Soyayyanovels
Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel
Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel
By Sajida Niger
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel

Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel

Author: Sajida Niger
Chapter 1 of 11
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters

Subul da baka 2 page 1 Posted by ANaM Dorayi on 07:10 AM, 21-May-15 Under: Subul da Baka Kwance take rub da ciki da gani tana cikin damuwa mukayi sa'a ba kowa da gani korarsu tayi. Ya jefar dani gefe ya isa bakin gadon tare da tallafota ya tada ta zaune kallon da take masa me dauke da mmiki, sha'awa tare da tambayoyi masu yawa ya durkusa gabanta yace fareda ki gafarci yarinyar nan ta tsorata da fushinki ki yafe mata domin kaunar da muke yiwa juna. Kallo daya zakayi mata kasan ta fara rasa hnklnta don hk tayi saurin kallona tace na yafe miki Humaira dama bakiyi min komai ba, idona shabe-shabe da hawaye saiga murmushi ya subuce min. Ta maida kallonta gareshi dahra tym din bai tashi dg durkusonta da yayi ba saima kallonta da yake yana smiling na tuba nima a gafarce ni amaryata kuma gimbiyata... Ban jira amsar da zata bashi ba nayi waje tare da karayin godiya da goge hawayena kowa ni yake kallo sbd ta gabansu muka wuce, banga su rabi ba don hk na wuce dakin kwanansu don na gyara gashi lokcn ya kusa. Ko rabi banyi ba ya shigo har kewayen na kalleshi tare da banko min harara kinsan Allah yau saina kai kararki ga inna na gaji da irin salon rigimarki wllh. Na mulmula maganar tare da lailayata kafin nace rigima ta wuce irn naka kuma kafin ka kaini kara nizan fara kaika In Shaa Allah. Haka kikace? To bari in riga ki isa gidan mugani. Ya fita yana yar dariya, yau saida muka hadu da amira a hanya ta makara ni kuma nayi rana a gurguje muka gaisa ta wuce a kofar lungunmu na tarar da tankamekiyar motar mmk ya kamani wato da gaske yake zai rigani. Daga bangaren yamma a inuwa yake zaune da wasu jakunkuna manya guda biyar inna kuma na can gefe idanunta jawur da alama kuka tayi. Wata irin faduwar gaba naji wadda ban taba jin irinta ba na karasa gabanta na dafa guiwoyinta nace inna lfy? Me kayi miki naga idanunki sunyi ja? Ta kara fidda kwalla tace dinkuna ne yayo mana kowa akwati guda sai kayan kwalliyarki shima akwati guda tsoro +fargaba ya dabaibayeni da kalamansa tare da cewar kada mu butulcewa rahmar Ubangiji domin shima bayin kansa bane. Taci gaba da kwarar hawaye nima kawai sai naj kukan ya subuce min musmmn da aisha ta fara bude min kayan ina kallo. DonAllah inna kiyi hkr kinga har kin sa itama ta fara abnka da ruwa-ruwa. Ya mike na barku lfy inna danAllah kuyi hkr saina kara zagayowa ya fice. Mun dade muna sharbe kafin mukai kayan daki su aisha har an fara gwadawa da takalma kala 5-5. Inna ta kalleni humaira naso kama yaron nan akan abnd nake zargi amma saina rasa hanyar da zanbi sbd hausawa sunce idan baka iya kama barawo ba shi saiya kamaka. Kuma shirun nawa yayi amfani domin daga nasihar tasa na gane cewar haduwar jinin kawai da kuma tausayinmu da Allah ya dora masa. Tsoro na daya saka kayan nan mu shiga jama'a anya baza'a zarge mu ba? Kafin nayi magana mukaji