Soyayyanovels
Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel
Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel
By Sajida Niger
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel

Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel

Author: Sajida Niger
Chapter 3 of 11
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters

waya nunawa gimbiya gidanmu? Na fita daga kofar dakin ganina ya kara mata bacin rai. Don ubanki ina kazamar uwarki? Yanda tayi zagin gabana ya kara faduwa anya zan iya dauke cin mutuncin iyaye? Yana iya dama inna tace saina jure. Motsin inna naji a bayana tana cewa ganinan... Ta nunata da yatsa ba asiri ba wllh ko tsafi kike da bakar jaba yarki bazata auru ba munafuka. Tsautsayi yasa inna ta matso tana bata hakuri ta kuwa kundumo mata wani mugun zagi ba tare data girmamata ba. Zan nuna miki cewar sarki da talaka akwai bambanci sai kun raina kanku a garin nan shegu MATSAFA! Maganr ta daki zuciata anya zan iya shanye wulakancin su? Magnr ta tunzuro hrt dina tsanarsa ta bijiro min don shine musababbin karar marurrukan dake sauka kuncin inna yasa ta tangal- tangal nayi saurin riketa gabana yana faduwa kada ciwonta ya tashi aiko nan da nan ta fara shessheka ina kokarin zuwa dauko mata magani naji gimbiya na cewa a dakemu. Kota ina duka mukeji maza da mata su Aisha sai kuka sukeyi ganin an hada mana jini daga ni har inna niba dukan ke damuna ba ciwon inna kada ya galabaitar da ita amma rashin imani da tausayi baisa sun kyalemu ba saida muka matukar galabaita tuni inna ta sume rai yana kokarin fita ganin haka suka fita daga gidan jini yana fita a hannuna da goshina Na rarrafa na dauko mata maganin su sumayya suna watsa mata ruwa ina shaka mata maganin. Cikin ikon Allah ta farfado amma hannunta yaki motsawa, ihun su Aisha ya tara jamaa lokacn su gimbiya sun tafi abinka ga safiya ba kowa ya fito ba mal bala ya kalli hannun yace kamr karaya? Inna ta rintse ido mike cikin radadi suka kamata hannun yayi baya sai kawai ta zube tare da yin wata kara nima na kurma ihu na tallabeta jamaar gurin suka rude wasu suka ruga kiran mai dori kafinsu dawo mukaga bataliyar abokansa tun daga waje suka gidan dankam da mutane suka karaso a kidime basu jira komai ba suka dauki inna sukai asibiti da ita tuni ya tasa keyar su Aisha dama ni tun shigowata ya rike hannuna ya cika da tambayoyi. Bani iya masa fitsara dana gwada masa yau, kafinmu isa zazzabi ya rufeni ruf. Ni asibitin ma tsoro ya bani sbd kyaunsa nan da nan aka shiga da ita tiyata ni kuma aka bani daki da gado allura 2 akayi min sai magunguna da nasha shiys dressn din da akayi min banji zafi ba ita kuwa inna gurin kare dukan ne suka karyata kai Allah ya isa! Bacci ya daukeni wasan kusan 3 na farka gadon da ke kallon naga inna kwance itama tana ta sharar bacci. Su Aisha da abokansa suna zaune shi kuma yana tsaye ya jingina da bango ya harde hannuwa. Gaba 1 suka taso zuwa gaban gadon nayi saurin rufe idona sbd wani abu danaji yana harbin zuciata. A hnkl naji ana mgn kusa da fuskata kiyi hkri ki tashi kiyi sallah tym yana wucewa komai yayi zafi mgninsa Allah! Da sauri na bude ido jin muryar sadauki ya kada min kai ya kalli yarima ya maido