Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
party ko bazaki halarta ba? Gsky ban zuwa, me yasa? Hakanan, wllh baiyuwuwa duk mai hnkli bai wani abu saida dalili. Yace shikenan dauko min tabarma nima ban zuwa na kalleshi da mmki yayi murmushi wllh idan ba zaki ba nima ban zuwa dama tilastani akayi. Na rasa yanda zanyi da rigmarsa kullum da wacce zai bullo nace muje ka tambayi inna, da mmkina inna tace a dawo lfy muka fito yace ki saka leshin nan ja da takalmi silver kinji? Na daga kai, zan tafi saina dawo anjima nace to. Ni kadai nake bidirina a daki inna tana tsakar gida ina kwalliyata harda ta saman gira na feshe turaruka na fito tsakar gida inna ta kalleni ido waje tana mmki wann kwalliya haka humaira anya baki wuce gona da iri ba? Na yi murmushi, nace. " Inna ban yi kyau ba? " " kin yi kyau, amma kmr tayi yawa".Na zumbure baki da fadin. " wlh inna haka ake yayi".Ta harareni, "Ina ruwan ki da yayi? kin ga wlh ki dunga tuna matsayin ki, kada ki janyowa kanki damuwa".Shiru kawai nayi. karfe 9 naji ana sallama, na kalli inna. " zamu tafi, Ina jin shine ya aiko".Ta ce a dawo lfy, Allah ya tsare".Na ce "Ameen". Har na Kai bakin kofa, tace."kada ki wuce 11 dk abinki"."INA". na ce tare da ficewa. Sbd tsinin tklm ga rashin sabo sai na dinga takawa a hnkl kada na fadi, ckn direbobin gidan sarki na gani da alama bai ganeni ba. Motoci 4 na tarar a jefe, ya bude min Wacce tafi ko Wacce kyau da girma, na shiga Ina addu'ar neman tsari kmr Klum idan na baro gida hk ya zame min tamkar sallah. Yana rufewa naji an janyo ni a tsorace na kalli gefena, sai kawai naga Yrm. Kunya ta kamani, na ce, " Ba ni na gyara".Ya sakeni na matsa nesa da shi Ina fadin. " Ban son haka, don Allah ka daina".Ya yi murmushi, sai ya matso na kara takurewa ya ce. " kin yi kyau kmr ruwa. Cire 'yan kunnen na baki sarka".Ya fada yana laluben aljihunsa. A ciro bakaken 'yan kunnena dk sun yi baki sbd tsufa. Ya miko min wata dankareriyar sarkar zinare da 'yan kunnen ta.Na make hnn, "kayi hkr bazan karba ba, sbd wdnn zobunan ma inna tayi mini fada sosai"."sanya aro na baki ba kyauta ba, zan karba idan mun dawo".Jin haka na Sanya. " Ina alkawarin mu?"Na yi murmushi, " ya na nan"."Zaki bani ynz? ""Idan kana ganin Ina da shi a nan din".yayi 'yar dry, " Ai ko Yaushe kina tare da shi".Na ce, " Bisimillah".Ya yi Kasa da murya, "kada ki manta kin fa mallakamin tun kafin ki san ko menene".Na yi shiru kawai. Ya kama hnnyna duka biyun. "Humaira Ina barar soyayyarki, don Allah". A firgice na kalle shi daidai lkcn mota ta tsaya. Harabar wurin dankam da jama'a duk hankalinsu kuma ya dawo ga motocin da suka tsaya lkc guda. Dogarawa suka rugo suna bude mini kofa, ta kowane bangare barori kuma na watsa filawoyi. Abokansa suka rufa mana baya, naja tunga da sauri na tsaya, suka yi gaba. Wuri na nema na tsaya kusa da wata mota zufa kawai ke tsatsagomini ta ko'ina. Na kasa fassara yanayin da nake ciki.A hnkl naji an dafa kafadata, kafin na dago naga an zagaye ni. Na kalli sauran abokansa, nayi Kasa da kaina. " she is pretty".Na ji wani ya fada. Na kusa da shi ya ce."Akwai class