Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
har lokacin kwalla ke fita a idanunsa kamar anbude famfo. Nadafe kaina, shin kowace mace haka take samun wadannan kalubalen ga maza, kokuwa ni tawa halittar ke da haka? Da kyar Yaya ya shawo kansa abinka ga fari mai idanu fuskar nan tayi jawur, musamman hancinsa, idanun suka rikide suma sannan girmansu yakaru... Yanayi yanda inna fa Yaya ke masa bayanu yasa shi kara nitsuwa, nitsuwa irinta sauraron magana don a fahimta. Suna gamawa ya kalleni wasu siraran hawaye suka biyo baya.. Na yarda Inna sannan na amince amma don Allah ku rokar min ita idan zata maye mani gurbin Hafsat. Da sauri nace an fidda min miji kayi hkr bana.... Inna ta dalle min baki. Yayi murmushi mai nuna daci da kuncin zucia. Humaira sunanki bayyi kama dana marasa tausayi ba ki tausaya min ko don halin dana shiga donAllah.yaya ya dafa kafadarsa wane hali ka shiga safwan? Yayi dan smiling tsaya kaji LABARI na: ina dan 3yrs mahifiyata ta rasu don haka na tashi a hannun kishiyarta. Ni kadai ta haifa ita kuma tana da yara 4, tunda na tashi naga mahaifina yana yawace yawacen kasashen dunia don gudanar da harkar kasuwancinsa wato ba mazauni bane, yana int'l biz. Na tashi cikin wahala da azaba irinta kishiyar uwa sai nayi bara gidaje nake samun abncin da zanci kamar yanda umma ta umarceni duk da arzikin mahaifina kuwa. Sakamakon dangin mahaifiyata ba'a nan suke ba yan asalin yamai ne ta jamhuriyar nijar su kuma dangin mahaifina an rasa wanda zaiyi hobbasa kada tayi zuga ya daina basu abun arziki. Taimako daya da Allah yayi min skul 1 mukeyi da yayanta tayi ta rabamu Abbana yakiya amma fa ko ruwa bana tfy dashi. Tun ina kukan yunwa harna daina gashi ba'a tadamu sai karfe 3. Da mun koma ggida sai islamiyya hakan ya zame min jiki abnc baifi na samu sau daya a rana ba shima sai bayan maghrib idan nayi bara. Allah mai tausayin bayi na shiga wani gida a bayan gidanmu naga wata yrny da sharbebiyar wuka cikin dabara na dauketa zuwa cikin gidan. Zaune suke ana rabon wasu kaya kamr tsaraba nayi sallama tare da gaidasu nace wann yrnyr tafita da wukar nan tana wasa ai nan da nan suka dau salati suka rude sukaita samin albrk sukace daga ranar na dinga zuwa karbar abnc. Abin mmki Hafsat kullum bata cin abncinta sai nawa har muka shaku sosai da ita mahaifinta yasan shakuwqrmu har aka sanya mata hafsar safwan. Da yake sunsan ni da lbrn wuyar da nake sha saina koma kamr dan gidan. Lokcn da tafara girma sai muka juye soyayya wacce ita tafara bullo da hakan. Kowa ya fahimcemu har iyaye sun bani ita. Kwatsam muka tafi karatu akayi mana waya bata da lfy ana gobe zan taho ganinta aka karamin waya TA RASU...... Ya fashe da kuka.... Gashi ban taba soyayya da wata ba ban shaku da kowace mace ba sai ita. DonAllah ku taimakeni kuce Hafsat ce wann wllh kamr su daya. Wani takaici ya rufeni bawai na rashin tausayin sa bane a'a kawai yana musulmi zaiyi wasa da imaninsa. Wallh gwara matsalarsa da tawa shifa mutuwa tayi ni fa? Gashi da rai amma yayi min nisa nisan da bani tunanin zai dawo gareni nima saina fashe da kukan. Kamr inna takaranci