairi," saude tace "mention not pls," sannan tafice don tabasu damar wataya wa,
"Jahad kinji yadda iska ke shiga jikina, ga wani ƙamshi dake fitowa sako da lungu na hammata ta," hosana ce tayi maganar wadda fitowarta kenan daga toilet ɗin,
A lokacin jahad ta kammala sanya doguwar rigar da saude ta fiddo masu, na materials ne pink colour masu kyalkyali, ba karamin kyau su kayi mata ba, cikin 6acin rai take kallon hosana
"Meyasa wai baki da hankali ne, ke shashashar ina ce? Ba sai da nace miki ki wanke sumar kanki ba,"? ta tambaya a ƙule tana kallon hosanar,
Da buÉ—ar bakinta sai cewa tayi "Gashina ne ko Gashin ki"? Shiru jahad tayi don tasan ynx zata tada rigima har ajisu,
"Gashin ki ne hosana, zo kisanya kaya gashi nan aunty ta fiddo mana mu sanya," wuto wa tayi daure itama da towel ajikinta, ta zura rigar materials ɗin, tayi kyau amma gashin kanta sai uban wari ya ke yi, babu yadda jahad ta iya da ita, bayan sun kammala shiryawa, atare suka haye saman gadon suna facing ceilling, "what are u thinking about jahad"? Hosana ce ta tambaye ta, cikin sanyin murya jahad tace "SEHRISH, ke fa me kike tunani? Murmushi hosana tayi kafin tace "Wannan kyakkyawan mutumin, mai ƙarfi wanda ya ceto rayuwarmu daga shiga haɗari, daga na rufe eyes ɗina shi nake gani, lokacin da na faɗa jikinsa, bakiji ƙamshi ba wlh ya haɗu" 😇
Jahad tace "shegiya ashe kina cikin hayyacin," 😂 dariya su kayi gaba ɗayansu

......................SEHRISH.....................

Ta gyara komai tsaf na bedroom ɗinsa, tsayawa tayi tana kallon hoton dake jingine saman side drawer ɗinsa bayan bedside lamp, hannu takai ta ɗauki hoton tana kallo, wata mata ce acikin hoton fara tas baturiya, mai kyan gaske kai kace itace tayi kanta don kyau, jikinta sanye da uniform ɗin na sojoji, kakin ba ƙaramin kyau su kayi mata ba, tsaye take tayi saluting a cikin hoton, bin sumar kanta sehrish tayi da kallo, launin gashin matar yayi yellow mai tsayin gaske, kwayar idonta kuma blue colour ce, wannan ba kowa bace face*Alexandra* Ummu Rafayet, ummun Ayan da jahan kuma ummun micheal(makel) da ROMEO 💞

Murmushi sehrish tasaki matar ta burgeta, duk da batasan kowacece ba amma kamannin fuskarta sak irin na Babban yayansu, akwai kyau, daga ganinta wayayyiya ce ajin farko,"
Hannu sehrish tasanya tare da shafa hoton a fili tace "kowacece wannan matar amma ta haÉ—u kuma ta burge ni, gashi tana kama da Babban yaya sosae," ta karasa maganar tare da mayar da hoton inda yake ta ajiyesa,
Sannan ta tura kopar toilet ɗinsa ta shige 😯 uhmmm hmmmmmm, tsayawa sehrish tayi tana tunanin anya ba kuskure tayi ba, wannan ae ba toilet bane, jimmmm tayi tana ƙarewa toilet ɗin kallo, lokaci guda ta dabarbace saboda haɗuwarsa, an raba shi biyu 6angaren toilet da kuma na bathroom wurin wanka kenan, ba ƙaramin girmane dashi ba, kamar a mafarki take bin komai da kallo, shiga ciki tayi ƙamshin wurin na dakar hancinta,
ba komai yaja hankalinta ba face wurin wankansa, wato irin standing jacuzzi É—in nan ne (kwamin wanka), wande ke zagaye cikin glass, sakin baki sehrish tayi galala tana kallon ikon Allah, mayar da eyes É—inta tayi kan bathroom cabinet É—insa, jerun wasu matsiyatan Shampoo ne, mayuka iri iri masu kyau da tsadar gaske, duk na gyaran jiki ko mace albarka wannan,
Jinjina kai kawai sehrish ke yi, haɗaɗɗen mirror ɗin dake cikin toilet ɗin mai girman gaske, ga wash basin agabansa, mai ɗauke da taps biyu na ruwa, daga gefe kuwa soap dispenser ce, gashi an ƙawata shi da vase a ajiye ƙasa, (Tukunyar flowers)