I see".A hnkl yace, "Humaira mu je ki bani kwarin gwiwa, wlh bana son partyn nan ". wani ya matso, "kada ki biyewa zcy Humaira, ki tallafawa mai kaunar ki kada ki jefa shi...""kan uban can". Na ji saukar uban zagi kmr daga sama, ckn karaji Gimbiya ce tsaye tana hura hanci gefenta kawaye da sauran barori na kewaye da ita. Na zaro ido Ina yin baya- baya ckn matsanancin tsoro da firgita. " Ni Zaka ciwa mutunci? Ni zaka kunya ta a gaban jama'a ka rasa Wacce zaka hada sonta da nawa sai BAIWATA? Dama duk zame-zamenka a nan ka sauke? Haba biri yayi kama da mutum, ban manta abubuwan da suka ringa faruwaba, sai dai ka haddasa mata fitina, bala'i da tashin hkl ita da iyayenta a garin KANO!" ji kake tas! tas!! mari na wanke fuskarta ko ta Ina. " shut up! Idiot! " Ya bita da wdnn kalmomin, "kin isa ki yi abinda Allah bai nufa ba ne? ko kina ganin za ki iya hana abinda Allah ya hukunta?" To bude kunuwanki kmr ydd na sha fada miki, ba ki daga ckn tsarin matan da nake muradin aure.Bacin hadin iyaye babu abinda zan yi da ke a AURAKA! snn ki sanya wa ranki cewar Zaki yi kishi da baiwar da kika raina a kirata da GIMBIYA kmr ydd kike takama da sunan".Ta fashe da kuka, abokansa suka janye ta suna bata baki, amma har lkcn bata bar fadin, " ita ka cusawa wnn bakin cikin, wnn zan bambance muku MULKI da TALAKA sai an batar da su a kasar nan! !" Yunkurin cafkota yake yi ana rike shi, sauran abokan suka yi min zobe ganin Ina da niyar kwasa a guje. Tashin hnkln ya hana ni kuka, zcyta ta daskare kmr dutse, na kalli wnd ke bangaren damana ckn wani irin yanayi na ce. " ka taimakeni ka maidani wurin inna".Ya juyo da sauri jin muryata, hnn ya kama zamu bar wurin. wdnda suka janye Gimbiya suka tare mu da sauri. "Haba, Ina kuma zaka je kana ganin mun shawo kan Gimbiya? sauran 'yan korenta mun ja musu kunne su yi shiru da bakinsu".Ya kalle su, "Ba zan attending ba..." Suka rufar masa kowane da abinda yake fada, da kyar suka shawo kansa. wnd naji ya kira da suna sahabi ya karbi mukullin hnnsa zai mayar da ni gida, har mota ya Kai ni, snn ya saki hnn yana fadin "komai dare zan zo, kada ki yi bacci kin ji?" kmr na wawuro fuskar in cije don takaici, me kuma zai yi mini? wane bacci gare ni Ina ckn wnn tashin hnkln? A daidai Lungu ya tsaya na fita da sauri Ina jin yana cewa. " Mu kwana lfy ". Amma na yi kmr ban ji shi ba, zaman da na yi dabas ya sanya ta kalle ni da sauri, "Lfy? ""Da sauki inna ". Na fada ina rike kaina."Me ya faru? "Ta bukata a rude. Na zayyana mata komai. Ga Mamakina sai na ga ba ta wani razana ba, ta ce. " Ni dama na yi zargin haka tun farko, ganin cewar bai furta da bakinsa ba ya sanya na yi shiru, sbd maganar Hausawa idan baka iya kama barawo ba shi sai ya kama ka. Ba zan yi saurin cewa ba zai yiwu ba, sbd ba mu san hkncin Allah a kan lamarin ba, kada mu yi masa shishshi har mu saba masa. Amma da kmr wuya BAIWA ta auri DAN SARKI, kina karkashin mulkin gimbiyarsa". Na rike kaina da ke fizgawa tmkr zai bar wuyana tare da runtse ido, ba wai son shine ba ni yi ba, a'a ina hangar wa kaina tashin hnkln da ke gaba. Kmr inna ta karanci zcyta