zuciata saita karyar da murya tace Safwan! Inason ka tuna cewar kai muslmine wanda yayi imani da Allah ko kafirai sunyi imani da mutuwa ballantana kai musulmi ashe kayi imanin wanda ya mutu zai dawo? Ya girgiza kai a'a inna, ta bata fuska wallh kayi mana tunda gashi kana kiran wata da Hafsat. Ina mahaifyarka? Maiyasa ita bata dawo ba sai hafsat? To ahir dinka wllh kaji tsoron Allah kayi imani a mutuwa don akwai ta kuma duk wanda ya muutu baya dawowa har abada. Sai naga yana goge kwalla alamar maganr ta shigeshi. Wann yarnyr sunanta humaira haifaffiyar nan ce kawar amira ce, kusan tare mukai goyonsu da mahaifiyarta gidan su na can gaba da an sha kwana snd haka..... Bakomai inna wllh kamr ce har tayi yawa shiyasa.... Allah yafi da haka bai kamata ka firgice haka ba sbd soyayya har kayi sabo. Ya karkatar da wuya wllh inna bazaki gane ba amma bakomi ni yanzu ki taimakamin da yar taki donAllah... Kafin inna tayi magana ninayi ina mike nace kayi hakuri anyi min miji. Ban jira wata mgn ba nayi waje cikin fushi.ko zaure ban fita ba wayata ta dauki kara kmr abin jira, alamun kira ne ya shigo. sunn Ibrahim ne alamar shi ya kira, na lafe bakin kofa sbd na tsani tfy ina waya kmr wata sabon shiga.sllm nayi kafin ya amsa, sai da yayi wata ajiyar zcy na yi dan murmushi sbd inda sabo na saba da jin hk.A hkl yake maganar kmr mai tsoron furta kalmomin, "Humaira zcyta Zata fashe kaunar ki ta hanani aiwatar da abinda na zo yi, ki taimakeni na turo a daura mana aure ckn satin nan a kawo min ke ko na sami sukuni".ban San lkcn dana kyalkyace da dry ba nima ckn zolaya na ce, "to na taimake ka". Ya yi murmushi mai fidda sauti wani abu ya taso min wnd nake ji kullum idan na kasance ina irin wnn hirar, na runtse ido kawai. Ya kara narkar da murya, "wlh da gsk nake na takura mata nake so kusa dani".Na bude idona ina jin alamar kwalla, amma na daure na maida su tare da kokarin kawar da damuwar da nake neman shiga, na ce. " Ibrahim ka zamo mai adalci, shin mai zai hana ka tafi da matarka don Allah ka yafe mata mana". "Baza ki taba gane abin da nake nufi ba ynz matata ta wuce muguwa, wlh shaidaniyace, ke dai ki dage da addu'a Allah ya tserar da ke daga sharrinta". Gaba daya jikina ya yi sanyi, gaba na ya fadi, tsoro ya kama ni, amma sai ban nuna masa hakan ba, sbd ina son jin tushen mgnr. Ina 'yar dariya nace. " Nima abin ya shafeni kenan?" "ku san haka, sbd wai ta ji ana mgnr neman aure shi ne ta bugo mini waya jiya da daddare cewar wlh sai ta gano ko Wace ce, km sai ta kashe ta ko ta yi sanadiyar nakasata kin ji muguwa". Ckna ya bada wani kululu. Na zaro ido tare da dafe kirji. Ya yi murmushi, " kin san wnn ai haukane, ni dai sai kawai na bi ta da karya ne dona zauna Lfy. Ibrahim da na daure na cije ba don ina sonsa ba, kawai gudun bacin ran inna, shi kuma ga Inda tashi matsalar take. shi kansa yana tsoron sharri da tuggu na matarsa ina ga ni karabiti? shin in fadawa inna ko in yi shiru? Fadar babu abinda zai janyo mata sai tashin hkl da rashin kwanciyar zcy. wayyo ni Humaira ga 'yan uwan ubana sun tasoni a gaba, kr2 ma sun hana mini sbd jin zafi da