Zuƙunnawa sehrish tayi ƙasan hadaɗɗen tiles ɗim mai walkiya, ta zabga tagumi, aranta tana mamakin cewa wai nan toilet ne ? Idan har nan toilet ne to mukuma irin namu toilet ɗin ya sunan shi ? (Nace ba kewaye ko ki ce banɗaki) 😂

ta jima tana shirita, domin ba abun da ke buƙatar gyara a toilet ɗinsa, komai tsaf, kallo kawai ta tsaya yi daga bisani ta ɗanyi goge goge kawae ,
Fitowa sehrish tayi ta sauko down tana ko zata ganshi, basa nan ba kowa duk sun fita,
Wuce wa nata room ɗin tayi, tayo wanka, ta fito ta zura riga ta maza dai dai guiwa, ta zauna gefen gadon tana tunanin duniya, kallon sama tayi tana cewa "Oh ni yanzu wata rana nima zanyi saurayi, har nayi aure na haifi ƴa'ƴa,? When ? Ina so nima nayi shiga irin ta mata, na wataya nayi rayuwar ƴanci yaushen hakan zata faru ? 😥
Ajiyar xuciya tasaki tana tunane tunane,
Kwankwasa kopan akayi, cikin sauri tace" wanene? Azmee tace "wa kika sani yake zuwa É—akin ki in ba ni ba,"?
Murmushi Sehrish ta saki tare da miƙewa ta buɗe mata kopan, sanye take da hijabi milk colour hannunta riƙe da Cazbaha, da murmushi a fuskarta tace "ƙanwata ina fata dae ba zaune kike hakanan ba kina tunane tunanen duniya? karfa ace bakiyin zikri? Ba istigfari da sauransu?
Sunnar da kai sehrish tayi, don kuwa batayi, ae tun ran da tasanya SGR a idonta, ta rage duk wani abu da take yi,
"Hmmm dama raina ya bani, gsky zamuyi faÉ—a dake muddin baxaki, daina zama hakannan ba kina sa damuwa aranki ba,
"Insha Allah aunty azmee zan rinƙa ƴi," jinjina kai azmee tayi kafin tace "Albishirin ki,"?
Cikin mamaki sehrish tace "Goro,"
Azmee tace " an bani sabuwar waya nabaki,"
Ɗan zaro ido sehrish tayi cikin mamaki tace "Who"? Murmushi azmee tayi tare da cewa, " i will let u know but not now, yanzu dae da anjima bayan magrib kina da baƙo,"
Waro ido sehrish tayi tare da cewa "baƙo kuma aunty azmee ? wurin wa zai zo? Tayi maganar cikin ruɗu,
Azmee ta dafa kafadarta tare da cewa "bakowa bane , fa ce wanda nace miki, yasan cewa ke maca ce !! yau zaku haÉ—u, na shirya muku haÉ—uwa a Garden, ki same shi immediately after magrib prayer,"
Murmushi sehrish tasaki tana jujjuya ido, ta É—an jinjina kai kafin tace "shikenan aunty azmee Allah yasa naga alkairi," yanayin yarda tayi maganar taba azmee dariya,
"Ni zan wuce, maganar wayarki kuma, sai zuwa gobe zan baki ita, salon kuma in ga yarinya ta buɗe tiktok ko insta don na lura kan ƙanwar tawa rawa yake yi," ta ƙarasa maganar cikin zolaya da dariya a face ɗinta,
Itama sehrish dariyar take yi, duk da batasan menene tiktok da insta É—inba, sunan kawai ta ta6a ji ana faÉ—a," .
Bayan azmee ta fita, sehrish ta daka wani uban tsalle sai saman gadonta, tsananin murna ne ya bayyana a fuskarta, rawa ta dinga yi tana tsalle tsalle asaman gadon jin an mallaka mata waya, gashi kuma zata haɗu da wanda yasan cewa ita maca ce acikin gidan, addu'a take yi Allah yasa koma wanene acikinsu yakasance mai sauƙin kai kamar hafsat bature,

😇😂

Yini tayi tana zullumi acikin ranta,wanene wannan dayasan cewa ita maca ce ba namiji ba, wayyo Allah yasa junaid ne don yafi su sauƙin kai, ko ba komai wannan wani mataki ne nasara arayuwata, ga kyautar waya kuma an bani, wayyo daɗi bisa daɗi yanzu ya'azayi na rinƙa waya da ƴan uwana? ta faɗi jiki a mace,.
Zama tayi saman gadon ta janyo pillow tare da rungumesa jiki amace, taso ace lokacin da zata riƙe waya, ta rinƙa samun su Hosana da jahad, amma kash tun time ɗin da junaid ke ara mata wayarsa, ta daina jin ɗuriyarsu kullum switch off, sehrish ta jima tana tunanin menene yasa ba'a samun wayar tsohuwa ne ? What's happening wit them?

End of Chapter 63Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next