sallamar baba Alh Sheetu inna ta amsa ta fito da sauri daman da hijabi a kanta. Duk muka fito ya kalli inna me kike nufi da hanamu albashin humaira ko kuwa kina tunanin zaki cinyesu ne ranar aurenta kibarmu da siyan kayan daki kinci bulus? Ya girgiza kai zaki dinga bamu rabi duk wata kuna amfani da rabi wann shine babban adalcin da zamuyi miki idan kuma kin amince zaki aurar da ita ne toh! Inna ta sunkui da kai a'a yaya ai bansan haka tsarin yake ba tuni na aiko bari na dauko maka, ta shigo daki bata ko kalli inda muke ba yace maza dauko tunda kinaso ki koyawa yarki son abun dunia shiyasa kika dage abar miki yayanki don kiyi jari. Inna dai batace komai ba ta mika masa 10k ba kunya karba tare da tusawa yace sun cika dama an fada mana 20 ne nayi ta mmkin ina yaji? Ya mika mata yar leda daga aljihunsa ungo goron sanya auren mansura ne wato yarsa sati 2 masu zuwa. Inna ta shigo tare da wasance maganar makarantar su sumayya. Batayi min zancen ba nima na tsuke bakina sbd munga abnd yafi hk. Da dadaare yaxo na tsinci kaina da faduwar gaba na fita da kwanon fura ba tare da nace ya shigo ciki ba sbd banason hirar ta dade kamr kullum jikin nawan ina jinshi wani iri. Muka gaisa nace ga fura. Ya karba amma yau kadan ya sha na maida sauran gida na dawo. DanAllah ka rage zuwa min dadare kaini ziyarar ma gaba daya kadaina idan baka iya dainawa ba. Sbd baki damu dani ba? Ya fada cikin yanayin takura nace a'a. Da kinsan abnd ya kawoni yau wllh da baki fada ba amma bakomai. Tausayi naji ya bani har saida idona yayi kwalla nace kayi hkri danAllah. Idan banyi hkri dake ba humaira ya zanyi? Damuwata na kawo miki kamr kullum su fareda sun hada min tuggu mai martaba ya kirani wai sati mai zuwa sunan nan tafe za'ayi bikinmu da gimbiya kuma ana gama daurin aure zamu tafi gaba daya zuwa yola. Gaba daya hanjin cikina suka kada take suka bada wani irin kara mai kamar sautin hadari. Ya matso gabana Humaira mutuwa zanyi banason yin nesa dake rabuwarmu zata zame..... Kwallar da nake makalewa ta zuraro kuka bazai yi mana magani ba ki bamu mafita domin nasan kinajin yanda nakeji karancin shekarunki da kuruciya zasu barki ki fahimci wani abu dake bin jininki... Kiyi mgn kada nima kiga nawa kwallar. Allah ya sanya alhairi na fada kamr me koyon mgn, ameen tunda kin ambaci alhairi saidai inaso kimin alkawari zanje nayi shawara da mahaifiyata idan ta amince zanzo in rokeki wani abu zaki bani? Na kalleshi nawa ne? Kwarai kuwa mallakinki ne har abada Nayi murmushi cike da kuruciya ko ince wauta nace ba komai ko menene tun a yau ba sai watarana ba idan mahaifiyarka ta amince ka dawo ka amsa ko kuma tun a yanzu na baka ka tafi dashi idan taki amincewa saika dawon dashi. Yayi murmushin dake kara masa kyau yace what a confidence' kawo hannunki, nayi hamzarin mika masa sai naga ya zura min manyan zobuna na gwal baki bude na kalleshi sai yace na alkawarine saina sadda kai kasa. Gobe zamuje Kd sai jibi zan dawo me zan siyoi miki? Nace bakomai ya watsa hannaye kinyi daidai gobe kizo da wuri don mu kara bankwana 7am zamu wuce nace to. Maza shiga gida banda tsawon hira kada a makara. Bacci da wuri bashi ke sa tashi da wuri ba sbd uwar makarar da nayi