kallonsa gareni muna tausaya muku anci zarafinku kuma zamuyi saurin daukar mataki wannan cin mutnci yayi yawa they have crossed their limit! Ga maganarsa ga kuma sannun da sahabi yake min narasa wanne zan saurara yarima kuwa har tym din ya kasa cewa komai da alamu ni yake kallo amma na kasa bude idona na ganshi Bayan nayi sallah suka fitineni saina ci abnc saida na cusa kadan. Sahabi ya kalli sadauki yace muje ko? Yace su Aisha muje waje muyi kallon haraba...... Turo kofar da akayi ne yasa maganr ta makale saura kadan na kwasa da gudu wata shamkiyar mata ce ta shiGo da dogarawa 4 a bayanta kallo 1 zaka mata kagane fuskarce bambancin tana mace yana namiji. Sadauki da sahabi suka zube a kasa suna barka da yamma Mama. Nayi saurin sunkui da kaina inajinta amsa kasa-kasa a tym din ya taho daga tsayuuwar da yake sai kawai ya fada jikinta baice komai ba ita kuma tasa hannu tana dan bugun bayansa alamar rarrashi, ta janyo hannunsa zuwa bakin gadona ga mmkina saita zauna kusa dani shi kuma ya zauna muka sata a tsakiya. Nayi saurin sauka kasa na zauna kusa da kafafunta. Sai naga dogarawan sun fice da alama umarni ta basu. tace dawo ki zauna nan ta nuna inda na tashi na girgiza kai kawai ina mmkn zuwanta a wnn tym din. Tayi shiru kamr yanda dakin ya dauki shiru cikin dabara sahabi ya fiddasu sumayya sanna ya dawo ayi komai a gabansa. Ta gyara murya toni yanzu mezanyi mk Hameed? Kamr yana jiran tambayar ne ya kalleta ido jajur cikin damuwa yace Mama duk duniar nan baya ga Allah banida wani gata saike ki dubi girman Allah zucita tana cikin tsananini ki rabani da wann auren na gimbiya bani kaunarta da duk wanda ya shafeta... Ta katseshi Bazan iyayi maka wann alkawarin ba sbd mai martaba ya bar wasicci ko bayan ransa idan baka auri farida ba bai yafe ba. Ya sassauta murya mama yarinyr nan bata da hnkl ki dubi inna... Sun karyata sannan dubi raunukan da sukaji mata ita da humaira shin Sarauta hauka ce mama? Ni nace inason yarnyr nan wllh har yanzu ban sami wata amsa dg gareta akan abnd tayi musu shin meyasa zucoyata bazata buga ba? Kina ganin wanda yayi wann aika-aikan bazai iya kisan kai ba? Kafiya gareka Hameed ina jiye maka fushin mahaifinka kana sane da cewa bazai amince maka ka auri wacce ba jinin sarauta ba gaba na ya buga da karfi taci gaba da cewa... Zuwan nan kadai ya fahimtar dani wani abu wllh na yaba da kunya nutsuwa da kuma hnkl kana da tabbacin kai sarki yabar wasiccin ka gajeshi idan ka tsaya akan wann ra'ayin lallai sarauta zata bar hannunka har abada. Wani abu naji ya tsikareni jikina yayi sanyi lakwas. Mama ya kira sunanta cikin wani ayanayi ta amsa ta kalleshi cikin jimami, duk dunia ba wanda yasan damuwata halina da kuma al*amurana kamar ke sbd ko tari nayi ko a bayan idonki saina sanar dake dn hk nakeso kibani mafita ayau wllh mamana zuciyata tana min zafi. Ina kallon sadauki ya matso kusa dashi ya dafa kafadarsa daidai tym din inna ta farka na mike zuwa gareta amma saiya rigani. A hnkli mama ta iso inna ta kallemu sai tayi smiling. Sannu ya karfin jikin ne? Mama Ta fada tana kallon hannu daya karye, da sauki ta fada tana kokarin tashi muka kamata har maman ta zauna saman gadon ganin hk yasa na koma na zauna