ta ce. " ynz kam dole runtse idanunmu, mu kuma toshe kunnuwanmu akan abinda zai biyo baya. A gaskiya zan roki yaron nan da ya janye bukatarsa abu ne mai whl ya rufa mana asiri, ya dubi maraicinmu". sai ynz kuka ya zo mini. Ta kalle ni. " ynz kika fara hawayenki su kare a banza, ko ki janyowa kanki wata matsala" "Ban katse ka ba, ina son ka gane abu guda. Yrnyr nan marainiyace, ka ga kuma ydd muke ba Wani boye-boye ynz, don hk son da ka ce kana yi mata to ka nema mata kwanciyar hnkl a rayuwarta. Gsky kayi hkr, wlh ba zan baka Humaira ba, sbd ka fi karfinta, ba km daya kukeba kai ni Ina shakkar son da kake yi mata da mamaki".Ga mamakin inna ta ga ya zube gwiwa bibiyu yana kwalla. " Haba inna, kada ki yi jayayya da ikon Allah mana, akwai wnd ya fi wani ga Allah ba ya ga mai tsoronSa? shin ya tsoron Allah ya ke? yin tawakkali da yrd akan dk abinda ya hukunta".Tausay insa ya far mata, sai kawai ta sunkuyar da kai. " Na amince, Allah ya yi mana jagora".sauran kwalln sk shatato masa."Nagode inna, Allah ya kara girma, ya kuma bani ikon rike Humaira bisa yrd da aminci". Yace ameen ya mike Zan koma sbd nabar gida kamr sansani yanzu abokaina basu sami runtsawa ba tace Allah yai mana jagora yace ameen. Har ya kai bakin kofa ya waigo donAllah Inna ku toshe kunnuwanku da duk maganganun da za'a zo muku dasu tace ISA ta fada tana mikewa shi kuma ya fice yana fadin zan dawo anjima idan humaira ta tashi. Kwalla ta zubo min burinsa ya cika ya rabani da aikina, motsin inna naji ta sassauta murya ki tashi wann kwanciyar bata da wani amfani a gareki. Ba'aja da ikon Allah sbd har abada bazan mance alhairin yaron nan ba sanadiyarsa ina neman rasa cutar tun shekaru masu yawa nake fama da ita tun magungunan da alluran da yayi min bai kara tashi ba. Na fahimci Allah ya dasa masa kaunarki matsayinsa yafi gaban ya zubda kwalla akanki ko yaudara yazoyi zan iya mallaka masa ke sbd yaudarar tazo cikin tsafta sai gashi ya tsugunna a gabanki ni mahaifiyarki yana kuka yana rokon amincewata kina tunanin Allah bazai kamani ba da alhakinsa? Ko kuwa mun yaba kyautarsa kenan? Ta girgiza kai tunda fahimci kyautar da yake mana wllh zan jure duk wani wulakanci da cin mutunci kema sai kin jure sbd bayan wuya sai dadi. A matsayina na mahaifiyarki humaira yanda nasanki da rashin sun magana tashin hankali da sauransu ina jiye miki kishi da gimbiya. Sai a lokacin kuka kuka yazo min da karfi na dinga sharbe harda majina Ta girgiza kai yanzu kika fara kuka dama kin daina wahalar da hawayenki a banza sbd yanzu aka fara bamusan abnd gaba zata haifar ba. Mutane muka hango a tsakar gida ai bansan yanda akayi na ganni a kofar daki ba hanjin cikina suka kada
More Hausa novels
Rayuwarmu Book One Complete Hausa Novel
By Saadatu
Kururuwar Shaidan Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Kwarton Manya Book 3 Complete Hausa Novel
By Ubeera
A Garin Mu Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Rubuce Take Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Hariji Book 3 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Search across the available chapters.