bakin ciki, Innalillahi wa'inna Ilaihi raji'un. kai dole in sanar da inna, domin itace mai yi mini addu'ar da Allah zai amsa da gaggawa. A kfr gida na tarar da su tsaye kallo 1 nayi musu na gane 1 daga cknsu shine muka hadu wurin biya wa su Aisha kudin makaranta na farkon zango Ni sai da ma na ganshi na tuna ban kai kudi an aka sanyo musu baje ba jikin uniform din. Da fara'ata na karasa sbd ban mance taimakon da yayi mana ba, na cika mana #30 sbd babu canji a lkcn, ya ce mu bari zai bayar. Har Kasa na durkusa don gaida su. Ina murmushi nace, "Mun fa gode ". Ya yi murmushi, " wai ni har ynz gdyr nan bata karewa? "Na yi 'yar dariya kawai. Abokin yace ," Nan muka zo gurin musbahu tun dazu muna nan unguwar sai ga kannenki (su sumayya) za su tafi islamiya, abin mamaki yaran nan suka ganeni. shi ne suka gwada mini gidanku nace bari "Eh wlh nan baya na je kai wani sako ". Abokin yace, " to madallah, mu zamu wuce sai wani lkcn ". Na ce, " to nagode ". Na wuce gida Ina kallo ya Kai masa duka da harbi na yi kmr ban gani ba, na yi ciki abina. " wai lfy kika dade hk? ko lbrn ne naku ya tashi ke da innar taki? " Ta karasa mgnr tana murmushi, na ce. " Humm bari inna na zauna tare da ba ta lbrn duk abinda ya faru hr wayarmu da Ibrahim ". sai na ga tana dry.Na bata fuska." to me zan yi? " "Duk ciki banga abin dry ba sai na kuka kika gani? " " wlh ba komai ke dai ki ci gaba da addu'ar Allah ya warware mana, wlh nasa Allah ma ji rokon bawansane, ba zai ki amsar mu ba, wataran sai lbr, INA lkcn da Zaki tuko zukekiyar mota ki zo kina alfahari da mijinki". Na yi murmushi, " waye inna?" " Allah kadai ya sanshi". Mafarkina suna nuna min mijinki sai dai har yau banga fuskarsa ba, ni na San..." sllmr su Baba Auwalu ne da wasu dattawa guda 4. Ckn ladabi na gaida su tare da yunkurawa zan tashi ya dakatar da ni. Inna ta mika musu tbrm 3 suka zauna, Baba Auwalu zakakke shi ya fara mgn.Abu 1 ya kawo mu nan mgnr Humaira gabana ya fadi. Wani ma'aikacinmu ne yaga Humaira yana so shi ne ya turo abokansa su ji masa mgn, to na fada musu gsky yrnyr ba ta aje kanta nan ba mai kudi take so, ko dan sarauta ko kuma likita mai kwasar albashi da tsoka. wnd ta sami daurin gindi daga uwarta aka maishe da iyayenta maza banza. ko da Allah ya azurta 'ya'yanmu da auran masu kudi ba tallarsu mukai ba, sune suka biyo su har gida, muna kora suna likewa don hk nace gwara mu zo su ji daga bakinku. Tashin hnkl ba'a sa masa rana, wnn cin mutunci da wulakancin ya isa.Na kalli dattawan akalla kowanne zai yi 55-56 yrs wai abokinsu ne ke sona, Yaushe ya ganni, km a Ina? wnn abu daga ji tsarine km salon wulakanci da tozarta ne. " ku nake saurare shin akwai wnd kuka
More Hausa novels
Rayuwarmu Book One Complete Hausa Novel
By Saadatu
Kururuwar Shaidan Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Kwarton Manya Book 3 Complete Hausa Novel
By Ubeera
A Garin Mu Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Rubuce Take Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Hariji Book 3 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Search across the available chapters.