yana ta koakrin mu hada ido amma naki. Mama ta dafa hannunta sannu inna, murmushi kawai tayi. Ganin hk ta fara magana donAllah kuyi hkri an zalinceku an shiga hhakinku amma danAllah kuyi hkri. Inna tayi shiru ta kauda kai, bazan gaji da baku hkri ba wllh inajinku har cikin raina domin duk abnd Hameed zai so ina son shi kamr yanda nake kin abinda bayaso. Nayi farin cikin ganin Hameed ya sami wacce tayi masa kuma ya furta yana kaunarta da bakinsa. Abnd na dade ina mafarkin gani yau gashi Allah ya tabbtr min dashi sbd kowa yana tunanin ko bashi da lfy ne baligi kamr sa ace baisan SO ba kullum sai yace bai sami wacce tayi masa ba don har dariya mukeyi masa tare da yan'uwansa idan yana suffanta yanayinta. A gsky na gasganta halayen Humaira dan zuwan nan da nayi nasan Hameed nice mahaifyarsa nasan kuma wayeshi wllh bazan taba jayayya da kaunar da yake mata ba nasan na gsky ne daga Allah. Kamr yanda nayi farin ciki ta wani fannin kuma ina bakin ciki sbd lokacin daya tsinci kansa cikin kaunar wacce yake mafarkin samu a lokacin ne mahaifinsa yasha alwashi akansa. Nasan halin mahaifinsa da tsatstsauran raayinsa akan duk abnd ya zartar mutum ne me zafin gaske me kishin sarautarsa baya kaunar talaka ya shigo masarautarsa da sunan haduwar jini duk kaunar da yake wa dansa zai iya yafeshi akan wann. Bani ba har inna saida ta razana da wann maganar a hnkli na zame na sulale kasa jikina ya dauki zafi sosai. Taci gaba da cewa shiyasa ayau abun ya daga min hnkl sosai jin kalaman da yake fada min a waya nasan zai aikata abnd yake fada. Ta kalli inna kaunar da yakewa Humaira ya zarta tunani amma ina da wata shawara guda, mu duka mu dage wajen fadawa Allah yanda ya hada wannan soyayya da yardarsa zai warware komi cikin sauki idan abun zaiyuwu yafimu sanin tsarin yanda zaiyi haka idan bazai yiwu ba. Ta dafa kafadar inna danAllah muyi hkri wata rana sai lbr. Kada muyi shisshigi na tabbata mai kudi da talaka da mai sarauta duk Allah guda suke bautawa. Kuma ba wanda yafi wani a gurin Allah sai wanda yafi tsoronsa. Zan tafi dashi don ya halarci bikin gudun faruwar wani abun zamansa anan zai iya zama wani tashin hnkln nizan bar wanda zai kula da kamar... Inna ta kalleta ISA bazamu kara kwana a nan ba yau zamu tafi gida. Da sauri ya dago kai gsky mama ba inda zanje gobe idan an kai amaryar da daddare na taho washe gari ayi budar kai amma dole in tsaya in kula da lfyrsu inna don nine musabbabin faruwar komai. Inna ta girgiza kai ko kadan bazakyi wann danyen aikin ba wllh mun yafe duniya da..... Ni inna ban yafe ba. Dakata to yanzu me kakeso ayi? Wane irin so ne mama ke masa batason bacin ransa kokari take tayi masa yanda yakeso. Ya bata fuska yace a kyaleni na zauna da inna gashi tfyta tasa zasu koma gida suma... Inna tayi murmushi na rantse da Allah ba wann ne yasa zamu tafi ba asibitin ne kawai bana son zama . Sadauki yace to ai ba'a gama dubaku ba ko inna? Tayi shiru bata tanka ba. Tace to zuwa yaushe za'a sallamemu? Ya langwabar da kai nan da kwana 4 da an kwance daurin. Ta kauda kai tace Allah ya kaimu suka amsa ameen. Mama ta mike zan bar mace 2 ta dinga kula

End of Chapter 3Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next