yau har tafi ta kullum ko wanka bansamu yiba kwaskwarima kawai nayi inata uban saurin na isa amma ina! Ana kokarin rufe get har sun dau hanya sai kurarsu na gani wani irin zazzabi naji ya rufeni inajin saukar hawaye a idona. Sashen gimbiya yau aka kiramu zamu kammala mata kaya tare da wasu shirye shiryen biki na tsinci kaina cikin rashin jin dadi ni kadai nasan yanda nakeji a zuciyata to meke damuna? Yaushe mukai irin wannan shakuwar da har nakejin haka a raina? Meyasa nakejin haushin gimbiya a yau? Wasa sabon aji sabo kuma tirken wawa bansan cewa na shaku dashi saida dare har kuka nayi acikin mayafina tsoro da fargaba suka rufar min na fara zargin kaina kona kamu da SON SA ne? Bani da yawan magana haka bani da kazar kazar sosai amma duk da hk saida inna ta tambayeni ko banijin dadin jikina ne? Shiru kawai nayi mata duk wanda ya ganmu a yanzu sai yayi mmki sbd sauyin da muka samu musmmn fannin cima da sutura yan unguwa sai gulmarmu suke kowa da abnd yake cewa wasu ma cewa suke sata nakeyi a gidan sarki tuni ftar jikinmu ta fara sauyawa ga cima me kyau ga sabulai masu gyara jiki. Washe gari muka shirya zuwa sunan gidan kawu mande nan mukaga jin zafi da bakin ciki karara babu kuma wanda ya kula. A gida bayan mun dawo inna ke shaida min wai ana gulmar yanzu maza nakebi nayi murmushin takaici. Maimakon yayi 2days saida sukayi 4days sannan suka dawo lokacin gidan ya kacame da hidima duk yan aiki sun hadu ba maganr sauyi gaba 1 muke haduwa sai maghrib muke tafiya ba muna can anata soye- soyenaji ana rade radin ya iso da bataliyar abokansa harda yan'uwansa ina jin ana nemana na boye bayan katuwar tukunyar kaji nida amira muka fito zamu tafi na hangoshi tsaye sai wurga idanu yake nasan ni yake nema saina dan boye. Abayantakwana 4 nan ya kara kyau da girma muka wuce bai ganmu ba amira tace min zakije party? Nace Allah ya tsareni. Amira ta tabe baki nima bazan je ba nace mata meyasa? Tace ina gudn dizgi da wulakanci kinsan halin gimbiya musamman idan ta ga jama'a nayi murmushi kawai a kofar gidansu mukayi sallama ina shiga gida na tarar da inna a tsaye a tsakar gida ko sallama ta bata amsa ba tace ina kikaje? Zuwansa 4 nemanki ba kyanan yace duk an duba gidan sarki ba'a ganki ba? Yar dariya kawai nayi haba inna da kinsan girman gidan sarki da bakice haka ba muna can wani bangare suyar kaji kawai mukeyi. Na mika mata bakar leda me dauke da soyayyun kajin da aka bamu nace inna aiki fa mukeyi shi kuma yana can ga abokansa shiru kawai tayi ta fitar da naman daga ledar na dauki cinya ina ci aka fara kiran sallahr maghrib nayi saurin cinyewa na tashi na gabatar. Na hada goldenmon ina sha kenan naji ana sallama a tsakar gida Aisha ta leka naji tana cewa la yaya sannu da zuwa gabana ya fadi inna ta kalleni nayi saurin tashi sbd nasan ma'anar kallon koda ya ganni sai yayi baya kofar gida ya tsaya inda muka saba. Yace fushi kikeyi dani humaira? Nayi shiru kiyi hkri wllh gida na koma na kammala wasu abubuwan kuma mamana ta amince nazo na amshi alkawarinmu. Kafin nan ina son ki shirya zan aiko a daukeki ko inzo da kaina mu tafi gurin

End of Chapter 1Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Login to Save Next